Showing 93001 words to 96000 words out of 141223 words

Chapter 32 - RASHIN IYAYE Complete Document by Rabi'atu Muhammad Rabi'u Oum ARQAM.txt

saka muku abinda sukai muku, yanzu haka bana tare da ita, Usman kam abunda yai miki duniya ce ta isheshi Riga da wando, silar komai mahaifiyarsa, wacce haka kawai tacemun zai dawo Gidan nikuma, batare da ƙin nuna amincewa ba na Amince, ashe da abunda zai aikata miki, kiyi haƙuri kinji, tun d Abbu yafara magana AKEELA tai shiru ta kafeshi da idanuwa, ita kam itace tasan abunda takeji a kanta tun lokacin da Abbu ya Kira sunan Usman (azzalumi a gareta kuma mara imani ko tausayi) taji ƙwaƙwalwar kantata na tafarfasa, kamar ana kwara MATA Ruwan zafi, daga bisani kuma tayi wata mahaukaciyar ƙara da sume wa. Abbu da su AKEEL hankalin su ya tashi, dan haka da sauri AKEEL ya tafi office ɗin Doctor Maryam domin ya kirawota ganin abunda AKEELA takeyi na fisge_fisge da ƙara................




Muje next page.........




Oum ARQAM ce ontop 🥰
3/8/24, 1:16 AM - Rãbi'atou Aminou {Oum ARQAM}: *RASHIN IYAYE*
(Babbar musiba)




Daga *Al 'kalamin✍️ Rabiat Amin (oum Arqam)*


*08128131163*


✍️ Marubuciyar...
*Komai Nisan jifa* 📚
*Hakan ba kuskure bane*📚




*_____________*
MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION📚🖊️ *(M°W°A)*


'Kungiyar d'aya tamkar da dubu masu Nazari da Aiki da ilimi burin 'kungiyar a koda yaushe shine ta fad'akar ta Kuma wa'azantar ta Nishad'antar da masoyanta🤙
*_____________*








*PAGE FIVETY TWO 52*




Ƴan amana ga wannan Page ɗin saboda ƙaratowar wata mai Al farma na Ramadhan da AJIYE Post zanyi Zuwa bayan Sallah,Amma ga wannan idan ALLAH Yasa kun samu wani bayansa to, ALLAH Yasa mushiga watan a Sa'a ALLAH Yasa muna da rai da lafiya, Yasa muyi ƙarɓaɓɓiyar ibada




"Ko da AKEEL doctor Yaje office ɗin doctor Maryam domin kiranta hankalinsa a tashe,Kwantar Masa da Hankali tayi Kafin su tawo tare,har lokacin AKEELA ƙara takeyi da fisge fisge, Hankalin AQEEL da Abbu inka duba fuskarsu zaka gani a tashe take, Amma CIKIN ikon ALLAH Doctor Maryam ta dinga Kwantar musu da Hankali Daga ƙarshe tace musu, ai wannan ba wani abu bane alamu ne suka nuna cewa ruɗewar da ƙwaƙwalwar AKEELA tayi Yanzu idan aka MATA Allurar barci zata farka normal.


Kamar yadda doctor Maryam ta faɗa CIKIN ikon ALLAH kuwa AKEELA ta farko normal, Amma kuma sai ku ka takeyi, ta rungume Abbu ta dinga zayyana Masa Irin cin zarafin da Usman yai MATA, Abbu sai rarra shinta yakeyi Duk da zuciyarsa ba bu daɗi,hakama ƴan uwanta su AKEEL, ALLAH ya taimaka AQEEL bai sume ba wannan karon Amma fa idanuwa sunyi ja jur kamar garwashi Hakanan sai shaƙuwa yakeyi CIKIN sauri aka Bashi ruwa yasha Kafin barci ya ɗauke shi, hankalinsa ya tashi ganin yadda AKEELA take ku ka,da yadda ta dinga faɗar gallazawar da Jimmai take MATA, da tsawon lokacin da Usman yakai ya na kai MATA Hari,har ALLAH yakawo lokacin da yai galaba akanta,Hakanan Abbu ya dinga bata Haƙuri Akan Irin da ƙiletan da yakeyi idan tazo MATA da xancen jimmai, inda ya nuna MATA cewa shi ya zata Duk ɗaya ne da Mahaifiyar su da Jimmai ɗin, nan Abbu yai MATA al bishir da cewa ya rabu da Jimmai yanzu.


Kwana uku tsakani aka sallami su AKEELA daga Asibiti, su ka koma gida ta warke ragal, Baba Sallau ya na gidan kuma Duk wani kulawa ya na Bawa gidan, dan haka da suka dawo sai ABunda ba'a rasa ba, kusan kullum suna Zuwa gidan.


AKEELA ta koma school wanda da ma Abbu ya faɗa ba ta da lafiya ne, yarinya mai surutu da ƙwazo da ƙokari Amma yanzu Duk tazama so silent,daga malamai har ɗalibai sun ɗauka RASHIN lafiyar da tayi ne,aka Kwana Biyu zata koma normal.


Haka ma su AQEEL sun koma school Duk da haka dai kowa ya ga canji ga waɗannan twin's ɗin me walwala da marar walwala Duk sai a slow.


Abbu yanzu tsoron MATA yakeyi, ganin Yadda jimmai taiwa gudan jininsa,ita ma gudan jinin ƴar uwarta, yanzu wa zai ɗauko wacce zata Kula da su musamman ma AKEELA da take mace, Kullum tunanin da Abbu yakeyi kenan,tun dawowarsu da ga Asibiti,Ya sa a Ransa zaiyi Aure ko dan su har a Kullum yanawa wacce zai aura fatan ta zamo kamar inna Rabia a halaye da ɗabiunta wajen Kula masa da ƴaƴa, kullum ya na addu'a.




Mahaifiyar Jimmai kakarsu AKEEL ta Kira Abbu akan me jimmai tai Masa Hakanan zai MATA saki, Abbu ya danne zuciyarsa yacewa Inno "Inno ba bu abunda ya faru kawaii dai kinsan Aure rai ne da shi dan haka Aure tsakaninmu da Jimmai ya ƙare,Amma Inno jimmai ba bu abunda taimun, Inno tasan Abbu yarone mai biyayya tun lokacin Aurensa da Ummul khair, dan haka bataja aBun ba tai Masa addu'a da fatan alkhair, daga ƙarshe ta sako Masa zancen zamansa ba bu MATA ga Yara Harda mace ma kamar AKEELA, nan yace Inno ki tayani da addu'a, Nima ina tunanin hakan,lokacin Jimmai tana ɗakin ta na jin muryar Abbu har suka gama tattauna da Inno yai MATA sallama ya fice.


Sai sannan ta fito "Inno na gaya miki haka kawaii Ɗalhat yace ya sakeni, Amma Babu abunda ya faru,Kika ƙi yarda Yanzu kinji ta bakinsa, da share ƙwalla Jimmai da ƙarasa zancen murya gwanin tausayi, ɗa da mahaifi nan Inno ta tausayawa jimmai, ta dinga Kwantar MATA da Hankali Akan idan da rabon komawa saita koma ga Ɗalhat tun da da sauran igiya ɗaya, tun da ga sannan Jimmai ta sake a gidansu haka ma CIKIN ƴan uwa, idan tace haka kawaii Ɗalhat ya saketa wasu suna yarda wasu ku ma suce da wata a ƙasa.




______________




Usman ko da Jimmai ta faɗa Masa yadda suka ƙarke da Abbu ko a kwalar rigarsa,sai cewa yayi Maama can ta matse Masa, ya barmu da ALLAH ,to ai dama dashi yaganmu kuma da shi zai kalemu, ita dai Jimmai Ajiyar zuciyar tayi suka gama hirar su ta kashe wayar.




jikin ƙanin ba ban Usman sai a Hankali ya yi zafi har sannan suna Asibiti, dan haka yana Zuwa asibitin, Shukra in ta dawo daga school kuma tayo gida ta shirya Kafin ta bi Umma(mariƙiyar su) a Hankali shaiɗan ya dinga ƙawatawa Usman Shukra musamman idan ya yi mankas da kallon sa na banza ita kuma ta dawo daga school, da kunya dai ABunda zuciyarsa take shirya Masa ya yi, Amma kuma fa abunda yakeji game da Shukra ya fi ma abunda yakeji game da AKEELA na sha'awa, dan haka zuciyarsa ta yanke Masa shawara Akan ya zubawa Shukra, Maganin da zai bugar da ita kawaii ,ya yi amfani da ita bata sani ba,da ma kuma yana siyowa Shukra ƙanwarsa ice cream da sauran kayan makulashe ta nan kuwa ya zuba MATA, ta na dawowa daga school kamar yadda ya saba ya ɗauki ice cream da su juices ɗin ya bata aikuwa tai ta murna ta shige da su ɗakin ta , Shukra akwai son Zaƙi daƙar tayi wanka daga ita sai towel aikuwa ta ɗauko ice cream da juice ɗin da Usman ya bata ta hau Sha ta na lumshe idanu, gama Shanta ko minti 5 batai ba barci ya ɓingireta aikuwa nan Usman yazo ga Shukrah da yake wannan ya tsara abunsa cikin lallama yai Amfani da ida dan bazance fyade ba, Yasan Umma batanan ku ma bamai shigowa gidan war Haka ƴan aiki suna wajensu da ban,cikin kwanciyar Hankali yagama aikinsa ya gyara Shukra kamar yadda take yai shigewarsa ɗaki, bayan yai MATA allaurar kashe zugi wacce ya siyo a chemist.


Ko da Shukra ta farka batayi tunanin komai ba, Amma tayi mamakin barcin da tayi wajen awa biyu, dan haka sai gaɓoɓin jikinta da taji sun mata tsami, da kuma Yanayin jikinta da taji sai a slow, cikin sauri da shiga bayi tayo Alwala tai Sallah Duk da taji ƙasanta ba kamar da ba, Amma bata kawo komai a Ranta ba, a gurguje tai haramar Zuwa asibitin,ko da taje Asibitin umma batayi wani tunanin zuwanta ba kamar yadda ta saba ba, tunda wataran ma bata Zuwa.


Tun daga sannan Usman ya mayar da Shukrah kamar matarsa Duk lokacin da ya buƙaci kasancewa da ita hakanan yake Amfani da ita, lalläi Usman anya yanada Hankali kuwa ƙanwar ka uwa ɗaya uba ɗaya, ko da Yake abunda Jimmai ta shuka shi zata girba, lokacin da.yaiwa AKEELA fyade jimmai Harda cewa Usman mai Yasa bai bata wani abu ba kafin yai MATA fyaɗen, to Yanzu ga shi ya bawa Shukra ai kuma,Kunga kenan karatun Jimmai ya tuno dashi. Cikin ikon ALLAH jikin Baban su Usman ya yi sauƙi sosai har an sallamo su, sun dawo gida, kuma komai ya dawo normal,yaji sauƙi sosai, har Baban yake cewa "Usman kadawo gida ne? Ea baba na dawo ai shi ABBU ɗin ya saki Maama ne, kaga kuwa me zai kaini Zama a gidan na dawo gidanmu Usman d shagwaɓa yake ƙarasa maganar ga Baban nasa,
Ai shikenan Usman ni da ma banso ka koma Gidan Jimmai da Zama ba, da ka nuna kanaso ne, Yanzu ai ga shi ka dawo ALLAH ya kyauta, inji Baba wanda yaji sauƙi sosai.








_______________




Tun da Abbu ya saki Jimmai dai ƴan uwansa suka dawo Masa a kwanyar kansa, aikuwa cikin Tashin hankali Yaje gida, Inna Rabia tayi murna haka sauran ƴan uwa, su ma hakanan sukace Rana tsaka Ɗalhat mukaji tunanin ka da komai naka mun Mance, shi ma yace musu ai shima hakanan, baisan meyasa ya Mance su ba, akai ta jimamawa da koke koke, Saida suka keɓe da innar sa da Abba (tsoho mai ran ƙarfe) nan Abbu ya bayyana mahaifansa yadda Jimmai tai Masa, Amma ya roƙi karsu gayawa kowa, Inna Rabia da Baba Hankalunsu ya Tashi jin yadda Jimmai taiwa Ɗalhat da kuma ta'asar da ɗan ta Usman yaiwa AKEELA, nan dai Abbu ya kwantr musu da Hankali Akan cewa komai ya wuce ai, AKEELA ma ba bu wanda zaice wannan abun ya faru da ita idan ba faɗe akayi ba.


Cikin satin kuwa Abbu dasu AQEEL ya kwashe su gidan inna Rabia da Baba,iyaye sai farin ciki da murna hakama su AQEEL.


Nan akaita mamakin girman su AQEEL da kuma AKEELA, lokaci weekend ne dan haka suka kwana biyu a gidan.


Aisha(mommah) da mahaifiyar Abbu da mahaifiyar ta ya da ƙanwa ne, karatu ta yi batafi 30_32 ba ƴar boko ce sosai, dan haka inna Rabia tace "Talle (haka take kiransa) ga Aisha nan tagama karatunta, Amma ALLAH bai kawo miji ba ka aureta kawaii, ina kyautata Zato a gareta, yarinya ce mai hankali da tunani da nustuwa, haka ma Baba yasa Baki, ba bu ja in ka Abbu ya amince da zaɓin iyayensa a Karo na Biyu Bayan Jimmai, ko da inna Rabia ta tunkari Aisha da maganar bata musa ba, ALLAH yagani da ma tana son Abbu a zuciyar ta, kuma tana tausayawa ƴaƴansa jin Irin wahalar da suka Sha Hannun jimmai,kuma ko ba bu Aure ai za'ta iya kulawa dasu.


Dan haka ba bu jimawa aka nemarwa Abbu Auren Aisha dangin mahaifinta,ko da Abbu ya gayawa su AKEELA wacce zai aura basuyi baƙin ciki ba, dan kuwa sun santa Aunty Aisha tana da kirki, Amma su AQEEL kam kadaran kaga ham suka amshi Auren.


CIKIN ƙanƙanin lokaci akayi Aure Aisha ta tare a gidan Abbu, ya sameta kamar yadda Yake fata dan kuwa tanada halayen kirki,a Hankali a Hankali ta dinga gogewa Abbu dasu AQEEL tabon da Jimmai taiwa MATA na kuɗin goron da sukai musu, har suka sake da ita AKEELA ce take ce Mata mommah sai kowa yakama Mommah har su AQEEL ɗin.


CIKIN ƙanƙanin lokaci walwalar Abbu da AKEEL ta dawo Amma AQEEL da AKEELA sai a slow,Duk wani ga ta da kulawa Mommah ta na Bawa Abbu da ƴaƴansa.


Baba da Inna Rabia sunyi murna da wannan Aure da aka hada, walwalar Abbu ta dawo da komai Amma asirin da Jimmai taiwa Abbu da Ammar BN Yasir kam har sannan bai warware ba, Bai tuna shi ba, haka ma sauran ƴan uwa Basu tuna ba.


CIKIN ikon ALLAH foundation ɗin da Abbu yake ginawa ya kammala,wanda taci sunan *TALLAFY CHARITY FOUNDATION* sunan ya samo asali da sunan sa inna Rabia take kiran Abbu dashi wato *Talle* sai ya gyarashi da *TALLAFY* Duk wani abu da za'ayi an gama hakama gomnati tasan da zamansa,kuma Alhamdullillahi aBun ya karɓo, dan tashin farko yara da yawa aka kai, hakama Duk kangarar da RASHIN jins yaro ana kaishi CIKIN ikon ALLAH bazai fita ba, sai ansamu waraka Akan hakan.


Wanda hakanne ya ƙarawa Abbu albarka a dukiyarsa, tuni gidan da suke ciki ya kuma siyen wasu filayen da gidajen kusa ya haɗe da nasa, su kuma ya sallame su da wani, yan uwa da abokan arkizin kam ana wutawa da Abbu, hakana zuwan Inna Rabia da Baba makkah nawa, Duk wani rufin asiri da arziƙi ALLAH yaiwa Abbu kuma hakan ya samo asaline Daga taimako da tallafawa marasa shi.


Abbu ya mallaki kadarori da kamfanoni ba bu adadi,mai sunan *TALLAFY GROUF OF COMPANY*. Su AQEEL da AKEEL suna kammala secondary ya samar musu admission A *CANHWU UNIVERSITY* dake New Delhi, CIKIN ikon ALLAH kuwa suka tafi, sai fatan NASARA.


Abbu bodyguard ɗin sa sunfi Ashirin waɗanda suke kula da lafiyar dayi Masa rakiya a kowanne lokaci, kuma suna jin daɗin mu'amula kai bakace a ƙarƙashin sa suke ba, hakana Ma'aikatan Tallafy foundation Suma.


Zamansa da Mommah sai son barka, a yanzu kam sai kace AKEELA da AQEEL da AKEEL ƴaƴanta na cikinta ne, SABODA kulawar da take Basu, hakan yanawa Abbu daɗi,shiyasa a koda Yaushe yake ƙara ƙaunar ta a Ransa, tana kiranta da ABU AQEEL shikuma yake OUM AKEELA KO AKEEL,tuni Abbu ya manta da wata jimmai Tunda dama abunda tai Masa yace yabarta da ALLAH, Yasan tabbas ALLAH zai saka Masa yasakawa ƴaƴansa.




___________________






Tun da Babansu ya gama jiyya ya dawo daga asibiti kuma Usman tabbatacce ya ƙyale Shukra haka, to aina zai samu da ma.


Cikin ƙanƙanin lokaci Shukra ta ƙara cika da fari, fiye da da, kuma ba bu wanda yakawo komai a Ransa game da hakan,tun da dai ita ba Rashin lafiya take ba,sai dai cikin dare Zuwa asba zazzabi yake kamata da zarar asba ta yi kuma zata dawo normal,sai kwaɗayi da takeyi kuma a school ne, irinsu agwaluma da su aya me gishiri haka zata dinga siya tana ci har tayo guzirinta, a gida ma haka taita kwaɗayi Akan abinci kenan yau tace wannan zata dafa gobe wannan, ko tace batason wannan, wannan take so, gidan kowa harkarsa yakeyi ƴan aiki suna wajensu,Hakanan Umma aikin gomnati takeyi ba zaman gidan take sosai ba lokacin da Shukra zatayi kwaɗayinta bata nan ko tananan ma ba mai kula bace........






Lalläi fans meyake damun Shukra ne Hakanan




Wane irin Usman ne wannan wai kamar ƙuda yake baya gudun Haram




ALLAH sarki Mommah lallai kin biyo halin inna Rabia goggonku gaba ɗaya keda Abbu ɗin




Su AQEEL da AKEEL an cale India ALLAH yabada ilimi mai amfani


Foundation ɗin Abbu ta kammala ALLAH ya taimaka ya ƙara arziƙi mai amfani da Budi




✍️oum ARQAM ce ontop 🥰






Muje next page ƴan amana idan ALLAH yayi Kafin ramadhan nakuma wani idan kuma sai Bayan Sallah ne to ALLAH ya ƙaddara ganawarmu yasa muyi ibada karɓaɓɓiya






I love you All my fans🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰
4/14/24, 12:03 PM - Rãbi'atou Aminou {Oum ARQAM}: *RASHIN IYAYE*
(Babbar musiba)




Daga *Al 'kalamin✍️ Rabiat Amin (oum Arqam)*


*08128131163*


✍️ Marubuciyar...
*Komai Nisan jifa* 📚
*Hakan ba kuskure bane*📚




*_____________*
MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION📚🖊️ *(M°W°A)*


'Kungiyar d'aya tamkar da dubu masu Nazari da Aiki da ilimi burin 'kungiyar a koda yaushe shine ta fad'akar ta Kuma wa'azantar ta Nishad'antar da masoyanta🤙
*_____________*








*PAGE FIVETY THREE 53*




Godiya ta tabbata ga ALLAH daya bamu kammala ibada ta RAMADHAN, ALLAH Yasa munyi karɓaɓɓiya ya biya Mana bukatun alkhair,




Inawai yan uwa barka da sallah ALLAH ya maimaitamana


*🕌EID MUBARAK All my fans*🥰🤗


A wannan halin shukhra ta kasance na kwaɗayi Babu wanda yasan meke damunta,tayi fresh da ita jiki sai sheqi yake indai mutum me Hankaline yana ganinta zaisan akwai labari, Saida aka kwashe wata huɗu a haka lokacin tafiya ta miƙa Sannan Umma ta fuskanci abunda ke faruwa da Shukrah, bata daɓa Haihuwa ba Amma kuma ko budurwa taga Shukra tasan akwai labari! Hankalin Umma ya tashi batayi Wani tantanma ba, ta tsare Shukra da Jan Ido Akan yaushe rabonki da ganin al al adarki? Shukra tai shiru kanta a ƙasa tunani ta lula ai zatayi wata biyar batayi ba, Umma 5month kenan dama inason gaya miki ko bani da lafiya ne! Akaini Asibiti! Umma dai idanuwa ta zaro waje Shukra waya miki ciki? Na shigesu! Ciki kuma Umma Babu kowa nida bana zuwa ko ina daga school sai gida cewar Shukra tana kallon idon Umma data zuba MATA shi!
"Karki Raina min Hankali Shukrah ki gayan tun muna shedar juna! Innalillahi Umma ALLAH ya tsareni da abun kunya bana kula kowanne namiji ALLAH kema kinsani! Cikin kuka Shukra ta ƙarasa zancen"
Suna wannan zancen Abba ya shigo yaga Shukra na kukan! Yace lafiya nan Umma ta gaya Masa meke faruwa! Salati ya Fara yana "Shukrah ki faɗa Mana GASKIA wane ɗan iska ne ya cuceki sai munyi shari'ah dashi ya qarasa faɗa da shafa kan Shukra alamun rarrashi,Duk irin lallashi da ban bakin da Umma da Abba sukewa Shukra Akan waya MATA ciki haka take cewa ita bata saniba, dan Haka Abba yakira lititansa domin ya tabbatar da hasashen su,Hasashen su yazama gaskia ciki ne da Shukra 5month harda sati biyu ma, Abba kam take hawan jininsa ya tashi umma sai Kuka takeyi abun babu daɗi, wannan Ahali abun tausayi Shukra dai batasan wanda yai MATA wannan ɗanyen aikin ba, an buga an Raya, haka sukayi kwanan baƙin ciki,balle Shukrah sai Kuka take Akan batasan ko wanene ba.
USMAN kuwa daya dawo gidan yaga umma da Abba yanayi Babu daɗi, Shukra tana Kuka dai yai tunanin Wani abune daban!
My sis meke faruwa ne wai? Usman yafaɗa lokacin da yake shiga ɗakin Shukra ɗin!
Da sauri Shukra taje ta faɗa jikin Usman tana Kuka! Yaya wai cikine dani kuma ni Babu Namijin danake kulawa! Da ace Shukra tana cikin nustuwarta xata kula da halin da Usman ya shiga! Amma ina tashin hankalin da take ciki ya kore!
Jikin Usman sharkaf yayi da gumi, cikin in ina yace ci...ci....ki k..u.m.a! Eamn Yaya nashiga uku na! Innalillahi wa Inna ilaihi rajiuun sis kidai tuna meke faruwa! Ciki da yadda akayi aka sameshi domin ba'a Sha a ruwa! ALLAH yaya ban saniba, haka dai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login