Showing 225001 words to 228000 words out of 273152 words

Chapter 76 - FULANI BOOK COMPLETE DOCUMENT by Khadijah Candy .txt

29 Aug 2024

72710

saboda ta samu idon yai ja ace ita ma ta yi kuka, domin abu ne mawuyaci ka ga maye na kuka, is hardly, suna da karfi halin bala'i da bushewar zuciya, sai da ta murza idon har ta ji ya dan soma mata ciwo sannan ta nufi gidan tana ta mitsika idon kamar munafuka.
Haka ta ratsa cikin manyan motocin ta shiga cikin gidan, kai tsaye ta nufi bangaren Hajiya Talatu, tun a bakin gate din ta fara hango mutane a harabar wasu akan kujeru wasu akan tabarma wasu akan carpet, cikin karfin hali ta nufi gurin tana isa ta fara musu sallama tana kukan karya.


“Jama'a to sannu mu da wannan rashi”


Mutanen da ke kusa da ita suka masa mata duk da kasancewar ba kowa ya san ta ba a gurin, wadanda ta sani suka santa suna daga can ciki, sai da tai musu gaisuwa sannan ta mike tsaye tana kuka ta fara tsallaka mutane har ta isa bakin kofar falon ta shiga ciki tana fashewa da wani sabon kukan, can ta dago kai ta karewa mutanen da suke cikin falon kallo ka zata ga yaran Hajiya Talatu tai musu gaisuwa ko kuma wanda ta sani sai tai arba da abun da ba tai zato ba balle tsammani, tsaye tai cak lokaci daya ta daina kukan tana kallon ikon Allah. Maijidda take gani tsaye a kofar dakinta tana kallonta fuska babu annuri.


“Ahhh ahh ahh Jama'a ba Maijidda ce ta rasu ba?”


Iya ta tambaya da karfi tana kallon Maijidda da ita kadai take ganinta. Duk mutanen da ke kallon kallonta suke har Ammy dake zaune a one seater rike da carbi da kuma abokiyar zaman Hajiya Talatu wato Hajiya Maryam dake kusa da kujerar Ammy.


“Jama'a ba ku amsa ni ba, ba Maijidda ce ta rasu ba?”


Ta sake tambaya da karfi.


“Ita ce mana”


“To ya nake ganinta gata nan a tsaye tana kallona”


Iya ta fada tana nuna kofar dakin Maijidda, kusan duk wanda ke cikin falon sai da ya juya yana kallon kofar dakinta dake rufe babu wanda ke ganinta sai Iya, sai mutanen da ke kusa da ita suka fara matsawa suna mata kallon tsoro.


“Maijidda...”


Iya ta kira sunanta bata amsa ba, kuma bata motsa ba sai wani mugun kallo iya take ganin Maijidda na mata.


“Ke kika cinyenta kenan shiyasa kike ganinta, ku nemo maza su fitar mana da matar nan a tsareta can waje”


Ammy ta fada daga inda take zaune, da saurin mutanen da ke gabanta suka tashi domin aiwatar da abun da ta fada, Iya kam bata ma san wainar da Ammy take toyawa ba domin hankalinta na gurin zanenta da ta ji ana ja, tana duba kasa sai ta ga Luna Luma da Labib.


“Luma Luna Labib?”


Ta fada tana dukan kirjinta, sai zaro ido take jikinta nata rawa, kamar jira ake ta dago nan ma sai ta soma ganin yayan Ammy da ta cinye da kuma Jakadiya da wata Jekadiya da duk matan da ta ci na Shattima sai da ta fadi sunansa domin ganinsu take ido da ido suna mata mugun kallo.


“Miyasa na ke ta ganin mutanen da na cinye? Miyasa zan yi ta ganinsu bayam na riga na cinye kurwarsu? Ya haka wai haka? Lafiya dai? Me ke faruwa ne?”


A gabar da tai maganar ne mazan da Ammy tace a kira suka shigo sai Ammy ta daga musu hannu alamar su dakata, matan dake jikin kofar kam tuni wasu sun yi waje wasu kuma sun masa can nesa da inda take.


“Miyasa na ke ta ganin mutanen da na ci? Mai Martaba? To ai shi ban ci shi ba, na kurwarsa na nan aje ban cinye ba”


Ta fada tana kallon Mai Martaba dake tsaye gabanta.


“Jama'a ku min rai, ya haka wai?”


Tana kiran jama'a sai kowa ya kara nisantarta, Ammy kuma ta mike tsaye da sauri tana nuna ta.


“Mai Martaba fa kika ambata Iya? Innalillahi Wa'inna Ilaihirraji'un ku kira min Wazari”


Duk wani abun da Ammy take fada da hayaniyar mutane bata jin ko daya gaba daya idonta baya nuna mata komai sai nutanen da ta ambata su kawai take gani. Wani irin zafi ta soma ji a jikinta kamar ana yanka mata reza a fata, can kuma ta soma jin kankarar maitar dake cikin cikinta ta soma motsawa tana mata yawo. Da farko bata ganin kowa yankan kawai take ji ta ko'ina har sai da tai magana.


“Yankana ake fa! A jikina ina jin yakan wuka”


Kamar jira ake tai magana sai ta soma ganin mutane da ta cinye suna yankanta ta ko'ina kamar an aikosu. Mutanen da ke falon kam kowa ya hade waje daya yana kallon yadda take tisge tufafin jikinta tartsatsin wuta na fita a jikinta kamar ana ƙira. Ƙofar Kitchen aka bude mutanen dake cikin falo suka samu fita ta gurin domin Iya na tsaye kusa da kofar falo ne.


SIRLEEM POV.


Cikin gidan ya koma a tunaninsa Hajiya Babba tana ciki kamar yadda ya fita ya barta sai ya samu bangaren Babu kowa sai Hadimai, wayarsa ya ciro ya kira Kausar sai ta dauka tana tana ta kuka ta sanar masa cewar suna asibiti, jikin na rawa ya koma motarsa ya dauki hanyar asibitin, kamin ya isa har ya matsu domin gani yake kamar yana sa za a sanar masa cewar ya rasa Hajiya Babba. A lokacin da ya isa ana cikin gwaje gwajen jininta ne yana gurin aka mata allura ta samu bachi, sai a lokacin ne suka samu labarin rasuwar Maijidda sai ba su da kuzarin zuwa dukansu domin hankalinsu yana gurin mahaifiyarsu. Karima ce ta kira sauran yan'uwa tana sanar musu abun da yake faruwa ita da Kausar, Sirleem dai yana zaune daga waje sai tunanin Falmata yake yana ta motsa hannunsa da ta rike shi da shi a hankali, sai a yanzu ya tabbatar yana sonta, sai dai idan har Hajiya ta zabi ya rabu da ita dole ne ya aikata ko dan samun farincikin mahaifiyarsa
Yana a gurin har la'asar a masallacin dake asibitin yai sallah zahar da la'asar abinci da aka kawo ma kasa ci yai gaba daya ba shi da natsuwa kuma hankalinsa ba zai kwanta ba har sai ya ga Hajiya ta dawo normal.
Jurry kam tun 2pm ta bar asibitin sakamakon wani azababben ciwon kai da ya saka ta gaba kamar kan zai cire har wani abu take ji a ciki kamar gero. A hankali Sirleem ya tura kofar dakin ya shiga sai ya samu Kausar a zaune ta kurawa mahaifiyarta ido, kana ganinta ka san ta yi kuka har ta gaji.


“Sis”


Ta juyo ta kalleshi, sai ta ji tsanarsa cikin ranta saboda tana ganin shine silar ciwon Hajiya Babba. Dauke kai tai ba tare da ta amsa ba ta cigaba da kallon Hajiya Babba.


“An fadawa Ammy kuwa? ”


“Aa ban kira ba ina ganin suna gurin gaisuwa, kuma ko na kirata ai dadi kawai zata ji”


“Wani irin dadi kuma Kausar?”


“To son Hajiya take yi balle”


“Ki daina wannan maganar, abun da ke tsakanin Hajiya da Ammy dabam babu ruwanki a ciki”


Har zata sake magana sai dai ganin Hajiya ta motsa yasa duk suka maida hankali gurinta suna kallonta, ta dade tana motsin sannan ta bude ido tana kallonsu.


“Sannu Hajiya”


Kausar ta fada, sai ta daga mata kai ta amsa daker


“Yauwa su waye ku?”


Daga Sirleem har kasar kallon juna su kai da mamaki, ga bakinta yana nan kamar da be dawo daidai ba, sai dai wanna karon ta samu damar magana yunkurawa tai ta tashi tana karewa dakin kallo.


“Hajiya ni fa Kausar”


“Kausar kuma? Wace Kausar din? Ko. Ke ce mu ka je tare da ke gurin bokan nan?”


Ba shiri Kausar ta bude baki idonta na cika da kwalla.


“Hajiya ta yi losing memory ta Ya ya”


Kamin Sirleem da ke tsaye yace komai Hajiya ta girgiza kai.


“Aa ke ce dai ban san waye ke ba, Shi ai Sirleem ne dana ko?”


Sirleem ya daga mata kai cike da nauyin bakin da ya kasa barinsa ya amsa. Sai ta kama rigarta tana wasa da ita kamar wata yar yarinyar tana turo bakinta dake gefe gaba.


“Ina Falmata? Daman ance yarinyar nan zata lalata mana komai, da Falmata da Fadime, da Sardauna, kuma sun lalata, babu abun da ban saka ayi ma Falmata ma amman bokan nan sai cewa yake wai na yi latti, daga nan muka tashi muka tafi Katsina ni da Hajiya Talatu da Jarma da Juwairiyya, saboda kawai abubuwa su daidaita amman komai be mana kyau ba, har sata an laka mata amman sai da ta lalata mana shiri”


“Kausar je ki kira likita”


Sirleem ya fada zuciyarsa na bugawa da mugun karfi, da gudu Kausar ta tashi ta fice daga dakin tana kuka, Sirleem ya zauna kusa da Hajiya Babba yana kallonta cikin tsananin damuwa, sai ta kalleshi tana kokarin fashewa da kuka irin yadda shagwababbin yara suke yi.


“Ka ga sun fada mana akwai tafiyar da ba dawowa ashe Talba ne zai mutu”


Sai kuma tai shiru kamin likita ya shigo ta sa ke cewa.


“Kuma na sake sa an yi ma yarinyar Fadime aiki fa, na kira aljani aka mata magani ta bata, da muka je can garin Garuk ma na fadawa wacan bokan ya nisanta ka da Falmata ya saka maka son Nana, kuma Nana ta lalace, a kashe min Shattima da Mai Martaba saboda na samu Talba ya hau sarauta amman duk na yi a banza...”


Sirleem ya mike tsaye da sauri yana jin kunnuwansa kamar ba za su iya daukar abun da Hajiya take fada ba, da gaske ta aikata ko kuwa dai fitar hankaline ya saka ta haka? Runtse ido yai yana jin duniyar na juya masa, likitan na shigowa sai yai saurin daga kansa sama domin hana hawayen da suka cika idonsa zuba.





_________
Ina mata matan kwalisa Matan da suka ansa sunansu na Mata? Ina wadanda ke cewa mun yi mun yi bamu ga amfaninshiba? Hmmm to ku zo ga Yar gidan Maifata ta zo maku da Al ajabu, dan tsugunno, gumba da tsimi da Zuma daban daban, maganin sanyi na maza da Mata. Ga kuma garurruka irinsu mallakau sabuzu kuwa, sa bahaushe saibi, Dan hubbare kafi malam aiki, ke kadai ke da miji, dahuwar kaza, tattabara, ciccibi da dai sauransu. Ba anan kayanmu suka tsaya ba, muna hadin amare na musamman turaren sutura turaren tsugunno turaren wanka da na daki da na jiki duka 4amare nasu na musamman ne, amma ga tsuhuwar da ke son komawa yarinya itama zata iya zuwa ahadata kai abundai sai wanda ya gani, dan haka karkubari abaku labari, domin neman karin bayani zaku iua nemana ta wannan number 09029891757 ko 08169311410, muna aikawa ko'ina a fadin kasar nan har waje kasar nan muna aika kaya.
Address: Nasarawa Samaru Area gurin masallacin mai sola Gusau Zamfara state Nigeria.
03/12/2021, 18:59 - 🤐🤐🤐🤐: Ina mata wadan da suke son sayen kaya kamar su laces, atamfa, materials,shadda lace, normal shadda, atamfa lace, veil's, shoes and bags, da sauransu kuzo ga MAMAN AHMAD tazo dan tashare hawayenku kudai kunemeta ta wannan number 08032350261 banan kadai tatsayaba tanada kayan order kama dana kitchen,tufafi,kuma order ta Bata dadewa ,tana saida kayan gyara kamar su Al'ajabu,shu'umar humra wannan inbakida aure Bama saida maki,hadin kaza me yasin,akwai na mallaka wanda wannan ana rubuta shi atafin hannu ke zakiyi wannan,turaren wuta,kulacca,da sauransu
Mazauninsu nanan a samaru Gusau Zamfara state
Muna aika kaya kowace jaha da wajen kasar nan cikin aminci da yardar Allah kunememu kusha mamaki


https://wa.me/qr/MYY56BH3RMFDG1






*Khadeeja Candy*




*BAN YARDA KOWA YA DORA MIN LITTAFI A YOUTUBE CHANNEL BA TARE DA IZININA BA, YIN HAKAN ZAI IYA JEFA CHANNEL DIN CIKIN MATSALA, DOMIN BA ZAN KYALE BA. DON HAKA AKIYAYE!*




Kuka take sosai daker Momy ta shigo da ita cikin falonta.


“Yaushe kuka yi aure?”


Momy ta tambaya cike da mamaki, sai dai Falmata ba ta iya amsawa ba saboda kukan da take, Momy ta zauna kusa da ita ta dafa ta.


“Ki daina kuka kuka ba zai miki maganin komai ba, da kuka yana magani da ya miki magana tun a lokacin da kike matsala”


Iyakar kokari Falmata ta yi na ganin ta daina kukan amman abun ya garara domin zuciyarta ta ki aminta cewar Sirleem ya bar ta kenan a lokacin da take tsananin bukatarsa.


“Ina takardar da ya baki? Ko da baki ya furta miki?”


Falmata ta girgiza kai alamar aa ta nuna ma Momy upstairs, Momy dake tsaye ta nufi upstairs din ta shiga dakin Ameer tana dubawa sai tai arba da takardar a kasa, dukawa tai ta dauka ta bude tana karantawa.


‘Ban abun da na aikata kuskure ba ne sai a yanzu da mahaifiyata ta shiga damuwa saboda ni, Na san kina tsananin bukatata, kuma na san rabuwar mu zai jefa ni a matsala fiye da ke, sai dai ba zan iya kin bin umarnin Hajiya ba, matukar ta bukaci na sake ki zan aikata hakan ko kuwa hakan na nufin karshen rayuwata ne, idan har ta zabi na sake ki, zan aikata haka zan aiko miki ta takardar sakin ba za sake dawowa gareki ba’


“Ta ya akai Sirleem ya auri yarinyar nan? Yaushe? Miyasa ya boye min?”


Momy ta tambaya sannan ta juyo ta fito daga dakin.


“Wannan ai ba saki ba ne”


Momy ta fadi hakan a yayinda take saukowa daga stairs din, sai Falmata ta dago da sauri tana kallonta tare da mikewa tsaye.


“To minene?”


Momy ta karasa kusa da ita ta karanta mata abun da ke rubuce a cikin takardar, sai Falmata ta shaye hawayenta tana jin sanyi a ranta. Momy kam kallonta kawai take irin kallon na na babba da yaro, ko ba a fada ba ta san Sirleem ya kai a so shi amman Falmata ta haukaci tana kuka ya bata mamaki domin a tunanin Momy Falmata bata san wani abu so ba.


“Zauna”


Momy ta fada sai Falmata ta zauna ta sunkuyar da kai kasa. Momy ma ta zauna tana kallonta.


“Yaushe akai auren? Ya akai ya aurenki?”


“Ni ma ban san shi ne mijina ba har sai daren da aka daura auren... ”


Sai ta labartawa Momy abubuwan da ta sani har zuwa yau. Ba karamin mamaki Momy tai ba, so that's mean tun a lokacin da tai masa maganar Ameer kenan yana da wannan plan din ko kuwa daga baya ne? Shiyasa ya ki yarda da Ameer ya aureta? Momy ta sake kallon Falmata tana murmushi.


“Ko da ace Sirleem ya sake ki, na tabbata zai dawo gareki, kin san saboda me?”


Falmata ta girgiza kai alamar aa.


“Saboda yana sonki kuma so ba na wasa ba, duk namijin da zai yarda ya auri mace ba tare da sanin kowa na shi ba kuma auren fari ba dan komai ba sai dan ya taimake ta, to hakika wannan namijin ba karamin sonta yake ba, ko da makoci kike da shi ya damu da ke, za ki jidadi balle wanda ya zabi dauke ke kacokan daga wacan duniyar marar dadi a saka ki a wata rayuwar mai cike da daula da farinciki, kamin ke Sileem yana soyayyah da wata Mansura, amman be duba halin da zata shiga ba, shi ma be damu da duk irin abun da Hajiya da mu yan'uwan mahaifinsa za mu masa ba, ya runtse ido baya ganin kowa sai ke da damuwarki, duk da kasancewar ba ki yi boko ba, kuma ke ba yar wani mai arziki ba ce, Sirleem yana sonki sosai Falmata”


Falmata ta dago ta kalli Momy sai Momy ta kama hannunta ta rike.


“Na jidadin da ba ki auri Ameer ba, da yanzu dan'uwanki kika aura kenan? Kuma na jidadin da zuciya bata saka ni na aikata kuskure ba, da yanzu ban san da wane idon zan kalleki ba ke da dan'uwanki, Na miki alkawari Falmata Sirleem ba zai taba sakinki ba, ba zan bar shi ya sake jefaki a matsala ba, domin ba Hajiya kadai take da iko da shi ba, ni ma muna da iko da shi, kuma Allah be ce a bi uwaye a tsaba masa ba, ki kwantar da hankalinki kin ji?”


Falmata ta daga kai wasu hawayen masu kama da na farinciki da alhini na sauko mata. Momy ta tashi ta shiga kicin ta sake hada mata wani tea tana da godiya ga Allah da be saka ta aikata dashen da kawarta Umaima ta zugata tai ba, kenan da ta yi mata dashe da kwan mijin mahaifiyarta kuma mahaifin yayanta. Falmata ta saka hannu biyu ta karbi kofin tea, tana sha a hankali kalaman da Momy tai mata suna ta mata yawo a kwakwalwa, upstairs Momy ta nufa after like 30 min ta sauko rike da jakarta da makullin motarta.


“Zan tafi gurin aiki”


“Allah ya tsare Momy ya dawo da ke Lafiya”


“Ameen”


Momy ta amsa tana kallonsa sannan ta nufi kofar fita ta fice. Sai da ta ji tashin motar Momy sannan ta aje kofin tea da ta gagara shanyewa ta kwanta kan 3 seater din tana sauke numfashi a hankali, idonta sai ciwo suke. Tana kwance a gurin har aka sallah azahar, sannan ta tashi ta shiga dakin Ameer tai sallah, ta hau gadon ta kwanta tana ta kallon hoton mahaifiyarta, sai kusan uku da yan kintuna Momy ta dawo, sanin ta bar Falmata a gida yasa ta biya tai musu takeaway, da key dinta ta bude kofar falon ta shigo, sai da ta da ta shiga dakinta ta aje jakarta da kayan hannunta sannan ta dauko leda daya ta nufo dakin Ameer inda Falmata take, ta tura kofar dakin a hankali domin a tunanin ko Falmata tana bachi ne sai ta ganta farke tana kwance saman gadon idonta na kan hoton mahaifiyarta hawaye sai sauko mata. Momy ta karasa kusa da ita ta aje mata ledar.


“Tashi ki ci abinci na san ba ki ci komai ba ni ma kuma na dawo a gajiye shiyasa na yi mana takeaway be zama lallai na iya dafawa ba”


Falmata ta yi saurin boye fuskarta tana amsawa Momy.


“To na gode”


Momy ba ta ce mata komai ta nufi gurin da hoton yake ta juya shi, sannan ta fice dakin. Sai da ta fita sannan Falmata ta tashi ta share hawayenta ta sauko kasa ta bude abincin ta fara ci, turashi kawai take ba dan tana jin dadinsa ba, kamar yadda bata jin yunwa


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login