Showing 126001 words to 129000 words out of 273152 words

Chapter 43 - FULANI BOOK COMPLETE DOCUMENT by Khadijah Candy .txt

29 Aug 2024

72713

after like thirty minutes Jurry ta dawo dakin ta mika mata wasu yan kunne yara kanana masu kyau da kyalli.


“Karbi wannan na baki”


Falmata ta girgiza mata kai.


“Aa ki bar shi na gode”


A take Jurry ta hade mata fuska.


“Karbi mana, sai ki kulle a dankwalinki dan kar ya fadi”


Abun ka da mai tsoro sai ta karba gudun kar ta mata fada ta yi yadda ta umarce ta wato ta saka a dankwalin da kulle sannan ta maida dankwalin a kanta ta daura ta cigaba da abun da take, sai kusan 10am ta gama jera kayan, hannunta har yayi sanyi ga gajiyar tsayi da tai, komawa tai gefe ta tsaya tana jiran shigowar Jurry ko Hajiyar ko wane sannan ta fada musu ta gama. Cikin sa'a kuwa Jurry ta shigo dakin.


“Ranki ya dade na gama”


“Okay”


Jurry ta karasa cikin dakin ta bude drawer madubin Hajiya ta dauko wata sarka ta gold cikin gidanta ta mikawa Falmata.


“Gashi Hajiya tace a baki”


Ta fada da karya yadda Falmata zata ji, sai ta girgiza mata kai da sauri tai baya da hannayenta.


“Aa ba zan karba ba, fada za a min a gida”


“Oh Ammy ko? Zata ce waya ce ki karba? Ai ba sai kin bari ta gani ba, a boye zaki shiga da shi idan kin je gida sai ki aje abun ki, ba a maidawa Hajiya Kyauta”


Ta girgiza kai tana jin bata son karba duk kuwa da bata san muhimmancin sarkar ba balle ta san ta zinari ce ko azurfa ko kuma sarkar ce kawai ta fashion.


“Dan Allah karki saka ni na karba dole, Wallahi a zan iya saka ta ba”


“Ki karba na ce, you're very stupid ina cewa ki yi abu kina cewa aa yar talaka da ke useless girl”


Jurry ta fada a tsawace da sauri Falmata ta kai hannu ta karba ta saka a cikin Hijab.


“Na gode”


Ta juya da sauri ta fice daga dakin, tana tafe gabanta na faduwa, kamar wacce ta sato sarkar haka ta rika boyonta a cikin hijabin har ta fita daga bangaren Hajiya. Cikin fargaba da tsoro na rashin dalili ta shigo bangaren Ammy ta danna door bell din ba bata lokaci aka bude mata, ganin Ammy da Jekadiya a falon yasa gabanta faduwa saboda ta fita ba tare da ta fada musu ba.


“Ke daga ina kike?”


Jekadiya ta jefa mata tambaya tun kan ta karaso cikin falon, sai ta tsaya nesa da su ta risina kasa kamar yadda ta saba.


“Daga bangaren Hajiya, ta saka ni gyaran kayanta ne”


“Amman babu neman izini zaki tashi ki fita dan kin raina mutane? Wa kika tambaya da zaki tafi? Ko gyaran kaya kika zo yi nan? Tun da kike nan an taba saka ki wani aikin da ba na raino ba”


“Aa dan Allah ku yi hakuri ba zan sake ba”


“Wallahi kin kuru da Shattima be wuce ba, da sai kin karbi hukuncinki, ki bar masa yara kije gurin wani aikin dan rainin hankali”


Jekadiya ce take ta fadan Ammy dai tun da ta kalli Falmata sau daya ta dauke idonta bata sake kallonta ba, domin hankalinta da tunanin yana can gurin abun da Nana ta fada mata ta yi jiya, tun jiya da abun ya soketa be barta ba har yau sai dai bata iya labartawa kowa ba, saboda ba labari ne mai dadi ba. Tunanin abun da zai zame mata mafita take, wanda zuciyarta take raya mata aure ne kadai mafitar Nana, idan akai mata aure wata kila zata natsu kuma zata yi hankali, and controlling dinta zai koma karkashin kulawar mijinta ne, beside bata son karatu then zaman me zatai a gidan? Shigowar Jurry tare da wata hadimar ne yasa Ammy dawowa daga duniyar tunanin da ta tafi, bata ji karar door bell da aka danna ba har tashin da Jekadiya tai ta isa gurin kofar ta bude mata bata sani ba sai da ta iso cikin falon ta mika mata gaisuwa.


“Ammy barka da hutawa”


Ta fada daga tsayen da take fuska a hade.


“Sannu Juwairriya”


Jurry ta mikawa Falmata hannu.


“Ba ni sarkar da kika sata”


Falmata ta mike tsaye da sauri tana kallon Jurry, da mugun mamaki, ta ji abun da Jurry ta fada sarai domin a tsawace tai maganar.


“Ba ni sarkar da kika sata... Ke chajeta”


Jurry ta fada tana kallon hadimar da suke tare, Falmata kan mutuwar tsaye tai har hadimar da isa kusa da ita ta daga hijabinta ta karbi sarkar.


“Gata kuwa a jikinta.”


Hadimar ta fada tana mikawa Jurry sarkar.


“Ka ji yarinya daga shiga tai ma Hajiya gyara sarka na kan gado ta sace, ni na dauka daga daga cikin hadiman gidan nan ne shiyasa ma na kirata, ashe barauniya ce, ke ni ban ma yarda da ita ba chajeta a ko'ina”


Falmata na tsaye kamar ice hadimar ta shiga bincikar jikinta, ta cire mata hijabi ta kwance dankwalinta a nan ta lura warware kullin dake jikin dankwalin ta sai ga yan kunne gold na yara, wanda hakan ya bawa Ammy da Jekadiya mamaki ganin irin yan kunne luma.


“Wannan na yara ne har shi kika sata kenan! Allah ya shirya ki”


Har lokacin Falmata bata iya furta komai ba, mamaki da al'ajab ya hanata kuka ko magana balle ta motsa daga inda take tsaye.


“Wuce muje ma Hajiya ta ga fuskarki kar ta sake sakaki aiki daga yau, ko bangarenta ma karki sake shiga”


A nan ma Falmata kallon Jurry kawai take tana ganin komai kamar a mafarki, wanda hakan ya kara tabbatarwa Ammy cewar ta yi satar da gaske kenan.


“Rikota”


Jurry ta fada sannan ta juya ta nufi kofar fita, hadimar dake take mata baya ta ta rika hannun Falmata ta jata babu ko mayafi akanta suka fice zuwa bangaren Hajiya. Ammy ta bisu da kallo Jekadiya kam bata ce komai ba, daman can indai sabgar Jurry ce bata shiga saboda rashin kunyarta da kuma izza, gashi kuma Falmata ta tafi bata fada musu ba.
Ammy ta mike tsaye ta shige dakinta tana jin wani iri tunawa da Nana, idan har wannan tana da hujjar sata wata kila ba zai wuce talauci ba, Nana fa? Hawaye ya cika idonta sai ta saka hannanyenta ta rufe fuskarta ta fashe da irin kuka da ta manta rabon da tai irinsa.


Kamar akuya haka Hadimar ta shigo da Falmata cikin falon Hajiya, Jurry ta tsaya daga falon tana kwalawa Hajiya kira.


“Hajiya fito ki ga munafunar”


Hajiya da jiki ya gama mutuwa saboda kalaman Nana ta fito daga dakin zuwa falo, shouting din da Jurry tai ne yasa hankali Sirleem daya shirya yake kokarin fita ya dawo falon har ya kura da Falmata.


“Ita ce yarinyar”


Hajiya ta tambaya tana doso inda suke, Sirleem ma ya nufo gurin ganin Falmata. Sai a lokacin hawaye ya fara saukowa Falmata ta girgiza ma Hajiya kai, sai kuma ta kasa magana.


“Miya faru?”


Sirleem ya tambaya, a daidai lokacin da Rima da Kausar suka doso gurin.


“Wannan yarinyar ta saci sarkar Hajiya, daga gyaran tufafi ta dauke sarkar Hajiya ta miliyan uku da rabi”


Jurry ta fada tana nuna masa Falmata.


“Sarka....”

Sirleem ya fada kamin ya kalli Falmata, sai ta girgiza masa kai alamar aa tana wadansu irin hawaye masu ban tausayi. Tasss Jurry ta dauke ta da mari.


“Oh karya zan miki kenan dan ubanki...”


Bata aje hannun ba Sirleem ya mayar mata da marin a kuncinta na dama kamar yadda ta mari Falmata a kuncin dama.


“Ba zaki barta tai magana ba?”


Ya fada wani irin zafin rai na taso masa marar misaltuwa. Daga Jurry har yayarta Rima da kanwarta Kausar sai da mamaki yasa su wani shock, balle Hajiya dake kallon Sirleem kamar ta ga wani abun tsoro.


“Ka mari jinin sarauta saboda wulakantacciya talaka? Ba a taba ba, ba a taba cin zarafin yar sarki a gaban kaskantattun mutane ba sai a yau, you take her side ka yarda da ita ka karyata yar'uwarka?”


Sirleem ya kalli Hajiya try to control himself.


“I know this girl, she can't even read and write, i don't think ta san abun da ake cewa gold, idan ma ta sace sarkar ta kaita ina? Me zata yi da sarkar mikiyan uku da rabi? Ina zata kaita? And miyasa ta kirata ta gyaran tufafin from first place? Ba akwai enough Hadimai da masu aiki a bangaren nan ba?”


“And now ni kake dorawa laifin kenan?”


“No laifin Jurry ne, daman tun da na ga shigowar yarinyar na zuciyata ta raya min wani abu, there's something behind it, Jurry zata iya kisa komai saboda bata da hali, baku san halin da yarinyar take ciki ba, Falmata ba zata yi abun da zai saka a koreta daga gidan nan ba, you must explain it”


Ya karasa yana kallon Jurry, kamin ya rika hannun Falmata ya fice da ita daga falon. Hajiya ta bishi da kallon mamaki.


“He hold her hand, and he know her name, taya? Ban gane ba, ya haka wai? Yau ko yau ce?”


Ta tambaya kamar wacce ta rikice, daga Kausar har Rima kallonta suke da kuma Hadimar data riko Falmata domin ba su san abun da take nufi ba, duk kuwa da kasancewar su kansu suna mamaki da abun da Sirleem yai.








_________
Ina mata matan kwalisa Matan da suka ansa sunansu na Mata? Ina wadanda ke cewa mun yi mun yi bamu ga amfaninshiba? Hmmm to ku zo ga Yar gidan Maifata ta zo maku da Al ajabu, dan tsugunno, gumba da tsimi da Zuma daban daban, maganin sanyi na maza da Mata. Ga kuma garurruka irinsu mallakau sabuzu kuwa, sa bahaushe saibi, Dan hubbare kafi malam aiki, ke kadai ke da miji, dahuwar kaza, tattabara, ciccibi da dai sauransu. Ba anan kayanmu suka tsaya ba, muna hadin amare na musamman turaren sutura turaren tsugunno turaren wanka da na daki da na jiki duka 4amare nasu na musamman ne, amma ga tsuhuwar da ke son komawa yarinya itama zata iya zuwa ahadata kai abundai sai wanda ya gani, dan haka karkubari abaku labari, domin neman karin bayani zaku iua nemana ta wannan number 09029891757 ko 08169311410, muna aikawa ko'ina a fadin kasar nan har waje kasar nan muna aika kaya.
Address: Nasarawa Samaru Area gurin masallacin mai sola Gusau Zamfara state Nigeria.
03/12/2021, 18:51 - 🤐🤐🤐🤐: *Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 300 to 0314795884 Abubakar Hadiza Gt bank, then send the evidence via 08036126660*




IYA POV.


Napep din data hau be sauketa ko'ina ba sai bakin gate din gidan Waziri, sai da ta sallame shi sannan ta buga gate din aka bude mata ta shiga, bangaren uwargidan ta fara zuwa wato Hajiya Maryam ta fara zuwa suka gaisa sannan ta nufo part din Hajiya Talatu, tana tafe tana addu'ar Allah yasa wacce daje dan ita tana nan, cikin sa'a kuwa tana tura kofar falon ta shiga sai tai arba da ita a tsakar falon ta saka indomie a gaba ta kasa ci, kanta ba dankwali sai wata doguwar riga dake jikinta, dayan hannunta rike da wayarta tana lasawa duk da kasancewar fuskarta tana facing plama dake falon ne, Iya bata san lokacin daya washe hakora ba.


“Mashallah, sannu dai Maijidda jiddalo farar mace alkibbar mata, farar mace lantarkin gida, kowa ya auri baka kudinsa ne be kai ba”


Maijidda ta yi murmushi tana dan sosa kanta.


“Iya yau ke ce a gidan mu?”


“Ni ce fa, tun da ku kunki zuwa ba dole mu zo mu kawo muku gaisuwa ba, yayan sarakuna jikokin sarki, jinin sarauta jinin kima da martaba, jinin da baya zuba talaka ta tsallaka, Allah ya kara imani da mubbiba”


Iya ta karasa tana daga mata hannu irin yadda ake ma yayan sarakuna, Maijidda dai sai murmushin karfin hali take domin tana ciki damuwa matuka, ba yau Iya ta saba mata kirari ba, halin iya ne shisshigi da iya yi, indai ta san kana da alaka da sarautar gidan to ta dinga zuba maka kirari kenan har sai ka gaji.


“Ina giwar mata? Hajiya mai dubun nairaro mai yi ws talaka da marar uba gata? Wacce bata kyashin badawa?”


“Yanzu nan ta fita, zata je gidan Hajiya Hansai daga can ta wuce Masarauta gurin Hajiya Babba”


Iya ta dafe kai kamar gaske.


“Kai amman yau na yi baka tafiya mai kama da baka, na yi rashin sa'a gashi na taso tun daga masarauta saboda kawai na kawo gaisuwa”


“Ai tace zata je can idan kin je zaki ganta”


Maijidda na fadar hakan ta mike tsaye ta nufi dakinsu, bata dade ba ta fito rike da 5k ya mikawa Iya, a gurin karba Iya ta hada da kurwarta ta karbe.


“Kai abu yai daidai abu yayi kyau, na taki sa'a na yi farar tafiya, ai ni a sai na ga Hajiya ba ma, kin biya ni Allah dai ya hada fuskokinmu a lahira”


“Ameen”


Maijidda ta amsa tana jin kanta na dan sarawa kadan, kamin ya koma daidai har ta samu zaunawa ta cigaba da juya abincin.


“To yar albarka zan tafi, sai kuma wani jikon inji kare da ya zubar da tsamiyar kura”


“To Iya a gaida gida”


Iya ta mike tsaye tsabar farinciki har jin take kamar ta daka tsalle, cikin kudin ta jimke kurwar Maijidda har sai da ta fito sannan ta ciro kurwar ta kulle a zanenta, ta kama hanya ranta fes.




HAJIYA BABBA POV.


Hajiya Talatu ta girgiza kai tana mamakin jin abun da Nana tai, domin ya fi komai bata mamaki sama da wanda Sirleem yai.


“Yanzu wuyan Nana har yayi kauri haka? Ita nan har ta samu hankalin iya tufafi da labe da furta irin wadannan”


Hajiya Babba ta tabe baki


“Hmmm har tana min barazanar zata fasa auren Sirleem, sannan kuma wai zata fadawa Mai Martaba matukar ban saka an saki yaron ba”


“To wai son shi take ne?”


“Ga alama kina gani, idan ba son shi take ba ta isa tai min wannan ne? Nana ni zata kalli tsabar idona ta fada min haka? Hmmmmmm”


Hajiya Talatu taja dogon numfashi ta sauke.


“Ki kwantar da hankalinki Hajiya, abun da ya fi kawai mu koma garin mutanen nan ba a fa bori da sanyin jiki, sannan ni a tawa shawara ki saka a saki yaron kawai in yaso idan munje sai mu fada musu su rufe mata baki, kuma su shiga tsakaninta da yaron, kuma su kara mata son Sirleem a ranta, shi kuma Sirleem din a rabashi da wacan yarinyar idan ya kama a haukarta da ita duk ayi, ni ma kuma ga tawa matsalar ina son su saka Waziri ya fasa maganar auren nan”


“Haka na yi niya daman, na fadawa Jarma a saki yaron, yau idan ya dawo zan masa maganar zuwa garin, kuma tun yau zan fadawa Mai Martaba cewar Hajiya Hansai bata da lafiya ina son naje dubata jibi, sai mu wuce kawai domin zama be gan mu ba, kin ga idan muka je ma sai su fada mana wacece Fadimen har ita din mu yi maganinta, tun kam ma ta shigo ciwon kan ya mana yawa”


“Eh haka ne, sai dai wani hanzari ba gudu ba, kin san Jarma be san da ni ba a lamarin nan idan ya san da ni za a tafi asirina zai iya tonuwa”


“Karki ji komai, ai ba fada masa zan yi cewar ga abun da zai kaiki ba, zance zaki rakani ne kawai, ke kuma sai ki fara shirinki tun yau”


“Eh tun yau zan fara, gobe zan bar gidan daman ina da zimmar yin yaji saboda auren nan, to daga gobe ma zan bar gidan na koma gidan Yaya Rakiya zan fada mata komai ta nan zan samu hanyar zuwa, domin na san halin Waziri wani irin murdaden mutum ne, ba zai nemi ba sai an kwana biyu”


Hajiya Babba ta kalli tsadaddin kulolin abincin dake gabanta tana fadin.


“Ni mamakina ta ina Sirleem yasan yarinyar nan? Har yana fadar wai ban san halin da take ciki ba?”


“Shine abun mamaki ai, amman dai idan muka je can ai zamu ji”


“Bari ma na kira Jarma tun yanzu”


Hajiya ta dauko wayarta ta lalabo number, bata dade tana ringing ba ya daga.


“Hello Hajiya, na fada musu a sake shi, gani nan a mota gani nan hanyar zuwa Masarauta yanzu”


“Tau yayi sai ka iso”


Ta sauke wayar tana wani kankance ido, irin na manyan matan nan dake cikin damuwa.


“Yace gashi nan a hanya, sai ki wuce kamin ya iso”


Hajiya Talatu ta mike tsaye da sauri tare da daukar jakarta.


“Kara na tafi kar ya tararda ni a nan kam, duk yadda kuka yi sai ki sanar min a waya”


Kai Kawai Hajiya Babba ta iya daga mata, ta maida dubanta gurin window dakin, abubuwan nan biyu sun tsaya mata a rai.
Hajiya Talatu bata dade da fita ba, Jarma ya shigo dakin da sallama, kamin ya zauna Jurry ta turo kofar dakin ta shigo ita ma, ta zauna kusa da Hajiya. Jarma ya zauna yana kallonta domin duk abun da suke be taba magana da Hajiya a gabanta ba sai dai idan ya tashi Hajiya ta labarta mata komai. Kamin Jarma yace komai Hajiya Babba ta kalleshi cike da damuwa ta ce.


“Jarma ina son zuwa garin mutanen nan jibin nan”


Jarma ya kalli Jurry kamin ya kalleta.


“Jibi fa kika ce Hajiya”


“Eh mana Jarma, baka ga halin da muke ciki ba? Ina da tabbacin mutanen nan ne kadai za su iya man maganinta, tun ba aje ko'ina ba mun fara ganin lalacewar shiri balle kuma nan gaba? Me kake tsammani? Daman kace sun fada Falmata Sardauna da kuma Fadime za su lalata mana shiri ga shi kuma mun fara gani tun yanzu, ba kuma lalacewar shirin ba tonuwar asiri wanda zai saka mu ji kunya”


Jarma ta sauke ajiya zuciya yana kallon Jurry, so yake yai magana kuma yana jin nauyinta domin be taba irin wannan maganar da Hajiya a gabanta ba, ganin yadda yake dari-dari da Jurry yasa Hajiya tace.


“Karka damu Jarma, Jurry ta san komai na san ka sani, tafiyar nan ma da ita za ayi da yardar Allah, ka sake jikinka kai magana”


“Hajiya kina ganin tafiya jibi jibin nan be yi sauri ba?”


“Ba wani sauri ni idan zan samu dama ma yau zan tafi Wallahi, yanzu haka ji nake kamar a kaya, idan fa mu ka yi wasa za mu ga wasa”


“Haka ne gaskiya, to ai ni bani da matsala, sai na fara shirina tun yanzu,


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login