Showing 120001 words to 123000 words out of 141223 words

Chapter 41 - RASHIN IYAYE Complete Document by Rabi'atu Muhammad Rabi'u Oum ARQAM.txt

Advertisement

sai kin nuna halin ko? Ai shikenan bro ya nunan cewa kece tawa dan haka sai yadda nayi dake! Ya ƙarasa maganar haɗe da kaiwa ba kinka sassanyan kiss,Sai da zuciyar Hidayah ta tsinke jin abunda AKEEL y MATA,sai ta tuno da ƴar uwarta Hadiyyah koya zasu kaya da nata, ita da yake nuna Masa maitarsa a fili,shikam AKEEL yai yanzu da yayi MATA a aikace!
Ya jima bai saki bakin ba sai da ya tsotse lipstick ɗin data saka,kafin ya bari haka!murya cike da Sanyi yace karki kuma saka wannan in Zaki fita Kinga yadda bakinki yayi kuwa salon Wani ya kallemun shi ya cucan,Kinga yadda Nima kaina bakin yatafi da imanina kuwa" AKEEL ya faɗa haɗe da zaunar da Hidayah kan kujerar shima yana Zama kusa da ita yana ƙwaƙwume da ita kamar Wani zai ƙwace Masa ita! Ira dai Hidayah Babu bakin magana,tana ji tana kallo AKEEL sai taɓe taɓe yake yi a jikinta,mamaki ya kasheta sai kuma canta da surutunsa yakeyi amma ina taƙi kulashi(ba dole ba AKEEL wannan sabon al amarin da kazowa da Hidayah shiyasa ta hakan.


Hadiyyah tana gefen gadonta a Zaune jin abunda AKEEL ke faɗe yasata murmushi jin bai san kowa cece ba,sai kuma jare idanu da tayi jin cewa AQEEL ya dumfaro cikin ɗakin nasu tana a Wannan halin AQEEL yaƙaraso ɗakin,fuskarsa cike da murmushi mai nuna alamun yana cike da farin ciki,Itama murmushin yaƙen tayi, yana zuwa gefen gadon ya zauna haɗe da cirewa Hadiyyah hannun ta na dana daga haɓarta wanda ta tallafe dashi tsabar tsoron daya kasheta, "wannan tagumin na menene mine? Nazata murna zakiyi da zuwana gareki! AQEEL cikin murya mai taushi da nuna kulawa yai zancen! "Ba haka bane kawai dai ina Mamakin shigowa ɗakin da zakayi ne?
"ALLAH ko kina mamaki na kenan,wajen matata nazo fa kuma tana ɗaki dole nabiyota ai ko? Ya faɗi haɗe da tsure fuskarta da kallo 'ita kuma ta sunne kai ƙasa dan ganin Irin kallon ƙurillar da Yake mata tun daga fuskarta da ma ko ina inda idonsa ya kai! Wannan kallon fa! Inji Hadiyyah tana murmushi wannan kallon tanada ma'anoni da yawa, mamakin kamarku sa Hidayah nakeyi yasin baza'a shaida ku ba a yanzu dana shigo sai naga kamar ke nabaro a faloun ya wayance da bata wannan amsar! Amma a zahiri ba haka bane kallon tsantsar soyayya ce da buƙatuwa zuwa ga yarage Zafin abunda yakeji ne game da ita to amma ina, doctor yace Masa "matukar Yayi wani Abu na taddo da sha'awarsa al Halin bai kawar da ita ba akwai babbar matsala, wanda wannan Maganin da aka ɗorashi akai ne Yake zanyo hakan, sannan shima akwai daɗewar da yayi tana muradin abun shine sila.
Dan haka ba bayan kama hannun Hadiyyah da yayi Babu abunda yai MATA,zuciyarta sai godiya ga ALLAH takeyi, nan kuwa batasan nata gwanin ba irin na wasu bane kawai lokacin da zai fanshe bashin Hakan,ya ɗan zata da hira an danan ta saki jiki dashi kafin daga bisani AQEEL yace "to Angon Hidayah zamu fito mufa kar muyi mummunan gani ya kimtsa cike da dariya ya ƙarasa zancen Saboda yasan ya rama tsokanar da AKEEL ɗin yake Masa, Aikuwa sai da aka dan Jima sannan AKEEL ya iya amsawa (wai dama haka Akeel ɗinnan yake shima), saboda sannan shikam yayi nisa wajen damun Hidayah ta taɓe taɓen sa na babu gaira babu dalili,Duk ya takurata, "Angayama kowa irinka ne,mukam hirarmu mukeyi sai dai idan kaine zaka shiga Wani halin dan kuwa nasan Hali shima AKEEL ɗin ya rama cike da kawar da abunda yakeyi ɗin.
Da su Hadiyyah suka fito falourn a tsaye suka samu Su Hidayah ita dai sai sunne kai take zuciyarta fal mamaki,itama Hadiyyah hakan jin abunda AKEEL yace to amma ai dai yanzu gaisuwa sukayi dashi kawai bai MATA komai ba ko kawai dai tsokanar juna suke ne? Nikam oum ARQAM nace akwai Lokacin da Zaki tantance.
Duk Halin da zuciyoyin su Hadiyyah suke bai hanasu kallon Twin's ɗin Abbu ba dan babu maraba garesu sai ta glass da ɗaya yake dashi Yanzu kuwa Hadiyyah da Hidayah sun san AQEEL ne mai glass.
A haka suka fice daga gidan, Wanda Sa'adatu sai mamakin Twin's ɗin Abbu take lalläi waɗannan sai abarsu Basu da kunya gaskia daga shiga ku huta sai ku shantake waiku masu MATA ko kunya? Sai kiyi ke kaɗai sukam basusan kinayi ba ma,
Har sukaje gidan Yaya Zakiyyah sai Hira suke kowanne a motar su gwanin burgewa motar a jere suke tayi fa,Duk da Hidayah bata sake da AKEEL ba ganin abunda yai MATA, a zuciyarta sai tunanin yadda Hadiyyah ta kwashe da AQEEL take,ganin yadda take bata labarinsa baida sauƙi.
Sunje sunyi wa Yaya Zakiyyah barka an musu tarba ta mutunci,su AQEEL sun sha godiya wajen mukhtar da wannan karamci,haka suka baro gidan sai da su AQEEL suka mayar da Su Hidayah gidansu sannan sukayi gida.
An sha sunan su Twin's ɗin Zakiyyah Hassan(na'eem) Hussain(na'eef) nan na hango su Haseena da seerat da Aisha Sulaiman da MamaGee da sauran ƴan RASHIN IYAYE Fans group anwa su Haseena da seerat kara anata hada hada aci wannan asha wannan,anko naga sunyi abunsu,gasu ga mai jego,Su AQEEL ma sun koma again suda su Hadiyyah nan naga anata gaggaisawa tsakanin su AQEEL da HADIYYAH dasu Haseena kai wannan abu yayi Armashi! sunan ƴaƴan ƙawarsu ne ai nan naji wai Sunan ƴaƴan ma saboda ƙauna Zakiyyah suta bari sukawa ƴaƴan Al kunya ,Amma fa Nima sunan yamun daɗi yasin na'eem da na'eef ALLAH ya rayasu. Saura bikin su Twin's kuma bansan wane irin shagali za'ayi ba kuma!


_Kamar yadda Abbu yai alƙawari hakan akayi dan kuwa ba'ayi sati biyu ba,su AQEEL suka runtuma New Delhi chanwu university domin Exam da take gabansu dafa sun dawo kuma sai shagalin biki.




______USMAN______
Yanzu kam sai sam barka ALLAH yahadashi da wata bazawara wacce mijinta ya saketa Akan bata Haihuwa ƴan uwansa suka tilasta y saketa,saboda ya ƙara Aure matar ta Biyu ta Haihu, alamu sun nuna dai itace bata Haihuwa ɗin, Aikuwa nan danan Usman yayi wuf da ita,tunda shima Babu batun Haihuwar,ko wata Biyu ba'ayiba akayi bikin Usman da Amaryarsa zulaiha,sai fatan zaman lafiya, Usman yayi gidansa mai kyau nan ya tare sa matarsa,jimmai tayi murna da Hakan,hankalinta ya kuma kwanciya Yanzu,aikuwa dai Usman karɓe Daddy yayi sai abashi shi,shima daddyn yaso haka,baison Abban sa yayi nesa dashi.






______JIMMAI_____
jimmai cikin ikon ALLAH sauƙi sai samuwa Yakeyi saboda yanzu tension ɗinta ya ragu sosai ta kawar da Usman da ke zaune gidanta ga Shukrah Suna tare,Duk da tana zulumin mai Aurar Shukrah yanzu Alhalin batada budurci, Yanzu tana takawa babu mai riƙeta Amma dai kan ƙafa da hannu sun nakasa fa bamu sani ba ko in tanashan magani,mma tana sharar ƙafa hakama hannun yayi sanyi,a hakan tanawa kanta Abubuwa dayawa kuma tagodewa ALLAH, Shukrah kam bata sa batun aure a Ranta ita to Wanene zai aureta ne? Da wannan mummunan tabo da yayanta yai MATA aiko wanine yai MATA ta rasa miji balle yayanta,dan haka ta cire Aure a Ranta, Shukhra karki karaya ALLAH yana sane da kowa komai kuma akwai iyakarsa wannan ƙaddara ce da sakayyah Kika Gani akanki ko ba haka ba my fans!


____KAWU ISMA'IL__
komai Alhamdulillahi Yanzu zuciya ta tsarkaka yabi ALLAH Yanzu,Duk yayi Wani so silently dashi kamar ba shiba,shida Abbu yanzu sai girmamawa da mutunta juna gwanin burgewa, Hakan dama akeso ai.




Su snake sun miƙa wuya ga kotu Akan sunyi saranda Akan Abubuwan da suke aikatawa mutane na fashi da makami, sannan kuma kotu ta nemi ko Duk waɗanda sukawa fashi zasu ganesu Amma sukace ina,idan sunyi fashin ashe a banki Suke adana kuɗaɗen sai dai su siyi abun bukata wajen fashin da sauransu dan haka mutanen da sukayiwa sata Baya Baya kawai suka tuna ciki harda Kawu Isma'il dan haka kotu ta kirashi ko da Yaje andawo masa da kuɗaɗen da suka sata shi kuma na danƙawa Abbu wai a ƙara a Tallafy foundation ,shikam Abbu yace bazai karɓa ba ai dukiyarsa ce yayi yadda yakeso da ita man,nan dai kawu Isma'il ya gina masallaci da borhole yace ladan wa Abbyn su Hidayah.lallai Kawu Isma'il anyi taubatun nasuha.
Su snake Ragowar kuɗin da basusan inda zasu mayarwa da masu suba tunda wasu ba a gida suke musu ba a hanya ne ko a banki, dan haka kotu ta dinga Gina makarantu da masallatai da siyen kayan sawa dana Abinci ana kaiwa gidan marayu,anawa marashi dai hidima Akan ALLAH yakai ladan ga wanda suka cuta,wanda suka kashe kuma suda ALLAH, (wannan shine ƙa'ida a sari'ar musulunci yadda Akeyi da kuɗin hannun ƴan fashi idan sun musulunta) sannan aka yankewa su snake da yaransa hukuncin ɗaurin rai da rai a gidan gyaran Hali. ALLAH yasa mufi ƙarfin zuciyarmu akoda yaushe.








_____GIDAN ALHAJI GAMBO_______


Tuni Hajiya Sahura ta haifi ƴarta mace kuma an mayar da sunan Hajiya suwaiba ana kiranta da Asalamiyyah! Shikam Abbas tuni yayi wayo kai bakace maraya bane yayi ɓulɓul dashi,zaman lafiya sai ABunda yayi gaba tsakanin Ikilima da Sahura kamar ba kishiyoyin juna ba, musamman da mutuwar Sauwaiba ta dakesu sosai, Alhaji Gambo ma Hankalinsa ya Kwanta sosai ga kyautar ƴaƴa biyu lokacin da baiyi tsammani ba,ko Yanzu ya godewa ALLAH ai,yanawa Hajiya suwaiba addu'a a koda Yaushe.




_____SA'ADATU____


Tuni ta gama iddarta ta shiga felelenta na Addu'ar samun miji mai kuɗi,wanda zata dinga ta tsar kuɗi, dan itafa tanason namiji mai kuɗi!
ALLAH ya amshi roƙonta kuwa dan kuwa ta haɗu da Alhaji Hamza mai kuɗin gaske,matansa Uku da ita zaiyi ta huɗu,tun da yazo yake MATA ɓarin kuɗi dama haka takeso, sai murna takeyi,Amma tace Masa ya dakata Zatayi bikin ƴaƴan mijinta idan aka kammala sai Ayi maganar nata,kuma yace gidan mijinta ta saka ƴan haya, gidansa zata tare shi bazai iya zuwa Gidan Wani ba.........


Topha Fans ya wannan Aure na Sa'adatu zai kasance shin wannan ma zataci bulus ne yadda ta Saba kubiyi Oum ARQAM




Wayyo idona My Fans idonfa har yanzu da saura muddin najima da screen yadinga raɗaɗi kenan, ALLAH yakawomun sauƙi


✍️Oum ARQAM ce ontop 🥰
8/19/24, 10:07 AM - Rãbi'atou Aminou {Oum ARQAM}: RASHIN IYAYE
(Babbar musiba)




*MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION (M.W.A)*


*PAGE SIXTY FOUR 64*






______AKEEL & AQEEL______




"Cikin ikon ALLAH sun Fara exam wanda dama itace ta mayar dasu India,kuma har sannan Suna waya dasu Hadiyyah yadda ake soyayya kamar za'a cinye juna abun sai wanda yagani.


Ɓangaren su Hadiyyah ma haka abun yake,karatu yayi nisa Suma kamar haɗin baki exam ɗin suke tunkara,tuni Baaba tazo daga Kaduna ita dasu Hunaif da Zeenah tunda anyi Hutun school,da guzurin maganin sanyi ta tawo mai yawa kuwa tabawa Twin's tace sufara amfani dashi tukunnah.bata Fara Basu ba Sa'adatu ta kaiwa tai MATA bayani,Amma sai taga Sa'adatu ɗin tana Wani ciccin magani,tayi watsi da ledar dan haka sai kawai Baabah tasa Hannu ta ɗauki kayanta,tanawa Sa'adatu Addu'ar shiriya a zuciyarta dan kuwa abun nata yayi yawa.
Dan haka taiwa su Hadiyyah bayani yadda zasuyi dasu kuma su Fara abunsu,Zuciyar Hidayah akwai zulumin AKEEL tun ranar da sukaje barka wa Yaya Zakiyyah,ita kuwa Hadiyyah ko ajikinta saboda taga yadda suka kwashe da AQEEL lafiya lau!Amma fa kuma a waya ya dinga MATA sambatu da zantukan da Yake sawa tanajin kunya,a zuciyarta kuma tace iya baki ne,wai haka ne?






____GIDAN ABBU___




Mommah zata Aurar da Yaya har uku aikuwa tun sannan sai gyara gyaran gida akeyi Duk da ba Wani gyara yake so ba Amma dai kunsan idan da kuɗi Babu abunda baza'ayi ba,saboda haka ma sun bar gidan yanxu Suna Wani gidan Abbu shi wannan main house ɗin ana gyara shi ne kuma bazasu koma ba sai Bikinsu AQEE.


Ɓangaren AKEELA kam cikin ikon ALLAH sun kammala neck/waec exam, soyayya kuwa ana Shanta ita da doctor Najeeb ɗin ta,Duk da a Kullum tanajin Wani ɗaci a Ranta na cewa ita fa ba budurwa bace Duk wannan zumuɗin da Doctor yakeyi a kanta,shi kuma yana Kwantar MATA da Hankali Akan cewa shi fa ba don wannan budurci zai aureta ba,so ne da tausayi tsakani da ALLAH,kuma ai ƙaddara ce ta sameta,daga ƙarshe kuma ya ƙarasa MATA tsokana "ai tana dai na ɗinke wajen cike da bai bazan ganeba,kin manta yanzu haka zaurawa sukeyi da ƴan MATA marasa kamun kai,ta yadda mijin daya Aurensu zai zata a leda suke sai yayi murmushi! Cikin shagwaɓa kuma AKEELA tace " ba waninan kuna ganewa man, kataɓa ganin anyi amfani da sabon abo yakoma kamar yadda yake,kuma kai ai kasan komai! "Ea naji ɗin a haka nakeson ki kuma har a raina budurwa nake ɗaukarki, kar kiji komai my soulmate! Ire iren maganganun da sukeyi da doctor Najeeb kenan Duk sanda mikin baƙin cikin AKEELA ya tashi na Cutarta da Usman yayi,Duk da ta yafe masa,kuma ta samu mijin da zai rufa MATA asiri wanda shine yai MATA aikin ma.


Tsakanin AQEEL da AKEEL kam su da Usman ana gaisawa ta waya ko a haɗu online,komai ya wuce Yanzu Duk da dai Wani lokacin AQEEL yana jin raɗaɗi da ɗacin abunda Usman ɗin yai masa,to amma ai yanzu sai Mai da magana.


Itama AKEELA kadaran kadahan da Usman tunda indai taganshi saita tuna azabar daya gana MATA, ita da Shukhra kam an koma an jone dama kamar twins suke dan kuwa sa'o'in juna ne,dan haka suna mutunci tana Zuwa wajenta itama AKEELA ɗin tana Zuwa Gidan Jimmai ɗin,Duk sanda jimmai zataga AKEELA sai tayi ƙwalla da neman yafiya,ita kuma AKEELA tace komai ya wuce ai,indai zata dinga MATA haka zata daina zuwa Gidan,to tahaka Jimmai ta ƙyale AKEELA.




yanzu Usman Sa'i da lokaci yana zuwa gidan Abbu wajensa(A gurin Abbu yake odar kayan communication center ɗinsa,har wayoyi Abbu me auno Masa) haka ko Mommah su Gaisa idan sun haɗu Akan ɗanyi magana.dama shi Abbu mai yafiya ne,


Usman yanzu ma Sha ALLAH Suna zaman lafiya shida zuhaiha matarsa, kuma Daddy yana wajenta bata kuma cutarsa,hakana Dukiya ta Usman sai daɗuwa takeyi plaza anata ƙara wasu,da shawarar Abbu inda har ba shin kayansa yake bashi,kuma Usman Baya masa wasa.




Jimmai da Shukrah komai na rayuwa Usman yana tsaya musu akai, maganar jimmai ta ƙara washewa Amma fa hannu da ƙafa kam sai a slow har sannan Basu koma daidai yadda suke ba.


Shukrah anyi candy (tare sukayi da AKEELA) kuma cikin ikon ALLAH ta haɗu da is'haq ɗan sa ɗaya wajen haihuwar ɗan matarsa ta rasu,baiyi Aure ba sai yanzu da ALLAH ya haɗashi da Shukhra ɗin, ALLAH maji roƙon bayinsa, kuma Duk abunda yafaru da Shukhra is'haq yace yaji yagani yana sonta ƙaddara ce bata wuce kan kowa ba,yanzu kuma ai komai ya wuce!


Tun Shukrah bata kulashi har tafara kulashi da nasihar da AKEELA take MATA,da nusar da ita cewa tunda yasan Abunda yasameta shine rufun asirinta,Amma yanzu ta auri wanda bai sani ba akwai matsala,Duk da dai sunsan munafincin ɗan adam za'a tareshi a gaya masa,da haka Zuciyar Shukhra ta Amince da is'haq har suna waya da zuwa zance,kafin Ayi maganar Aure.






_____KAWU ISMA'IL___
Alhamdulillah kuɗi fa sai hayaƙa sukeyi yanzu,hankalinsa ya kwanta haka na Hauwa itama tana godewa ALLAH da mijinta yadawo hankalinsa,ya zubar da makaman zalunci, yanzu hankalinsu ya kwanta,tana godewa ALLAH da godewa Alhaji tallafy tunda shine tushen farin cikinta da mijinta.


Waya Aunty Hauwa taiwa su Hadiyyah tace sudawo gidanta da Zama har zuwa biki zata Fara Basu kayan gyara na amare ne,kafin afara gyaran jiki dan bazai yiwu ana gyaran jiki Suna fita rana ba,sai da suka gama magana da kawu Isma'il sannan tai musu wayar, nan suke gaya mata ma ai Baaba takawo musu na sanyi.
Ko da suka gayawa Auntynsu Sa'adatu cewar zasu koma gidan Kawu Isma'il ko tari bata musu ba sai daga ƙarshe tace "Zaku koma gidan gayyar tsiya dai, ai Isma'il azzalumi ne(kuji fa) da wannan makirar Hauwa(ke kai makira) kuje sai kun dawo ALLAH ya tsare hanya.
Zuciyar Sa'adatu ba komai bane illah baƙin ciki dan taji Duk sauyin da kawu Isma'il ya samu da kulawar da Alhaji tallafy yai Masa, Yanzu da Basu rabu ba Shikenan wannan arziƙin da ita za'a ci, ga baƙin cikin Alhaji tallafy komai sai dai yayiwa yaran nan(su Hadiyyah da ƴaƴanta) ita kam ko abun ƙwandala,sai dai arziƙin Abinci da kayan more rayuwar daya Sanya a gidan nasu wanda tasan arziƙin ƴaƴan Alhaji Ammar ne yasa itama ta dandala,kowanne yaro yanzu privet school suke zuwa ƴaƴanta Hydar, farouk,da Auta Hafsat, hakana Khadijatu(wanda tuni anzama ƴan MATA yarinya mai hankali, yanzu haka ta samu Saurayinta itama,Shikenan sai Sa'adatu tai abunda zatayi ita kaɗai ƴaƴan Ummu Rumana dai kam ALLAH ya sittura su duka,saura Zeenah kawai) wanda,da mutan Kaduna ma Zeenah da Hunaif ,Duk Wani jin daɗi suna samunsa daga Alhaji tallafy, Baabah kam gidanta kyace na Amarya ne!
sai kuma tai ajiyar zuciya bayan tagama wannan tunanin, da kuma tuna Alhaji Hamza wanda ta samu yafi Isma'il komai ai har shekaru ma.


Tun lokacin da Zancen biki ya Fara gabatowa Kawu Isma'il ya kafe kai da fata Akan cewa shine fa zaiwa Twin's kayan ɗaki komai da komai, Abbu yace ya barshi Amma yace shikam a'a,yabarshi yayi wannan haka Abbu ya Haƙura,ba ƙaramar dukiya Kawu Isma'il yai niyyar kashewa su Hadiyyah ba a Wannan biki,saboda magiya yaiwa Abbu Akan yabarshi dan ALLAH yayi Hakan kodan zumunci!


Kawu Isma'il fa sai kyautatawa yakeyi yanzu dan Zakiyyah da Zahra ma bai barsu haka ba shine siyi wancan har kayan gado ya canza musu alhalin nasu baiyi komai ba sai yace abawa marayun da za'ayi Aurensu shi fa dole ya kyautata musu abunda bai musu a Baya ba, musamman Zahra wanda Lokacin Aurena Kawu Isma'il SHAIƊAN yana kansa lokacin,su Zakiyyah kam suna jin daɗin kawunsu yanzu sai sukaga kamar Abbiy ne yadawo da kyautatawar sa garesu lokacin yana raye!
Takanas har china Yaje wajen ALHAJI(anzama Saurayi sosai) wanda Karatu yafara nisa,yanemi gafararsa,kuma shima sa'i da lokaci yana tura Masa kuɗin buƙata na kashewa dana harkar school nan ma sai da ya roƙi Abbu ya barshi sannan ya Amince,dan Hakan yanawa Abbu daɗi saboda Kawu Isma'il yana gyara kuskuren daya aikata ne,shi kuma Burin Abbu dama kenan.




Gidansu Hadiyyah na gado wanda Kawu Isma'il ya riƙe,Ashe yananan,aikuwa kafin kace me Kawu Isma'il ya Tashi ƴan haya yafara gyaran Gida, so yakeyi daya kammala gyaran gidan yadawo da Baabah gidan ta zauna saboda su Hadiyyah suji daɗi,ace dai akwai Wani naka a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login