Showing 102001 words to 105000 words out of 273152 words

Chapter 35 - FULANI BOOK COMPLETE DOCUMENT by Khadijah Candy .txt

29 Aug 2024

72717

ni wa na sani a can, ita tace zata je tare da police ko?”


“Eh akwai wadanda za su min jagora zuwa can, a nan zan dauki hotuna ne kawai”


Fadime ta mike tsaye da sauri ta nufi gurin garken shanunsu.


“To zo ki fara”


Zainab ta mike tsaye ta nufi kofar fita, sai da ta fice sannan Inna ta kira Fadime tana mata gargadi.


“Ke wa kika sani a garin Garuk? Kin san yadda ake fadin garin nan ko? Fadime ki kama kanki ban son janye-janye”


“Ba ni zan kaita ba, ni ma fa tsoron garin nake, ai ban je ba”


“Na dai fada miki”


“Tau”


Ta amsa da baki, zuciyarta kuma cike da son zuwa daman tana neman dalilin zuwa garin. Shigowar Zainab yasa Inna ta mike tsaye ta koma bukkarta, Fadime kuma ta tsaya jikin shannun har sai da Zainab ta gama gyara camera ta soma daukar hoto da ma gidan gaba daya. Suna fitowa waje abun ka da mutane kauye sai aka musu taro ana ta kallonsu, tun daga kan gidaje har gonaki sai da Zainab ta dauka, ba laifi garin ya burgeta ita kanta ba zata iya shaidar when last taga inda ake gidajen zana kamar a nan ba. Sai da ta gama sannan ta janyo Fadime gefe tana tambayarta.


“Yanzu ya za'ayi muje garin?”


“Bari naje ma fara dubawa idan yana nan”


“Okay karki dade”


Da sauri Fadime ta sace kafa a cikin taron mutane ta zagaya zuwa inda zata ga Wasim, sai da taje ta duba ta dan jira na lokaci bata ganshi ba, ta dawo ta sanar mata, ko kadan Zainab bata jidadin hakan ba domin ta kwallafawa ranta zuwa garin, domin hotunan can da za su dauka zai fi daukar hankali fiye da na garinsu Fadime, ita kanta a yadda aka bata labarin mutane tana tsoron zuwa garin, ba dan tana neman suna da kuma daukaka ba babu abun da zai sakata tai wannan kasadar.
A garin da wuni har yamma after every one hour sai Fadime taje ta duba ko zata ga Wasim amman shiru, duk yadda Inna ta so Zainab ta ci abincinta bata ci ba, ita wai kyankyami take, sai police din aka bawa ita kuma aka siyo mata biscuits da lemun roba ta sha. Sai da yamma lis Fadime ta koma dajin tun kan ta karasa ta ji busarsa saita dawo da gudunta ta sanarwa Zainab.


“Ya zo, na ji busarsa”


“Da gaske?”


Zainab ta tambaya gabanta na dan faduwa domin har ga Allah tsoro take ji kawai karfin hali ne irin na ɗan maye.


“Amman yanzu zan fadawa Inna cewar zan rakaki rijiya mai gaba dubu ki dauki hoto, sai ki sa police din nan su kori yaran nan kar su bi mu”


“Okay”


Ta amsa mata tana gyada kai, domin da kamar rada suke maganar dan kar Inna ta ji. Sai Fadime ta kalli Inna dake wanke-wanke tace.


“Inna wai zan rakata rijiya mai gaba dubu ta dauki hoto”


Inna ta yi ma Fadime wani wawan kallo ta shiga mata fada da yaren fulatanci.


“Fulani wai baki da hankali, taya zaki je rijiya mai gaba dubu da yamma haka? So kike ki kwaso wani abun kuma”


A maimakon Fulani ta maida mata da yaren sai tai da hausa saboda Zainab ta ji.


“Ai ba zuwa zan yi kusa da rijiyar ba, nuna mata kawai zan yi n dawo”


“Dan Allah ki taimaka min, shine kawai abun da ya rage min, sai n a koma in ya so gobe sai na dawo naje can garin Garuk din”


Zainab ta fada da siffar magiya. Sai Fadime ta zaro ido kamar gaske.


“Ahaa har da can zaki je? Ni tsoro nake ji”


“Ba da ke zanje ba, ba man zan biyo ta nan ba, yanzu dai muje ki rakani na dauki hoton”


Fadime ta kalli Inna da ta tsayar da wanke wanke da take tana kallonta.


“Inna na raka ta? Ba zan matsa kusa da rijiyar ba na miki alkawari”


Ba kasafai Fadime take requesting abu a gurin Inna ta kasa mata ba, ba dan komai ba sai dan tana son ta sosai da kuma ganin ita kadai ta rage mata a duniya.


“Karki dade”


“Tau”


Fadime ta amsa tana washe baki, Zainab ta mike tsaye da sauri suka fita. Ko da suka fito ma babu mutane a waje sai police din dake zaune karkashin wata bushiyar dogon yaro, kai tsaye Zainab ta nufi inda suke ta sanar musu inda zata je tare da Fadime sannan ta bi bayan Fadime dake tafiya. Hanyar da zata ta sadasu da rijiyar Fadime ta bi sai da su kai nisa sannan ta karya kwana ta dauki hanyar da zata sadata ta bakin dutsen. Suna tafe tana tunanin abun da Wasim ya fada mata dazun, daman abun ya tsaya mata a rai.


“Wai idan mutum yace maka i like you yana nufin so kenan?”


Ta tambayi Zainab tana kallonta, a maimakon Zainab ta amsa mata sai tai mata banza, ba dan bata ji ta ba sai dan tana ganin Fadime ba ajinta ba ce da zata tsaya tana magana da ita, ba dan ma tana neman abu a gurinta ba da ko kallo bata isheta ba. Banza da Zainab tai mata sai yasa ta ji ba dadi sai dai bata nuna ba bata kuma sake ce mata komai ba har suka nisa cikin dajin. Busar sarewar Wasim ne abun da ya fara sauka a kunnuwan Zainab, daman Fadime ta saba da jin busar b tun yau ba, ita kam a gurinta ba bakon abu ne ba, wani irin natsuwa da shauki ne suka ziyarci Zainab, busar sarewar irin busar nan ce mai shiga zuciya da jini ta kwantar da hankali mai saurarenta, irin busar dake dacewa da ko wane kalar yanayi, a take ta ji ta kagara tai arba da mai busar, a rayuwarta bata taba arba sa wani abu mai burgewa da daukar hankali kamar haka ba, indai haka al'adar mutanen garin take tabbas zata burge kowa.


“Wow.... ”


Ta furta jin yadda suke kara dorar inda busar ke fitowa, ita kuma tana jindadin busar na karuwa a kunnenta, babu tsoron komai take ta ratsawa cikin gonar masarar tana ta son arba da mai busar. Fadime na gaba Zainab na binta a baya har suka haura saman dutsen, zaune yake ya basu baya ya saka sarewarsa a gaba sai busa yake, Fadime ta taka har kusa da shi sai ya mike tsaye ya juyo yana murmushi.


Wani irin faduwa gaban Zainab yai kwarjininsa da haibarsa suka tsaya mata cak a zuciya, ta saba ganin maza babu riga a jikinsu, gaisa da namiji taba jikinsa ko zama kusa da shi duk ba bakon abu bane a gurinta, amman a yau tana jin ta wata iri ta dabam ganin Wasim da irin kirar da ba ko wane namiji ke samu ba, komai na fatarsa Jikinsa a jere yake, fatar jikinsa jata ba kamar ita b da take fara fol, ga jiknsa all his muscle ya fito gwanin sha'awa, wani abun daya kara masa kyau walkin dake daure a kugunsa ko ba komai ya dabbaka al'adarsa, ga kuma kyau fuska a dogon hanci da fararen idanuwa da suka kara masa kwarji da haiba.


“Wow....”


Wannan karon a ranta a furta tana ta kallonsa irin kallon nan na burgewa. Shi kam kallo daya yai mata ya dauke kansa ya maida hankalinsa gurin Fadime.


“Tun dazun nake ta zuwa ban ganka ba, wannan matar tana daukar hoto ne kuma tana zon zuwa garin ku na fada mata zaka kai ta”


A take murmushin dake fuskarsa ya gushe, ya saka hannunsa biyu ya dafa kafadar Fadime.


“ A garin mu ba a yarda da duk wani abu na cigaban zamani ba, kamar waya camara da sauransu, kuma ba kasafai ake karbar baki ba sai da wani dalili, idan nace zan kai ku zaki jefa ni a matsala”


Fadime ta turo baki ta bata fuska.


“Ni dai n riga na ce mata zaka kaita fa...”


Bakinsa ya cikawa iska ya busar ya maida dubansa gurin Zainab, matsowa tai kusa da shi ta mika masa hannunta ba tare da tunanin komai ba.


“Hi sunana Zainab...”


Kallon hannunta yai kamin ya kalli fuskarta, sannan ya mika mata nashi hannun yana kallon cikin idonta, wanda hakan be yi ma Fadime dadi ba sai ta ji wani iri zuciyarta ta sosu.


“Ke jinin Iya ce...”


Wani irin dauke numfashi Zainab tai tana kallon Wasim idonta kamar za su fito, tambayarta yake ko kuma fada mata yake? Tsoro ne ya kamata.


“Ka santa ne...?”


Ta tambaya murya na rawa, be bata amsa ba yanje hannunsa yana kallon Fadime data kara bata fuska saboda ya gaisa da Zainab, shi kuma a zatonsa saboda yace ba zai kai su ba ne.


“Shikenan...”


Sai kuma yai shuru yana nazari. Zainab kam mamaki ya kusa kasheta, wata kila ya sani ne saboda shi matsafi ne ai zai iya karantar komai a tare da ita, sai a lokacin ta kara gasgata abun da ake fada a game da mutanen garin.


“Zan kai ku amman ba yau ba, ko kuma na tafi da ita kawai ke ki zauna”


Ya fada yana kallon Fadime sai ta makkale kafada kamar wata yarinya.


“Aa ni ma ina son na ga garin ai”


Zainab ta dora da.


“Ni ma yau kawai na ke da dama, gobe zan koma garin mu”


“Ina ne garinku?”


Fadime ta tambaya sai Wasim ya amsa mata.


“Yola”


“Eh Yola...”


Zainab ta maimaita cikin tsananin mamaki.


“Ka san garin ne?”


Nan ma be ce mata komai ba ya rika fuskar Fadime dake ta mamaki ace tun daga kasar Yola ta zo nan dan kawai daukar hoto.


“Komai aka baki karki ci, ki min alkawari ko minene aka baki ba zaki ci ba?”


“Na yi”


Ta fada tana daga hannu.


“Ko da nama ne”


Ta bude baki tana yar dariya.


“Kai har da Nama?”


“Eh”


Ya amsa mata da fuskar dake nuna ba da wasa yake ba. Sai tai yar siririyar dariya ta kawar da kai.


“Tau”


“Ni fa...?”


Zainab ta tambaya ganin ita be ce mata komai ba.


“Ki ci”


Ya amsa mata ba tare da ya kalleta ba, yana cigaba da kallon Fadime ya ce


“Zan je na samo muku tufafin da za ku canja”


“Har sai mun canja tufafi? Ni gaskiya tsoro nake ji ko dai mu bar shi, Inna ma bata san zan je ba”


Fadime ta fada da iyakar gaskiyarta domin tsoron ya fara ratsata tunawa da gargadin da Inna tai mata. Zainab ta fisgota da karfi.


“Wallahi baki iya ba, sai da muka samu dama zaki ce a fasa...”


Bata karasa ba, Wasim ya daka mata tsawa yana nunata da yatsa.


“Karki sake...”


Shan jinin jikinta tai ta make a gurin kamar babu mutum domin b karamin razana tai ba.








FALMATA POV.


Babu wanda ya san abun da ya samu goshinta har sai da garin Allah ya waye, ganin Baba n tsaye yasa Tumba ta nuna damuwarta kamar gaske.


“Ke miya samu goshinki?”


Ta tambaya cikin daga murya da nuna tashin hankali kamar da gaske ta damu.


“A gidan da nake aiki ne na bugu da kofar ban lura ba”


Falmata ta amsa tana tana goshin nata daya kumbura yana mata ciwo.


“Ayyah sannu”


“Yauwa”


Ta amsa tana kallon Tumba domin ta san ba dan Allah take mata sannun ba. Sai da risina har kasa ta gaishe da mahaifinta sannan ta kalli Tumba tace.


“Zan wuce aikin”


“To Allah ya tsare”


A natse ta nufi kofar fita tana tafiya da sauri sauri, domin jin take kamar da ta isa ne Sirleem zai kaita gurin gyaran kunne, babu abun da take so a yanzu kamar jinta ya dawo daidai. Kusan tun da ta fara aikin bata taba jin tana son zuwa ba kamar yau, duk wani nisa da gajiya da take ji idan zata ji sai ta neme shi ta rasa a yau, ko da ta isa masarautar 7:39am. Kai tsaye ta nufi bangaren Ammy kamar yadda ta saba, tana kokarin shiga gate din ta ji an tabota, sai ta juyo da sauri, hadinar data taba ta ta nuna mata Jurry, daga inda Jurry take tsaye ta daga mata hannu alamar ta wuce, sai ta sanda kanta kasa ta shige gate din b tare da tunanin komai ba. Sai da ta isa kofar falon Ammy ya danna door bell din sannan zuciyarta ta raya mata cewar wata kila bangaren da matar take shi ne bangaren Sirleem.


A yau ma Jekafiya ce ta bude mata kofar, Falmata ta risina har kasa ta gaisheta sannan ta fada mata bukatarta.


“Dan Allah ina nemn izini misalin 3pm zan je asibiti”


“To za a sanarwar Ammy”


Jekadiya ta amsa mata da karfin sanin cewar bata ji sosai sai an yi da karfin. A natse Falmata ta mike tsaye ta nufi dakin yaran ta fara aikinta. Bayan ta gama aka kawo mata abun karyawa sai ta dauki tray ta fita waje can gurin Garden ta zauna ta ci abincin mai rai da lafiya, sannan ta dawo da kayan gurin data saba aje su ta dawo dakin yaran gurin rainonsu. Cikin kwana biyun nan sun fara sabawa da ita musamman Labib yadda yake far'a da zillo idan ya ganta sai ka rabtse da Allah daman can a hannunta ya bude ido, ita da su da gan game da an dace ne domin ita na tana son yara balle kuma wa'dannn da suka kwanata mata a rai, take wuni tare da su basa barin hannunta har sai sun yi bachi. Misalin biyu da yan mintuna wata hadima ta shigo dakin ta sanar mata cewar an mata izini fitar, a lokacin tana goye da Luma dake ta aikin kuka alamar bachi take son yi.


“Dan Allah kin san agogo ki duba min ko karfe nawa?”


“Eh biyu da minti arba'in da takwas”


Hadimar ta fada tana kallon agogon bangon dake dakin yaran.


“Na gode”


Falmata ta amsa ta, sannan ta dauko Labib da abun wasansa ta nufo falon Ammy da shi, Jekadiya na zaune falon tare da Iya, Iya na ganin Falmata ta yi wani abu da kai ta dauke fuska kamar ta ga kashi, gaban Jekadiya Falmata ta sauke Luma da Labib sannan tai mata sallama ta tashi, sai ta juya sannan iya ta iya dago kai ta kalli bayan Falmata domin a yanzu tsoron hada ido take da ita.


“Ni kam Jekadiya da ni ce, da n bawa Ammy shawara, Babban Mutum ya nemi matar aure ya huta da irin yaran nan yan kama guri zauna, ba a san halinsu ba”


Jekadiya ta yi murmushi.


“Ai ko matar aka kawo kin san ba su ke raino ba, dole mai raino za a dauka, kuma an kusa inshallah ni ma dazun Ammy take min albishir”


Iya ta gyara zama cike da son jin labari.


“An samo masa wata kenan...?”


“Eh inshallah”


“Allah yasa ma yar gida ace a huta, idan kuma ya kasa samun waje ba ga Hajiya Karama ba”


Jekadiya ta mata kallon mamaki jin furuncinta.


“Hmm ita ma wannan yar gida ce, tun da Mai girma Waziri ba bari ba ne”


“Eh haka ne, kam kai Mashallah Yar wajen Waziri ce kai mashallah”


Iya ta fada ba dan ranta ya mata dadi ba, zuciyata sai kokarin gano mata take wace yar Waziri a ciki.




**
Wajen gate din Falmata ta fito ta tsaya, tana ta raba ido, ta kusan minti ashirin a tsaye sannan ta hango Sirleem ya fito daga bangarensu cikin wata motar wacce ba ta jiya ba ash colar, tun daga nesa da gane shi ne domin ta dade da haddace fuskarsa sai da ya kawo kusa da ita sannan ya rufe gilashin motarsa ya mika hannunsa ya bude mata front seat sai ta zagaya ta shiga ya tashi motar suka nufi gate.


“Ina wuni”


Be amsa mata ba sai ya sakar mata murmushi yana cin apple.


“Bismillah”


Ya mika mata da dayan hannunsa dayan hannun kuma yana tuka mota da shi.


“Aa”


“Da dai kin ci ni da matsala”


Bata ce matsa komai ba, domin bata ji abun da ya fada ba, bisimillar da yai mata ma ta gane ne saboda ya miko mata.


“Zan kai ki na aje ne, saboda akwai aikin da zan yi idan kin gama sai Momy ta dawo da ke”


Ya rada mata.


“Tau”


“Fada min me kika yi har Babanki ya mareki haka?”


Ta yi shiru tana mursa yatsun hannunta.


“A lokacin da aka kore ni aikin a nan gidan ne, sai Umma ta ce ma Babana wai ta gan ni da wani mutum muna aikawa assha”


Ya kalleta yanayin yadda take maganar kadai ya isa ya sakar maka cewar tana daf da fashewa da kuka.


“Abun nan akwai ciwo sosai kazafi, bayan shi kuma aka hada miki da duka I'm sorry”


Bata ce masa komai ba, sai kokarin tare hawayenta take. Wannan karo daga muryarsa yai ta yadda zata ji.


“Shiyasa kika yi kokarin guduwa ko? Now i realize irin wuyar da kike sha a gidanku, amman kin san me?”


Ta girgiza kai.


“Idan kika yi hakuri wata rana zaki ga ribar hakuri, amman idan kika gudu zaki afka wata rayuwar ne da ba lallai ne ki dace hannun kwarai ba, kuma idan zaki yi aure ko kika haihu abun zai biki ya bi zuri'arki ne, ki bata future dinki ki koma dana sani”


Nan ma shiru tai bata ce komai ba, ido ya kura mata kamar ba tuki yake ba.


“Ya ma sunanki?”


“Falmata...”


“Kina da Kyau...”


Wani irin dadi ne ya lullubeta, an sha fada mata tana da kyau daga maza har mata yan'uwanta amman bata tab yarda da tana da kyau ba saia yau da Sirleem ya yabe ta, bata taba jindadi dan an fadi cewar tana da kyau a sai yau da Sirleem ya fada.


“Kina da Kyau”


Ya sake maimaitawa yana kallon pretty face nata.


“Da kin bi duniya zaki yi arzik ki samu duk abunda kike so, amman zaki rayu cikin kunci da nadama, just like Mansura, banbancinki da ita ke wahala ce tasa kika gudu ita kuma auren dole za ayi mata shiyasa ta gudu”


Ta dan dago kadan ta kalleshi cike da jin nauyinsa.


“Bata son shi ne?”


Ya tabe baki yana kallonta sai kuma ya kalli titi ya kwanto kamar saurayi da budurwa suna fira.


“Uhmm kusan haka, kin san su yarbawa idan akaiwa mace aure mostly su suke ciyardar mazansu, ita kuma tace ba zata iya wannan ba, hasalima bata son auren yarenta, daga haka ta gudu daga Ondo zuwa Lagos, sai ta fada hannun wani mawaki dan iska, shi ya koya mata iskancin har ya zame mata business, idan


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login