Showing 9001 words to 12000 words out of 141223 words
Chapter 4 - RASHIN IYAYE Complete Document by Rabi'atu Muhammad Rabi'u Oum ARQAM.txt
ya shanye Babu Mai jinyarta, kawai sai Amina mahaifiyar Ummu Ruman Takoma Kaduba state d'in take jinyar Mahaifiyarta.....
Yanzu ma rashin lafiya d'in Ummu Ruman d'in ce takawota Kano, gashi Kuma allahya kar'bi, Abarta....
Da aka share makoki ta tashi tafiya Kaduna state sai tace zata tafi da 'yan biyu *Hadiyyah da Hidayah*, Amma sai Hadiyyah tace ita bazata iya barin unguwar da aka haifeta ba, anan ummy da Abby suke San sun rasu, bazata bar unguwarba tananan itadai, cikin kuka take magana, kowa ya tausaya Mata, anan Ra'ayin tagwaye masu Kama d'aya ya banbanta, ita kuma Hidayah tace qafarta qafar Baaba wato kakarta, bazata iya zaman unguwar da take da iyaye guda biyu ba acikin shekara d'aya ta rasasu, kullum batajin dad'in unguwar, dama burinta tabarta, gashi Kuma Baaba tace zata tafi dasu......
Kowa akan Ra'ayinsa ya zauna tsakanin Hadiyyah da Hidayah, d'aya yaqi haqura yabi Ra'ayin d'aya, wannan shine ya raba tagwaye masu Kama d'aya, d'aya tana Kano state d'aya tana Kaduna state.........
Ita dama Zahra a gidansu zata zauna, karatunta yafara nisa,dasu Khadija da zeenah ma suna gidansu,Allah sarki Allah yayi Ummu Ruman bazata zauna a gidan da ake Gina Mata ba, itada Y'AY'ANTA, Dan haka a gidan Sa'adatu zasu zauna gaba d'aya, ta had'a da Y'AY'ANTA ta riqe, Dama Kuma qanin mahaifinsu ne, ze Aureta, da kud'in ribar da ake samu na kasuwanci da kud'insu, ake musu wahala.....
Saida aka had'a kayan Ummu Ruman data mutu tabarsu, kayan sawa da sauran kayan amfani aka warewa Y'AY'ANTA, gadonsu, haka sukace basaso abayarwa ummy sadaka Allah yakai hasken kabarinta itama Baaba aka bata wasu kayan.....
Kayan d'akinta Haihuwar Hunaif Abby ya canza Mata, Yan Dubai ne masu tsada saboda haka sai, Zakiyyah aka batasu, ita Kuma ta siyar da kayan nata gud'a d'aya, tunda baduka Yan Dubai Abby yai Mata ba lokacin Aurenta, da Yan gida Nigeria,saita siyar dasu, ta fanshi na ummy d'in bataso a siyardasu, ta dinga tunawa da mahaifiyarta.....
Har sannan da sauran kayan sawar Hunaif Wanda bai ta'ba sawa ba, da kayan barka da Ummu Ruman ta samu,Dan hakan aka. Tarkatawa marikiyarsa Tai Masa amfani dashi......
Saida aka kammala kasafta kayan Ummu Ruman sannan Baaba tayi Shirin tafiya Kaduna state itada Hidayah,ranar tafiya ansha kuka kamar ranar Ummu Ruman ta rasu, Hadiyyah tayi kuka kamar me saidai haka ta haqura tana kallo Hidayah tayi nesa da ita,Zahra Khadija da zeenah Suma sunsha kuka sai haquri yara, mutuwa Mai tonon silili kenan......
Haka su Hadiyyah da Zahra da Khadija da Kuma zeenah, sukaci gaba da Zama a gidan Sa'adatu,Babu uwa Babu uba, kullum sai Hadiyyah tayi kukan hakan,da Kuma rashin Yar uwarta ta haihuwa, Wanda komai sukeyi tare, a haka sukaci gaba da Zama anan suna zuwa makaranta, kawu Isma'il Yana ajiye musu abinci, yabasu kud'in cefane acikin ribar kud'in dayake zuya musu.....
An d'aura Auren Sa'adatu da Isma'il, anan gidan yake zuwa duk ranar girkinta.......
Tunda Aisha qanwar Ummu Ruman ta d'auki Hunaif Babu Wanda acikin dangin mahaifinsa dayake zuwa dubashi, duk da suna unguwa d'aya da Hajiya sakinah d'in, da wasu Yan uwan Alhaji Ammar d'in, ko biyar Kuma Shi ba'a Kai Masa ace ase Masa wani abun acikin ribar kud'in da ake juya musun, komai Aisha ke Masa, itada mijinta duk da ba wani kud'ine dashiba, Amma haka ya dauke nauyin Hunaif, har yoghurt yake siyo Masa, Yana tausaya Masa sosai, a hakan Hunaif yadinga rayuwa a gidan Aisha, itadai tana ganin ikon Allah, lallai kan Wai Alhaji Ammar d'an da akewa haka, Babu Mai kulashi, da ace Yana Raye Ummu Ruman ta rasu Aida rikon Hunaif Hunaif xazaizo hannunta ba, rubibi za'ayi a Yan uwansa, saboda duk Wanda yad'auka kud'i Alhaji Ammar zai dinga kashe masa, ga Kuma kayan abinci da na masarufi, Allah dai ya kyauta, saboda Babu idonsa Amma yanzu ko kar Babu Wanda take xai d'auki dansa riko....
Banda Amina mahaifiyar Ummu data d'auki Hidayah, sai Aisha data d'auki Hunaif, Amma sauran duk suna gidansu wajen Sa'adatu, itama ga nata, Y'AY'AN an barwa dai Isma'il riqonsu gaba d'aya, (....shima fans Allah yasa hakan ya d'ore, ba Dan zai Auri Sa'adatu take kula suba...)
*******************"
Acikin kud'in da ake juya musu ake turawa Hadiyyah can Kaduna state kud'in sabulu, da dai abunda zata buqata da kud'in, duk wata kamar yadda ake bawa Y'an uwanta...
saboda dama itama Baaba acan Kaduna state d'in ba wani kud'i be da y'an uwanta ba kawai dai rufin asiri, ga Kuma jinya da take cinye kud'in, Yan uwanta maza din kowa yanada Y'AY'ANSA, saidai rufin asiri, ga halin rayuwa sai haquri
******************
Allah sarki Zakiyyah duk yazama shiru jikinta yayi Sanyi, Allah yasadai ta canza Hali, tayi hankali yanzu, zata daina Tarawa mijinta Mata agida, da Kuma fitar gaira Babu dalili, da rashin iya magana da ga'bunta Allah yasa ta daina, Shi Kuma Mukhtar Allah yasa dai yajure halin Zakiyyah d'in, Kar yaga Babu idon mahaifanta ya dinga Mata hulakanci Kuma, Dan kuwa darajarsu takeci a idonsa................
Yanzu aka Fara labarin, abubuwan suna gaba, akwai tausayi cin amana ha'inci dadai
sauransu
✍️ ©️ Rabiat Amin (Oum Arqam 👩🍼 ce)
2/7/24, 4:28 PM - Rãbi'atou Aminou {Oum ARQAM}: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/Cy82IooiC1LE5S0e2tkKcj
*RASHIN IYAYE* (babbar musiba)
*✍️Daga Al 'kalamin ©️ Rabiat Amin Oum Arqam 👩🍼*
*08128131163*
✍️Marubuciyar.....
*Komai nisan jifa📚*
*Hakan ba kuskure bane📚*
*__________________*
*MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION📚🖊️ (°M°W°A)*
Kungiya d'aya tamkar da dubu masu Nazari da Aiki da ilimi Burin'kungiyar a ko da yaushe shine ta fada'akar ta Kuma wa'azantar ta Nishad'antar da masoyanta🤙.
*__________________*
*PAGE ELEVEN 11*
Zakiyyah tana xaman gidan mijinta, halin ta Kuma baamta fasa ba, na tara Mata da zuwa yawon makota, komai yasiyo Mata Mukhtar Nan danan zatace ya qare, tun Yana haquri da halinta harya Fara gajiya da halin nata, dama tanacin darajar iyayanta ne, idonsu yake gani ya qaleta yanzu Kuma Babu su, saura kakarta Hajiya sakinah wacce ta nuna Masa qauna lokacin aurensu......
"Yauma da zai fita kasuwarsu yace "Zakiyyah karki fita banason fitarki maqota, banson kina taramin kata a gidana, kiyi zamanki a gida, me Kika rasa,hakan dai yagama nata fad'a da nasiha, kamar taji, karku manta dai fan's Zakiyyah dai yarinya ce Kuma goyon Kaka, wacce Bata iya komai ba, sai ga'bunta da sangarta...
Yana fita kasuwa tasa 'kafa tayi ficewarta itama,ta mance fad'an da yayi Mata na fita, Wanda dama ba ranar yafara fad'an tana sa qafa tana shurewa ba, mantuwa yayi a gidan wajen azahar ya shigo motarsa yadawo gida, Yana zuwa gidan yafara bugu Amma shiru kakeji, alamu sun nuna matar gidan yau Bata Tara mata ba, yau itace ta bisu gidansu, gajiya yayi da bugu,ya dauki wayarsa ya kirawota a zummar Kiran d'aya Saba mata ne, Mukhtar yace" fatan dai kina gida Zakiyyah yau Baki fitaba ko? Babu komai acikin ran Zakiyyah tace "eamn kaganni ma barci nakeyi wayarkace ta tasheni, Mukhtar yace "yawwa haka nakeso mamata kidaina fita yawo kina taran Mata, dama yanzu ma mantuwa nayi ne akan kujera, shine can dawo na d'auka ganinan zuwa gidan, sannan Mukhtar ya kashe wayarsa, Yana mamakin lallai halin Zakiyyah yafara yawa, hardasu karya Kuma, gashi a kofar gida bayanan,Amma tace yananan, shikam zaiga ikon Allah daga gidan zata fito ko Yaya?
Ita kuwa Zakiyyah tana can wani layi, da taji yace gashinan dawowa saita maza ta fito zuwa gida,Kar Mukhtar yadawo yaga bataban, tana shawo kwana motar Mukhtar ta gani yayi parking, ya fito ya zauna akan dakalin barandar kofar gidansu, yayi tagumi, sai Kuma tayi turus, kunya duk ta kamata......
Ko magana Bai mataba kawai miqa mata hannu yayi, alamun ta bashi mukulli, a sanyaye tabashi, ya bud'e kofar gidan yashiga, ta biyo bayansa, "sannu da zuwa kadawo kaga dama fita nayi gidan Aunty na karbo kalanzir na zuba a risho zanyi girki, gas yaqare namance ban gaya makaba, shine kadawo baka sameni ba, Amma yau ba inda naje...
Cikin fushi Mukhtar yace " Amma Zakiyyah ke wace irin yarinyace marar hankali, kalanzir ajiye Miki nakeyi, saboda irin hakan, gas yaqare bada saniba, saikiyi amfani daahi,to ya kikayi da kalanzir din cikin jarkarsa?
"Aunty ce ta ara, gani nayi ba amfani zanyi dashi sannan ba, to tace za'a siyo Mata, nata na qare shine nataba, shine sainaje karba yanzu, Zakiyyah ta fad'a cikin ga'bunta da sangarta, Wanda hakan ya fusata Mukhtar sosai.....
Kaca_kasa Mukhtar yaiwa Zakiyyah, yace "babu abunda na raga Miki na abun amfani, Amma kindinga 'barna kenan komai naki baya dad'ewa yake karewa, saboda kinfi kowa iya Aiko, to wlh kin Fara kaini bango kinacin darajar su Abby da ummy yanzu, kuwa Kinga basa Raye, tunda bakisan mutunci ba, wlh duk sanda Kika 'batamun sai Kinga abunda Zan Miki, banza ballagaxa sha_sha_sha kawai , yanzu kinci darajar Hajiya, Yana nufin kakarta.....
Haka Mukhtar yayiwa Zakiyyah tatas ya qare mat tanadi, sannan yayi ficewarsa yakoma kasuwa....
Zakiyyah ranar tayi kuka sosai, tunda suke da Mukhtar vai ta'ba Mata irin cin mutuncin yau ba,lallai ta tabbata iyaye wata katangace ga y'ay'ansu, Ashe dama haka mukhtar yake? Idon Abby da ummy ne yasa take qaleta? Lallai ma, Wai a hakan ma yace saboda kaaka yai Mata wannan da sauran Ido akanta, lallai maraici masifane,(.... Fans Allah yasadai hakan ya gyarawa Zakiyyah halinta, tayi hankali tadawo hanya, tasan cewa yanzu fa komai nata ya canza Bata da gata saina Allah, Allah yasa ta riqe maraicinta...) Haka suka kasance tsakanin Zakiyyah da Mukhtar duk sanda tayi ya bud'e Baki ya wanketa tatas, saidai tayi kuka, Hmmm Zakiyyah kenan, ki daina halinki, karkikai Mukhtar bango fa .......
********************
"Bangaren Aisha kanwar Ummu Ruman kuwa, haka da dad'i Babu dad'i, take ruqon Hunaif, Kuma har sannan Bai daina kukan dayakeyi ba, na rigima, yaita kuka kenan, ga itama yaronta Mai rigima ne, Allah ya taimaketa ma rainon Hunaif Yana dawowa wajenta, sai Shi Kuma Allah yasa Masa dangana yadaina daidai kawai Hunaif d'in yayi Shi kad'ai, ga rashin barci ga kashin kwance Dana wando, rikon maraya dama ai sai haquri, Haka Aisha taketa wahala da Hunaif, yau da dad'i gobe Babu dad'i, har Allah yasa suka Kai lokacin yaye, zata yayesu, ai kuwa har gidan Hajiya sakinah ta aika cewa Allah yayi lokacin yayensu Hunaif yazo zata yayeshi, Hajiya sakinah tace " oh kuce Mata Allah ya rayashi......
Kwanan Hunaif uku da yaye, Dan rigima kenan, ai rigima ta dad'u tafi tada, sai ga aike daga wajen Hajiya sakina ta Aiko Asiya 'kanwar Alhaji Ammar Wai abata Hunaif tunda an yayeshi a had'a Shi acikin 'yan uwansa, can gidansu wajen Sa'adatu....
Tashin hankali Wanda ba'a saka Masa Rana, haka Aisha tashiga cikin tashin hankali tana kuka mijinta yana kuka, suka bada Hunaif yaro Mai shiga Rai, tasa Rai tare da Abul khairi d'anta zasu taso kamar Yan biyu, suna tafiya tare duk da Shi Hunaif tafiyar batayi kwari ba, saboda maraici ya ta'ba Shi,tayi kuka Aisha sunyi saboda da Hunaif, duk da yanada rigima, Amma tana sonsa, sai haquri Aisha Allah yaso kema kinada naki............
********************
Haka Hadiyyah da Zahra Khadija zeenah, suke zaune a gidan Sa'adatu suna zuwa makaranta, aikin gidanga komai Zahra keyinsa, itada Hadiyyah, Mai aiki Dama bayan mutuwar Mai gidan aka sallameta, Ranar girkin Sa'adatu dayake kawu Isma'il tasan zaizo yaga suna aiki Mai wahala ne kawai itama Sa'adatu takeyin aikin, Amma duk ranar girkin Hauwa a a gidan yakeba sune suke aikin komai,(...kun mance fan's lokacin da Ummu Ruman ta fita daga gidan suna qanana haka tadinga Basu aiki Kuma da me aiki sannan, balle yanzu taga sun girma Kuma Babu Mai aiki, lallai Sa'adatu halinki yananan.. )
Wankin su Zeenah, Hafsa, Hydar duk sune masuyi Hadiyyah da Zahra ita Kuma Khadija tayi nata, itada Farouk Dan wajen Sa'adatu, sun d'an girma su ai.......
Shikam Alhaji d'an wajen Sa'adatu tun bayan rasuwar mahaifinsu, dama yafara fita yawo sai yayi fitarsa a mance dashi sannan zai dawo gida, yafara had'uwa da abokai marasa kirki da Kunya, sunason Fara koya Masa shaye_shaye, wataran sai an kulle gida dare yayi sannan yake kwankwasawa abud'e Masa, sai ranar da kawu Isma'il yaje gidan sannan yake dawowa da wuri, Sa'adatu fa abunda Alhaji yake Yana damunta Amma Kuma qaunar da tasa batai Masa fad'a.....
A wannan halin Kuma Hajiya sakinah ta kawowa su Zahra Hunaif, wahalar aikin gida ma ta ishesu, ga Kuma qaramin yaro kamar Hunaif, aikinsan yadawo hannunsu shima Domin, kuwa Sa'adatu ko kallonsa batayi, balle ta tausaya ta daukeshi ta had'a da Hafsat ta rainesu, yamanta dasu kuka kawai yaketayi Babu dare Babu Rana, cikin dare yayi Kashi sau nawa, kunsan d'an yaye wasu suna Kashi, Wanda dama tun kafin yaye Shi yarone Mai kashin kawance, ya hanasu barcin dare da kuka da safe Kuma wankin Kashi, Allah sarki Zahra da Hadiyyah,idan Yana kukan Suma kukan sukeyi, Yara y'an Mata, 'kanana an had'asu da jego, mutuwa ta jawo muku, tunda Hunaif yadawo gidan, mutuwar Ummu tadawo sabuwa a garesu, idan Yana kukannan, sai sun tuna da ummy lokacin tana Raye baya yarda dasu kullum Yana gurinta ....
Wannan wahalar ta Hunaif da aikin gida yasa yaran suka Fara ramewa makaranta sai ta Zama ba kullum suke zuwaba, to wa zasu bawa rainon Hunaif?, Ba kullum suke zuwa makaranta ba, ga Zahra Mai University Kuma karatun fannin lafiya, akwai son kwanciyar hankali da karatu akoda yaushe da wannan suka Fara samun matsala.............
********************
"Hadiyyah anacan Kaduna state tunda taje garin tafara samun canjin rayuwa, Rashin y'ar iwarta Hadiyyah komai tare sukeyi yanzu sai ita kad'ai a gidan kullum sai tayi kukan hakan, harta Fara Kuma sakewa Y'AY'AN kannen Baaba suna zuwa gidan itama Kuma tana zuwa can, Saida tayi sati biyu acan sannan akayi Mata cuku_cukun makaramtar boko, tare da islamiyyah, alhmdllh komai ya kammala tana zuwa makaranta, Amma kullum tana cikin damuwa, sai Baaba tana Mata nasihar tayi haquri kowa da tasa kaddarar su tasu kaddarar itace maraicin iyaye guda biyu a tsakankanin watanni shida, ga Kuma rabuwa da y'an uwa tayi haquri kawai , aikin Baaba ga Hidayah kenan kullum nasiha, Baaba tanada waya anan suke gaisawa da y'an uwanta, sa'i da lokaci in Allah yasa akwai kud'i a wayar..............
Muje next page FANS 😭😭😭😭😭 yanzu aka Fara labarin akwai tausayi cin amana ha'inci dadai sauransu.......
Domin sharhi ko shawara ku tuntubeni a wannan number d'in *08128131163*
✍️ *©️Rabiat Amin Oum Arqam 👩🍼 ce dai*
Bissalam👋
2/7/24, 4:28 PM - Rãbi'atou Aminou {Oum ARQAM}: https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
*MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION (M°W°A)*
*RASHIN IYAYE* (babbar musiba)
*✍️daga Al'kalamin Rabiat Aminu (Oum Arqam 👩🍼)*
Marubiciyar✍️
Komai nisan jifa📚
Hakan ba kuskure bane📚
*PAGE TWELVE 12*
"Zama yayi Zama tsakanin Sa'adatu da kawu Isma'il, ana xaman dad'i, tsaninsu, gidan da take ciki yafi nasa girma Wanda matarsa Hauwa take ciki, Dan hakane ma kawu Isma'il yace ta fansar Masa da nata gidan kason Y'AY'ANTA Wanda sukaci gadonsa, ya had'esu itada Hauwa hankalinsa zaifi kwanciya,wajen kula da yara, haka yace mata, shikuma yabata nasa Wanda yake ciki sai yayi Mata cikon kud'i (...kujifa fan's Koda yake Babu ruwana tsakanin Mata da Miki be...), Sa'adatu ta Amince Masa kuwa da hakan,nana gaba Wai zai cika mata kud'in Nan gaba, tabashi natan kuwa shikuma yace xai cika mata kud'in,
Hauwa matarsa da Y'AY'ANSA sun dawo gidan Sa'adatu da Zama , Shi Kuma gidansa Sa'adatu ta kar'ba zata saka haya cikinsa...
Gidan Alhaji Ammar sama da qasa ne, su Hadiyyah da Hidayah d'akinsu d'aya, zahra ma d'akinta ita kad'ai, sauran yaran Khadija zeenah suma d'akinsu d'aya duk aqama suke, d'akin Alhaji Dan GIDAN Sa'adatu shima nasa aqama yake, sai d'akinsu Farouk da Hydar Suma su biyu a qasan, sai sama Kuma d'akin Alhaji Ammar turakarsa tana sama, d'akin Matansa ma a sama yake, babban falon gidan ma a qasa yake da dakunan Sa'adatu da Ummu Ruman ma a qasa, gidan Alhaji Ammar babban gidane sosai, ga farfajiyar gidan wajen ajiye mota,kafin kishiga gidanma akwai tafiya, wannan gidan Sa'adatu ta mallakawa kawu Isma'il Wai yabata nasa, zai Mata cikon kud'i..........
Bayan rasuwar Ummu Ruman sai su Hadiyyah da zahra Khadija da Kuma zeenah, suka koma kwana d'akin ummy d'in gaba d'aya,sama suka koma kenan, sun bar qasa........
Ita Kuma Sa'adatu ta dawo qasa da Zama d'akinta na qasan, saman Kuma tabarwa su Alhaji dasu farouk da Haidar, Suma anan suke kwana.....
Bayan aurenta da kawu Isma'il Kuma, saita dawo da yaran gaba d'aya qasa, kawu Isma'il saita bar Masa saman turakar Alhaji Ammar lokacin Yana raye(... Lallai abun yayi yawa ta aureshi Kuma tabashi turakar mijinta, dad'in xama. D'akinta na saman nan ma tana zuwa........
Da Hauwa matar Isma'il ta dawo gidan kuma, sai suka koma kamar yadda suke zamansu da Alhaji Ammar da Ummu Ruman, d'akin Sa'adatu dana Hauwa sai turaka sune a saman, Yara kuma suna qasa, lallai fan's gidafa yazama na kawu Isma'il duk girmasa duk kyaunsa.......
Tunda Hauwa tadawo gidan basa zaman lafiya da Sa'adatu, duk wannan mutuncin da qawancen anbarshi, Hauwa mugun haushin Sa'adatu takeyi, taci amanarta ta Aure Mata mijinta,har lokacin su Hadiyyah da kud'in ribarsu ake musu wata wahala, kud'in makaranta, sabulun wanka na wanki, takalma, rashin lafiya dadai sauransu, abokin Alhaji Ammar ko d'aya yadaina kawowa Y'AY'ANSA tallafi, kamar yadda ake Masa lokacin da bashi da lafiya kafin ya rasu.....
Dawowar Hauwa gidan saita d'auki Hunaif, in zasu tafi makaranta a gurinta yake zama, sai sun dawo ydawo gurinsu, har sannan rigimar sa tananan, kashin wando Dana kwance yananan, tana tausayawa su Hadiyyah, tana jansu ajiki sa'banin Sa'adatu, sai Kuma Sa'adatu da taga hauwa tadawo saita daina azabtar dasu Zahra d'in, tana sasu dai aiki dai_dai gwargwado, wanke_wanke, shara, wanki Kuma nasu kawai sukeyi, Sa'adatu takoma yima yaranta yanzu,
Su Hadiyyah sun Fara samun sauqi fa ganin idon Hauwa, lallai Sa'adatu Babu tsoron Allah (... Yakamata Mata musan cewa duk abunda kukayiwa d'an kishiyarku na alkhair Kona sharri za'ayi naku, ...)
Alhaji d'an Sa'adatu fa shaye_shaye yafara nisa, tun Yana 'boyewa har Abu yafito filo, qiri_qiri yake zuwa da kwalaben maganin tari, wiwi acikin d'akinsa yakesha warin yaita fitowa daga d'akin, Kawu Isma'il yakama yai Masa warning had'e da duka, Amma me sai Alhaji ya miqe yanawa kawu Isma'il rashin kunya, har Yana karya Kuma dukansa zai Rama ne, ai ba ubansa bane, da Sa'adatu tasa Baki akan abunda yakewa kawu Isma'il gaba d'aya ya had'asu yai musu tatas, ya zagesu, ya gaya musu magana, Babu uban daya Isa ya hanashi abunda yaga dama(... Kunsan dai Yara maza masu tashen balaga, jinsu suke dai_dai da kowa musamman