Showing 180001 words to 183000 words out of 273152 words
Chapter 61 - FULANI BOOK COMPLETE DOCUMENT by Khadijah Candy .txt
ta tambaya, ganinta a gurin zaune bayan ta duba dakinta bata ciki.
“Har zuwa lokacin da zan mutu...”
Ta amsa mata ba tare da ta bude idonta ba.
“Na san zaki samu kanki a damuwa shiyasa ban taba labarta miki wannan ba, shiyasa na boye miki kuma na shimfida miki wata karyar wanda zaki rayu akanta kuma jiki dadin rayuwa”
“Ko ba ki fada min a yanzu ba, wata rana gaskiya zata bayyana kanta, dole ne za a binciko wannan abun, dole ne za a bukaci sanin asalina, domin shi n martaba ya mace”
Iya ta sauke ajiyar tana jin damuwar da yarta take ciki, ba damuwar abun da ta aikata ba.
“Na sani, amman dai yanzu ki manta da komai ki kwantar da hankalinki, bana son damuwarki....”
Zainab ta mike tsaye sannan ta juyo ta kalli Iya hawaye na bin fuskarta.
“Ba ki son damuwata? Amman kina son damuwar wasu? Me Ammy tai miki kike cutar da ita? Ba mu cancanci mu taka bakin kofar falonta ba, amman ta bar mu mun rabi jikinta, sanadim mijinta da yayanta ake min kallo mace mai kima bayan ni ba kowa ba ce, ba ki auna yadda wata uwar zata ji ba idan ta rasa nata yaya? Baki ayyana yadda Ammy take ji saboda halin da Shattima yake ciki? No Iya fada min akwai hannunki a jikin Mai Martaba ko?”
Iya ta daga mai kai, kai tsaye tana kallonta da idanuwanta na maita. Zainab ta yi kasa da kai tana murmushin da ya fi kuka ciwo, can kuma ta dago ta kalleta.
“Ke kika kashe Auwal?”
Nan kam ta daga mata.
“Ina yin komai ne saboda ni da ke...”
Zainab ta girgiza kai tare da kada mata tsawa.
“Ba saboda ni da ke kike ba, saboda son zuciyarki kike, wace irin macece ke? Wace irin zuciya ce a kirjinki? Baki da tausayi Iya? Baki jin be kamata ki yi wani abun ba? Miyasa zaki cutar da bayin Allah? Me suka miki? Why? Why?”
Ta tambaya tana dukewa a kasa ta fashe da kuka.
“Na yi nadamar haihuwata da kika yi a yau, ina ma na zo a mace, ina ma na mutu tun kamin wannna burin ya shiga rayuwarki? Kin cutar da mutane da dama, kin cutar da ni ta hanyar haihuwata ba ta hanyar sunna ba, kin cutar da Ammy da iyalan gidanta bayan ba su miki komai ba sai kyautata, har Auwal da be miki komai ba kim cutar da shi, kin maida yayansa marayu kin maida matarsa bazawara...”
Iya bata ce komai ba ta juya ta koma ciki, ko kadan bata taba jin nadamar abubuwan da tai ba, bata taba jin tausayin kashe rai ba, bata taba jin tausayin cutar da kowa ba, saboda babu tausayi babu imani a zuciyar maye, shiyasa ake cewa su bada wani shakiki na su, kamar uwa ko uba ko da ko wani dan'uwa ta yadda ba za su taba jin tausayi ko fashin cin kurwar wani ba, babu komai a cikin zuciyar mayu sai keta da hassada ga rashin tausayi da rashin imani, domin sai mutum ya siyar da imaninsa sannan yake iya yin maita.
SARDAUNA POV.
Farin bokitin wanki ne a gabansa ya maida hankali sai wanke kayansa yake, yana amsawa Anti Rabi firar da su ke sama ma, da fira tai dadi ne take dauko masa zancen mutuwar da akai a gidan Sarki.
“Ni ma na aji, indai ta bangaren Ammy ne gaskiya ba zan ji mata dadi ba, amman idan bangaren Hajiya Babba ne Allah ya jikan musulmi, ta fi kowa a duniyar nan bakar cuta da zalinci”
Ya fada yan murza wandon dake hannunsa da dukan karfinsa, Anti Rabi ta yi dariya tana saka kananan itace a wuta.
“Kai ba baka a taba ka baka iya yafiya ba”
“Wallahi na zance yafiya tsakanin da baiwar Allah nan, ta cutar da ni ina maraya na ta cutar da ni, bayan Annabi yace wanda ya taimaki maray kafada da kafada za su shiga aljanna tare da shi, amman ita neman cutar da ni take, hakam ya nuna ba karamin cutar mutanen gidan nan take ba”
“Ai kai yanzu ka wuce maraya, ka girma ka isa tallafawa kanka fa”
“Aa ni ban tashi a maraya ba, sai ranar da na gina kai, irin ginuwar da zan iya taimakon wasu”
“Ni na tsorata sosai a lokacin nan, Allah ne dai ya saka abun ya zo da sauki”
“Ni Wallahi na dauka ko akashe ni za su yi, babu imani a fuskar police din nan, dukana suke kamar sun samu kayan wanki a take suka sauya min fuska, ina da dan haskena yanzu na zama baki, jikina be gama dawowa ba”
Anti ta girgiza kai tana murmushi, ashe sara sukai akan gaba, suna tsaka da zancen wani katon bafade ya sallamo musu kofar gidan. Tun daga yanayin sallamar da tsayarwar mota ya isa ya sanar musu masu sallamar na musamman ne. Sardauna ne ya sama sannan ya wanke hannayensa ya nufi kofar gidan, yana ganin mutane dake sanye da jajayen kaya ya ji gabansa ya fadi domin ya san daga fada suke, tsoronsa daya kar ace wani laifi ya sake aikatawa, dan baya tunanin Nana zata aiko masa wannan tawagar.
“Lafiya dai?”
“Lafiya kalau dan talakawa? Kai ne Sardauna?”
“Aa yayana ne, me ya faru?”
Ya amsa da sauri numfashinsa har gargada yake tsabar tsoro.
“Daga masarauta ake nemansa, ka kira shi a duk inda yake yanzu nan”
“A gaskiya baya garin nan, ya tafi nijar gurin nema”
“Babu ta inda za a iya samunsa?”
“Gaskiya a yanzu dai baya nan, amman lafiya dai?”
Ba su ce masa komai ba suka juya, sai da suka kusa kai wa gurin motarsu sai zuciyarsa ta raya masa ba lallai ne dan wahala da yi kiransa ta sake kiransa ba, idan kama sa za ayi ai da Police za a zo ba da dogarawa ba, idan kuma rabo ne yak kiransa ya ki amsawa ba, what if wani samu ne yake kwankwaso masa kofa yaki budewa.
“Kai ku dakata ni ne Sardauna”
Kusan a tare suka juyo suna kallonsa da mamaki.
“Ban san ku ba ne shiyasa na boye ina fatar dai ba wani laifin ba ne”
“Kasan daga inda aka aiko mu kiranka har kake mana karya?”
Dayan su ya fada yana nuna shi.
“Ayi hakuri dan Allah, ka san duniyar ce yanzu sai da haka”
“Kai dan talakawa ka shiga hankalinka ba ayi ma gidan sarauta karya, yanzu nan zamu koya maka hankali”
“Gafarce ni dan Allah ayi min afuwa”
“Shiga mota muje”
“Okay bari na fadawa Yayata”
Ya juya da sauri ya koma cikin gidan, ko da ya shiga ya samu Anti Rabi a tsaye dafe da kirji tana sauraren abun da zai fada mata domin hankalinta be bata sallamar Allah da Annabi ake musu ba.
“Su waye?”
“Daga masarauta suke”
Ta dafe kirji tana zaro ido.
“Masarauta kuma? Me kai? Ko ka sake zuwa ne bayan abubuwan nan da suka faru?”
“Wallahi ban sake ba, ni ko hanyar masarautar ban sake bi ba, amman da yanzu zan je na ji dalilin kiran”
“Aa karka je, baka sani ba ko wani abun ne aka shirya maka”
“Idan ban je ba ai wulakanci za su min, kara naje na ji ko minene dai”
“Allah ya tsare, muna ta zancensu aje suna kan hanya da wani kiran, Allah yasa wannan kiran alheri ne, ya tsare”
“Ameen”
Ya amsa sannan ya shiga dakinsa ya canja tufafin jikinsa daga karamin wando da vest zuwa dogon wando ta jallabiya. Ya fito zuwa waje, har bakin kofar waje Anti ta bishi tana kallo tana jifarsa da addu'a kariya. Daidaikun mutanen da suke waje ne suka rika binsa da kallon ganin dogarawan sanye da tufafi har su uku kuma ga sy da mota mai kyau sun saka Sardauna a gaba. Sai da yai addu'a sannan ya shiga motar suma suka shiga mai tukin yai ribas suka juya. Ba su faka a ko'ina ba sai cikin masarautar, sai dai hankalin Sardauna ya dan kwanta ganin a bangaren Ammy suka faka ba bangaren Hajiya ba. A cikin motar suka bar shi har sai da dayan ya fita ya shiga ciki ya fito sannan ya bude masa motar.
“Fito”
Sardauna ya fito da tunani kala kala, sai dai zuciyarsa ta fi raya masa cewar Ammy zata masa tambayoyi ne akan abubuwan da suka faru, ko kuma Nana ce ta saka a dauko shi saboda tana son ganinsa wata kila ita ma ta yi missing dinsa kamar yadda yai nata. A dakin aje baki na musamman aka kaishi na bangaren Ammy, har ya zauna saman kujera sai kuma wata zuciyar ta raya masa ya zauna kasa kamar ko wane talaka. Cikin mintunan da ba su fi talatin ba hadimai suka jera masa kayan marmari ta soyayen namam kaza da na rago ga farfesun kayan ciki, ga jalof ta ji kayan lambu da kayan ciki sai kamshi take, a gafe daya kuma ga kayan sanyi da plates an aje masa.
“Ammy ta ci ka ci abinci kamin ta fito”
Dayat hadimar ta fada sannan suka fice tare da sauran, at first ji yai kamar mafarki yake, tun a kawo shi falon dake cike da kayan alatu da akai kadai ya isa ya sanar masa cewar kiran alheri ne ake masa, balle kuma yanzu da aka kawata zuciyarsa da abubuwan da take so, baki yai arba da abubuwan da suka dade ba su ga juna ba.
“Ammy suke nufi ko Nana dai?”
Ta tambaya kansa cike da kwankwanto, har ga Allah yana son duka abubuwan da aka jera masa sai dai a karon farko ya samu kansa da kasa taba komai, a tunaninsa a zuwa yanzu ya kamata ya rika kawar da kai akan wasu abubuwan musamman wadanda za su zubar masa da kima. Gorar ruwan kawai ya bude ya sha, shi ma saboda ya samu ya jika makoshinsa ne. Ya kusan awa daya a dakin sannan aka turo kofar dakin wata hadima ce a gaba wanda ta rikewa Ammy kofar ta shigo ta zauna a kujerar dake fuskantar Sardauna. Cikin natsuwa Ammy ta zauna tana kallon Sardauna, wanda ya sadda kai kasa ya kasa dagowa ya kalleta, sai kokarin risinawa yai yana mika mata gaisuwa irin gaisuwar da be taba yi ma wani ba.
“Lafiya Kalau”
Ammy ta amsa masa da kanta tana dagawa Hadimar dake kokarin amsawa a madadinta.
“Je ki kira min Nana”
“An gama ranki ya dade”
Hadimar ta juya da sauri ta fice, Ammy ta kalli Sardauna da duba irin na tsanaki ta ce
“Ya sunanka ma?”
“Ahmad Abubakar, amman anfi sanina da Sardauna Hajiya”
Ya amsa mata da sauri yana jin faduwar gaban da ba ta tsoro ko shakka ba face kwarjini da jin kunyar Ammy.
“Yayi kyau, Nana na fada mana abun da kai, kuma na jidadi sosai na yaba”
Ammy ta fada sai kuma yai shiru tana kara sanar da shi isa da izza irin ta matan sarakuna.
“Akwai aikin da kake a yanzu?”
Kamin ya bata amsa Nana ta turo kofar dakin ta shigo, wani irin jan numfashi tai tana zaro da sauri taje kusa da Ammy ta zauna can kuma ta ji zaman be mata ba ta rumgume Ammy tana jin kamar ta je ta rumgume Sardauna, bata tabbatar ta yi missing dinsa sosa ba sai a yau da tai arba da fuskarsa.
“Aa bana aikin komai a yanzu gaskiya”
Ammy ta yi shiru tana karantar natsuwarsa.
“Ka yi karatu?”
“Eh na yi diploma”
“Kana son ka cigaba?”
“Ina so ranki ya dade, burina kenan”
After some sec Ammy ta ce.
“Wace makaranta kake so? Ko kuma aiki kake so?”
“Idan zan samu karatun na fi son sa gaskiya, kuma ba ni da zabi duk inda na samu damar cigaba da karatu zan yi farinciki”
“Zaka iya karatu a waje?”
Sardauna be san lokacin da ya dago ya kalli Ammy ba, sai kuma ya kalli Nana wanda ita ma kallon Ammy take da mamaki.
“Zazzzazzz.....zan iya”
“To zamu bincika maka best universities da suke waje, inshallah zam dauki nauyin karatunka sai ka kawo takardunka da wuri”
Da sauri Nana ta rumgume Ammy tana murna, Sardauna kam mantawa yai ya mike tsaye sai kuma ya fadi zaune kamar ta rude, i cant believe ba mafarki yake ba. Take a gurin yai ma Allah sujada godiya ya dago da hawaye a fuskarsa yana kallon Ammy.
“Na gode na gode na gode, Wallahi ban san abun da zan fada ba zan san iya addu'ar da zan miki ba, na gode Allah ya biyaki da aljanna”
“Ni ma na gode, ka cancanci komai daga garemu, bayan shi akwai abun da kake so?”
“Kin gama min komai Hajiya”
Sardauna na fada har lokacin idonsa na cike da hawaye. Nana ta yi karaf tace.
“Aa Ammy, ba ki gama ba, a gidan Yayarsa yake zaune kuma gidan duk ya lalace, aAmmy dan Allah ki yi wani abu”
“Wannan kuma za a sanarwa Mai Martaba, na san zai yi wani abu akai inshallah”
Nana ta sake rumgume ta tana murna.
“Thank You so much Ammy na gode”
Ammy ta yi murmushi, Sardauna ma murmushi yake yana kallon Ammy yana jin kamar ace yana da damar da zai rumgume ta saboda murna da jindadin abun da tai masa.
***
Kamar yadda suka tsara washe garin ranar Bappa da Kawu Dan iroro suka shirya suka tafi Katsina, bayan mota ta sauke su suka tari napep suka fada mata inda zata kaisu, wato unguwar su Shattima har ba kin gate din gidan Mai Napep din ya sauke su, sai da suka kira Shattima ya sanar musu yana cikin gidan sannan suka sallami mai napep, suna waje tsaye mai gadin ya bude gate din ya shiga da su, shi yai musu iso har cikin falon Shattima, kallon kallo Bappa da kawu suka rika da ma juna kamin su koma kallon tsarin falon da uban dukiyar da aka zuba.
Shattima ya sauko sanye da manyan kaya shadda da hula sai kamshi yake zubawa kamar wani sabon ango, da kansa ya dauko musu lemu sannan yai musu izinin zaman kan kujerar tsabanin kasa da suke zaune. Kalamai na natsuwa da mutuntawa yake musu duk tambayar da suka masa sai ya basu amsa, daga karshe ya kira Ammy video call ya ce ta saka akaiwa Fadime saboda kawai su yarda da shi kuma su samu natsuwa. Ganin Fadime a video call din ya tabbatarwa su Bappa gaskiyarsa, tana jin muryar Bappa ta hau murna tana jindadin jin muryar mahaifinta duk da kasancewar bata ganinsa hakuri ta hau bashi tana ta kuka da hawaye sai fadin take ya zo ya dauke ta.
Bayan sun gama Shattima ya karba yana ta kallon fuskarta ba tare da yace mata komai ba, sannan ya kashe wayar. Da kansa ya tabbatar musu cewar zai siye musu tickets na jirgi na zuwa can Yola din tare da shi, har waje ya rakosu ya saka direbansa ta kaisu har garin Bandalo bayan yayi musu kyauta 100k.
Cikin far'a da jindadi suka isa gida suna da godiya ta sakawa Shattima albarka da yaba halinsa. Tun a daren ranar Shattima ya siya musu tickets kuma ya kira Bappa ya fada masa cewar ya shirya da safe zai aiko direbansa ya dauke su, washe gari tun 6am direban Shattima ya kama hanyar zuwa garin Bandalo dan dauko su Bappa ko da ya isa har sun shirya, suka shiga motar ya juyo da su zuwa Katsina, maimakon a wuce da su airport sai da aka fara biyawa da su gidan Shattima suka karya da lafiyayen abincin da yai musu order sannan suka shiga wata motar ta alfarma tare da shi zuwa airport.
Ba su wuce 30 min da isa airport din ba jirginsu ya tashi zuwa Yola...
FALMATA POV.
Bata yarda da gaske auren za a mata ba sai da aka saka ta lalle gidansu ya cika da mutanen na bangaren Baba da Mamanta, sai dai duk wanda ya ganta ya kuma san yanayinta ya san bata maraba da auren ganin irin damuwar da ta shiga wanda ta haddasa mata rashin iya cin abinci, sai yawan kuka da tagumi, idan aka tambaye ta tace babu komai bata, babu yadda kanen mahaifiyarta ba su yi ba, akan ta fada musu idan bata son aure amman ta ki tace komai, Tumba kam sai karew take har da fadin wai ita ta kawo shi da kanta tace tana sonsa. Kudin da ya bata yace a siya mata kaya sai ta siyo mta atamfar roba 5 sai talkama da yan tarkace kamar budurwar kauye.
Tana jin yadda yan uwan suke labarin gyara gidan da suke je suka gani wanda za a kaita sai yabawa suke suna fadar ya gyara mata abunta ba laifi, suna ta saka masa albarka saboda yace baya son komai, gashi yayi duk wani kokari da ake na al'ada daidai gwargwado, sai dai abun da ya bawa kowa mamaki cewar da yai baya son tai walima a nan sai washe garin ranar da ta tare, wani abun da ya kara bawa Falmata haushi da bakinciki ko ganinsa sau daya tai be sake zuwa ba, sai dai yace yana gaisheta. Sai wasu mutanen da suke zuwa da sunan danginsa kana ganinsu ka san su ma ya ku bayi ne, masu neman a gurin Allah.
Ranar yau ta kama friday ranar da ake daurin aurenta, irin ranar da wasu mata sa'o'in suke jira suke dakon zuwanta, sai dai ita a gareta ta zama kamar ranar mutuwa ce, tana jinta kamar ranar da ta fi ko wace rana bakinciki ce a gurinta, tana jin cewar zata bar wata wahalar ne ta fuskanci wata, taya zata yi rayuwa da tsoho? Samun kanta tai da kuka tun safe ta kasa karyawa da komai har sai da Tumba ta jata gefe tana mata masifa.
“Wai Falmata so kike ace auren dole aka miki ne? So kike a fara zaginmu ni da mahaifinki? Me ke damunki wai? Kina ta kuka kamar wance aka cewa ga mutuwa? Aure ai abun so ne, kamata tai ki yi murna ki yi farinciki Allah ya kaiki gaba, kuma wata kila ma b dadewa zaki ba ya mutu tun da ya tsufa, idan kika tonawa babanki asiri ke da shi ne ni ba ruwana”
Jin haka yasa Falmata ta dago ta kalli Tumba.
“Umma da gaske auren min zaku min?”
“Gashi kina gani anjima za a daura aure? Ko so kike a fasa? Tsab Malam zai iya tsine miki Wallahi”
Falmata ta share hawayenta wasu na sauko mata ta bar Tumba a gurin tsaye ta nufi dakinsu, guri ta samu can karshen shimfidarsu