Showing 75001 words to 78000 words out of 141223 words

Chapter 26 - RASHIN IYAYE Complete Document by Rabi'atu Muhammad Rabi'u Oum ARQAM.txt

zata aiwatar.


Haka jimmai da Ɗalhat suka tare, ita ke kula da AKEELA, ta goya ta sauke Amma bata shayarta ba,madara ake bata, sai kuma jimmai ta ƙalla Ido Akan su AKEEL da ke wajen Ummu Ruman ta ƙarkashin ƙasa tabi ta farraƙa su rana tsaka ƴan biyu, dama suna zuwa gidansu kodan ƴar ƙanwarsu akwaisu da son yara dan Haka suna zuwa,wani zuwa kuma sai suka ƙi dawowa wajen Ummu Ruman ɗin, jimmai ta ƙulle baƙin su shi Alhaji Ammar BN Yasir baice meyasa su ƴan biyu Basu dawo ba haka ma itama Ummu Ruman bata tambaya ba.
Haka zaman yaci gaba da tafiya,ba bu irin muguntar da jimmai batawa ƴan biyu, bata ba su abinci ga duka a zagi,Amma ba a gaban idon Ɗalhat ba,dai taga bayanan tukunna, shi AQEEL da ma can bamai yawan surutu bane, idan ya zauna sai yayi shiru AKEEL ne ma me ƴar ƙuriniya da surutu ga ɓarna, aikuwa yana Shan duka wajen jimmai,
Tuni lokacin Ummu Ruman ta na da zahra har tayi wayo ma abunta itama.
Ƴan biyu ba bu kalar azabtarwar da jimmai bata musu,asiri kuwa tuni taiwa Ɗalhat yanzu a gabansa take musu bashida bakin magana,ya na kallo, lokacin ma Sha ALLAH Ɗalhat ya kammala karatunsa ya ka ma aikin gomnati, tuni ya sai mota kuɗaɗe sun zauna a hannu, tun farko da ma shi ALLAH ya yishi da son taimakawa na ƙasa dashi indai ya na da abu sai ya bayar, maƙotansa ma yana kyautata musu, balle ƴan uwansa kuma, sai son barka.
Jimmai bata haihu ba har sannan AKEELA ta tasa, Ummu Ruman matar Ammar BN Yasir ita kuma ALLAH ya bata ƴan biyu Duk MATA,itama zo kuga murna wajenta, abun nema ya samu, ALLAH sarki Ummul khair , ALLAH baiyi zata ga ƴa biyun Ummu Ruman ba, dan intana nunawa su AQEEL da AKEEL ƙauna sai yace ALLAH kema yabaki ƴan biyun nan dai, in mata ne sai mu haɗasu Aure,idan maza ne kuma sai su Zama abokai kuma ƴan uwan juna!
shima Ammar sai murna yake, shima hakanan Ɗalhat ya dinga hidima da su Hadiyyah da Hidayah, aikuwa su AKEEL da AQEEL a Karo na biyu, suka dawo gidan Ummu Ruman sanadin su Hadiyyah, dama kunsan akwaisu da son yara,abun ya musu daɗi sosai yara guda Biyu Iri ɗaya, kowannen su ya ɗauki ɗaya, yace itace ta sa, Hadiyyah akwai rigima ita AQEEL yake ɗauka bata minti biyar zata Fara Kuka, haka zai dawowa da Ummu Ruman ita ransa a ɓace, ganin shi AKEEL tasa Hidayah bata Kuka idan ya ɗauke ta har sai ya gaji ya dawo da ita dan kansa, idan kuma AQEEL yace wa AKEEL yabashi Hidayah sai yace Masa a'a ina taka kaje ka ɗauko Mana, a haka suke rainon su iyayen suna musu dariya ganin, yadda suke ta shirme Akan su Hadiyyah da Hidayah waɗanda Basu san sunayi ba, su ma su AKEEL da AQEEL ɗin yarinta nada munsu, dan haka idan ana wannan diramar Ummu Ruman ko Ammar sune masu musu vedio ko photo,har lokacin da su Hadiyyah suka Fara wayo, sai ku ma ta ɗan daina rigima idan AQEEL ya ɗauke ta yana Fara mata wasa zata kama dariya, shi kuma hakan yana birgeshi, yai MATA wasa ta yi dariya, saɓanin Hidayah ita kullum fuska cunkushe har sannan bata fara dariya ba, AKEEL yai tai Mata wasa ba bu dariya, shi kima AQEEL shi ma yasamu abun tsokana, suyita dariya shida ƙanwarsa Amma ƙanwar AKEEL ba bu dariya, Kunga kenan AQEEL ya rama shi ma kenan, aikuwa wannan abu na ƙonawa AKEEL rai sai ya kama Kuka yana shure_shure, a haka fa gidan Ammar BN Yasir yake kasancewa shima idan Ɗalhat yazo ana wannan rigimar aita kwasar dariya, shi kuma AKEEL na kuka, ana Masa vedio ko photo yanawa Hidayah wasa Amma fa fur taƙi dariyar..............




Muje next page muƙarasa acan akwai sauran badaƙala a gaba tsakanin Jimmai da Ɗalhat da kuma ƴaƴansa AKEEL da AQEEL.....




✍️oum ARQAM ce ontop 🥰
2/9/24, 1:57 PM - Rãbi'atou Aminou {Oum ARQAM}: *RASHIN IYAYE*
(Babbar musiba)




Daga *Al 'kalamin✍️ Rabiat Amin (oum Arqam)*


*08128131163*


✍️ Marubuciyar...
*Komai Nisan jifa* 📚
*Hakan ba kuskure bane*📚




*_____________*
MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION📚🖊️ *(M°W°A)*


'Kungiyar d'aya tamkar da dubu masu Nazari da Aiki da ilimi burin 'kungiyar a koda yaushe shine ta fad'akar ta Kuma wa'azantar ta Nishad'antar da masoyanta🤙
*_____________*


*PAGE FOURTY FIVE 45*






Dariyar da Hadiyyah takewa AQEEL ce ta sama Masa lafiya a wajen AKEEL ɗin,haka rayuwa ta dinga tafiya.
Ita jimmai ta tsani Ɗalhat yayi mata zancen Ammar da Ummu Ruman kwata_kwata,shi kuma bai ganeba,indai zai zauna sai yayi zancen su,duk da tun farkon auren su yaso itama tazama kamar Ummul khair da Ummu Ruman amma abu yaci tura, fa fur taki yarda ta saki jikinta,in yayi magana sai tace ita dai ya kya leta ita bafa Ummul khair bace kowa da irin halinsa,kuma ma ita mijinta nabaya bayason irin wannan saboda me kulle ne to ta saba ko ma'kota bata shiga, hakan data fad'a sai 'Dalhat ya rabo da ita kawai,dan kuwa a halin yanzu shidai bai ta'ba samun matsala da ita ba, daidai gwargwado tana kamantawa y'ay'ansa tana kulawa dasu wanda shine burinsa da ma, ku ma bashida tantama akan hakan,saboda shi ganau ne ba jiyau ba,Umman sa Rabia ta kyautata rainon sa, itama jimmai hakanne ga y'ay'ansa ...lallai kam 'Dalhat besan wacece jimmai ga y'ay'ansa ba....


Rayuwa taiwa AKEEL da AQEEL wahala a gidan ubansu,duk lokacin da 'Dalhat zaije dasu gidan suna cin ba'kar wahala,basu da abinci a gidan ga d'an karan aiki da sukeyi,a matsayinsu na yara 'kanana,shiyasa basason zuwa gidannasu, saboda 'kanwar su Akeela suke zuwa gidan,suna son yarinyar,in sun cewa Abbu ya kawo musu ita gidan Ummu Ruman sai jimmai tace wa 'Dalhat d'in abun yai mata yawa ai,babu 'yan biyu sannan ita Akeela d'in ma d'auketa za'ayi, hakan ne ma yake sa 'Dalhat d'in lokaci zuwa lokaci kawo su gurin jimmai din.


Su AKEEL da AQEEL Suna tasawa kulawar su ga Hadiyyah da Hidayah tana 'karuwa suma yaran duk kama da juna da AQEEL da AKEEL suke kowacce tasan me d'aukar ta muddin aka samu akasi AKEEL ya d'au Hadiyyah tanajin ba hannun data saba ji bane, Dariyar da take batayi, karshe sai kuka ya biyo bayan hakan, shi da ma AQEEL koda wasa baya d'aukar Hidayah saboda batai masa ba,shi bayason yaro mara fara'a, shiyasa yake cikin fara'a da Annushuwa in dai Hadiyyah tana hannunsa, dan kuwa shi dai ba ma'abocin Dariyar bane,Amma Hadiyyah ta canza shi,yanzu sai fara'a da murmushi,sa'banin AKEEL ɗin mai fara'a da murmushin yanzu yazama mai kuka,saboda tsokanar da AQEEL yake masa,na cewa 'kanwarsa bata dariya,kullum fuska a cunkushe shikam 'kanwarsa dariya harda kyakyatawa,ire iren tsokanar da AQEEL yakewa AKEEL kenan, karku manta fans shima yanzu AQEEL ramawa yakeyi, irin tsokanar da yake masa lokacin Hadiyyah tana rigima..
"Me zai hana Mu had'a yaranmu aure ne aboki! A yadda nake ganin wannan sha'kuwar hakan shine daidai, kuma ko bayan ranmu zuri'ar mu zata zamo gaba d'aya! Shine burinmu daman" 'Dalhat yake gayawa Ammar a wani tattaunawa da suke I junansu!
Nima nayi tunanin hakan aboki, kaga babu wani abu aciki ai, rana kawai zamusa a d'aura Auren in yaso idan suka girma babu ruwanmu da wani daurin Aure,dan wannan sha'kuwar zata kai ga hakan!Ammar ya mayarwa da abokinsa da wannan amsar! Hakan akayi kuwa dan an d'aura Auren kamar yadda kawu isma'il ya bayyana muku.
Har sannan kuma Amincin wannan abokai yana nan,su AKEEL da AQEEL suna gidansu suna gidan Ummu Ruman, wajen kula dasu Hadiyyah da Hidayah,wanda kowa matarsa yakewa Hidima bai sani ba😂,ga azabtarwar jimmai garesu kullum abu gaba yake, takai yanzu bata shayin cutarsu,ko a gaban 'Dalhat ne sai tace laifi sukai mata, ga asirin data masa,ga kuma yana kallon ta kamar Umman sa Rabia inda bata cuce shi ba, haka itama jimmai ai bazata cutar dasu AQEEL d'inba, farkon abun inta hanasu abinci ko aiki me wuya,suna gaya masa a take zai gwale su,yace shi bayason Hakan, ai jimmai mamansu ce karya kuma ji, shiyasa ma suka daina gaya masa,sai dai suyi kuka su godewa ALLAH.itama AKEELA duk da 'kan'kantarta haka jimmai take dukanta,bata tausaya mata,kunsan maraya sai a hankali,akwai 'barna da kiriniya,middin zatayi sai jimmai da doketa,ko da a gaban 'Dalhat ne sai tace ai tafiya 'barna haka take yini idan bakanan, kasan shi kuma yaro idan ba'a tsawatar masa tashi yake a sangarce babu saiti, ko mutane su zagen suce dan ba y'ata bace shiyasa na sangartata,ire-ren zantukan da jimmai ke gayawa 'Dalhat kenan, shi kuma ai yana ganin gaskia ne,shiyasa wahalar tai yawa gasu AQEEL da AQEEL har ma y'ar 'karamar su AKEELA.


Lokacin tuni ALLAH ya had'a Ammar da Sa'adatu, Bayan Haihuwar Zahra harda 'Dalhat ake zuwa zance,wanda da farkon 'Dalhat d'in da 'kar ya amince da Sa'adatu d'in har fad'a sukaso suyi,akan me Ammar zaiwa Ummu Ruman kishiya,shikam badashi ba,har sai da Ummu Ruman ta fuskanci akwai wata a 'kasa tsakanin mijinta da Abokinsa,dan haka ta matsa masa,akan ya gaya mata mene? Amma ya'ki,sai da 'Dalhat ya kawo su AQEEL gidan bayan sun kwana biyu a gidan su,'Dalhat bai 'boyewa Ummu Ruman komai ba akan cewa Ammar ya samu budurwane, shi kuma yana ganin hakan bai dace ba, shine fa suka samu sa'bani, Ummu Ruman murmushi tayi a lokacin tace "Babu Komai ai shi aure lokacine Allah ya had'a kansu, shine fa tun daga sannan suka koma kamar da, Ammar yaci gaba da neman Auren Sa'adatu,babu matsala ga Ummu Ruman,Saadatu ta shiga ta fita sai da ta Auri Ammar dai, Ba'a jima sosai da Haihuwar Su Hadiyyah ba itama ta haifi 'Danta na fari Alhaji, har sannan dai su AQEEL suna wajen Ummu Ruman kuma suna kula Sa'adatu da d'an ta,zuwan Sa'adatu taso jan jimmai a jiji amma ta'ki bada had'in kai.


To tun bayan Auren Ammar da Sa'adatu sai jimmai take tsoron kar itama fa 'Dalhat ya 'karo Aure, da kuma wata rana yazo gidan ya tarar Jimmai tana dukan Su AKEEL ,kuma a gaban 'Dalhat d'in bai magana ba,daya tambaya dai shi 'Dalhat d'in yace ai fitina sukayi,lokacin jimmai ta kawo kai ne taji Ammar yana fad'ar "Gaskiya 'Dalhat wannan dukan yai yawa,su da su AQEEL basu da hayaniya,wane laifi sukayi da za'a musu wannan dukan!gaskia kai mata magana,'Dalhat yace shikenan zan mata magana!dama jimmai akwai haushin Ammar da takeji, tun farko na son Hanashi aurenta, ga kuma yanzu zugashin da yakeyi akan wai 'Dalhat yai mata magana dukan da takewa su AQEEL yai yawa.


Tun daga sannan kuwa indai Jimmai ta daki su AKEEL sai yai mata magana,ita kuma hakan yana damunta,kuma tana tsoron Shima karya 'kara aure, kamar Ammar d'in,kuji banza batasan Auren Ammar da Sa'adatu 'kaddara da nufin ALLAH bane..


Jimmai taci galabar raba abota tsakanin Ammar da 'Dalhat kuwa dan farra'ku tai musu rana tsaka suka rabu babu mai neman kowa,y'an uwansu ma babu mai cewa ya hakan, hakama su AQEEL kwata-kwata suka daina zancen zuwa gidan, da zancen wasu Hadiyyah.


Haka dama Jimmai take so, sai ta bud'e shafin cuta da zalunci gasu AKEEL,da mallake 'Dalhat ta hana yaiwa kowa hidima daga ita sai y'ay'anta agololi,dan suna zuwa gidan,kota aika musu,iya azaba AKEEL da AQEEL da kuma AKEELA sunasha ta,babu mai ceto sai ALLAH.


Inta kamasu da duka kamar ALLAH ya aikota,musamman AQEEL mai taurin kai idan tana dukan su baya bada ha'kuri, ko kuka sai ya cake,to tu yana neman taimako daa kuka da bada ha'kuri har ya sire,wata rana data kamasu da duka aikuwa ta kawo zata daki AKEEL da yake belt ta samu, to akwai 'karfe sai a idon AQEEL,saboda rashin tausayi kuma tana gamawa AKEEL d'in shima dama sannan batawa AQEEL nasa dukan ba,ta dawo kansa da dukan,shima garin dukan ta kuma samun sa a d'aya idon,kafin kice me sai ga jini a idon AQEEL, a sannan jimmai ta razana,amma kuma saita basar,ta d'au waya ta kira 'Dalhat tace AQEEL ya bige a idonsa, da ga sama 'karfe ya fad'o ya falle masa ido, aikuwa sai ga 'Dalhat akai asibiti da AQEEL wanda tuni ya suma saboda azaba, ta gama dasu AKEEL yadda tace 'karfe ya falle masa idanu a haka aka bar zancen, to dama akwai 'karfunan a saman gidan,wanda aka yi musu gyara dasu, kuma ALLAH baisa an d'auke ba,dan tuni akayi gyara-gyare a gidan an 'kawatashi kud'i sun 'kara zama a hannun 'Dalhat.
Sana din wannan dukan ne hasa AQEEL baya gani sosai da idanun,farko ma anyi tunanin ya daina gani, sai da aka masa aiki yake gani dishi dishi, da taimakon medical glass,duk da haka,a hakan ma angode ALLAH, dan a 'kila a 'kala akayi aikin,zai dinga gani ko akasin hakan, abun gwanin tausayi,tun daga sannan AKEEL da AQEEL suka zama abun tausayi, lokacin sun dan tasa zasuyi irin 10-11years abun ya faru,duk da haka babu abunda jimmai ta rage na azabtarwa gasu AKEEL d'in sai ma gaba, shara,wanke-wanke,girki wanki, da duk aikin gida su AKEEL sunayi,duk da akwai masu aiki komai amma ina jimmai ta sallamesu,sai tacewa 'Dalhat aikin guda nawa yake,ita dasu AKEELA ai zasu iya,kuma 'karya takeyi,sune sukeyi.




Haka shekaru suka da d'u, tuni AKEEL da AQEEL suna cikin wahala, anzama samari zasuyi 17years haka,AQEEL tun a sannan yake fa ma da ciwon ciki mai tsanani, idan yafara har fita yake a hayyacinsa,sai da aka kaishi asibiti,likitoci suka rufa akansa, da'kar numfashinsa ya daidaita, anan akai masa gwaje-gwaje da kuma hoto aka gano cewa yana daga cikin jinsin maza masu tsananin sha'awa, tun daga sannan AQEEL ya kame kansa, duk da 'karancin Shekarunsa Azumi ya mayar kamar me idan yau yaci abinci gobe xai tashi da azumi,ya kame kansa ga duk wani abu da ALLAH yai hani a aikata, tun daga sannan yazama so silent baya shiga harkar kowa, to girma ya kamashi da wuri haka,sa'i da lokaci ciwon cikinsa ya na tashi,kamar bazaiyirai ba, kuma sai ya sha suwa da allurai, kafin yadawo normal,Wannan abu yana samun 'Dalhat d'an sa guda nawa yake? Dama shekerun sa sunfi hakane sai ya masa aure, fans 'Dalhat fa ya manta da wasu su Hadiyyah fa balle auren sa aka 'kulla,amma guda nawa AQEEEL yake, 17 years ma basu cika ba, 'Dalhat yana mama kin wannan abun, koshi lokacin da yana saurayi yafi AQEEL,sha'awa ta dameshi....kunga badon Jimmai tayi farra'ku ba ai dama akwai aurensa ko fans?


sa'banin AKEEL shi kam ba bu ruwansa da wannan, yara ne masu ilimi daga addini har na boko, tuni sunyi saukar Al 'kur ani, Boko kuma suna Ajin 'karshe a secondry bana zasuyi candy,


AKEELA itama anzama budurwa ma sha ALLAH wajen 14-15years fa take,an tasa,irin masu jikin nan ne murjajje, jikinsu yafi shekarunsu.


Tuni Usman d'an wajen Jimmai yadawo gidansu AKEEL da zama, irin 'yan iskan yaran nan ne masu tasowa, da tashen rashin mutunci, Bf kala-kala yake download a wayarsa haka zaita kunnawa yana kalla,yaso jan AQEEL ya koya musa kalla, musamman yai masa nuni da cewa idan yana kalla wannan ciwon cikin zai daina kuma zai samu nutsuwa da salama..kunji dan iska, karku manta ya d'an girmi su AQEEL d'in.. amma ina AQEEL ya'ki kulashi ko shiga harkar sa bayayi,balle AKEEL kuma shida wannan yanayin bai dameshi ba.


Tunda Usman ya dawo gidan ya takurawa AKEELA, buni kad'an sai yace zai kai hannu jikinta, ita kuma bataso saitai masa RASHIN kunya akan bataso, kuma baya fasawa,Ranar da yakai hannu jikin AKEELA kuwa, wankeshi da mari tayi,aikuwa jimmai tai mata dukan tsiya akan dan rashin kunya zata daki Usman dan yana mata wasa, shine sai kuma raini, da'kar ta tashi bayan dukan data mata, da 'Dalhat yadawo ta shirya karya da gaskia ta fad'a masa cewa AKEELA tanawa Usman rashin kunya, harda mari, ba bu ba'asi an riga an mallake shi shima yaiwa AKEELA tatas akan ai yayanta ne,bayason RASHIN kunya, duk wannan abu dake faruwa su AQEEL basu sani ba, su na school exam suke................




Lallai akwai bada'kala nan gaba, had'e da cakwakiya'''''
me kuke tunanin zai faru tsakanin Usman Da AKEELA
Ya rayuwar AKEEL da AQEEL zata kasance, ga dai halin da AQEEL ya tsinci kansa aciki a 'karancin shekarunsa, sa'banin dan uwansa AKEEL me hakan zai janyo??????? Da sauran tambayoyin da suke bakunan ku muje next page






✍️oum ARQAM ce on top 😍
2/13/24, 12:45 PM - Rãbi'atou Aminou {Oum ARQAM}: *RASHIN IYAYE*
(Babbar musiba)




Daga *Al 'kalamin✍️ Rabiat Amin (oum Arqam)*


*08128131163*


✍️ Marubuciyar...
*Komai Nisan jifa* 📚
*Hakan ba kuskure bane*📚




*_____________*
MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION📚🖊️ *(M°W°A)*


'Kungiyar d'aya tamkar da dubu masu Nazari da Aiki da ilimi burin 'kungiyar a koda yaushe shine ta fad'akar ta Kuma wa'azantar ta Nishad'antar da masoyanta🤙
*_____________*






*PAGE FOURTY SIX 46*






Hakan ce taci gaba da faruwa da AKEELA a kullum burin Usman shine hannunsa yakai jikinta,kuma bata da bakin magana,Amma duk da Hakan tana gaggaya masa baƙaƙen maganganun,Amma a banza duk lokacin da yakai hannun ga jikinta, ita kuma saita kai Masa Mari ko bugu a ƙirjinsa, Amma gogan naku sai yayi murmushi kawaii, ya girgiza kai alamun ko a jikinsa,baiji zafin dukan ba.




Su AKEEL da AQEEL zaman gida yai Musu wahala, balle ko Wataran idan sunga iskancin da Usman kewa ƙanwarsu su taka Masa birki, ko da Yake ina suke da wannan ikon,Suma takansu sukeyi, Amma kuma Kota halin yayane in kaga dan uwanka a halin cutuwa ko za'a cuceshi sai inda ƙarfin ka ya ƙare, saboda hausawa sukace bakin rai bakin fama.....


Ɗalhat kam arziƙi yaci uban nada,kunsan dama abunda yake haɓɓaka dukiya shine, taimakawa ƴan uwa, zakkah, idan ALLAH ya kai dukiyarka matakin,sadaƙa taimakawa miskinai da marayu da Marasa shi, to Ɗalhat yanayi,tun dukiyarsa bata kai haka ba,balle yanzu kuma, ƴaƴansa duk wani jin daɗi suna samunsa,inka cire cutarwa da azabtarwar da Jimmai take musu, Basu da wata matsala,sai kuma AQEEL shima da matsalarsa, wanda yanashan magani sosai,kuma yana yawaita azumi, Alhamdullillahi Hakan kuma ya tsareshi daga duk wata fitina ta zamani da matasa kamarsa suke tsintar kansu aciki na samarwa kansu biyan buƙatarsu ta Zina ko kallace_kallacen banza,shikam baya ciki,ya miƙawa ALLAH kansa shi zai kawo Masa mafita, sannan Abbu kullum yana Masa nasiha da cewa ya riƙe kansa,idan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login