Showing 243001 words to 246000 words out of 273152 words
Chapter 82 - FULANI BOOK COMPLETE DOCUMENT by Khadijah Candy .txt
ciwon kai, duk asibitin da aka kaita cewa suke ba su ga komai ba, wasu kuma su ce tana shaye shaye ne ko ta taba yi shine abun ya dawo mata yana son taba mata kwakwalwa, alhalin bata taba shaye shaye ba, sai dai mutanen da suka ji abunda Hajiya Babba take fada ya san tare suka shirya sherin suna gane cewar hakkin mahaifinta ne da kuma abubuwan da suka kulla ne ya dawo kansu, daman can idan kai sheri abun ya dawo maka zai maka illa fiye da wanda akai wa sherin, musamman abun da ya shafi aljanu.
Two days after an maida Hajiya Babba gurin Familynta da suke nan Yola Karima da Kausar suka koma can domin kula da mahaifiyarsu yadda ya dace kasancewar bata da wanda ya fisu a yanzu domin mostly wadanda suke uwa daya uba daya duk sun rasu, sai dangin yaya da kane ko kuma yayansu, and when ever abu ya same mutun mai nauyi irin wannan ba kowa zai Iya jinyarka ba sai na ka, su kansu zama gidan ba zai musu dadi ba saboda abun da Hajiya Babba ta aikata duk da kasancewar babu mai tsangwamarsu sai dai su suna tsarguwa a cikin gidan sun saka sakewa, musamman Kausar da take ganin gidan ya mata empty saboda babu Hajiya Babba a ciki.
Sati daya da maida Hajiya Babba Family house aka sallamo Jurry daga asibiti ba dan ta ji sauki ba domin babu abun da ya hausa, daman can babu jikin balle yanzu da ciwo yake ta mata dariya, sai ta koma kamar wata ce mai cutar kanjamau, daga asibitin kai tsaye aka wuce da ita family house na su, a ranar ne Sirleem ya shigo masarautar domin rabonsa da masarautar tun a lokacin da aka kai Hajiya Babba asibiti, bamgaren Ammy yai parking motarsa ya fito a matse ya nufi kofar da zata sada shi da cikin falonta, kamar wani bako haka ya shiga bangarenta, a da idan ya shiga kai tsaye yake wucewa dakinta saboda yana daukar kansa kamar dan gidan saboda Ammy bata tana nuna masa banbanci ba ko kadan, sai dai a yau sai ya samu kansa da kunyar shiga dakin nata, ba dan komai ba sai dan abun da mahaifiyarsu ta aikata, kusan Kausar da Karima da suke cikin hankalinsu ma duk suna cikin damuwa balle kuma da yake yayansu, a falo ya zauna har sai da Jekadiya tai masa sannan ya shiga dakin da sallama. Ammy dake zaune rike da cup ta amsa mata tare da aje cup din kasa.
“Sirleem ya ka zo mana da bakon abu haka? Daman can ka saba idan zaka shigo inda na ke sai an maka iso ne?”
Ammy ta fada da muryar da ke karantarda mai saurarenta wato Sirleem cewar ranta a bace da abun da yai. Kasa dago kai ya kalleta kana kallonsa kasan yana cikin matsala da damuwa kala kala.
“Agafarce ni Ammy”
“Na maka uzuri na yau kadai amman karka sake min haka, akwai abinci a dinning”
Ammy ta fadi hakan ba da dan ta san yana jin yunwa ba ko akasin haka sai dan sanin cewa Hajiya bata masarautar a yanzu, bayan kuma ta san most zamansa a masarautar ne tare da mahaifiyarsa kusan cikin masarautar yake gudanar da rayuwarsa gaba daya.
“No na gode Ammy, daman magana na zo mu yi, kuma na roki wata alfarma a gurinki”
Sirleem ya fada murya can kasan makoshi, har lokacin yana jin kunyar ya dago idonsa ya kalli Ammy. Ammy kuma sai ta gyara zamanta tana fuskantarsa domin alamunsa sun nuna mata maganar da yake son mata mai muhimmanci ce.
“Ina saurarenka”
Ajiyar zuciya ya sauke a hankali sannan ya dan dago kadan yana matsar hannunsa na hagu a cikin na dama tare da hade yawun bakinsa.
“Ammy... Na san kin ji komai kuma kij san komai a yanzu, kuma na san abun da Hajiya da Jurry su ka aikata ba abu ne mai kyau ba, kuma na san irin zafin da kike ji, amman hakan ba zai hana ni roka musu gafararki ba, dan Allah Ammy ki yafewa Hajiya abun da tai miki, kuma ina rokon ki ki roki Mai Martaba shi ma ya yafe mata, ita da juri, ba dan komai ba sai dan su samu sassauci a nan duniya kuma su tashi kiyama ba tare da hakkinku ba, Wallahi har ga Allah Hajiya ko wani be taba labarta mana wani abu ba ni da Kausar da Karima, na mu san komai ba kuma ina fatar laifin Hajiya ba zai yafe su ba...”
Yana cikin maganar idon Ammy ya cika da hawaye.
“Madallah da da kamar kai Sirleem, hakika Allah yayi yana fitar da mai kyau daga marar kyau, kuma yana fitar da rayeyye daga matacce, hakika Hajiya ta yi sa'ar samun da kamar kai, Allah ya maka albarka”
Ta yi shiru tare da sauke ajiyar zuciya sannan ta cigaba.
“Ko kadan ban taba rikon Hajiya da wani abu a raina ba, duk da an san kishi gaskiya ne, amman a tunanina yadda muka girma a haka muna gina rayuwa da yaya komai ya wuce, sai dai ka san zuciyar dan'adam kowa da irin tasa kuma, hakika abun ya ba ni mamaki kuma ya tsorata ni, kuma zan yafewa Hajiya saboda saboda kai kadai Sirleem, ina son ka shaida Allah ma ya shaida na yafewa Hajiya abun da tai min na boye da na bayyane, ina kuma fatar saboda wannan abun da na yi Allah ma ya yafe min, kuma ina tabbatar maka cewar inshallahu Mai Martaba ma zai yafe musu, daman shi sarki ai baban kowa ne, koda baka da alaka da shi ka samu matsala a wani gurin ya sakan kira yayi sasanci balle kuma abun a gidansa? Na tabbatar zai yafe masu”
Sirleem ya saka hannunsa ya taba idonsa dake cike da kwalla.
“Na gode sosai Ammy Allah ya saka da alheri, kuma ina son ki roka min izininsa ina son na fitar da ita waje saboda nema mata lafiya”
“Aa wannan kam hakkin Mai Martaba ne, nema mata lafiya cin ta da shan ta duk abubuwa da suka rataya a wuyansa saboda shi yake aurenta, hakki ne da Allah ya dora masa, kuma na san zai fitar da ita Inshallahu, duk abun da Mai Martaba zai yi a yanzu, yana cikin fushi ne da bacin rai dole mu masa uzuri, amman ina tabbatar maka idan ya sauko komai zai wuce”
Sirleem ya kalleta da duba na girmamawa da ganin kima.
“Na gode sosai Ammy, hakika da ko wace kishiyar uwa za ta zama kamar ke, da yayan kishiya da yawa ba su yi maraici ba”
Ammy ya yi murmushi irin na su na manya.
“Sirleem kenan, kai ma ai da ce yayan kishiya za su zama kamar kai da ko wace kishiyar uwa ba tai bakinciki ba, baka taba ba nuna min banbanci tsakanina da Hajiya ba, Allah ya maka albarka”
“Amin na gode, ni zan tafi a tashi lafiya”
Ya fada sannan ya mike tsaye da zimmar lafiyar sai Ammy ta kira shi.
“Sirleem”
“Na'am”
Ya amsa tare da juyowa ya, sai ta nuna masa gurin zama, komawa yai ya zauna.
“Kar abun ya faru ya saka ka ji wani iri! Har yau har gobe har a bada mi mahaifiyarka ce, kuma Mai Martaba mahaifinka ne, bana son na ga wani canji ko rashin sakewa, kuma kar wannan abun ya saka wata matsala ko rashin jituwa ya shiga tsakaninka da Nana! Ka ji ko?”
Ya dan dago kadan
“Ammy, maganar gaskiya ni a yanzu ba ni da ra'ayin auren Nana, daman can ra'ayin na Hajiya ne ba nawa ba, kuma a halin da ake ciki a yanzu ina da aure...”
Ammy ta masa wani kallo na ban mamaki tana gyara zamanta.
“Na yi aure few days ago ba tare da kowa ya sani ba, kuma na yi hakan ne saboda na ceto rayuwar yarinyar da na aura duk da na san Hajiya ba ta son ta...”
“Ban gane wannan maganar taka ba Sirleem ka yi aure kamar yaya? Kai kake ka haifi kanka balle kai aure ba tare da sanin mu ba? Hajiya ma bata sani ba kenan balle dangin mahaifinki wane irin aure ne wannan?”
Sosai Ammy ta rufe shi da fada, domin hakan da yai ba karamin bata mata rai yai ba, tana masa fada ne a matsayinta na babba kuma mahaifiyarta wanda ko da ace Shattima ne ya aikata haka irin fadan da zata masa kenan.
“Amin aikin gafara Ammy, na san ban yi daidai ba, amman ba ni da yadda zan yi ne saboda....”
Tsinta tsinta ya labartawa Ammy halin da Falmata take ciki da kuma yadda akai aure har ma da yadda Hajiya ta san komai.
“Ba dan aure yana da girma da kima kuma sunna ce mai karfi ba, da sai na saka ka saki yarinyar ba dan komai ba sai dan ka san cewa abun da ka aikata laifi ne babba, amman ba zan yi hakan ba saboda rayuwarka da tata, kuma abun da kai abu ne mai kyau sai dai ka yi kuskure babba gurin aikata hakan”
Sirleem yayi shiru yana sauraren Ammy dake nuna masa bacin ranta.
“Bangaren mahaifinka ka bar mana wannan mu za mu sanar da su, saboda kar abun yai maka yawa, kai kuma ka je kai ta neman yafiyar Hajiya, saboda ba a son bacin rai mahaifiya, Allah ya baka ikon rike matarka da amana kuma ya hada kanku”
“Amin Ammy na gode sosai, Allah ya faranta ranki”
“Idan ka gama boyun sai ka kawo mana ita mu gani, hakika yi dacen mata mai hakuri da tarbiya ga karatun addini na yaba da yarinyar sosai”
“Inshallahu Ammy”
Ya fada sannan ya dan risina mata alamar girmamawa ya mike tsaye ya fice yana mata a tashi lafiya. Sai da ya fito zai shiga motar ya ji wani iri b dan komai ba sai dan tunawa da ada ne sai dai ya nufi bangaren mahaifiyarsa, amman a yau kam sai dai ya bar gidan zuwa na sa gidan..
Cikin damuwa ya isa gidansa, ya dade a motarsa kamin ya fito ya nufi kofar falon, da key din hannunsa yai amfani ya bude kofar falon ya saka kafarsa kamar wani marar lafiya kana ganinsa kasan yana cikin damuwa, kicin ya fara lekawa a zatonta Falmata na ciki, ganin bata nan yasa ya nufi upstairs kai tsaye, dakinta ya fara turawa ya shiga sai ya same ta tsaye tana duba rigar jikinta da alama wanka ta fito take shiryawa cikin rigar da skirt din yan kanti. Tana dagowa sai ta hangeshi ta cikin nadurbi yana takowa zuwa inda take, juyowa tai tana kallonsa.
“Sannu da zuwa”
Be amsa mata ba ya sakar mata murmushi.
“Shiryawa kika?”
“Eh”
“Juya na saka miki zip”
Ta juya kamar yadda ya bukata, amaimakon ya karasa saka mata zip din da ta fara sakawa sai ya zoke shi kasa ya saka hannyensa yana shafa bayanta kamin ya ganganra da su zuwa ya cika hannayen nasa da kirjinta ya lumshe ido ya kai bakinsa ya sumbanci wuyanta, sai ya ji kamar an yaye masa damuwarsa gaba daya a duniyar nan.
“I love you...”
Ya furta mata murya can kasa kamar mai rada. Shiruuuuu tai tana sauraren yadda ta aiki da kirjinta idonta a cikin na shi suna kallon juna ta madubin da ke gabansu. Wani irin bugun kofa da karar bell suka ji lokaci daya, ba kara ta hankali ba, zare hannunsa yai daga jikinta yana motsar lips dinsa, sannan ya juya ya fita, sai ta maida zip dinta ta biyo bayansa ko da ta sauko har ya kai gurin kofar ya bude.
“Mansura... Me kike yi a nan?”
“Dole ka ce me na ke yi a nan tun da ka yi aure macuci mayaudari”
Ta fada cikin kuka sannan ta kutsa ta shigo cikin falon ta kalli Falmata dake tsaye gefen kujera.
“Ai daman na sani, wannan yarinyar ko? Wallahi ka ja mata matsifa kuma ka ja kanka, Wallahi yau har Hajiya sai ta ji maganar nan, kuma wallahi ba zan kyale ta ba”
Falmata ta yi baya baya cikin tsoro idonta na cika da hawaye, Mansura kuma sai yin cikinta take kamar zata riko ta ta doketa.
“Shiiiiiiiiiiiii”
Sirleem ya fadawa Falmata ganin tana son yin kuka. Sannan ya kalli Mansura.
“Ji yadda kika tsoratata, miyasa ba ki yin komai cikin natsuwa ne Mansura”
Mansura ta nuna kanta sannan ta nuna Falmata.
“Saboda wannan shegiyar yarinyar zaka fada min haka?”
“Kar bakinki ya sake furta mata irin wannan kalmar, ba zan lamunta ba get out of my house”
Sirleem ya fada a fusace sannan ya matsa kusa da Falmata ya ja matarsa ya rumgume.
“Ni ni ni ka yi kuskure Sirleem, sai na illataka na illata matarka mark my word”
“Za ki maimaita wannan maganar a kotu, kuma duk abun da ya samu matata ke ce”
Tafi tai tana dariya.
“Eyyyy heyyyy Onídàrúdàpọ̀, apẹ̀yìndà, atannijẹ, daman hausawa ba su iya komai ba sai cin amana, kuma Wallahi i swear to God sai ka san ka taba Yoruba, jẹ itiju, oleshiiiiii oooooooo”
Ta fada cikin daga murya tana masa ihu, ya kyaleta ne saboda ba ya fada da mata a rayuwarsa balle kuma ita da ya san tana cikin jin haushi.
“Fita ki bar min gida ko na saka a wulakanta ki yanzu nan”
“Zan fita ba gida ba ne, zan fita ku kuma zai gagareku zama tun da kuka taba Yoruba kuma yarinyar sai da ya gama cin duwawuya tukuna ya auro ki..... Heeeeeee”
Ta murguda ma Falmata mazaunanta cikin haushi sannan ta nufi kofar falon ta bude ta da karfi ta buga kofar sannan ta fice. Sakin Falmata yai ya karata har gate sannan ya gargadi mai gadin cewar kar ya sake bari ta shigo masa gida, ko da ya dawo cikin falon ya samu Falmata zaune tana kallon kofar cikin tsoro, domin ita dai bata taba shiga wani abu tashin hankali akan namiji ba sai yanzu.
“Ta tafi?”
Yayi murmushi yana zaunawa kusa da ita.
“Ba dole ta tafi ba tun da ba gidanta ba ne, duk wannan iskanci da take tana yi saboda tana ganin kamar ba zan iya mata komai ba, amman zan yi magana da lauyana, za a mana tsakani da ita, domin ba zan yarda tai miki wani abun ba, ke kuma sai ki dage da addu'a”
“Daman bana wasa da addu'a, kuma bana jin wani abu nata zai same ta indai na tsafi ne, ni da Umma take ba ni magani da rubutu na sha, amman addu'ar da nake bata bar komai na ta yayi aiki a kaina ba, na yarda da Allah Sirleem babu abun da zai same ni”
Murmushi yai yana kallon kyakyawar fuskarta.
“Come here”
Ya jata jikinsa ya rumgume tsantsan kamar za a kwace masa ita.
FADIME POV.
maimakon fada ko duka da Fadime za ta sha a gurin Bappa sai ya tarbeta da soyayya da kauna, ya kuma bi ta da addu'ar Allah ya shirya, mutanen gari kuma sai shigowa suke suna yi ma Inna da Bappa barka da arziki, yan rugar sai zuwa ganin Fadime ake tana burge su, a nan dadi ya kumeta tana jin ta samu abun da take so. Babu wanda ya san da labarin wayar da Shattima ya bata sai kawarta Ma'u, bata yarda ta fadawa Inna ba balle Bappa balle kuma har ta kai ga ta nuna musu, kullum wayar na cikin jikinta, bata tabawa sai idan ta shiga bukka ko bandaki, wani lokacin kuma sai ta fakaici idon Inna ta ga ba ya kanta sannan ta dauke ta hoto tana dariya ta boye. Sati daya da faruwar haka Bappa ya kira Shattima akan maganar gidan da Shattima yace ya siya masa. Shattima da kansa ya aiko aka dauki Bappa tare da wasu yan'uwansa Fulani har su uku aka ta fi da su Katsina Ra'ees ya kai shi gidan da aka siya masa, kana ana hannata masa takardun gidan da makullin, take Bappa ya fadi yai ma Allah sujidar godiya yana kuka da hawayensa, yadda yake ma Ra'ees godiya sai ka rantse da Allah shi ya bashi kyautar gidan, Shattima ma kan kasa yi masa magana yai sai da yan'uwansa suka karba su kai wa Shattima godiya sosai su kai masa addu'a da yaren fulatanci kana suka karasa da hausa, ba Bapppa kadai ba ko Inna kasa bachi tai a ranar duk da kasancewar bata ga gidan ba sai ayyana shi take a ranta.
Washe gari Inna da Fadime na zaune waje Inna na zancen gidan da take ganin siyarwa ya kamata Bappa yai wai ya dawo nan ya siya katuwar kona sauran kuma ya siye shanu, Fadime ta turo baki gaba.
“Haba Inna ke ba ki je bunni kin ga yadda suke rayuwa ba, lokacin da n dawo nan ma sai na rika ganin kamar a daji na ke, gaskiya dai mu koma bunni mu ma mu rika cin kaza da kayan dadi”
Inna ta yi magana wayar dake jikin Fadime tai ringing, tun da Shattima ya bata wayar be taba kiranta ba kuma bata san numberta, balle kuma ta shi balle tace ta kira shi kiran ma bata san yadda zata daga ba idan an kirata, arzikinta daya tana gane abun da aka rubuta. Wani irin zillo zuciyarta tai tsabar dadin kiran sai dai bata isa da daga ba a gaban Inna, sai tai zaune tana kallon Inna ko motsi bata yi.
“Kamar waya?”
“Ba waya ba ce”
“Minene?”
Inna ta tambaya cikin mamaki bayan ga karar abu tana ji.
“Memory ne na hade”
Cewar Fadime tana mitsika idon na rashin gaskiya.
“Ina na taba jin memory na waka a cikin mutum? Ina kika gan shi?”
“A lokacin da na je can birni na tsince shi sai na hade da ruwa, shiyasa yake waka yanzu”
“Kuma be tashi waka ba sai a yanzu? Fulani ba za ki daina halinki ba ko?”
Kyalkyalewa tai da dariya ta fiddo wayar da har ta gaji da ringing ta tsinke.
“Na san ba ku iya karbewa ko kuma ku yi min fada shiyasa na boye ta, Shattima ne ya ba ni ita”
Inna ta buge mata baki kamar wanda tai sabo.
“Ke ki rika cewa ranka ya dade, Fulani ba ki da natsuwa”
“To ranka ya dade ne ya ba ni wayar”
Tana cikin fadin haka wayar ta sake ringing, tashi tai da sauri tana kallo red da