Showing 264001 words to 267000 words out of 273152 words
Chapter 89 - FULANI BOOK COMPLETE DOCUMENT by Khadijah Candy .txt
da tausayinta ya rufe shi.
“Sorry Baby I'm sorry, yanzu kin zama cikakkiyar mace”
Bata dai ce masa komai ba sai kuka take, tana ganin jini ta kara rudewa ta fashe da kuka tana girgiza tana mamakin rashin imani irin nasa, sai yanzu ta gane dalilin Inna ta dace duk wanda ya taba ta tai masa ihu ashe ta san zafi ake ji shiyasa take kokarin kareta.
“Yadda kike wankan haila haka zaki yi wannan, sai dai niya ta banbanta ki kulla niya a ranki cewar zaki yi wankan janaba okay Baby”
“Ba baby ba babalo bebalo”
Ta fashe da kuka tana jin wani irin haushinsa, sai ya kyalkyale da dariya kamar ba dare ba, ya sumbance ta.
“Wallahi ina sonki yarinyar nan”
Daker da sudin goshi tai wankan sannan ya nadota cikin tawul kamar wata baby ya zo ya sauke ta tsaye ya canja bedsheet din kana ya kwantar da ita ya lullubeta, shi kuma ya koma yai wankan ya fito ya kwanta bayanta ya rumgume abunsa yana jin sonta har kasan zuciyarsa.
Da asuba ma daker ya tashe ta tai sallah, sai kuka take masa tana fadin zafi zafi a dayan bangaren kuma zuciyarta ta cika da mugun tsoronsa, abubuwan da suka faru suka zo mata kamar a mafarki.
“Kuma ban ce ki fadawa kowa ba”
“Wannan abun ya fi karfin a fada wannan abun babba ne, dan Allah karka sake min dan Allah”
Wani irin kuka take mai ban tausayi tana rokonsa, sai ya kara jin tausayinta ya kama shi, ya jata jikinsa ya rumgume yana bata hakuri.
Bata wani ci abuncin da aka aiko musu ba, sai ruwan tea da ya hada mata kawai ta sha, haka ya zauna yana gasa mata jiki yana saka ta tana dan takawa gudun kar ta tona masa asiri, be bar gidan ba sai azahar shi ma dan mutane sun fara zuwa ne, duk wanda ya ganta zai san ta sha kuka domin fuskarta da idonta ya nuna, sai dai bata labartawa kowa komai ba, daman ba sanin mutanen tai ba duk yan'uwan Shattima ne.
Kamar jiya yau ma da wuri ya dawo, tana jin motsinsa gabanta ya fadi sai ta fara hawaye, zuwa yai kusa da ita ya zauna yana share mata hawayen.
“Minene na kuka kuma?”
“Yau ma zaka yi?”
Ya girgiza mata kai alamar aa ba dan baya bukata ba sai dan yana tausayinta.
“Aa”
“Rantse”
“Ba zan rantse ba amman idan na ce aa ina nufin aa”
Ya kwantar da kanta jikinsa wasu hawayen na sauko mata. Bata yarda da gaske yake ba har sai da ta ga sun kwanta salun alun be mata komai ba har gari ya waye, sannan ta dan samu sallama har ta sake jiki ta ci abu mai dan nauyi da safe, tissue yaja ya goge mata bakinta yana gyara mata zaman a saman cinyarsa.
“Yar gidan Bappa, raguwa sai baki, kin iya kiran Bappa da Inna ko?”
Murmushi tai ta rufe fuskarta da kirjinsa tana jin kunyarsa. Sai ya shafa bayanta yana murmushin.
“I love you”
Ya rada mata yana kara rumgume ta, sai ranar ya samu wuni da ita tun safe har dare domin babu wanda ya ziyarce su a ranar, wunin ranar duk a jikinsa ta wuni, be ya yarda ta zama nesa da shi yana mata haka ne saboda ta saba. Da sannu kuma abun ya fara bin jikinta within a week ya kai idan zata zauna sai dai a saman jikinsa ko kusa da shi, haka a gurin bachi sai ya rumgumeta ya mata kira'a sannan take bachi, 3 days after ya sake taba ta a nan ma ta masa kuka sai dai ba irin na wacan karon ba domin ta ji zafin ya ragu sama da na farkon da ta ji kamar zai cire mata rai, haka ya rika binta after 3 days yake taba ta saboda ya samu ta sake da shi.
The first gift da ya fara mata a gidan shine ya siya mata waya da sabon line ya saka mata number Bappa da Inna da ita na take da waya a yanzu tana gaisawa da su, ya saka mata number Nana da Ammy da duk wani wanda yake ganin ya dace tai hula da shi, sannan yai mata downloading games kala kala da littafan musulunci yana koya mata abubuwan da bata sani ba, a dole yake cilasta yin azkar da safe har ya soma zame mata jiki idan tai ta gama sai ta kwanta a cinyarsa tana sauraren karatunsa.
Sai da tai month a gidan ko ruwan tea bata taba dafawa ba komai yi mata ake, hadimai ke zuwa suna wanke komai su gyara gidan a saka turare, abinci kuma kullum daga masarauta ake kawo musu, two da cika wata daya Shattima ya dauke ta suka tafi Masarautar ta gaishe da Ammy da Mai Martaba, Nasiha sosai Ammy tai mata haka ma Mai Martaba, a nan Ammy ta sanar da ita cewar daga gobe ba za a sake aika musu da abinci daga nasarautar ba.
“Ke zaki rika yi da kanki, na san zaki ji wuya amman ki daure a haka har ki saba, karki taba yarda mai aiki ko hadimai su zama su ne za su rika dafa abincin mijinki, kuma karki yarda Mijinki ya rika cin abinci a waje sai idan ta kama dole babu yadda zaki yi, kuma ladabi da biyayya rike su, ki rike aure da kyau domin Annabi yace macen da ta tsare farjinta ta bautawa ubangijinta kuma ta bi mijinta to wannan matar ta ma shiga aljanna, ai kina son aljanna ko?”
Ta daga kai tana jin nauyin Ammy sosai.
“Sannan ki rike kamshi, ki samu turare kaloli ki hade a guri daya ta yadda zai zama kamshi zai fito wani kala na dabam da ba kowa zai gane wani kalar turare kika saka ba, ki rika amfani da shi ya zama da shi mijinki zai gane ki, ko wane guri ya tafi idan ya ji kamshin turaren ke zaki fado masa a rai, turare yana da fa'ida sosai a gurin ma'aurata, ko da yaushe ki kasance a cikin tsafta da kamshi”
“To Ammy”
Ammy ta hada wasu turarunka ta bata tace tai amfanin da su, sai goma suka baro gidan a mota yake mata albishir din cewa jibi za su tafi su gaishe da su Bappa, tsabar murna bata san lokacin da ta rumgume shi ba.
Washe gari suka shiga katuwar super maket suka si ma Inna da Bappa siyayya kala kala, ita ya siya mata chocolate domin ta gaji da kazar da yake siyo mata kullum da dare bayan wanda ake kawowa a soye daga masarauta, a yanzu bata ma son jin warin nama duk ya fita ranta. Siyaya sukai mai yawa suka dawo da ita gida, hadiman da aka aje mata a gidan Shattima ya saka suka gyara komai suka saka a jaka, ita kuma ta shiga ciki tai wanka, ta fito ta shirya cikin wando da riga English wears, kayan su karbe ta sosai dan man leben da ta shafa ya kara mata kyau ta saka ma gashinta ribbom sai ta fito kamar wata balaraba.
“Woooo wow look at my girl”
Ta yi murmushi tana kallonsa ta cikin madubi har ya karaso kusa da ita ya rumgumeta ta baya yai kissing dinta.
“Kin yi kyau”
“Na gode”
Ta fada tana dariya.
“Two days din nan jikinki da dan zafi”
“Eh nima ina ji, amman bana jin zazzabin komai”
“Yeah canjin yanayi ne?”
“Saboda ana sanyi yanzu?”
“No saboda na yi ajiya a cikinki”
Ta dan wara ido domin bata fahimta ba.
“Ajiya kuma? Mayu fa suke haka?”
Yayi dariya ya sumbanci kumatunta tare da kai hannu ya shafa cikin.
“I mean you're I'm pregnant....”
Ta ji wani shock da sauri ta juyo ta kalleshi.
“Ba da gaske ba? Miyasa ban yi amai ba ban yi ciwo ba ban yi komai ba”
“Zaki yi soon, ai ko wane ciki da yadda yake zuwa”
“Ya kai ka sani?”
Ya kai goshinta kan nata yana goga mata hancinsa.
“Ni fa likita ne, ke ba ki ji canji a jikinki ba? Ba ki daina son wasu abubuwan da kike so ba? Tun da kika zo gidan nan kin yi period? Kuma ga girarki nan ta layin kasa yayi fari sosai ko dai haila ko ciki, ni kuma a san ciki ne hannunki da halshenkin ma sun nuna, kuma ke ai baki son cin abinci amman yanzu kina ci sosai”
Ya fada mata cikin rada sannan ya mikar da ita tsaye ya duka ya bude cikin yai sumbance a cikin.
“Idan kin gama ki sauko mu ci abinci”
Ya fada mata sautin kunnenta sannan ya murza yatsun hannunta ya fice yana mata murmushi, juyawa tai ta kalli madubin dake bayanta ta bude cikin tana kallo ta madubi.
“Kenan yanzu dandan yana ciki?”
Ta shafa cikin tana ta mamaki, sai kuma tai murmushi tana jin mugun dadi. Tana tsaye a gaban madubin tana kallon cikin har ya sake dawowa dakin, zuwa yai bayanta ya tsaya yana kallonta ta cikin madubin ya saka hannunsa yana zirya da shi a fuskarta.
“Matata ta kusa zama uwa”
Sai ra rufe ido tana dariya ta juyo ta saka kanta cikin kirjinsa.
“I can't wait...! To be a father again Allah yasa twins ne ko triple”
Ta dago ta kalleshi.
“Kai har uku? Akwai wuya ai”
“Ai sauki Allah yake sakawa bawayinsa”
Ya sumbance ta sannan ya kama hannunta suka fito, da kansa ya ja kujera ya zauna sannan ya zaunar da ita samansa ya shiga zuba abinci yana bata tana ci idan zata hade sai tai a hankali wai kar ta ji ma cikin ciwo.
Washe gari ta farka da wuri ta shiga kitchen tana kokarin kunna gas din da ya nuna mata yadda zata yi amfani da shi tun kwana uku da suka wuce, ta kunna lafiya lafiya gurin dora ruwan ya zama rigima wai tana jin tsoro saboda ya fada mata a wasa da gas zai iya illata mutum, tana haka ya shigo ya same ta sai ya karba ya dora ya sa ta fasa kwai ta kwada shi kuma ya hada komai ya karyarwa.
Da rana ma haka ya girka musu jalof yana nuna mata yadda zata yi, duk da ya san idan tai ba lallai ne yai dadi ba domin bata saba girki a gida ba sai dai yana da kyau ta fara koya tun a yanzu, da dare ma haka ya nuna mata yadda zata dafa indomie. Washe gari misalin 11 jirginsu ya daga zuwa Katsina, suna sauka Ra'ees ya iso ya dauke su, zuwa gidan Shattima dake cikin garin Katsina. A gidan suka huta sai yamma suka shiga Bandalo, zo ka ga kauna Inna kamar zata hade Fadime, sai mamakin yadda Fadime ta soma canjawa take cikin kankan lokaci, Fadime ma tana ta murna ganin an gyara gidansu kamar a birni. Bappa kam dukawa Shattima ne kawai be yi ba tsabar murna da farincikin ganinsu, duj yadda Fadime ta so ta kwana a gidan Shattima be barta wai saboda matsalar tsaro duk da kasancewar zuwan na su ma ba kowa ya san da shi ba. Da za su tafi ne yake shawartar Bappa cewar zai sama masa wani gidan a cikin garin Katsina ya koma domin a ganinsa zai fi samun tsaro a can fiye da nan.
Ba dan ya fada mata gobe zai kawo ta ta sake ganinsu ba da ba zata yarda ta be shi ba su kwana a Katsina ba, hakan kuma be hana ta yi masa kuka ba. Washe garin da za ta koma ta tashi da zazzabi mai tsanani, ko kanta bata iya dagawa sai da Shattima ya bata magani ta sha, bayan siyayyar da sukai musu ta Yola Shattima ya aika yaronsa aka siyo musu kayan abinci masu yawa ya aika direba tare da kayan aka kai musu sannan ya kara ya sanar musu ba zata samu zuwa ba saboda bata jindadi. Kwananta uku a Katsina tana jinya sai da ta fara samun sauki sannan Shattima ya saka ta mota da police aka kaita ta wuni ta kwana a can ta sake wuni ta kwana sannan tai musu bankwana tana ta kuka ta dawo Katsina, washe garin ranar suka bar Katsina zuwa Yola, kar ku so ganin yadda ta labe masa a jiki cikin girjin daman tana jin jikinta babu kwari tun rashin lafiyar da tai.
ZAINAB POV.
Yayi murmushi ya dauki karan dake gabansa ya saka a wuta.
“Miye alakar addini da soyayya?”
Kallonsa tai a zatonta idan ta fada masa haka zai janye kudinsa ne akanta, hakan yasa tun a lokacin da yai mata wacan maganar ta daina sakewa da shi.
“Yana da alaka mai karfi, a iya abun da na sani addinina be yarda mace ta auri mijin da bashi da addinin musulunci ba, amman an yarda miji ya auri mace ko bata irin addininsa”
“Kina fada min wannan ne da gaske ko kuma kina neman nisanta kanki da ni ne?”
“Ma zai saka mace ta nisanta kanta da kyakkyawan namiji irinka? Kana da kyau Wasim, kyau na halitta da na zuciya, duk da kasancewarka ba musulmi ba kana da tausayi kuma baka cutar da kowa, baka wasu halaye na banza, babu macen da za ka taya wa kaunarka ta ki karba, sai idan da wani dalilin kamar wanda na fada ko makamancinsa”
Yayi murmushi a yanzu ya gamsu Zainab tana sonsa kenan ba kamar yadda zuciyarsa take raya masa ba.
“Me zai hana mu aje addini a gafe?”
“Babu wannan damar a gareni domin rayuwata tana tafiya a tare da addnina ne, addinin musulunci addini ne mai sauki da kuma mai dadi, idan har na bar addinina to wuta ce zata zama makwancina ranar gobe kiyama”
“Ban gane ba”
“Ranar da za a tashe mu, ayi mana tambayoyi kan abun da muka aikata, kuma ayi mana hisabi daidai gwargwadon abun da muka aikata, daga nan wanda ya aikata zubuni za a yafe masa idan Allah ya ga dama, idan kuma tsakaninsa da bawa ne dan'uwansa kamar ni da kai, sai a cire wani abu daga aikinsa a biya wacan idan kuma ba shi da komai sai a ciro zunubin wacan a tafta masa, idan dan wuta ne zai dauwama a wutar idan kuma dan aljanna ne zai shiga aljanna bayan an gama kona shi, wanda yai aiki na gari kuma sai a saka shi aljanna daidai gwargwadon aikinsa gwargwadon matsayinsa a aljanna”
Wani kallon mamaki yai mata.
“Wai kina nufin bayan wannan rayuwar da muka yi zamu sake yin wata? Bayan mun mutu kenan”
“Sosai kuwa, za a sake wata rayuwar da za a bi hakkin wanda aka zalunta, kuma azabtar da wadanda sukai zaluncin, tabbas bayan wannan rayuwar akwai wata rayuwa, wata rayuwa mai ban tsoro mai tsananin firgitarwa, musamman ga mutanen da ba su bi Allah ba”
“Amman miyasa abubuwa bauta suke da yawa ne?”
“Abun bauta daya ne Allah Subhanahu wata'ala, shi ne dauwamammen kuma rayayye, shi kadai ya cancanci bauta kuma shi kadai za a bautawa a rabauta, shaidan ne yake raya ma mutane cewar akwai wasu abunuwa da suka cancanci bauta bayan ubangijina, ban taba burge ka idan ina sallah ko alwala ba?”
Ta tambaya tana kallonsa.
“Tun kamin ke akwai wanda nake ganin suna sallah da yawa, abun yana burge ni, amman ina ganin kamar akwai wahala ayin hakan”
“Babu wata wahala idan ka saba, kuma zaka samu natsuwa sosai a cikin ibadar”
Kadan ta labarta masa daga ibadar sannan ta jadda masa.
“Idan har kana son na kuma ka shirya zama da ni, dole na ka aje addininka ka bi nawa, bin addinina kuma yana nufin watsi da al'adunka ka zama mutum kamar ni, ka aje tsafinka da komai”
Yayi murmushi.
“Kina da tsada kenan?”
Sai ta kai hannunta ta taba fuskarsa.
“Sosai”
Yayi murmushi ya sake deban wasu karan ya saka a wuta, sai ta kwanta jikinta tana kallon wutar.
“Addinina be bani damar taba jikin namijin da ba muharramina ba”
“Minene haka?”
Ta fada masa da gamsasshen bayani.
“To miyasa kike yi?”
“Zan daina duk ranar da na samu wanda ya zama mijina halal malak”
Yayi murmushi.
“Barin addinina ba abu ne mai wahala ba, haka na al'adata domin ina jindadi idan nai shigar mutanen kirki masu saka tufafi irin naki, ina jin na cika cikanken mutum, ina jin natsuwa idan an saka tufafin da suka rufe min jiki gaba daya, sai dai barin tsafi ina jin kamar zan cutu”
Ta dago da sauri ta kalleshi.
“Ba zaka cutu ba, ina tunanin saboda ni zaka yi, inda zamu je babu wanda zai mana sheri ko ya jefe mu da wani abu, zamu yi rayuwa ne cikin farinciki da kaunar juna, kuma saboda ni zaka yi ba kace kana son farincikina ba? Ba kace zaka zama min komai ba? Ashe ba so kake na jidadi ba?”
Ya karasa hawaye na sauko mata tana kallonsa, shi ma kallonta yake yana jin kamar ba zai iya ba, barin tsafin da ya zame masa jiki? Ba dan kalubalen da zai fuskanta ba sai dan sabon da yai da shi. Kawar da fuska tai tana cigaba da hawayen.
“Ashe ban cancanta ba, ashe ba da gaske kake ba, amman na sani wata rana zan samu wanda yake so na da gaske, wanda zan iya yin komai saboda farinciki”
Ta mike tsaye sai shi ma ya mike tsaye ya riko hannunta.
“Ban taba yin karya ba, zuciyata bata raya min na fadi abun da ba shi ne ba, idan nace idan son ki to ina sonki ne da gaske Zainab har cikin raina...”
Yayi shiru yana kallonta kamin ya cigaba.
“Idan har hakan zai faranta miki rai, kuma zai sa na rabauta, zan aikata na miki alkawari sai kin samu farinciki saboda ni...”
Murmushi da kuka ne ya zo mata a lokaci daya sai ta lumshe ido tana maida numfashi a hankali.
FALMATA POV.
“Kenan ke yanzu cigaba zaki yi da karatun?”
“Eh ai sai da muka yi magana da shi yace ya yarda zan cigaba da karatuna bayan aure”
“Gaskiya haka yafi, ni ma yace idan na haihu zai saka ni a makaranta, a gida yake dan koya min su gaisuwa da kuma yadda zan iya karatun hausa, gashi har ina iya hada hausa na karanta”
“Hakan yayi gaskiya, ai kin samu miji mai sonki da gaskiya Falmata, daman hausawa sun ce mai hakuri mawadaci”
Falmata ta yi murmushi tana kallon