Showing 105001 words to 108000 words out of 273152 words
Chapter 36 - FULANI BOOK COMPLETE DOCUMENT by Khadijah Candy .txt
za ayi rawa ko wani abu da ita ake zuwa, ni kuma naje studio wani aiki sai na hadu da ita, ta fada min tana son waka kuma she's my big fan, hakan yasa na hada ta da wani manager na dake Kaduna, after ta zo Kaduna ta yi waka sai wakar ta karbu saboda ta fadi dalilin guduwarta, ba ni kadai ba mutane da yawa sun tausaya mata, at that time da muke magana da ita sai ta nuna min da ace zata samu ta gina kanta da zata daina karuwancin domin abun yana damunta, i like that girl saboda tana da addini but a lokacin can Zina ta zame mata ado, so i decided to help her sai na kama mata gida a Kaduna, na zuba mata komai a ciki saboda ita ta daina karuwancin, and i got lucky ta daina din, amman sai duniya ta dauki cewar na kama mata gidane saboda na maida ita karuwata, i face alot of challenges saboda haka har daga gurin Hajiya, to me taba mace rumgumarta gaisawa da ita ba komai ba ne a gurina, amman ban taba zina ba, har gaban Ubangijina zan fadi wannan, so kazafin da akai min ya min zafi amman hakan be saka na rabu da ita ba, ina ziyararta time to time, kamin na ankaro boom...! ta fada so na, a lokacin da ta tallata min kanta ba zan iya ce mata a'a, i accept it na saka ta istibira'i and guess what?”
Ya karasa yana kallon Falmata da murmushi a fuskarsa, sai kuma ya bawa kansa amsa.
“Sai Hajiya tace ba zan auri ta, saboda yare ce kuma karuwace sai dai na auri Nana, bana son ta amman haka na daure ina ta koyawa kaina sonta, saboda Nana bata daga cikin irin matan da nake so, ina son mace mai hankali da natsuwa da sanin ya kamata ba irin Nana ba, kuma ni bana son farar mace a yadda nake fari sai na samu baka zai fi bada kala ai, ina son mace mai addini da natsuwa kuma black beauty just like you”
Ya fada daidai lokacin daya fakin harabar asibitin yana murmushi. Duk wani abu da Sirleem ya fada Falmata ta ji shi sai inda ya saka turanci ne kawai bata gane ba. Kallonsa tai kadan sai ta ji ya ji ya cika mata ido sosai har sai da gabanta ya fadi, sunkuyawa tai har ya fita motar ya zagayo ya bude mata side dinta.
“Ke baki ba ni labarinki ba”
Ya fada saitin kunnunta bayan ta fito motar.
“Ba ni da labari”
“No kina da your Family Papa Mama da kowa ma karatunki shekarunki and so on...”
“Ni...”
“Eh... ”
Sai kuma ta shiru bata sake ce masa komai ba har suka soma nitsawa cikin asibitin, a lot of people sai kallonsa suke wasu na gaisawa da shi ciki har da masu daukar hoto da shi.
Ina mata matan kwalisa Matan da suka ansa sunansu na Mata? Ina wadanda ke cewa mun yi mun yi bamu ga amfaninshiba? Hmmm to ku zo ga Yar gidan Maifata ta zo maku da Al ajabu, dan tsugunno, gumba da tsimi da Zuma daban daban, maganin sanyi na maza da Mata. Ga kuma garurruka irinsu mallakau sabuzu kuwa, sa bahaushe saibi, Dan hubbare kafi malam aiki, ke kadai ke da miji, dahuwar kaza, tattabara, ciccibi da dai sauransu. Ba anan kayanmu suka tsaya ba, muna hadin amare na musamman turaren sutura turaren tsugunno turaren wanka da na daki da na jiki duka 4amare nasu na musamman ne, amma ga tsuhuwar da ke son komawa yarinya itama zata iya zuwa ahadata kai abundai sai wanda ya gani, dan haka karkubari abaku labari, domin neman karin bayani zaku iua nemana ta wannan number 09029891757 ko 08169311410, muna aikawa ko'ina a fadin kasar nan har waje kasar nan muna aika kaya.
Address: Nasarawa Samaru Area gurin masallacin mai sola Gusau Zamfara state Nigeria.
03/12/2021, 09:25 - 🤐🤐🤐🤐: 28
*Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 300 to 0314795884 Abubakar Hadiza Gt bank, then send the evidence to 08036126660*
FALMATA POV.
Shine a gaba tana biye har suka shiga office din Momy, tsaye suka same ta basu baya tana sanye da rigar likitoci tana duba wasu takardu dake gabanta.
“Momy how are you”
“Fine kun shigo?”
“Eh amman nan zan barta akwai aikin da nake, idan an gama sai na aiko driver ya dauke ta”
“Okay you can go”
Ta fada ba tare da ta juyo ba, shi kuma be damu ba ya nunawa Falmata kujera.
“Je can ki zauna”
“Tau”
Sai da ta zauna sannan ya juya fice yana yi ma Momy sallama. After ya fice Momy ta juyo fuskarta shakaf da hawaye ta kalli Falmata tana kokarin danne kukanta, sai kuma ta zagaya ta zauna a kujerarta tana hawaye. Falmata dai sai kallonta take ganin babbar mace kamar Momy tana kuka. Kuka sosai Momy tai sannan ta saka tissue dake gaban teburinta ta goge fuskarta.
“Ya goshinki...?”
Ta tambaya da muryar kuka sai kuma ta sake fashewa da kuka. Ganin hakan yasa Falmata ta ce.
“Ko na kira Sirleem?”
“Aa, ba matsalar shi ba ce matsala ta ce ni kadai”
“Baki da lafiya ne?”
“Ina lafiya, kawai ina jin ciwo ne idan ana min gorin haihuwa, akwai ciwo a rashin haihuwa, idan na ga yara kamar ke ko kasa da ke ina jin kamar na sace, yan'uwan mijina da abokiyar zamana suna min abubuwa saboda ni ban haihu ba, kun zo a lokacin da wani abun ya bata min rai ne”
“Inshallahu zaki haihu, aure haihuwa, mutuwa duka lokaci ne”
Momy ta share hawayenta tana jin yadda kalaman Falmata suka saukar mata da natsuwa.
“Haka ne, haka mijina yake fada shi ma be cire rai da cewar zan haihu ba, ni ma ban cire rai ba ko dan rikon da nake ma Ameer ina fatar Allah ya dube ni ya ba ni haihuwa”
Ta karasa idonta na cika da hawaye. Sannan ta dauko takarda ta rike biro tana tambayar yadda Falmata take ji da kuma lokacin da abun ya fara, after ta yi nata bincike ta kira likitan kunne ya dubata ya rubuta mata magani, da kanta ta karbi takarda maganin taje ta siyo mata a pharmacy dake asibitin sannan ta dawo office din waya a kunnenta.
“To ka biyo ka sauke min bakuwa a Masarautar su Sirleem”
Tana fadar hakan ta sauke wayar ta mikawa Falmata maganin, kamin ta shiga mata bayanin yadda za ta yi amfani da shi. After like thirty minutes Ameer ya shigo Office din, hannunsa rike da makullin mota.
“Tashi kuje shi zai sauke ki gida”
“Tau na gode Allah ya saka da alheri”
“Ameen, drive carefully”
“Okay Mom”
Ya amsata sannan ya juya suka fita tare da Falmata, a tare suka jera har gurin da ya aje motarsa, sai ya shiga sannan yai unlock din motar ta bude ta shiga.
“Ina wuni”
Ta gaishe shi ba dan ta san zai amsa mata yadda zata ji, bata a damu da sai ya amsa mata din ba, ta maida hankalinta gurin titi tana kallon motocin dake shigowa cikin asibitin a yayinda su suke kokarin fita. Lokaci zuwa lokaci yake kallonta haka nan yake jin takwanta masa a rai natsuwarta ya masa. Sau daya ta juyo ta kalleshi sai ya sskar mata murmushi ba ta sake kallonsa ba har suka isa bakin gate din Masarautar, sai da ta masa godiya sannan ta bude motar ta fita, be bar gurin ba sai da ta shige cikin Masarautar sannan yaja motarsa ya gaba. Cikin masarautar ta shigo rike da ledar maganinta dake cikin hijab, kai tsaye ta nufi bangaren Ammy, tana isa ta danna door bell din wata hadimar ta bude mata, babu kowa a katon falon sai ac da katuwar plasma, dakinsu yaran ta nufa, a hankali ta tura kofar ta shiga, sai ta samu Luma ta yi tana ta bachi, Labib kuma baya dakin, fita tai daga dakin ta sauka saka gaba daya ta nufi Garden daman da yamma haka a gurin take zama ko da yaran, balle yanzu da babu ko daya a hannunta.
SHATTIMA POV.
Ya farka da tunanin maganar da sukai jiya da Baba Waziri, babu abun da yafi tsaya masa a rai kamar maganar aure da kuma transfer, ba wai baya son zama kusa da iyayensa ba ne, irin halin da Mai Martaba yake ciki yana daga masa hankali gashi kuma idan yana gari dole ne sai an saka shi cikin harkokin sarautar. Sakon DSP Nura ne ya shigo wayarsa cewar police din daya bukata suna waje suna jiran Zainab, call list dinsa ya shiga ya kira Zainab ya sanar mata, sannan ya mike tsaye ya fito harabar gidansa, a zahiri motocin dake jera a harabar gidan yake kallo, abadini kuma zuciyarsa na can ta lula wani gurin da tunani. Juyawa yai koma ciki yana shiga ya tube tufafin jikinsa ya shiga bathroom yai wanka ya fito ya shirya cikin kananan kaya sai kamshin turare yake kamar wani sabon ango. Keys dinsa ya dauka da wallet dinsa ya nufi motarsa Baba Adamu na ganin haka ya taso da sauri.
“Ran ya dade masarauta zamu je?”
“No zauna abun ka ni kadai zanje”
Ya furta yana bude motar ya shiga, kamin yai warming din motar har mai gadi ya bude masa gate. Kai tsaye ya dauki hanyar da zata sada shi da masarautar daman can a ka'ida ba a masarauta yake kwana ba sai idan ta dauro, duk wani abun daya shafi masarautar yana nisanta kansa da shi domin ko kadan sarautar bata burgeshi. Tun daga babban gate din har cikin gida ake ta mika masa gaisuwa amman be amsa ko ka daya ba, daman can kasaita bata barinsa amsa gaisuwa balle kuma yanzu da tunani ya saka shi gaba. Yadda ya fito cikin motar yana takawa sai ka rantse da Allah ba zai mutu a saka a cikin kasa ba, kallo daya zaka masa kasan cewa jinin sarauta ne, domin sarautar ta nuna a tafiyarsa da maganarsa da isarsa da fuskarsa da kamalarsa ga wani irin kasaita a tafiyarsa kamar shi ne sarkin ma. Kai tsaye ya nufi bangaren Mai Martaba sai ya kararda shi yana bachi, hakan yasa ya dawo bangaren Ammy, sai da ya fara duban yaransa dake hannun Jekadiya sannan ya nufi dakin Ammy ba tare da ya tambayi mai rainonsu ba. Ammy bata dakin Sai Nana dake aikin mata abincike a wardrobe ganin Shattima yasa jikinta ya fara rawa.
“Ya Shattima sannu da zuwa”
“Yauwa Sis Morning baki je school ba”
“Eh sai gobe?”
“Why”
“Bana jin dadi ne, kuma na fadawa Driver yaje makarantar ya fada”
“Me ke damunki?”
“Fever amman an sha magani”
Tana amsa masa ta nufi kofa da sauri, shi kuma ya bita da kallo cike da kulawa. Tana fita Ammy ta shigo rike da plate din wainar kwai a hannunta.
“Morning Ammy”
“How are you?”
Ya dan tabe baki alamar ba Kalau ba.
“Tunani ko rashin lafiya?”
Ammy ta tambaya yana mika masa farantin.
“Tunani dai”
Sai tai murmushi.
“Waziri ba zai yi abun da zai cutar da kai ba, ni kaina na dade ina son ka dawo garin nan da aiki ka ki, yanzu kuma baka isa ka sabawa Umarninsa ba”
Ya sauke ajiyar zuciya a hankali yana kallon Ammy.
“Maganar Auren ma bana fatar ka saba masa, tun da har ya zabi rufe ido ya aura maka yarsa be kamata kace aa ba”
“I accept it”
Daga haka be sake cewa komai ba. Be koma bangaren Mai Martaba ba sai da suka fito daga sallah la'asar. Ko da ya shiga falonsa sai ya same shi a ciki zaune, ko'ina na falon duhu ne kamar dare, bayan kuma yamma ne akwai haske a ko'ina. Ganinsa a falo ma abun ma farinciki gurinsa domin a da kullum yana kan gado kwance, amman yau gashi akan kujera zaune. Kamin ya karasa kusa da shi yai masa sallama, Mai Martaba ya dago kansa a hankali ya kalli Shattima, wanda siffarsa da ke shimkide a siffar Shattima kallo daya zaka masa ka san jini daya ne. Gaban Mai Martaba Shattima ya zauna yana murmushi.
“Barka da Yamma Mai Martaba ya kufan jiki?”
“Alhamdulillah”
Mai Martaba ya amsa yana ta kallon Shattima.
“N ga jiki ya fara kyau Alhamdulillah”
Shattima ya fada cikin jindadi, sai Mai Martaba yai murmushi ya ce.
“An samu shigowa?”
“Eh Baba Waziri ne ya kira ni jiya, akan maganar fitar da kai waje da kuma aurena da neman transfer”
A hankali Mai Martaba ya sauke ajiyar zuciya.
“Hakan yana da kyau, ni kaina aurenka yana cikin rai na, neman transfer ma yana kyau, domin kai ne babba a yanzu, sai dai magana fita da ni waje a bar wannan maganar”
Shattima ya dago ya kalleshi.
“Saboda me? Ba san inda za a dace ba Mai Martaba duk fata muke yi”
“Hakan yasa nake son maka wata wasiya, na san matsalar auren nan yana damunka, ina son nai maka wasiya cewar kai ta aure ko da kuwa yau zaka aura gobe ta mutu, to jibi ma ka sake auren wata, a koda yaushe ina maka kallon babba a cikin iyalina, ina jin dadi da alfaharin da Allah ya bani kai a matsayin da, Omar ina maka wasiya da ka ji tsoron Allah, kuma ka rike yan'uwanka tsakani da Allah babu banbanci ko nunawa wani ya fi wani...”
A take jikin Shattima yai sanyi, sai ya ji kamar Mai Martaba na masa wasiyar bankwana ne. Shiru mai Mai Martaba yai na dan lokaci sannan ya cigaba.
“Rayuwa a gida da Family irin wannan akwai wahala, amman idan ka jure Allah zai taimakeka, bana son ko bayan raina a samu rabuwar kai a tsakaninku, bana son tsabani ko kiyayya ta shiga tsakaninku, ka yi kowa biyayya ka bawa kowa hakkinsa...”
Mai Martaba bai karasa ba Shattima ya katse shi jin kamar kunnuwansa da zuciyarsa ba za su iya daukar abubuwan da Mai Martaba yake fada masa ba.
“Inshallahu zaka samu sauki Mai Martaba”
Mai Martaba ya gyada kai.
“Sauki yana tafe da yarda Allah, amman sauki na har abada, sauki wanda daga shi babu wani ciwon Inshallahu, ni kadai na san me nake ji akan ciwon nan Omar, bayan ciwon jiki a nake kwana da shi kullum na tashi da shi, ga ciwon tsoron rabar mutane da tunani, na yarda wannan jarabawa ce, babban Sarki kamar ni ace bana iya shiga cikin mutane, bana iya sauraren al'ummata, ina jin tsoron abun da zan fadawa Ubangijina, ina jin kamar sauka ta cancance ni wata zuciyar kuma na raya min idan nai hakuri nan ba da jimawa ba zan tafi na bar Sarautar, ba barin sarautar ce tashin hankalina ba, yadda zan tafi n bar ku, rashin hadin kanku da irin matsalolin da kuke samu tun a yanzu da nake raye, babu uban da zai so ya tafi ya bar iyalansa a watse kansu a rarrabe, kai ne babba Omar dan Allah ka kula da yan'uwanka, na san na dora maka abu mai nauyi, amman Allah zai taya ka, ka bi Hajiya Bilki kamar Ammy, kuma kai ta hakuri da yan'uwanka, musamman Mama Aisha (Nana) ita ce karama a cikinku ita ce kadai ta tashi bata san gata da dadin uba, bata san ta rabe ni ba saboda lalurata, ka kyautata mata ka zame mata uba, kuma kai hakuri da halayenta akwai kurciya a tare da ita, sannan ka saka ido akan tarbiyar Karima, ka bi kanen mahaifinka kamar ni.... Kuma kai ta hakuri da rayuwa”
Shattima ya rufe idonsa da suka gama cika da hawaye.
“Inshallah zaka same ni mai cika umarninka Mai Martaba”
“Allah ya maka albarka”
“Amin”
Ya amsa yana jin kamar ya fashe da kuka.
“Anjima idan Ammy ta shigo, zan sa ta duba maka takardun wasu filaye da gidajen da baka san da su ba, akwai kuma takardar da nai rubutu na wadanda nake bi bashi da kuma wadanda kasuwanci ya hada mu, zan hannata maka su ka aje inshallah”
Uffan Shattima be ce zai iya kara cewa ba ya mike tsaye.
“A tashi lafiya Mai Martaba”
Ya fice daga falon da sauri kamar zai tashi sama, be taba daukar haka wasiya take da nauyi ba sai a yau. Gaba daya jin yake duniyar na juya masa, ta ina zai fara ina zai sauke why mai martaba yai masa wannan wasiyar a yanzu.? Why him? Har ya iso bangaren Ammy kirjinsa be daina nauyi ba, ga zuciyarsa sai bugawa take kamar zata fito, nauyin ba kirjinsa kadai yake ba har a kansa ji yake kamar Mai Martaba ya dauki wani katon dutse ya dora masa a kai. Sai ya samu kansa a falon Ammy sannan ya soma tambayar kansa abun da ya kawo shi a falon, but he need to see his mother maybe ko zai samu saukin abun da yake ji. Hakan yasa ya nufi dakin yana kokarin tura kofar dakin ya shiga ya ji muryar Nana.
“Ni sai na tafi”
“Nana kina ganin rashin kunyar da kika min zai barki ki rayu in peace, kina min tsawa your own biological mother”
Tsaye yai jikin kofar yana kallon Ammy dake zaune kasa ta jingina da gadonta tana kallon Nana kamar Nana ce uwar ita ce yar.
“What is happening?”
Nana kamar mai jira ta juyo gurinsa da sauri ta soma masa bayani kamar zata yi kuka.
“Ya wai bikin yar Farin gida da ake wai Ammy ba zan je ba, kuma Amal kawata ce ita ce ta gayyace ni ita kanwar Amarya ce class din mu daya”
“Yaushe ake bikin?”
“Yau ake budar kan Amarya, kuma ba cikin manyan zan tsaya ba, ni gurin su Amal zan tsaya”
“Shikenan je ki fara shiri tun yanzu, zaki je anjima”
Da sauri ta rumgume shi tana murna.
“Thank Youu Ya I love you”
Ta sake shi sannan ta fice daga dakin cikin murna ranta fes tun da Shattima yace zata je. Sai da ta fice sannan ya nufi inda Ammy take ya zauna gefenta sai shi akan gadonta ya zauna tsabanin ita data ke kasa zaune.
“Ammy why kika hana ta zuwa?”
“Bata son makaranta, duk abun da aka ce tai ba zata yi ba, sai kuma a rika bin ra'ayinta ana mata yadda take so?”
Shiru yai yana kallon yadda idon Ammy ya cika da hawaye, sai ya ji tausayinta ya rufe masa zuciya.
“Amman idan kina irin kalaman nan marar dadi a gareta wani abu zai iya samunta, kuma still