Showing 201001 words to 204000 words out of 273152 words

Chapter 68 - FULANI BOOK COMPLETE DOCUMENT by Khadijah Candy .txt

29 Aug 2024

72774

a kuskura a taba idonta, kuma yace akwai masu kokarin cutar da ita, komai zai same ta kar a taba ta ko a ce za a mata magani”


Jekadiya ta juyo tana kallonta kamin ta gyada kai ta dan saci kallon Iya dake tsaye bakin kofa sannan ta juya ta cigaba da tafiyarta har ta isa gurin motar ta bude ta shiga, hankali be kwanta ba sai da ta ga sun bar gidan, har ga Allah da ba umarnin Shattima ba ne babu abun da zai saka ta zuwa gidan mayya har tai mata bincike bayan kuma ita Ammy ta saka tai mata turaren nan ko dan shi kadai ya isa ya saka ta kame mata kurwa, hakan yasa tun da suka kamo hanya take ta addu'a.
Bayan sun wuce Zainab ta dawo cikin falon tana ta mamakin batan Fadime? Daman abun da Wasim yake nufi kenan da cewar za a cutar da ita? Ko kuma dai wannan batan nata ne na kanta daga baya cutarwa zata zo? Ko kuma wani abun ne dabam? Tana ta kokarin kawar da abun da zuciyarta take son raya mata akan mahaifiyarta na ganin kamar tana da hannun a batan Fadime idan ma ta bata din da gaske. Dakinta ta nufa tana kara nitsawa cikin tunanin, ko dai Wasim ne ya dauke ta? Ko kuma Iya ce tai wani abu?


“Ko dai minene ita ta sani can, ai ita ta jawa kanta”


Ta furta tana zaunawa saman gadonta, mamaki da tunanin da ya bijiro mata ya saka ta manta da zancen fitsarin da take ji, babu abun da ta hango a abun da akai musu sai cin zarafi da zubar da mutunci wanda take ganin Iya ce ta haifar da komai, domin da ada ne ko wani ne ya ce zai yi musu haka hanawa zai yi saboda yana ganin kimarta da kuma ta Iya sosai, amman a yanzu Iya ta barar musu da komai.
Ba ta yi waya daya da kwantawa ba ta sake jin an bude gate din, saurin tashi tai ta leka window sai ta sake hango motar dazun, daman ta san indai ba daga Masarauta ba ne babu yadda za ayi mai gadinta ya bude gate a irin wannan lokacin. Kamar dazun haka ta sake fitowa ta bude kofar falon da kanta sai dai wannan karon tsoro ya cika mata zuciya, sama da dazun da mamaki ne kawai da tunanin dalilin zuwan.


“Shattima yace mu ta ho da ke?”


“Ni..?”


Ta nuna kanta.


“Akwai wanda take tsaye a gaba ne bayan ke?”


Jekadiya ta amsa mata ta sigar da ba ta yi zato ba, daman can basa jutuwa ita da jekafiya saboda tana da dagawa da ji da kai wanda 80% din mutanen gidan suka tsaneta da shi musamman wadanda suka san asalinta. Bata ce komai ba ta juya ta koma ciki, Wardrobe dinta ta bude ta dauko after dress dinta ta dora kan rigar bachi, bata damu da saka mayafi ba daman can rufe jiki ba al'adarta ba ce, tana daf da isa kofar falon gurin da Jekadiya take tsaye Iya ta bude dakinta ta fito.


“Lafiya ina zaki je?”


Jeakdiya ta fara karanto addu'a tana dan kawar da kai wai dan kar ta ga kurwarta.


“Shattima ne yake nema”


Zainab ta amsa mata kamar bata son magana, ba dan tana a halin da bata isa tai fada da kowa ba da sai ta fadawa Jekadiya maganar da har ta mutu ba zata manta da ita ba. Wannan karon Jekadiya ta riga fita sannan Zainab ta biyo baya, mota daya suka shiga, zuciyar Jekadiya na raya mata wata kila ita ma Zainab din tana yi, take ta cigaba da addu'a babu kakkautawa. Har suka isa masarauta ba ta kalli gefen da Zainab take zaune ba kuma ba ta fasa addu'a ba.




SHATTIMA POV.


“Amman ka aika gurin mahaifinta a sanar masa halin da ake ciki ba sai gobe ba yana tunanin tafiya da ita”


Ya mike tsaye.


“Da kaina ya kamata na yi magana da shi...”


Ammy ta kalleshi da mamaki.


“Da kanka...?”


“Yes Ammy ba ki san yadda na ke jin yarinyar nan ba”


Ya fada kamar ya manta cewar a gaban Ammy yake, a karo na biyu ta sake masa irin kallon dazun, sai ta dauke kai yana jin kamar be fadi daidai ba.


“Ammy ba ki irin sadaukarwar da tai mana ba? Ko tantama bana yi saboda mu ta bata idan ma ta bata din da gaske”


Ammy bata sake ce masa komai ba bayan kallonsa da take, shi kuma ya juya ya fice daga dakin, kamar yadda ya fada da kansa ya isa bangaren da akai wa su Bappa masauki, tun kan ya isa hadiman gidan kd faduwa kasa suna kwasar gaisuwa sai dai be kula ba har ya isa. Wani hadimin ya saka ya sallamo masa Bappa da kawu suka fito, su ma masa suka fadi suna kwasar gaisuwa kwarjinin Shattima ya cika musu ido sosai. Hannu ya daga musu alamar su tashi tsaye ko wannensu ya ki suka maida kai kasa ko kallon inda Shattima yake basa iya yi.


“Am... Daman tafiyar da na ce za ku yi gobe...”


Sai kuma yai shiru kamar mai nazari ko fargabar abun da zai fada.


“Ina tunanin za a daga ta har zuwa wani lokaci.. Saboda Fateema mun nemeta a cikin gidan ba mu ganta ba sai dai a gama bincike ba...”


Wani irin abu ne ya soki kahon zuciyar Bappa, sai ya ji abun kamar almara, ya san ko a kamanni da sura Shattima ba zai iya shimfida muau irin wannan karyar ba dan kawai ya fadar musu da gaba ko ya tsorata su ba, balle kuma ga sarautar da ta isar ta sanar da ko wane talakawa cewar dan sarauta da sarki basa karya musamman wandanda suke jigo a sarautar, sai dai abun da Bappa be fahimta ba shi ne cewar Fadime ta bata, ta bata ta fita zuwa wani guri ko kuma ta bi wani ko sace ta akai? Ko kuma Shattima ne ya canja shawarar tafiyar? Lokaci daya Bappa ya jero ma kansa wadannan tambayoyin da ba shi da amsar su, gashi kuma yana jin be isa ya daga ido ya kalli Shattima ba balle har ya sake yi masa wata tambayar.


“Ku kwantar da hankalinku za a ganta Inshallah”


“To to ranka ya dade mun gode”


Kawu ya fada, Bappa kam be iya cewa komai ba har Shattima ya bar gurin Bappa be iya tashi daga duken da yake ba, gaba daya sai ya ji kamar ba shi da lakka, dan kuzarin da zai saka ya mike tsaye sai ya neme shi ya rasa.


“Ka gani ba, wannan Fadime ban san wani irin hali take son saka mu ba, yanzu kuma wa ta bi ga gudu? Ko kuma shi din ya sake sace ta? Ni Wallahi da Shi Mai Martaba zai yarda da ya bar mu mun tafi gida gurin harkokinmu”


Cewar Kawu dan Iroro cikin fusata da bacin rai. Bappa ya numfasa ya yunkura daker yana ambaton Allah tare da kokarin mikewa tsaye, sai ya ji kirjinsa ya rike kamar an soka masa mashi. Komawa yai ya duka yana jin wani irin zafi a kirjinsa da be taba ziyartarsa ba, duk abubuwan da Fadime take be taba bata masa rai matuka irin wannan ba, gashi sanin gaskiyarta sai Allah, zuciyarsa na ta raya masa cewar saboda yace ba zata auri Wasim din ba me yasa ta gudu ko kuma ta hada baki da shi Wasim ya sake dauketa.


“Wallahi yarinyar nan tana jefa mu cikin matsala, da na san abun da zai faru kenan da ban zo garin nan ba, yanzu wani garin zata sake jefa mu kenan”


“Daga nan ba za mu sake zuwa ko'ina neman Fulani ba, na san ita kadai ta rage min, amman na yafe ta kawu, idan ta dawo zan karbe ta idan kuma bata dawo ba ba zan sake nemanta ba, wani nawa kuma ba zai neme ta ba, Allah ya ba mu dangana”


Bappa ya fada cikin wani irin bakinciki marar misaltuwa, numfashinsa har wani taushewa yake saboda nauyin da zuciyarsa tai, sake yunkurawa tai ya mike tsaye sai ya kasa, gaba daya abubuwan da Fadime take masa na bacin rai sai suka taru suka masa tsaye lokaci daya. Kawu ya dafa shi.


“Lafiya dai?”


“Kawo ka fita ka samu wanda zai yi magana da shi Mai Martaban a fada masa muna son mu kama hanyar tafiya gobe Inshallahu”


“Idan mu ka yi haka ai sai yace ba mu ji maganarsa ba, mu dai hakuri mu ga abun da Allah zai yi”


“Ba zan fasa tafiya saboda Fulani ba, komai take so taje tai, kuma komai take ganin yinsa daidai a rayuwarta na bata dama”


A karo na uku Bappa ya sake yunkura sai yai nasarar mikewa tsaye, sai dai ko kadan zuciyarsa bata barshi ya samu sukunin yin numfashin kamar yadda ya saba ba. Hanyar da ya ga Shattima ya bi ya fara bi yana jin kamar baya iya cira kafarsa sosai, Kawu yayi saurin rikosa.


“Aa Jauro, karka ce zaka musa masa akan maganarsa, mu hakura kawai har sai yadda hali yai”


Bappa ya saka hannunsa ya cire hannun Kawu dake rike da rigarsa.


“Aa Kawu ka bar ni magana kawai zan yi da shi, idan be yarda ba sai mu hakura”


Kawu ya ja da baya yana jin mugun tsoro kamar shi ne zai tunkari Shattima da maganar. Bappa kuma ya cigaba da tafiya ba dan yana da tabbacin zai gadu da Shattima ba kuma ba dan yana da tabbacin zai hadu da wanda zai sadashi da Shattima ba. Duk wani tsoro da fargabar tunkarar masu sarauta da yake sai ya cire shi ya aje gefe saboda ransa yayi mugun baci, duk karfin halinsa da dakiyar zuciya irin nasa sak da hawaye suka cika masa ido. Kamin ya fito harabar da suke har jin yake kamar baya iya numfashi, babu abunda yake tunanin sai abubuwan da Fadime take tun tana karama har girmanta har kawowa yau da ya kamata ace ta yi hankali ta natsu, domin zuciyarsa ta fi raya masa cewar da saninta komai ya faru, idan ma bata sanin ba ai duk laifinta ne da ace tana jin magana tun farko da yanzu komai be faru ba. Can kusa da Bangaren Ammy Bappa ya hango Shattima tsaye ya maida hannayensa baya, tare da wasu mutane hudu sun zube a gabansa, a kokarin Bappa na cira kafa ta isa gurin da Shattima yake tsaye sai ya ji shi a kasa, daman tafiyar kawai yake yana jin kamar kafafuwansa basa iya daukarsa. Faduwar da yai ne ya saka mutanen da suke gaban Shattima juyawa su kalli inda yake ban da Shattma da kasaita ta hana shi, sai dai kana kallonsa ka san ransa a bace yake. Bappa ya tattara dukan karfinsa da kuzarinsa ya yunkura ta tashi ta isa gaban Shattima sai dai ya tsaya nesa da shi ya zube kasa. Shattima na ganin haka ya dagawa mutanen da suke gabansa hannu sai suka tashi da sauri suka bar gurin suna masa godiya. Takawa Shattima yai ya isa gaban Bappa da ya daga masa hannu alamar girmamawa.


“Tashi mana Baba”


“Aa ba zan tashi ba, alfarma dai na zo nema idan zaka amince mana”


“Ina jinka”


Shattima ya fada yana gyara tsayuwarsa wanda hakan ya ba wa talkamin sarautar da suke kafarsa motsawa.


“Dan Allah ranka ya dade kai mana alfarmar tafiya gobe, saboda akwai abubuwan yi a gaban mu, musamman ma Kawu, ni kaina na baro mahaifitarta da sana'a a can hankali ba kwance ba”


Fahimta daya Shattima yai ma maganar Bappa wanda kuma ita ce gaskiya, yanayin fuskarsa da yanayin yadda ya ke furta kalaman cikin dannewar numfashi kadai ya isa ya saka Shattima fahimtar cewa Bappa fushi yai kuma ransa ya bace a kan hakan.


“Idan kuna ra'ayin zuwa ba zan hana ku ba, kuma ba zan ga laifin ku ba, idan kuma kuka tsaya zan yi maraba ku na san cewa ka damu da yarka”


“Ranka ya dade, ban so musa maka ba kuma ban isa na ki bin umarninka ba, amman tabbas yarinyar ta wuce inda kake tunani”


Shattima ya dauke kai yana jin dacin maganar Bappa akan Fadime, ko kadan baya son ya ji a fadi laifinta musamman a yanzu da be an halin da take ciki ba.


“Shikenan za'a sanar da direba sai ku shirya da wuri”


“Allah yasa dai ban bata maka rai ba, a gafarce ni idan na bata maka rai dan Allah, tuba na ke tuba na ke”


Bappa ya fada, Shattima dai be ce komai ba sai dai shirun da yai ya isa ya karantar da Bappa cewar ransa ya bace. Bappa ya mike tsaye yana cire talkaminsa ya juya ya baro gurin yana jin wani irin ciwon kirji da be taba jin irinsa ba, numfashim ma idan ya fita sai yayi da gaske sannan yake dawo masa. Shattima ya bishi da kallo yana mamaki wane uba ne irin wannan da za a cewa yarsa ta bata har ya zabi tafiya ya barta ba tare da ya tsaya bincikar inda take ba.
Yana tsaye gurin motar su Jekadiya ta iso, tun da suka hangoshi tsaye yasa suka kashe fitilar motar gudun kar su haska shi, nesa da shi suka aje motar suka fito Jekadiya na gaba suna binta a baya har suka iso gaban Shattima, ta risina kasa tana fada masa cewar sun bincika ko'ina ba su ga yarinyar ba.


“Amman Hajiya Karama ta ce a sanar maka, wai wani Wasim ya ce a fada maka kar a taba idonta kuma wai akwai masu son cutar da ita komai ya fara kar a ace za a bata magani ko ayi mata wani abu”


Shattima ya kurawa Jekadiya ido yana mata kallon fahimta.


“Waya fada miki wannan?”


“Hajiya Karama”


“Je ku ta ho min da ita”


Ya fada kai tsaye sai ta mike da sauri tana fadin.


“An gama ranka ya dade”


Kansa ya daga sama yana kallon bangaren Hajiya Babba a zahiri bangaren yake kallo sai dai hankalinsa yana can ya tafi wani gurin, mamakin abun da Jekadiya ta fada masa yake, sam zuciyarsa bata yarda da abun da Zainab ta fada ba, maybe tana da hannu a bacewanta ne saboda ta tona asirin mahaifiyarta, ya san yadda Zainab take da zafin zuciya da kuma rike abu a zuci zata iya yin komai akan Fadime, tun da har ta fadi wannan hakan na nufin ta san wani abu kai kenan. Sai a yanzu zuciyarsa ke raya masa cewar akwai abun da ya saka suka son kar a taba idon Fadime din ita da Wasim wata kila saboda kar ta warke ne. Ji yai ba zai iya barin gurin ba har sai an iso da Zainab, a dan yana kokarin hana zuciyarsa tsanar Iya balle Zainab amman a yau yana jin har Zainab din ya tsana balle kuma iya, a tunaninsa Zainab ta san komai akan abun da Iya take aikatawa amman bata fadawa kowa ba, ta bar mahaufiyarta tana aikata abubuwan da ba su dace ba, ciki har da cutar da shi da yayansa.
Ko kadan be ji ya gundura da tsayuwar ba balle har ya nemi gurin zama, yana tsaye sai safa da marwa yake yana tuna wasu abubuwan da su kai ta faruwa da shi, sai a yanzu ya gane hikimar Ammy na korar Iya a gidan tare da Zainab saboda ta talaka mata auren Zainab din, a yanzu kam jin yake da sanin Zainab Iya tai masa tayin auren saboda ta auri yarta.
Kamar dazun a yanzu ma nesa da shi suka aje motar Jekadiya ta saka Zainab dake sanye da rigar bachi ta dora bakar riga sama, ita kanta yadda ta hango fuskar Shattima sai da gabanta ya fadi, tana ta tunanin dalilin kiran duk da ta san ba zai wuce akan Fadine ba, sai dai bata ga ta inda ta hada da batan Fadime ba bayan ita bata masarautar.
Gabansa ta karasa ta dan risina masa tana gaishe shi.


“Me kika ce a fada min?”


Ta maimaita irin abun da Wasim ya fada mata.


“Hakan na nufin kin san wani abun akan batanta kenan?”


“Aa ban san komai ba”


“Ban gadi daidai ba kenan?”


“Aa ban ce haka ba, ka gafarce ni amman baka fahimce ba, bana ni hannun a batan ta kuma ban san komai ba ka yarda da ni?”


Shattima ya kura mata ido yana mata wani kalar kallo da be taba mata irinsa ba, gaba daya sai ya ji tsanarta ta cika masa zuciya.


“Ta ya zan yarda da ke? Kina da wani abu ne da zai saka na yarda da ke? Na san ki za ki iya yin komai dan ki cutar da yarinyar nan saboda ta tona muku asiri”


Sakaka Zainab tai tana kallonsa, wani kalar muzanci da na kusantantar ta.


“Ko dai ki nemo inda wannan yaron yake ya kawo Fatima ko kuma ke ki fadi inda take ko kuma a tafi da ke gidan horo yanzu nan”


Zainab ta kasa cewa komai sai hawaye take.


“Jekadiya”


Jekadiya ta matso da sauri tana kara daga masa hannu.


“Ranka ya dade”


“A fadawa Alkali ya akai ta gidan horo”


“An gama ranka ya dade”


Jekadiya ta fada tana mikewa tsaye.


Zainab ta nuna kanta, hawaye na sauko mata.


“Ni... Shattima?”


Wani kallo ya watsa mata daga sama zuwa masa.


“Ke din wacece?”


Da sauri ta rufe ido tana jin kamar ya soketa da mashi.


“Saboda an bude miki hannu an miki gata an miki maraba har ya saka kike jin cewar ke din wata ce a masarautar nan? Wani ya fada miki magana yace ki fada min ba ki ji za ki iya fada ba har sai da aka aika neman yarinyar? Na saka a miki hukunci ki nuna kanki kina tambaya ta wai ke?”


“Tuba take ranka ya dade a yafe mata ta tuba”


Jekadiya ta fada, Zainab kuma ta hade wasu kalar yawu masu daci da suka tsaya mata a makoshi. Shattima ya juya a fusace ya nufi hanyar da zata sada shi da kofar fadar Ammy ta waje. Jekadiya kuma ta saka Zainab gaba zuwa wani bangare na gidan, Zainab na tafe hawaye na sauko mata.




FADIME POV.


Ataa bata taba ta ba har Aliyu ya dawo, yana ganinta zaune a falon ya san ba lafiya ba.


“Are you okay”


Ta daga masa kai tana labarta masa abun da ya faru. Karasa yai kusa da Fadime ya duka yana kallonta kuka take sosai tana kallon silin


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login