Showing 135001 words to 138000 words out of 141223 words

Chapter 46 - RASHIN IYAYE Complete Document by Rabi'atu Muhammad Rabi'u Oum ARQAM.txt

ɗin sannan ya juye Mata a baki,haka take karɓa yata iya,Hakama Naman saiya tauna saiya Saka mata a baki sauran fruits ɗin ma Hakan, lallai AKEEL Naka salon daban yake.
Tun Daga Cin Abinci Abubuwa suka Fara sausaya ga AKEEL daqar ya iya kaita sukayi brush,kafin su sake danganawa ga haɗaɗɗen bed ɗinsu,komai cikin nutsuwa AKEEL yake aiwatarwa kama Daga romance har zuwa Mai gaba ɗaya Bayan ka karanta Addu'ar da Ma'aiki ya koyar damu idan Mai iyali Zai mu'amalanci matarsa ,Bazance Hidayah bataji jiki ba a Wannan daren saboda nafarkonta ne,to dama Ta ina za'ace guri a rufe Babu alamar hanya sannan ace Wani abu Rana tsaka zaizo Yayi hanyar ai za'a Sha wuya,shima AKEEL farin shigane Yaji gajiya Sosai ta Rashin Sabo.


A hakan Asba tayi a kunnen AKEEL Dan haka a daddafe ya Tashi ya Shiga bayi ya Tara Ruwan zafi,yazo wajen Hidayah wacce taci Kuka harta gaji idanu ya kumbure,abunka fa farar fata, fuskar nan Kamar Jan kosai,a Hakan ya sunkuceta zuwa bayin,Tasha Kuka wajen Gashin da AKEEL yamata na Ruwan zafi tun tana kuka harta daina, taji sauƙi sosai kuma sannan shima yayi wankan,yamata sukayi na tsarki sannan suka fito,a Hankali ya ajiyeta a gefen bed,ya shirya zuwa Masallaci,itama ya ɗauko Mata kayan sawa marasa nauyi,ya shimfiɗa Mata sallaya Amma ina bazata iyayi a tsaye ba, sai a Zaune Dan haka ya ajiyeta,da sauri ya fice,saboda sun shirya Hakan shida AQEEL zasu fita zuwa masallacin,Shi dama abunda Yasa yacewa AQEEL ɗin suje Masallacin shine, Doctor yacewa AKEEL ɗin Ranar da AQEEL yasamu biyan buƙatar sa in ba ALLAH ne ya taimaka ba zai samu Suman wucin gadi, sai an Masa wata Allura, wacce a Hankali a Hankali idan yana sex ɗin in Yana samun matsala har ya daina,saboda ƙarfin allurar da aka dinga Masa shekarun Baya.


AKEEL Baya fatan Hakan ga ɗan uwansa,to Amma ina tunda yafito baiga alamun ƙofar AQEEL an buɗe taba,hankalinsa ya Tashi ganin Hakan,Dan haka yakoma cikin gidan sa,ya samu Hidayah harta idar da Sallah tana zaune,shima sallar yayi, sannan ya ɗauki Hidayah ya ɗora a kan bed,wacce har sannan bata daina matsar ƙwalla ba.


"ALLAH yamiki albarka Hayateeenah, ALLAH yabamu zuri'a Mai albarka tagari, yadda Kika tsare mutuncinki har zuwa gareni ubangiji ya nesantaki Daga azabarsa, AKEEL ya faɗi haɗe da kallon idanun Hidayah yana Mata murmushinsa me kyau, ita dai sai Ameen take cewa,tanajin Daɗin wannan addu'a, sannan kuma tana tausayawa masu yawon tazubar Kenan Inda bata kawo mutuncinta ba ga mijinta na Sunnah Shikenan Duk wannan yabon da addu'oin bazata samuba,Saima fitina da zargi!


"Hayateeenah Twins brother ɗina bai fito ba,alamu sun nuna........... Nan ya gayawa Hidayah komai game da AQEEL na ciwon sa,ta tausayawa AQEEL ɗin,Amma kuma fa Tana hango Azabar da Twins sister ɗinta zata Sha a hannunsa,Dan kuwa ita yanzu mijinta normal yake Tasha wannan wahalar Inaga wanda baida lafiya cikakkiya!


Nan suka dinga tattauna yadda za'a ɓullowa Al amarin,game da halin da AQEEL yake ciki, sun yanke shawarar Kiran AQEEL ɗin a waya,ki ALLAH zaisa ita Hadiyyah ta ɗauka,Duk zuciyarsu fal tunanin Halin da itama zata kasance,Dan kuwa zataji jiki ainun a wajensa.










Mrs AQEEL (Hadiyyah)






Har sannan AQEEL bai farfaɗo ba,itama Hadiyyah ɗin a sumen take,ƙarar wayar AQEEL ce ta dawo da ita hayyacinta, ALLAH yaso tana kusa da ita,Dan haka motsawa tayi daqar,saboda azabar datake ji a ƙasanta,ga wani mugun ciwon jiki, haɗe Dana qirji daya sameta dare ɗaya,sai katsewa jiran yake daqar dai Takai hannu tadau Wayar sunan 'twins brother' ne Dan haka tasan cewa tabbas AKEEL ke Kira,juyawa Tayi ta dubi AQEEL dake gefe a sheme tayi tunanin barci yakeyi,Dan haka da dashashshiyar murya ta Kira sunansa Amma ina shiru kakeji,sai taga idanunsa ma a buɗe suke alamun Suma yayi,Dan Haka Daga ƙarshe ta ɗauki wayar cikin ƙarfin Hali 'Assalamu alaika' ta faɗa da murya ƙasa ƙasa 'yawwa Yaya (nufinsa yayar Hidayah abokiyar tagwaitakarta ,kuma shima matar yayansa Abokin tagwaitakarsa,🤣)
Ga Hayateeenah , yafaɗa haɗe da karawa Hidayah wayar a kunne!




Meke faruwa sister ina AQEEL ne?
Fashewa da Kuka Hadiyyah Tayi tana faɗawa Hidayah halin datake ciki,dashima AQEEL ɗin cike da tausayawa Hidayah tadinga kwantarwa da Hadiyyah hankali haɗe da faɗa mata yadda zatayi tayiwa AQEEL ɗin sannan sukayi sallama.


Yadda sukayi da Hadiyyah haka Hidayah ta faɗawa AKEEL,ya tausaya Mata, sannan ya tausayawa AQEEL shima.




Itadai Hadiyyah da dabara ta yunƙura wanda sai da tayi dagaske, sannan ta Sauka Daga bed din,Bayan ta fashe da kukan azaba,Amma dole ta tallafi rayuwar abun ƙaunarta,Kamar yadda ƴar uwarta ta faɗa mata,




Kaya tasa ajikinta daqar, sannan tasawa AQEEL ɗin nasa wanda yacire,Takoma takwanta tana kuka haɗe da Mai DA numfashi,sai da tahuta sannan Takuma yunƙurawa,ta tafi toilet ta haɗa Ruwan zafi tashiga ciki wanda Sai daqar ta iya Shiga ciki,Amma Hidayah tace Mata idan tayi zata samu sauƙi sosai,itama Yanzu haka Shi tayi, yanzu normal take jinta! Dan haka tadaure tadinga canza ruwa harta samu relief,tai wankan tsarki ta fito a hankali,Amma fa har sannan tanajin raɗaɗi a ƙasanta!
Daqar tasamu Kaya marasa nauyi ta sauya Takoma bed ta kwanta,tana kallon AQEEL har sannan yana Kamar matacce.






Can ɗaya ɓangaren kuma Doctor ne ya aiko da nurse da allurar da za'awa AQEEL yadawo hayyacinsa,Dan haka AKEEL aka bawa shikuma yakira Hadiyyah Akan tazo ta buɗe kofar room ɗin, ƙofar falourn Pin ne Wannan yabuɗe yasani,ciki kuma key ne daƙyar Hadiyyah ta fito ta karɓi Allurar,saboda ta iya Allura shima AKEEL ɗin ya iya to Amma ai wannan cikin ɗakin sirrinsune bai kamata ya shigar musu ba.




Ko 10mins Hadiyyah Bata yi da Masa Allura ba yadawo hayyacinsa,sai sauke ajiyar zuciya yakeyi,yana jinsa Kamar Wani sabon mutum,mararsa data Masa nauyi haɗe da Tauri yanzu saura kaɗan, 'godiya yayiwa ALLAH a zuciyarsa na yadda ya Sanya Mata suttura ga maza Suma mazan suttura ga matansu, yanzu gashi yasamu nutsuwa wacce bai taɓa tunanin akwai irinta a Duniya ba, shikam yazata mararsa da cikinsa bazasu taɓa komawa daidai ba,tun bayan Hakan da sukayi, yanzu yaji alamun zasu koma normal saboda yadda yaji Daga yi ɗaya harya samu relief.


Janyo Hidayah yayi jikinsa,yana Kuka haɗe da fadin ' ALLAH yayi miki albarka ya shafe kura kuranki,ya Amintar dake 'Halawateeynah' kinmun Abunda Duk duniya Babu wanda zai iya Mun Ko mahaifiyata inda tana raye balle mahaifina dayake Raye,saboda wannan wata baiwa ce DA sururi tsakanin ma'aurata da ALLAH ya Sanya Shi,nan dai AQEEL yaita yabon Hadiyyah dasa Mata albarka, yaci gaba da magana 'Kin kawomin Abunda Yake tsada a Wannan zamanin wato budurci, bakowacce budurwace take dacen kaishi gidan miji salin alin ba,saboda lallacewar Zamani,Yarinya budurwace Amma ina ta siyar da budurcinta,kekam Yar baiwa ce ALLAH yajiƙan Iyayenmu da Rahma yasa aljannah makoma.


Bayan Hadiyyah tagama Shan yabo DA addu'oi,yadawo hayyacinsa sosai, ƙarfin jikin sa yadan dawo,Amma fa gajiya akwaita Dan yaji jiki, Abubuwan da suka faru bai yisu da sauƙi ba dan haka gaba ɗaya jikinsa ciwo yake Masa musamman,bayansa da ƙafafuwansa.


Hadiyyah Tayi gaddamar binsa bayi tace Masa ita tayi wankan ta Amma dole ya tursasa ta Akan dole saita kuma yi,Babu yadda ta ita haka tabishi Saida yakuma gasata,shima ya gasa jikinsa yayi wankan tsarki suka fito, ganin Yadda take ciccije baki da tafiya a Hankali yasan tabbas Yayi ɓarna.


Bayan sun gama kimtsawa yakira AKEEL,tunda Hadiyyah ta faɗa masa cewa yakirashi,Jin muryarsa a sarke yasa AKEEL bai tsonake ba kamar yadda Yayi niyya! Ka kirani lokacin ina bayi ne!cewar AQEEL yana lumshe idanu!


'To Zubair nasan komai fa, karka ɓoyen komai,Babu abunda bansaniba, ka fice hayyacinka ne saboda samun nutsuwa!Dan haka yanzu ya jikin Naka?Amma normal kake jinka ko?fuskewa AQEEL yayi sannan yace kakiramin Doctor yanzu Halawateeynah Babu lafiya fa!to dama ina zatayi lafiya ka cuci Yar mutane ka kasarata! AKEEL ya ƙarasa maganar haɗe da dariyar shakiyanci! Shikam AQEEL kashe Wayar yayi.


Kamar yadda AQEEL yabuƙata,Doctor yazo haɗe da nurse,aka Masa alurai aka Bashi magunguna,


Itama Hadiyyah anbata magunguna Saida aka Mata Ɗinki Amma kaɗan,


Hidayah ma ambata magani, Shikam AKEEL Babu abunda aka bashi normal yake.




Daga AQEEL har AKEEL haka suka dinga kulawa da matan nasu kamar kwai a cokali,haka Dama abun yake muddin Kika kai budurcinki ga mijin Aurenki,Zaki samu kulawa fiye da yadda kike tunani,Hakan take kasancewa ƴan mata mu riƙe mutuncin ku ku killatashi wa mazajenku,akasin Hakan najanyo kaskanci da wulakanci koda kuwa shine ya kawar miki da budurcin saboda zargi ne Zai Shiga tsakaninku.






Lafiyayyen Abun Kari Mommah ta Aiko musu dashi,haka ma da rana,sai tarairaya sukesha wajen mazajen nasu, AQEEL ya Fara komawa normal,




Su Seerat da Haseena da Aisha Sulaiman da mummy Waleed sunso komawa gidan Amare Amma ina angwaye sunbada umarnin kar Abar kowanenne yashigo musu gida Har zuwa sati ɗaya.






Amarci akesha Babu algus a Wannan gidaje musamman gidan AKEEL,Shi AQEEL an kwafsa Masa saboda ɗinkin da akawa Hidayah,Amma kwana biyu ya sarara Mata, Daga bisani aka baje harkar Cin amarci babu kama hannun yaro.


Tun Hadiyyah taqi harta ware abunta Takoma Kamar AQEEL kullum shikam yajishi a network.


Saɓanin AKEEL daba kullum ba muddin za'ayi romance shikam anan yafi Kauri.to dama haka abun yake ai kowa d abinda ALLAH ya Sanya yazamo abun sonsa.




Sunji abunda yasamu Auntynsu+
(Sa'adatu)sun Ji Babu daɗi sunwa Alhaji Hamza Tofin ALLAH ya tsine.






Su Hydar farouk da Auta Hafsat dama Suna wajen Baaba,Dan haka Daga Asibiti Bayan sallama Gida Ƴan uwan Sa'adatu sukayi da ita,wacce tayi nadama ba kaɗan ba Akan halinta Nason abun duniya da cin Amana DA yaudara,sai istigfari takeyi,Ta warke Takoma normal Yanzu Kamar Babu abunda yasameta,so take ta samu lokaci tajewa waɗanda ta zalunta Akan su yafe Mata.




Daga wannan page ɗin Rashin iyaye yayi ƙarewa🥳🥳🥳🥳🥳🥳🥳






✍️Oum ARQAM


08128131163
10/7/24, 10:55 AM - Rãbi'atou Aminou {Oum ARQAM}: *PAGE SEVENTY ONE 71 END*












✍️oum ARQAM ce.......










Kamar yadda Sa'adatu ta kudirce a ranta Hakan tayi,Bayan ta warke ragal sumul tasa zuwairah yayarta wacce take Zaman gida Yanzu ta rakota gidan Baaba,lokacin duk Yara Suna school,Cikin Kuka tadinga zayyanawa Baaba irin mugunta da Cin zalin da tadingawa su Hadiyyah,tacewa Baaba ta nemar Mata afwa gunsu, Baaba tace Babu komai aidama rayuwa ita haka take,Nan Baba Tabata shawarar taje wajen mazajen data aura tanemi yafiyarsu haɗe da matansu kawayenta waɗanda taci musu Amana, Sa'adatu taiwa Baabah alƙawarin zata aikata Hakan,tajima a gidan Har Saida Yara suka dawo Daga school.


Taga yadda su Hydar farouk da Auta Hafsat sukayi kyau abunsu Babu abunda yadamesu DA rashinta Ko abinda yasameta!tayi Hamdala ga ubangiji,ita ta cuci ƴaƴan wata ga nata ba'a cutar Mata ba(koda yake ai dama haka abun ALLAH yake ba Duk abunda kayi za'a maka ba,Wani sai kaje can lahira ALLAH zai biwa wanda Kawa hakkinsa,Ko kuma kai idan ba mutumin kirki bane,maybe mijinka Ko iyayenka Wani ɗan uwanka Nagari ne to sai Kaci wannan darajar tasa Ko ƴaƴanka su ci,haka kuma koda kai mutumin kirki ne maybe iyayenka Ko Wani ɗan uwanka bana gari bane wannan abunda yayin sai ya samefa, sakayyah tazo a kanka,Dan haka idan kana mutumin kirki Wani abu yasameka bana Dadi ba karkaji Babu daɗi Ko mutane sudinga cewa ai tunda kukaga Abu kaza yasamu wane maybe yana aikata irin abun a ɓoye,hakana idan mutumin banza ne shima abun alkhair yasameshi karka ce Wani abu Ko kace Shi wannan ba mutumin kirki ba Amma Babu abunda ya Sameshi ba haka ba ne akwai Lokaci,hakana Duk wanda yayi zina da ƴar Wani za'ayi da tasa,hakane Amma wlh Wani bashine ya aikata ba maybe mahaifinsa Ko kakansa na farko Ko acikin Jerin kakanninsa Wani yayi zinar Amma sakayyar batazoba sai a kansa, Kunga Ai shima sai Yar tasace Shi wanda ya aikata ɗin koda Baya duniya,ya UBANGIJI kaimana me kyau ka Tabbatar samu Akan tafarki madaidaici alfarmar masoyina shugabana Annabi muhammad Saw✍️)




Kamar yadda Sa'adatu taiwa Baabah alƙawarin zata nemi yafiyar waɗanda ta zalunta ta aikata Hakan!


Takanas har gidan Alhaji Gambo taje wajensu Hajiya ikilima da Hajiya Sahura ta nemi yafiyar su dayake yanxu sun Zama mutanen kirki Babu Wani jayayyya suka yafe Mata, musamman Hajiya ikilima wacce Sa'adatu tafi ciwa Amana sai sannan tai musu gaisuwar Hajiya suwaiba,taga Abbas ma Sha ALLAH ya Girma sosai hakana taga ƴar wajen Hajiya Sahura wato Asalamiyyah itama hakan ta zauna a gidan Har saida Alhaji Gambo yadawo ta nemi yafiyarsa d irin tozarcin data Masa yace ALLAH ya yafemu gaba ɗaya,haka tabaro gidan cike da murna.


Taje gidan Kawu Isma'il shima tanemi yafiyar Aunty Hauwa tace Mata Babu komai ai dama haka rayuwa take.
Shima Kawu Isma'il tanemi yafiyar sa yace ya yafe Mata ai dagashi har ita masu laifi ne sai dai sudage da istigfari.


Takanas taje Har gidan Alhaji tallafy shima tana kuka, ALLAH yasa Ranar weekend ne yana gida nan tanemi yafiyar sa Bayan ta zayyane Masa makirci da tuggun dasuka dinga aikatawa itada jimmai sune silar rabuwar abotarsu ta har abada shida Amininsa ta yadda har yakoma ga ubangiji Basu gana ba,Abbu yace Babu komai ai komai yawuce.


Zuciyar Sa'adatu Yanzu tayi wasai Amma idan tatuno da Ummu Rumana DA irin zaluntar ta datayi gashi Babu halin neman yafiya shike ɗaga Mata hankali,kullum cikin istigfari take.






______ƁANGAREN JIMMAI____




komai Alhamdulillahi za'ace Dan kuwa Yanzu ta saita kanta ta Dage da bin ALLAH itama tuni akasha bikin Shukrah da Angonta Is'haq kuma Alhamdullillahi Babu wata matsala a zamansu, Saida tayi satittika ya ɗauko dansa Shaheed yakawo mata tana ƙaunar ɗan nan, yayanta Usman ne yai mata komai kuma sosai yakashe Mata kuɗi wanda bazasu lissafu ba,saboda Yanzu Usman kuɗi sun zauna sai Sam barka.


Jimmai tuni ta warke saidai fa akwai sharar ƙafa da harshenta ya ɗan karye idan tana Magana ba'a ganewa sosai,jimmai a Hakan ma tagodewa ALLAH.




___GIDANSU TWINS BROTHER (AKEEL DA AQEEL) DA TWINS SISTER (HADIYYAH DA HIDAYAH)____




AQEEL tuni ya warke tun Bayan kammala allurorin da doctor yace za'a Masa, yanzu sai Shan harka akeyi babu wata fargaba, Hadiyyah da AQEEL Suna zaman lafiya da fahimtar juna tsakaninsu komai tare sukeyi,Bayan kammala biki da wata Biyu Abbu yai Musu maganar komawa India domin Dora karatunsu,Suma su Hadiyyah za'a Samar musu gurbin karatun acan,sai dai me ai tuni Hadiyyah tafara laulayi me zafi wanda shine ma ya dakatar da tafiyar tasu sai zuwa Wani lokacin kuma,karkuso kuga tarairayar da Hadiyyah takesha wajen sahibinta (lalläi ne Yanzu Hadiyyah wata Tara zakiyi a gidan miji ki haife lallai Haseena dama haka kikace maybe nan da wata Tara kuzo Suna ga hasashenki yazama gaskiya)
Tsakanin Hadiyyah da AQEEL narasa wayafi wani nunawa ƙauna aradu,Nikam oum ARQAM nace ALLAH yaƙara danƙonta.








AKEEL baban Rashin kunya na Hidayah Sha Alwashi wata irin ƙauna da soyayya Ake Sha,surutun nan da Rashin kunyar sa dai da yayi Alwashi sai da yakoyawa Hidayah Shi,takoya kuwa kunsan dai makoyi yafi wanda ya iya Abu in yatashi yin nasa!
Yanzu Hidayah idan ta Tashi tana sambaɗa surutu Haseena seerat Aisha Sulaiman mummy Waleed Ko MamaGee Yasin baza ku ce ita bace sai dai kuce Hadiyyah tashi ɗaya Dan ita tajuye Yanzu,ita kuma Hadiyyah takoma ita,Amma ita Hadiyyah bamu sani ba Ko cikin jikinta bane tun Yanzu yasa tayi laushi!


Zaman AKEEL da Hidayah akwai tausayi da fahimtar juna sosai,Babu batun ace Babu faɗa ai zo mu zauna zo mu saɓa ne,kuma Duk daɗin Zama bai kai harshe da haƙori ba Amma wataran haƙori taune harshe yakeyi,to Hakan Zaman nasu yake!sai sharɓar soyayyah akesha Kamar ba gobe!


Lokacin da cikin Hadiyyah ya bayyanawa bakuga tsiyar da AKEEL yadinga wa AQEEL ba "kai ai dama nasan za'a Rina wannan jaraba taka kai kullum kajika a network ai dole ma wata Tara Ka haife,inda ana Haihuwa kwana ɗaya kai Kam Daka haife ai! Sai kuma ya sheƙe wa AQEEL da dariyar shakiyanci!
(Kuji iskancin AKEEL fans dama namiji yana haihuwa?😂)
AQEEL Baya kulasa sai yaga abun nasa yaje magaryar tukewa sannan
"Ina ruwanka da ni ne wai ɗan sa Ido aidai naji,kai ina cikin ajikin matarka Ko sai Rashin kunyar aka iya!
AKEEL yace
" Mu ba Yanzu ba Yaushe mukaci amarcin da Har ciki Zai Mana sammako ,la,la,laaaa,la sai Mun wuta tukun,mu ba irinku bane kaida matar Daga kace gashi itama gayyar kwaɗayi ta amshe! Sai ya kuma fashewa da dariya!
Nan danan AQEEL sai fusata
"Kasan ALLAH bro in baka kyaleni ba xan maka Rashin kirki ALLAH! Muma a Hakan muma amarcin mu ai GA kuma sakamakon mu a gefe! AQEEL Zai ƙarasa zancen da murmushin daya Saba idan Abu yamasa daɗi!
"Naga alama kam shiyasa naga kullum ana amaye_amaye da ciwe_ciwe Raina za'aci amarcin,kullum amsawa "Hayateeenah" da zafi kullum ta tare wajen matarka Yasin Zan hanata zuwa kaida kayi aika aikar ka zauna Kayi jinya mana,sai wacce bataji ba bata Gani ba!cewar AKEEL sai ya gudu shashin sa ganin AQEEL ya shaƙa ba ƙarya!!!!!!




(Haka wannan tagwaye suke Rayuwarsu gwanin burgewa abun sha'awa wacce da za'a samu Maza ƴan biyu si aure Mata ƴan biyu ai da zumunci ya ɗore Sosai Har ƴaƴa da jikoko,Amma in Wani can ya Aure ɗaya Wani ma ya aura sai Kuga Duk shakuwarsu ta yarinya zuwa ƴan matanci ta Saraya kowacce ta zauna gidanta watama Wani Garin,may be ma ɗaya cikin rufun asiri ɗaya sai a slow! Duk da haka ALLAH Ke tsarawa bayinsa Rayuwa yadda yaga ta dace dasu ubangiji ya kyautata Rayuwar mu DA ta ƴan uwanmu baki ɗayanta alfarmar shugaba Saw)


Kullum Hidayah tana wajen Hadiyyah tun kafin tayi ciki ma Suna Shan hirarsu komai tare suke gwanin burgewa,Yau wannan Na nan Yau wannan nanan,Amma yanzu Hadiyyah sai a slow Dan haka Hidayah ta tare acan!
Sai Hadiyyah tana kwance Ko tayi Amai nan zakuga Hidayah ta zaro zance
"Lalläi sis ni fa kinfara gajiyar Dani Yasin! Sai kace Nina miki cikin kiyita wahakarni,Amma DA mijinki yadawo Zaki maƙalemasa Kamar super glue!
Ke ƴar daɗi miji ai GA ribar nan! Itama tana dariyar like mijinta!
Hadiyyah Babu bakin magana ya mutu! Sai Daga can zatace
"Kisha kuruminki indai cikine zaizo kanki ne yarinya naga nawa saura naki! Cewar Hadiyyah
"Hohoho angaya miki koya irinkine sarkin raki! Zakiga nawa nema? Ai saidai kiga ciki ya Girma ya Zama ƙatoto saboda jarumta!
Sai sannan Hadiyyah zata saka dariya tana kallon ƴar uwarta "e lallai da akace idan ka girmi mutum Ko da da 1mns ne ka girmeshi!Amma ALLAH yakaimu lokacin lafiya! Sai Hadiyyah ya ƙyale Hidayah!


Wata Rashin kunya sai AKEEL yashigo zasu tafi shashinsu ma, Hayateeenah nagaji da zuwanki gidannan!
Nima Hakan my huub ni Bada ciki

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login