Showing 144001 words to 147000 words out of 273152 words

Chapter 49 - FULANI BOOK COMPLETE DOCUMENT by Khadijah Candy .txt

29 Aug 2024

72756

same ki dole nai nisa da ke, zan yi marmarkin kuma zan rika ziyartar ta hanyar da be zama lallai ki gan ni ba”


Juyawa tai a hankali tana karewa guri kallo, sai a lokacin ta gane inda take, bayan gidansu na zana ne ya aje ta da inda gonaki suke, gashi safiya ce babu wanda zai ganta. Hannunsa ya kai ya kama fuskarta yana kallon cikin idanuwanta.


“Kina na raka ki gurin babanki nai masa bayani?”


“Kam Wallahi ubana zai ci, ka tafiyar ka dai”


“Bana son babanki ya doke ki”


Ta yi shiru tana tunanin irin hukuncin da Bappa zai mata. Can kuma ta kalli Wasim tana tuna abun da ya fada mata.


“Da gaske ba zan sake ganinka ba?”


“Zaki sake amman kamar da ba, kuma be zama lallai Bappa ya barki ki sake fitowa ba”


Sai ta ji wani iri, tausayinsa ya kamata.


“Zan iya satar kafa na fito ba?”


Ya daga kansa sama yana murmushi kamin ya sake kallonta.


“Ba kin ce ba zaki sake kin jin magana ba?”


Sai tai shiru tana kallonsa kamar marar gaskiya.


“Fateme ina son na fada miki wani abu, ki saka a ranki ina kaunarki tun a ranar da na bara ganinki ba tare da kin sani ba, rayuwarki da mu'amalarki tana burge, wannan rawar kan da mutane suke ganin rashin natsuwarki da shi, ni burge ni kike kina saka ni nishadi, ko da baki kusa da ni idan na tuna da ke sai na samu kaina cikin nishadi da marmarin ganinki ina kaunarki sosai Fateme, duk da na san addininmu da al'adarmu ba daya ba ne...”


Tun da ya fara maganar ta ji kanta na juyawa yana wani hayaki, zuciyarta ta buga da mugun karfi for the first time in history wani ya furta yana sonta yana kaunarta tana burgeshi.


“Wayyo zuciyata...”


Ta dafa zuciyar ta fadi kasa zaune dafe da zuciyar dake buga mata da mugun karfi. Risina Wasim yai yana kallonta, suna hada ido sai duk taji ya cika mata idon kunya da nauyinsa sun yi rufeta, sai ta saka hannayenta ta rufe fuskarta tana wani irin murmushi da bata san ta ina yake zuwa mata ba. Ta dade a haka kamin ta bude idon, a zatonta zata ga Wasim ne tsugune a gaban ta kamar dazun sai ta ga babu kowa sai ita kadai. Da sauri ta mike tsaye tana kabe jiki tana waige waige.


“Yau ko na shiga uku ga dadi ga wuya Wallahi sai Bappa ya doke ni”


Ta fashe da kuka, nan da nan ta nemi farincikin furta mata kalmar so da Wasim yai ta rasa, hannanyenta ta saka cikin gashin kanta ta yamutsa gashin kamar wata mahaukaciya, sai ta bi hanyar gida tana wani langadi kamar wacce ta sha giya ta birkice ido kamar ba nata ba. Sai da ta isa bakin kofar sannan ta kwange hannayenta ta fara jan kafa kamar wata musaka haka ta shiga cikin gidan, tana dalalar da yawu kamar gaske. Inna dake zaune gaban murhu tana damu kunu ta shure bokitin kunun da sauri ta nufi gurin shanu tana kiran sunan Allah, Nappa kuma ya fito daga bukkar Inna da sauri yana kallon ikon Allah domin shi ma kansa ya tsorata da yanayinta. Daga bakin kofar Fadime ta fadi kasa tana da nishin karya, can kuma ta fara ashisshawa har uku alamar aljanun sun tafi kenan. Zumut ta tashi zaune tana waige waige.


“A ina nake a ina nake? Bappa ina Inna?”


Bappa dai na tsaye yana kallon ikon Allah tsoro duk ya kama shi, domin be taba ganin Fadime a irin wannan yanayin ba, kuma baya saka ran zata iya irin wannan abun. Inna na jin an kira sunanta ta susuda ta fito cikin tsoro tana leken Fadime.


“Fulani...”


“Na'am Inna”


Ta fashe da kuka, sa sauri Inna ta nufo inda take ita tana kukan murnar ganin yarta ta rumgumeta. Tun batan Fadime bata iya cin abincin kirki ga fadan Bappa ga tashin hankalin da take cikin ga kuma maganganun mutanen kauye dake fadar Fadime ta kai kanta ga halaka, wasu kuma na fadin wai wata ta zo daga birni yar yankan kai ta tafi da Fadime, kowa da da abun da yake fada.


“Ina kika je Fulani?”


Shine abun da ya fito daga bakin Bappa, cikin kuka Fadime ta kankame Inna tana bayanin karya.


“Ban je ko'ina ba Bappa bakin rijiyar can mai gaba dubu kawai na raka wannan matar, sai tace min ita zata kara cikin dajin ta dauki hoto, ni kuma na tsaya ina leken rijiyar sai na hango wani tsoho cikin rijiyar yana kallo sai cewa yai ke ce Fadime ko? To zan dauki fansa abun da Bappa ki yai min a bakin kasuwa, lallai sai Sama'ila ya dandana kudarsa, da ke zan fara amman zan zo kansa shi ma, sai na juyo da gudu daga nan ban sake sanin inda nake ba sai yanzu a ganni a nan....”


Ta kara fashewa da kuka, gaba daya sai jikin Bappa yai sanyi, karyar data tsara sai ta shiga cikin kwakwalwar Bappa tai zaune ras, jin an ambaci bakin kasuwa gurin da yake neman halalinsa, duk da dai ya san shi ba mafadaci ba ne, sai dai dan adam tara ne be cika goma ba, zai iya yiyuwa ya tsabawa wani cikin rashin sani kuma ya kasance ba mutum ba ne.
Sai dai abun mamaki miyasa wacan matar bata dawo ba, kuma police din da suka ce zasu je gobe su dawo su ma ba su dawo ba? Ga tufafin jikinta ba kalar na su ne na fulani ba, to kodai ita ma matar da police din duka aljannu ne.? Gaba daya sai Bappa ya rasa wanne zai yi tunani, wata zuciyar tana kin bashi hadin kan yardar da maganar Fadime, sai dai kuma ya san bata san kowa a wacan garin ba balle yace a can suka tafi tare da matar, amman idan ita matar ce ta tafi da ita fa? Kamin yai wani yunkura har mutane sun cika gidan suna ta yi ma Inna barka da dawowa Fadime, irin karyar da tai ma Bappa ta dora Inna tana ta fadawa mutane haka, kowa sai fadar albarkacin bakinsa yake, wasu sun yarda wasu kuma su karyarta abun a zuciyarsu. Har mazan da basu yi sammakon fita ba suka rika sallamawa Bappa suna masa barka da arziki. Inna da kanta ta hadawa Fadime ruwan wanka Fadime ta shiga tai wanka ta fito ta shiga bukkarta ta saka wasu tufafin tana ta tunanin Wasim, ta kasa daina murmushi kuma gabanta ya ki ya daina faduwa kan abunda ya fada mata a yau, da zarar ta tuna sai ta ji kunya duk ta rufe ta kamar yana gabanta yana kallonta.
Inna ce ta shigo cikin dakin ta aje mata sabuwar fura da ta ji nono ta fice tana amsa kiran da Bappa ke mata.
Fadime ta dauki furar ta sha cike da marmari sai kace wanda ta shekara goma bata gida sai a yanzu take jin sakewa nishadi. Sai da ta sha furar sosai sannan ta dauko jakar littafanta ta bude ta dauko littafin da take rubuta ta fara sana'arta wato rubuta abubuwan da suka faru tun farkon zuwanta garinsu Wasim.
Tana tsaka da rubutun sai ga duhu ya maye ko'ina na dakin, kamar an dauke wutar nepa da dare haka idanuwanta suka cika da duhu ta ko'ina kai kace ba 11am ba ce.


“Inna ranar ta dauke ne?”


Ta tambaya tana murza ido, kamin ta mike tsaye rike da littafin tana lalaben hanya.


“Wayyo na boni... Wayyo.... Wayyo... ”














FALMATA POV.


Gaba daya jin tai duniyar na juya mata idan za ta yi tunani sai ta rasa ta inda zata fara, miyasa za a aura mata tsoho? Hakan na nufin an kashe mata rayuwa kenan gaba daya.
A yanzu kam ta yarda bata da wani buri da zai cika, bata da wata dama na yin komai ciki har da na zabin wanda take so, ta ya zata rayu da tsohon mutumen da ya tsofi mahaifinta? Mutumen da bata taba ganinsa ba sai jiya? Idan bata amince ba tana da wani zabin ne? Ta isa ta musawa mahaifinta ne balle kuma Tumba da take tsoro?
Bayan gargadin da Tumba tai mata jiya cewar idan ta ki amincewa zai iya korarta, idan ya koreta ina zata tafi? Wa zai karbeta? Ya rayuwarta zata kasance? Idan ta tuna wani bangaren na rayuwar Mansura da Sirleem ya bata labari sai ta ji bata son kasancewa a irin yanayin! Amman haka zata zuba ido rayuwarta na tafi kullum bata da gata bata da iko akan komai? Tabbas wanda ke da uwa raye kuma ubansa yake kula da shi yayi babban dace, bata tana jin kewar mahaifiyarta ba irin wannan lokacin da ta gama yarda cewar bata da gata. Domin ta tabbatar da ace mamanta tana raye da haka be faru no matter how bad Tumba zata so ta auri mutumen, tana son ta aure shi ne saboda taje ta wahala, da mutumen arziki ne da Naja za a bashi ko kuma a koreshi gaba daya.


Jin kamar yawun bakinta zai shaketa yasa ta tashi zaune hawaye na mata zuba.


“Mama ashe kin hango irin wahalar da zan sha shiyasa kika ce nai hakuri, shiyasa kika ce zaki tai ki bar ni a cikin kunci, kin ce min nasara tana nan tafe, amman har yanzu ban ganta, sai karin wahala”


Ta fada murya kasa kasa tana fashewa da kuka. Can kuma ta yunkura ta tashi tsaye ta nufi kofar dakinsu ta bude ta fita tsakar gidan, gurin da suke ake botocinsu ta nufa ya dauki butar da ta fi alwala da ita zuba mata ruwa ta shiga bandakinsu haka nan cikin duhu tai fitsari sannan ta fito tai alwala a tsakar gidan. Bayan ta gama ta koma dakin ta dauko tabarmar da suke sallah da ita ta shimfida a waje ta saka hijabinta.
Sallah tai raka'a biyu raka'ar farko ta karanta ayatul kursiyu da kulhuwallahu, raka'a ta biyu ta karanta fatiha da kulhuwallahu kafa uku sannan ta zauna tai zaman tahiya, bayan ta sallame ta daga hannunta sama tai fara salati ga annabi salatin ibrahimiya, sannan tai istigari sai kuma ta fara yabo da jinjina ga Allah, ya rabbana ya rabbana ya rabbana sannan ta fara karanta huwallahul lazi la'ilaha.... Har zuwa karshe kalmomin da wasu malamai suka ce sune ismillahul azeem, bayan ta gama ta fara kankantarda kanta tana kuka.


“Ya Allah ya baiwar makaskanciya a cikin bayinka, Ya Allah ga mai yawan aikata sabo mai yawan zunubi, Ya Allah ga mai kaunar Rahamarka mai tsoron azabarka, ba ni da kowa Allah sai kai, gatan da nake da shi naka ne ya mahallicina, ya gata na, ya ubangijina, ya mai jinkaina, Allah ina godiya akan ni'imominka, rahamar a gareni ba zata kirguba, na gode maka Allah, kuma ina kara kawo kuka na a gareka babu mai ba ni sai kai, idan ka hanani wani be isa ya bani ba, Allah yau ma gani da kokon bara, Ya Allah ga Fateema a kasa na daga hannuna a sama ina rokonka, Allah ina cikin damuwa da bakinciki kuma na san ka sani, ba dan ka manta da ni ba, kuma ba ka so na ba, sai dan haka ka rubuta zai same ni, haka ka rubuta rayuwata zata kasance, Allah ya dubi ka tallafi rayuwata ka zame min gata, Allah wannan zabin da mahaifina yai min bana so kuma ka sani, amman Allah ina rokonka idan wannan hadin alheri Allah ka bani ikon bi musu biyayya ka bani ikon dauka kuma ka bani ikon juriya, idan kuma ba alheri ba ne Allah ka musanya min ka canja min kuma karka saka matsalar ta taso daga gareni, Ya Alimu ya Azizu ga gatan marar gata, ya gatan mai gata, ya Ubangijin sammai da kassai....”


Haka ta cigaba da yabon Allah tana fada masa damuwarta, daga karshe ta cika da fatiha ta rufe da salatin Annabi, sannan ta tashi ta koma ciki, tana kwantawa sai ta ji ta samu sa'ida da sakewar zuciya sabanin farkon daren da tunani da kuka ya ki barinta tai bachi. Bata farka ba sai da asuba, ta farka da nauyin zuciya na damuwa da kukan da ta sha kamin ta kwanta domin idonta har ya soma kumbura, sai dai ta nemi bacin ran ta rasa, tana jin bata son mutumem amman bata jin kunci da damuwa kamar na jiya abun ya mata sauki sosai.
Bayan ta gama sallah tai azkar dinta na safe data saba sannan ta dauko qur'ane ta karanta sai da rana ta fara dan bullowa sannan ta rufe qu'anen ta dauko maganinta ta saka a kunne ta saka kada, sannan ta maida ta aje ta fito harabar gidan tana gaishe da Tumba.


“Lafiya kalau”


Ba da wani karfi ta amsa mata ba, amman hakan be hana ta ji ba duk kuwa da kasancewar ta saka kada a kunne. Lumshe ido tai ta bude tana jin wani irin sanyi a ranta, sannan ta mike tsaye ta nufi inda Babanta yake zaune rike da redio asuwaki a bakinsa ta durkusa har kasa ta gaishe shi.


“Baba ina kwana?”


“Lafiya kalau, Tumba ta fada miki sako jiya ko?”


“Eh ta fada min”


“To yayi kyau bana son na sake ganinki da wani a waje, kuma bana son ki samu matsala da mutumen nan”


“To Baba”


Ta amsa sannan ya daga mata hannu ta mike tsaye ta juyo gurin iya tana kallon dumamen tuwon da take yankawa.


“Zan tafi gurin aiki”


“To Allah ya kiyaye, kin san dai Babanki ya hana a baki abinci da sai na zuba miki ko da sanyi ki ci”


“Aa a can nake karyawa ai”


Tumba ta juyo ta kalleta da kyau.


“To ki ce kayan dadi suke baki, shiyasa na ga kin yi kyau jiki sai fitowa yake, kwai kike ci ko?”


Falmata dai ta yi shiru sai kallon yatsun hannunta take.


“Wata dai ya kusa yau sauran kwana biyar kar a baki kudin nan ki taba su, dan na san halinki da keta”


“Ba zan taba ba Umma”


“To Allah ya tsare hanya”


“Ameen”


Ta amsa sannan ta sa kai ta fice daga cikin, fitar ke da wuya Naja ta dawo kusa da Tumba ta risina tana mata magana murya kasa kasa dan kar Baba ta ji.


“Umma da ni aka maida aikin nan, ji fa har zuwa daukarta, kuma Allah kadai ya san dadin da take sha a can”


“Wuyar da take sha dai, wani dadi zata sha? Ke baki masu kudin nan ba? Ai ko kallo bata ishesu ba, kuma rainon yara an fada miki sauki ne da shi? Ita ce kashinsu fitsarinsu da komai na su, kuma idan suka yi kuka ita zata dauke su tana basu hakuri ta ciyarda su, way sani ba ko har wanki take musu, kuma ke da kika karatu? So kike ki lalata karantun na ki ne?”


Cewar Tumba tana tubo baki gabana irin yadda magulmata suke yi idan za su yi magana.


“Gashi ma idan ta fita bata dawowa sai dare, ni ina zan iya wannan”


“To kin gani ki daina wahalar da kanki ma”


Sai da Naja ta saci kallon Baba sannan ta mike tsaye ta bar gurin.


***


A inda mai napep din jiya ya sauke ta ta tsaya, tana ta kwankwanto ko dai ya zo be same ta ba ne ya tafi? Ko kuma yana kan hanyar zuwa ne, domin tun jiya ya fada mata cewar ta rika jiransa a nan, saboda Napep da Mota basa shiga longunsu sai dai achaba. Sai dai tai jiran minti shirin sannan ya iso, daidai ita ya faka ta shiga tana masa ina kwana.


“Lafiya kalau, kin ta jirana ko? Wallahi na tsaya daukar wasu ne, na dauka baki shirya ba”


A nan ta ji abun da ya fada, duk d be daga murya sosai ba, sai ta ji wani irin dadi marar misaltuwa, sai dai tana jin maganar ne kamar daga wata duniya, kamar ana fisgo maganar da karfi aa jefowa kunnenta haka take ji. Sai dai ko kadan hakam be dameta ta san idan ta cigaba da amfani da maganin zata warke ta koma kamar da, daman lafiya raguwa ce da rarrafe take farawa.


“Ni ai tun bakwai nake tafiya”


“Kai kina kokari gaskiya, aikin me kike yi a gidan?”


Rasa tai abun da zata ce masa, Momy dai bata da yara balle tace raino take.


“Aikin gida haka, kuma ina tsare mata gidan saboda tana zuwa aiki”


“Okay. Allah ya taimaka ya sunanki ma?”


“Falmata”


“Falmata ai ba suna ba ne”


“Fateema”


“Ashe ke Mamana ce”


Ta yi dariya kamar yadda yai daga haka bata sake cewa komai ba, har ya isa bakin gate din gidan.


“To Mamana sai kuma na dawo daukarki ko?”


“To Allah ya tsare”


“Ameen”


Yaja Napep dinsa yayi gaba ita kuma ta kwankwasa kofar gate din mai gadin ya bude mata.


“Ina kwana?”


“Lafiya Kalau an iso”


“Eh”


“To madallah”


Ya bude mata gate din ta wuce ciki. Harabar gidan take ta kallo ciki har da wata bakuwar mota da bata taba ganinta a gidan ba. Kamar yadda ta ga Sirleem haka tai bayan ta danna door bell din kuma ta kwankwasa kofar, Momy ce da kanta ta bude mata kofar.


“Ahhh na dauka ma Sirleem ne shiya ko ya miki wannan knocking din ko?”


Ta yi murmushi sai Momy ta matsa mata ta shigo cikin falon.


“Bakowa kika yi”


Cewar Hajiya Umaima tana kallon Falmata.


“Eh to ba bakuwa bace, yata ce tana dan rage min aiki ne”


“Oh Allah sarki”


Cewar Hajiya Umaima tana murzawa yarta Nafiza allurar da akai mata.


“Ki shiga kitchen akwai dankali sai ki firaye, zan zo na dora girkin a gas saboda ki ga yadda ake”


“Tau”


Falmata ta amsa sannan ta mikawa Hajiya Umaima gaisuwa ta nufi kitchen din. Da kallo Hajiya Umaima ta bita har sai da ta shiga sannan ta kalli Momy ta ce.


“Ke kuma haka kawai zuciyarki ta raya miki ki samo mai aiki? Kina zaune kalau ta aure miki miji”


Momy ta yi dariya tana kokarin zama.


“Ah haba dai wannan yarinyar da kika gani bata da matsala Wallahi ko kadan, magana ma be dame ta ba, tana cikin halin rayuwa ne, ni ma ba son me aikin nake ba ai kin sani kawai dai dan na taimaka mata ne”


“Allah sarki, to ko dai dashen za a mata ne?”


Ta


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login