Showing 81001 words to 84000 words out of 141223 words
Chapter 28 - RASHIN IYAYE Complete Document by Rabi'atu Muhammad Rabi'u Oum ARQAM.txt
ta faru oho? Dan kuwa tare suke dawowa! cikin Kuka take wannan maganar... lalläi fans Jimmai ko kwalaba batakai ta Sharri ba.
Data shiga ɗakin sai da ta tausayawa AKEELA ganin yadda Usman yai MATA filla_filla yai MATA raga_raga,alamu sun nuna gaskiya ba wannan karon ya Fara mu'amula da mace ba, kenan Usman neman MATA yakeyi? Ta jefawa kanta wannan tambayar! Lallai ALLAH yasa kar likitoci su gane hakan,dan kuwa Babu yadda ja'ace ƙaramin yaro kamar AQEEL ya aikata wannan aika aikar, guda nawa ma yake banda ALLAH yayi halittarsa mai sha'awarce Amma kamarsa wasu ma Basu balagaba, ga ɗan uwansa ma!
Tana waɗannan zantukan a zuci ta sakawa AKEELA kayan, wacce takenan kamar mara Rai ta jigata,shima AQEEL ɗin saka Masa kayan tayi,ko ganin halin dayake ciki baisa jimmai ta tausaya Masa, ta warware wannan Sharri da aka ƙwallafa Masa ba!
Tana gama saka musu kayan cikin Kuka tai waje,alamun zuciyarta Babu daɗi Akan abunda AQEEL yayi.
Tana fitowa falourn kuma ta samu doctor yana waya da Abbu inda shi doctor yazata jimmai ta faɗa Masa komai, dan haka yace " Alhaji gaskia abun Babu kyan gani yanzu dai sai munje Asibiti, dasu baki ɗaya, shima kansa baya. Hayyacinsa balle wacce yaiwa aika aikar, cikin ɗaurewar kai Ɗalhat yai wa doctor tambaya " ban gane abunda kake nufi ba, cikin girmamawa doctor Najeeb wanda hankalinsa bai kawo Ɗalhat baisan komai ba, "AQEEL yaiwa AKEELA gaikiya illa sosai, dan alamu sun nuna har dai da ta Suma kafin ya rabu da ita daga fyaɗen da yai MATA, tamkar saukar aradu ko fashi Ɗalhat yaji wannan zancen a kansa! kafin yadawo hayyacinsa kuma doctor yaci gaba da magana " dan haka zamu ɗaukesu zuwa Asibiti shi da ita, harma AKEEL dan shima mun sameshi a sume, ƙarshen zancen da doctor yayi ne ya dawo da Ɗalhat hayyacinsa, da ok kawai ya faɗa yana gimtse wayar, zuciyarsa da ƙirjinsa suna suwa wai AQEEL ne yaiwa AKEELA fyaɗe? To jimmai tana ina wannan abun yafaru? Meyake damun AQEEL ɗin? AKEELA zai wa Hakan?ta yaya ma? Inda ace Ɗalhat da tsautsayi ko ace yanada hawan jini da tuni yakai ƙasa zuciyarsa ta buga, Amma yanada ƙarfin zuciya, kuma sai addu'a yake a harshensa, najin wannan bala'i da ya tunkaro shi, wazai gayawa wannan magana ai abun kunya ne, sakayyar da AQEEL zai Masa kenan, Kullum nasihar dayake Masa kenan,ya kame kansa idan yaga bazai iya ba yafaɗa Masa shi zai Masa Aure bazai duba ƙanƙantar shekarunsa ba, Amma ina sai da AQEEL ya aikata Zina zinarma da ƴar uwarsa! innalillahi wa Inna ilaihi rajiuuun Allahumma ajurni fi musibati wa a ka lifni khairan minha! Adduar da Ɗalhat yake azuciyar sa kenan, da kuma tunanin AQEEL ɗin lallai ma. A haka har ya shige jirgi har zuwa tashin jirgin baisan a wane yanayi yakeba, gashinan ga kamarsa dai.
Dan haka doctor Najeeb ya Kira wani doctor daban, haka aka cicciɓi su AQEEL aka Sanya a mota zuwa Asibiti.
Koda sukaje asibitin abunka da kuɗi sai nan nan ale dasu, Amma kuma ganin halin da AKEELA take ciki yasa doctor da yawa zub da hawayen tausayi,dan doctor mace aka bawa ita, Usman yai aika aika,dan kamar ƙwarya haka aka ɗinke AKEELA, ALLAH ya kiyayeta da yoyon fitsari ko ƙwaƙwalwar ta ta samu matsala, cewar doctor Maryam tana duban abokiyar aikinta, dan sun san irin wannan matsalar tanasa Hakan, koda ake ɗinkin, sai da aka kusa gamawa sannan AKEELA tai wata mahaukaciyar ƙara tana fisge_fisge, sai da aka saka MATA Robar ƙara numfashi, kafin numfashin ya daidaita, sannan aka haɗa MATA da allurar barci, aka maƙala mata ƙarin ruwa,abun tausayi AKEELA dole ai ki galabaita! Yarinya ƙarama kamarki,ai miki fyaɗe fyaɗen ma na acire tausayi da imani a keta ki tun daga sama har ƙasa.
Ɓangaren AQEEL ma taimakon da aka Saba Masa Duk sanda irin Wannan matsalar ta faru shi aka Masa, kafin ai Masa gwaje gwaje, anan kuma Doctor ɗin sukasha mamakin abunda gwajin ya tabbatar, dan doctor Najeeb bai ɓoye musu komai ba Akan abunda yafaru tsakanin AQEEL da AKEELA ɗin!
Bayan doctor Najeeb ɗin yafito ne ya samu doctor Maryam, Akan ya kuma jikin AKEELA ɗin, sai sannan doctor Najeeb yai MATA bayanin abunda ya faru, fasta doctor tayi jin abunda doctor Najeeb ya faɗa MATA " wannan yaron ne ya aikata wannan aika aikar? Gaskiya da sake doctor daga ganin wannan Aikin babbane yayi shi, babban ma wanda yasan takan MATA, yasaba mu'amula dasu,Amma yaron nan ace farkon mu'amula da mace yai MATA haka, ina bazai iyaba, ai akwai Rashin sabo a harkar, da karancin shekarun sa ma ALLAH yasa in anbashi mace ya iya shigarta sosai, balle yai mata filla filla haka,ina da ja Akan wannan zancen, doctor Maryam cikin ƙaraji take zancen nan, doctor Najeeb yace "kwantar da hankalin ki doctor, gwajin dana fara Masa kenan, inda sakamakon ya fito, cewa tabbas yaron nan bai aikata komai ba,dan kuwa in da ya aikata kusantar bazai shiga halin dayake ciki yanzu ba, saboda azabar dayake ji ajikinsa, kusantar yarinyar zai rage masa wani abu, Duk da dai yakai limit, Amma kamar yadda in yasha magani daidai wannan matsalar ta sameshi Hakan zeyi, bazai Suma ba, Amma fa a sume muka ganshi, inda dai yakeyi in bai Sha magani ba,shima doctor Najeeb ya ƙarasawa doctor Maryam bayanin cikin jimami! Kafin yaci gaba dai MATA bayanin "lallai akwai lauje cikin naɗi kam, Amma abun da mamaki halin dana tsintsi yaran aciki, alamu sun nuna tabbas yaron shine yaiwa yarinyar fyaɗe,yanzu dai farfaɗowar yarinyar shine babban burinmu, Duk da muna da hujja muma! Doctor Maryam, ki kwantar da hankalin ki! in Sha ALLAH abun zaizo da sauƙi, mu jira Alhaji yanzu ya ƙaraso dan da muka gama waya dashi, yace mun yanzu zai tawo daga kaduna, sauke Ajiyar zuciya doctor Maryam tayi da doctor Najeeb ya ƙarasa MATA bayani, ai shikenan kawai tace shikam doctor Najeeb ficewa daga office ɗin yayi.
Shima dai AKEEL an samu numfashinsa ya daidaita allurar barci aka Masa, shima.
Jimmai dai sai kaiwa da kawowa takeyi alamun tana cikin tashin Hankali.
Usman wanda ya fice daga gidan, hankalin sa Duk da haka bai kwanta ba, na halin daya leƙa yaga AKEEL shima ya shiga, Amma kuma zuciyar sa fesfes tun da dai ya fita daga tarkon zargi, sai kuma idan ya tuna AKEELA inta farka asirinsa dai zai iya tonuwa,dan haka yake ƙissima Abubuwa da yawa a zuciyar sa game da itan.
Waya ya Kira uwar tasa dan yaji meke faruwa? Lokacin kuma jimmai tana kai kawo a Harabar asibitin ne ALLAH yaso ta ɗauko wayar tata, ko da Yake me zai hanata ɗaukowa, mutuniyar da Tashin Hankalin datake ciki na ƙarya ne, tana ɗaga kiran Usman yace MATA "ya dai maama meke faruwa? Ajiyar zuciya jimmai ta sauke sannan ta ce" gamu a asibi ma ai Alhaji nakira,nagaya Masa cewa ƴaƴansa Babu lafiya, shine ya turo doctor nan dai ta kwashe yadda akayi ta faɗawa Usman ɗin ajiyar zuciya kawai yayi ya kashe wayar! Miƙa yayi daga kwancen dayake, dan gidan wan ubansa ya tafi,inda ake riƙonsa shi da Shukra ƙanwarsa, wan ubansa bai taɓa Haihuwa ba shiyasa da Babansu Usman ya rasu shi ya ɗaukesu ya riƙe, tun suna yaran, Duk wata kyautatawa yana musu shida matarsa Basu rasa komai ba, ko da Usman yace zai koma gidan jimmai da Zama basuji daɗi ba,Amma haka suka haƙura..
Jimmai ta gaji da kaiwa da kawowa sai ta samu kujera ta zauna tai uban tagumi, a haka Ɗalhat ya iso asibitin, jikinsa a sanyaye gwanin tausayi,Duk wanda yaganshi yasan baya cikin Hankali da tunanin sa, Jimmai ta ganshi Amma sai ta nuna alamun ta zurme cikin tunanin abunda ya faru, sai da yazo kusa da ita ya dafa ta sannan tai firgigit, alamun ta dawo daga hayyacinta, ai Kuka ta rushe dashi " shikenan Ɗalhat AQEEL ya cucemu ya Ɓata Mana zuri'a, ya cuci AKEELA kamarsa ƙanwar sa zai lalata, wannan masifa dame tayi kama! Jimmai ta ƙarasa zancen cikin Kuka tana mai dafa kafaɗar Ɗalhat cikin tashin Hankalin data nemowa kanta na ƙarya, shi dai Abbu zuciyarsa shima ta tsinke ganin irin kukan da Jimmai takeyi! Lalläi AQEEL ya aikata abun ƙyama a rayuwarsa, wannan wane irin hali ne dashi, Amma fa ya cuce kansa kuma ya cuceni a matsayin mahaifinsa, kuma ya cuci ƙanwar sa, tur da halin ka AQEEL! Abunda Ɗalhat yake faɗa azuciyarsa kenan, lokacin tuni jimmai ta shige jikin Ɗalhat yana gursheƙen Kuka! Wanda Hakan yake daɗa tunzura zuciyar Ɗalhat ɗin da kuma ganin baƙin AQEEL ɗin................
Innalillahi wa Inna ilaihi rajiuuun kawai zance ni Oum ARQAM Amma Usman ya cuci AQEEL fa.......
ALLAH sarki AKEELA😭😭😭😭
Gaskiya jimmai batada imani fa abun yakai ga haka
Muje dai Zuwa next page yan Amana, Amma tsakanin wannan Page ɗin na 47 dana baya 46 bansan wanda yafi wani taɓa zuciya dasa Kuka ba Nikam wannan yafi ban tausayi🤧🤧 wancan ma yabani shima Amma wannan ya famamun mikin wancan🤧
✍️oum ARQAM ce ontop 🥰
2/24/24, 5:29 PM - Rãbi'atou Aminou {Oum ARQAM}: *RASHIN IYAYE*
(Babbar musiba)
Daga *Al 'kalamin✍️ Rabiat Amin (oum Arqam)*
*08128131163*
✍️ Marubuciyar...
*Komai Nisan jifa* 📚
*Hakan ba kuskure bane*📚
*_____________*
MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION📚🖊️ *(M°W°A)*
'Kungiyar d'aya tamkar da dubu masu Nazari da Aiki da ilimi burin 'kungiyar a koda yaushe shine ta fad'akar ta Kuma wa'azantar ta Nishad'antar da masoyanta🤙
*_____________*
*PAGE FOURTY EIGHT 48*
Tun shigowar Ɗalhat Asibitin Doctor Najeeb ya san shigowar tasa,dan haka ko lokacin da jimmai take wannan kukan bai ƙaraso wajen ba,sai da ya ƙaraso kuma sannan yai tozali da jimmai tana ta gursheƙen Kuka, tun daga sannan Doctor Najeeb jimmai kukan da take ya Fara tsaya Masa a rai! Ga kuma sakamakon gwaje_gwajen da akayiwa AQEEL aina matsalar take? Yasan dai Hajiya jimmai Ba Mahaifiyar su AQEEL bace? Amma kuma shaƙiƙiyar Mahaifiyar su ce! Abunda Yake hasashe Anya kuwa ? To in ba AQEEL bane waya aikata wannan mummunan Aikin? Tunanin da Doctor yake a Ransa kenan har ya ƙaraso wajen nasu!
Ɗalhat kuwa yana tsaye kamar dutse! Shi yasan abunda yake damunsa kawai!Amma wannan tashin Hankali haka! Aiwa ƴar ka fyaɗe! Abun Tashin Hankalin ma ace ɗan uwanta ne yai wannan Aikin! Ai ba kowane uba ne wannan abun zai sameshi zuciyarsa ta zauna lafiya ba! Shima kansa yanzu ya san inda za'a Auna jininsa za aga ya hau, dan lokacin da Doctor yake faɗa Masa abunda ke faruwa ba don ya Fara jero adduoi a Ransa ba,ai da tuni yaje ƙasa yanzu wani zancen ake ba wannan ba!
"Yallabai ka ƙaraso kenan! Doctor ya faɗa
Shi dai Ɗalhat Bai samu damar mayar da amsa ga doctor ba!
Dan haka doctor yaci gaba da magana, yallaɓai inason Muje office Yanzu,ka Kwantar da Hankalin ka dan ALLAH,kar wani abu ya same ka, komai da ya faru muƙaddarine daga ALLAH abun da ya faru ya Riga ya faru! Kema Hajiya kiyi Haƙuri ki daina kukan doctor ya ƙarasa maganar yana kallon jimmai da ke share hawaye dan lokacin tabar jikin Ɗalhat ɗin, ganin bai tofa tasa ba, taso a Ranta ya dinga tsinewa AQEEL ɗin,Amma shiru ita kanta bai lallasheta ba sai yanzu da doctor yazo yai magana.
Jiki sanyaye Ɗalhat yabi Doctor Najeeb office,kamar yadda ya buƙata, ruwa Doctor ya bawa Ɗalhat yasha, dan yaga alamu maƙogaronsa ya bushe da wannan tashin hankalin da ba'a saka Masa Rana! Ɗalhat Bai yi Musu ba karɓa yayi ya Sha ya sauke ajiyar zuciya!
Doctor yai gyaran murya sannan ya Fara magana!
Duk wani taimako da za'a yi wa yaran Duk anmusu, ita yarinyar tana CIKIN wahuyacin Hali, Amma an MATA Duk wani abunda take buƙata, yanzu haka an MATA ɗinki ciki da waje, ALLAH yasa ta farka Hankalin daidai kamar yadda Muke fata,Amma kam ƴar nan abun gwanin ban tausayi, Tunda doctor Najeeb yafara bayani Ɗalhat zuciyarsa take ƙuna, lallai ma yaronnan kamar sa shine zai wannan mummunan Aikin, lalläi yaro kana tare dashi ka haifeshi baka Haifi halinsa ba!
sannan shi kuma ɗan uwansa ba wata matsala bace Babba firgici ne yasa shi Suma, Amma yana farfaɗowa in Sha ALLAH komai normal ne, shi kuma AQEEL ɗin shima Duk abun...... Tunanin da Ɗalhat yake sai da doctor najeeb ya Fara magana sannan yadawo hayyacinsa, sai kuma da yaji ya sako zancen AQEEL ne ya ɗago a fusace ya zubawa Doctor Najeeb idanuwansa wanda sukayi kamar garwashi,Hakan yasa Doctor ɗin ƴar in ina ........ Sai kuma yaji maganar sa kar kayimin zancensa Anan Duk abunda zai sameshi ma ya sameshi, ko Alhakin ƴar uwarsa da na ɗan uwansa ganin abunda yayi yasashi Suma, ga Alhakina ai bazai barshi ba Ɗalhat ya ƙarasa maganar yana sauke ajiyar zuciya wacce daga ji ta Tashin Hankali ce
Tunda yafara magana doctor be katse shi ba, dan kuwa yayi dauriya shi kam dan ace danƙa yaiwa ƙanwar sa fyaɗe ai abunda yafi hakama zai faɗa,in wani mai raunin zuciya da tunani ne ai tsinewa ɗan zai Fara, da gaya Masa kalamai marasa daɗi, wannan ma ai kaɗan ne doctor Najeeb ya faɗa a Ransa!
"Yallaɓai yadda dai yaronnan yake shiga mawuyacin Hali a Duk sanda lalurar sa ta tashi hakane! Babu wani sabon al amari a tare dashi wanda za'a ce ya samu nutsuwar da wata mace!shiyasa ma dan gudun tantama muka Masa gwaje gwajen da zai tabbatar da Hakan, tun kafin ma muyi Masa allurar da ale Masa,kuma munga alamun ba shine ya aikata fyaɗen ba,Hakan shine ni da doctor Maryam muka shiga cikin jima mi da tararbin ya Hakan ya faru? Yallaɓai kuma ta ni ganau ba jiyau bane ganin halin da AKEELA da AQEEL ɗin suke ciki Babu wanda zai ce bashi bane ya aikata! Doctor Najeeb ya ƙarasa yiwa Ɗalhat bayani cikin sanyin murya!
Duk bayanin da doctor najeeb yakeyi Ɗalhat yana saurara har doctor yakai aya bai topa tasa ba! Amma kuma zuciyarsa ta shiga maimata maganganun da doctor yai Masa,to wanene ya aikata wannan mummunan Aikin kenan? Sai zuciyarsa ta shiga wasi wasi Akan Hakan! Doctor Najeeb ya cigaba da bayani " kuma yallaɓai ina Hajiya take wannan abun ya faru? Dan yarinyar zatayi ihun neman taimako kafin ƙarfinta ya ƙare, mun aunata munga Babu alamun an sheƙa MATA wani na juyar da Hankali kafin Hakan yafaru, kuma ma yadda doctor Maryam ta faɗamin,lokacin da yarinyar ta farka da Ihu ta farka da fusge fusge alamun lokacin da zata Suma ƙwatar kanta take Shirin yi, yallaɓai yanzu dai mujira farkawar yarinyar cikin Hankalinta, da shi AQEEL ɗin dan anan zamu daɗa tabbatarwa, da kuma AKEEL tun da shima maybe yaga wani Abu!
Duk bayanin da doctor Najeeb yakewa Ɗalhat yanaji Amma kuma zuciyarsa da tunanin sa ta bashi tabbacin lallai ne ajira su farfaɗo,Amma kuma in na AQEEL bane wanene ya shigar masa har gida ya ketawa ƴar da mutunci, sannan aka fake da Lalurar AQEEL aka jefeshi da wannan baƙin ƙazafin?koma dai wanene yasan kan Gidan! Kamar yadda doctor Najeeb ya faɗa ina Jimmai ta tafi wannan mummunan Aikin ya faru? Duk wani bayani doctor Najeeb yaiwa Ɗalhat, hakama ya kira doctor Maryam ta ƙara Masa nata, daga ƙarshe suka dinga Kwantar Masa da Hankali Akan karya sa abun a rai in Sha ALLAH ko wanene yai wannan Aikin ALLAH zai tona Masa Asiri, daga haka ya fice daga office ɗin, in da yasamu Jimmai a Zaune a reception tana ta sharar hawaye, sai yaji zuciyarsa tana wasi wasi Akan jimmai sosai!
Tana ganin Ɗalhat ya taho ta yunƙura tana mai kuma share hawaye na makirci,ta ƙarasa wajensa,shi dai har sannan bai mata magana ba, Meyake faruwa? Me sukace maka game da AKEELA da AKEEL ɗin? Dan ni bazan tambayi AQEEL ba kome ya faru shine sila,Yaro kamar bunsuru, ƙanwarka zaka Haikewa duk cikin Kuka jimmai take maganar kai kace gaske ne!
Cikin baƙin ciki Ɗalhat yace koma mene ya faru kina ina? ɗuf kukan da Jimmai take ya ɗauke jin tambayar da Ɗalhat yai MATA! Sai tafara in da in dar kare Kai,fita kikayi kenan baki gayan ba? Ai shikenan Zanyi bincike Akan komai daya faru a Gidan, Ina da me gadi Zan tambaye shi komai, kuma Doctor sun mun bayanin cewa Ba AQEEL bane ya aikatawa ƙanwarsa fyaɗe ba, Kinga kenan akwai lauje cikin naɗi, wanda yasan sirrin gidan mune ya aikata Hakan, kuma kece Kika ba da ƙofa inda baki fita ba Babu ta yadda Hakan zai faru! Tashin Hankali wanda ba'a saka Masa Rana ga Jimmai! Duk bayanin da Ɗalhat yai MATA taji shinenan asirin Usman zai Tonu! Ita ma ta shiga uku kenan, sai ta Fara magana cikin karaya " kayi haƙuri daban fita ba Hakan bazai faru ba, Amma kuma nacewa ba AQEEL bane ina mamakin wane? Babu mai shigo Mana gida gida, kuma fa Yadda na ga halin da AKEELA da AQEEL suke ciki abun akwai mamaki fa, Amma tun da kace zakai binkice Shikenan! Jimmai ta ƙarasa maganar da alamun tausayi! shi dai Ɗalhat Bai kula zancen da Jimmai takeyi ba,Duk haushin ta yakeji,na yadda idan ba dan ta fita ba ai da ba ta yadda Azzalumin da yashigo ya cuci yarinya ƙarama zai samu da ma ba!
Ɗalhat dai yana zaune a kujera yayi jugum yana jiran tsammani,yayin da Jimmai take kusa dashi taketa soke burutsun ta! Yana tsaka da tunani Usman ya Faɗo Masa a rai dan haka yaiwa jimmai tambayar da ta Lisa tsarwatsa MATA kwanya
"Ina Usman yake wannan abun ya faru? Ban ganshi ba? Inji Ɗalhat ya na kafe Jimmai da Ido, Amma a Ransa baya tunanin Usman zai aikata Hakan,kawai dai tambayar yai MATA, ita kuma dayake Babu gaskia shine ta razana ta tsargu, kafeta da idon da yayi kuma na mamakin daga yace ina Usman shine ta tsargu!
Ai tun washe garin da kayi tafiya shima ya tafi gidansu, wai babansa (wan baban su)bai ji Daɗi ba shine yaje gurinsa, Oh shikenan,Amma baki gayan ba ai shikenan.
Suna wannan tattaunawar Zuciyar Ɗalhat Babu daɗi, yanzu AKEEL da AQEEL da AKEELA su farka shine burinsa!
Zuciyar jimmai itama haka,Amma ita Rashin daɗin Zuciyarta na son zuciyarta ne da zalunci, ɗan ka yaiwa yarinya ƙarama fyaɗe har ka rufe abun,kuma