Showing 192001 words to 195000 words out of 273152 words

Chapter 65 - FULANI BOOK COMPLETE DOCUMENT by Khadijah Candy .txt

29 Aug 2024

72758

duk wani shirye shirye da ya kamata na fara shi, kuma yau zan yi magana da mahaifiyarta Inshallah”


Shattima yayi shiru yana saurari kamin ya dago kai da zimmar yin magana sai Ammy ta hana shi da ido, hakan yasa shi yin shiru har sai da Baba Waziri yai ma Ammy sallama ya fita, sannna Ammy ta kalli Shattima cikin damuwa ta ce.


“Abun da kake be kamata ba, na san ba lallai ne ace kana son Maijidda ba, amman ko dan darajar Waziri da irin yadda yake maka tsaye a komai ya kamata ace ka amince, idan tsoro a ranka ka cireshi, indai har da gaske iya ce take cinye maka mata, zan tabbatar kuma zan yi magana da Hajiya Talatu da kaina”


“Ki yi magana da ita kuma? To ai za ki jefa rayuwar Fadime ne a hadari, aa gaskiya kar a cutar da ita, tana fama da makanta a kara mata wani”


“Sai na fada maka zuwa zan yi na fada mata cewar wata ce ta zo ta fada min? Kamar baka san wacece ni ba? Kowa ya ji haka a ba zai dauki abun da gaske ba”


“No Ammy bana son yarinyar ta shiga matsala, karki yi magana da Hajiya Talatu, ni nasan abun da zan yi”


Yana fadar hakan ya tashi cikin rashin jindadi, ya fice daga daki. Ammy da bishi da kallo har ya fice sannan ta dauki wayarta ta kira jekadiya.


“Ki shigo ina nemanki”


Ta aje wayar ba tare da ta jira abun da Jekadiyar zata fada ba. Cikin yan dakiku Jekadiya ta shigo dakin da saurin ta bayan ta yi knocking Ammy ta mata izinin shiga.


“Ranki ya dade gani”


“Jekadiya ina son ki samo min hantiti, da tsakin kuka, sai bushenshen kashi, ki hade su guri daya, idan an samu ki fada min, sai na aika kiran Iya, idan zata shigo nake son ki turara shi a falo”


“To ranki ya dade za a nemo da yarda Allah”


Ammy ta dauko 3k ta mika mata, duk da ta san hantitin ne kawai abun da zta nemo domin tsakin kuka bushesshe da ƙashi ba abu ne mai wahalar samu ba.






SIRLEEM POV.


Shi ya fara shiga yai alwala ya fito sannan ya rika hannunta ya shiga ta ita bandakin, kusan rabin alwalar duk shi yai mata sannan ya sakota gaba suka fito da kansa ya shimfida katuwar carpet ya shiga gaba ita kuma ta tsaya daga baya tana yafe da mayafin da aka kawo ta da shi ta kabbarta tana binsa a baya, raka'a biyu yai ya sallame sannnan ya dora da addu'a kana ya juyo ya kama kanta ya karanta addu'a, sai ya ji wani irin natsuwa da nishadi yana sauko masa, duk da kasancewar yana a halin da shi kansa ya san ba son Falmata yake ba, sai dai yana tausayinta kuma kuma yana jin idan har ya aurenta yayi dacen mace mai hakuri da tarbiya kuma zai taimaki rayuwarta.


Sai ya ji wani girma da dattijanta ta kama shi, look at him wai shi ne mai aure a yanzu kuma matarsa ce a gabansa abu kamar a mafarki. Naman da ya siyo ya dauko ya aje gabanta ya fara cira yana kai mata a karamin bakinta, sai ta kasa karba saboda kunya da nauyinsa da ya kamata, tashi yai ya koma kusa da ita ya zauna ya jata kusa da shi sosai ya kwantar da kanta a kirjinsa, sannan ya kai mata naman a baki, a hankali take taunawa tana jin wani irin kunyarsa ya cika mata ido, bata wani ci da yawa ba tace masa ta koshi, sai ya zuba lemun ya bata ta sha shi ma kadan, sannan ya hada komai ya maida gefe.


“Teema...”


“Na'am”


Ta amsa ba tare da ta kalleshi ba, hannunsa ya kai ya kama hannunta ya soma mata magana a natse.


“Na san kin saba da kalubalen rayuwa, kin saba shiga abubuwa kala kala, ina son ki san rayuwar yanzu da kika shiga da ta baya ba daya ba ne, ada can ke budurwa ce yanzu kuma matar aure, matar auren ma matar Sirleem, mutumen da ya aureki a boye, na fada miki wannan ne saboda kin san cewa akwai kalubale a gareki nan gaba, ban ce zaki shiga wani tasku na rayuwa ba, amman na san kamin ki sha da dadi a gurin Hajiya zai kin fara karbar azaba, so ina son ki daure saboda mahaifiyata ce, ni kaina a yanzu ta hana yin waka, ba abu ne mai sauki a gareni ba, amman a haka na tattara komai na aje, saboda na bi umarninta, na san idan ta sani ranta zai bace sosai, shiya saka ko dangin mahaifina ban labartawa ko wa ba, domin na san maganar zata koma a kunnenta, saboda akwai shakuwa da fahimtar juna a tsakaninsu dole za a samu wanda zai labarta mata, ba daga Hajiya kadai ba har dangin mahaifina na san ba lallai ne su karbe ki da wuri ba, kuma ba lallai ne su nuna miki so kamar sauran matan yan'uwa ba, saboda banbanci matsayi da kuma yanayin yadda na auro ki, ina son ki saka a zuciyarki cewar kina da kima da daraja mai yawa a gurin mijinki, kuma duk wani abu da zai bata miki rai zan yi kokarin kiyayewa domin a yanzu farinciki kike bukata, ina son na fada miki wani abu wanda be zama lallai yai miki dadi ba, idan har Hajiya ta cilasta cewar sai na auri Nana ko wata, ba zan bijirewa umarninta ba, sai dai hakan ba yana nufin na wulakanta ki ba...”


Yana soma fadar hakan sai jikin Falmata yai sanyi, tabbas ta baro wata wahalar zata fuskanci wata, ta san a yadda take ba kowa ba idan Hajiya ta ji ya aureta sai ta sha wahala da wulakancin a duk familynsa, bayan ta laka mata sata a lokacin da babu hadin komai a tsakaninsu balle yanzu da danta ya aureta, a take ta nemi farincikin auren Sirleem din ta rasa, zuciyarta na raya mata kara wacan da wahalar da wannan da zata fuskanta.


“Ba ina fada miki wannan ba ne saboda hankalinki ya tashi, ina tunatar da ke ne abun da ke gaba wanda be zama lallai ya zo kusa ba, wata kila sai nan da shekaru”


Ya fada yana murza tsiraran yatsun hannunta a hankali yana kallon fuskarta.


“Karki min kuka fa come here”


Ya kara janta jikinsa ya kwantar yana shafa kanta zuwa wuyanta.


“Ko da wasa wata ta tambaye ki waye mijinki karki fada mata”


Ta gyada kai, sai ya sumbanci kanta.


“Good girl”


Ya rada mata saitin kunne sannan ya tsotsa kunnen kadan, wani irin yarrrrr ta ji har cikin kanta tsigar jikinta ta tashi. Sai yai murmushi jin yadda take rike hannunsa da yake kokarin saka mata yatsan a baki, hakan ya bashi damar kama lips dinta yana wasa da shi, dayan hannunsa kuma rike da hannunta sai murza yatsunta yake.


“Fada min yanzu idan step mother din ki ta ji cewar ni kika aura za ta yi?”


“Ba zata jidadi ba, domin bata son na samu cigaba ko kadan”


“Hmmm”


Ya fada yana zira yatsansa ta cikin rigarta ta sama, tana jin haka sai komai nata ya tsaya cak ciki har da numfashinta. A hankali yana kara zira hannun yana goge mata fuskarsa a kanta, sannan ya saka dayan hannunsa ya sauke zip din rigarta, saurin barin jikinsa tai jikinta na ta rawa, na rawa na tsoro ba rawa irin na bakom al'amari ya ziyarce ka.


“Zan ...zan kwanta”


Daker ya daga ido ya kalleta da idonsa dake ta lumshi har wani ruwa ya fara taruwa ciki.


“Yeah ni ma bachin nake ji ai”


Ya mike tsaye ya kama hannunta.


“Zo mu wanke baki sai mu kwanta”


Kamin tace komai yaja hannunta zuwa bathroom din, sai da ya fara wanke mata nata bakin da brush sannan ya wanke na shi suka fito. Sakin hannunta yai ya cire rigar shaddar dake jikinsa, sai tai saurin yin kasa da kanta tana jin wani irin kunya ya kamata gabanta ya shiga faduwa da karfi, murmushi yai.


“Ni bana bachi da riga, komai sanyi sai dai na lullube”


Ita dai bata ce komai ba kanta na kasa, gaba daya kwarjinsa ya kara kamata, yadda ya cire rigar nan sai ta ji ya mata girma sosai kamar ba shi ba. Ya nufi wardobe ya bude ya dauko kamin wando.


“Juya karko fara tsorona kuma”


Ta juya da sauri kamar daman abun da take jira kenan, sai yai murmushi ya cire wandon shaddar ya saka boxer sannan ya dauko wani karamin boxer na maza da vest dinsa ya nufo inda take.


“Saka wannan, gobe zan siyo miki na ki kayan bachin”


Ta juyo sai kuma tai saurin rufe ido ganin har lokacin babu riga a jikinsa, zuwa yai ya kashe wutan dakin ya dawo kusa da ita ta fara cire mata rigar da kansa, amaimakon ya saka mata wata sai ya tsayar da hannayensa a kirjinta yana aikin da ya dade yana jiran zuwan ranar shi, jin abun da yafi karfin kwakwaltar yasa ta fara kokarin zame jikinta.


“Sirleem”


“Shiiiiiiii”


Ya dauke ta cak ya kwantar saman gadon sannan shi ma ya hau ya daga ta ya kwantar a kirjinsa ya lumshe ido yana jin yadda kirjinta ke taba na shi, a hankali yake maida numfashi yana shafa bayanta.


“Ban saka rigar ba”


Ta fada tana jin kamar ta fashe da kuka, abun ka da wanda be saba ba, sai wani abu take jin na rashin dadi da kuma kunya.


“Ki fara koyon bachi babu riga daga yau, wannan al'adata ce”


Ya fada cikin rada sannan ya mirginota ya kwantar ya rage tsayensa ta hanyar yin kasa ita kuma tai sama, sai ya dora kansa a kirjinta ya lumshe ido.


“Hmmmmm i miss alot”


Ya fada cikin rada kamin ya kai hannunsa gurin Skirt dinta... Ganin d gaske yake yasa ta fara kokarin tashi da sauri tana jin kuka na rashin dalili yana zo mata.


“Tsaya ka ji”


“Babu abun da zan ji, bana jin komai a yanzu, na dade ina jiran zuwan wannan ranar, na y iya kokarina wajen hana kaina haram, yanzu kuma na samu halal sai na hana kaina? No way”


Ya fada yana kai bakinsa ajikinta, light kiss yake aika mata hannayensa duka biyu suna mika mata sakonsa, akwai tsoro sosai a tare da ita na sakon da jikinta ya kasa dauka balle ya sakewa kwakwalwarta, sai dai ta samu natsuwa sosai a lokacin da yatsunta da na shi suke tarayya...






Ya so ya saurareta, sai dai ko kadan zuciyarsa bata kusanto masa ta tausayinta ba ta wannan fannin, ko da wasa zuciyarsa bata raya masa yayi kusa ba, kamar yadda yake ganin safiyar ta yi masa saurin wayewa, a lokacin ne ya tabbatar lallai shi ango ne, kuma ya dade da barin abun da ya kamata ace ya san muhimmanci tun da dadewa, ita kanta Falmata ta san ba karamin jihadi tai ba na barin jikinta ya karbi bakon lamari da be taba ba, ta yi kuka sai dai kuka tai irin na masu hakuri da danne cuta a zuci, bata bar ihunta ya fito ya cika dakinta ba, babu abun da take ambato sai Allah zuci da baki. A daren ranar Falmata ta san me ake kira da aure, ta gane banbanci ta da da, ba kasanta kadai ba ko kirjinta da be gama nina ba ciwo yake mata sosai. Idonta biyu har akai sallah asuba tana jin lokacin da ya shiga bandakin yai wanka ya fito ya kabbarta sallah asuba, bayan ya gama sallah ya nufo inda take ya kai hannunsa ya shafa fuskarta. A zatonsa bachi take domin idonta a lumshe suke, bakinsa ya kai ya sumbanci goshinta yana jin kamar yaja bukatar kari, sai da ya san ba zata iya ba, shi kansa ya sha wahala kamin Falmata ta maida shi cikakakken namiji.










HAJIYA BABBA POV.


Suna zaune a gidan Hajiya Tatula har kusan magariba, sannan matar ta iso tare da bokanyar a cikin motar kasuwa. Kofar Kicin Hajiya Talatu ta bude musu suka shigo sannan ta shigar da su wani dakin da bata cika amfani da shi ba, kana ta shigo dakinta ta sanarwa Hajiya Talatu da Jurry isowar matar.


Kamin Hajiya Babba tai wani yunkuri Jurry har ta kai tsaye domin hankalinta a mugun tashe yake, ko da Hajiya ta isa dakin ta samu Jurry da Hajiya Talatu a zaune gaban matar sua gaisawa, kallo daya zaka mata ka san akwai manyan kuma gawurtattun aljanu a kanta. Idonta a tsaye yake ga tufafin jikinta ma ba irin na mata ba ne, wando da riga ne na maza sai hijabin da ta dora akai, tana tare da wata katuwar jaka a gafe sai warin turaren aljanu take.
Hajiya da kanta ta mika mata gaisuwa, ta amsa tana wani gyatsa kamar wanda ta sha lemu mai gas.


“Baiwar Allah, ina cikin matsala....”


Tun daga a har za sai da Hajiya Babba ta labarta mata komai na zuwan da sukai garin su Wasim da abubuwan da aka fada musu da kuma abubuwan da suke gani.


“Kudi ake ba ni ko naira biyar ce a miko min sai na dubo muku abun da kenan”


Hajiya Talatu ta tashi da sauri taje ta dauko dari biyu ta mika mata, sai ta karba tana gyatsa, ta bude jakarta ta dauko kwalbar turare ta madara ta kurba kadan ta shafa kadan a kudin ta mursa a hannunta sannan ta dauko goro ta tauna ta cire hijabin da ke jikinta, ta dauko wani abu mai kamar duba da wasu yan duwatsu a ciki tana kadawa.


“Gaishe dai nake Inna kirarinki nake, inna mai uwa da da, inna mai cin uwa ta ci danta, jini na ki dan mutum na ki, idan kin ga dama ki cinye kafar yaro ko hannunsa, doguwa matar kure, jini na ki tsoka ta bayinki, inna gwarzuwa kowa yayi kira sai ya ganki...”


(Irin wannan aljanar ita wasu suke kira da Inna, wasu kuma su ce mata doguwa, wasu kuma su ce mata uwa, idan ana son kashe mutum ko yi masa wani mummunnan aiki ita ake kira, wasu mutanen ma da ita suke maita, ko kadan bata da tausayi ba bata da imani, idan tana tare da uwar yaro zata shanye kafarsa ko hannunsa ko ta juya kwakwalwarsa haka take yi ma yaran mace idan tana tare da uwar, kuma jini take sha, ko da wasa kai mata kirari ka kirata sai ta zo sai dai be zama lallai ka ganta ba, Allah ya tsare mu)


Bata gama kirarin ba jikinta ya fara rawa, ta fara gyatsa fiye da ta dazun, sai lausayar da kai take can kuma yawu ya fara mata zuba, muryarta ta canja.


“Ga ni ma iso, mai shiga kogo in hau tsani, in ci sha jinin mutum in bar tsaka, ga uwa mai ciwa ta ci danta, kashe ta kuke son ayi?”


Hajiya Talatu da Hajiya Babba sun kalli juna, sai jurry ta girgiza kai.


“Aa a dai mata wani abun dabam, ba kisa ba”


Ta furzar da goron da ke bakinta.


“Idan ba a kisa ba a rike hannu ko kafa, idan ba jini za a sha ba, ku bar kiran Inna Inna mai hadari ce, wannan aikin sai duna bakin iska...”


Gaba daya tsoro ne ya kama su, jurry ta ja baya. Cikin dakiya Hajiya Babba ta ce.


“Ina zamu ga duna?”


“Yanzu zan turo muku shi”


Ya fara wani rangaji tana birkice ido, sosai jikin matar yai tsami saboda fitar inna. Fita tai daga jikin matar sannan bokanyar ta farka ta dauko wani turare binta sudan tare da danduwala ta hada guri daya ta murza a hannunta tashaka, take muryata a sauka jikinta ya amsa kiran Duna wanda wasu suke ki kira da junnul ashiq, duna gawurtaccen aljanine ga sauri da karfi ta keta, ba ko wane aljani ke iya karawa da shi ba, hakan yasa idan ya shiga jikin mace kamin ayi mata maganinsa sai ta sha wahala sosai, ayoyi ne kadai abun da ke nisantar da shi daga jikin dan'adam, idan kuma akai aiki da shi yana da wahala mutum yayi saurin warwarewa sai an kira shi an bashi kwatankwacin abun da wadancan mutanen na farko suka ba shi sannan ya rabu da mutum, aikinsa kuma sha yanzu ne magani yanzu matukar an bashi abun da yake so, sai dai komai karfin aljani yana tsoron bakara da ayatul kursiyo, matukar mutum na karanta su basa kusantarsa idan ma suna tare da shi za su nisanci mutum indai har an dage, domin idan aka karanta baqara har kashe a gida sai gidan yayi wata daya aljani ko wani abun cutarwa be kusanci gidan ba, amman sai idan ba a shan waka ko wani abun da baya haduwa da kur'ane.


Sai da yai ma kansa kirari yai gyatsa yana kankance ido fuska babu annuri sannan yace.


“Za ku siye kwaryar zuma, ku siye bakaken zakaru guda ba bakwai, sannan ku siye bakin sa, kuma ku samo dutsen tsakar hanya”


“Ina zamu iya neman wannan abun, idan aka ga muna nema, ai sai asiri ya tonu ace wani abun muke shirin yi, ina laifin mu bada kudi a nemo idan zai yiyu”


Cewar Hajiya Talatu ta sigar roko, ya daga idonsa kadan ya kalleta.


“Zaku biya dubu dari uku har kudin aiki”


“Ba matsala, ni dai a ayi aiki kar asirinmu ya tonu”


Hajiya Babba ta dora da nata sai ya maida dubansa gurinta.


“An gama, gobe gobe aiki na babbatuwa in dai kun biya kudi”


“Yanzu nan zan saka aje a ciro kudi a bata da yardar Allah mun gode”


Ya rufe ido yana wani fisgar jiki, sai ta fadi kasa kwance baki na fitar da kumfa. After like 5 min ta bude ido ta tashi zaune.


“Sannu”


Duk suka ce mata sai ta amsa tana yamutsa fuska tana gyara. Jurry ta mike tsaye.


“Bari na je na ciro kudin na kawo”


Kamin hajiya ta amsa ta ta nufi kofar ta bude ta fita da sauri, sai da ta kawo kudin sannan matar ta tafi, Hajiya da Jurry kam ba su bar gidan ba sai da aka kira sallah isha'i.




TUMBA POV.


A daren ranar kasa bachi tai, tunani kala kala ya zo mata a rai, tsohon ne da gaske ko kuma wani ne yai siffar tsofin? Idan na tsohon ne indai har arzikinsa yayi yawa be kamata Falmata ta aure shi ba, Naja ta dace da shi duk da kasancewarsa tsoho. Abun ta tarar da kuma abun da


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login