Showing 78001 words to 81000 words out of 141223 words

Chapter 27 - RASHIN IYAYE Complete Document by Rabi'atu Muhammad Rabi'u Oum ARQAM.txt

kuma yaga Hakan ya gagara yai Masa magana,a halin yanzun zai masa Auren kuma yaci gaba da karatunsa,to Alhamdullillahi Babu matsala da Hakan,yama ƙudirce a ransa shikam karatu zaiyi Aure kuma ba yanzu ba, shida ɗan uwansa zasuyi Aure rana ɗaya ma, kuma ƴan biyu kamarsu, ko yaya da ƙanwa zasu Aura suna da wannan burin a ransu.


Karatunsu ma Sha ALLAH,sun Zama samari komai nasu iri ɗaya yake tun daga kayan sawa,kamanni abunda ya banbantasu wannan glass da Jimmai tai masa sanadi,sai kuma halaye kowa da kalar nasa, AQEEL shi shiru-shiru ne dashi,hakanan baya magana da kowa idan ba ɗan uwansa ba,abokai sai dai ayi zaman kurame,ya zauna yayi shiru, saɓanin AKEEL akwai surutu ga faran faran da mutane, Abokai kam gasunan, kowa nasane.


Usman ya samu jimmai "Mamah nidai inason AKEELA, dagaske kuma nakeyi a aura min ita" Jimmai zubawa Usman idanu tayi kawai tana kallonsa sai da yakai aya sannan tace "wannan abun Bazai yiwu ba,bazaka Aureta ba,Akan me!kar nakuma jin wannan zancen nan abakin ka, me zaka aura kayi da wannan yarinyar? So nake ka samu ƴar manyan mutane ka Aura,Amma in ƙudine ai gani ina Auren mahaifinta,anason samun ci gaba ai "Shikenan Mamah angama,bazan kuma zancen ba kinji" yawwa ɗan albarka,nasan ai bakason ɓacin rai na ..dama Usman bawai son gaskia yakewa AKEELA ba, Aurenta zaiyi daga zarar ya samu abunda yakeso a jikinta ya rabu da ita ya sake ta, sha'awar ta dama ce take damunsa,kuma yaga yarinyar bazata bada haɗin kai ba.


"Lallai maama ai da kin amince da Aurenta gareni,dama ɗanɗanawa zanyi naji, yanzu kuwa kome ne zai faru sai dai yafaru, nida yarinyarnan mai hanani ɗanɗana ta sai ALLAH!Usman ke wannan tunanin a zuciyar sa, yana kuma juyi a gadon da yake kwance, yana ƙissima Abubuwa marasa kyau da Rashin daɗi ga AKEELA marainiyar ALLAH.





Jimmai tana fice ficenta na yawan asirinta da mallaka to kusan kullum bata gida,shikam Usman dama ya samu gida,kamar Gidan ubansa, baya Zuwa ko ina yaci ya kwanta, sai kalle kallensa na banza, shine aikinsa a Kullum.


Yau ma kamar kullum jimmai ta fice Usman ne kaɗai a cikin Gidan,Duk suna makaranta.
Ya baje kolinsa sai kallen kallensa yake na Rashin mutunci, gaba ɗaya ya hau network ya fice a hayyacinsa, bashi da buri sama da yasamu Abar ɗebe kewa a daidai wannan lokaci!


Kwatsam sai ga AKEELA ta dawo daga makaranta, tana shigowa falourn ta ga Usman yana kwance a kan sofa, ya kama pillow ya rungume sai wani juye juye yakeyi, ga vedios ɗin dayake kallo ya haɗa da bluetooth sai kauɗin Ƴan iskan ke tashin abun ba bu kyan gani,
Usman dama yasan jimmai bazata dawo da wuri ba, AKEELA kuma bata kaiwa 4:00 take dawowa daga school,Abbu(Ɗalhat) kuma yayi tafiya yau kwanan sa uku,sai jibi zai dawo,su AKEEL kuma ana school, suna extra lesson, saboda exam ɗin da zasuyi, basa dawowa da wuri wataran sai magrib shiyasa a masallacin suke tsayawa su ɗau karatu a wajen liman ɗin, shiyasa Usman ya tamawa wannan ranar, Jimmai ta ga Abbu baya gari sai takai dare sosai, ga gida ba bu Ƴan aiki,sai mai gadi kawai shi kuma yanacan bakin aiki.


Ai da wani mugun sauri ya tashi jin sallamar AKEELA ɗin, yatawo gadan gadan, tsuntsu daga sama gasasshe kenan, ai kuwa kano AKEELA yayi abunka da namiji, Duk shure_shuren sa take bai sauke ta ba, sai da ya dangana ga sofa ɗin a kan cinyarsa ya ɗorata, sannan ya ɗauko wayarsa vedios ɗin, daya kunna yaketa ƙokarin sai AKEELA ta kalla,ai kuwa taƙi kalla,Duk da yai mata kamun mage da ɓera,ko juye_juyen da takeyi ta kasa, ƙarfinta ya ƙare,ita dai AKEELA runtse idanu takeyi,alamun bazata kalla ba "ok shikenan yarinya tun da bazaki kalla ba shikenan, matsalar kice inda kin kalla sai rage miki wani Abun, dan kuwa yau me hannani Cika burina a kanki, ban ganshiba,dole na kashe ƙishirwa ta,na mayar da yahu na! AKEELA kam bata jinsa ma tashin hankalin da take ciki yayi yawa,yarinya 14_15 years mai ta sani, banda ALLAH yakawomu wannan zamanin, ihun kuka take na neman taimako Amma ina Babu maceci, Usman dai saiya cika burinsa a kanta tun a falourn yafara lallatsewa AKEELA jiki kafin ya dangana ga ɗakin su AQEEL da ita, tuni dama ya kashe vedios ɗin.


Duk ihun da AKEELA take haka Usman yasa Rashin imani, ya keta mata mutuncinta, yai MATA fyaɗe, na Rashin mutunci wanda Duk wanda yagani sai yayi kuka,sai da ya kammala komai Babu imani da tausayi ya barta a wajen hakanan,sai kuma sannan tsoro ya kamashi na yanzu ya zaiyi?






__________ Yau da ma tunda AQEEL ya tashi, yakejin yanayinsa yana sauyawa,da aziminsa da ma ya tashi, Amma sai a Hankali, har sukaje school wajen magrib sukayi sallah, AQEEL yasha ruwa ai sai abunda yake bujuro Masa yafi na da(irin masu sha'awa tabbas hakan yana faruwa dasu koda suna azimin yana rage sha'awa sosai,Amma kuma suna buɗa Baki sai sha'awar ta bujuro musu,Duk da Hakan dai da sauƙi yafi basuyi ba) Hakan yafaru da AQEEL, dan uwansa yashan yanayinsa, dan haka yace Masa" jarabuna kaje Gida kawai,yau ɗaukar karatu bazai yiwuba ba,ana yanayi, kaidai bro kashige su kamar ka sai jaraba, aje Gida asha magani kuma,kafin asamu relief! cikin shakiyanci AKEEL ya faɗi maganar, shi dai AQEEL bai kula shiba, takansa yakeyi,Amma sau tari yana kare kansa, su biyo sukayi niyyar tafiya gida kawai sai AQEEL yace "baza ayi hakaba bro, ka ɗau karatun in yaso sai ka ƙaramin, cikin dauriya yayi maganar! Kana ganin ba matsala zaka iya ƙarasawa gidan "ea Babu matsala cewar AQEEL,Amma gaskia baza kayi driving ba kabarmun machine ɗin kahau abun Hawa,saboda yanayinka! Cewar AKEEL "to shikenan sai ka tawo Inji AQEEL.


Hakan kuwa akayi AQEEL ya hau abun Hawa zuwa gida, yabar AKEEL a masallaci ɗaukar karatu,liman yace ina ɗan uwan naka yau? AKEEL yace bai da lafiya yayi gida!liman yace ALLAH ya sauwaƙe.


Lokacin da AQEEL ya ƙarasa Gida,yanayinsa yayi tsanani, shi kuma Usman tuni ya ida nufinsa Akan AKEELA yayi shiru yana tunanin mafita a gareshi, ya kawo kai kenan zai fito daga ɗakin sa,sai yaga AQEEL yana tangaɗi, ya shigo falourn, ai da sauri ya lafe a jikin labule, yana ganin AQEEL ya shiga ɗakin su ya biyo bayansa, abunka ga ɗan Iska yana ganin yanayin AQEEL yasan me yake damunsa, kuma dama sau tari yasan indai irin wannan yanayin ya samu AQEEL ɗin matuƙar bai Sha maganinsa Akan lokaci ba sumewa yakeyi, ya fice a hayyacinsa, sai anje ga likita,an Masa allurai da ƙarin ruwa kafin yadawo hayyacinsa, dan haka yana ganinsa yai hamdala ga ALLAH ga mafita, cikin Ruwan Sanyi!cewar Usman acikin zuciyarsa


shi AQEEL ta kansa yakeyi burinsa Yaje ga maganinsa yasha, ko kula da AKEELA dake kan gadonsa, cikin mawuyacin Hali bai ba idonsa ya rufe, kafin Yaje durowar da maganin sa yake ciki domin ya ɓalla yasha abun yaci tura, tuni numfashinsa ya ɗauke, in irin haka ta faru AKEEL yana kusa dashi shine mai ɗauko Masa,maganin cikin gaggawa ya bashi, Duk da haka sai yasha baƙar wahala kafin yadawo normal, yanzu kuma yabarshi wajen ɗaukar karatu, Usman yana ganin haka da sassarfa ya ƙaraso ga AQEEL ya tallafo shi jikinsa, bai kai ƙasa ba, lokacin tuni har ya Suma, dan haka ba bu Ɓata lokaci Usman ya shiga cirewa AQEEL kayan jikinsa yaba ɗaya, sannan ya ɗauke shi ya ɗorashi Akan gadon kusa da AKEELA ta yadda Duk wanda yagani yasan tabbas shine tai mata wannan fyaden, jikin dake jikin AKEELA Duk yabi jikin AQEEL dasu inda yazama dole ya shafa, abundai ba bu kyan gani, Duk wanda ya ga wannan yanayin da AQEEL da AKEELA suke ciki, lallai zai tsinewa AQEEL ne musamman ace Abbu ko AKEEL yagani.


Sai da Usman ya saita komai sannan yayi godiya ga ALLAH, cikin dariya yace" Shikenan mafita tazo min Babu wanda zaice ba AQEEL bane ya aikatawa ƙanwarsa wannan Aikin, Duk wanda yagani tabbas zai tsine Masa albarka, na kawar da ƙishirwata cikin salama Babu wanda yasani, ita kuma yarinyar nasan yadda zanyi da ita ta yadda bazata ce nine na aikata MATA wannan Aikin ba, kai gaskiya Nikam Usman inada Sa'a a duniya, gwanda ma maama da baki amince na aureta ba, ya ƙarasa maganar da kuma tunanin Ina AKEEL yake? meyasa AQEEL shi kaɗai ya dawo gida, kar dai tare suke, yana ganin abunda ya aikata, zuciyar sa kuma ta kawo Masa wannan tambayar, aikuwa juyowar da zaiyi yaga mutum a bayansa da Alamun Duk zantukan da yayi da abunda ya aikatawa AQEEL shi mutumin yaji, a razane ya ɗago idanuwan sa domin yaga wane yaga abunda ya aikata da jin zantukan da yayi, ai yana ɗagowa sukayi Ido huɗu da ...............




Lallai akwai cakwakiya fa


Shin fans wa Usman ya gani? Da alama dai asirinsa ya tonu fa


Gaskiya Usman Babu imani fa,


Ko da yake ta ina zai Imani, Jimmai ce fa mahaifiyarsa


ALLAH sarki AKEELA tabani tausayi sosai






Ya Rayuwar waɗannan Ahali zata kasance da wannan ƙaddara ta rayuwa da suka gamu da ita




Muje zuwa fans


Inada tambaya....


TSAKANIN SU HADIYYAH DA SU AQEEL SU WANE SUKA FI SHAN WAHALA? DA KUMA GANIN MARAICI?




✍️oum ARQAM ce ontop 🥰
2/18/24, 1:04 PM - Rãbi'atou Aminou {Oum ARQAM}: *RASHIN IYAYE*
(Babbar musiba)




Daga *Al 'kalamin✍️ Rabiat Amin (oum Arqam)*


*08128131163*


✍️ Marubuciyar...
*Komai Nisan jifa* 📚
*Hakan ba kuskure bane*📚




*_____________*
MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION📚🖊️ *(M°W°A)*


'Kungiyar d'aya tamkar da dubu masu Nazari da Aiki da ilimi burin 'kungiyar a koda yaushe shine ta fad'akar ta Kuma wa'azantar ta Nishad'antar da masoyanta🤙
*_____________*






*PAGE FOURTY SEVEN 47*




Jimmai ce a tsaye ta kafe ɗan nata da idanu, alamun tagama jin Duk abinda ya aikata, bai gane a wane yanayi Mahaifiyar tasa take ba, dan haka ya matso cikin firgici! dan ALLAH Maa... Dakata fito Daga cikin ɗakin ko sai wani yazo ya ganka asirinka ya tonu! Cewar jimmai! Aikuwa cikin azama Usman ya biyo maaman sa zuwa falourn, sai ta zarce ɗakinta Usman ma binta yayi,
Sai da suka ƙule cikin ɗakin, sannan ta zauna a gefen gado shima Usman ya zauna
! Abunda ka aikata kenan ko? ALLAH ya shirya mun kai, Yanzu kuma shi AQEEL ɗin taya kai Masa Hakan, ko tsoron ALLAH ko kunya ya bawa uwarsa labarin yadda AQEEL ya shigo da komai da komai, Ajiyar zuciya jimmai ta sauke! Sannan tace yanx kuma inda AQEEL ɗin bai shigo ba fa? Ai maama Hankali na ya tashi lokacin na rasa yadda zanyi da ita, Yanzu dai shikenan ka ga cikin ruwan Sanyi ALLAH ya kuɓutar dakai, ubansu ba abinda zaiyi akai ai dai ɗan sane ya aikata bazaiso abun ya fito sarari ai abun a tsinewa yaron ne ka lalata ƴar uwarka cikin ummanka! "Aikuwa maama ALLAH ya rufan Asiri ai cewar Usman yana sauke ajiyar zuciya..... Lallai wannan Daga ɗan har uwar basuda imani, ko halin da AKEELA take ciki bai damesu ba,balle AQEEL wanda akama Sharri,wanda shima yana cikin mawuyacin Hali na taimakon.
"Innalillahi wa Inna ilaihi rajiuuun! Usman an kashe maciji ba'a sare kansa ba, idan ita yarinyar ta farka ai zata faɗi ko wanene! Jimmai ta faɗa tana dafe kanta alamun wani abu ya sameka bakayi tsammani ba! A firgice Usman ya ɗago fuska cikin jimami ya Lallai Maman tasa! Ƙwarai kuwa maama mene mafita kenan, tana farkawa na shiga uku dam sai ta faɗa me kike tunanin zai faru dani har dake ma?jimmai dai ta kasa magana hannunta dai yana kanta har sannan tayi suman wucin gadi... Kuji fans anya jimmai tana da imani kuwa, ɗan ka yaiwa ƴar Ƙanwar ka fyaɗe irin Wannan na Rashin imani, sannan ɗan ki ya ƙallafawa ɗan uwanta Duk baki shiga tashin Hankali ba sai asirin ɗan ki da zai Tonu shine fargabar ki, Daga ita har ɗan basuda imani, ko ya ɗa yake ai bai uwa bama!dan dai suka zauna cikin jimami mafita a garesu, ƙarshe jimmai harda cewa dan nace bazaka Aureta ba shine kai MATA Hakan, ai da kasani shammata kayi ko kasa mata wani abu wanda nazata san Kaine kai MATA ba.. fans jimmai tanada imani kuwa? Ko da abunda ka shuka!?
Haka dai suna saƙawa suna kwancewa akan mugun nufinsu ta yadda zasu samu mafita....






_____________ Tun da AQEEL ya tafi sai kuma Hankalin AKEEL ya tashi ta ganin a halin da ɗan uwansa ya tafi gida! Dan haka karatun kawai yajishi ne Amma bai ɗauka ba, hankalin sa ya rabu Biyu, ɗaya anan ɗaya acan, sai da yayi tunanin" infa AQEEL yakai wannan matakin daƙar yake kaiwa yasha maganin nasa ma, to inya ɗauko maganin wazai bashi ruwa yasha? Jimmai tana wajenta, ko tana nan ma ba kulashi zatayi ba, Usman ai basa shiga harkar sa gwanda ma shi AKEEL ɗin suna ɗan magana sallama da maiamancin Hakan,Amma shi AQEEL ko kallonsa bayayi, tun lokacin da yai Masa tayin kallon fina_finan banza,dan ragewa kansa damuwa... ALLAH sarki AQEEL kamar yasan Usman zai Masa wannan mummunan sharrin, da lalatawa ƴar uwarsu Rayuwa! Sai da yayi wannan tunanin ne kuma bai kammala karatun ba ya bawa liman uzirinsa Akan zaije gida yau, ya duba halin da ɗan uwansa yake ciki.


A haka ya hawo machine ɗinsu yayo gida, yana tafe yana wasi wasi a zuciyarsa...Dan uwa kenan kamar yasan meke faruwa da ɗan uwansa AQEEL da kuma ƙanwarsa AKEELA abune marar daɗi,a haka har ya ƙaraso cikin gidansu mai gadi ya buɗe Masa gate, Sannu da dawowa yai Masa sannan malam sallau ya tambaya ina ɗan uwan naka? AKEEL yace ya rigani dawowa bayajin daɗi ne!oh lokacin na zaga kenan bansan yadawo ba,kai Masa Sannu, malam sallau a zuciyarsa yana tausayawa AQEEL dan kuwa yasan abunda Yake damunsa, sau tari a gabansa ake fita dashi in ciwon yatashi, ko likita yazo dubashi har gida, sau tari ma sai an dangana ga Asibitin ake samun lagon abun.




Jimmai da Usman suna tufka da warwara sukaji alamun machine ɗin su AKEEL, sai sannan ma sukasan AQEEL shi kaɗai yadawo gidan, kenan ciwon ne yadawo shi gida, cewar jimmai tana kallon Usman, Ea gaskia maama saboda gaskia ko da yashigo alamu sun nuna baya hayyacinsa sosai ai!
Yi Zamanka anan idan ya shigo sai ka sulale ka fice alamun baka gidan ma, Amma kuma idan ƴar nan ta farfaɗo ta faɗi wannan maganar akwai matsala!


A Hakan AKEEL ya shigo falourn yai sallama Duk da yasan daqar zai samu wani a falourn dan Hakan ya nufi ƙofar da zai sadasu da ɗakin barcin su, yana shiga idansa ya hasko Masa AKEELA da AQEEL a Wannan halin da Usman ya sakasu, bakinsa yana rawa "B....ro m.e.z.a.n g.a.n.i h.a.k.a! yana dumfarar ƴan uwansa Hankali a tashe, ai ƙara kawai ya saki lokacin daya ƙarasa kusa dasu, ganin halin da AKEELA take ciki da shima AKEEL ɗin, zuciyarsa wani irin bugawa tai baisan lokacin daya saki wata ƙara mai rikitarwa ba yakai ƙasa a sume!
Daga Usman har jimmai sun dan meyasa AKEEL wannan ƙarar, dan haka taiwa Usman nuni Akan yafita daga gidan,aikuwa da gaggawa yafice daga gidan ko tausayi ko ya duba halin da AKEEL ɗin yake ciki irin wannan ƙara da yayi ta firgitarwa wanda ba'a ɗayan biyu har mai gadi yajita,Duk da zurfin gidan!
A gaggauce Jimmai ta shigo ɗakin nasu samu tayi shima AKEEL a sume yake alamu sun nuna wannan abun ya bugeshi kenan, ina kuma ga Ɗalhat inda shine yagani ko yaji labarin abunda AQEEL ɗin yayi!
Cikin gaggawa ta ɗau waya ta Kira Abbu cikin Kuka tace Masa AQEEL da AKEEL Basu da lafiya, sannan itama AKEELA Hakan ai Ɗalhat gigicewa yayi jin ance iyalinsa Babu lafiya yaji jimmai tana Kuka dan haka zuciyarsa da ruhinsa suka tabbatar Masa abun babba ne, bai tsaya tambayar meya samesu ba kawai yace MATA gashinan, kunsan Ɗalhat da son ƴaƴa, dama ba wani nesa sosai yai ba, magana ce Akan foundation ɗin da yakeso ya kafa, shiyasa kwana biyu baya Zama, yau yana kano gobe yana wannan gari, so yake foundation ɗin sa ta kafu a gida Nigeria, bawai iya kano ba so yake ta ko ina ya taimakawa marasa shi da marayu, suna gama waya da Jimmai ya Kira likitan da yake zuwa dubasu idan basuda lafiya, Akan Yaje gida ya duba yara, basuda lafiya,shima gashinan dawowa.


Abunka da kuɗi nan danan yasamu ticket jirgin da zai tashi daidai lokacin Babu Ɓata lokaci ya ɗauko hanya, to dama yana kaduna ne.
Ɗalhat ya Kira Jimmai yace MATA ta kwantar da hankalin ta ga doctor nan ya turo ya dubasu, har sannan makirar Kuka takeyi, dan haka Hankalin sa yakuma tashi, ko da Ɗalhat yacewa jimmai ga Doctor nan batayi wani abuba Akan ta gyarawa AKEELA da AQEEL jikinsu, dan bai kyautu a gansu a haka ba, Amma ina sai tayi funfurus,a zuciyarta gwanda doctor yagani yazama shaida ai shima,ko da AKEELA ta tashi tace Usman ne ai doctor zai ce yazo yagani shima.
Tanajin Horn da buɗewar gate tasan Doctor ne ya ƙaraso, dan haka sai ta zauna a falourn tana sharar hawaye! Doctor Najeeb yana shigowa ganin jimmai na Kuka yace MATA meyake faruwa! Cikin Kuka ta nuna ɗakin AQEEL tana magana " doctor shiga kaga ɗanyen aikin da AQEEL yai wa ƴar uwarsa! Abunnan yabani tsoro da mamaki, fita nayi shine fa ita shigowa na tsintsi wannan bala'in kai duniya ina Zaki damu! Ɗan uwa ya nemi ƴar uwarsa, ya lalata MATA rayuwa, yai MATA fyaɗe! yarinya kamar AKEELA guda nawa take, shi kansa AQEEL ɗin guda nawa yake, Nikam Jimmai naga Rashin imani Yau! Maganganun da Jimmai take kenan, kan doctor kullewa yayi jin wai AQEEL yaiwa AKEELA fyaɗe garin Yaya kenan, yana wannan tunanin ya shiga cikin ɗakin,ai da gaggawa ya fito, ƙirjinsa yana harbawa, lallai wannan yaro yacika marar kunya da tausayi ƴar uwarka zakaiwa haka, fitowa falourn yayi inda Jimmai take sharbar kuka, doctor cikin jimami yace "Hajiya gaskiya wannan abun bana gida bane sai munje ga Asibiti, Yanzu shiga ki sittirawa yarinyar jikinta shima Hakan,dan kuwa yana cikin wani Hali, cewar doctor yana ɗaukar waya dan yayi Kira! Cikin Kuka jimmai tace "ga kuma ɗan uwansa a ƙasa a sume, alamu sun nuna shigowa yayi yaga wannan ta'asar da ɗan uwansa yayi shine ya sume, ko ya Hakan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login