Showing 222001 words to 225000 words out of 273152 words
Chapter 75 - FULANI BOOK COMPLETE DOCUMENT by Khadijah Candy .txt
ya fito, be kuma koma gurin Hajiya Babba ba sai ya wuce gidansa ya kwana a can. A harabar gidan ya faka motarsa, ya bude gurin da yake aje paper, ya dauko diary ya dauko bironsa, sai ya dora kansa saman sitiyarin motar ya yana hawaye yana jin zuciyarsa kamar zata rabe gida biyu. Sai dai ba shi da zabin da ya wuce haka, sai dai har ga Allah baya son sakin Falmata. Dago kansa yai ya runtse ido ya cige bakinsa hawaye na cigaba da sauko masa, daker ya bude idon ya bude diary ya dora hannunsa dake rawa yai rubutu a jiki, sai ya fashe da kuka kamar ba namiji ba. Sai kuma yai sauri zarar tissue ya goge fuskarsa ya cire paper da yai rubutun a jiki ya bude motar ya fita. Brown jallabiya ce jikinsa kana ganinsa ka san yayi kuka ba kadan ba domin idonsa da farar fuskarsa ya nuna, sai da ya sauke ajiyar zuciya ya fi a kirga sannan ya nufi entrance din ya fara takawa har ya isa gaban kofar falon, wasu hawayen ne suka cika masa ido sai yai saurin sharewa ya danna door bell din. Babu bata lokaci Momy ta bude masa kofar daman tana zaune falo cikin shirinta na tafiya office domin duty safe take.
“Sirleem Lafiya?”
Sai ya kasa kallonta kuma ya kasa ce mata komai har ta ba shi hanya ya shigo cikin falon.
“Ina Falmata?”
Ya tambaya daker tana danne numfashinsa dake fisga.
“Tana sama, wai me ke faruwa ne? Tun jiya bata ci komai ba ko tea da na kai mata da safen nan bata sha ba, ni ban gane komai ba kuma...”
Kamar zata labarta masa zancen Ameer, sai kuma tai shiru ganin kamar be dace tai maganar ba a irin wannan lokacin da damuwa da samu muhalli a fuskar Sirleem. Be ce ma Momy komai ba ya nufi upstairs din zuwa kamar baya som tafiya, Momy dai ta bishi da kallo har ya haye sama ya shiga dakin Ameer inda Falmata take.
Yana shigowa Falmata ta mike tsaye da sauri tana kallonsa, shi ma kallonta yake sai hawaye suka samu hanya a idonsa, tana ganin haka jikinta yai sanyi sai ta hade hannayenta guri daya nata idanuwan suna ma hawayenta lalle marhabun. Takawa tai ya karasa kusa da ita yana kallonta sai kuma ya rasa abun da zai fada mata, ita ma kallonsa take tana hawaye daman ta dade da raya cewar Hajiya zata cilasta shi ya sake ta.
“Ka sake ki Sirleem matukar sakina zai saka Hajiya ta yafe maka, ka sake ni matukar sakina zai shirya tsakaninku da Hajiya...”
Ta fada ararrabe saboda kukan da ke cinta. Kansa ya daga sama ya kalli pop tare da jan numfashi ya sauke, sannan ya sauke idonsa a kanta, cike da nauyin kafa ya cira ya taka zuwa inda take tsaye sai ya rumgume ta tsantsan a kirjinsa kamar zai sakata cikin jikinsa, hakan da yai sai ya bata damar fashe kurjin kukan da da ya girma yai kumbura a zuciyarta, ta dago hannayenta ta rike rigarsa saitin kirjinsa tana ta kuka kamar ranta zai fita, shi ma hawayen yake sai daya jika dankwalin kanta.
“I love you, Sirleem Love you so much”
Ya furta cikin muryar mai karkarwar kuka, sannan ya hade yawun bakinsa ya sake ta ya kama hannunta ya danka mata takarda, karba tai tana wani irin dauke numfashi tana kallon fuskarsa tai baya baya sai ya juya da sauri domin ba ya son hada ido da ita, cikin hanzari ta kai hannunta ta kamo hannunsa.
“Sirleem karka bar ni dan Allah, idan ka tafi ban san ya zan kasance ba, kai ka kadai ne gata a yanzu kai ne rayuwata...”
Ta fada tana jin wanin irin yanayi da bata taba jin kanta a ciki ba, idonta har wani hayaki suke.
“Ni kuma mahaifiyata ita ce rayuwata, ba zan iya jabar ki na bar mahaifiyata ba, ban taba ganin Hajiya a irin halin da na ganta a yau ba, ba zan jama silar bakincikinta ba...”
Ya saka dayan hannunsa ya banbanre hannunta da ta rike hannunsa na dama da shi, ya fice daga dakin cikin sauri. Faduwa tai kasa tana wasu kalar hawaye masu zafi da kona fuska sai ta matse jikinta ta rumgume kanta tsantsa, ta sauke idonta akan hoton mahaifiyarta.
“Ma... Ma... Ma... Mama...”
Ta furta daker muryarta na rawa, wani irin abu ta ji kamar zuciyarta zata kone mata kirji, faduwa tai durkushe ta kasa yarda Sirleem ya rabu da ita a lokacin da ta fi tsananin bukatarsa. Mikewa tai tsaye ta fita dakin da gudu, yadda ta sauko downstairs din ma sai da ya ba Momy tsoro kamar zata tashi sama haka ta nufi kofar falon ta bude, ta bi motar Sirleem dake kokarin fita gate tana wani irin kuka tana kiran sunansa.
“Sirleem.... Sirleem.... Sirlee....”
Bata karasa sakamakon shakewar da muryarta tai sai ta fadi a harabar ta fashe da matsanaicin kuka. Momy ta fito da sauri ta yo kan Falmata ta kamata.
“Lafiya?”
Kamar mai jira sai ta juyo da sauri ta kama hannayen Momy ta rike gangam.
“Momy ya sake ni, Sirleem ya tafi ya bar ni dan Allah Momy ki ce ya dawo...”
“Innalillahi Wa'inna Ilaihirraji'un”
Momy ta furta cikin rudani da rashin fahimta. Sirleem ma tukin yake yana hawaye yana jin jikinsa kamar ba shi ba numfashinsa har kokuwa yake da shi.
Ina mata wadan da suke son sayen kaya kamar su laces, atamfa, materials,shadda lace, normal shadda, atamfa lace, veil's, shoes and bags, da sauransu kuzo ga MAMAN AHMAD tazo dan tashare hawayenku kudai kunemeta ta wannan number 08032350261 banan kadai tatsayaba tanada kayan order kama dana kitchen,tufafi,kuma order ta Bata dadewa ,tana saida kayan gyara kamar su Al'ajabu,shu'umar humra wannan inbakida aure Bama saida maki,hadin kaza me yasin,akwai na mallaka wanda wannan ana rubuta shi atafin hannu ke zakiyi wannan,turaren wuta,kulacca,da sauransu
Mazauninsu nanan a samaru Gusau Zamfara state
Muna aika kaya kowace jaha da wajen kasar nan cikin aminci da yardar Allah kunememu kusha mamaki
https://wa.me/qr/MYY56BH3RMFDG1
03/12/2021, 18:59 - 🤐🤐🤐🤐: *Khadeeja Candy*
Tana yunkurin ta tashi sai ta ji cikin ya mata nauyi kamar an jefa mata katon dutse a ciki, da farko ta yi tsammanin ko dan ta cinye naman ne duka duk da ta san bata saba haka ba, ko mugun ci tai yana da wahala ta gagara tashi. Jinginawa tai da gadon tana dan hutawa na mintuna kamin ta sake yunkura ta ji ya fi na dazun nauyin gashi ba ciwo yake mata ba. Kallon cikin tai da mamaki yana da da girmansa kamar da, amman ya mata nauyin da bata isa ta mike tsaye ba. Hannunta ta kai ta bude rigarta tana duba cikin.
“Aa wai ya haka ne?”
Ta tambayi kanta tambayar da bata da amsa, sai kuma ta rufe cikin ta sake mika dukan karfinta ta yunkura ta tashi nan ma ta kasa, ta sake yunkurawa a karo na hudu nan ma dai ta kasa tashin.
“Ma ke faru da ni?”
Ta sake tambayar kanta, kamin ta sake yunkurawa sai ta ji nauyin ya sake karuwa fiye da dazun ma, shiru tai tana ta tunanin dalilin faruwar hakan a gareta bayan taba taba hakan ba, sam ba ta kawo cewar saboda ta ci kurwar Maijidda ba ne, har sai da ta ji kankarun dake cikinta na maita sun fara mata motsi, a firgice ta kai hannu ta dafa cikin tana zaro ido.
“Miye haka kuma? Miyasa na ke jin haka yanzu yanzu?”
Kadan kadan suke motsa mata sai kuma su tsaya, sau uku suna mata wasa a ciki sannan ta ji abun ya tsaya mata, a nan ta sake yunkurawa da dukan karfinta sai gata ta mike a tsaye nauyin da take ji duk ya daina ta koma normal kamar da, sai dai mamaki be bar ta domin bata taba yin haka ba kuma bata yi tunanin akwai wani abu da zai saka ta tai haka ba.
Kwantawa tai saman gadon tana ta tunani kala kala, wata zuciyar na raya mata wata kila iyayen Maijidda sun bata magani mai karfi ne ta sha bayan ta kama kurwarta shiyasa ta ji haka, wata kila kuma wani izon ne akai mata, da wannan tunanin bachi yai gaba da ita, ta kwashi bachinta mai dadi har sai da ta hatse bata barka ba sai kusan la'asar, kamar wanda ta tuna wani abu haka ta sauko saman gadon da sauri.
Bandaki ta shiga tai wanka da ruwan sanyi duk da kasancewar akwai sanyi sanyin hadari a garin, tana fitowa bata ko tsaya shafa komai bata saka wasu tufafin ta dauki tsohon gyalenta ta yafa ta saka talkami ta fito ta shiga dakin Zainab. Kwance ta same ta ruf da ciki tana ta aikin kuka.
“Wai ke yaushe za ki daina kukan nan ne?”
Zainab ta dago ta juyo tana kallonta da idanuwanta da sukai ja sosai saboda kuka.
“Babu rana, domin babu ranar da bakincikin nan nawa zai gushe, dan haka babu ranar da wadannan hawayen za su tsaya”
Iya ta tabe baki tana mamakin yadda Zainab take son wahalar da kanta.
“To idan kin gama kuka sai ki ta tafi gidan Waziri ayi gaisuwa da ke”
Zainab ta tashi zaune da sauri tana kallon Iya cike da mamaki.
“Waya rasu?”
“Maijidda yar wajen Hajiya Talatu”
Baki sake Zainab take kallon.
“Maijidda matar za a aurawa Shattima? Yar wajen Baba Waziri?”
“Ita fa, rai yai halinsa kin san kowa da lokacinsa”
“Waya fada miki ta rasu?”
Iya ta dauke kai ta juya ta fita ba tare da tace komai ba. Zainab na ganin hakan tai saurin saukowa saman gadon ta biyo bayanta
“Hakan na nufin ke kika kasheta kenan?”
Iya ta juyo ta kalleta.
“Duk abun da zuciyarki ta raya miki ki dauka shi din ne, domin ba zan iya wanke kaina daga zarginki ba”
“Ba zargi na ke ba, na san ai ke ce, amman ban yi tsammanin za ki sake aikata irin wannan abun ba, ko dan halin da na shiga, ammn hakan be dame ki ba, bayan duk zargi da kyamar da aka fara nuna mana? Kuma yanzu duk wannan be dame ki ba? Har zaki iya takawa ki je musu gaisuwa? Iya ke wace irin halittace?”
Zainab ta karasa cikin kuka.
“Idan ban tafi ba ai su ma sai su zarge ni kamar ke, kara na shiga ayi komai da ni, na watsar da komai nawa yanzu babu ruwana da wani Shattima balle danginsa har ta kai ga matar da zai aura, idan kim ga dama ke ma ki zo ki musu gaisuwa, domin babu ruwan Hajiya Talatu da abubuwan da suka faru bata mana komai ba”
Zainab ta share hawayenta cikin wani irin bakinciki da takaici marar misaltuwa.
“Ba zan zo ba, kuma ba za ki dawo ki same ni ba”
Tana kaiwa nan ta juya ta shige dakinta, Iya kam bata ce komai ba ta saka kafata ta fice daga gidan, a tunaninta Zainab ta yi hakan ne kawai saboda ta hana ta tafiya. Jikin window Zainab ta tsaya tana kallon Iya har ta fice daga gate din da mai gadin ya bude mata.
“Ya isa haka yanzu kan, komai ya kare”
Ta juya cikin damuwa ta fice daga dakin ta shiga dakin Iya, wardrobe dinta ta bude ta soma bincikar kayanta har ta kai gurin atamfar da ta nade tukunyar tsafinta ciki, dauko dankwalin tai ta bude ta fiddo tukunyar tana kallo jikinta sai rawa yake, sai da ta hade yawu sannan ta dora tukunyar a saman gadon Iya tana ta jin tsoro. Can kuma ta tashi ta nufi wardrobe din tana ta kara dubawa ko zata ga wani abun, sai da ta zazzage komai na ciki ta duba bata ga komai ba, sai ta koma gurin da take yan komatsanta wato karkashin gadonta ta soma janyo abubuwan da suke nan, yawanci duk kayan cin abinci ne sai yan ledodi da talkalmi, mikewa tai tsaye ta dage katifar ta yadda zata ga komai, sannan ta dawo tana ta bude bude kwanonon, har ta bude kwanon da Iya ta zuba naman Maijidda a ciki, ganin maskin yasa ta dauka ta shinshina tana mamakin na inda ta samu nama domin ita har yau bata san ta kan maitar ba balle ta san Iya na cin kurwa ne, a tunaninta kashewa kawai take. Aje kwanon tai ta bude wani babu komai a ciki ta sake budewa shi ma wayam, hka ta rika budewa duk wani abu mai murfi ta kai ga kitsen da iya ta aje, shi ma shinshinawa tai ta aje tana mamakin inda ta samu nama ta soya ta cinye ba ta bata ba, bayan bata saba mata haka ba. Hannunta ta kai ta bude kwaryar dake rufe da faifai sai tai arba da aci balbal a ciki na gwangwani sai tsohuwar kaya da allurar, allurar ta fara dauka ta duba zuciyarta na raya mata cewar wata kila iya na tsafi da ita ne, sannan ta dauko kayar ita ma ta duba har ta yi baki sabar tsufan da tai.
“Me take da wannan abubuwan kuma?”
Ta tambayi kanta tana kallon kayar cike da kyankyami, daukarsu tai ta je ta shiga bandakin Iya ta jefasu a ciki, sannan ta fito ta dauki tukunyar dake saman gadon tana dubawa. Tukunyar kasa ce da aka rufe bakinta da jan kyalle, sai da tai kamar ta bude kyalle ta gani ko miye a ciki sai wata zuciyar ta hana ta, daga tukunyar tai sama ta buga ta da kasan tile din iya karfinta. Take rukunyar ta watse kasa sai ga wani dan karamin maciji a ciki mai kai biyu. Wani ihun tsalle Zainab da daka tare da saka ihu ta ta ranta a ana kare sai waje. Mai gadin na ganinta ya mike tsaye da sauri yana tambayar ba'asi.
“Hajiya Lafiya?”
“Maciji dakin Iya”
“Maciji kuma ta ina ya bi”
“Oho je ka kashe shi dan Allah”
“Kai ai sai dai a kira mutane, ina ni ina kashe maciji wani ma aljani ne, ai shiyasa ake cewa kar mu yi saurin kasu su mu hada su da Allah su tafi”
Ko kamin ya gama maganar Zainab ta bude gate din ta fita daga gidan gaba daya, shi ma binta yai gurin neman mutanen da za su kashe macijin, ba su wahalar samun zaratan maza ba domin unguwar akwai manyan samari duk da kasancewarta sabuwar unguwa, har cikin gidan suka shiga Zainab ta tsaya daga waje tana fada musu inda dakin Iya yake, daga bakin kofa suka tsaya suna dubawa ba su koma ba hakan yasa suka fara yamutsa dakin ko za su ga inda macijin ya boya, tun suna yi da dan tsoro tsor har su kao ma dakin daidai ba su ga komai ba, hakan yasa suka fara tunanin ko ya fito falo ne duk da kasancewar falon babu wani guri da zai iya buya, amman a haka suka rika duba ko'ina har kasan kujerun, har cikin kicin ba su ga komai ba. Daya daga cikinsu ya zo yana tambayar Zainab.
“Amman ke kin ga macijin da idonki? Ko kuma tsoro dai kika ji?”
“Na ganshi Wallahi da idona”
“Abun mamaki ni ban ma ta inda zai iya shigowa ba, ko ban dakin ban ga wata hanya da zai iya biyowa ba”
“Wani lokacin a sabon gida ana samun irin haka gaskiya, domin iskokai suna haka, ko a gidansu Najeeb an yi musu haka kamin su samu zama lafiya”
Dayan ya fada, maganar da yai sai ya saka Zainab ta tuna cewar tukunyar da ta fashe ta tsafi ce wata kila macijin aljani ba macijin gaske ba.
“Sai dai idan iskan ne kamar yadda ka fada, amman dai ni na san na ga maciji gaskiya”
“To sai dai ayi ta addu'a Allah ya tsare gaba”
Amin din ma ta ji ba zata iya amsawa ba balle tace musuta gode, haka ta bi su da ido har suka fice sannan ta dawo kusa da dakin mai gadi ta zauna tana ta tunanin yadda zata koma cikin gidan.
********
Kusan kofar gate din gida biyu dake gefen na Baba Waziri dama da hagu fake suke manyan motoci na alfarma saboda rasuwar Maijidda, domin mutuwa mai ban tsaro duk wanda ya ji Maijidda ta rasu sai yayi mamaki domin ba a san ta yi ciwo ba sai idan na kusa da ita ya fada cewar ta kwana a asibiti da zazzabin taifot, hakan yasa har wandanda ba su san ta ba jin cewar budurwa ce suke zuwa gaisuwa, daman kuma Baba Waziri mutumen mutane ne, ta ko'ina zuwa ake masa gaisuwa ga familyn Hajiya Talatu da Hajiya Maryam su ma sai zuwa suke kamar an turosu, yan uwa abokai da suruku kai ma sai zuwa suke.
Sai dai abun da kewa kowa tausayi shi ne Hajiya Talatu da ke ta shikar dariya ta fita hankali, sai kuma ta hada ta waka, duk wani abun da ta gani sai ta fade shi tace na jiya, hakan yasa aka sake maida ita a dakin aka rufe har sai da aka dawo daga kai Maijidda a gidanta na gaskiya, sannan Baba Waziri ya bada izinin a janyo mota a sakata a ciki a kaita asibiti.
Ana fitowa da ita duk abun da ta gani sai ta ce.
“Kai wando na njiya? Ke riga ta jiya? Takalmi na jiya? Hijabi na jiya? Kai mota ta jiya, fulawa ta jiya... Fadime ta jiya, Falmata ma ta jiya, Sardauna ma na jiya, Jarma ma na jiya, Shattima ma na jiya, ga Ammy ta jiya, ga Nana ma ta jiya, kai Jurry ma ta jiya, Mai Martaba na jiya, Hajiya Babba ta jiya...”
Komai ta gani sai ta fada ta ce na jiya, idan kuma bata fadi wani abun ba to zata kama sunanyen mutanen da suke ranta tana fada sai kuma ta bushe da dariya, sai dai babu wanda ya kawo komai a ransa kowa yana tunanin mutuwar Maijidda ne ya taba ta, haka aka sakata a mota aka nufi asibiti da ita yaranta sai kuke suke, ga mutuwar yar'uwa ga rashin lafiyar uwa.
Ana kiraye kirayen sallah la'asar mai napep ya sauke Iya gida na biyu kamin gidan Waziri, sai da ta fito sannan ta ba shi kudinshi tana jin jikinta na wani tsam tsam tsam kamar ba lafiya ba, habar zanenta ta kamo ta kai a idonta tana murzawa