Showing 42001 words to 45000 words out of 141223 words
Chapter 15 - RASHIN IYAYE Complete Document by Rabi'atu Muhammad Rabi'u Oum ARQAM.txt
yi tunanin ziyara ya kawo musu, yai abun da zaiyi yai tafiyar sa gida.
Zakiyyah ta na d'aki, abun duniya ya ishe ta,babu Mai kula ta. Gidan, y'an uwanta za su kwana su ta shi, tare Amma ba bu Mai mata magana, Hadiyyah da Hidayah su na zuwa koyarwar su, su na samun kud'in su dai dai gwargwado, ku ma abun da su ke so su na saya,wa ni kud'in ku ma suna tarawa sabo da Bikin Zahra da yake 'karatowa, Amma babu Mai kulata, kuma Wannan Duk hud'ubar Baaba ne.
tana fa ma da ciwon ciki CIKIN ta har za fi yake ma ta, yunwa ce Kuma ta sa HAKAN,ga ciwon kai tana ta shi jiri ya ke d'ibar ta, kamar za ta Fad'i, shi Yasa take wuni a kwance, Duk da hakan ba bu Mai kulata, a kwance ma gani ta ke garin yana juya mata, yau kwanan ta d'aya da wuni babu abinci, sai ru wa da ta ke sha, yanzu kuwa ruwan ma ta kasha Shan sa, kulle ma ta ciki yake yi,ga zafi da CIKIN ta yake mata.
Sai tu nanin zaman gidan Hajiya Sakinah kaakarta miri'kiyarta take yi, irin jin dad'in take ciki, Wannan ai Duk da jimawa ne , zuciyarta ta ba ta amsa, ki tuno zaman mijinki me kika rasa? Mijin ki komai bai raga Miki ba, sai abun da Kika ga damar dafa wa, kiyi kwanciyar ki WANI ba yi kikeyi ba, sha ra da wanke_wanke ne ki keyi in kin so, Amma har ya ran ma'kota zuwa su ke su na Mata ta Basu abinci,irin Marasa 'karfin nan, ta ba su abinci da y'an kud'i,Amma wai yau ita ce akan Abinci ta Zama cu ta tana Shirin kama ta, ta yunwa, zantukan da Zakiyyah take ayyanawa a ranta kenan, ALLAH sarki *ABIE* na ko yana wane hali yanzu oho, ALLAH yasa dai Bilkisu ba zaluntar mun shi take ba, wad'annan zantukan dai Zakiyyah take tayi, zafin ciwo ne ko kuma nadama tayi ALLAH ne masani, sai nan gaba zamu ga yau Zakiyyah da zancen mukhtar da kuma ABIE ai da bata zancen su amma yau tayi maybe zafin yunwa ne, ta na samun abinci ta 'koshi zata da wo kan bakanta, tun da dai halin Zakiyyah sai ALLAH Anya kuwa zatayi nadama.
Su Hadiyyah da Hidayah kamar yadda Alhaji tallafy yai musu Al 'kawari HAKAN ne kam yafaru, ana Fara registration ya Aiko musu da form da komai da komai suka cike, sai mur na kamar ba bu go be, ALLAH yakusa cika musu burin su,har ku kan murna sukayi da tuno Abby ai da yanzu Suna level two ma may be tun candyn su in da sannan suka d'ora.
Hajiya Zahra amare sai 'kyallin Amarci akeyi ALLAH ya kusa yanke mata wahala xaman yunwa da talauci, uwa uba ga gallazawar Sa'adatu, a garesu,sai mur na takeyi ALLAH ya kawo lokaci,sai dai murnar ta na komawa ciki idan ta tuna da 'kannenta y'an biyu Hadiyyah da Hidayah da 'karamarsu Khadija, idan Allah yakawo Auren su za'a iyayi rana d'aya, ita kam khadijatu zata Zama sau ra ita d'aya ta na ba ta tausayi sosai, yarinya ba bu ruwanta shiru_shiru da I ta kamar babu ita a gidan,ita fa wat rana mancewa ta ke da ita,balle kuma oum Arqam wacce ba Y'ar uwar ta ba,shi yasa bana zancen ta sosai mance wa nake da ita, saboda babu hayaniya gareta.
Bata saka Zakiyyah a sahun zan cen ta ba, d'an lokaci ne zata koma gidan mijinta, saboda ta Fara gano alamar nadama a tare da ita, Duk ta fice hayyacin ta, Babu walwala tare da ita,tana tausaya mata Amma Kuma ga ta ne Baaba take so tai mata zaman gida bai kama ce ta ba, idan ta ji wuya da 'kafarta zata koma gidan mijin ta, haka babba tace musu, shiyasa ma suka fita daga harkar ta tan,Amma d tafara Basu tausayi,zasu ci ga ba da kulata har su Hadiyyah da Hidayah d'in su dinga ba ta abinci sai su ka tu na,idan sukai mata ga tan hakan bazata koma zaman gidan mijinta ba, iskancinta zata ci ga ba dayi, Amma yanzu sun Fara ganin Amfanin nadamar Zakiyyah d'in, ALLAH sarki d'an uwa Mai dad'i ALLAH yasa Zakiyyah tayi nadamar kamar yadda y'an uwanta suke buri Nima inaso tai nadamar seerat na san kema kina son 'kawarki ta yi nadama ta koma gidan mijinta ko?
**************
Alhaji tallafy ya 'kudiri niyyar gyara gidan su Hadiyyah da Kuma din ga kai musu abinci, Amma idan ya tuna da da wacece Sa'adatu sai yaji Baya son yin HAKAN,gwanda dai ya dinga bawa twin's kud'in zu wa makaranta da Yawa, yasan bazasu 'ki tallafawa 'kannensu ba, Amma shi kam Sa'adatu ya san idan ya ya gyara gidan, ya ajiye musu abinci buhu_buhu gallazawar da takewa marayun ba fasawa zataiba HAKAN kawai shine mafita, ALLAH yaba wa Alhaji tallafy hangen nesa da samu mafuta a irin hayayensa ma su kyau je ne ma da hangen nesan sa ya assasa tallafy Charity foundation, shi ne solution d'in sa na tallafawa al uma, da kuma bi gidajen marayu, da ma'kota da dangi Duk wad'anda ba su da rufin asiri yana tallafa musu da jikin sa da kud'in sa.
Hajiya Aisha da Alhaji tallafy sun ga amfanin zuwan su tallafy foundation da su AKEELA da AQEEL, sabida an sa mu ci gaba ba KA'DAN ba, idan Suna tare musamman AQEEL da AKEEL Suna jiyo hirar su, har da Y'ar dariyar AQEEL d'in, Amma ba kamar AKEEL ba sai Alhamdulillahi da da Ba'a samu HAKAN ba kuma fa,
Bangaren AKEELA ma HAKAN Suna had'uwa da y'an uwanta ita ma ayi hirar da ita, Hajiya Aisha d'in ma Suna Hira da ita,
'Nikam AKEELA Anya ba 'kawance kike so ku kulla da twins d'in nan ba? kiyi ta zancen su, in mun zauna!
Cewar Hajiya Aisha fuska d'auke da murmushi, tana sha fa kan AKEELA da ke kan cinyar ta!
"Habadai Ummu na gor me su fa, waje 'kawance?kawai dai burge ni suke, ai shinenan dan zan gani ne idan ba 'kawancen ake son 'kullawa ba, ai shi abo ta ba sai sa'an ka ba in ji Hajiya Aisha tana murmushi,ita dai AKEELA ba ta kuma magaba ba.
Ita ma Hajiya Aisha shirun tayi tun da ta ga Mai zancen ta gaji kuma.
AKEEL ma hakane zancen AKEEL su Hadiyyah da Hidayah, shi ya kewa AQEEL indai sun zauna, sai kuma zancen abun da ya sha fe su, sai kuma wata Ra na a tattauna matsalolin da aka fuskanta a Baya, Amma fa AQEEL ne me zancen, dan idan AKEEL ne ta taddi zancen Ranar kam babu lafiya dan ciwon sa sai ta kusa ta shi, Amma idan shine ya ta do zancen da sau'ki saidai idon sa yayi ja yana ajiyar zuciya......
😭😭😭😭ALLAH ya gafartamawa zainab da iyalanta gaba d'aya Yasa aljannah makomarsu ALLAH ya kar'bi shahadarsu baki d'aya ya dad'a bawa mijinta haquri da juriya dan kuwa yayi Haqurin, da y'an uwanta baki daya🙏🙏🙏🙏🙏
In Sha ALLAH FANS next page 31 zamu kammala hidimar Auren zahra da kuma zancen Sa'adatu, Duk aciki da abun da Ba'a rasaba,page 32 ku wa in Sha ALLAH xamu ji ya rayuwar su AKEEL AKEELA da AQEEL takasance a Baya shin me yake damun su ne Duk da CIKIN kwanciyar hankalin da suke nasan wannan lokacin kuke ta jira to yazo Muje zuwa dai.....
✍️Oum ARQAM ce ontop
I love you All FANS🥰🥰🥰🥰🥰
2/7/24, 4:28 PM - Rãbi'atou Aminou {Oum ARQAM}: *RASHIN IYAYE*
(Babbar musiba)
Daga *Al 'kalamin✍️ Rabiat Amin (oum Arqam)*
*08128131163*
✍️ Marubuciyar...
*Komai Nisan jifa* 📚
*Hakan ba kuskure bane*📚
*_____________*
MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION📚🖊️ *(M°W°A)*
'Kungiyar d'aya tamkar da dubu masu Nazari da Aiki da ilimi burin 'kungiyar a koda yaushe shine ta fad'akar ta Kuma wa'azantar ta Nishad'antar da masoyanta🤙
*____________*
*PAGE THIRTY ONE 31*
Abun na yine fa! an saci d'an barawo babu Zama, tsakanin Alhaji Gambo da Sa'adatu fa sai wani d'inkewa akeyi, Baya sa ti yake zuwa gidan, a kufi a kufi sai ya zo,tun ya ran ba su ga no ba kin zaren ba har suka ga no cewa lallai fa Akwai wata a 'kasa tsakanin Auntyn su da Alhaji Gambo Abokin Abbyn su. Abun ka da ba Yara ba an tsayar da Ranar d'aurin Aure dai_dai da Ranar d'aurin Auren Zahra, lallai ne Amarya Y'ar lallai Sa'adatu za'a amarce da angonta ra na d'aya da Y'ar ta lallai abun na yi ne uwa Amarya Y'a Amarya ALLAH yakaimu lokacin.
Munafikin! Wato Alhaji gambo ko ma tan sa bai gayawa zancen ba zai 'kara Aure ba ma! sai da magana ta fasu a gari suke jin zancen,
Tsakanin Hajiya suwaiba da Hajiya sahura sai habaici wa Hajiya ikilima suke mata da dariya, bawai basajin kishin bane wannan sun barwa zuciyarsu,Amma Amintar Hajiya ikilima D'IN da sa'adatu suke hange,
Saboda tsabar Amince ko kulasu batayi in tazo gidan, an dinga dariya da shewa kenan, Duk da ba part d'insu d'aya ba sai tabi Duk hanyar da sa'adatu zata had'u da d'aya daga cikin su sai tayi ko ta aika Y'ar Aiki da habaici wa d'aya daga cikin su.
Kowacce Y'ar masifa ce Hajiya sahura da Hajiya suwaiba sun yiwa Alhaji Gambo bala'i kala_kala Amma Duk da haka yace Auren Sa'adatu Babu fashi!babu gudu babu ja da baya! Sun bi malaman da suka saba Amma shiru kakeji Akan fasuwar Auren, Amma ina!sun ba shi ya ci! sun ba shi ya sha! sun zuwa Masa ya ta ka!Amma ina Auren Sa'adatu dai yananan, iDan Allah dan ya sakawa mutane daya wa ne yasa Sa'adatu shigowa cikin su ne oho😇
Bangaren uwar gayya kuwa Hajiya ikilima 'kawa kuma Aminiya ga Sa'adatu Duk abunda kishiyoyinta sukeyi ta na Jin su ta na ganinsu, ta sa Audiga ta to she kunnuwanta,
Taji labarin Auren Sa'adatu ga mijinta Amma har yau batayi ma sa zancen ba yadda bai gaya mata ba I tama bata nuna ta sani ba, sun taci a HAKAN, Amma fa can 'kasan zuciyarta kam ALLAH ne yasan me take 'boyewa!
Sai harkokinta takeyi ta toshe kunnanta ga maganganun sauran Aminansu da kishiyoyinta da suke mata na Auren Sa'adatu d'in.
Hajiya ikilima fa Hmmm! Sanin halinta sai Allah Allah ne yasan meta kullata Akan Sa'adatu.
Amarsu Sa'adatu ko ajikinta cin Amanar da tayiwa Hajiya ikilima, ta sha fe a cinya, harkokin gabanta ta keyi, sai shirye shirye takeyi hankalin kwance, koda yake mene aciki Duk amincinsu da Hauwa facalarta matar 'kanin mijinta haka ta Aure mata miji balle Aminiya matar abokin miji.
'Bangaren Gi dansu Ibrahim bala Mijin Zahra ma sai shirye shiryen biki ake, abun ka da d'an ga ta akwatuna dozen y'an uwansa suka had'a Masa abunka ga Auta! sai tausayawa Zahra suke na halin maraicin ta,Hajiya Maimuna surukarta kam ta na son Zahra, tun da d'an autanta ya nuna yana sonta ita ma take sonta, kishin da ta Fara da ita Duk ta sauke shi da Zahra d'in, farko ma ita Allah haka ya halicceta da kishin Amma yanzu kam ta daina Akanta, Lallai Zahra Allah ya taimakeki ya dubi maraicin ki allah yakaimu lokacin lafiya,
Ibrahim bala ya kammala gidansa Mai kyau da tsari sama da 'kasa ne Mai shegen kyau sai Wanda ya gani, ku hango gidan d'an autan masu kud'i Wanda yayyansa Duk matane zaiyi aure Kum suma Duk ma su kud'in suke Aure, Zahra Allah ya lad'd'afa miki saura su Hadiyyah da Hidayah d'ina suma..
Ankawo lefen ma sha allah y'an uwa da abokan arzi'ki sai zuwa gani akeyi Duk da ba abun mamaki bane! Badanan allah ya d'auke musu uba Mai share kukan su ba ai da abun sai yafi haka,
Su Hadiyyah da Hidayah da Khadeeja y'an ma ta sai shirye shiryen biki suke anata murna ankawo lefen yaya Zahra,Amarya Zahra sai gyaran jiki ake na Aure sai 'kamshi ake ana wal'kiya.
Duk Wannan Hidimar da ake ba bu Zakiyyah aciki domin ta kanta takeyi, ta rame ta 'kwanjale abun gwanin ban tausayi,ga yunwa na cinta tana raraketa, Amma su y'an uwan sun ramewar yana da nasaba da Rashin kulata da sukeyi, da kuma ra shin ko shi da batayi, dan y'an uwan su na bata Abinci yanzu tun gatan cutar da tayi ta kwanakin baya, Wayyo olsa ta kama Zakiyyah iDan ta ci abincin ma baya mata magani, kamar ta sawa kan ta wuta ha ka takeji, shiyasa ma bata cin abincin in ambata, har y'an kud'i suke ba ta, sunyi tunanin da kud'in take cin Abinci tunda sun ga Tana Aiken Farouk.
Zakiyyah fa sai a hankali babu lafiya, sai Kuka take tana tunanin Mukhtar Anya ba alhakin sa bane, da na ABIE ita kam ALLAH yakawo Mukhtar gidan nan za'a yita ta Kare.
Ko da aka kawo lefe Sati uku aka saka, kawu isma'il yace ai babu damuwa Duk abinda ALLAH ya hore Masa Wanda akewa yarinya iDan za'ayi aurenta,zan mata Amma fa babu bidi'a, Lallai kam kuji fa sai kace kud'in sa Ya ra da kud'insu Amma zai fad'i WANI zance,
Duk WANI Abu da ake bu'kata na kayan d'aki, kamar yadda Alhaji Ammar bn Yassir yaiwa Zakiyyah guda biyu d'aya y'an waje d'aya y'an Gida Nigeria haka kawu isma'il ya saiwa Zahra,da sauran kayan da uba yakewa Y'ar sa wannan acikin kud'in da ake juya musu yayi ma ta Hidima,su kujeru, labulaye zannuwan ga do, da dai kayan da uba yakewa Y'ar sa idan zai aurarta,
Sai da akazo ba tun kayan kitchen kuka kawu isma'il yazo da wata maganar banza! Karku man ta fa gidan su Zahra Wanda suka ci ga do kawu isma'il Yasa musu haya a ciki,kuma yace ALLAH yakaimu Auren yaran sai Ayi musu wahalar da uwa takewa y'ay'anta dasu, ga Ranar ta zo! Acikin shekara biyar da rasuwar Ummuh Ruman,kuma tun sannan bayan kammala ginin gidan aka saka y'an haya, da akayi ma sa zancen, yabada kud'in zataje siyayyar kayan kitchen sai ya ce ai shi yanzu gaba d'aya kud'in hayar da yake hannunsa gaba d'aya dubu d'ari biyu ne, Lallai kam acikin shekara biyar fa gida kamar irin nasu Zahra d'in Wanda suke zama acikinsa fa ace a cikin shekara biyar dubu d'ari biyu aka Tara , sabon gida ginin ma su kud'i Ayi wannan zaluncin.
Haka babu wanda yace Masa komai kowa ta ciki ja ciki ta baka na baka, aka rabu da kawu isma'il,yabada kud'in haka sai y'an uwan Sa mata da su Baaba da kud'in da su Hadiyyah da Hidayah su ke tarawa aka harhad'a akaje akayo kata tsince tsince, abun babu ya bo babu fallasa, su flasks da y'an abubuwan da Ba'a rasa ba aka siyo, ba'aje bangaren Television da su fridge da sauran kayan 'kale 'kale ba, ALLAH sarki Zahra tayi ku ka da tuna irin shagalin da akayi a bikin Zakiyyah da irin kud'in da Abbynsu ya kashe, sai Kuka sukeyi ba ita kad'ai ba, ALLAH ya saka muku dai y'an marayun ALLAH.
Ranar Suna ta kukan ba bu dad'i Alhaji gambo yazo kuma yayi alqawarin saiwa Zahra tv da fridge, ALLAH yasa gaskene kar amarya Sa'adatu amaryarsa ta hana shi kunsan halinta.
Haka dai wannan Biki yake ta qaratowa anata shirye shirye DUK da sai a hankali.
Itama Sa'adatu tana nata Shirin, Mutanen Kaduna state su Hajiya Baaba da Hunaif da Zeenah anzo yarinya tayi 'bul'bul abunta babu takura babu hantara, kuma tana zuwa school.
Da ragowar kayan sawar Hidayah suka tawo kamar yadda Baaba tai mata alqawari,da kuma y'an kayan kitchen Wanda Baaba ta tanada matsayinta na kaaka kuma mahaifiyar yaran bata raye,DUK bidirin da akayi da kawu Isma'il su Zahra sun gaya mata tace su barshi da Allah bubu komai Yau ina iyayensu.
Biki budiri bire d'e!!
Haka fa lokaci yazo na bikin Zahra da Angonta Ibrahim an sha shagali kamar baabu gobe ranar Dinner haka na hango y'an Rashin IYAYE fans group sunata cashewa irinsu Seerat qawar Zakiyyah da Haseena Habiebty ma naganta kowanne ya sha anko abunsa nikam ina waien su y'an biyu kunsan ni da su akwai amana Allah dai yabiya Hadiyyah da Hidayah kai kwace sune amaren sun yi kyau sosai wal'kiya sukeyi ha ka akace aka sha aka gwangwaje Abun Ba'a magana Y'an uwan ango Ibrahim sun yi 'barin kud'i Ba'a magana sai nan nan suke da Amarya kamar itace Y'ar su ba angonba, itama Hajiya Maimuna surukarta itama taje wajen Dinner din sai jawo Zahra jikinta takeyi Abun sha'awa sai Wanda yagani.
Ranar d'aurin Auren ma ba'a magana dubban jama'a suka shaida d'aurin Auren Zahra Ammar bn Yasir da Angonta Ibrahim bala kan sadaki duba d'ari lakadan ba ajalan ba, kud'i yazo FANS sai su qara siyan abunda ba'a siya ba na kitchen d'in.
Hakama aka d'aura auren Sa'adatu da Alhaji gambo Allah yabada zaman lafiya.
Bayan d'aura aure sai maza ne suke shigowa ana gaisawa ana pics da angwaye, Allah sarki Zakiyyah DUK wanda yaganta ya san ba tada LAFIYA sai tambaya ake sai tace Ea,itama babu laifi tayi kwalliyarta, a masu shigowa idon Zakiyyah ya qallo mata mukhtar dayake gaisawa da mutane uw una da sa'adatu Yana Allah yasanta alkhair da kuma Baaba, Wanda hannunsa yake ri'ke da hannun ABIE Abun gwanin sha'awa yaro yayi 'bul'bul dashi shigarsa iri d'aya da ta babansa ya ro d'an shekara Hud'u Amma yayi girma kamar d'an shekara shida ko bakwai, lallai yayo jikin uwarsa Zakiyyah, da sauri Zakiyyah ta tumfaro mukhtar Wanda take ganin yagama gaisawa da mutane yana Shirin ficewa.............
Muje zuwa FANS me kuke tunanin Zakiyyah xatayiwa mukhtar?
A next page zakuji da biography d'in su Alhaji tallafy da iyalansa
Yanzu aka Fara wasan da tafiyar CIKIN Wannan labarin Mai tausayi cin amana da sauransu
✍️Oum ARQAM ce ontop
2/7/24, 4:28 PM - Rãbi'atou Aminou {Oum ARQAM}: *RASHIN IYAYE*
(Babbar musiba)
Daga *Al 'kalamin✍️ Rabiat Amin (oum Arqam)*
*08128131163*
✍️ Marubuciyar...
*Komai Nisan jifa* 📚
*Hakan ba kuskure bane*📚
*_____________*
MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION📚🖊️ *(M°W°A)*
'Kungiyar d'aya tamkar da dubu masu Nazari da Aiki da ilimi burin 'kungiyar a koda yaushe shine ta fad'akar ta Kuma wa'azantar ta Nishad'antar da masoyanta🤙
*____________*
*PAGE THIRTY TWO 32*
Shi dai mukhtar ya jiyo domin fita,sai ga Mace ta nufo Alamu sun nu na cewa wajensa zata zo,shi ya sa ya daka ta da fitar da ya ke shirin yi Amma kuma ya saki hannun ABIE, yana ma maki ita kuma wannan data ta wo gareshi wacece? A fusge ya