Showing 267001 words to 270000 words out of 273152 words
Chapter 90 - FULANI BOOK COMPLETE DOCUMENT by Khadijah Candy .txt
kawarta Khadija.
“Komai ya wuce, ni kaina ban tsammaci zan samu rayuwata a haka ba, Baba ma ya dawo kamar ba shi ba ko shekaranjiya sai da ya aiko Inna A'i ta kawo min daddawa da kayan yaji mai yawa, ita ma tana da kirki sosai, ko kanen na tana kula da su sosai kamar yayanta, dawo da su da Baba yai a hannunsa ba karamin dadi n ji ba Wallahi”
“Ai yanzu kowa kirki zai miki Falmata, saboda anga kina auren mai arziki, da dai a dane za ki fi gane mai son ki da gaske da mai miki sheri, ita kanta Tumba da zata samu damar rabarki soyayya zata nuna miki”
“Haka ne, ko tana ina yanzu? Wannan matar ta cutar da ni sosai”
“Wallahi ni a yadda na ji wai tana cikin garin nan gidan wani kawunta”
“Da gaske ashe bata koma kauye ba? ”
Khadija ta mere baki.
“Hmm ina zata iya zaman kauye ta saba da birni, ba shiyasa tai yadda tai ta aure Babanku bayan mijinta ta mutu”
“Su ma ai yau da gobe gajiya za su yi”
“Wallahi kuwa ai ni idan ban ga Tumba a titi tana bara ba, burina ba zai cika ba”
Cewar Khadija tana mikewa tsaye ta dauki atamfar ankonta, sai Falmata ma ta mike tsaye da cikinta tana fadin.
“Ni dai idan akwai babbar ki siyo min”
Khadija ta mata wani kallo.
“Iyyyyy yayi matar manya wato kin bar bangarenmu ko? To dole sai kin saka irin ta mu Malama”
Falmata ta yi dariya.
“To ai ina son kalar atamfar ne, ko bayan bikin ne na rika sakawa”
“Eh na ji dai, sai kin saka kalar ta mu, ko kuma na kawo kayan lefena duk mijinki ya siya min masu tsada sai mu zama daidai”
Falmata ta yi dariya.
“Ai zai siya miki indai mijina ne ba shi da matsala, Amaryar ba kya laifi, zan miki order kaya na musamman gurin yar gidan Mai Fata, kayanta na da kyau sosai”
“Yauwa kawata haka nake so dai, a gyara ni”
Falmata ta kai mata duka.
“Khadija ba ki da kunya”
“Ke kina da kunya kika yi ciki ne? Ana ganinki ai an san me kenan”
Dariya sukai dukansu sannan ta raka kawarta har gurin gate, sannan ta dawo ta kwashe plates din da suka ci abinci ta kai cikin ta gyara ko'ina na falon, sannan ta haye sama tai alwala tai sallah ta azahar tai addu'a tai ma mijinta sannan ta mike tsaye ta nade carpet din ta aje a muhallinsa, ta sauko downstairs ta shiga kitchen ta soma dora girki, sai biyar ta gama komai tuwon shinkafa tai miyar taushe sannan ta dauko komai ta kawo dinning da jera duk da ta san mijinta ba mutum ne mai son cin abinci a dinning ba, musamman da cikinta ya girma din nan ya fi son su zauna kasa su ci abinci a tare.
Bayan ta gama komai ta shiga tai wanka ta shirya cikin jar abaya ta saka hula ta zauna saman gadonta tana kallon tv, after like 30 minutes wayarta tai ringing sai ta mika hannunta ta dauka ganin number Sirleem yasa ta murmushi.
“Hello”
“Babyn Baby?”
“Na'am ya aikin?”
“Da godiya i miss you”
“I miss you too”
“Fada min me zan siyo miki?”
“Bana son komai kuma karka mana takeaway na dafa tuwo”
“Oh baby ke da kanki?”
“Yes”
“Kin saba alkawari”
“Na ji zan iya ne, kuma ai likita yace na rika motsa jiki”
“I love you, kuma ina big surprise da zan miki ina tafe da shi?”
“Minene?”
“Idan na fada miki ai ta zama ba surprise ba, ina tafe da shi ke dai ki shirya kawai”
Kamin tace komai ya yanke wayar yana murmushi, mamaki ne ya cika ta jin yace yana tafe da surprised na minene, tana ta tunani kala kala amman ta kasa cankar ko minene, tana zaune a dakin har ta ji karar bude gate, wanda hakan yai daidai da kiransa a wayarta.
“Ban yarda ki leko ni ba, kuma ban yarda ki fito ba”
Shine abun da ya fada mata a wayar sai gai shiru tana sauraren wayar da be yanke ba har ya fita motar ya rufe, sannan ya nufo falo manne da wayar a kunnesa ya bude ya shigo sannan ya ce.
“Za ki iya fitowa yanzu”
Aje wayar tai ta sauko saman gadon tana jin gabanta na faduwa for no reason, tafiya ta fara yi kadan kadan kamar wanda bata son fita daga dakin, kamin ta kai hannunta ta bude kofar dakin ma wani aiki ne, a hankali ta bude kofar dakin ta fito ta janyo kofar ta rufe ta fara saukowa a hankali, da Sirleem ta fara arba ya sauko mata da sakon murmushi, sai ta mayar masa kamin idonta ya sauka gurin Ameer da ya mike tsaye daga zaunen da yake yana kallonta, idonsa cike da hawaye tsayawa tai cak tana kallonsa hawaye na sauko mata, sai kuma ta sauko da gudunta har sai da Sirleem ya tsorota ganin cikin dake jikinta, sanin zata iya rumgumar Ameer ko kuma shi ya rumgume ta yasa Sirleem yai saurin riketa ya rumgume sai ta fashe da kuka.
_________
Ina mata matan kwalisa Matan da suka ansa sunansu na Mata? Ina wadanda ke cewa mun yi mun yi bamu ga amfaninshiba? Hmmm to ku zo ga Yar gidan Maifata ta zo maku da Al ajabu, dan tsugunno, gumba da tsimi da Zuma daban daban, maganin sanyi na maza da Mata. Ga kuma garurruka irinsu mallakau sabuzu kuwa, sa bahaushe saibi, Dan hubbare kafi malam aiki, ke kadai ke da miji, dahuwar kaza, tattabara, ciccibi da dai sauransu. Ba anan kayanmu suka tsaya ba, muna hadin amare na musamman turaren sutura turaren tsugunno turaren wanka da na daki da na jiki duka 4amare nasu na musamman ne, amma ga tsuhuwar da ke son komawa yarinya itama zata iya zuwa ahadata kai abundai sai wanda ya gani, dan haka karkubari abaku labari, domin neman karin bayani zaku iua nemana ta wannan number 09029891757 ko 08169311410, muna aikawa ko'ina a fadin kasar nan har waje kasar nan muna aika kaya.
Address: Nasarawa Samaru Area gurin masallacin mai sola Gusau Zamfara state Nigeria.
03/12/2021, 18:59 - 🤐🤐🤐🤐: *Khadeeja Candy*
*Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 300 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith bank, then send the evidence via 08036126660*
Kuka tai sosai kamin ta samu natsuwa, sannan Sirleem ya rikata suka zauna saman kujera daya, Ameer kuma yana zaune a dayar kujerar yana kallonta idonsa cike da kwalla.
“Momy ta fada min komai, na fahimci komai a kuraren lokaci...”
Ya fada hawaye na sauko masa, Falmata kan kuka take tana kallon dan'uwanta tana jin wani irin shaukin kaunarsa na ratsata, bayan kanen da take da su yanzu ma tana da wani yaya. Sirleem ya sake ta ya nufi kitchen ya dauko musu ruwa da cup ta zuba ma Ameer ita kuma ya dauka ya bata da kansa ta sha.
After ya sha ya aje cup din yana murmushin takaici.
“I wonder how ban gane cewar ke jina ce ba, na tafi na bar gida ina da dan wayo na, amman sai komai ya soma shafe min a kai, and the most painful thing”
“An shafe maka komai ne saboda barin gidan da kai ba a banza ba ne, na san kana som Mama a yadda ka lake sai ka dawo kusa da ita kadai ya isa ya sanar da kowa ba da son ranka ya bar gidan ba, amman na san shirrin na Umma ne”
Ya daga kai.
“Haka ne ni kaina ina ji a jikina kamar ba a banza ba, saboda na saka zuwa neman mahaifiyata, bayan kuma tana cikin rai a kullum, na yi sa'a a lokacin da na bar gida, na yi nisan zango ban san inda zan je ba kawai dai na ji ina bukatar nisa da gidan ne, Allah yasa na hadu da abokin Daddy shi ya dauke ni ya kai ni gida gurin Daddy, tun daga lokacin sai na fara fuskantar wata wahalar daga gurin Inna Kulu (Uwargidan Daddy) a kullum ina mafarkin Mama ina ji kamar zata nemi inda nake amman shiru, na sha wahala kamin Allah ya budewa Daddy ya zama babban mutum kamar haka, sai kuma na kara samun wata sa'ar na aurin Momy da yai mace mai hakuri da sanin ya kamata, ganin irin wahalar da nake sha a can yasa Daddy ya maida mi hannun Momy saboda bata da yara kuma tana nuna tausayi da kulawa a gareni sosai, Matar nan ta rike ni kamar ita ta haife ni, ban san zafin rashin uwa ba saboda ita, sai dai hakan ina fatar wata rana zan ga mahaifiyata, ashe lokaci ya kure min”
Ya fashe da kuka.
“Da Mama tana raye, ta ga yadda ka zama da ta yi farinciki”
Sirleem ya rumgume matarsa dake ta kuka yana lallashinta.
“Yadda Allah ya tsara abu haka yake kasancewa, kin ga da Allah ya so sai yayi ki a gidan masu hali inda ko ciwon kai kika yi sai an shiga damuwa, Allah yana da iko da power da zai iya haka amman be yi ba, sai ki fahimci akwai hikima a cikin lamarin, ku yarda da kaddara ku gode Allah da yai muku tsawon rai har kuka gane junanku”
Sirleem ya fada sai Ameer ya girgiza kai yana murmushin da yafi kuka ciwo.
“Haka ne, ni kaina na san Allah ne ya tsara min haka, sai kuma ya kawo min Momy kalar yadda ya kawo miki dauki a yanzu bayan abubuwa da yawa sun faru”
Ita ma kan ta daga masa tana cigaba da kuka da yaki ya tsaya mata. Sai da Sirleem ya tabbatar ta daina kukan sannan ya tashi ya basu guri sun yu maganganu da yawa masu taba zuciya da tuna baya, Falmata tana fadar yadda Mama take yawan maganarsa. A gidan ya ci abincin tare da Sirleem da Falmata abincin da kanwasar Falmata ta girka, duk da kasancewar baya cikin walwala saboda abun da ya faru sai dai kana ganin fuskarsa kasan yana cike da son yar'uwarsa ko'ina tai binta yake da kallo irin na kauna da mamakin yadda ta zama jininsa lokaci daya, sai a yanzu yake ganin yanayinta yana yin kama da na Mamarsa.
***
Rayuwa da ciki a gurin mace ba abu ne mai sauki ba, musamman cikin fari kuma ga mai kananan shekaru kamar Falmata, sai dai kasancewar mai juriya da hakuri ya bata damar iya daukar nauyin cikinta cikin ma Sirleem yana hana ta yin abubuwa da dama gudun kar ta wahala, domin har ya fita kula da rawar kafa dan abu kadan zai yace zata gajiyar masa da baby ko tana son ta ja masa babynsa ya wahala. Sai da tai da gaske sannan ya barta ta tafi bikin kawarta Khadija domin ko fita baya son tana yi wai ciki ya tsofa tana ta wahalar da abun ke cikin, idan ya fita komai ya gani sai ya siyo mata idan kuma yana gida kullum tana jikinsa shi kuma hannunsa ko kansa na kan cikinta, har mamakin yadda yake ta zumudin cikin take wata kila. Saboda be taba yi ba ko kuma saboda an kawo gunsa ne, domin wani rawar kafar dai bata taba gani ko jin irinsa ba sai da aka kawo gunsa, haka dai akai ta fama Allah ya kai ta shiga watan haihuwarta, a nan ta gane ashe abun ba sauki sai ga wanda Allah ya kawo wa, asibiti ta haihu tana dakin haihuwa tana nakuda Sirleem ya waje cikinsa na murdawa kamar shi zai haihuwa daman tun kamin nakuda ta kama ta ya fara nashi zazzabin da ciwon kai.
Sai yamma ta haihuwa cikin nasarar Allah, take Sirleem ya fadi yai ma Allah sujuda yai godiya. Kamin dare hotunan baby sun cika Media kasancewar mijinta sanannen mutum ne.
FADIME POV.
Zuwa tai ta tsaya gabansa ta mika masa hannu.
“Miko min kofin can”
Ya dauke kai daga laptop din dake gabansa ya kalleta.
“Shi kofin?”
Ta turo baki gaba.
“Eh”
Sai yai murmushi ya kai hannu ya dauka ya mika mata, haka take masa ita ala dole tana da ciki ba zata duka ba, musamman idan ta san yana cikin gidan ko wanka za tai sai dai ta rage tsawo a hankali har ta kai kasa saboda cikinta kamar wata mai tsohon ciki, babu ranar da bata bude cikin tai ta kallo tana shafawa, har tana cewa wai bata ji motsinsa ba wai ko ba shi da lafiya ne ko kuma dan tana yawan cin abinci mai yawa ne, hakan yasa ta rage cin abinci mai nauyi kuma da yawa wai kar ta cutar da ciki, wani abun idan tana yi Shattima sai yai ta dariyarta yana mamakin yadda take wauta sosai. Ya fada ciki sai ya kai wata hudu yake fara motsi amman bata yarda ba, kullum sai ta masa complain.
Haka akai ta shan rainon cikin kamar akanta aka fara ciki a duniya ko numfashi ba ta yi da karfi, sai dai duk abun da take tana yi idan tana ita kadai ko kuma ita da Shattima, bata yi a gaban mutane musamman idan suka leka masarauta hakan yasa Shattima ya gane shagwabar har da shi ake yi ma. Daman kuma shi dan nema ne domin shi ya fara nuna mata tun farko ita kuma sai ta samu guri, haka zata tashe shi cikin dare ta ce zata ci abu, idan be nemo mata ba sai kuka kamar karamar yarinya, wani lokacin lallabata yake da sunan zai nemo mata sai ya samu tai shiru har bachi ya dauke ta, wani lokacin kuma fitowa yake da sunan zai fita ya nemo mata sai ya dawo falo ko dakinsa ya zauna sai ta yi bachi sannan ya koma ciki.
Ba ma kamar da cikin ya tsofa a lokacin ne yake son ta motsa jikin sai ta tsaya kai ta fata ta ce ba zata yi komai ba, sai fadar take cikin ya mata nauyi wani lokacin idan ta shiga bandaki fitsarin ma a tsaye take sakinsa, sai dai ta saka ruwa, domin idan ta duka zata ji kamar cikin zai fito mata ko kuma ta gagara tashi, hakan kuma baya hana ta fita cikin mutane da cikin saboda shegen son yawo, idan yace zai hana ta wata rigimar ce zai takalowa kansa. Yau ma ta kama weekend Shattima na gida amman hakan be hana ta shiryawa da sunan zuwa Walimar wata cousin dinsa da ake ba. Yana zaune falo ta sauko da shirinta karfin hali har su jaka. Shi dai kallonta kawai yake har ta sauko.
“Da gaske zuwa zaki yi?”
“Eh ni dai ina son zuwa”
Ta fada tana dan turo baki gaba, so kawai take yace mata ba zata je ba ta fara masa kuka tana cewa ba zata ji abinci ba saboda ta san yadda yake shiga damuwa idan bata ci ba. Murmushi yai ya mike tsaye ya nufi dakinsa, be dade ba ya fito ya shiga dakinta ya sauko inda take tsaye tana jiransa ya cire gyalen dake jikinta ya mika mata Hijab.
“Ki saka wannan zaki fi rufe jikinki”
“Ni nauyi yake min”
“Daure ki saka haka nan haba baby na dan Allah”
Ba dan ta so ba ta saka Hijab din sannan ya aje gyalen akan kujera ya rika hannunta suka fita daga falon, ya riga isa gurin motar ya bude mata ta shiga ta zauna sannan ya zagaya mazauninsa yai ma motar key.
“Allah ya taimake ni karki min raki gurin haihuwa”
“Wallahi sai na yi haka kawai waya ce kai ciki waya ce? Mutum cikin mutum kuma zai fito a ciki mutum ace ba zai yi raki ba? Lallai fa”
Yayi dariya.
“Kina da gaskiya fa, mutum cikin mutum ko?”
“Eh mana, kuma ni zan sake haihuwa ba ma daga wannan idan na haihu yar mace mai kyau”
“Kamar ni?”
Ta yi dariya.
“Ke da kika ce twins kike so? Ai mutum biyu ne zai fito a jikinki yarinya”
“Ni dai da na ji wani abu ka kaini asibiti”
“Aa asibiti? Ga asibiti a gida? Wa zai kula da ke kamar mijinki?”
“Ai kai ta yaranka za kai”
Ya kai hannu ya taba kumatunta.
“Kamin na ga yaran waye na fara gani?”
Ta mika masa bakinta sai ya maso da nasa tai masa kiss.
“Ni ka fara gani”
“I love you”
Ya dora hannunsa a kan katon cikinta yana murmushi.
“Kin san dai kina saurin jin yunwa ko? Ki daina zama baki ci ba yunwa tana damunki”
“To zo ka bude min”
Ya fita daga side dinsa ya zagaya dayan side din ya bude mata ta fito sannan ya rufe ya fita da kallo har ta shige cikin falon shi kuma ya shigo motarsa ya dawo gida, bayan yayi sallah azahar ya kwanta be farka ba sai 4 shi ma alarm din wayarsa ne ya vmuslim app ya farkar da shi, bathroom ya shiga yai alwala ya fito ya sauko yana hamma ga mamakinsa sai ya ganta zaune saman kujera tana kallon plasma dake falon.
“Hajiya yaushe kika dawo?”
Juyowa tai ta kalleshi da idanuwanta da suka mata ja tsabar kuka.
“Tun dazun, kaje kana ta bachi wai ni kuma ina ta daukar nauyi, kai ba ruwanka tun da ba a jikinka ne ba”
Zaunawa yai kusa da ita, ya san kullum abun kuka take nema, but abun mamakin kar dai ace dan yana bachi take kuka, ya hana ta bachin ne ita?
“Shi ne kike kuka?”
“Eh mana, kuma mutane sai cewa suke a a ashe ciki ya tsufa mai ciki mai ciki suna ta ce min haka....”
Ta kara fashewa da kuka domin a yanzu babu abun da ta tsana kamar ace mata mai ciki, daman tana ta daurewa a can amman a gida dole ne tai kuka saboda abun ya mata ciwo, gashi kuma tana zuwa ta tararda Shattima yana bachi abun shi. At first dariya ce ta zo masa sai yai saurin gintseta ya ja jikinsa ya rumgume.
“Na san kina fama da abu, shiyasa na ce ki daina shiga mutane amman kin ki, da kina nan ai ni ma ba zan fara yi bachi ba, balle har su rika ce miki Mai ciki Mai ciki Mai ciki Mai ciki... ”
Dagowa tai ta kalleshi.
“Cewa kake yi kai ma?”
“Aa ni ai ba zan fara ba, ina fadar yadda suke fada ne, Allah ya ba ni hakuri?”
“Ya baka?”
“Ya baki”
Yayi saurin gyarawa yana maidata