Showing 213001 words to 216000 words out of 273152 words
Chapter 72 - FULANI BOOK COMPLETE DOCUMENT by Khadijah Candy .txt
fada sannan ya juya da sauri ya fice daga office din. After ya fita Muhseen ya dauki wayarsa ya kira likitan ya fada masa ga yarinyar an kawo, yana dagowa sai ya ga tana kallonsa baki bude ta gwalo ido waje kamar zata yagasu, a hankali ya sauke wayar ya baro tebur din ya karaso kusa da ita yana yawo da hannunsa a fuskarta sai ya ga tana bin hannun da kallon sai kara fito da ido take. Wani irin ihu ta saka tai cikinsa ta rumgume shi da mugun karfi, kamin yai wani yunkiri ita da shi sun kai kasa...!
Ina mata wadan da suke son sayen kaya kamar su laces, atamfa, materials,shadda lace, normal shadda, atamfa lace, veil's, shoes and bags, da sauransu kuzo ga MAMAN AHMAD tazo dan tashare hawayenku kudai kunemeta ta wannan number 08032350261 banan kadai tatsayaba tanada kayan order kama dana kitchen,tufafi,kuma order ta Bata dadewa ,tana saida kayan gyara kamar su Al'ajabu,shu'umar humra wannan inbakida aure Bama saida maki,hadin kaza me yasin,akwai na mallaka wanda wannan ana rubuta shi atafin hannu ke zakiyi wannan,turaren wuta,kulacca,da sauransu
Mazauninsu nanan a samaru Gusau Zamfara state
Muna aika kaya kowace jaha da wajen kasar nan cikin aminci da yardar Allah kunememu kusha mamaki
https://wa.me/qr/MYY56BH3RMFDG1
03/12/2021, 18:59 - 🤐🤐🤐🤐: Ina mata wadan da suke son sayen kaya kamar su laces, atamfa, materials,shadda lace, normal shadda, atamfa lace, veil's, shoes and bags, da sauransu kuzo ga MAMAN AHMAD tazo dan tashare hawayenku kudai kunemeta ta wannan number 08032350261 banan kadai tatsayaba tanada kayan order kama dana kitchen,tufafi,kuma order ta Bata dadewa, akwai turaren wuta,kulacca,da sauransu
https://wa.me/qr/MYY56BH3RMFDG1
*Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 300 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith bank, then send the evidence via 08036126660*
“Abun kamar na Iska”
Ataa ta fada.
“Damuwa ma na saka haka”
Cewar Muhseen yana kai hannayensa biyu ya rika kanta, sai tai tsit kamar ba ita ba.
“Kina na saurarena?”
Ta yi shiru.
“Idan kina ji ki daga min kai ba sai kin yi magana ba”
Sai ta daga masa kai idonta a rufe.
“Ki daina kokarin tuna komai kin ji?”
Nana ma kam ta daga.
“Ki dauka wacan matar da mijinta da suka tsince ki yan'uwanki ne, ni Sunana Muhseen likita ne ni, zan rika kula da ke ina baki magani, so kina son ki dauke ni a matsayin yayanki and daga yau sunanki ....Yasmin”
Ya fada bayan dogon nazari.
“Da zarar kin ji ance Yasmin to da ke ake sai ki amsa, kin ji? Kuma idonki ma zai bude kin ji?”
Ta daga masa kai a hankali tana kokarin kwantar da hankalinta.
“Yasmin”
Ya kirata murya kasa kasa, da farko sai ta ji kamar ba da ita yake ba, can kuma sai ta amsa.
“Na'am...”
“Good girl”
Ya juya ya kalli Aliyu da Ataa dake tsaye bakin kofar dakin.
“Zan tafi da ita asibitin idan ta kama a kwantar da ita zan kwantar da ita a can, idan kuma dawowa zan zan dawo da ita nan”
“No ka kaita gidan Mama Fulani kawai”
Aliyu ya fada, sai Muhseen ya hanye hannunsa daga rikon kanta da yake, ya kama hannunta. Ya fito da ita dakin zuwa motarsa, har gurin motar Aliyu ya bi shi ya fada masa.
“Duk abun da ake bukata ka fada”
Muhseen dai be ce komai ba ya bude mata gidan gaba ta shiga sannan ya zagaya ya shiga mazauninsa yaja motar. Daga gidan be tsaya da ita ko'ina ba sai asibiti, farkon abun da ya fara bincika shi ne kwakwalwarta, a tunanin idam hankalinta y dawo zata iya bayanin yadda akai ta rasa idon ko kuma irin maganin da take kai. Hotuna ya rubuta mata har guda hudu kuma masu tsada ya saka wani ya kaita aka dauki hoton abun da ke cikin kanta, akai mata gwaje gwaje, at first what he thought is ko ta yi hadari ne ta rasa tunaninta da idanuwanta domin hatsari babu abun da be saka wa, daga ya fara tunanin ko an dura mata kokin ne, kamin ya fara tunanin wata kila damuwa ce tai mata yawa.
Sai dai abun da ya bashi mamaki a duk hotunan da aka dauka da kuma bincike da yai be ga wani abu da zai iya sakata haka ba, komai na kanta kalau yake.
Amman saboda ya tabbatar yasa yai magana da wani kwararen likitan kwakwalwa, sai dai be samu dubata a ranar kasancewar yamma ta yi sosai, ya dai yi alkawarin dubata gobe idan ya shigo asibitin. Sai da Muhseen ya gama komai da yake a cikin asibitin sannan ya sakata mota ya nufi gidan Mama Fulani da ita. Gidan yana nan a yadda yake kamar da a tsari da fasali, sai dai an canja fenti da furnitures. A harabar gidan yai fakin sannan ya bude motar ya fito ya zagayo ta bangaren da Fadime ta ke ya bude mata ya fito da ita.
“Yauwa ya ma sunanki?”
“Yasmin”
Ta fada a hankali.
“Yauwa na kawo ki gurin Mamana kuma mamankin daga yau ita ce mamanki, kuma a nan gidan za ki zauna kamin ki samu lafiya kin ji ko?”
“Too”
Ya riko hannunta suka nufi kofar shiga falon Mama Fulani. Door bell din falon ya danna, babu bata lokaci mai aikin ta bude masa kofa.
“Baaba”
“Na'am Alhaji an shigo”
Tsohuwar ta fada tana yar dariya.
“Eh me kika girka mana?”
“Aa ban girka da kai ba, ban san zaka zo ba ai”
“Mama na ciki?”
“Tana sama ina ga ko bachi take ne”
Ya shigo cikin falon yana rike da hannun Fadime, karasawa yai da ita gurin da set din Kujerun falon ya zaunar da ita.
“Baaba a kawo mata abinci da abun sha, idan ta gama a fada mata yadda za ta yi sallah please, sai dai bata gani”
“To Likita yanzu kuwa”
Baaba ta fada tana kallon Fadime. Muhseen ya nufi dakin Mama Fulani yana cire rigarsa suit dinta. Sai da ya kwankwasa sannan ya tura ya shiga, zaune ya same ta gaban laptop idonta sanye da farin gilashi tana duba wasu laces na manyan mutane. Shigowar Muhseen yasa ta cire gilashin ta kalleshi tana murmushi.
“Yau kuma?”
Ta tambaya domin ta manta when last su shigo gidanta da sunan sun dawo aiki shi da Aliyu, ba kamar da ba da kullum suna nan.
“Bakuwa na kawo miki”
“Bakuwa kuma?”
“Yes danki ne ya tsintota kin san shi da tsince tsince, kuma ya laka min ita”
Ya fada yana kokarin zama.
“Aliyu kuma? Ban gane ba”
A natse Muhseen ya fada mata komai, sai ta cika da tausayinta kamar ba Mama Fulani ba.
“Allah sarki ai ba a wulakanta mutum, baka san ko shi waye ba, wani lokacin ma har shi zai taimake ka, ina yarinyar take?”
“Tana kasa, gobe za a kaita asibiti ko ban biyo ta nan ba zan kira sai ki saka a mota direba ya kaita”
“To ba matsala, Allah sarki...”
Ta fada tana sauka daga kan gadon ta nufi kofar fita, Muhseen ya mike tsaye ya shiga bathroom, ita kuma ta sauko kasa tana kallon Fadime dake zaune a kasa Baaba na bata abinci a baki.
“Hajiya an sauko”
“Eh abinci ake bata ne?”
Mama Fulani ta amsa ma Baaba tana zaunawa.
“Eh na ga zata bata jikin ne shiyasa na soma bata da kaina”
“Allah sarki baiwar Allah ya sunanki?”
“Yasmin, wannan yace na Yasmin ne sunana kuma yace ke ce Mamana”
Mama Fulani ta rausayar da kai tanawa da Ataa.
“Eh haka ne ai da na kowa ne, sannu Yasmin sannu kin ji Allah ya baki lafiya”
Fadime ta daga kai tana tauna abinci. Sai da ta ci ta koshi sannan Baaba ta dauke plates din ta bata ruwa ta sha, ta kama hannunta suka shiga dakinta ta zuba ruwa a buta tai mata alwala ta yadda zata fi fahimta sannan ta saka ta tace tai da kanta, da ido rufe ta kokarta ta yi yadda Baaba tai mata tana ta son ta tuna minene alwala sai ta soma jin abun irin na dazun, take ta kawar da tunanin kamar yadda Muhseen ya fada mata. A gurin sallah kam Baaba daga mata hannu take tana nuna mata yadda za ta kabbatarta sallah, a gurin ruku'i kuma sai ta rikata ta lakwasa yadda zata gane.
BAPPA POV.
Tun da Bappa ya doro gidan ba tare da Fadime ba, Inna ta gane akwai abun da ya faru, sai dai bata masa magana ba duk kuwa da son ganin Fadime da take, sai da ta ba shi abinci ya ci ya koshi ta ba shi ruwa ya sha ta zuba masa wani yai wanka ya gabatar da sallah la'asar sannan ta zauna a inda ya gama sallah tana ta kallonsa kamar ta tambaya ina yarta kuma tana fargabar irin abun da zata ji. Bappa na ganin irin zaman da tai ya san cike take da son ta ji labarin komai. Tunanin ta inda zai fara bata kabarin ya fara, daman ya tafi ya barta ba dan lafiya ta ishe ta yanzu kuma idan ya labarta mata abun da ya faru ya za ta ji?
“Ko dai wani abun ya same ta n Malam?”
Sai da Bappa ya tattaro dukan kuzarinsa sannan ya iya labartawa Inna abun da ya faru, take ta fashe da kuka tana masa magana da yalshen fulatanci.
“Ka ce min kawai na rasa Fulani, damn ita kadai ta tsaya a cikin yayan yanzu kuma na rasata...”
Kuka ta saka sosai wanda ya saka jikin Bappa sanyi wanda har ya ji ina ma ya tsaya a can a bincika ko za a ganta, shi kansa ba wai baya son Fadime ba ne, bacin rai ne ya saka shi haka bacin rai da har yanzu be bar zuciyarsa ba.
“Sai da na ce maka karka je, wata kila zuwan ku ne ya saka ya dauke ta ya kaita wani gurin, babu yadda ban yi da kai ba akan karka je garin nan amman baka ji ba, yanzu ga shi nan ka saka ya sake dauketa wa san inda zai sake jefata? Gashi ba gani take ba”
Bappa ya ja tsaki.
“Ai duk laifinta ne, yarinya bata jin magana kom...”
Be kai karshe ba Inna ta rufe shi da fada tana mikewa tsaye.
“Eh kullum ai daga ni sai ita ne masu laifi a gidan nan, kullum cikin fada kake da ita, dan abu kadan ka ce zaka dake ta, shiyasa har take boye maka bata fadar komai saboda ta san dukanta za ka yi, ni Wallahi sai ka nemo min ita, ka tashi ka tafi garin mutanen nan ka nemi Wasim ka bashi hakuri ya kawo min Fulani, wollahi in ba haka ba sai da na abar maka gidanka, ban zama gidan babu da babu jika, wacan bakar mata ta cinye yayan yanzu kuma yar wannan da ta rage za ka ce ta bata wollahi ni kam ban yadda...”
Bappa ya daga kai yana kallon iko Allah, shi be dora mata laifi ba sai ita ce zata dora masa laifi.
“Aradun Allah ba ni kai kaina ga halaka, sai dai ki tahi duk inda za ki, amman ba ni zuwa wacan gari in mutu”
Ta fada cikin fusata har yana cire rawanin dake wuyansa, Inna kuma ta fashe da kuka mai karfi tana jin kamar ta rasa Fadime ne gaba daya.
IYA POV.
Shiru shiru Zainab bata dawo ba, tun tana sauraren dawowar Zainab har ta gaji ta kwanta da tunani kala kala. Zuciyarta ta fi raya mata cewar an ga Fadime wata kila ta fadi wani abu akan wanda hakan yasa aka kirata.
Bata yi wani bachi kirki ba ko kadan hankalinta be kwanta ba, saboda tunanin tafiyar da akai da Zainab daman tsakanin uwa da da sai Allah. Washe gari tun da ta tashi ta wanke baki bata damu tai sallah ba ta shiga kicin, daman can sallah bata dame ta tana kokarin yi ne kawai idan ta ga idom mutane, musamman a lokacin da take a masarautar saboda ayi mata kallon mutuniyar kirki.
Dumamen shimkafar da ta dafa jiya tai ta fito falo ta zauna tana turawa ba dan tana jin son cin ba domin gaba daya hankalinta ba a kwance yake ba, kadan ta ci ta aje plate din ta mike tsaye ta nufi dakinta hannunta ta wanke sannan ta cire tufafin jikinta ta dauko wasu ta saka ta saka hijabinta ta dauki jakarta ta dauki makullinta ta rufe dakinta ta fito ta leka dakin Zainab, sannan ta nufi kofar fita. Sai da ta kai bakin gate sannan ta kira mai gadin.
“Mun fita, karka budewa kowa gidan nan ya shigo ka ji ko”
“To Hajiya Allah ya tsare”
“To Ameen”
Ya bude mata gate din ta fice, tafiya tai mai nisa kamin ta samu abun hawa, daman sabuwar unguwa irin wannan ba a ciki samun abun hawa da wuri ba. Sai da ta fada masa inda zai kaita sannan ta hau. Suna daf da isa ta fara jin tsoron zuwan, zuciyarta ta soma raya mata cewar wata kila an rike Zainab ne saboda ana son ta zo waya sani ko wani abun aka shirya mata, take ta tuna da kalaman da Zainab tai mata cewar idan ba ta daina abun da take ba zata bata mamaki wata kila ta fadawa Ammy ko Shattima wani abun ne, wani bangare na zuciyarta kuma yana raya mata ba haka ba, domin jikinta na bata yarta na cikin matsala. Kamin su isa masarautar ta tsayar da mai achaban ta sauka ta dauko kudinsa ta mika masa, ya karba ya bata canji sannan ta karasa masarautar da kafa.
Tana daf da shiga gate din masarautar sai kuma ta ja ta tsaya tana tunanin idan ta shiga zata iya jefa kanta a matsala. Daga nesa ta kira wani police dake gadin masarautar daman tana mutunci da shi sosai, domin yana girmamata. Shi kanshi yayi mamaki da bata karaso a inda suke ba kamar yadda ta saba sai ta tsaya can nesa da su sai dai ba sosai ba ta kira shi.
“Hajiya Iya lafiya dai?”
“Lafiya kalau Jekadiya na ke son gani”
“Hajiya Iya ganin Jekadiya ai baya miki wahala ke da kika fi mu gata cikin gidan na, ko dai akwai matsala ne”
Ta yi dariyar karfin hali.
“Aa babu komai Wallahi, sauri na ke ne ina son na tafi wani guri kuma ka san gidan sarauta idan ka shiga dole ne sai ka shiga ka gaishe da kowa idan ba haka ba kai laifi, shiyasa bana son asan na zo”
“To a kira miki ita?”
Ta dan yi shiru tana tunanin idan wani abun aka shirya mata, idan Jekadiya ta zo ta ganta a nan ba tsira tai ba.
“Aa kira min ita a waya ma”
“To”
Ya ciro wayarsa yana fadin.
“Ai ni ranar na ke samun labarin wai kun bar masarautar nan”
“Eh Hajiya Karama ce ta matsa ta matsa, dole na bita tun da ba a kyale mace ta zauna ita kadai a gida ba”
“Haka kam ai kara da kika koma kam”
Ya shiga neman number Jekadiya tare da aika mata kira, wayar bata dade tama ringing ba ta daga sallama, sai yai saurin mikawa Iya.
“Gashi ta dauka, sai dai bata san ni ne ba domin ni kadai na ke da number ta bata da tawa”
“Too”
Iya ta karba ta matsa can nesa da shi inda ba zai ji maganar ta ba tana sallama.
“Jekadiya..Iya ce, na ce Hajiya Karama har yanzu bata dawo ba”
“Oh daman yanzu nan Shattima ya shigo yace a fada miki ba zata dawo yanzu ba”
A take gaban Iya ya fadi.
“Saboda me? Me ya faru?”
“To be fada min ba gaskiya ya dai ce a fada miki an kaita gidan hoto”
“Hoto? Ita Zainab din?”
“Eh sai anjima”
Jekadiya ta kashe wayar tun kamin Iya ta sake fadar wani abu, domin har ga Allah tsoronta take kuma tana gudun tai wata maganar da zata sabawa abun da Shattima ya fada mata. Iya ta gyada kai yana jinjina lamarin.
“An kaita gidan horo? Saboda batan yarinyar nan? Ko kuma saboda wani abun na dabam? Amman ko minene ai be dace Ammy tai mata haka ba!”
Tana tafe tana wannan maganar har ta iso inda Police din yake tsaye ta mika masa wayarsa.
“Amiru na gode sosai”
“Ai ba komai, kin fi karfin nan Iya”
Ita dai bata sake ce masa komai ba, domin tashin hankalin da take ciki ya dauke mata hankali.
“Ko kuma saboda ni za su hukunta ta? Shattima ne da wannan aikin ko Ammy? Ba mamaki Ammy ce domin ita ta saka aka min turaren nan kuma ta fi kowa bakin hali a gidan ai”
Tana tafe tana magana da kanta har ta isa babban titi ta tari napep ta hau.
“Malam million quarters za ka kai ni”
“To kudinki dari uku”
“Mu tafi”
Ta fada tana ta tunani, yana tafe tana kallon ababen hawaye zuciyarta kuma cike fal da tunani kala kala. Har bakin gate ya sauketa ta ciro dari hudu ta ba shi ya bata naira dari sannan ta juya dama da hadu ta ga idan babu wanda ya biyo ta, sai da ta tabbatar ita kadai ce sannan ta kwankwasa gate din. Mai gadin ya leko yana tambayar waye, ganin ita ce yasa ya bude mata ta shiga, ko sannu da zuwa da yake mata bata amsa ba tsabar hankalinta baya jikinta. Sai da ta shigo cikin falon ta zauna sannan ta samu yar natsuwa ita ma kadan, gaba daya hankalinta ya tattara ya koma kan Masarautar, sai neman dalilin kama Zainab din take ta rasa tudun dafawa idan ta kulla wannan ta kwance wacan. Mikewa tai tsaye ta isa gurin kofar falon ta rufe da makulli sannan ta dawo ta bude dakinta ta shiga ta maida kofar ta rufe. Hijabinta ne farkon abun da ya fara cirewa sannan ta aje jakarta ta nufi gurin da take aje tukunyarta ta bude ta dauko tukunyar tai magana a cikin sai kuma ta maida tukunyar ta aje, ta nufi karkashin gadonta ya janyo kwayar nan da take ajiyar kurwa a ciki, ta bude ta dauko kurwar Maijidda ta warware zaren jiki taka bakin mayafin dake saman gadonta ta lullube kurwar da shi. Tana cirewa sai ga kurciya a hannunta fuska a hade ta kama wuyan kurciyar ta murde iya kar karfinta har sai da jini ya fito ta tabbatar da ta kashe ta sannan ta saka a wani karamin kwanon, ta dauko dayar kurwar ta warware ta saka bakin zanen ta lullubeta, tana budewa sai wani tsohon zakara marar lafiya ya fara motsawa.
“Yanzu idan masarautar ta girgiza sai mu ga waye kuma za a dorawa laifi? Sai na ga yadda za ki yi ke