Showing 171001 words to 174000 words out of 273152 words
Chapter 58 - FULANI BOOK COMPLETE DOCUMENT by Khadijah Candy .txt
tana jin wani irin bakinciki a ranta. Ji tai ba zata iya tafiya ba tare da ta tabbarta Fadime tana cikin gidan ba, juyawa tai ta koma ciki sai da wannan karon ta gurin dawakai ta nufa, domin tana da tabbacin a can ne kadai zata yi abun da take so ta gama ba tare da an ganta, domin ta saba shiga gurin. Sai da ta gaisa da mai kula da dawakan sannan ta shiga ciki tana fadin.
“Wai dokin Babban mutum zan duba, na san yayi kewata kwana biyu”
Shiga tai can kurya har ta wuce dokin Shattima ta karasa can ciki sannan ya duke kasa gurin dawakan, ta fara karanta wasu abubuwan tana tsutsar halshe, jikinta na tsama sai kafafuwanta suka fara nadewa guri daya suna yin shatin jikin kadangare irin ogan nan (Kiski a hausar ta Sokoto da Gusau) idanuwanta suka fara rikidewa ko'ina a jikinta ya dauki dumi tana ta fisga a hankali, sai da kafafuwanta suka fara zama siffar kiskin sannan jikinta ya soma dauka idanuwanta suka fara rikidewa suna kara ja daman can jajaye ne irin na mayu, har ta fara kankancewa sai kuma ta koma daidai.
“Oh Oh”
Ta furta tana aje numfashi da karfi kamar wanda tai gudun fanfalaki. Tana ganin hakan ta san ba zata iya rikada a yanzu ba, domin rabon da ta rikida ta zama wani abu tun kamin cikin Zainab, idan har tana son ta koma tana rikida kamar da sai ta sha garin maganinsu da suke amfani da shi suna sha duk shekara wasu kuma duk sati wasu duk wata wasu kuma kullum ne, ya danganta da kalar maitar da ka dauka da kuma irin karfinta, domin wata maitar tafi wata karfi, akwai wadanda basa gashi idan sun kama kurwa a take suke cinyeta danya ba tare da sun soya ba, irin su ne suka fi kowa hadari a cikin mayu domin su kap daya suke yi wa mutum, bayan su sai masu saidawa su ma idan sun siyar basa karbowa sai wani ikon Allah, akwai kuma masu siyarwa basa ci, wasu kuma su ci kuma su siyar, irin su ne suka fi arziki a cikin mayu.
Mikewa tai tsaye ta kabe jikinta ta fito a gurin ba dan ranta ya so ba, sai dan ta san idan har ta sake yunkurin zata wahalar da kanta ne kawai, idan har tana son tai saurin riki dole ne sai ta sha maganin wanda zai suma jikinta ta taimakawa aljanin maitar da take yawo da shi. Mai kula da dawakan na mata magana bata ko kula shi ba tsabar haushi da takaici ta wuce shi kamar ana turata ta nufi gate.
WASIM POV.
Bappa ya mika wakawa Wasim hannu suka gaisa, sannan Wasim ya cire hular kansa ya kalli Bappa.
“Sunana Wasim, na san baka san ni ba, duk da bani da tabbacin ko Fadime ta taba labarta maka wani abu akaina”
“Aa bata taba fada min komai ba, lafiya dai”
Wasim ya gyara tsayuwarsa tare ta saka hannayensa duka biyu aljihun wandonsa na jean.
“Na dade da sanin yarka sai dai bata tana sani na sai daga baya, ina yawan ganinta idan taje kiwo ko diban ruwa, amman ban taba mata magana ko nuna na santa sai daga baya, cikin kankanen lokaci muka shaku da ita, ni ne mutumen da ta bukaci na yi mata dabon maciji na yi mata ta dawo gida da maciji a tulu an yi haka?”
“Tabbas la shakka an yi haka”
Bappa ya fada yana kara kallon Wasim da kyau a take ya nemi gajiyar da yake ji ya rasa sawun giwa ya take na rakumi.
“Na yi mata, bayan haka ni ne mutumen daya sauya mata murya a ranar da wani zai zo ganinta daga birni sai dai ba tare da ita din ta so haka ba, ka tuna”
Bappa ya daga kai cike da gamsuwa.
“Na san da wannan”
“Ni ne mutumen daya fada mata akwai wuta maita da take bibiyarta, kuma ni ne mutumen da na kama mayyar na daki cikinta a lokacin tana cikin siffar mage, ban san iya abun da tai ba, amman ba dukan wasa nai mata ba, doka ne wanda ke taba hankali duk wata halitta mai jini da hanta, wanda n tabbatar har yanzu bata samu lafiya ba”
“An yi haka, hakikanta amri”
“Ban yi zato ba yarka ta zo tare da wata mata ta fada min cewar tana son na shiga da matar garinmu ta dauki hoto, na kaisu ba saboda matar ba sai dan saboda Fadime duk da na san garin mu gari ne da basa karbar bako, a lokacin ne muka samu akasi har mahaifina ya ganta, yasa aka kira mu ya bata naman kura yace ta ci, ta ci naman da ke saka duk wanda ba dan garin ba kaiyi a makoshi da baki, a kokarin mahaifina na horani sai yace be yarda a fitar da yarinyar daga garin ba, wanda na san yayi haka ne saboda ya san zata matsu ni ma kuma zan ji ba dadi na takurar da mahaifina yai mata, sai a nan ma na kasa bin umarninsa saboda ta matsa min da kuka cewar tana son na dawo da ita a nan, na fito da ita ba tare da izinin sarkin garinmu ba, mahaifina kenan wanda haka ne ya haddasa mata makanta, shi ma daga mahaifina ne a kokarinsa na sake min horo ni da ita, wanda ko gobe aka ce ta zo garin ko kuma ni na kaita ba zan kara ba, Kaka ne ya fada min cewar an tura mata makanta kuma kun dauketa zuwa asibiti har a inda zan same ta shi ne ya fada min kasancewarsa matsafi ne, ni na na shiga asibitin na dauke na fitar da ita daga garin da sunan zan kawo ta gurinku sai na kaita wani gurin ajiya, a inda na kaita kuma na kafeta irin kafin da ko mutuwa tai ba za a iya dawowa da gawarta har sai idan ni naje na dawo da ita...”
Bappa jin yai kafafuwansa ba za su iya daukarsa, sai ya nemi guri a kusa da kofar gidan ya rage tsayunsa, wanda hakan yasa Wasim din shi ma da kansa ya rage nasa tsawo. Ban da kallon Wasim babu abun da Bappa yake, a yadda yake ganin kamala da natsuwa a fuskar Wasim da kuma ladani alamansa sam ba zaka ce zai iya yin wani tsafi ba.
“Kenan kai dan garin can ne da ake kira da Garuk?, amman miyasa ka dauke ta?”
“Saboda za a iya taba idonta a nan, idan baku kaita asibiti wata kila zaku iya gwada yi mata na hausa, wanda ko wane a cikinsu yana da illar da zai iya saka ta rasa ganinta gaba daya, bayan wannan a nan za ku yi mata fada ba zaku saurareta ba, musamman kai da kake mahaifinta, domin a kullum maganarta Bappa zai karyata ko sai ya kusa asheta, na zabi zuwa na fada muku gaskiya domin na san ba lallai ne Fadime ta fadi gaskiya ba saboda tana tsoron ku, kuma saboda na kwantar muku da hankali ku samu natsuwa kuma ku sn cewa yar ku tana nan cikin koshin lafiya, kuma da zarar idonta ya bude zan dawo da ita dawowa ta har abada”
Bappa yayi shiru out of words be san abun da zai sake cewa ba for now. Abun da Fadime ta fada masa cewar aljanu ne kenan ba gaskiya ba ne? Ashe duk abun da take fada masa karya take shirya ba, sai a yanzu Bappa ya tabbatar Fadime ta wuce tunaninsa da iya tsara abu kamar ya faru da gaske. Dagowa Bappa yai yana fadin.
“To amman da ka....”
Da sauri Bappa ya mike tsaye yana waige waige ganin babu kowa a gurin sai shi kadai.
“Subhanallahi”
Ya furta cike da tsoro marar misaltuwa.
“Ya bace bat...!”
Da sauri Bappa ya juya ya koma cikin gidan, a gaban makociyar su Inna ya labartawa Inna komai, a take Inna ta tashi zaune tana jin kamar ta samu lafiya.
“Amman da ya taimaka ya kawo mana ita, in ya so sai mu kiyaye duk abun da ya fada”
“Ni ma abun da na tashi fada masa kenan ina dubawa sai na ga babu mutum”
“Kasan tsafi ne da su, wata kila yana da layar bata, layar zana”
“Ba mamaki, amman Fulani akwai karfin hali yanzu har ta taka taje garin nan? Anya kuwa Fulani bata da aljanu gaske? Kwata kwata babu tsoro ko fargaba komai a idonta”
Inna ta rausayar da kai.
“Fulani kam Allah dai ya shirya, gaba daya rayuwarta ban san wace iri bace, kuma babu yadda ban yi mata gargadi ba akan kar taje garin nan amman bata ji, to yanzu ya zamu yi kenan?”
“Hakuri zamu yi kawai, kuma gobe idan Allah ya kai mu sai na tafi na fada musu na na jany karar”
“Bappa Fadime ai ba kara ka kai ba, kai cijiya ka kai musu, dan haka ka kyalesu kawai domin idan ka koma wata kila ma za a ce ka kawo wani abu ne, ka kyale su kawai idan ma sun ji wani abu ai za su kira tun da Shatu tace ka bada number wayarka”
Cewar mamansu Ramla. Bappa ya amsa mata cike da gamsuwa.
“Haka ne kuma da zancen ki, amman dai idan kana jin mu bawan Allah ka daure ka kawo mana ita, mu kuma ba zamu nema mata maganin komai ba”
Inna ta daga kai tana kalle kalle kamar ance mata zata ganshi.
HAJIYA BABBA POV.
Tun rasuwar Talba Hajiya ta koma kamar wata marar lafiya, bata da kuzari walwalar duk ta gushe kullum tana dakin sai idan za ta yi wani abun sannan ta fito waje, zuciyarta ta saka sakin tunanin Talba, ba mutuwarsa take ji ba kamar rushewa al'amuranta, gashi a da tana tunanin zata fi Ammy gado ko da Mai Martaba ya rasu, saboda Talba yana a matsayin Shattima Juwairiyya da Karima kuma suna matsayin namiji daya sai Kaunar dake matsayin Nana, yanzu kuma sun za daya tun da Talba ya tafi, Sirleem kuma ba zai gaji Mai Martaba tun da ba dansa ba ne, Tunanin hakan yasa tun farko ta zo a haihu da yara a gidan amman be bata da yawa ba, sai ya bata hudu, namiji hudu mace uku.
Ga burin da take da shi na son Talba ya samu sarauta yanzu ya kau, sai abubuwan suka taru suka mata tsaye a zuciya ko abincin kirki bata iya ci. Tana zaune tana ta tunanin duniya Sirleem ya turo kofar ya shigo yana sallama, sai ta amsa masa da muryarta dake karantar da shi tsantsan damuwar da take ciki, kusa da ita ya zauna yana jin babu dadi a yanayin da ya same ta, domin duk dan kwarai ba zai so ganin mahaifiyarsa a cikin damuwa ba.
“Hajiya...”
Juyowa tai ta kalleshi cikin kwanakin nan naman fuskarta ya sauka fiye da da, ma'ana ta yi rama sosai.
“Sirleem kana lafiya?”
“Lfy kalau ya jikin?”
“Alhamdulillah, magana nake son yi da kai, magana ta karshe ba shawara zan baka ba umarni ne”
Tun kamin ta karanto masa abun da take so gabansa ya fadi.
“Minene Hajiya?”
“Bana son wakar nan da kake yi, kaskanci ne a gareka da mu da kowa ma naka, bana son wakar da kake, baka rasa komai ba a duniyar, me zai kasa ka zabi waka?”
“Waka sana'a ce Hajiya”
“Na yarda sana'a ce, amman ba ga dan babban mutum kamar kai ba, mu ya kamata ace muna kyautatawa mawaka muna musu alheri muna basu dukiya, kai fa idan ana son kiranka kai kayatar a taro ko biki, ina jin zafi kuma kaskanci ne a gareka a matsayinka na a gola a gidan Sarki kuma dan former vice president, abun da ko wane dan babban mutum yake a yanzu kokarin yaga ya yi kamar ubansa ko ma ya wuce ubansa, ka yi karatu a waje kai fa engineering ka karanta miye hadinka da waka? Why? Bana so kuma ina mai umarta ka daina, kai kadai ka rage namiji a yanzu, so nake ka zama babban mutum kamar mahaifinka ba mawaki ba”
Tun daga cikin kansa ya ji wani abu na taso masa yana saukowa har kasan kafafuwansa, be taba jin nauyi wani abu a duniya kamar maganar Hajiya a yanzu ba, sai yaji kamar ta dauki wni katon dutse daya fi garin Kano girma ta dora masa a kai. A duniya babu abun da yake so yake jindadin yinsa kamar waka, ya dauke a amatsayin sana'a kuma abun da ke bashi farinciki da sayyana a cikin al'umma, mahaifinsa ya bar masa dukiya da kamfanona masu yawa amman kanen mahaifinsa yake kula da komai shi kuma ya maida hankalinsa gurin wakar. Sanin kansa ne Hajiya bata son wakar tun farkon tashinsa ta kyale shi ne kawai saboda yana ra'ayin abun, yanzu kuma ta masa mai gaba daya wanda be san ta inda zai fara ba, the most painful part is tace masa umarni ne ba shawara ba.
“In dai hakan zai faranta miki rai, kuma ya saka ki koma da walwala kamar dai, na miki alkawari zan tattara duk wani abu daya shafi waka na aje a gefe, zan maida hankali gurin dukiyar da Daddy ya bar min inshallah”
Ta yi murmushi daman ta san indai har ta bawa Sirleem umarni ba zai iya tsallakewa ba, ba kamar Talba ba da bata isa tai masa haka ba, har sai idan abun ya biyo da son zuciyarsa.
“Allah ya maka albarka ta taimaka maka, ai kara ka maida hankali tun wuri domin nan gaba kadan kenen mahaifinka zasu iya cewa rabin dukiya ta su ce”
Shi dai be ce nata uffan ba ya mike tsaye ba dan yana da tabbacin ta kare maganarta ba sai dan yana jin duniyar tana juya masa a yanzu. Da kallo ta bishi har ya fice sannan ta sauke ajiyar zuciya, ta bar shi ya tafi ne kawai saboda ta san abun da ta dora masa mai nauyi ne, ba zata bijiro masa da zancen Mansura da Falmata ba a yanzu sai hankalinsa ya kwanta, daman kuma ba fasa shiga malamai zata yi ba.
Karamar wayarta ta dauka ta aikawa Hajiya Talatu kira, sai da wayar tai daf da katsewa sannan Hajiya Talatu ta dauka tana randaga sallama.
“Hajiya Talatu ban ji ki ba”
“Yanzu yanzun nan na fito wanka Hajiya, gidan zan zo amman kamin na iso bari nai miki albishir, na yi magana da matar nan laraba tace min zata zo, kin ga sai mu je gidansu Hajiya Uwani tun da yafi sirri, idan kuma kina ganin ba matsala bace idan ta zo gida sai ta tsaya bangare mu yi duk abun da zamu yi”
“Aa bana son zancen Hajiya Uwani, zuwa gidan ai tonon asiri ne, kara dai inda kike tun da Hajiya Mairo ba shigo miki take ba”
“To ba Ba matsala sai ayi haka din”
“Ya maganar wacan Malami kin tafi?”
“Eh na tafi, shi ma ya duba mana yace yarinyar ma aure za ayi mata, Na Mai Martaba ma ya bada magani a kawo miki ki bashi wai a abinci ya ci, na fada masa a warware kullin, Nana kuma ya bada wata laya yace a samu katon dutse a saka karkashi idan za a saka a ambaci sunanta sau uku, ya tabbatar min da an yi haka ba zata iya fadawa kowa ba ko da kuwa an dora mata wuka a wuya ne”
“To yayi kyau ba sai kin kawo min ba, ki samu dutsi a can ki yi, ko kuma ki saka wani wanda kika yarda da shi yai, ai kara a warware kam tun da mai gaba data ta afku, Allah na tuba ko mutuwa yai a yanzu ai Ammy da Jarma ne ke da harka”
“Shine ai, ita da su kowa wane murna zai yi tun da danta take zaton a bawa Jarma kuma kan sa zai yi wa yaki”
“Hmm Ai indai ina da rai Wallahi Shattima ba zai yi sarauta ba, ko Jarman idan ya samu ai ba gata zai mana ba, ni Wallahi har gani nake kamar da sa hannun Jarma ko Ammy a mutuwar Talba, ko tsawa suna iya tura musu ko kuma ayi wani abun jirgin ya fadi”
“Tsab za su aikata, musamman ma Jarma, ko da yake ita ma Ammyn ba kanwar lasa ba ce tun da gashi ta mallakewa kowa ta kama komai ta rikr sai yadda tace ake”
“Hmmm ai wannan matar ko? Allah kadai yasan irin tsafin da take takama da shi, ke kina ganin wani abu kin san ba banza ba ne, wai ya maganar auren Maijidda?”
“To har yanzu dai be sake ce min komai ba, kin san daman wannan bokan na can ya fadi cewar ba za ayi auren ba, ban sani ba ko dan an yi mutuwar nan ne ko kuwa saboda na yi yaji ne, ko kuma Ammy ta sake masa wata shawarar oho”
“Allah dai ya rabaki da wahala, wannan ai kisan kai ne za ayi miki da ya, Allah dai ya kyauta”
“Ameen Hajiya sai na shigo, yanzu da na gama shiri”
“To sai kin iso, daga nan ki ji yadda muka yi da dan gidanki Sirleem”
“Au to gani zuwa yanzu kuwa”
Hajiya ta sauke wayar tana dan murmushi da be kai ciki ba.
SHATTIMA POV.
Sake fita yai ya dauko key wata motar ya saka ta tashi, har sai da ya juya kanta ta kalli gate, sannan ya fito ya riko Fadime ya fito da ita a motar da take cikin ya saka a wacan Fadime na zaunawa Motar ta mutu, zagayawa yai ya shiga driver side ya kunna ta ki tashi, haka yai juyin duniya motar ta ki tashi. Can wani tunanin ya zo masa sai ya fita ya zagaya side din Fadime ya cireta a motar ya sake zagayowa ya shiga yai mata key sai mota ta tashi.
“Oh... ”
Ya furta sannan ya fita, a kunne ya bar ya sake zagayawa ya saka Fadime sai motar ta sake mutuwa.
“Miyasa motar take mutuwa?”
“Saboda kina ciki ne”
Ya amsa yana jinginawa da kujera yana kallonta.
“Wallahi ba dai ni ba, sai dai idan daman can motarka bata da kyau”
“Duka motacin uku?”
“Na sani ko mota daya ce kake juyani kana min wayo”
Yayi murmushi duk da baya cikin yanayin nan.
“Yanzu ba wannan ba, idan tafiyar da ke ba zata yiyu ba, ki zauna sai naje na fadawa iyayenki idan ma kama na zo tare da su sai