Showing 21001 words to 24000 words out of 141223 words
Chapter 8 - RASHIN IYAYE Complete Document by Rabi'atu Muhammad Rabi'u Oum ARQAM.txt
mantaba Page d'in mu na farko Hadiyyah tana d'aukar albashi fa Wanda Sa'adatu take kar'beshi shin wane albashine wannan? sai next page zakuji. yanzu labarin yafara bamuyi komai ba......
✍️ Oum Arqam ce
2/7/24, 4:28 PM - Rãbi'atou Aminou {Oum ARQAM}: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/Cy82IooiC1LE5S0e2tkKcj
*RASHIN IYAYE*
(Babbar musiba)
Daga *Al 'kalamin✍️ Rabiat Amin (oum Arqam)*
*08128131163*
✍️ Marubuciyar...
*Komai Nisan jifa* 📚
*Hakan ba kuskure bane*📚
*_____________*
MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION📚🖊️ *(M°W°A)*
'Kungiyar d'aya tamkar da dubu masu Nazari da Aiki da ilimi burin 'kungiyar a koda yaushe shine ta fad'akar ta Kuma wa'azantar ta Nishad'antar da masoyanta🤙
*____________*
*PAGE EIGHTEEN 18*
Kawu isma'il fa dun zuwan da Hadiyyah tayi wajensa akan xancen cigaban karatunsu itada Y'ar uwarta, Bata Kuma ganin saba, Kuma bai Kuma xancen ba, xaman gida ya isheta ga rashin kud'i wataran sai su tashi basuda abunda zasuyi Karin kumallo balle abincin rana, a unguwar tasu wata islamiyyah ta baza komar neman malamai wad'anda dazu dinga yiwa Yara karatu, shugaban makarantar har gida yazo ya nemi alfarmar Sa'adatu akan tabar Hadiyyah tana zuwa koyarwa makarantar tunda tanada ilimi sosai aikuwa take Sa'adatu ta amince duk wata xa'a Bata 10k aikuwa Hadiyyah akaita murna, saboda itadai har sannan Bata Saba da shan koko ba idan sun samu da safe ba da cin garin rogo shima, Amma tunda Bata sana'a haka takesha idan yunwa ta dameta,Ranar da ciwon ciki take kwana,aikuwa Ana Bata albashin farko Babu inda ta zarce dashi sai provision store taje taiyo siyayyar kayan shayi da pad abarda zasu buqata itada Y'ar uwarta Zahra, Dan kuwa WANI fannin ma Saida tsinma suke amfani(Allah sarki rayuwa) Babu kud'i gashi Basu sababa, musamman Hadiyyah irin mutanen da suke da kyankyami ne, Amma saboda wahala tai wahala daina jin wannan kyankyami d'in tayi,tana dawowa gida da kaya sai y'an ragowar canji aikuwa Sa'adatu ta rufe ido tai maya tatas Wai ai ko xatayi siyayya tabari ai takawo gida tagani, itadai Hadiyyah Babu bakin magana tunda tasamu abunda takeso, ai kafin wata kayan data siyo sun qare, saidai ta dinga ranta wajen Sa'adatu itakam ko biyar Bata Basu a matsayinsu na mata dole zasu buqaci pad da sauran abun amfani, hakane Yasa take rance a wajen Sa'adatu d'in, aikuwa ko kunya harda saka littafin bashi biyar ta kar'ba sai anrubuta, ai kafin wata ta kar'bi kud'i wataran sama da albashin ma, itakam Sa'adatu Babu lamuni haka ake rubutawa Ana albashi zata kar'beshi duka sannan tace Ina binki ragowar..........
Ita Kuma Sa'adatu tun bayan da Kawu isma'il yadawo maya da gidanta,sitting room ta mayar dashi shaguna guda biyar ta zuba y'an haya Ana Saida kayan miya,Me refelling na gas yakama,Mai islamic chemist da Mai siyar da kayan d'inki, Mai cajin waya, dayake layinsu irin babban layinnan ne duk irin wad'annan Sana'ar ba'a Yi kowa Yana cikin gidansa saidai yayi tafiyayyiya idan yana buqatar wad'annan abubuwan ai kuwa Sa'adatu tana saka haya kafin kuce mene sai aka Fara kasuwanci a gurin masu shagunan Suna samun ciniki, da kud'in hayar tayi wadaqarta aciki take arawa Hadiyyah kud'i, aciki take musu koko da jiqa musu garin rogo d'in, (...to FANS zara Bata barin dami ai Sa'adatu kud'in xai qare ai, Kuma shekara ba kwana bace, kafin kud'in hayar su sake dawo miki kinji jiki...)
*************
Can Kaduna state ma da Hidayah sukayi waya da Hadiyyah tagaya mata cewa kawu isma'il Bai Kuma xancen cigaban karatunsu ba saita haqura Amma zuciyarta babu dad'i domin na 'kwallafa ranta akan hakan, tun bayan da sukayi candy shikenan kawu isma'il saiya ga damar tura musu kud'in da yake tura musu balle man shafawa dasu sabulu d'in, suma Haka su suke kasancewa yau da dad'i gobe Babu dad'i, shi dai Hunaif dayake har sannan Yana zuwa makaranta ta account d'in shugaban makarantar yake tura kud'in term to wannan ne bai fasa ba ,Dan kuwa da term yayi koda kawu isma'il Bai turoba take headmaster d'in xai kirashi yai Masa tuni Kuma babu batun yaqi turawa, Hadiyyah taci gaba da zuwa islamiyyah Suna Y'ar Sana'a acikin gida da ita suke rufawa kansu asiri, in sun samu suci idan babu suyi haquri............
*************
Ansha bikin mukhtar da bilkisu Y'ar uwarsa, Kuma har sannan ko ajikin Zakiyyah harkar gabanta takeyi, ba gida d'aya ya had'asu ba, saboda bayason bilkisu taga irin rashin arziqin da Zakiyyah takeyi itama bilkisu tadinga Masa shi,(... Lallai mukhtar baison mataba ne, Amma mace Mai hankali ai burunta taga abunda kishiyarta ta gazawa mijinsu ita Kuma ta zage dantse tana masa, nikam dana bawa mukhtar shawara ai had'asu waje d'aya yayi, ta yanda ko idan bilkisu tana bashi kulawa sosai yada Zakiyyah tayi hankali itama su dinga rige_rige wajen faranta Masa, ko fita yawon maqota da shashancinta xai ragu ta koma xaman gida ya kilukace FANS😅...) Saidai Kuma unguwa d'aya suke da Zakiyyah d'in, Babu nisa, mukhtar yayi kwana bakwai a gidan amarya kamar yadda musulunci ya koyar da ayiwa budurwa ga mijin da yayi Aure idan yanada wata matar, zaman da yayi da bilkisu mukhtar yaga soyayyah da kulawa uwa uba ga tarairaya, to dama ita bilkisu tasan me Zakiyyah takewa mukhtar, tasan duk halayenta, koda ta shigo itakam ta qudurce a ranta duk WANI kulawa da tarairaya da farantawa zata dinga Masa kodan taxamo, matar so wajen mukhtar, taxamo Babu ya ita, tasa mukhtar yadaina rangwantawa Zakiyyah a duck sanda tai masa ha daidai ba yanuna Mara kuskurensa, shikam mukhtar sai yaji kamar karya koma wajen Zakiyyah, saboda babu abunda yake kwasa sai ba'kin ciki da 'bacin Rai (... Yakamata y'an uwa mudaure mugyara musani cewa,koda mazajenmu sunyi aure karsu manta da kulawar da suke samu a gurinmu, karmu yadda muxamo kamar Zakiyyah🙏 miji yadinga tunanin kamar karya koma wajen mu...) Koda yadawo gidan zakiyyah dai WANI kunbure_kunbure takeyi, shi ko takanta bai biba, harkar gabansa yakeyi, ya d'au ABIE Wanda yake tai masa dariya, nufin yaron ina kashiga Daddy Kwana biyu, itama Zeenah taita murna, duk da darana Yana leqosu ai kwanane bayayi kawaii a gidan,Kwana biyu dayayi a gidan zakiyyah Babu abunda ya kwasa sai ba'kin ciki,da baqaqen maganganu da tadinga gaggaya Masa,shima dama zuciyarsa tana kusa bai qale taba, ta gaggaya mata magana Kuma yace "daga yanxu duk abunda kikaimun wlh saina rama nadaina tausaya miki tunda Baki tausayawa kanki ba,Babu yanzu Wanda nake ganin mutuncinsa, ko idonsa naki Wanda zaisa na raga Miki, tunda Baki da mutunci baki da tarbiyyah, tun iyayenki da kakarki Suna raye ake sulhu tsakaninmu Amma ko bayan rasuwar su HAKAN baisa kin daina halinkiba,sai abunda yayi gaba to muzuba mugani, ni dake shege kafasa,to tun daga auren da mukhtar yayi tsakanin Zakiyyah da mukhtar kullum Suna ta fad'a sai kace karnuka, lallai FANS baxa kubawa Zakiyyah shawara ba........
*************
Alhaji mutanen TALLAFY CHARITY FOUNDATION anacan duk WANI 'ka'idojin da ake buqatar d'an makarantar yacike ya kammala yanzu haka Shirin fitar dashi ake daga ajin dayake zaune shi kad'ai, a had'ashi da sauran dalibai, saboda ana ganin nasara sosai a wajensa duk Wannan kunbure_kumbure dayake yadaina, Rashin kunya itama yadaina, shaye_shaye kuwa dama aina zai samu,Masha Allah Allah yad'orar a hakan Alhaji Allah ya shiga lamarinka marayan Allah........
Alhaji 'Dalhat Abdur_rahman *(TALLAFY)* wannan satin xai kawowa TALLAFY CHARITY FOUNDATION ziyara, domin yakwana biyu baya qawar, yaje ganin likitansa da Kuma ziyarar y'ay'ansa a *NEW DELHI* Wato india can suke karatunsu, to wannan satin xai dawo, sai muce Allah yadawo dashi lafiya..........
Salon daban yake Muje zuwa FANS
✍️Oum arqam ce ontop🥰
2/7/24, 4:28 PM - Rãbi'atou Aminou {Oum ARQAM}: *RASHIN IYAYE*
(Babbar musiba)
Daga *Al 'kalamin✍️ Rabiat Amin (oum Arqam)*
*08128131163*
✍️ Marubuciyar...
*Komai Nisan jifa* 📚
*Hakan ba kuskure bane*📚
*_____________*
MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION📚🖊️ *(M°W°A)*
'Kungiyar d'aya tamkar da dubu masu Nazari da Aiki da ilimi burin 'kungiyar a koda yaushe shine ta fad'akar ta Kuma wa'azantar ta Nishad'antar da masoyanta🤙
*____________*
*PAGE NINETEEN 19*
Ina godiya ga seerat, mumy Waleed, Alhamdulillahi da irin kulawar da kuke bani Dan ganin ina typing akoda yaushe, nagode da adduarku gareni naji sauqi sosai, RASHIN IYAYE zai dinga zuwar Muku a koda yaushe sai uziri ya sameni 🥰🥰🥰
IDan kadubi cikin TALLAFY CHARITY FOUNDATION kai kace Biki akeyi ko wani babban taro, kowa sai hada_hada akeyi tun daga kan ma'aikata da d'aliban wannan cibiya,bakomai yajanyo hakaba sai ziyarar da Alhaji TALLAFY zai kawowa Wannan cibiya, yau Kimanin wata hud'u Kenan bai zoba, dama kaidarsa wata uku_uku shiyasa ma'aikata suke cikin Murna idan yazo Ranar rabon kud'i kawai yakeyi musu.........
Alhaji dai yau dai yasamu y'ancinsa xa'a fito dashi daga d'aki na musamman da aka killaceshi, a wannan lokacin ne Kuma Alhaji TALLAFY yace Ranar yanason ya gana da wad'annan da xa'a fito dashi,(... Indai irin wannan lokacin yazo na fitar yaro daga cikin d'aki na musamman a Ranar Alhaji TALLAFY zaizo to kafin a fitar dashi daga d'akunan, Alhaji TALLAFY dakansa zaije wajensu yai musu nasiha ta musamman sannan Kuma ya saurari mene matsalarsu meyasa suka jefa kansu a wannan matsalar, duk Wanda yanar dazai fita daga d'aki na musamman Alhaji TALLAFY yazo to tabbas sun ciri tuta...)
Duk abunda ya kamata Alhaji TALLAFY yayi a cibiyarsa, sannan yayi ganawa da d'aliban da suka Samu y'ancinsa, haka duk yagana dasu kowanne yai Masa nasiha da illolin shaye_shaye duk jikinsu yayi sanyi, ayoyi da hadisai yadinga janyo musu wad'anda Allah da manzon sa suke tsoratarwa Akan Mai shaye_shaye da Kuma illolin sa'bawa iyaye, domin kuwa iyayensu basason shaye_shayen da sukeyi, kowanne Saida jikinsa yayi sanyi,Kuma suka yiwa Alhaji TALLAFY alqawarin sun daina in Sha Allah, Alhaji yayi murna da Wannan, Kuma duk yaji mene ne musabbabin Fara shaye_shayen yaran mafi yawanci, sanadin abokai ne wad'anda suke had'uwa dasu a makaranta, suke Fara zuwa da maganin tari azuba a lemo wannan azo ga manyan su wiwi, taba uwa uba giya, yawanci dama duk y'ay'an masu hannu da shuni ne..........
Alhaji 'Dalhat Abdur_rahman (TALLAFY) dayazo kan Yassir Ammar Yassir (Alhaji) lokacin ma shi, yatafi duniyar tunani Halin daya tsinci kansa aciki, wai kamarsa shine aka kawo nan aka killace akan shaye_shaye da rashin Kunya, kullum tunaninsa Kenan, Yana tuno Aunty(Sa'adatu) da Kuma irin cin amanar da Kawu isma'il yai musu Dan yaga Abbynsu baya raye, uwa_uba da irin xaluncin da Aunty takewa su Zahra da Hadiyyah,shine yake sawa yake shiga cikin qunci, Wanda shine Kuma yake shan wiwi saboda yafita daga cikin tunanin, yanxu Daba wiwi d'in in Yana tunanin kawaii Saidai aga hawaye Yana zuba a fuskarsa musamman idan yatuna irin gatan da Abby ya nuna musu, da Kuma kulawar Ummy(Ummu Ruman mahaifiyar su Hadiyyah) ta nuna musu Bata banbantasu dasu Hadiyyah, Amma yanzu ita Aunty gashinan Bata yiwa su Hadiyyah hakaba sai wahalar dasu take, har Mai tsaron bayan Alhaji TALLAFY yazo kan Alhaji Yana Masa magana baisan Yana yiba,Saida Alhaji TALLAFY ya taso dakansa yazo ya tallafo fuskar Alhaji d'in (... Domin yaron tun farkon ganinsa dashi yake bashi tausayi, Yana Masa kama da Halin da y"ay"ansa guda uku suka shiga shekarun baya, suma Haka suke takurewa aguri guda suna hawaye🥹meyasa HAKAN FANS? Nagadai Alhaji TALLAFY yayansa me zasu rasa...)......
Saida yad'ago da fuskar Alhaji sannan yadawo hayyacinsa, ya duqa a kasa Yana gaisar da Alhaji TALLAFY d'in, sannan Yana goge fuskarsa,ruqo hannunsa Alhaji TALLAFY yayi suka qarasa gurin da aka ajiye Masa abun Zama, sannan Alhaji yasamu kasan wajen ya zauna, sai sannan Alhaji TALLAFY yaiwa Alhaji magana dayaga yanxu yasamu nutsuwarsa," yaro wannan tunani namene kakeyinsa kamarsa kana d'an yaronka? Shin meyasa kajefa kanka a wannan mawuyacin hali, inason karka boyemin komai kaji Ammar, yawarasa maganar a tausashe(... Tausayi yaron yake bashi, tun farkon ganinsa dashi,daga gani d'an gata ne, Amma wannan damuwar dayake gani a fuskarsa ta menene kodai irin abunda yasamu su AKILA ne.. FANS inada tambayoyi Akan iyalan Alhaji TALLAFY fa kufa.?..... )
Tiryan_tiryan Alhaji ya zayyanawa TALLAFY labarinsa da maraicin da suke ciki da labarin y'an uwansa su Zahra da Hadiyyah Khadeeja da Kuma zeeenah sai babbar banza Zakiyyah, da irin maraicin da suke ciki duk WANI gata da suka kasance acikinsa da yagayawa Alhaji TALLAFY masu takewa Alhaji TALLAFY baya duk Saida suka tausayawa Alhaji sosai,Amma Kuma ababan tausayi a yanzu y'an uwansa mata su Hadiyyah Wanda Suna y'an biyu Amma Saida aka rabasu d'aya tana kano d'aya tana Kaduna.....
Alhaji TALLAFY ya jinjina kai bayan Gama jin labarin Alhaji, shima yai Masa nasihohi sosai Akan yacire komai a ransa, indai saboda y'an uwansa ne zai tallafa musu, Kuma idan kawu isma'il yazo zasuyi magana, Alhaji Kam yaji dad'i sosai, dajin abunda TALLAFY ya fad'a, dama burinsa shi dai yanzu kawu isma'il ya saki Aunty(baisan kawu isma'il ya saketa ba ) yadawo musu da gidansu daya kwace musu, da dukiyarsu da take hannunsa yake cinye musu, itama Aunty(Sa'adatu) yanzu haushinta yakeji ganin irin azabtar dasu Hadiyyah data keyi..... Akwai qura fa FANS...........
*************
Zakiyyah anadai zaune itada mukhtar babu mutunci kwata_kwata rashin mutunci salo_salo take Masa, ABIE yayi wayo Dan kuwa an yayeshi Amma kafin yakai Wannan matsayin Yasa wuya qonewa kala_kala yayita da ruwan zafine da abinci, Zeenah kam tuni tabar gidan,tun WANI gurmi da akayi tsakanin Zakiyyah da mukhtar d'in, yai mata dukan tsiya aikuwa yasha zagi ta uwa ta uba, shikam yakorata gidansu yace ta tafi, baya buqatarta a tare dashi, ya d'auke ABIE da Zeenah zai kaiwa amaryarsa bilkisu Akan ta riqe Masa, aikuwa nan fa Zakiyyah tabud'e baki tadinga zagin mukhtar har dacewa ABIE idan ka kar'ba bazan hana kaba saboda d'an kane,badashi dama nazoba, Amma Zeenah kam ba ikon kabace ba uban ta bane kai, baka Isa ka kar'beta ba da ita zan tafi, Kuma in kai ba d'an halak bane ka kar'beta ka kaiwa Wannan jakar(bilkisu), duo da HAKAN baiyi gaggawar Bata Zeenah ba(... Tsakani da Allah yakeson Y'ar nan, Yana sonta kamar Y'ar cikinsa, Kuma karatunta yake tsoro Takoma baya, yanzu tana aji hud'u a primary ne, Kuma Yana tsoron Mata shiga cikin halin da y'an uwanta suke ciki Khadeeja dasu Zahra, domin kuwa tun kafin ya d'auko ta tadawo wajensa bayan rasuwar Ummu Ruman hydar 'Dan wajen Sa'adatu yafara dukanta batada sakat a gidan Wanda da Baya mata HAKAN Saida yaga Ummu Ruman ta rasu, saidai taita kuka, inya daketa sakontane ya girmeka da Wajen wata biyar, su Zahra Babu damar magana, suma Basu tsira ba, wayyo Zeenah FANS halin da Zakiyyah zata kaita ciki kenan, Allah dai Yasa karya badata...).......
Saboda kar mukhtar yayi gaban kansa sai da ya d'au wayarsa ya Kira Mana( mahaifiyarsa Hajiya Jamila) domin yaji shin yabawa Zakiyyah Zeenah ta tafi da ita, gidansu itama Zakiyyah d'in ya koreta............
Muje zuwa FANS shin Hajiya Jamila zata bar mukhtar ya kori Zakiyyah ko Kuma abunda ta Saba zatai Masa nacewa ya qaleta.........
✍️ oum ARQAM ce ontop🥰
2/7/24, 4:28 PM - Rãbi'atou Aminou {Oum ARQAM}: *RASHIN IYAYE*
(Babbar musiba)
Daga *Al 'kalamin✍️ Rabiat Amin (oum Arqam)*
*08128131163*
✍️ Marubuciyar...
*Komai Nisan jifa* 📚
*Hakan ba kuskure bane*📚
*_____________*
MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION📚🖊️ *(M°W°A)*
'Kungiyar d'aya tamkar da dubu masu Nazari da Aiki da ilimi burin 'kungiyar a koda yaushe shine ta fad'akar ta Kuma wa'azantar ta Nishad'antar da masoyanta🤙
*____________*
Kuyi haquri da wannan nagama typing page Mai shegen tsayi Amma ya goge😭😭😭 gaskiya banji Dadi ba nasha wahala a banxa
*PAGE TWENTY 20*
Hajiya Jamila Mukhtar ya Kira bayan ta d'aga wayar sun gaisha zuciyarsa nai masa quna a muryarsa babarsa tasan cewa tabbas Yaronta yanada damuwa" meyake damunka mukhtar cewar Hajiya Jamila cikin kwantar da murya" duk yadda sukayi da Zakiyyah ya kwashe yagayawa mahaifiyarsa karshe yace" Mama abunda Zakiyyah takemun takaini bango cewa nayi ta tafi gidansu nasa hannu na d'auki Zeenah da ABIE shinefa taketa cimin mutunci wai ai iDan na d'au ABIE nine babansa ita Kuma Zeenah wai ai bamu da had'i da ita dole nabata ita su tafi.......
Kwarai dagaske haka nace aiba Y'ar ka bace Zeenah mene had'inka da ita? Kace natafi gidanmu itama Zeenah yau sai kwanan gidan ubanmu, domin kuwa Banga me zaisa ta zauna a gidanka ba!! Abunda Zakiyyah take fad'a cikin d'aga murya kenan, Kuma Hajiya Jamila tana jiyowa ta wayar, cikin muryar damuwa mukhtar yace" Mama kinji irin abunda take gayan ko? Tunda na Auri Zakiyyah bana cikin kwanciyar hankali itace yawan ma'kota, Tara mata acikin gidana, itace banzatarmun da kayan abinci, komai nawa Baya jimawa tace ya qare, a haka mama kike goyuwa da bayanta kona kawo qararta wajenki saidai kibini da fad'a kice banida haquri ai Zakiyyah yarinyace, haka nake haquri da ita,karshe kikace ai iDan ta haihu xatayi hankali to YANZU wane hankali tayi, bayan Haihuwarta wane irin wahala ce d'an data Haifa baisha ba, 'konewa kala_kala,ciwuka wanne irine baiji ba a tsawon shekara uku da haihuwarsa! Mukhtar yake fad'a cikin muryar damuwa itakam Hajiya Jamila tanajin d'an ta Bata katse Shiba,saboda tasan mukhtar yanada haquri Amma idan aka kaishi bango bai iya fushi da fad'a ba, Saida yaja ajiyar zuciya sannan yaci gaba daga inda ya tsaya kince mama idan Zakiyyah ta ta haihu xatayi hankali to YANZU haka ina hankalin yake? Cewar mukhtar tana duban indai Zakiyyah take a tsaye tana girgiza jiki alamun babu mutunci......
Sai sannan Hajiya Jamila taja doguwar ajiyar zuciya alamun duo maganganun da d'an nata yafad'a sun shigeta zata Fara magana ne Zakiyyah ta d'ora da cewa" duk abunda zaka gayawa mama kagaya mata wallahi saika bani Zakiyyah Kuma daga yau d'in nan kwanan gidanka bazan yiba, ita Maman ba itace ta zugaka tasa ka aure Y'ar kanin taba, me xata gayan? Inma ta fad'a baji zanyi ba ehe! Inji Zakiyyah tana tattafa hannayenta....
Ikon Allah gaskia mukhtar yayi haquri da xama da wannan yarinyar dama haka take? Batada tsinkaya, lallai kam na takurawa yarona xaman haquri shida ita, Allah yai maka albarka haqurinki ya biya maka, ha kowanne najimi bane zai zauna da irin wannan matar Mai Rashin kunya ga miji abunda yafi duka ma saikayiwa mace abunda Hajiya Jamila take fad'a acikin zuciyarta kenan"" YANZU dai samu waje ka zauna zanyi magana dakai mukhtar cewarta, to Mama ya fad'a yana riqe da hannun Zeenah yana dosar d'akin barcinsa da ita, saboda karya saketa Zakiyyah ta d'auketa ta fice, aikuwa saiji yayi Zakiyyah ta wawuri Zeenah dake hannunsa tana cewa' wallahi baka isaba Ina zaka da ita? Wato xaka je ka shige da ita d'aki ka kulle? Wallahi saika bani Zeenah ai ba Y'ar