Showing 156001 words to 159000 words out of 273152 words
Chapter 53 - FULANI BOOK COMPLETE DOCUMENT by Khadijah Candy .txt
dawo falon ta zauna.
Momy bata dawo gidan ba sai kusan la'asar, a lokacin Falmata na kwance a kasa tana bachi, Momy kamar ta sani ta saka makulli ta waje ta bude kofar ta shigo, sai da ta kawo tsakiyar falon ta tsaya tana kallonta, ta takure guri daya tana ta bachi, irin yadda marasa galihu suke yi, hakan yasa tausayinta ya kara shiga zuciyar Momy, a ganinta kamata yayi ace tana gaban mahaifiyarta ko kuma gidan mahaifinta, amman tana a nan rakube tana bachi.
“Fulani”
Momy ta taba ta, sai ta farka a firgice, ganin Momy yasa ta tashi zaune.
“Sannu da zuwa Momy”
“Yauwa, ki hau kam kujera mana ki kwanta ya zaki kwanta a kasa sanyin tiles din ai sai ya shiga jikinki ga kuma sanyin ac”
“Tau na gode”
Ta mike tsaye ta hau saman kujera ta kwanta, Momy kuma ta hau sama ita da tufafin aikinta, bata sauko ba sai da tai wanka ta shirya cikin wasu tufafin kuma ta sauke nauyin sallah, la'asar sannan ta sauko kasa, ta shiga tashin Falmata.
“Tashi ki yi sallah la'asar”
“Tau”
Falmata ta mike tsaye.
“Ki shiga dakina akwai bandaki a ciki ki yi alwala idan kin fito akwai carpet a gurin sai ki yi sallah”
“Tau na gode”
Momy ta bita da kallo har ta haye sama ta shiga dakin. Sannan ta busar da iskar bakinta ta nufi kitchen, ba karamin mamaki tai ba ganin Falmata ta yi girki, duk da ta san ta fada mata ta girka abun da take so, gas Momy ta kunna ta dauko tafassashen naman dake firgin ta soya sannan, ta soya kwai ta zuba saman shimkafar sannan ta zubawa Falmata nata dabam a plate ta dauko ta fito kicin din, ko da ta fito Falmata ta sauko tana zaune kasa tana kallo.
“Ungo ga wannan ki ci nasan dai kin ci abinci ko?”
Falmata ta saka hannu biyu ta karba.
“Na gode Allah ya saka da alheri”
“Daga yau idan zaki girki ki rika saka nama, wa ke da abincin kula daya?”
“Ya Sirleem”
Ta amsa kanta a kasa tana jin kunyar da bata san dalilinta ba. Momy ta yi murmushi.
“Ai yana da wahala Sirleem ya dawo yanzu, kin ba mai gadi?”
“Aa”
“To ki zube a wata kula tana nan rawaya ki zubawa a ciki ki kaiwa mai gadi”
“To”
Ta mike tsaye ta nufi kitchen din ba dan ta jidadin yadda Momy tace a bawa mai gadi ba, domin ba dan shi ta zuba ba, sai dai babu yadda ta iya dole ta bi umarninta, juye abincin tai a kular da momy ta fada mata ta dauka ta fito da shi.
“Ki bar kofar a bude ba sai kin rufe ba”
“Tau”
Ta amsa sannan ta nufi kofar ta wangale ta fita, kamar wacce bata son tafiya ko take bakincikin a bashi abincin haka ta isa inda yake ta gaishe sannan ta aje masa abincin.
“Momy tace na kawo”
“Tau Allah yayi albarka”
“Ameen”
Ta juyo ta dawo falon cikin rashin dadin rai. A inda ta zauna dazun ta sake zama ta fara cin nama sai da ta cinye tsokokin sannan ta fara cin kwan, shi kam kadan ta ci ta ji ya isheta ba dan bata son kwai ba sai dan cikar da cikinta yai, sakamakon abincin data ci dazun.
Tana zaune a gidan har dare, sai duk ta ji ta takura, sai ta ji tafi sakewa a masarautar duk kuwa da kasancewar a nan Momy tafi sake mata fuska da komai ba, amman acan tana wuni da su Labib suna rage mata kewa, kuma a can tana fita ta zagaya har garden din tana wasa da su, a nan kam wuni tai kallo, duk yadda take da son kallo sai ta ji a gudireta.
Ta inda abun ya zo mata da sauki ana kiran magariba sai ga mai daukarta ya iso ya aiko mai gadin kiranta.
“To gata nan zuwa”
Momy ta amsa masa sannan ta kalli Falmata tace.
“Tau sai ki je yana kiranki, kin koshi dai ko? Na ga ma baki ci tuwon da yawa ba, ko baki son miyar shuwaka ne?”
“Aa ina so, na ci ai ya ishe ni”
“To Allah ya tsare hanya”
“Ameen na gode sai da safe”
Ta fada sannan ta nufi kofa tana gyara Hijabinta, duk abunda ya faru a masarauta Momy bata da labari hakan yasa Falmata bata san komai ba. Bata tare da tsoro ko fargabar komai ba ta shiga gidansu bakinta kumshe da sallama, daga Naja har Tumba aka rasa mai amsa mata, Tumba ta ranka uban tagumi tana kallon kofar kamar mai jiran shigowarta.
“Makira... Macijiyar soshiya...yar bakinciki, ke wannna da dake nai kishi dana shiga uku.. Da yanzu ina can gidanmu ina zawarci”
Gaban Falmata ya fadi jin irin kalaman da Tumba take jifarta da su, sai ta tsaya cak tana kallon Tumba da fitilar touch light take haskawa. Sai ta rasa dalilin wannan kirari da Tumba tai mata, domin bata san ta aikata wani laifi ba kamin ta fita, sai dai inda sabo ya kamata ace ta saba da abun da ake mata a gidan, domin ko bata da laifi ana kakaro shi a dora mata.
“Daga gidan uban wa kika?”
“Daga gurin aiki”
“Gurin aikin ubanki, makira annamimiya, barauniya”
Jikinta ya fara bari zuciyarta ta shuga bugawa da mugun karfi.
“Gurin wasu mazan kike zuwa kenan?”
“Aa Wallahi daga gurin aiki nake”
Ta fada da muryar dake nuna kuka na kusanto, Tumba ta dauki butar dake kusa da ita ta jefa mata iya karfinta tana jin kamar ta saka wuta ta kone ta, Falmata ta kauce da sauri tana kuka.
“Shegiya mai bakin hali, yar gadon mugun abu, ke dai ba burinki ki saka a bakinciki ba? To Wallahi sai dai ki ganshi a dakin tsohon nan da zaki aura, barauniya kawai ashe an koreki gurin aiki shine kika ki fada kina yawon bin maza? To bari ubanki ya dawo, sai na fada masa komai kuma Wallahi na ba zan iya zama da ke ba, kara ya aurar da ke kawai na huta da bakinciki, da kuma zubar da mutuncin da kike mana, ba zan iya jira nan da wata hudu ba, ai bakincikinki kasheni zai yi ya zo a canja shawara, kara ya aurar da ke kar ki dauko mana cikin shege, ina jiran wata yai a bani kudi sai kawai na ji wani bakin labari, da yake kin yi gadon makirci sai kika kama zancen kika rufe, kika samu lasisin bin maza ko?”
Falmata ta fashe da wani irin kuka jikin ta sai bari yake tsakanin kalaman da Tumba take jefarta da su, da kuma irin duka da Baba zai mata idan ya dawo da zancen auren da tai a yanzu sai ta rasa wanne yafi tayar mata da hankali.
“Umma dan Allah dan Annabi ki yi hakuri, Wallahi ba sata nai ba, kuma kudinki idan wata yai za a baki na rantse da Allah”
“Uban waye zai bani kudin? Ni zaki maida shashasha, uwarki ma a tafin hannuna take balle ke da aka haifo a gaban idona”
Ajewar Tumba sai tai daidai da shigowar Baba dake rike da fitila kasancewar unguwar ba wuta sai dan buhunsa daya saba zuwa da shi kasuwa, Falmata na ganinshi ta tashi da sauri ta nufi gurin da ake wanke wanke tana kuka, Tumba ma ta saka nata kukan na munafurcin, daman tun da ta samu labarin take jin kamar tai kukan sanin cewar albashin ba zai samu ba.
ZAINAB POV.
Baya baya take tana kallon Wasim kamin ta juya da gudu ta shiga kofar falon, shi kuma ya cigaba da takowa yana nufo inda take ko kula Mai Gadin be yi ba dake masa magana yana fadin.
“Malam dakata a nan mana, lafiya dai?”
Shi kanshi mai gadi ya tsorata ganin matar gidan ma ta tsorata balle shi da yake tsoho, kuma be san abun da ya hada su ba, hakan yasa be yi gangancin taba shi ba, sai dai ya dage yana ta masa magana Wasim kam ko kallon inda yake be yi ba.
“A ina muke Wasim? Miyasa ake cewa ka dakata?”
Fadime ta tambaya tana lalabensa da dayan hannunta, jin kamar suna a wani gurin sabanin inda ya fada mata zai kaita. Ita dai tasan yace zai kaita gurinsu Inna sai kuma ya fito da ita harabar asibitin ya fita gate da ita suka hau napep yana fada mata wai Inna sun tafi wata asibiti, by pass ta ji yacewa mai napep din bayan an sauke su, mai Napep din ya wuce sai kuma ta ji ya rike ta kamar suna tafiya a iska, kamin ta ji sun sauka ya kwankwasa gate din da suka shigo yanzu, ga kuma hayaniya ta biyo baya gashi sai tafiya suke.
“A Ina muke Wasim?”
Ta fisge hannunta daga rikon da yai mata ta tsaya cak kamar tana ganinsa. Matsawa yai kusa da ita ya soma mata magana a hankali kamar mai rada.
“Wani guri inda zaki zauna kamin ki samu lafiya”
“Ban gane ba”
“Ciwonki bana asibiti ba ne, idan likitoci suka taba miki ido zai lalace ne kawai, kin samu makanta ne saboda na fitar da ke ba tare da izinin Babana ba, ba zai yiyu na maida ke garin ba, ba kuma zan iya barinki a gurin iyayenki a saboda kar su ja miki wani ciwon”
Nana da sai kuka da hawaye kamar ba ita ba.
“To a ina ka kawo ni?”
“Wani guri”
Ya fada sannan ya rika wuyan hannunta ya janyo yana forcing dinta tana takawa ba dan ranta na so ba, sai kuka take tana nadamar abun da ta aikata. Kamin ya karasa Iya ta fito rike da wuka, tana tambayar lafiya ganin Zainab ta shiga falon da gudu ta boya a dakinta. Iya na ganin Wasim ta saki wukar hannunta fadi kasa, ta hade yawu da karfi cikinta yai wani irin hargagi da haniniya kamar fitinannen doki.
“Wasim...”
Iya ta furta tana ja da baya, nunfashinta har wani gargada yake.
“Wasim...”
Ta sake furtawa tana shiga falon da baya baya, Wasim kuma be fasa doso inda take ba, har ya shiga cikin falon ita kuma ta tsaya daga can karshen falon tana kallon.
“Ga ajiya na kawo miki”
Ya furta yana zaunar da Fadime kan kujera, jin muryarsa yasa Zainab ta bude kofar ta leko.
“Idan kin ga dama ki cinye, idan kin ga dama ki aje ta har sai na zo dauka, ki zo ta fiye da yadda kike so”
Fadimen na jin haka ta zabura ta mike tsaye.
“Ta cinye kuma na boni mayya ce kenan? Ni dai na boni na lalace, dan Allah ka maida ni gida dan Allah innalillahi wa'inna ilaihirraji'un Allah ka kawo min dauki wayyo Inna, wayyo Bappa kuna ina?”
Ta fara lalaben hanya tana ta kuka, sai ya rike ta ya motsa da ita kusa da shi.
“Ba zan yi komai dan na cutar da ke ba, ban bar maihaifina ya taba ki ba, ba zan bar kowa ya tabaki ba”
“Ka kawo ni gurin Mayyan mayya fa mayya kace wai ba za a taba ni ba, nama har gida”
Ta fada cikin kuka, tana kara rike shi da dukan karfinta. Fitowa Zainab tai gana daya a take da manta tsoron zuwan Wasim da kuma mamakin yadda aka ya gane inda take, a da tana tunanin gurinta ya zo, sai dai kalaman da suke fita daga bakinsa yasa ta shiga rudani, Iya kawai take kallon.
“Hakan na nufi akwai wata alaka a tsakaninku kenan? Kuma hakan yana nufin kun san juna, akwai abun da kike boye min, kuma akwai abun da kike aikatawa Iya...”
Iya ta kasa cewa komai idonta ya kade yayi ja sosai, gaba daya hankinta ya gama tashi ganin Wasim, ganin take kamar ba gaske ba ne, komai ya zo mata kamar a mafarki.
Fadime kam ta kama Wasim ta rike gam ko motsin kirki ba shi da damar yi.
“Dan Allah karka bar ni nan, ba zan iya zama gurin mayya ba, wacece ita?”
“Ita din uwata ce, ki sake jikin dole a nan zaki zauna”
Ya kai bakinsa saitin kunnenta yana kallon Iya.
“Aa ni ba zan zauna ba, Wayyo Allah na, na boni na kusa mutuwa dan Allah karka bar ni nan”
Cewar Fadime tana kara fashewa da kuka, Zainab ma hawaye take tana kallon Wasim kamin ta kalli mahaifiyarta, dake kara shigewa jikin ginin falon tana jin kamar ta bace bat.
_________
Ina mata matan kwalisa Matan da suka ansa sunansu na Mata? Ina wadanda ke cewa mun yi mun yi bamu ga amfaninshiba? Hmmm to ku zo ga Yar gidan Maifata ta zo maku da Al ajabu, dan tsugunno, gumba da tsimi da Zuma daban daban, maganin sanyi na maza da Mata. Ga kuma garurruka irinsu mallakau sabuzu kuwa, sa bahaushe saibi, Dan hubbare kafi malam aiki, ke kadai ke da miji, dahuwar kaza, tattabara, ciccibi da dai sauransu. Ba anan kayanmu suka tsaya ba, muna hadin amare na musamman turaren sutura turaren tsugunno turaren wanka da na daki da na jiki duka 4amare nasu na musamman ne, amma ga tsuhuwar da ke son komawa yarinya itama zata iya zuwa ahadata kai abundai sai wanda ya gani, dan haka karkubari abaku labari, domin neman karin bayani zaku iua nemana ta wannan number 09029891757 ko 08169311410, muna aikawa ko'ina a fadin kasar nan har waje kasar nan muna aika kaya.
Address: Nasarawa Samaru Area gurin masallacin mai sola Gusau Zamfara state Nigeria.
03/12/2021, 18:54 - 🤐🤐🤐🤐: *Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 300 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith bank, then send the evidence via 08036126660*
Yana zaune garden din har la'asar, sai da ya ji kiran sallah sannan ya mike tsaye ya fito daga garden din, a fanfan masallaci yai alwala kamar sauran mutane sannan ya shiga cikin masallacin ya daidaita sahu tare da sauran talakawan gidan.
Bayan sun sauke nauyin sallah la'asar ya addu'a sannan ya fito ya nufi bangaren Mai Martaba. Yau ma kamar ko yaushe yana zaune falo, sai dai wannan karon yana tare da Waziri ne da alama suna tattauna wata maganar ne. Da sallama Shattima ya shigo ya zauna a kasa yayinda iyayensa suke zaune akan kujera.
Sai da ya fara gaida Baba Waziri sannan ya mikawa Mai Martaba tashi gaisuwar.
“Omar ya hakuri?”
“Alhamdulillah Mai Martaba”
“Ayi ta hakuri, rayuwa tana zuwa haka daman, abubuwa biyu sun zo maka a lokaci daya, rashin dan'uwa da kuma yaya, amman idan kai hakuri sai ka ga komai ya wuce”
“Inshallah na gode Allah kara girma”
“Ameen”
Waziri ya amsa sannan yana murmushi, Shattima ya mike tsaye tare da yi musu sallama sannan ya fice. Sai ya fito ya saka hannunsa aljihu ya ji babu keys din motarsa sai a lokacin ya tuna da ya bar su a dakin Ammy. Ba dan yana son zuwa ba babu abun da zai maida shi part din daukar keys saboda mutanen dake shiga shi kuma ba mutum ne mai son hayaniya ba, da kallo. Gashi kuma bayan son kowa ya tuka shi da sai ya kira Baba Adamu, hakan nan ya daure ya koma bangaren Ammy din. Be kalli kowa a falon balle ya lura da mutanen da suke ciki duk kuwa da irin gaisuwar da ake mika masa, sai da yai knocking sannan ya tura kofar a hankali ya shiga. Wata kawar Ammy ya samu a dakin tare da Ammy suna gaisawa.
“Shattima ya aka ji da hakuri?”
Cewar Matar sai ya amsa mata a takaice.
“Alhamdulillah”
“Allah ya masu ceto ne”
“Amin na gode”
Har ya dauki keys din zai juya Ammy ta kira shi.
“Shattima”
Sai ya juyo ba tare daya amsa ba.
“Yarinyar da kace a kira tana falo”
“Okay”
Ya juya ya fita, har ya iso tsakiyar falon be daga ido ya kalli kowa ba.
“Jekadiya yarinyar ta same ni waje”
Ya fada ba dan yana da tabbacin Jekadiya tana wajen ba, sai dan ya san ko bata nan dole a nemota a fada mata sakonsa, sai kuwa aka yi sa'a tana gurin ta amsa da to tare da yi ma Falmata a lama data mike tsaye, Falmata ta mike tsaye daker tana dingishi ta bi bayan Jekadiya suka fita daga bangaren, daker da wahala ta sauko stairs din saboda kafarta da bata ko son motsawa, haka ma da zata hawa sai da tai ta wai wai sannan ta samu ta haye har ta shiga cikin falon ita da Inna wuro.
Iyakar inda zata iya hange sai da ta duba ita da jekadiya amman ba su ganshi ba, gasu tsaye a rana suna ta duban inda yake ba su gashi ba, shi kuma isa ta hana shi yi musu wata alama da za su ganshi, ya hakimce cikin motar sai kallonsu yake, Jekadiya bata sa ran yana gurin motarsa ba, idan ma yana can wace daga ciki? Can dai wata zuciyar ta raya mata taje ta duba ko yana gurin ko kuma Garden duk da ta san be cika zuwa gardn din gidan ba.
“Zo mu duba nan”
Ta nufi gurin Motacinsa da suke fake a dabam da sauran motocin gidan, ta hanyar kukan motar da ta ji a kunne ne ta gane cewar yana cikin bakar motar, sai ta ja ta tsaya ita da Falmata har sai da yaga dama ya sauke gilashin motar. Da hannu yai mata alama da ta tafi sai ta juya ta koma inda ta fito, Falmata kuma ta sirina a gaban ganbun motar idonta a kasa, gabanta sai faduwa yake domin bata san dalilin kiran ba.
“Me ya samu kafarki?”
Ya fada yana kallon saman kanta daga inda yake zaune cikin motar. A tunaninta be kamata ta fadawa kowa cewar mahaifinta ne ya daketa ba, ba kuma zai mata kyakkyawar fahimta ba.
“Faduwa na yi”
Yana son ya ce garin yaya ta fadi har ta samu rauni haka, sai dai yana jin nauyin bakinsa da ganin zai shiga safgar da ba tashi ba. Dauke idonsa yai ya maida kan wayarsa yana latsa kamar ba mutum ya bari a gurin ba.
“Fada min gaskiyar abun da ya faru”
Ya furta bayan ya dauki tsawon lokaci yana chatin da Ra'ees a wayar. Ko be fito fili ya furta abun da yake nufin ya faru ba, ta san satar da ake magana yake nufi.
“Ban dauka ba, ban tana sata ba, ta shirya min abun ne ta yadda ba zan iya fitar da kaina ba, ita ta kirani tace na zo na gyara kayan Hajiya, kamin na gama ta ba ni yan kunnen yara tace na kulle a dankwalina, bayan na gama ta bani wannan sarkar tace kar na nunawa kowa na boye a hijbina.....”
Har ta