Showing 123001 words to 126000 words out of 273152 words

Chapter 42 - FULANI BOOK COMPLETE DOCUMENT by Khadijah Candy .txt

29 Aug 2024

72762

sannan ta ya sakarwa yaransa murmushi, sai wasa suke cikin walwala da kuzarinsu, cikin wata irin tafiyar kasaita ya taka ya isa gaban yayansa ya shafa kansu, da za a bude zuciyarsa a yanzu da babu abun da za a gani sai farincikin addu'ar da Falmata tai wa yayansa, da kuma irin walwalar daya tarar suna yi. Wayarsa ya ciro ya dauke su hoto sannan ya sake shafa kansu ya fice daga dakin, dakin Ammy ya shiga sai ya samu bata ciki, hakan yasa ya nufo dakin Nana domin yi mata sallama, sai ya same ta kwance saman gadonta ta dunkule kamar marar lafiya.


“Nana lafiya kike kuwa?”


“Lafiya Kalau, kaina ke ciwo”


Ta amsa masa ba tare da ta bude blanket din ba.


“Kin sha magani?”


“Eh”


“Wane iri?”


Ta yi shiru, sai ya kai hannunsa ya yaye zanen data rufa da shi, hakan yasa ta tashi zaune idonta a kumbure kana ganinta kasan ba tai bachi kirki ba.


“Fada min damuwarki, me ke damunki Nana?”


Ya tambaya hankalinsa a tashe, ta yi shiru sai hawaye take.


“Fada min mana, kina da wanda ya wuce ni ne? Kina da gata bayan ni? Tell”


Har ta bude baki ta fada masa sai kuma wata zuciyar ta hana shi, what if yai mata abun da Ammy tai mata jiya? What if ya juya mata baya ya bata da ita?


“Ba komai Yaya I'm fine”


“No you're not, fada min matsalarki pls”


“Ammy tana fushi da ni... ”


Sai kuma tai shiru, hakan yasa shi sauke ajiyar zuciya ya juyo da kyau ya kalleta yadda zata fuskance shi.


“Nana my dear ki daina damuwa da abun da Ammy take miki, kin san Ammy tana da saurin fushi da zafin zuciya a gurin kowa right? Shiyasa mutane ke tsoron fadanta, amman zata daina miki haka i promise you, kuma zan yi magana da ita, ki daina kuka okay”


Ta gyada kai tana hade yawun bakinta da karfi.


“9 zan wuce Katsina me kike son na siyo miki?”


“Perfume”


“Okay, amman ke ma ki daina yin duk wani abu da kika san Ammy bata so, ki daina bijirewa umarninta, kuma idan ta saka ki abu ki rika yi okay, kuma ban da wasa da karatu”


“Yes”


Ya mike tsaye yana sakar mata murmushi.


“Ki fito ki yi breakfast”


“Okay”


Ta bishi da kallo har sai da ya fice sannan ta rushe da sabon kuka, she has alot to say abun da ta ji Hajiya Babba ta fada da kuma damuwar da take ciki na jefa AA a cikin wani hali, sai dai bata da wannan damar yanzu, wa zata fadawa wa zai mata maganin damuwarta? Nobody right ta kara fashewa da kuka kamin ta kai hannunta ta karkashin filo ta dauko wayar AA ta kunna tana kallon hotonsa. Did he deserve that? Ita ta aikata laifin fa, wani sabon hawaye ya sauko mata a daidai lokacin da kiran Anti Rabi ya shigo wayarta, rike wayar tai tana kallon kiran har ya katse aka sake kira ya katse, sai a ana iko ta daga ta kara wayar a kunne.


“Hello AA”


Anti ta fada daga dayan bangaren, sai Nana tai shiru kamar bata ji har sai da ta sake magana.


“Ba shi ba ne”


“Wacece ke?”


“Nana ce Sardauna yana gurin yan sanda”


“Saboda me me yai? Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un na shiga uku...”


Kit Nana ta katse kiran kana ta kashe wayar gaba daya tana jin wani sabon kuka na taso mata. Saurin maida wayar tai kasan fillon ta sauko kasa ta saka talkaminta na bedroom ta fice daga dakin sanye da kayan bachi, kanta ba ko dakwali. Ta jidadin samun falon babu kowa hakan ya bata dama fita ta fadar Ammy ta sauka kasa ta nufi bangaren Hajiya. Tana kokarin hawa stairs din ta hango Hajiya na saukowa tare da Jarma, hakan yasa taja ta tsaya har sai da Hajiya ta sauko kasa.


“Daughter har kin tashi?”


“Eh Good morning”


“How was your night?”


Cewar Hajiya tana sakar mata murmushi, Nana ta juya ta gaishe da Jarma.


“Baba ina kwana?”


“Lafiya Kalau Mamana”


Ya kiranta da irin sunan da Mai Martaba yake kiranta da shi, sannan ya kalli Hajiya.


“To ni na wuce sai an jima”


“Tau a gaishe da gida”


Sai da ya wuce sannan Nana ta kalli Hajiya da fuskar tausayi kamin tace komai Hajiya ta tari numfashinta.


“Daughter yanzu Jarma yake fada min ya gano inda yaron nan yake, yana cid, amman wai sun ce ba za su bada shi ba sai sun gama bincike ki kwantar da hankalinki zai fito soon kin ji”


Nana ta masa cewa sai kasa tai da kai, bata son ta nunawa Hajiya cewar ta ji abun da take fada jiya saboda tana jin nauyin Hajiya sosai kuma tana sonta fiye da Ammy, gaba daya ma ta rasa gane miyasa Hajiya tai kalaman jiya. Juyawa tai ta fara tafiya zuwa part dinsu ba tare da tace wa Hajiya komai ba. Dakinta ta koma ta zauna bakin gadonta tana ta tunanin halin da AA zai kasance, kamar an tsikareta ta mike tsaye ta bude wardrobe dinta ta dauko after dress ta saka saman kayan bachinta ta dauki mask dinta ta saka ta saka hijabinta ta nufi kofa, sai da ta fara lekawa falon ta ga babu kowa sannan ta fito da saurinta ta fice ta kofar gaba, kasa ta sauko gaba daya kamin ta isa gurin da tasan direbobin gidan na zama har da hadawa da gudu dan kar Ammy ko wani ya ganta. Direban Ammy na hangota ta doso gurin ya taso ya nufota da sauri.


“Almu, fita zaka yi da ni akwai key a hannunka?”


“Eh”


“Mu tafi”


Tun kan su karasa kusa da motar ya danna key hannunsa motar ta fita lock, da sauri Nana ta bude baya ta shiga shi kuma ya shiga driver side ya kunna motar yai warming dinta, sannan yai reverse ya fita harabar, kamin su isa gate Nana har ta matsu, sai da suka hau titi unguwar sannan hankalinta ya soma kwantawa.


“Gimbiya ina zamu je?”


“Cid”


“Police station Gimbiya?”


“Eh”


Daga haka bata sake cewa komai ba har suka isa, daga waje ya faka motar sai ta bude ta fito.


“Ka jirani a nan na dawo”


“Tau”


Ta doshi cikin cid din duk kuwa da kasancewar bata taba zuwa ba, gabanta sai faduwa yake kar ta hadu da wanda ta sani ko ya santa. Kai tsaye ta nufin cikin gurin ta shiga, gamin yawan police da kuma mutanen da suke tsaye dan shigar da kara ko sasanci sai yasa ta ji wani iri, sai da ta dake sosai sannan ta isa gabansu.


“Dan Allah ina neman Sardauna”


“Sardauna Sardauna, yaushe aka kawo shi nan?”


“Jiya da dare”


“Daga ina?”


“X&L Hotel”


Police din ya dauko wani littafi dake saman gurin yana dubawa.


“Ahmad Aminu Sardauna ko?”


“Eh eh..”


Ta amsa ba dan tana da tabbacin hakan ne cikakaken sunansa ba. Sai police din ya dauko keys ya mikawa na kasa da shi.


“Fito da Sardauna”


Police din ya karbi key din ya nufi cell din dake ta warin fitsari. Nana na tsaye aka fito da AA sanye da farar vest sai dan guntun wando, fuskarsa ta kumbure idonsa daya ma ya rufe baya iya gani da shi, kafarsa ta dama ma tsikarata yake yana takawa daker, kana ganinsa kasan ba karamar wahala ya sha ba. Wani sabon hawaye ne ya cika idon Nana tana ta kallonsa har ya karaso inda take tsaye. Yana ganinta ya gane ta, ga mamakinta sai ya sakar mata murmushin karfin hali da fuskarsa da ta kara bayyana ramarsa daman can ba wata ki bar kirki ce a jikinsa ba. Sai Nana ta rasa kalmomin da zata hada tai masa magana, har sai da ya fara mata.


“Nana...”


“Na'am dan Allah kai hakuri, laifi na ne”


“No haka Allah ya rubuto, don't say that da ace ke aka kama kara ni, daman ni dan talaka ne, na san zai taba mutumci na amman ba kamar ke ba, just ki yi wani abu a fitar da ni daga nn pls na san hankalin Antina yana can ya tashi”


“Ban san me zan yi ba, ba zan iya yin komai ba, Hajiya Babba ce kawai take taimaka min, ita kuma naji tana fadar ai tana son a juyar da case din zuwa kisan kai, Hajiya Karama kuma bata nan, Ammy kuma ba ta saurareni ba har marina tai jiya”


AA ya ziro mata kai jin ance ana son juyar da case din zuwa kisan kai.


“Kisan kai fa kika ce Nana? Miyasa me nai? Miyasa zata min haka? Baki fada mata gaskiya ba?”


“Na fada mata, ni ma ban san abun da yasa zatai haka ba, na ji tana fada a waya ban san da wa take wayar ba amman na ji, kuma na ji tana cewa har abun da ya fi sata sai na yi, kuma sai Ammy ta yi kuka da idonta, i don't know why Hajiya ta fadi haka”


“Waya haife ki tsakanin Ammy da Hajiya Babba?”


Ya tambaya duk kuwa da kasancewar be sansu a fuska ba sai a suna shi ma ta bakin Nana.


“Ammy amman Hajiya Babba ta fi so na, komai na ke so tana min kuma ita bata min fada bata kyamata kamar Ammy”


“So Hajiya Babba is your step mother right?”


“Yes kuma she is my mother in-law, saboda dan ta zan aura....”


Shiru yai yana kallonta, indai har haka ne miyasa zata ji dadin lalacewar Nana? Miyasa ba zata jidadin abun da yai ba sai ma ta nemi juyar da abun?


“Ammy tana miki fada akan zuwa makaranta right? While Hajiya Babba bata miki fada? Ammy tana miki fadan kashe kudi Hajiya Babba bata yi?”


Duk abun da ya fada sai ta daga masa kai.


“And tana so na sosai fiye da Ammy komai nake so tana min, har lallaba ni take na auri Sirleem danta”


“Kishiyar uwa bata taba son da fiye da uwar da ta haifi dan ba Nana, Hajiya Babba ba son ki take ba, wata kila tana miki komai ne saboda tana son rayuwarki ta lalace, kuma tana son ki auri danta ne saboda wata manufa, indai har tana son ki ba zata tai wannan furucin ba, kuma zata ji dadin abun da nai, ba wai ta juyar da abun ya zama babba ba”


Ya karasa hawaye na sauko masa, sam be dauka abun zai zama haka ba, be ji nadamar aikata abun da ya aikata ba sai yanzu, ya jefa kansa da yar'uwarsa a matsala bayan duk gargadin da tai masa.


“Amman zan fito da kai, zan yi wani abu, ban san miyasa na aikata ba, i regret this, duk laifina ne”


Nana ta fada tana kuka ganin hawaye na zuba a fuskarta AA. Hannu ya saka ya share hawayensa yana kallonta, duk sai ya ji tausayinta ya rufe shi, for what he understand Nana tana da damuwa amman a a saurarenta, tana son gata da rayuwar morewa amman ba a tsara mata rayuwar yadda zata jidadinta ba, sannan hankalinta da natsuwarta bata cika kamar na sauran yan mata sa'aninta ba, ga kuma abun da ta aikata jiya, da ace ba tare yake da ita ba da ta kunyata fiye da kima, and if he can remember ta fada masa bata san abunda ya saka yayi ba hannunta kawai yake kaikayi, ga kuma rashin son zuwa makaranta da take wanda shine silar haduwarsu, wanda be san dalilinta na kin makaranta ba.


“Nana”


Ta kalleshi da idonta da suka gama ja tun kukan data sha jiya.


“Promise me something”


“What it's?”


Ta tambaya daker saboda kukan da take mutane dake gurin sai kallonta suke.


“Matso da kunnenki”


Ta matsar da kunnenta kusa da shi.


“Ki min alkawari ba zaki sake fashin zuwa makaranta ba, kuma ki min alkawarin ba zaki sake daukar abun wani ba, ko da kuwa na Ammy ne ko na Hajiya, kuma ki min alkawari ba zaki sake zuwa bangaren Hajiya ba, komai ta baki ba zaki karba ba, and no matter how hannunki yake miki kaikaiyi karki dauki abun wani, ki bar wajen, kuma zaki yi ma Ammy biyayya a matsayinta na mahaifiyarki, ki cire cewar Hajiya tana son ki a zuciyarki ki aje gefe”


“Amman bana son makaranta”


“Ba zaki iya min wannan ba? Ba zaki iya daukar min alkawari ba? Ni da nai miki wannan abun kuma na shiga wannan halin saboda ke? Kuma kin ji sun ce case din zai juya zuwa kisan kai ne? Ba zaki iya zama yarinyar kirki saboda ni ba?”


“Na dauka na maka alkawari, zan yi duk abun da ka ce, kuma ba zan bari su juyar da abun ba, na san yadda zan yi, i will talk to Sirleem”


“Who?”


“Her son my boyfriend”


“Dan ta ne, karki sake kula shi ki samu wata hanyar ba wannan ba, wata kila a da hadin kansa ake komai, karki sake kula shi okay”


Ta daga mishi kai.


“I will find another way, and i will fulfill your promises”


“Thank Youu”


“Zan tafi”


“Karki karya min alkawari”


Ta gyada kai tana kura masa ido kamin ta juya ta fara tafiya tana ta sake-saken hanyar da zata fi ta fitar da AA daga wannan halin. Cikin motar ta koma ta shiga direban ya kama hanyar gida.


“Bangaren Hajiya zaka sauke ni”


Ta fada ganin sun doshi masarautar gadan-gadan.






FALMATA POV.


Shigowar Shattima dakin yasa ta fita daga falon Ammy gaba daya, sai da ta sauko kasa da zimmar zuwa garden sai ta tuna cewar Jurry tace ta zo ta yi ma Hajiya gyara. Da sauri ta juya sai kuma ta aikawa kanta wata tambayar, anya idan ta fita bata fadawa Ammy ba ba zata yi laifi ba? Hakan yasa ta koma cikin falon sai dai bata tararda da kowa ba, har ta zauna sai kuma ta ji tsoron kar ita kuma wacan ta ce bata zo ba, hakan yasa ta mike tsaye ta fice daga bangaren gaba daya. Da dan tsoro ta shiga bangaren Hajiya domin bata taba zuwa gurin ba sai yau, shi ma tsarinsa kamar na Ammy ne, banbancin na Ammy daga dama ne na Hajiya kuma daga hagu. Tana daga kai sama ta kalli stairs din ta hango Jurry tsaye rike da waya tana kallonta, Falmata ta kara cira kafa cira kafa ta hau saman ta risina gaban Jurry.


“Ranki ya dade ga ni”


“Okay biyo ni”


Ta fada tana mata alama da ta biyo ta din domin ta san ba lallai ne ta ji ba a yanayin da tai maganar. Falmata ta mike tsaye ta bi bayanta har suka shiga ciki, wannan bangaren ma ya hadu ya ji kayan alatu da abubuwan more rayuwa na zamani, tsarinsa da fentin da kofar irin na Ammy ne furnitures ne kawai banbanci. Tun da Falmata ta shigo falon kanta a kasa yake, hakan nan ta samu kanta da rashin sakewa kamar yadda ta saba a bangaren Ammy duk da a can din ma ba wani sakewa take sosai ba, bata kalli ko'in ba bayan gabanta hakan yasa bata kula da su waye a cikin falon ba, ciki kuwa har da Sirleem dake zaune can karshen falon gurin wasu set din cushion, ya baje documents da system a gabansa da alama wasu abubuwan yake dubawa, sai dai shi ya lura da ita idonsa na kanta har ta shige corridor da zai sadata da dakin Hajiya. Ita dai tana biye da Jurry har suka shiga dakin Hajiya. Tana shiga sau ta ji wani iri domin bata taba shiga bedroom din Ammy ba balle kuma Hajiya da take kamar bakuwa a gurinta. Daga jikin kofar ta tsaya ta risina kasa tana gaishe da Hajiya.


“Zo ga tufafi can ki jera min su a wardrobe can”


Hajiya ta fada ba tare da ta amsa gaisuwar da Falmata tai mata ba sannan ta mike tsaye ta fice daga dakin. Tana fitowa ta hadu da Nana ta doso dakin da alama shigowa za tai, da sauri Hajiya ta tare ta.


“Daughter zo muje wannan room din gyara ake min acan”


Nana bata ce komai ba ta bi bayanta suka second bedroom dinta, ta zauna saman kujera tana kallon Nana fuskarta da murmushi, Nana ta zauna kusa da ita tare da cire mask din fuskarta.


“Hajiya ba ki yi komai ba?”


“No na yi mana, i try my best, police din ne suka ce sai sun gama bincike”


Nana ta kalleta, a yau duk wata kima da kunya da nauyin Hajiya da take ji saita neme su ta rasa, abun da AA ya fada mata sai yawo yake mata a kwakwalwa, and yes he's right indai har Hajiya tana son ta zata yi murna da abun da yai ba wai ta juyar da case din ba, wanda har yanzu Nana bata san dalilinta na yin haka.


“Hajiya na ji kina waya jiya, ban san da wa kike waya ba, amman na ji abun da kika fada, kina son a juyar da case din Sardauna zuwa kisan kai, kuma kin ce zan yi abun da ya fi sata, kuma kin ce sai Ammy ta yi kuka”


Hajiya ta dafa Nana da sauri.


“Ke Nana ke ce kike fadin haka? Yaushe na fadi haka? Ni din? Ni Balkisu? Ko dai Ammy ce ta kitsa miki wannan abun?”


“Babu wnda ya kitsa min, kuma Wallahi idan aki fito da Sardauna ba, sai na fadawa Mai Martaba wannan maganar, kuma Wallahi ba zan auri Sirleem ba”


Nana ta fada kai tsaye tana hawaye, gaba daya Hajiya jin tai kamar babu duwawu a jikinta sai ta ji kamar tana kan ƙaya har sai da ta gyara zama sannan ta samu damar hade yawun daya cika mata baki.


“Nana ni Hajiya Bilki kike fadawa wannan maganar? Ni zaki shiryawa karya? Kin bata wayonki”


“Mai Martaba da kowa na gidan nan ya san ba zan miki karya ba, Wallahi Hajiya idan Sardauna be fito ba sai na fadawa Mai Martaba”


Ta karasa da kuka ta tashi da sauri ta fice daga dakin.


“Ni....”


Hajiya ta nuna kanta.


“Yaushe Nana ta lalace haka? Har ta iya labe? Ko dai wani ya ji?”


Ya mike tsaye wani irin gumi na keto mata ta ko'ina.








***
Falmata bata ji ba har sai da Jurry ta sake fada mata sannan ta tashi ta nufi gurin tulun tufafin da bata san ranar gama jerasu ba, saboda yawansu. Cikin natsuwa ta fara jera kayan da yawancinsu sabbi ne da ba a saka ba, sai kuma wandanda aka saka amman an goge su an shiryasu. Laces ta fara jerawa guri daya sannan ta shiga jera yadi,


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login