Showing 33001 words to 36000 words out of 141223 words
Chapter 12 - RASHIN IYAYE Complete Document by Rabi'atu Muhammad Rabi'u Oum ARQAM.txt
marayun ALLAH🤔)
"Hauwa dai sandarewa tayi daga zaune, jin ma'kudan kud'in da mijinta yace ya sanya su a harkar sana'o I har Kashi biyu!
" Bazakiyi magana bane? Na ga kin kafe ni da idanu ne?
"Mai gida kenan, ALLAH yakyauta zance, Amma nasan bakada wad'annan kud'in, daga lissafo, kaji tsoron ALLAH dai da kud'in marayu a hannun ka, kuma su ba'a Cinsu a zauna lafiya, nan dai Hauwa tafara wa Kawu isma'il wa 'azi Wanda abanza takeyi domin kuwa Wanda yayi miss ba yajin Kira!
Karshe tace Amma kwanakin Baya can Hadiyyah ta zo maka da zancen ci gaban karatunsu kace baka da kud'i, yau Kimanin wata biyu kenan, da fitowar Zakiyyah daga gidan mijinta Amma baka nemeshi kaji meyake faruwa ba, bana jin GIDAN ma kana zuwa, kana du ba y'ay'an D'an uwanka Wanda aka ba ka amanar su! Kadai ji tsoron ALLAH Mai gida akwai Ranar 'kin dillanci! Na tabbata in da Kaine ka rasu Alhaji(Ammar) bazai wa y'ay'anka haka ba, ko baka bar komai ba shi Mai tsaya musu ne, balle ka bari, bana tantama kud'in ga don su biyar ba ta'ba musu zai ba a aljihun sa zai wayalta musu! Inji Hauwa kulu tana 'karasa zancen da jima'in rashin Alhaji Ammar bn Yassir
" Gaskiya ne malama kin iya wa'azantar wa, Amma ki sani Duk abunda Zaki fad'a na fiki sani, wai ma ina ruwan ki da harkar y'ay'an Wana? Kin san dai bazan cuce su ba ko? Ko ki sarara min, Duk abunda ya dace zanyi musu
zancen Zakiyyah banson ci gaban karatunsu ne shiyasa nace bani da kud'i, ita Kuma Zakiyyah Wannan shegiyar yarinya ce(kina ina seerat kinji abunda kawu isma'il yake cewa' kawarki😂) zaman gida takeso, gata ga shinan, shiyasa na daina kai musu kud'in ce fane, da sabulun wanka Dana wanki, nasan ai baza su rasa ba, dai kuma Zeenah inason Sanya ta a makaranta tun daa yanzu bata zuwa!
Nan dai kawu isma'il ya zayyanawa Hauwa Duk WANI kud'irin da yake ransa .
WANI tayi mamaki WANI kuma, tana addua ALLAH ya ganar sa mijinta Akan marayu domin kuwa sha'anin su akwai wahala, zata ci gaba da yi Masa wa'azi ko ALLAH zai dawo dashi hanya madaidaiciya domin ta ga yayi nisa kuma yanzu bazai ji kiraba
Daga 'karshe yake ce mata su Hadiyyah zasuje visiting d'in Alhaji yana so itama su had'u suje, gaba d'aya har yaran, lallai ne Alhaji fa yayi goshi, ALLAH ya shirya kawu isma'il.........
**************
"Bro ka'ki sakar jikinka, tun da mukazo nigeria, me yake damun kane? Nace ka cire Wannan abunda ya faru daga cikin zuciyar ka, ji nake mu uku harda AKEELA abun ya faru, ita ma ta saki ranta, Amma kai kullum jiya iyau, ko a NEW DELHI a haka muke dakai, Amma ja yanzu abun yafi 'kasanta!
AKEEL naga ya dafa kafad'un d'an uwansa AQEEL Yana maganar!
Amma ko gezau Banga yayi ba, sai ma sa'bule hannun d'an uwan da yayi daga jikin sa yana kwanciya Akan bed d'in da suke zaune a gefensa!
"Nasan baza kayi magana ba Amma kana jina, sarai yakamata ko dan Abbu ka saurarawa kan ka hakan, muddin yana ganinka a wannan yanayin kana kallo damuwa yake shiga,kuma kana yana da matsala sosai Akan damuwa ko? Sai yaga kamar har yanzu akwai wata matsala tare dakai,(wacce iri FANS kodai bashi da Hankali ne Can baya?🤔)
AQEEL dai Duk wannan zantukan da AKEEL yake masa baice 'kala ba, sai lumshe ido da yayi kamar Mai bacci ma, shi ma d'an uwan bathroom naga ya nufa, babu alamun yaji haushi ta yadda d'an uwansa bai nuna yaji abunda yake fad'a bama, sai ma murmushi da naga ni akan fuskar tasa shi AKEEL, yayin shigarsa bathroom d'in yana waiwayen d'an uwansa AQEEL.
Haka y'an biyun Alhaji tallafy suka kasance tun dawowar su gida, AKEEL yana ta harkar gabansa dai'dai gwargwado, sa'banin d'an uwansa AQEEL da sai a hankali halinsa, y'an uwa da abokan arzi'ki sai zuwa sannu da zuwa ake musu(lallai FANS idan da kud'i babu abunda baza'a yi ba) ana ta tambayar AQEEL sai ace yana garden, ko study room ko Yana cikin d'akinsa,domin sune guraren zamansa,
"Yau ma Alhaji tallafy Suna zaune a babban falon gidan gaba d'aya, AKEEL Hajiya Aisha, da kuma AKEELA, Amma babu ko 'kurar AQEEL,
Alhaji tallafy yace "KEEL" ina d'an uwanka ne? Je room d'in sa ka Kira munshi,
"To Abbu ALLAH yasa ya fito fa Dan, naga brother tun da muka dawo 9ja sai a hankali fa, kuma Abbu har acan ma haka yakeyi, na rasa sai yaushe brother zai koma mutum kamar kowa, ya dinga walwala,abun da ya faru da can ya faru, Amma ya'ki dai nawa,
"ALLAH sarki d'an uwa Rabin jiki, AKEEL ai haka manta d'an uwanka ba tun asalinsa dama bayason hayaniya, haka ma magana Amma naga kai dashi kuna Hira "KEEL" cewar Alhaji tallafy yana shafa kan d'ansa AKEEL .
Je ka kirawo mun shi kaji maza_maza
Tashi yayi ya nifi room d'in twin's brother d'in sa.
"Acan falon kuwa duba Alhaji tallafy yakai kan AKEELA wacce ita ma,tana zaune tayi shiru, babu um bare um_um kallon tv takeyi, Wanda zai kayi duban tsanaki zaka gane ba tvn take kallo ba WANI tunanin can daban takeyi.
Nima duba nakai gareta, Lallai FANS badon AKEEL da AQEEL maza bane, da kuma cewa su sun fita girma, ita Kuma mace ce babu abunda bazai sa in ce su bane, kamar ta 'baci tsakaninsu, ko ince ma tafisu kyau, saboda ita mace ce su Kuma maza🤔
" Me ke faruwa AKEELA? Kema kin yi shiru ko? Wai yakukeso nayi. Da rayuwata? In kinzo gidan nan kiyi shiru, y'an uwanki suma suyi shiru, Amma gwanda AKEEL shi,
"Babu Komai Abbu kawai dai karatu yayi nisa ne kasani ai, ai shikenan AKEELA
In ji Alhaji tallafy yana Kai duba ga y'an tagwayen sa AKEEL da AQEEL Wanda yanzu suka 'karaso wajen, da 'kar AKEEL ya tattago AQEEL har yazo ya amsa Kiran mahaifinsu
Ita kam Hajiya Aisha sai kallon mijinta da y'ay'ansu take, Wanda abun sha'awa ne, y'an uku rigis maza biyu mace guda d'aya
Cikin ginshira AQEEL yace
"Abbu barda da dare, Ummu barka da dare"
(Inji AQEEL fa FANS) kinji muryar sa kuwa 🤔
Tare iyayen suka amsa Masa, kafin Ummu tace" ko kaifa yarona, Amma da kaje cikin 'kuryar d'aki kayi shiru, ka dinga sakin ranka kana walwala kaji d'an albarka!
"In Sha ALLAH Ummu"
Abun da AQEEL yace kenan, sai kuma yayi shiru.
Haka dai iyayen nasu suka dinga jansu da Hira, cikin y'ay'an uku AKEEL ne kawaii yake d'an tankawa, Amma AQEEL da AKEELA babu umm bare um_um,
Duk da sannan fuskokin nasu ba KAMAR d'azu ba ta d'an saki.
Anan Alhaji tallafy yake cewa y'ay'an nasa in Sha ALLAH jibi, zamuje daku gaba d'aya cibiyata, kukai mata ziyara, KAMAR yadda Duk wutu kuke zuwa
" ALLAH yakaimu Abbu da rai da lafiya"
Cewar AKEEL"
AKEELA da AQEEL kam jinjina kai sukayi,
"Abbu yace banji kunyi magana ba, masu Hali d'aya?
Ya 'karasa maganar da murmushi yana kai duba ga y'ay'an nasa AKEELA da AQEEL
Duk da yasan ba maganar zasuyi ba..
Nan dai suka cigaba da tattaunawa tsakanin wannan iyalai me magana nayi masu jinjina kai nayi.................
Kiyi Haquri da wannan FANS
✍️Oum Arqam ce ontop🥰
2/7/24, 4:28 PM - Rãbi'atou Aminou {Oum ARQAM}: *RASHIN IYAYE*
(Babbar musiba)
Daga *Al 'kalamin✍️ Rabiat Amin (oum Arqam)*
*08128131163*
✍️ Marubuciyar...
*Komai Nisan jifa* 📚
*Hakan ba kuskure bane*📚
*_____________*
MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION📚🖊️ *(M°W°A)*
'Kungiyar d'aya tamkar da dubu masu Nazari da Aiki da ilimi burin 'kungiyar a koda yaushe shine ta fad'akar ta Kuma wa'azantar ta Nishad'antar da masoyanta🤙
*____________*
*PAGE TWENTY SIX 26*
tun da nafara book d'in nan banyi kyautar ko page guda ba🤣🤔 Anya Kuwa babu rowa a wannan tafiyar🤭😂
"Yau take kamar sallah a gurin su HADIYYAH, hakama ga Alhaji Wanda za'a jewa visiting d'in, murna suke sosai, kana kallonsu zakasan akwai magana.
Hidayah ta 'kwallawa Zeenah Kira!
Baza kizo ki saka kayan ki bane Zeenah? Kina kallon kowa Yana shiri, Su Hunaif, Hafsa, dasu Farouk da haydar Duk sun kammala shiri Amma banda ke!
Hidayah ta 'karasa maganar tana le'ko kanta daga gefen labule, domin ta ga me Zeenah takeyi a tsakar gidan nasu da takejin surutun ta
Arba tayi da Zeenah a zaune ita da Hunaif da Hafsa su da kayansu masu kyau a shirye tsaf, sa'banin ita Zeenah Suna ta qasa
"Ta so Zeenah in sa miki kayan Mana Duk mun shirya fa,
Yaya Hidayatullah(haka suke kiranta y'an gidansu, Amma mutane Suna ta'kaitawa ne da Hidayah ) mammah(Zakiyyah) ce ta shiga wanka, bata d'auko min ka yana ba, tace in bari ta fito ta d'auko min ni da ita iri d'aya zamuyi(Zeenah sarkin surutu fad'i ba a tambayeki ba🤣)
"Tayi maganar dai_dai da fitowar Baaba daga d'aki a shirye tsaf,
"Wa cece d'in zakuyi anko? Mamma take ko momo(lallai seerat Baaba fa ta takurawa qawarki yasin) babu Inda zata bimu da izinin wa? In ba ta da Hankali to mu muna dashi, sai ta Kira mijinta ta tambaye shi tukun"
Ta 'karasa maganar da fincikar hannun Zeenah ta mi'kawa Hidayah ita"
" Ri'ke hannunta kije ki Samar mata,kayan sawa ki bata ta saka, ki hanzarta, rana ta farayi"
"Yadda Baaba ta gayawa Hidayah haka ta aikata.
"Lokacin ita Kuma Hadiyyah tana 'karasa d'aurin d'an kwalin ta,
"Jeki Wajen sis, ta zuge miki zip, ta d'aura miki d'an kwali na 'karasa zuba kayan can,
"To yaya cewar Zeenah"
"Yaya Hadiyyatur_rahman(lallai yau Zeenah fi'ili takeji dashi kowacce saita kirata da cikakken sunan ta, babu ragi, ai da sai ta hada da Hassana da Hussainar kawai 🤣) zugen zip ki d'auran d'an kwali...
Haka dai Duk suka gama shirin su ma sha ALLAH sai ma kaga y'an biyu Hadiyyah da Hidayah abun Ba'a magana kamar ka sace su ka gudu(twin's malam ai duniya ne, musamman iri d'aya idan mata mataa, ko maza duka)
"Duk maganar da Baaba ta fad'a wa Zeenah, Zakiyyah tana jin su.
'ko data fito daga wanka, fuskar ta a d'aure batayi magana ba, kaya ta d'auko zata saka,
"baaba tace fatan kin Kira mijinki kafin kisa 'kafa ki fita ko?
" Ni ban Kira shi ba,Akan me zan kirashi? Ya san da ni ne?
" Ai ke dama baki da Hankali, to mu muna dashi Kuma babu Inda Zaki, matu'kar baki d'auki waya kin Kira mukhtar a gaba na kin tambayeshi, ba babu in da zamu dake, sai dai ki sha Zama a gida, sha_sha_sha! kawai wacce batasan me yake mata ciwo ba!
" Baaba ta 'karasa maganar CIKIN 'karaji(kai Baaba ita ma masifaffiya ce dama, ko halin zakiyyah ya mayar ta HAKAN?🤔 Amma da babu ruwanta fa)
"Ita dai Zakiyyah batayi magana ba,HAKAN ya nuna kenan bazata visiting d'in ba.
" Baaba kenan kina tunanin ni zan Kira mukhtar a waya? Lallai ne kenan bani da Hankali kome? Shi Bai kirani ba saini ce zan kirashi ai ba ubana bane ALLAH ya raka Taki gona, sai kun dawo, Amma Kuma idan nayi niyyar zuwa WANI wajen wallahi bazan tambayeshi ba,
" Maganganun da zakiyyah takeyi kenan.
Ita dai Baaba bata kula taba, saboda taga,abun Zakiyyah sai an nata uziri,
" A haka sukai wucewarsu, suka bar Zakiyyah a gidan zuwa *tallafy charity foundation*
harda Sa'adatu za'aje
'A zuciyar Zakiyyah abun da take ayyanawa".
Kai ni nayi Masa text a waya ma ina jiran takarda ta da, saboda bazai mayarni Y'ar iska ba, ni ba sakakkiya ba ni ba Mai aure ba, fita ma Ace babu gurin zuwa, idan babu Auren sa kuwa fa sai in fita in da naga dama!........ lallai FANS 'kawar seerat zakiyyah fa tafara kaini bango yasin😡kufa.......?
**************
"Iya lan gidan Alhaji tallafy Suna dining area Suna breakfast ba kajin, 'karar komai sai na cokula, kowa sai bawa cikinsa yake bawa ha'k'kinsa, Alhaji tallafy, Hajiya Aisha, AKEEL, AKEELA, da kuma oga AQEEL.
"Bayan sun kammala kowanne ya tashi ya goge bakin sa da tissue,
" Yawwa y'an albarka kar lokaci ya 'kure Mana AKEEL da AQEEL kuje part d'in ku, ku shirya da wuri, ita ma AKEELA ta haura upstairs d'akin ta ta shirya,saboda ina da abunda zanyi acan foundation iDan mukaje"
Cewar Alhaji tallafy yana duban y'an ukunsa cikin fuska d'auke da Annushuwa.
"To Abbun mu, in Sha Allah ba bu matsala, yanzu kuwa zamuyi ready " cewar AKEEL,
Sauran kuwa girgiza Kai sukayi, hannun AQEEL ya ri'ke suka fice zuwa shashen su, ita Kuma AKEELA tana haurawa sama.
"Oum AKEEL bakya ganin zuwan mu da su, tallafy foundation bazai 'karasa cirewa AKEELA da AQEEL damuwar da tayi saura acikin rayuwar su ba, sabo da idan muka je, za'a duba file d'in Yara a za 'kulo ja wad'anda suka sha wahala a rayuwa fiye da wacce su kasha a baya, kin ga kamar yaron nan maraya Yassir(Alhaji) shikam zanso a koma bada tarihin rayuwarsu tun tasowar sa da sababbin shigar shi tallafy foundation d'in!
" Nasan za suji tausayin rayuwar yaran gaba d'aya,duk da acikin su dasu AKEEL bansan labarin wane yafi muni ba, Amma suma kam labarin su akwai ta'ba zuciya!
Alhaji tallafy ya kai aya a zancen sa a dai_dai lokacin da suke haurawa sama dakinsa, domin shi ma ya shirya d'in!
"Hajiya Aisha yace. "ma sha Allah Abu AQEEL akwai ka da hangen nesa sosai gaskia, Wannan ma ai kaga WANI dabara ce, ta yadda zamu kawo 'karshen damuwar y'ay'an mu cikin sau'ki!
" ALLAH ya tabbatar Mana da alkhair Abu AKEEL"
"Allahumma ameen Oum AQEEL"
ya qarasa maganar da dosar bathroom,itama Hajiya Aisha nata d'akin ta huce domin shiryarwa, bayan ta taimakawa mijinta da Abubuwan da zai bu'kata idan yafito daga wanka.
Can bangaren su AKEEL ma sun shirya d'in, har ogan naku,(tun Ranar da Alhaji tallafy yai Masa magana ya d'an saki ransa KA'DAN🤣 a HAKAN FANS🤔)
Masha ALLAH tagwayen Alhaji tallafy *iri d'aya sak!* suit Mai Arnan kyau tsa daddiya suka saka ba'ka, ku hangon farin mutum cikin ba'kin shiga! Takalmi white , kansu ba hula, shumar nan sai she'ki take alamun tana shan gyara
Babu banbanci sai na Glass da AQEEL yake sanye dashi, da kuma sakakkiyar fuska wacce AKEEL shima yake d'auke da ita shine banbancin, sai 'kwamshin turare sukeyi()
Itama AKEELA ma sha ALLAH tayi kyau abunta kamanninta da y'an uwanta ta fito sak! Tayi shirinta
Tana fitowa iyayenta Suna fitowa harabar gidan suka fito gaba d'aya, a dai_dai lokacin suka su AKEEL suka fito"
"Ma Sha ALLAH" Hajiya Aisha tace ganin yadda y'ay'anta sukayi kyau sosai, kamar ka sace ka gudu,
Shi kam Alhaji tallafy sai murmushi yakeyi ganin y'ay'an sa.
Body guard guda biyu ne suka taso daga wajen da aka tanadar musu, daya daka ciki ya bud'ewa Alhaji tallafy mota shi da Hajiya Aisha suka shiga, driver yazo ya ja motar bayan body guard d'in yashiga gaban motar shima.
" D'aya body guard d'in shi ma dae wata mota again ya bud'ewa su AKEEL, AKEELA da AQEEL suka shige suma body guard shima ya shiga gaban motar , Mai gadi wa wangale musu gate a jere suka danna hancin motar su, Wanda a gaban motar su Alhaji mota ce body guard biyar aciki suke take musu gaba, bayan ta su AKEEL d'in ma body guard d'in ne a mota daban.... Sai nace allah yakaiku lfy Alhaji TALLAFY! Baya goya marayu!
°°°°°°Can tallafy foundation kuwa, su Hadiyyah ai sun jima da Isa, Alhaji yayi murna sosai,da ganin y'an uwansa da mahaifiyarsa, DUK da dai a fuskarsa da alamun damuwa daya kai duba gareta,Basu dad'e da zuwa ba iyalan kawu isma'il suma suka hallara, nan fa akaita Hira, duk da TSAKANIN Hauwa kulu da sa'adatu ta ciki na ciki ta baka na baka, Wannan aminta ai ta kau tun bayan AUREN kawu isma'il da Sa'adatu tayi, DUK da an rabu.
Mazauna tallafy foundation kam suna kallo lallai Alhaji dama d'an gata ne haka, rayuwa kenan (Nikam nace ina gatan anan FANS basusan su wanene y'ay'an Alhaji Ammar bn yassir bane)
DUK abunda suka zo Masa fashi na masarufi, sun bashi,abin co ku wa anci an sha Alhmdllh,
"Hira ta 'balle TSAKANIN Hidayah da Alhaji sai tsokanar ta yake wai ta girma ta sha ruwan Kaduna, ita dai sai murmushi kawai takeyi, Hadiyyah ce mai tare mata, da cewa Wai kai meyasa ka yaron nan ka raina mu ne? Alhaji yace lallai yarinyar nan, nine ma yaro ko? Da nawa kuke girmeni? Wata hud'un?
DUK Wannan Hirar sunayi ne Inda aka killace shi domin visiting na d'aya daga cikin d'an foundation d'in in Allah yakawo lokacin, sai hirarsu u sukeyi....
A dai dai lokacin ne Kuma, hancin motar Alhaji tallafy da y'ay'ansa da body guard d'in sa ya danno harabar tallafy foundation.....
FANS yakuke ganin Wannan ziyara?
Shin me xai faru a lokacin?
Da kuma nan gaba
✍️Ku biyo Oum ARQAM domin kuji wad'annan amsoshin da wacce baku furta ba ma take ranku
Yanxu aka Fara wasan.............
2/7/24, 4:28 PM - Rãbi'atou Aminou {Oum ARQAM}: *RASHIN IYAYE*
(Babbar musiba)
Daga *Al 'kalamin✍️ Rabiat Amin (oum Arqam)*
*08128131163*
✍️ Marubuciyar...
*Komai Nisan jifa* 📚
*Hakan ba kuskure bane*📚
*_____________*
MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION📚🖊️ *(M°W°A)*
'Kungiyar d'aya tamkar da dubu masu Nazari da Aiki da ilimi burin 'kungiyar a koda yaushe shine ta fad'akar ta Kuma wa'azantar ta Nishad'antar da masoyanta🤙
*____________*
*PAGE TWENTY SEVEN 27*
"Bayan iyalin Alhaji tallafy sun gama 'karbar gaisuwa daga ma'aikatan foundation d'in, AKEEL nedai Mai amsa gaisuwarsu fuska a sake, shikam gogan naku saidai jinjina kai, ko d'aga hannu sai kace WANI gomna ko sarki yazo gaban talakawansa, itama dai AKEELA HAKAN ne gareta, tunda ita macece ai babu laifi dan tayi hakan ga maxa Wanda ba Muharramanta bane,
Ma'aikatan Tallafy foundation sai murna sukeyi Yau Alhaji yazo za'a Shana, sosai Dan kuwa Rabon kud'i yake musu,