Showing 132001 words to 135000 words out of 141223 words
Chapter 45 - RASHIN IYAYE Complete Document by Rabi'atu Muhammad Rabi'u Oum ARQAM.txt
me ankira ƴan jarida Suna jin ta bakin mutane.
Mutanen gurin sunyi niyyar kashe Alhaji Hamza Amma ina mutane masu hankali da ƴan Sanda day sukazo wajen Suka hana haɗe da tunasar dasu Akan dole aje dashi ya mayar da ƴaƴan inda ya satosu!
Acikin motar ƴan Sanda aka saka Alhaji Hamza wanda yaji jiki a hannun mutane dan kuwa sun cire Masa haƙoran gaba,ga raunuka aka fa sauran sassan jiki,A haka har sukaje inda ya ɗauki ƴaƴan mutane!
"wanda ya dauka a ƙofar gida kuwa koda akaje unguwar tuni uwar yaro ta fita a hayyacinta sai Kuka takeyi tayi nema harta gaji,ta tambayi yayar ɗan itama Dana wayo ba tace wasa yafito bata ganshi ba! Ta fitar da rai sai ga ƴan Sanda sun kawo mata yaronta,wanda yaci Kuka ya ƙoshi,Mata sai godiya takeyi haɗe da godewa ALLAH daya dawo Mata DA ɗanta lokacin data fitar da Rai, mutanen unguwa sai tsinewa Alhaji Hamza ɗan mafiya sukeyi.
Haka suka ƙarasa inda ya ɗauki ɗaya yaron shima dama ba nisa, iyayen yaran ƙawayene ma,tare suka rufa nema,gashi ƴaƴansu sun dawo sai Hamdala, da ALLAH wadai da Alhaji Hamza akeyi.
"Office ɗin ƴan Sanda aka koma da Alhaji Hamza ai Masa tambayoyi!
Kafin kace me Gari da duniya baki ɗaya tasan Abunda Alhaji Hamza yayi,da wanda suka sanshi da wanda Basu sanshi ba,masu saninsa ma sunfi yawa sai ALLAH wadai ake Masa.
"Mansurah kam a Facebook taga abunda yafaru da mijinta,dan Haka hankalinta yai matuƙar Tashi,data tuna da sharaɗin dodo Lokacin da zata saka Alhaji Hamza acikin ƙungiya, """mindiiiir Zaman sisoooo cikin ƙungiya zamanki cikinta! matuƙar yafita kema kin fitaaaaaa!
Nan danan Wasu ƙuraje suka fitowa Mansurah acikin jikinta,manya manya take suke fasewa sai wari kuma,bakin Mansurah ya karkace yana zubar jini ga tsakiyar kanta kuma yayi ƙa toton rami tsutsotsi wane Miliyan sai Shan ƙwaƙwalwarta sukeyi! Duk Wannan azabar mansurah haɗe take jinsu cikin abunda baifi minti Biyar ba.
"Alhaji Hamza sai raɗaɗi yakeji ajikinsa,ƙuraje sun fito Masa Duka cikinsa,sai ruwa me ɗoyi suke fitarwa! Ga shima again tsakiyar kansa tsutsotsi sun cika Masa,Wani abun mamaki ko guda ɗaya bata faɗuwa,sai wutsul wutsul Suke abun ƙyanƙyami!
Sai da D.p.o yazo yabada Umarnin a ɗauki Alhaji Hamza zuwa gidansa domin Ayi screening ,tunda bashi da Imani baza'a Rasa wasu a gidan ba, gaba ɗaya Ma'aikan gidan ƴan kingiyarsu ne Dan haka akayi ram dasu Babu wanda aka bari.
Aka Shiga cikin gidan kuma,shashen Mansurah suka Fara Shiga Nan sukaga abun tsoro da Al'ajabi ganin Irin halin da Alhaji Hamza yake ciki Itama Matara irinsa take Ciki Kenan,mugun abunsu ɗaya itama ram akayi da ita zasu fita daga gidan ne,Dan kwata kwata ba'a bi takan Sa'adatu ba wacce aka killace Wani ɗaki can taban.
Alhaji Hamza ne yana kukan nadama da dana sani Akan shigarsa ƙungiya yanawa Mansurah ALLAH ya isa,yake faɗar Duk wasu mugun Abu dayayi day haduwarsa da Sa'adatu da abunda yai MATA.
Babu Shiri aka je inda Suka killace Sa'adatu aka lalu bota,wacce tana Zaune kawai taji ta motsa kafafunta!DA hannayenta!tana yunƙurawa sai ta miƙe,abun Al Ajabi kuma shine jinin dake zuba ajikinta ya ɗauke, Amma fa sai Wari takeyi na jinin! Rashin ƙarfi da yunwa yasa takasa mikewa Daga wajen!
Zuciyar Sa'adatu sai Mamakin wannan abu daya sameta tunda ta Auri Alhaji Hamza takeyi,da kuma hulaƙanta daya keyi!tana waɗannan tunanikan Ƴan Sanda suka shigo ɗakin!
Dama da 6an Sanda mata suka tawo Suna toshe hanci suka ɗauko Sa'adatu suka Fito Da ita Daga ɗakin !
Sai ga ta razana ganin Halin da Alhaji Hamza yake ciki! Ga mansurah itama gaba ɗaya fatar jikinsu ta zagwanye Kamar waɗanda suka kone ga ƙuraje DA Ruwan dake zuba ga Wari!
Alhaji Hamza yana Arba da Sa'adatu yafara kukan nadama! Yana neman yafiyarta da Duk irin abunda yai MATA,itama Mansurah Kuka tafara tana neman yafiyar Sa'adatu ɗin na Kwantar da ita datayi!
Itadai Sa'adatu jiki Babu ƙwari sai Jin maganganun da Alhaji Hamza da mansurah takeyi sun razanata ba kaɗan ba, lalläi ma Ashe ALLAH ne ya ceceta, wai taga ƙarshen kwaɗayi ai sai Kuka takeyi.
Ana tsaka da wannan ne sai gidan gaba ɗaya kuma yafara girgiza haɗe da wani ihu Mai razanarwa, ƴan Sanda musamman Matan ciki gudu suka Fara!take suka Kira ƴan jarida haɗe da kunna waya Suna ɗaukar vedio saboda wannan Abun abun Al Ajabi da jimami ne!
Kafin kace me gidan Alhaji Hamza makota da sauran Jama'ar gari sunwa gidan tsinke,Bayan an ɗauki Sa'adatu zuwa Asibiti wanda ta jima da suma!
Take D.p.o ya Kira Sheik ARQAM😘 (shahararren malamun Sunna ne wanda ya ƙware wajen Tafsir a radio da television, yana yana tsage gaskia da ƙarya,har shugabanni bai barsu ba,gaskia fadarta yakeyi) Nan d.p.o ya faɗawa Sheik ARQAM abunda Ke faruwa,wanda yasan yanzu ma yasani.
Aikuwa Babu ɓata Lokaci Sheik ARQAM shida muƙarrabansa sukaiwa gidan Alhaji Hamza tsinke. Kuma Babu ɓata Lokaci suka Fara raira karatun Al kur ani Mai tsarki,saboda shine mafutar wannan girziga da ihun d ake a gidan Alhaji Hamza ɗin.
Lokacin Alhaji Hamza da mansurah kam jikinsu fa yafara zagwanyewa Kamar yadda kyandir yakeyi idan yanacin wuta
" Mindiir dama mun faɗa Miki ai kaɗan ma Kika Fara Gani! Wata katuwar murya ta faɗa wacce ba'asan Daga ina take ba, haɗe da cewa "Kaima sisoooo kasan sharɗinmu Dan haka Daga Yau Daga ku har mu Aljani gohliiiiiiiiiiii zaiga bayanmuuuuuu!
Cike da ƙaraji wannan muryar take Faɗi! Shikam Sheik ARQAM da muƙarrabansa sai cigaba da karatun Al kur ani Mai tsarki sukeyi mutane sunata kabbara, Daga can wata wuta ta Tashi tanaci Kamar ana zuba fetur! Tanaci Bal bal Bal!sai gashi ta ɗigo Akan Alhaji Hamza aikuwa sai ya kama da wuta,itama Haka Mansurah wutar ta kama cinta gwanin tausayi!shikam Sheik ARQAM sai Karatu sukeyi ganin wuyar tana Kara ƙaimi ne yasa suka Mata Daga ɗakin Suna kallon sarautar ALLAH!sai da Alhaji Hamza da mansurah suka kone kurmus Ko gawayi Babu sai Toka! Sannan wanda ihun da girgizar Babu sannan Sheik ARQAM suka bar karatunnan, ƴan jarida ansamu abun so DA Mutane sai post akeyi,wasu Kuka da salati nayi masu ALLAH wadai ma ga Alhaji Hamza da mansurah nayi.
Haka ƴan Sanda da tawagar Sheik ARQAM sukai tafiyarsu Bayan sun tabbatar da kowa yafice Daga gidan,aka haɗe tokar Alhaji Hamza da ta Mansurah aka Haƙa Rami aka bunne,mukulli aka sakawa gidan Alhaji Hamza (ALLAH ka karemu DA irin wannan Rayuwar, ALLAH kasa mugama da duniya lafiya,ka karemu DA saɓa maka DA kauce hanya Daga TAFARKIN sunnar manzon ka...oum ARQAM🙏 yanzu dai Alhaji Hamza da mansurah anzo duniya banza ankoma banza abunda Ake dansu Wato kuɗi an barsu an tafi Babu tsiya Babu arziƙi)
_____GIDAN AMARE___
Ɓangaren Gidansu Hadiyyah.......
Oga AQEEL dai kunsan a hannu yake Kamar lalle,Duk Yanda tsofaffi da su seerat suke jansa da surutu haɗe day tsokanar da akewa Angwaye! abun ya faskara sai Wani shan ƙamshi yakeyi! Yana daɗa ƙwakumar Hadiyyah wacce ya sauke ta Bayan ya shigo da ita a hannu ya sauke a hadaddiyar kujerar dake falourn,Suka karaci surutunsu da barwakcinsu yana ji yaƙi magana,ganin idanun AQEEL sunyi ka Kamar Gauta ne yasa seerat da raɗawa ƙawarta Zakiyyah a kunne cewar AQEEL fa bai DA nutsuwa yanzu,nan tagaya Masa irin lallurarsa aikuwa nan danan Zakiyyah ta dinga shelar cewa yakamata fa a tafi gida masu Motoci sunce zasu koma gida,kunsan fa ƴan kai Amarya da ance Mota zata tafi zakuga ana tsere kafin kice kwabo Babu kowa! Sai Daga ƙarshe Zakiyyah da Zahra sukaiwa Hadiyyah sallama itama Seerat da mummy Waleed sallamar sukai musu,zuciyarsu cike da tausayin Hadiyyah dan kuwa sun san Yau me raba Hadiyyah da AQEEL sai ALLAH! musamman Zakiyyah wacce yanzu tasan ya AQEEL ɗin yake.
Ai Suna ficewa AQEEL yabiyo bayansu haɗe da kulle ƙofar falourn...........
Gidansu Hidayah.......
Su Haseena kam Basu Wani Jima sosai a gidanba,Bayan AKEEL ya Shiga gidan da Hidayah a goye a bayansa bai ajiyeta a falour ba, bedroom yayi da ita su Haseena da ƴan tsofaffin zasu biyo bayansu ya dakatar dasu!
"Habadai mutanena ladan kuma ya isa hakanan,gatan yayi yawa, yanzu idan nace ki Shiga daƙina wanda zan Raya Sunna Nida matata sai ku biyo ni? Ku kallemun sirri to lala lala Lada ya isa! Nagode sosai da tayamu murnar aurenmu!
AKEEL ya faɗi haɗe da shigewa bedroom ɗin da Hidayah goye a bayansa ƙofar ya kulle saboda kar su Haseena su shigo Masa ɗaki,
Sukam su Bilkisu Da tsofaffin nan sun Sha mamakin AKEEL dawannan Rashin kunyar tasa,Amma Banda Haseena Dan kuwa tasan halin AKEEL.
Shikam AKEEL ajiye Hidayah yayi a tsakiyar gadonsu na Alfarma Bayan ya sumbaci bakinta ya fito Daga ɗakin,yakuma kulle ƙofar ya cire key ɗin yasa a aljihun sa.
Ya nufo su Haseena "Dan ALLAH Lada ya isa hakanan dare fa yanayi, Nikam inada abunyi fa,masu Mota sun mun waya Dana Shiga ciki Suna jira idan ba haka ba zasuyi tafiyarsu,sai kusan wajen zuwa Dan bazaku kwanamun a gidana ba, Alhalin ina sabon ango ku sanyamun idanu! AKEEL ya faɗi iya gaskiyarsa ko kunya.
Tsofaffi dai da sauri suka dinga rige rigen fita Daga gidan!jin abunda AKEEL yace! Haseena shewa tasa haɗe da Tafawa da Aisha sulaiman Suna kallon AKEEL ɗin wanda yai dakon su fice ya kulle ƙofar sa,aikuwa dai da suka kuma tsokanarsa ya biye musu sannan suka fito Daga gidan shima ya ƙulle ƙofar falourn sa..
Tsofaffin gidan Hadiyyah da na Hidayah kam a parking lot suka haɗu Suna sallalamin Suna faɗawa juna Rashin kunyar AKEEL Suma na AQEEL Suna faɗar yanayinsa sai shewa sukeyi Suna Yaba Rashin kunyar Twins musamman ma AKEEL!
Sukam su Haseena da seerat da Aisha Sulaiman da mummy Waleed sun haɗe sai kwasar dariya haɗe da Tabbatar da Rashin kunyar AKEEL a zahiri suke da dai oum ARQAM ce me gaya musu yanzu kuwa sunga Zahiri,haka ma kuma AQEEL sun Tabbatar da cewa shima fa babu sauƙi yanayinsa, a haka aka kwashe su gaba ɗaya a Motoci aka kai Kowacce gidajensu aka bar twins brother da twins sister a gidajensu domin barje amarci.......
Dama ita MamaGee tuni doctor Najeeb yasa an mayarta gida.....
Muje Next page 70 may be shine final Ko kuma 71
✍️Oum ARQAM ce ontop 🥰
08128131163
9/28/24, 2:19 PM - Rãbi'atou Aminou {Oum ARQAM}: *PAGE SEVENTY 70*🥳
✍️oum ARQAM ce.............
Burin kowanne masoya shine sukai ga Aure! musamman ma dai ace Suna matuƙar ƙaunar junansu!ai abun ba'a magana Hakan ce tafaru da AQEEL,Bayan ya kora su Seerat ya kulle ƙofar falourn,sai yaji kansa yaƙara Girma fiye da da! Wai Yau shine Yake da matar Aure,Abunda yajima yana kwaɗayin zuwan ranar tun shekaru da yawa,yake Fama da damuwa da lalura Akan Hakan,shikuwa me zaiwa ALLAH Idan ba godiya ba a daidai wannan lokaci, da yadda iyayensu suka musu Aure da wuri suka tsara musu rayuwa da ALLAH yayi nufin haka ai da tuni yajima da aure wannan lallurar dayake Fama d ita Aida tuni ta kau Daga gareshi,to dayake komai na ALLAH ne shine Yake tsarawa bayinsa Rayuwa sai yanzu lokaci yayi,kuma Duk da Hakan Alhamdullillahi! Shine abunda AQEEL ya Fadi lokacin yana tafiya zuwa falournsa.
A yadda yabar Hadiyyah Akan kujera a lulluɓe a Hakan yasameta!kirjinta da zuciyarta sai Duka sukeyi,saboda batasan ya wannan lokacin Zai zamar Mata ba,Duk da zuciyarta cike take da zullumi da tunanin Yar uwar Haihuwar ta wato Hidayah!itama Ko a wanne yanayi take sai ALLAH,Dan tasan gwamma ita akanta,ita mijinta baida kunya Ko kaɗan! Tana tsaka d wannan tunanin taji ƙarasowar AQEEL falourn haɗe da faɗin 'Sweet Baby' Wannan lulluɓin na jiki fa! Na zata zanzo na tarar dake kin cireshi! AQEEL yai maganar haɗe da Zama kusa da Hadiyyah yana cirata sama, haɗe day warware lafayar da take jikinta, wacce ta amshi jikin nata sai Wani warwali takeyi, haɗe da fitar da Wani sihirtaccen ƙamshi!
Amma ina yana warware lafayar sai yaji ƙamshin jikinta yafi na Lafayar sau nawa ma!
'Itadai Hadiyyah tun cirata sama day AQEEL yayi taji Wani tsoronsa ya kama ta!wai dama haka yake? Lalläi ne... Tana wannan tunanin taji AQEEL yana Mata wata irin sunsuna haɗe da yawo da hannayensa a Duk inda hannunsa yakai kai! Sai Wani sauke numfashi yake Akai Akai Kamar Zai shiɗe! Itakam Hadiyyah taga takanta Yasin.
'Daƙar ya saita kansa,ya mike tsaye da ita yana nufar ƙayataccen ɗakin sa,wanda yaji nera Kamar me!A makeken gadon sa yai mata masauki, haɗe dacewa 'Bari naje na dawo' kishiga Bayi kiyi wanka haɗe day alwala,akwai kayanki a ɗakinnan! Ki zaɓa kisaka,kinji sweet baby! AQEEL ya faɗa haɗe da sumbatar laɓɓanta! Itadai Hadiyyah batace komai ba.
'Yana fita Daga ɗakin aikuwa tayi saurin Shiga bayin, Aljannar duniya kenan, wannan bayi sai kace falourn shugaban ƙasa ko sarkin Zariya🤣,inda Yake walwali Duk abunda take buƙata akwai Dan haka tayi brush, haɗe da sauran abunda Zatayi,ga towel nan Kala Kala a hanger,sai dai Babu tsiya Babu arziƙi,ƙarƙarinsa inta Kaushi ƙirji yazo Mata cinya,in kuma ta Ɗaura a ƙugu shine zai kai mata ƙasa,Dan Haka Lafayar data shigo da ita bayin ita ta kuma mayarwa.
Bata Jima DA fitowa ba AQEEL yadawo shima day Alama wankan yayi,yacanza Kaya zuwa wata rantsatstsiyar Jallabiyya sai kamshi yakeyi fatar jininsa ya shining haɗe da fitar da ƙamshi Mai daɗi.
Kayan maƙulashen da aka tanadar musu a fridge ne ya ɗauko su,irinsu fresh milk, grapes, Apple, grilling meat wanda yaji haɗi na musamman!
Ican Daga nesa DA ɗakin Wani ƙayataccen carpet ne kuma yadda akayi tsarin gurin dama nacin Abincin ma'abota ɗakin ne,Dan haka nan Yaje ya jera kayayyakin,ya dawo gareta!
'Kinyi wankan kuwa? Girgiza Masa kai tayi alamun Ea
Amma Naga kin mayar sa kayan jikinki! Shiru Tayi Babu amsa!
Shima baija zancen ba, wardrobe Yaje ya buɗe ya ɗauko Mata wasu sleeping dress haɗe da Hijab Mai Girma,
Kayan ya ajiye a kan bed,hijab ɗin kuma ya miƙa Mata, Babu musu takarɓa tasanya, yashige gaba tabi bayansa, sallah yajasu,Bayan sun sallame ya juyo ya fuskanceta,ya dafa kanta ya karanta Addu'ar da Ma'aiki ya koyar damu Akan wanda yayi sabon Aure Ko ya sayi Bawa,sai ya dafa ta ya karanta wannan Addu'ar
"Allahumma inniy asaluka khairaha,wa Khaira ma jabaltaha alaihi a auzubika min sharraha wa sharra ma jabaltaha alaihi"
Bayan ya kammala yayi wasu addu'oi Akan ALLAH ya tabbatar da alkhair atare dasu,Lallai ne fan's dama haka AQEEL yake da ilimin Addini kai ma Sha ALLAH Abbu yayi ƙokari!
Ya riƙo hannunta zuwa wajen daya Adana kayan ciye ciyennan,Babu musu tabishi,ya zaunar da ita ajikinsa,yana ɗiba yakai bakinta,ta kawar da kai, aikuwa kallonta yayi "Ki karɓa kici ta lallami Ko nayi miki ɗura! Ya Fadi haɗe da niyyar sauke ta Daga jikinsa day aiwatar da abunda yafaɗa Zai matan!
DA sauri ta buɗe bakin,a haka yaciyar da ita wanda dole taci badon tanaso ba,sai da yaga tana Shirin Amai sannan ya ƙyale ta,shima yaci,Bayan sun kammala, bayi ya sungumeta ta kaita brush yasakeyi again,itama yamata sannan suka fito,Akan bed ya ajiyeta kafin yafara warware lafayar jikinta again,tana susunne kai Ko saura rarta baiyi ba,Dan Lokacin yafara fita a hayyacinsa!
Daga Sanya Sleeping dress komai ya kankama! daƙar AQEEL ya karanta "Allahumma jannabnash SHAIƊAN wa jannabish SHAIƊAN ma razaƙtana" Daga sannan kuma komai ya kankama AQEEL fa yafice a hayyacinsa,komai cikin zafi zafi yakeyi!wanda Daga Gani Baya cikin hayyacinsa, ALLAH Sarki Hadiyyah tabani tausayi matuƙa gaya,Kuka take tana neman taimako,shima AQEEL ɗin kukan Yakeyi Shi bansan nasa na taimako bane kona mene oho!
Iya wahala Hadiyyah tasha ta a hannun AQEEL,shima kuma yasha wahalar Sosai,saboda lalularsa,Yana samun nutsuwa tuni ya sume,itama Hadiyyah haka! Babu me taimakon juna Kenan,a haka Har Asba tayi Babu labari wajensu kowanne bai cikin hankalinsa..........
Mrs AKEEL (Hidayah)
AKEEL Ɗakin daya ɓoye Hidayah ya nufa ya sameta inda yabarta,Aida gudunsa yaƙarasa gareta haɗe da sumbatar laɓɓanta da warware lafayar jikinta itama, ƙamshin dayaji a hancinsa ne yasa Shi saurin ƙarasa cire Mata ita gaba ɗaya! Hidayah zata hanashi yace mata "Kul ɗin ki ai Yau Babu ɓoye ɓoye tsakanina dake,Dan kuwa idan kikace Hakan zakiyi,la shakka bazan lamunta ba!Ke kinsan Halina komai nawa a bayyane yake!
Cak Hidayah Kam ta tsaya da goce gocen datakeyi Jin abunda yafaɗa tasan Zai aikata!
Sai da yacire Mata Lafayar sannan yaga inner's ne kawai ajikinta!
Murmushi AKEEL yayi haɗe da faɗin "nazata ai bazakiji magana ta ba Dana faɗa Miki cewar,idan Zaki saka lafaya kawai ita nake buƙata,banson saka wasu kayan kafinta basaina Sha wahalar cirewa ba! AKEEL yaƙarasa maganar haɗe da shashshafa ilayirin jikinta, yana lumshe idanuwa kamar me jin barci!
Har inners Saida AKEEL yacirewa Hidayah, wacce Kamar zata kurma ihu,ganin illar da AKEEL yai mata,Zama Babu Kaya gareta,kuma shine yai mata ai wannan Abun da kunya,Amma yata iya,tasan datayi gaddama,tasan shauran,Dan kuwa Babu abunda bai faɗa mata ba,wanda zai mata Daren Aurensu,Dan kuwa tasan sahibinta Baya magana biyu! sannan ya ajiyeta a gefe a Hakan,shima kayan jikinsa ya cire sannan ya ɗaukewa zuwa bayi,wanda Kamar Zuciyar Hidayah zata fito waje,tsabar tsoron daya shigeta na AKEEL! A haka ya sakar musu shower shine yamata wankan, sannan shima yayi,da towel ɗaya ya rufosu,tunda babba ne,dama yafaɗa Mata cewa "tare zasu dinga wanka,kuma a towel ɗaya zasu dinga tsane jikinsu!
Koda suka fito Daga bayin tana maƙale ajikinsa,a haka ya ɗauko musu sleeping dress nasu yasanya Mata sannan shima yasanya,harda hijab ya ɗauko Mata, ya shimfiɗa sallaya ya zasu SALLAH,Bayan sun idar ya dafa kanta ya karanta Addu'ar da Ma'aiki ya koyar damu ga masu sabon Aure, haɗe da Mata tambayoyi Akan addininta,(wanda Hakan yanada kyau ga Duk Wani namiji wanda yai Aure,saboda yaji ya addinin matarsa yake,tun daga hukuncin jinin haila,nifasi,istihadha,DA kuma banbanci tsakanin maniy,maziy wadiy, kowanne mene hukuncinsa,da ita kanta janabar yadda take ta Yaya ma janaba take samun mutum da sauran su,ta yadda zakasan matarka shin da gyara a Al amuranta Ko komai normal,idan da gyara sai koyar DA ita,idan kuma Babu Shikenan,saika ɗora Mata, Hakanan shima idan mijin ne baida sani a Hakan Ke kin sani ki sanar dashi,ba Wani abu bane ai anzama ɗaya,saboda a gudu tare a tsira tare ALLAH yasa mudace,na rarraba bayanan ne daban daban Dana Su AQEEL kowanne cikin Daren nasu muƙaru da Abubuwa,Amma Duk Abu ɗaya suka aikatawa matan nasu, saboda Duk ƴan Ahlussunah ne) daidai gwargwado Hidayah tana da iliminta ba Addini.
Sai sannan ma yatuna DA kayan ciye ciyensu,a gaggauce ya fita sai gashi ya shigo dasu, inda aka tanada Dan cinsu nan ya kai sannan yazo ya ɗauketa,a Bakinsa ya dinga zuba yoghurt