Showing 57001 words to 60000 words out of 141223 words
Chapter 20 - RASHIN IYAYE Complete Document by Rabi'atu Muhammad Rabi'u Oum ARQAM.txt
kanmu ya baka ikon yin adalci tsakaninmu
Allahumma Ameen mar atussaliha cewar mukhtar yana tallafo hannun Bilkisu ɗin.
Bilkisu ta yi girki na tafiya asibitin, mukhtar yace kinga dai bakiyi barci ba jiya, ga Kuma yanayinki,ki zuba abincin ni da Husna da ABIE sai mu koma ke kuma ki wuta, ta so wutawar dan haka tace to shikenan zaujin saleh ALLAH yakaimu gobe na je.
Hakan akayi Husna da Bilkisu sun haɗa abinci mai rai da lafiya do akai asibiti wajen Zakiyyah, haka suka tawo asibitin da Husna da ABIE akabar Bilkisu a gida domin ta huta, da saƙon aiwa Zakiyyah ya mai jiki.
Koda mukhtar ya koma asibitin acan ya tarar da Hajiya(kunsan dai Zakiyyah ƴar lelen Hajiya ce, badon taiwa kanta ba) itama har Baaba tazo, nan dai akaita shiwa mukhtar albarka Akan cewa Zakiyyah inta samu sauƙi ɗakinta zata koma.
Zakiyyah kam ta na samun kulawa, tasha allurai da ruwa da jini da yawa,jikinta alhamdullillahi ta Fara samun sauƙi, kullum mukhtar sai ya zo gurinta,da kuma girkin da Bilkisu tayi akawo hakama Bilkisu tana zuwa sa'i da lokaci.
Baaba tana asibitin gurin jinya, Amma su zeenah da Hunaif suna kaduna saboda makaranta acan ta barsu.
Su Hajiya ikilima, da Hajiya suwaiba, da Hajiya sahura Alhaji gambo ya umarcesu da suke, Amma Kowacce daban ta zo, su Hajiya sahura da suwaiba ba su kula Sa'adatu ba dama kuma can basa shiri da ita, balle yanzu ta Zama kishiya kuma, ita dama ƙawar Hajiya ikilima ce shiyasa tun farko ba sa ga miciji, sun wa Zakiyyah ya jiki da abun alkhair ɗin su, sun gaisa da Baaba Amma Sa'adatu lala_lala.
Koda Hajiya ikilima tazo Duk mutuncin nan da ake da Sa'adatu ko kallon ta ikilima batayiba, sai dai jinjina kai da ƙwafa da suke "Lalläi kam naga har wata ƙiba Kika Fara ko? Da Sannu Zaki tsiyaye kamar mai a fashashshiyar leda, abunda Hajiya ikilima take ayyanawa a zuciyarta kenan, lallai Sa'adatu na tausaya miki.
Amarya Zahra kam ta zo duba ƴar uwarta, Ango ibrahim shine ya kawota da kansa, sunyi shar abunsu musamman Zahra harda wani fari da ƙiba da ta Fara, to tana cikin kwanciyar Hankali, kuma yanzu kuma haka aiki ake nemar mata,domin takardu sunyi kyau,ta ci exam ɗin ta,kunsan dai burin Zahra ta Zama Ma'aikaciyar jinya,kuma Ibrahim yace zai cika mata shi, ALLAH sarki Zahra kin fito daga ƙangin bauta,ga suruka da ƴan uwan miji kowa na sonta,kekam kin dace Nikam nace saura ƴan biyun mu Suma.
Kawu isma'il a tsaitsaye yazo dubiyar ya fice, kunsan dai sai a Hankali yana cikin matsala, Hakama Hauwa da ƴaƴan ta sunzo taiwa Zakiyyah nasiha sosai, Akan ta gyara halinta,taga dai yadda ALLAH yayi da ita.
Satin Zakiyyah biyu a asibiti ta samu sauƙi Alhamdullillahi, kuma a ranar aka ba su sallama,tare da nasihohi ga likita Akan adaina bata MATA rai, sannan kuma ta kiyaye shiga damuwa,ta dinga cin abinci da Shan magani kuma, in Sha ALLAH zuciyar data Fara samun matsala zata warke gaba ɗaya (Nikam nace ai cuta ta ƙare da ma mukhtar ne sai kuma Rashin abinci, yanzu kam Duk ansamu sai fatan warkewa) A haka suka dawo gida.
A washe gari kuma su Hadiyyah da Hidayah sukaje suka mata ɗan gyare_gyaren da ba'a rasaba, da wanke_wanken Abubuwan da sukayi ƙura a gidanta da Baaba Sa'adatu Hadiyyah da Hidayah sune suka MATA rakiya zuwa gidan mukhtar ɗin mu,Bayan tasha nasihohi da faɗa Akan yanxu dai yaga yadda rayuwa tayi da ita, in kuma bata canza Hali ba shikenan, matsalar ta ce....Ƴan team ɗin Zakiyyah ku matso kuna inane su Seeerat da Haseena, MamaGee Aisha sulaiman,Maman eyshat,mummy Waleed da sauran ƴan team ɗin Zakiyyah ku fito kunce harda ya yi zakuyi Ranar da Zakiyyah ta komawa mukhtar,da kuma ɗimbin nasihohi a gareta,da kuma gyara sai su fito kam gata dai a gidan mukhtar......
Murna a gurin ABIE ba bu dama, da Abbansa yace Masa "ummunka dai na dawo maka da ita" Sai yace "Amma da Ummunah da Ammie nagancu ba a tale ba? Mukhtar yace "eamn Kowacce gidanta da ban, ABIE aina zaka zauna to? Mukhtar yana murmushi yake maganar haɗa da shafa kansa, inanan inacan Abbana cewar ABIE (dama kunsani Basu da nisa tsakanain gidan Bilkisu da Gidan Zakiyyah.kunji ɗan nema......
**************
"Innalillahi wa Inna ilaihi rajiuuun me kake cewa Alhaji buubah? Kawu isma'il ke wannan maganar cikin ta shin Hankali a zaune yake Amma ya Miƙe tsaye!
"Kwarai dagaske kuwa isma'il kaya dai anyi odarsu ma Sha ALLAH,Amma cikin ikon ALLAH kuma daga jirgin har kayan gaba ɗaya sun nutse a teku gaba ɗaya,ta shin Hankali wanda ba'a sa Masa rana,Kawu isma'il ya shiga cikin bala'i yanzu dai ko biyar bashi da ita, a kuɗinsa wanda yake juyawa, kuɗin marayun Suma an damfaresu, yanzu haka akwai bashin 30millions akanshi na banki wanda yasan shi dai banki baya lamuni,tozartaka ne zaiyi, A gurin sa 15millions din da zaiyi gyaran gida ce ta rage masa a hannunsa kawai, yanzu ya zaiyi da ita ne? Ko dai ya mayarwa banki waɗannan In yaso da ga baya ya cika musu! To da wane kuɗin? Gidan su Hadiyyah dake hannun sa, ne ya Faɗo ma sa a rai Amma ta yaya zai siyar? Wata zuciyar ta bashi amsa,
Tun bayan gama wayar da sukayi da Manager na mummunan labarin da ya bashi ya nutsewar jirgi da zunzurutan kuɗin sa gaba ɗaya na jari da kadarorin sa ya siyar a haɗa kuɗin, ALLAH yaso shi kaɗai ne a ɗakin Hauwa bata kusa,dan haka yaso ya danne damuwar sa,Amma kuma Hakan yaci tura(kuɗi fa ba wasa ba,kunsan dai Kawu isma'il da kuɗi musamman ace nasane waɗannan,mugu Amma nasu Hadiyyah da akayi yahoo ɗin su bai damu hakaba?)
Hauwa ta so taga cewar mijinta ya na cikin damuwa amma da ta tambayeshi me yake damunsa? Cewa yayi zazzaɓine kawai dan Haka ta bashi magani,ya Sha ya kwanta,yaumshe idanu kamar yana barci Amma ina! Ba barci yake ba zuciyar sa ce take ƙuna da ɓacin ran rasa dukiyarsa baki ɗaya,ga bashin banki,sukuku Kawu isma'il yazauna a wannan yammacin ko fita bai ƙara ba.
Har yara suka dawo daga makaranta sukaga Abba,yace musu bayajin daɗine,har zuwa dare suka gama abunda zasuyi,suka kulle kofofin gidan gaba ɗaya dan shirin barci.
Wajen 12 na dare Hauwa ta na kwance ta Fara jin harbe_harbe a unguwar, dan haka tasan tabbas yau unguwar ba bu lafiya kenan, ƴan fashi sun shigo musu kenan,dana wannan tunanin ta ji harbi a cikin gidan, innalillahi wa Inna ilaihi rajiuuun Hauwa ta ambata kenan yau ƴan fashi gidansu suka kawowa Hari!
Tashin Hankalin da Hauwa take ciki da jin komai shima Kawu isma'il yaji wanda shima ba barci yakeba,dama likimo yayi sai tunani yakeyi Hakan yasa ciwon gaske na kai ya rufe shi,shine fa yaji harbi,cikin tashin Hankali Hauwa ta taɓa Kawu isma'il tace "Abban meenal kaji ƴan fashi cikin gidanmu! Kamar me barci ya tashi firgigit yana sallallami, kafin a rude suka tashi suka tafi ɗakin yara, sun samesu suna barci dan haka suka kullo musu ƙofar da key adai_dai faloun da suka isa ne kuma..........
Wayyo ALLAH Kawu isma'il😢
Anya kuwa zai I shanye waɗannan tagwayej bala'oin😄 batare daya gayawa kowa ba,koda yake da alama su SNAKE ne suka kawo agaji😢 Kawu isma'il ALLAH ya kareka daga sharri🙏
Zakiyyah kuma ankoma gidan mukhtar💃
Sa'adatu kam bani da bakin magana🤐 Zaki ganine komene!
Mike zuwa....
Yanzu aka Fara wasan yasin😄
✍️OUM ARQAM ce ontop🥰
2/7/24, 4:28 PM - Rãbi'atou Aminou {Oum ARQAM}: *RASHIN IYAYE*
(Babbar musiba)
Daga *Al 'kalamin✍️ Rabiat Amin (oum Arqam)*
*08128131163*
✍️ Marubuciyar...
*Komai Nisan jifa* 📚
*Hakan ba kuskure bane*📚
*_____________*
MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION📚🖊️ *(M°W°A)*
'Kungiyar d'aya tamkar da dubu masu Nazari da Aiki da ilimi burin 'kungiyar a koda yaushe shine ta fad'akar ta Kuma wa'azantar ta Nishad'antar da masoyanta🤙
*_____________*
*PAGE THIRTY EIGHT 38*
Lallai kam team ɗin Zakiyyah naga anata murna da komenta anci ansha harda su anko, tariya kamar Auren fari, to ALLAH yasa dai ƙawar taku ta fitar daku kunya wajen Sanja halaye saɓanin na da 😒🤨 idan ba hakaba yasin Bilkisu Babu ruwanta wannan karon sai dai Zakiyyah tayi tafiyar da Babu dawowa🤣💃
"Gidan su Sa'adatu kam yanzu yazama shiru kakeji, ALLAH yaiwa Zakiyyah ɗagawa sai fatan zaman lafiya mai ɗorewa a gidan mijin nata.
Sa'adatu ta Zama ita ɗaya abunta, Duk yara ana makaranta, sabo tirken wawa Duk da bawani abune yake haɗasu da Zakiyyah ba yanzu da ba bu ita a gidan sai taji ba bu daɗi ..lallai Sa'adatu gidan mijinta ai yafi ye mata nan gidan, kuma ma itada ba a gidan ta tasoba ko mugun nufi gareki😒 yau dau na tarewa Zakiyyah.
hankalin Hadiyyah da Hidayah ya kwanta sosai yanzu Yaya Zakiyyah ankoma gidan miji, kullum suna ma ta addua akan ALLAH ya gyara mata halayenta, yasa karta koma irin halin baya Nikam oum ARQAM nace Allahumma Ameen tagwaye.
Kuma har sannan su na zuwa school abunsu cikin NASARA, basa kula kowanne namiji, saboda mus'ab Saurayin Hadiyyah akwaishi da ɗan banzan kishi, bayason ya ga kowanne namiji ya kulatan, ita kuma da ma baisan Hakan takeba karatunta tasaka agaba, maza Basu isheta kallo na, har yanzu ma ƙawa mace batayi ba, ƙawarta ƴar uwarta Hidayah, tare suke Zama waje ɗaya abunsu, yan class ɗinsu suyita mamakin, wannan kama ta su hakanan, su fa basa ganesu komai iri ɗaya, sai in suna tattaunawa tsakaninsu ƴan ajin suna kallonsu anan suke ganin ɗaya tafi Jan ɗaya da Hira, ma'ana Ɗaya tafi ɗaya surutu, Mus'ab shi dama Hakan yakeso, kuma suna cigaba da soyayyarsu mai tsafta, Duk da dai Mus'ab ɗin kullum cikin busy yake baya bata wata kulawa sosai, ta fannin soyayya, Hadiyyah tana ganin yadda wasu ƴan matan suke soyayya wayar safe daban ta rana daban ta dare daban, Amma ita sai a slow basosai Mus'ab yake kiranta ba, wataran ma sai a online kawai zasu ɗan zanta idan bata hauba shikanan, bazai Kira yaji lafiya ba, Mus'ab kam wani bauɗaɗɗan namiji ne, wanda itadai Hadiyyah take sha'anin ta itama,karatu ne a gabanta shiyasa bata damuwa da halinsa.
Hidayah kam kunsan halinta dama na miskilanci, in Mahmoud ya kirata a waya sai taga damar ɗauka ma, ko bai kiraba bata damuwa,shima suna ɗan tarayyah da Mus'ab wajen halaye akwai kishi shima bai amince ta saurari wani namijin bayan shiba, kuma dama bata kulawa, shi yasa ita kam Babu wata damuwa ta ɓangaren ta nacewa baya ba ta kulawa ko wasu ba haka suke soyayya ba, shima ba sosai yake kiranta a waya ba,sai sa'i da lokacin shima.
Haka waɗannan tagwayen suke rayuwarsu ta ɓangaren karatu ma Sha ALLAH, ɓangaren soyayya ma dai hakanan, Basu da damuwa.
Kuma Duk waya kulawa Alhaji tallafy yana musu tun daga kan kuɗin school Duk wata yake tura musu ta account Duk suna dashi, littattafai ma hakanan yana siya musu da sauran handouts, Basu da damuwa.
Kuɗin school yana musu yawa(Alhaji tallafy yasan da haka saboda su dinga kashe wasu matsalolinsu ne) aikuwa sunayi Duk wani abun buƙata, Pad ɗan kayan sawa haka na yayi, takalmi jaka,tura ruka, sabulun wanke gashi, dan kuwa akwai gashin ma Sha ALLAH, ko wataran suje saloon(lallai ƴan biyu anfasi gari) da sauran abun buƙata da kuɗin school sukeyi kuma har su samu rarar wasu kuɗaɗen, Hakanan sukewa Khadija ma saboda ta Zama itama ƴan ma ta, yanzu fannin abinci sai godiyar ubangiji suna samu suci ko Babu yawa, sai su siyo wani abun da kudinsu su daɗa, Albarkacin kaza, ƙadangare ke samu yasha Ruwan kasko, Alhaji gambo ke ajiye abincin,sanadin Auren Sa'adatu dayayi, yanzu kam ma Sha ALLAH suna cikin rufin asirinsu dai dai gwargwado, kuma sani aiki da Sa'adatu take sakaso yanzu basanan, ina aikin ma yake ne, sai kuma sun dawo irin su wanke_wanke da shara sai wanki da suke ɗanyi, daga nasu saina Hafsat da Hydar, kiyi haƙuri ƴan biyu shima wannan ɗin lokacine.
**************
Kawu isma'il suka zuwa falour suka tarar da ƴan gashin har sun duro cikin ga su a falour ma, su biyar ne ƴan fashin kowanne da bindiga a hannun sa, a tsaitsaye, suka ƙaraso wa kuma suka ɗau saiti da bindigar gurin saita kan Kawu isma'il da Hauwa da bindigar, sauran kuma suka Fara bincike a flourn suna ina kuɗi! Ko mu fasa kawunanku da harshashin wannan bindigar!
Jikin Kawu isma'il dana Hauwa Ba bu abunda yake sai kakkarwa da tsima, Hauwa sai salati takeyi, shikam Kawu isma'il yakasa salatin ma, ya Zama kamar butun butumi a tsaye,
Babban su wato Snake yana hakimce a ɗaya daga kujerun flour kai kace gidan ubansane mo gidansa,ya ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya.
"Ya Awale ku fa ra sassaɓa masa kamanni tun da ana maganar ina kuɗi yaƙi magana" cewar Snake ya ciccije baki
Aikuwa Awale kamar Kira yake shida Funkaro da kuma duwalle (kaji wasu irin sunaye ALLAH ka shirya al Umar muslim baki ɗaya) nan suka saka bakin bindiga suka Fara dukan Kawu isma'il da shi!
Makyarkyata ya kama da kuma sa ihun azaba!
Ku ƙyaleshi hakanan yadawo hayyacinsa yanzu inji Snake!
Duwalle ne yakuma ma sa tambaya ina kuɗi suke?! Bakin Kawu isma'il har rawa yakeyi wajen cewa suna can! Yana nuna musu ƙofar Ɗakin sa, saboda anan ya Adana jakar kuɗin, ko Hauwa batasan da itaba.
Ba nuna Mana zakayiba ehe tashi zakayi ka ɗauko Mana!cewar Snake kamar irin kuɗinnan nasu
Ai da sauri Kawu isma'il ya Miƙe yana ɗingisa ƙafa, dan ana suka bubbuga Masa bindigar,daƙar ya iya kaiwa ɗakin,cikin durowa ya buɗe ya ɗauko jakar ya muƙawa Funkaro, yakuma tiso ƙeyarsa zuwa falourn.
Har sannan Hauwa tana durƙushe a gaban su an saita kanta da bindiga, sai salati takeyi kafin, snake yayi MATA tsawa da saurara Mana hakanan! Gum Hauwa tayi jikinta yana tsima, adai dai kuma nan ne su Duwalle suka taso ƙeyar Kawu isma'il da jakar kuɗin!
Hauwa ta Sha mamakin aina Kawu isma'il ya samu waɗannan kuɗin, haka a gida, shi da yace ya sa jari waɗannan kuɗin fa, ko kuɗin marayun ALLAH ne kuma?
Tana wannan tunanin ne Snake da duwalle ya miƙawa jakar kuɗin, ya buɗesu kuwa sai ga ƴan rafa_rafa na dubu_dubu sabbi farare, yanata fito da su, Har sannan Hauwa ta na cike da mamakin waɗannan kuɗin aina mai gida ya samesu hakanan, tasan yanzu yana tashan kuɗi Amma batayi tunanin akwai kuɗi a gidan ba,
Kawu isma'il kam yana tsugunne shima a gefe,yana ganin ana fito Masa da kuɗaɗe waɗanda sune suka rage masa,kuma ma banasa bane, na bankine a hakanma sauran sa 15million, tunanin hakanne yasa zuciyar Kawu isma'il harbawa da sauri, dage kirjin yayi jin abinda Snake yake faɗi!
Waɗannan kuɗin ba haka suke ba,ina kakai ragowar idan ba hakaba kuma...
Ragowar kuɗin kenan ai nayi amfani da sauran! Kawu isma'il ya faɗa cike da raunin zuciya!
Oh ka rage Mana kuɗinmu kenan saboda cuta(lallai ma kuji fa son zuciya a wajen Snake) meka yi dasu! cikin tsawa Snake ya faɗi Hakan
Da raunin zuciya da na murya Kawu isma'il ya faɗawa Su snake cewa wannan ma kuɗin banki ne ya ranta, rabin kuɗin yayi odar mota kuma yanzu Hakan baisan inda mutanen suke a ma'ana an damfare kuɗin, waɗannan ragowar ne yatawo dasu gida zaiyi gyaran gidan, kai har odar da yayi da nutsewar jirgi Duk ya faɗa musu,Kawu isma'il fa yafara fita daga hayyacinsa sai zubar zance yakeyi,har hannun jarin da ya saka da kuɗin su Hadiyyah Saida ya fallasa(innalillahi🙆♀️) wannan batasa su Snake sunji tausayin sa ba saima ƙara Masa duka da sukayi, nacewa Duk waɗannan dukiyar ya salwantar ai da yabari sunzo ai rabon sune, ALLAH ya isa kawai cewar su Snake ɗin suna ficewa daga gidan bayan sun tafi da kuɗin jakar da sumar da Kawu isma'il ɗin, itadai Hauwa tun zubar zancen da Kawu isma'il yafara tasa Kuka Akan mai gida ka cuci kanka ka cuci marayun ALLAH sakayyah kaɗan kafara ganin, cikin Kuka taketa ire_iren waɗannan maganganun, Hakan kuma ya tunzura su Snake itama Saida suka sammata dukan da bindiga Amma duka ɗaya a hannu, ta ke ta sume,kuma suka tsallake suka bar su nan, suka shige motar da suka zo da ita. ALLAH sarki Hauwa Kawu isma'il ya janyo miki.
Duk Abinda ke faruwa maƙota najin ƴan fashin,kuma hankulansu ya tashi, na cewa ko ba iya Gidan zasu shigi ba, Amma sunajin motar ƴan fashin ta tashi sukayi Hamdala, marasa shi na layin suka ALLAH shi ƙara, saboda Kawu isma'il kuɗinsa ba bu kyauta Babu sadaƙa, zakka wannan bayi yakeyi ba, daga shi sai ƴaƴansa,talakawa nawane a layin suke kawo kukansu gareshi Amma ya sa ƙafa ya Shure, har masu kuɗin layin sunsan Kawu isma'il bashida kirki ko ƙadan, shi yasa ba su damu ba da ƴan fashin suka shiga gidansa, aida baza'a rasa wanda zai Kira ƴan san da ba... (Wannan nasihace ƴan uwa daga oum ARQAM "kusani kyautatawa maƙota yanada tasiri sosai koda singa wani abu na cutarwa zasu iya ije maka ta kowanne Hali, koda ɓarayi ne suka zo maka bakanan sai indai ƙarfin su ya kare, ko gobara ta tashin maka bakanan zasu kare maka gidanka Amma idan bakada mutunci suna kallo za'a shiga ai maka sata suke gwanda wannan bashida mutunci ai masa ɗin, Hakama suna kallon wuta tanaci bazasu kashe maka ba,inda suna da kalanzir ko fetur ma zasu iya ƙarawa wutar saboda komai naka ya ƙare tunda baka tausaya marasa shi idan mutum ya kawo maka matsala baka warware Masa,irin dai halin Kawu isma'il, hakama a musulunci makoci yanada haƙƙi Akan maƙocinsa, wanda Manzon ALLAH saw yace jibril ya dingamin wasiyya akan maƙota har Saida nayi tunanin maƙoci zai gaji maƙocinsa, saboda irin girman hakkin maƙotaka, hakanan ko maƙocinka ba muslim bane akwai haƙƙi Akan ka dayawa nasa,Inaga kuma muslim yakamata ƴan uwa mugyara musan cewa maƙoci ɗan uwane, kuma kudinga saukewa juna haƙƙoƙi,wani fannin maƙoci yafi ɗan uwa saboda ina ɗan uwan naka yake abu zai sameka kafin ɗan uwanka yazo maƙocinka yai maka Rana,idan Babu zaman lafiya kuwa ai kafin ɗan uwan naka yazo koma mene ya faru ƴan uwa mu kiyaye)
Duk wannan bala'oin da iyayen suke cike ƴaƴan Basu sani ba, suna barci kuma hakanan dama akwai nauyin barci, mai wayon meenal ce zatayi 12_13 years sai ƙasa da Hakan,Umma ke tashin su da asba, yau bata tashesu ba har gashi gari ya waye, dan