Showing 114001 words to 117000 words out of 273152 words
Chapter 39 - FULANI BOOK COMPLETE DOCUMENT by Khadijah Candy .txt
ne, amma ga tsuhuwar da ke son komawa yarinya itama zata iya zuwa ahadata kai abundai sai wanda ya gani, dan haka karkubari abaku labari, domin neman karin bayani zaku iua nemana ta wannan number 09029891757 ko 08169311410, muna aikawa ko'ina a fadin kasar nan har waje kasar nan muna aika kaya.
Address: Nasarawa Samaru Area gurin masallacin mai sola Gusau Zamfara state Nigeria.
03/12/2021, 18:51 - 🤐🤐🤐🤐: 31
*Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 300 to 0314795884 Abubakar Hadiza Gt bank, then send the evidence via 08036126660*
AA POV.
Yana isa gurin ya nuna musu gate pass din sai suka bude masa kofar ya shiga, a inda ya san Nana ta zauna dazun ya kalla sai ya hango babu Nana a gurin ba kuma kowa a har jakar da take fada babu, a take zuciyarsa ta raya masa yarinyar ta dauki jakarta ko kuma wata ta sata, kai tsaye ya nufi gurin yana ta rabon ido ko zai hango Nana. Gaban teburin ya tsaya yana ta sake sake a ransa, be san yarinyar ba haka kuma be san inda zai sameta ba, wata zuciyar na raya masa ya aje sarkar a kasa yai tafiyarsa, sai dai kuma be zama lallai ta gani ba wani zai iya gani ya dauka, hakan kuma ba zai wanke Nana daga zargi ba, ba kuma zai hana idan an bincike CCTV ta gurin ta nunata ba. Be raba dayan biyu ba, wata budurwar da ba zata wuce sa'ar Nana ba ta doso teburin tare da Amal, hankalinta a tashen.
“To wai ina kika aje jakar?”
Amal din ta tambaya tana duba gurin, sai yarinyar ta amsa mata kamar ta fasa kuka.
“Wannan kawarki na bawa na ce ta rike min, ina gama karin kudin na dawo na ga jaka a bude ba sarka kuma ita yarinyar bata nan”
Jin hakan yasa AA ya dan matsa kusa da su.
“Malama ke kika jefar da sarka a nan?”
Daga Amal har yarinyar dagowa sukai suka kalleshi, kamin su kalli Sarkar da yake nuna musu, yarinyar ta kai hannu da sauri ta karba.
“Wallahi ba jefarwa nai ba, sai dai idan sata kai baka samu damar fita da shi ba ka maido”
“No a kasa na ganta, na dauka sai na rasa wa zan bawa”
AA ya fada da sauri yana kokarin kare kansa, Amal ta masa wani kallon rashin yarda.
“To me ya kawo nan bangaren mata ma? Kuma har ka ga sarka a kasa?”
“Believe me ban dauka sarkar nan ba”
Bata ko saurareshi ba ta nufi wajen securities din da suke kofar shigowa, AA ya ganin ta nuna inda yake yaji yawun bakinsa sun kafe, gabansa yai mugun faduwa, domin ba a taba zarginsa da sata ba, domin be tana daukar abun wani ba duk kuwa da kasancewar yana da son abun duniya. Tare da Amal din securitin suka zo suna zuwa ba su tsaya komai ba sauka yi ma AA wani irin mugun riko. Hango hakan da Nana tai yasa ta dawo gurin da saurin, daman can gefe a tsaye ta kara waya a kunne kamar yadda AA ya fada mata ta yi, tsaye tai a gurin rike da wayar tana kallon AA.
“Ban dauka ba, a kasa na ganta Malam karka cikin mutunci a nan”
AA na rufe baki Yarinyar ta soma karyata shi.
“Wallahi karya yake sarkata a jakata na sakata”
Take police din ya tsinka masa mari ya fisgi rigarsa suka turashi gaba, abun ka da abu a bainar jama'a sai mutane suka sako musu na mujiya, kallo ya dawo kansu. Mutuwar tsaye Nana tai ta rasa abun da zata yi idonta ya cika da kwalla ganin an tisa keyar AA gaba da sunan satar da ita ta aikata, gashi tun a gurin sun fara dukanshi, ta kasa cewa komai Amal kuwa sai kokarin labarta mata abun da ya faru take.
“Kin je can gurin waya kin bar jakar Rukayya ashe washe wannan mutumen ya hango sai zuwa yai ya daci sarkarta, mun kama shi sai fadin yake wai tsintarta yai a kasa”
Nana ta kasa cewa sai kallon AA take har aka fice da shi daga dakin taron, kamar a sama Hajiya Babba ta dafa Nana domin sai a lokacin ta lura da ita, sai dai ita Nana ta lura da Hajiya tun farkon shigowarta.
“Daughter lafiya dai?”
Rukayya ce labarta mata abun da ya faru, domin har lokacin Nana gani take kamar a mafarki ne komai ya faru.
“To sai ku yi hankali kuna sake jiki a ko'ina kuma kun san akwai inda ba mutanen arziki musamman irin wannan gurin”
Cewar Hajiya Babba kamin ta kama hannun Nana kamar gaske.
“Zo mu zauna a can”
Binta Nana tai kamar bawa da ubangidansa ta nufi inda Hajiya take ta zauna kusa da ita, kamar wacce bata cikin hayyacinta haka ta rika gaisawa da manyan matan da suke tambayarta ina Ammy, wasu abokan Ammy ne wasu kuma na Hajiya Babba, hannunta na rike da wayar AA sai shafa waya take a hankali. Bata taba sanin wani abu mai suna tashin hankali ba sai a yau, bata taba jin nadama a aikata wani abu ba kamar wannan, he is innocent right? Ita tai causing komai, kuma ya karbe ta ba tona mata asiri ba ya dauki laifin a kansa bayan ya san ba shi ya aikata ba. Bata san lokacin data mike tsaye ba, zata fara tafiya sai Hajiya ta rikota daman haka take nuna mata son munafurci har take ganin kamar ta fi son ta da Ammy.
“Daughter tafiya zaki yi?”
Nana ta kalli Hajiya idonta tab da hawaye, ta yi shiru sai kuma ta tuna Hajiya mai share mata hawayenta ne a koda yaushe.
“Hajiya ina son magana da ke”
Hajiya ta mike tsaye tana kai bakinta saitin kunne ta Nana a zatonta maganar ta baki da baki ce kawai, sai Nana taja hannunta suka fita daga gurin, sai da suka isa gurin da AA ya faka motarsu sannan ta sake hannun Hajiya ta sunkuyar da kai kasa.
“Lafiya dai daughter fada min matsalarki”
Nana ta kalleta tana fashewa da kuka.
“Hajiya wanda aka ce ya saci sarkar nan ba shi ya sace ta ba”
“Ban gane ba”
Cewar Hajiya tana kallon Nana da mamaki, zuciyarta na cika fal da farinciki jin furuncin Nana ta san wata kila zata fadi cewar ita ta saci sarkar wanda shi zai fi komai yi mata dadi a yanzu, saboda Ammy za a zaga ita kuma yabe ta na ganin tana son hada auren Nana da danta.
“Ni na sata.... Amman ban san miyasa n sata ba...ban san mi zan yi da sarkar ba...”
Hajiya ta kamo hannunta.
“To ya akai yace shi ne?”
“Ya fanshe ni ne, amman ba shi ya dauka ba, ni na dauka Hajiya ki taimaka masa kar a masa komai dan Allah, Wallahi Sardauna ba barawo ba ne na yarda da shi”
Hajiya ta ji wani abu ya sauko mata tun daga saman kanta har cikin kafafuwanta.
“Ke wa kika ce?”
“Sardauna”
Nana ta maimaita tana kuka sosai, domin wata kalar nadama ce ke rabarta.
“Ke sake fadi na ji”
Hajiya ta sake tambaya baki saki.
“Sardauna, Hajiya Wallahi ba barawo ba ne, dan Allah ki taimaka masa kar su masa komai saboda da ni”
A take kallo ya koma sama, sai murnar Hajiya ta koma ciki, wani kalar fever ta ji yana sauko mata.
“Saurayinki ne?”
“Aa shine sabon direbana”
Nana ta fada har muryarta a shakewa, jikinta sai bari yake irin na wanda kuka yake cinta sosai. A take Hajiya ta saka salati.
“La'ilaha illala muhammadu rasulullah sallalahu alaihi wassalam, ki ce ni na siya da kudina”
Nana bata kula zancen ba balle har ta gane inda ta dosa, wani irin dogon numfashi Hajiya ta ja ta sauke tana kara nanata sunan.
“Sardauna...”
Jin hakan yasa Nana ta rike hannayenta.
“Hajiya dan Allah ki taimaka kar a masa komai”
Hajiya ta jata jikinta ta rumgume tana rarrashinta kamar gaske.
“Daina kuka yanzu zan kira Babanki Jarma na fada masa ya binka inda aka kai shi”
Tana fadin hakan ta saki Nana ta nufi gurin motarta, Nana ta bi bayanta da sauri. Direban Hajiya na hangota ya fito cikin motar ya bude mata gidan baya, kamar daman abun da take jira kenan tana isa ta shiga gidan baya ita da Nana shi kuma ya tashi motar. Nana ta kwanto jikin Hajiya hawaye a sauko mata, can kuma ta dago hannunta tana ta kallon tafin hannun ita kanta bata dauka bayan Ammy da Mai Martaba da take yi ma sata ba zata iya yin wata a public place like this, kuma sarka. Ta jimke hannun wasu hawayen a sauko mata. Ganin hakan yasa Hajiya ta ciro wayarta a jaka ta nemo number Jarma, sai da wayar ta dade tana ringing sannan ya daga.
“Hello Jarma”
“Hajiya barka da dare”
“Dan Allah yar wata muka samu, wani yaro ne yai sata a gurin bikin da muka zo na yar Faro Ambassador, shine police suka tafi da shi, to ina son ka saka a binciko mana wane police station aka kai shi”
“To yayi, amman kin yaron ne?”
Hajiya kamar tana jira ta amsa da karfi.
“Eh sunanshi Sardauna, shine sabon direban Nana”
Daga dayan bangaren Jarma ya amsa da kuzarinsa.
“Sardauna fa kika ce Hajiya?”
“Eh a taimakawa daughter na kar ta shiga damuwa, gani tare da ita, zan kira ka anjima”
Bata jira abun da zai ce ba ta kashe wayar tare da kai hannunta ta taba Nana.
“Ki daina kuka ai komai zai zo da sauki tun da na fadawa Jarma”
Nana ta rumgume Hajiya tana jin wani irin son ta a ranta, domin ta tabbatar da Ammy ce ba zata mata haka ba. Apartment din Hajiya direban ya faka motar, sai Hajiya ta fito rike da hannun Nana ta nufi cikin gidan da ita, har cikin dakinta ta kai ta kwantar.
“Kwanta a nan ki huta”
Ba musu Nana ta kwanta a gurin, Hajiya kuma ta karasa ciki ta aje jakarta ta fice daga dakin rike da wayarta. Tashi Nana tai zaune ta kunna Power button din wayar sai ta samu wayar a pattern da katon hoton AA a din daya cika screen din wayar, wani irin tausayinsa ne ya kara sauka a ranta, ji tai kamar bata da natsuwa idan bata san halin da AA yake ciki ba, hakan yasa ta mike tsaye ta bi bayan Hajiya.
Hajiya ta na fitowa daga dakin, ta shiga second room dinta ta rufe ta kira number Jarma, wannan karon bugu daya ya dauka.
“Jarma”
“Hajiya”
“Jarma a nemo inda yaron nan yake, maganar bokan ta tabbata sunanshi Sardauna”
“Hajiya ai ni abun ya bani mamaki, ace har kin san shi”
“Ni ma sai yanzu nake saninsa, amman ni na siye macijin da hannuna, domin ni na dauke shi aiki ba tare da sani ba, kuma ba tare da na yi bincike ba, ina cikin tashin hankali Jarma ka nemo yaron nan”
“Dole zan saka a nemo shi ai, ba ke dai ce a matsala ba har da ni”
Jarma ya amsa daga dayan bangare.
“Kuma idan an samo shi, ka fada min da wuri, a juyar da case dinsa daga sata zuwa kisan kai, a tura shi gidan kaso, ko nawa ake ashewa zan kashe, ka shigo da safe zamu yi, domin dole ne mu koma gurin mutanen nan kar abubuwan su kara mana yawa, ina murna Nana ta fara dan hali sai kuma abu ya juye min haka”
“Gaskiya kam ya kamata mu koma garin nan daga can ma sai su sanar da mu wacece Fadime ita ma kar ta ribance mu”
“Haka ya kamata, muna ta sanyin jiki abubuwa suna faruwa da mu, ya kamata mu yi maganin komai tun a yanzu”
“Wai daman Nana ta fara dan hali Hajiya”
“Hmm Jarma kenan, ai har abunda ya fi sata sai Nana ta yi, ba ni da buri sai na ganin kukan Ammy kuma sai ta yi shi indai ina raye, yanzu dai ka nemo yaron kuma ka san wanda aka hannatawa case din, gobe ka zo ka karbi kudi ayi komai tun da wuri, abun ai ya zo mana da sauki tun da har haka ta faru”
“Shikenan Hajiya zan shigo gobe inshallah”
“Yayi kyau sai anjima”
Ta fada tana sauke wayar, tare da sauke wata doguwar ajiyar zuciya.
“Dole ne na shirya jibi nai tafiyar nan, idan ba haka ba ban san me zai sake faruwa ba, ya kamata na tari Fadimen ita kuma tun kamin ta tare ni”
Line Hajiya Talatu ta nemo ta aika mata kira, ringing daya ta dauka kamar daman can jiran kiran take.
“Hello Talatu”
“Hajiya ina cikin tashin hankali, Waziri ya dage sai ya hada auren nan”
Ta amsa da muryar kuka wanda hakan ke nuna ta ci kukan har ta gode Allah.
“Nima ina cikin nawa tashin hankali, amman dai ki shigo gobe sai mu yi magana, be kamata mu kyale yarinya akaita ga halaka ba”
“Shiyasa nake son tun wuri mu tafi garin nan tun da aikinsu kamar yankan wuka ne, su wargaza komai tun abu be yi nisa ba”
“Hmm ke dai ki shigo gobe kawai”
“Tau Allah ya kai”
Hajiya ta sauke wayar tana jijjina lamarin bokayen nan sai yanzu ta kara tabbatar ba da wasa suke aiki ba, kuma dama ta dade tana son irinsu masu aiki kamar yankan wuka. A yanzu ne take jin ya zame mata dole ta je garin ko dan maganin matsalolinta.
**
Shirun da Nana ta ji ne ya tabbatar mata da Hajiya ta gama wayar da take, sai ta daga daga jikin kofar wasu sabbin hawaye masu zafi na sauko mata. Why Hajiya zata juyar da case din to kisan kai bayan tace zata taimake ta? Mi Sardauna yai mata? Anya ya cancanci haka? Da sauri ta ta bar kofar ta dauki hanyar da zata sadata da part dinsu hawaye na sauko mata kamar ba gobe, daman ta bi bayan Hajiya ne da zimmar ta sake rokonta sai ta tararda kofar dakin a rufe tana kokarin turawa ta ji sautin muryarta na tashi kadan-kadan hakan yasa ta kai kunnenta domin ta ji abun da Hajiya take fada, domin azatonta zata ji ko Jarma ya gano inda suke ne ko kuma wani abu sai gashi ta ji mummunan abu da bata taba mafarkin ji ba, kuma ba tai zato daga Hajiya ba.
“Miyasa ma nai satar to? Why?”
Ta tambaya cikin kuka tana jin haushin kanta. Ganin bata da mai taimakonta a yanzu wanda zai fito da Sardauna, bata isa ta tunkari Ammy da wannan maganar ba, daman daga Hajiya sai Zainab ne suke mata gata a gidan, sai kuma Shattima, sai dai ba zata iya fada masa ba, gudun kar Ammy taji ko Baba Waziri. Silently ta isa bangarensu ta shige dakinta ba tare da kowa ya sani ba. Maida kofar dakin tai ta rufe ta jingina da kofar ta fashe da sabon kuka tana kallon hoton AA dake gaban wayarsa. Haka ta shafe awa uku zaune a gurin tana aikin kuka abun da bata taba ba, idanuwanta da fuskarta suka kumbura, tun tana jin kuzarin kuka har ta nemi kuzarin ta rasa. Can ta mike tsaye ta cire tufafin jikinta ta dauki tufafin bachi ta saka ta shiga bandaki ta wanke fuskarta, sannan ta fito ta hau saman gadon ta kwanta ba dan tana jin zata iya bachin ba sai dan jin jikinta da take da rashin kwari. Misalin 10 da yan mintuna kiran Anti Rabi ya shigo wayar AA dake hannun Nana.
Second Mother shine rubuce a wayar dauke ta emoji din heart. Kasa daukar kiran tai sai kawai tai rejecting call din ta kashe wayar gaba daya.
“Innalillahi”
Ta furta, she can't remember when last ta furta wannan kalmar ma. Bata taba jin ta a tashin hankali irin yau ba, abun da ta ji Hajiya Babba na fada ya fi daga mata hankali fiye da halin data jefa AA. Sauka tai saman gadon ta bude kofar dakinta ta fito falo, babu kowa a falon an kashe kayan kallo wanda hakan ke nuna Ammy tana bangaren Mai Martaba ko kuma tana shirin tafiya ne. Dakinta Nana ta dosa tana taba kofar ta ji ta a bude sai ta tura ta shiga, duk wani tsoron kar Ammy ta ji da take da gudun fadanta ko dukan Baba Waziri sai ta ne meshi ta rasa, bata da buri a yanzu da ya wuce AA ya zama free. Daga bakin kofar ta tsaya tana kallon Ammy dake tsaye jikin wardrobe dinta tana daukar wasu kaya, ta jikin madubin wardrobe Ammy ta hango Nana sai ta juyo tana wani kallo fuska ba yabo ba fallasa.
“Ya akai?”
Nana ta kalleta hawaye na sauko mata, sai kuma ta nufi inda take ta karasa har kusa da ita.
“Ammy... ”
Sai kuma tai shiru hawayen na sauko mata.
“Ammy na san ni da ke don't get along, amman dan Allah ki taimaka min”
“Minene?”
“A gurin bikin da naje dazun na su Amal na saci sarkar gold ta kawar Amal, nasan be dace nai sata ba right? Na sani amman ban san miyasa nai ba, direbana sai ya karbi sarkar yaje ya maida shine suka ce shine ya dauka kuma Wallahi ba shi ba ne ni ce, shine suka kira masa police aka tafi da shi, dan Allah ki taimaka Ammy a fito da shi pls”
Ammy ta saki kayan hannunta sun zube kasa, tana yi ma Nana wani irin kallo kamar na tsoro kamar na mamaki, a take idonta ya cika da kwalla. Tassss ta dauke Nana da wani irin mahaukacin mari, cikin wani irin zafin nama da bata taba sanin tana da shi sai yau.
“Sa... Sa... Sa... Sata Nana?”
Ta furta daker hawaye na sauko mata, Nana kam tun da Ammy ta tsinka mata mari tai bata da sauri tana ma Ammy wani kallo tsoro domin ji take kamar babu fuska a jikinta.
“Na san be dace nai ba Ammy na sani....”
Ta furta a rikice tana girgiza ma Ammy kai. Sai kuma ta juya da gudu da fice daga dakin, Ammy ta bita da kallo baki sake, wani abu ta ji yana mata yawo a zuciya yana neman numfashinta, da sauri ta rike murfin wardrobe din ta jingina ta zauna a kasa tana numfashi daker.
“Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un”
Ta furta daker tana ta kokuwa da numfashinta.
FADIME POV.
Hannu biyu Wasim ya saka ya dauki Fadime ya ya nufi kofar