Showing 234001 words to 237000 words out of 273152 words

Chapter 79 - FULANI BOOK COMPLETE DOCUMENT by Khadijah Candy .txt

29 Aug 2024

72723

da hankali, lamo tai tana ta sauraren yadda zakin muryarsa ke ratsa kunnenta yana isarwa zuciuayrta da sassan jikinta, can kuma ta lumshe ido tana maida numfashi a hankali. Be kai karshen ayar ba bachi mai dadi yai gaba da ita.




ZAINAB POV.


Sai da ta ci kukan ta koshi sannan ta fito ta baro dakin zuwa dakinta, sai kuma ta rasa abun da za tai a dakin kamar wanda ta manta komai haka ta zama sai safa da marwa take a dakin tana tunanin abun da za ta yi. Sake fashewa tai da kuka, tana jin cewar mutuwa zata yi idan ta bar garin Yola, ta ya zata iya rayuwa garin da bata san kowa a can ba, kuma bata saba ba, gashi ba su yarda da komai na zamani ba balle cigaba? How? Ji tai ita kan ba zata iya bin Wasim ba hakan yasa ta juya da sauri ta fice daga dakin zuwa dakin Iya da zimmar yi masa magana sai ta tararda dakin babu kowa a ciki sai ko matsan kayan Iya. Juyowa tai ta fito ta koma dakinta ya shiga bathroom ta hada ma kanta ruwan wanka ta watsa a jikinta ta fito kamar wata marar lafiya, wardrobe dinta ta nufa ta dauko wani yadi marar nauyi ta saka bata shafa komai a jikinta ko turaren da take so a yau sai ta ji bata bukatarsa abubuwa da yawa sun taru sun mata tsaye a rai, idan ta fara tunaninsu sai ta ji kamar ta kashe kanta ta huta. Tana cikin dakin ta ji sallamar Mai gadinta, ba karamin faduwa gabanta yai ba, domin a yanzu tsoron komai take ciki har da sautin mutane. Haka nan dai ta unkura ta tashi ta fita cikin rashin kuzari, sai ta same shi tsaye jikin kofa yana matsar kwalla.


“Hajiya yanzu aka kirani daga kauye wai Mahaifiyata ta rasu”


Ya fada mata karyar da ya ke ta tsarawa tun dazun, bayan mahaifiyarsa ta dade da rasuwa, kawai ya zabi yai haka ne domin ya tsorota da jin cewar mayu ne kuma ya zai iya tafiya ya bar hakkinsa ba. Zainab ta yi murmushin bakinciki domin ta san karya yake yayi hakan ne kawai saboda ya tsiratar da rayuwarsa.


“Ina zuwa”


Ta fada sannan ta juya ta koma ciki, albashinsa na watan gaba daya ta dauko ta ba mika masa.


“Kana da gaskiya, dole ne zaka tsorata kuma ban ga laifinka ba na gode”


Ta fada masa haka a yayinda yake karbar kudin, shi kam godiya kawai yai ya fice daga falon, sai ta juya ta koma ciki ta dauko babbar jakarta ta dauki wasu tufafin ta zuba a ciki da kuma wadansu abubuwan da zata iya bukata, sannan ta dauko wata karamar jakar ta zuba tarkacenta ta fito rike da makullin gidan a hannunta, sauran tufafinsa duk a ciki ta bar su sai da ita gurin motarta ta saka jakar sannan ta dawonta rufe ko'ina na gidan, sai kuma tai baya baya tana kallon gidan hawaye na sauko mata.


“Allah duk yadda ka tsara a gareni haka zai kasance, Allah ka min mafita ka yaye min damuwata ka shiga cikin lamarina”


Ta saka hannunta ta share hwayenta sannan ta juya ta nufi gate ta bude ma kanta ta dawonta shiga motarta ta fita da ita sannan ta sake dawowa ta rufe gate din ta saka masa key, har ta juya sai kuma ta juyo ta kai hannu ta taba gate din, sannan ta koma cikin motarta ta ja motar bata tsaya ko'ina ba sai gidansu kawarta Amina, duk da wani shiri suke irin sosai ba but ta san Amina mace ce mai amana kuma mai sanin ya kamata. Amina ta yi mamakin ganinta a irin wannan lokacin da ake ta kira kiren sallah magariba. Bayan sun gaisa Zainab ta kama hannunta ta danka mata keys din motarta da na gidanta, Amina ta kalli keys din da mamaki sannan ta kalleta.


“Na meye?”


“Na motata ne da na gidana, na yarda ke shiyasa na baki ajiyar wannan, kuma dan Allah a rika kula min da gidana”


“Miya faru?”


“Ba komai kawai zan bar garin nan ne, na wani lokaci ke kadai na yarda da ke a duk kawayena”


Amina ta mike tsaye tana kallon yadda hawaye ke saukowa a idon Zainab.


“Dan Allah ki fada min idan wata matsala ce”


“Zan kira ki a waya anjima, na baki mana, idan kuma kika ga na dauki lokaci ban dawo ba ki siyar da komai ki min sadaka”


“Wannan wace irin magana ce Lafiya kike Zainab?”


“Lafiya kalau na ke Amina”


Ta fashe da kuka, tare da saurin mikewa tsaye domin bata son mijinta ya dawo ya tararda ita a gidan.


“Amman zan fada wa Mai gidana, idan be aminta ba zan hannata fada miki a waya sai ki fadi wanda a hannatawa abun”




“Ba matsala na gode”


“Allah yai miki mafita ya yaye miki ko miye a ranki”


“Amin sai wata rana”


Zainab ta fada cikin kuka sannan ta juya ta fice da sauri, daman ta cire akwatinta a wajen motar sai ta karasa ta ja shi zuwa gate Amina ta fito ta tsaya bakin kofar falonta tana kallon Zainab hawaye na sauko mata. A Hotel Zainab ta kwana tun a dare ta siye ticket din zuwa Katsina, washe gari ta shirya ta nufi airport cikin shiga ta doguwar rigar atamfa da mask sai dan karamin mayafi da kwatinta sai yar karamar jakar hannunta.
Karfe goma daidai jirginsu ya daga zuwa Katsina, sai a lokacin ne ta ji wani irin kewa da tausayin kanta ya kara kamata.




<<<<<<<<
Da 9pm zan turo wani Inshallah, jiya ban samu na yi ba saboda ba nepa.




_________
Ina mata matan kwalisa Matan da suka ansa sunansu na Mata? Ina wadanda ke cewa mun yi mun yi bamu ga amfaninshiba? Hmmm to ku zo ga Yar gidan Maifata ta zo maku da Al ajabu, dan tsugunno, gumba da tsimi da Zuma daban daban, maganin sanyi na maza da Mata. Ga kuma garurruka irinsu mallakau sabuzu kuwa, sa bahaushe saibi, Dan hubbare kafi malam aiki, ke kadai ke da miji, dahuwar kaza, tattabara, ciccibi da dai sauransu. Ba anan kayanmu suka tsaya ba, muna hadin amare na musamman turaren sutura turaren tsugunno turaren wanka da na daki da na jiki duka 4amare nasu na musamman ne, amma ga tsuhuwar da ke son komawa yarinya itama zata iya zuwa ahadata kai abundai sai wanda ya gani, dan haka karkubari abaku labari, domin neman karin bayani zaku iua nemana ta wannan number 09029891757 ko 08169311410, muna aikawa ko'ina a fadin kasar nan har waje kasar nan muna aika kaya.
Address: Nasarawa Samaru Area gurin masallacin mai sola Gusau Zamfara state Nigeria.
03/12/2021, 18:59 - 🤐🤐🤐🤐: *Khadeeja Candy*




*Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 300 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith bank, then send the evidence via 08036126660*




Lumshe ido yai ya bude har lokacin idonta a rufe suke tana murmushi.


“Fateme..”


Ya kira sunanta da muryar da bata taba jinsa da ita ba. Hakan yasa tai saurin bude idon sai tai arba da hawaye da ke sauka fuskarsa. Take hamkalinta yai mugun tashi.


“Miyasa kake kuka? Me ya faru? Ko dan an taba min ido?”


“Aa”


“To me ya saka ka kuka?”


Ya kai dubansa gurin rigar da ke jikinta sannan ya kai hannunsa ya kama hannunta ya dora saitin kirjinsa.


“Ban kwana na zo na yi miki”


“Ina zaka je”


“Babu inda zan je?”


“To miyasa kake min bankwana? Ko mutuwa zan yi?”


Yayi murmushi wasu hawaye na sauko masa.


“Aa, bankwana na har abada”


“Mutuwa zan yi? Ko jirgin zai yi hadari damu mu mutu?”


Ya girgiza mata kainyana yawo da idonsa a fuskarta.


“Zan miki bankwana ne, irin na tafiya ba na mutuwa ba, zan tafi garinmu ja zauna tare da yan'uwana, ke kuma na bar ki da na kin yan'uwan?”


Take ta ji wani iri sai a bata fuska kamar ta fasa kuka.


“Me na yi?”


“Ba ki yi komai ba, ba za ki taba min komai ba”


Ya fada sannan ya kama tafin hannunta ya saka cikin na shi.


“Saboda wannan...”


Wani irin jan numfashi tai cike da tsoro, ba tsoro na ganin wani abun gudu ba, sai dan tsoro na sanyin da bata ji ba a hannunsa.


“Miyasa ban ji sanyin ba?”


Ta tambaya cikin tashi hankali. Sai ya bata amsa cikin kuka marar sauti.


“Saboda bani ne mijin ba”


Fashewa tai da kuka ta rumgume shi da sauri.


“Aa kai ne, kai ne Wallahi...”


Hannunsa ya saka ya banbanreta daga jikinsa ya kama fuska hawaye na sauko masa.


“Da gaske ba ni ba ne, ba ki taba hannun wani namijin kin ji sanyi ba?”


Ta yi shiru tana kuka irin kukan dake shigewa cikin zuciya saboda bakinciki da zafinsa.


“Ka kara zuba min to”


“Idan zan zuba miki sau dari ki rike hannuna sau dubu ba za ki ji komai ba, saboda ba ni ba ne”


“Amman ni ai ni ce ni dai ina sonka haka nan”


Ya sake rumgume kankan, sai ya lumshe ido hawaye na sauko masa.


“Karka bar ni dan Allah, kai kadai na ke so, bana son kowa ni da kai na saba”


“Za ki saba da kowa ma, domin kina da shiga rai, kina burge wanda ya fahimci rayuwarki”


Ta dago tana kallonsa.


“Miyasa to zaka bar ni? Mi na yi?”


Bude idonsa yai ya kalleta.


“Saboda, addina da na ki ba daya ba ne, al'adata da ta ki ba daya ba ce, kuma ba ne mijin ba, domin ba ki ji sanyi a hannuna ba”


“Ai ba dole sai na ji sanyin ba, Dan Allah Wasim ka daina min wasa”


“Ba wasa ba ne, dole ta sa ni kaina ba dan na so ba ne, idan ban rabu da ke ba, Idonki ba zai bude ba, kuma da yanzu ba ki dawo hayyacinci ba, mahaifina ya dage akan dole na rabu da ke, idan ba haka ba ba zai bar ki ba”


“To ka aureni a haka mana, Wasim dan Allah... Ina son idon ya rufe sai mu yi auren dan Allah”


Ta durkushe a gabansa tana fashewa da kuka.


“Ba za ki ga ne ba ne, idan na yi haka b zaki jidadin rayuwar ba, ni ma kuma ba zan so haka agareki ba”


“Na gane baka so na yanzu? Saboda bana jin magana ko? Saboda ina ta yawan magana ko? Na bari daga yau ba zan sake ba, ko na ji maganar ta zo zan yi sauri na rufe bakina, dan Allah kai hakuri Wasim ina sonka, ni dai ina sonka”


Juya mata baya yai ya dafe kansa yana ta hawaye, duk yadda za ta ji ya san b kai kwatar yadda yake ji ba, domin shi ya fara kamuwa da kaunarta, kuma ita zata iya samu wanda zai kula da ita ya biye rayuwarta ta manta da shi amman shi kamin ya samu haka abu ne mai wahala.


“Wasim... ”


Ta kira sunansa cikin kuka, sai ya saka hannunsa ya share hawayensa ya juyo ya kalleta.


“Ba ki taba hannun wani kika ji sanyi ba?”


“Ban son shi ban son ban son wacan, ni da kai na saba”


Ta make kafada tana ta kuka tana fadin haka, sai murmushi da hawaye suka zo masa lokaci daya, sai ya duka daidai ita.


“Zan tafi, daman na zo ne na yi miki sallama, ba zan sake dawowa gareki ba, ba za ki sake ganina ba, amman bana son ki manta da ni, kamar yadda ni ma ba zan manta da ke ba”


Ya kama hannayenta duka biyu ya sumbanta.


“Ina sonki sosai ina son ki san wannan, amman kaddara ta raba komai, ba mu isa mu canja kaddara ba, ina miki fatar alheri”


Ya saka dayan hannunsa aljihu ya ciro abun hannu mai kamar na azurfa ya kama hannunta ya saka mata, sannan ya sake saka hannunsa ya dauko sarewa yar karama kamar ta wasan yara ya mika mata.


“Ki busa wannan a duk lokacin da kika tuna da ni”


Ya sumbacin goshinta, sai ta lumshe ido ta matse sarewar a hannunta sosai, can kuma ta bude ido sai ta ga babu shi a gabanta take ta mike tsaye ta fara waige waige.


“Was... Was.... Was....”


Ba ta ko iya furta sunan saboda kukan da ya ci karfinta, sai waige waige take kamar sabuwar mahaukaciya tana kiran sunansa murya a dakishe, sai kuma ta tsaya can tana daukar numfashi kamar ba ita, domin zan ka rantse da Allah Fadime ba zata iya shiga irin wannan halin ba saboda wani ya barta. Jin tai a taba sai ta juyo da sauri, arba tai da Wasim dake sanye da tufafinsa na dazun wando tufafinsa sai dai fuskarsa ta yi kaca kaca da hawaye kamar an yi yakin kuka, idonsa ma sun rine sun masa mugun ja sosai kamar garwashi.


“Mutuwa zan yi dan Allah karka tafi, na ji wani abu a cikin zuciyata yayi min nauyi sosai kumaya danne numfashina.... Kuma... Yana sa ni ciwon kirj kamar zuciyar zata fito, dan Allah karka ta fi idan ka tafi abun zai dawo, zan iya mutuwa”


Ta fada daker numfashi na sarke mata saboda kuka da kuma nauyin zuciyar da take ji abun da bata taba ba. Ta fadi hakan ne saboda bata taba sanin wani abu heartbreak na ainahin ba sai a yau, a strong feeling of sadness har cikin bayanta take jin ciwon.
Hannunsa ya saka ya rike fuskarta sai ya hade goshinsu guri daya ya lumshe ido yana maida numfashi a hankali, yana jin fiye da yadda take ji.


“Ka ce ya rufe idon ka ji? Na yarda ya rufe idon sai ya bar ni na aureka? Ina son ka Wasim dan Allah”


“Ina sonki fiye da yadda kike so na Fateme amman babu yadda zan yi... Ba zan iya zuba ido ki cutu ba, ba zan iya rayuwa cikin farinciki ba bayan ke kinaa cikin wata damuwar”


Ta kama hannunsa ta sake tabawa, ta sake a karo na uku, sai sake karawa sau ba dadin tana ta kuka.


“Wayyo Allah na”


Tana ta yakar kukanta tana sakawa a zuciya domin bata son ya fito, sam bata ma son ta yarda cewar Wasim zai tafi.


“Ko wani abun na yi maka?”


Ya girgiza mata kai.


“Ba ki yi komai ba”


“Ko saboda na ce Zainab Mayya ce?”


“Zainab ba mayya ba ce, Iya ce mayya, kuma ba saboda haka ba ne, na fada miki idan ban rabu da ke ba, idonki ba zai dawo ba, kuma asirin da Hajiya Babba ta yi miki da Hajiya Talatu ba zai barki ba, asiri suka miki aljani ya dauke ki daga can ya dawo da kenan kuma ya mantar da ke komai, kaka ya ki aminta ya yi magana da aljanin har sai idan na yarda ya rabu da ke, kuma dole na aminta saboda ba ni ne mijinki ba”


“Wasim aa dan Allah... Ka bashi hakuri ka ce na ce dan Allah yayi hakuri”


Yayi murmushin tare da hawaye a lokaci daya.


“Babu wani abu da zamu iya yi, je ki yi ibadarki”


Ya sake ta sai tsaye guri daya tana jin cewar idan ta matsa tafiya zai yi.


“Zan yi marmarin murmushinki, kiriniyarki da ma komai na ki, ina son ki sosai”


“Sake zuba min maganin”


Ta tara mishi hannunta tana kuka sosai marar sauti, sai ya share hawayen idonsa yana kallon fuskarta.


“Ba ki yarda da ni ba ne Fateme?”


Ta daga masa kai alamar eh bata yarda din ba, sai yai murmushi idonsa suka sake cika da kwalla.


“To rufe idonki na miki na ido”


“Idan na rufe sai ka tafi?”


“Aa zan tsaya har sai kin yarda”


Sai ta rufe ido daya ta bude daya, nan ma Murmushi yai yana jin kamar ya kurma ihu saboda zai bar Fadime, dabi'unta na daga cikin abubuwan da ke burgeshi.


“Dole sai kin rufe duka....”


Ya fada cikin kuka irin na masa, domin ya san tafiya zai yi ya barta, ba kamar yadda take zato ba. Sai ta rufe idon tana ta saurare ko zata ji wani abu ko ta gani amman shiru, hakan yasa ta bude idon sai ta ga babu kowa a dakin. Ta fi karfin minti talatin a tsaye tana hawaye sai sauraren abun da ke mata yawo a zuciya yake, can kuma ya kai hannu ta dauki sarewar tana dubawa hawaye har basa bari ta ga komai daidai. Dukawa tai ta aje sarewar ta nufi inda take ganin Hijab ta dauka bata ko tsaya neman prayer mat ba ta yi sallah a kan tile, tana sallah tana hawaye har ta sallame, a lokacin da ta daga hannunta tai addu'a sai ta rasa abun da zata roka, sai kawai ta fashe da wani irin kuka sosai.






***


Muhseen na daf da shiga mota wayarsa dake aljihu tai ringing ciro wayar yai yana duba sunan mai kiran Shattima ne rubuce akan wayar, picking yai.


“Hello Shattima”


“Muhseen ya gida?”


“Alhamdulillah ya hakuri? Gobe zamu shigo Inshallah”


“Allah ya kai mu kana kusa da Fateema?”


“Eh ka yi sa'a yanzu zan bar gidan Mama Fulani”


“Ai kullum cikin sa'a na ke”


“Eh kan tun da ka samu wannan talkative din”


Muhseen ya fada da dariya sannan ya juya ya shiga cikin yana labartarwa Shattima yadda Aliyu ya fada masa sun tsinci Ataa. Kai tsaye ya nufi upstairs ya kwankwansa kofar dakin da Fadime take ciki sannan ya bude ya shiga, sai ya same ta zaune hawaye na sauko mata kamar wanda akai wa mutuwa. Mamaki ne ya rufe Muhseen sai ya sauke wayar daga kunnensa yana kallonta.


“Lafiya?”


Hade kukan kawai take bata iya cewa komai, hakan yasa shi tunanin ko ta sake losing memory ta ne?


“Yasmin?”


Nan ma bata amsa ba, domin jin take idan ta bude bakinta kuka ne zai fito.


“Lafiya?”


Shattima ya tambaya daga cikin wayar, sai Muhseen ya maida wayar kunnensa.


“Kuka take?”


“Kuka? Bata wayar”


Muhseen ya karasa inda take zaune ya mika mata wayar.


“Shattima zai yi magana da ke”


Kin karba tai sai hawaye take tana fisgar numfashi da karfi.


“Ba ta karba ba”


“Me akai mata?”


“I don't know”


“Kara mata a kunne”


Muhseen yayi yadda Shattima ya fada ya kai wayar saitin kunnenta ya kara mata.


“Fateema...”


Shattima ya kira sunanta a hankali tare da fatar ta amsa mishi sai ya ji shiru.


“Fateema talk to me, fada min matsalarki”


“Ai duk kai ne ka taba hannuna har sanyin ya cire gashi nan ya taba ban ji sanyi ba”


Bayan ta amayar masa da haka sai ta samu damar fashewa da irin kuka mai karfi wanda ya saka Mama Fulani


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login