Showing 3001 words to 6000 words out of 141223 words
Chapter 2 - RASHIN IYAYE Complete Document by Rabi'atu Muhammad Rabi'u Oum ARQAM.txt
wai ai itace mai 'ya'ya maza ai kuwa sai iya shegw suke musamman Alhaji wanda yafara tasawa shima,,,,,,,,,,,,,,,,
ALLAH sarki *hadiyyah* tagafa ummu taqi dawowa kuma kullum tana ranta, aikuwa ta sarki kuka kullum tana barci tana mafarkin ummu batada magana saita ummu, tadaina walwala, hakan yasata kuma cuta wacce saida takwanta a asibiti, kuma ummu din taje dubata aikuwa tana ganinta, tai wata ajiyar zuciya ta qanqameta, tana dariya, cikin maganarta wacce bata fita sosai, saboda ciwom dayake damunta, ummuna ina kika tafi kika barmu nida *Hidayah*? Sai nemanci mukeyi, kowa gurin saida ya tausaya wannan rayinya, lokacin kuma Ammaru yana wajen ga hajiya ma tazo dubiya, itakam ummu Ruman babu abunda takeyi sai tausayawa 'ya'yanta,musamman *hadiyyah* wacce take da qulafuci tun tana 'yar qaramarta, kiyi haquri kinji *kyautar ALLAH ne* (... Haka take ce musu itada hidayah mafi yawan lokuta...) zan dawo ne unguwa naje, bakyaso nasiyo miki kayan wasane, inaso ummu cewar hadiyyah " to kidaina kukan kinji yakiji sauki kuma zan dawo gareku kinji, a hakadai ranar Hadiyyah tunda taga ummansu saita ware harda su dariya da wasa a ranar kuwa aka sallameau daga asibiti, wanda kowa yayi murna da hakan, musamman 'yar uwarta Hidayah, domin sun shaqu sosai zuwanta asibitin ya janyo, rage walwalarta, duk da ita dama batada hayaniya kwata kwata, amma kuma tanason Hadiyyah d'in ta, 'yan biyu kenan masu abun mamaki (.... ALLAH kabamusu masu albarka👏....)
Wanda kuma a ranar dayake sai dare aka salllamesu, hadiyyah bata san cewa ba ummu suka tawo gidaba, domin lokacin tayi barci, safiya nayi data duba daga babu ummu aikuwa saita saka kuka babu ji babu gani, nan danan zazzabi ya dawo yarinya tafara shidewa alamun zata suma kenan...............
Lallai kam FAN'S anya kuwa hadiyyah meyake damunki kuma hakanan? Mujedai zuwa wannan salon daban yake da sauran.....
Nice dai taku ✍🏻 Rabiatu Aminu MUHAMMAD 'yar mutan kanawan dabo💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
2/7/24, 4:19 PM - Rãbi'atou Aminou {Oum ARQAM}: 🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️ *RASHIN IYAYE*
(babbar musiba) 🎗️🎗️🎗️🎗️🎗🎗️🎗️🎗️🎗🎗️️🎗️🎗️
✍🏻Daga Al 'kalamin
*Rabiatu Aminu MUHAMMAD*
✍🏻Marubuciyar
*KOMAI NISAN JIFA free novel*
*HAKAN BA KUSKURE BANE paid book # 300*
Anda now👇🏻👇🏻
*RASHIN IYAYE*
*(Babbar musiba) free novel*
*🌍MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION📚🖊*
*M. W. A*
```Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.🤙🏻```
*_________________*
Ina farawa da sunan ALLAH mai rahma mai jin 'kai, tsira da aminci suqara tabbata ga shugaba ANNABI abun za'bi da alayensa da sahabbansa da matansa da ''ya'yansa da duk wanda yake riko da sunnarsu har izuwa ranar sakamako, bayan haka ina mikawa ALLAH subhanahu wata ala godiya daya bani ikon fara wannan littafi *RASHIN IYAYE* ALLAH yasa yadda nafara lafiya ALLAH yasa nagama lafiya, ALLAH yabani ikon rubuta abunda zai amfanar da al'uma, inda nayi kuskure kuma ALLAH yagafartamin🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻
Na fara rubutawa wannan littafi ranar lahadi hijirar maaiki nada 8/6/ 1444 wanda yayi daidai da 1/1/2023
Note........ 'yan amana kuci gaba dasani acikin adduar ku akan ALLAH yabani lafiya, yanzu dai ga wannan babu yawa, da babu gwara babu dadi, idan naji sauki ssai zan dinga muki POST mai yawa wann ma karfin hali nayi wlh
*PAGE FIVE 5*
Hankalin Alhaji Ammaru a tashe, yafito da mota,lokacin Sa'adatu ta d'auko *hadiyyah* wacce lokacin a sume, lokacin dare yayi wajen 11:00pm ne duk yawancin yaran sunyi barci, amma idon *hidayah* biyu tana kusa da 'yar uwarta,wadda tayi kewarta kwana da kwanaki tunda ba tare suke kwana a asibiti ba,tana ganin halin da yar uwarta take ciki itama kukan tafara musu, a haka sa'adatu ta qaraso da *HADIYYAH* a hannunta itama *HIDAYAH* d'in biyosu tayi, babu 'bata lokaci Abby ya d'au hanya sai asibiti(... Da yake wani asibi ne na kud'i kuma 24hour ne...) Nan dana likitoci suka had'u akanta, kafin su samu numfashinta ya dawo........
Abby yacewa sa'adatu takoma gida saboda yara anbarsu su kad'ai, duk da akwai mai gadi,jikinta sai rawa yakeyi, wai ita a lallai taba tausayawa Hadiyyah d'in, wanda azuciyarta kuwa sai kwashe mata takeyi, saboda tasan wannan qarshe Alhaji yace zai mayar da Ummu Ruman, tunda rashin uwarta ne yasa mata wannan zazzabin da ciwon, hakanne yasa duk cikin 'ya'yan Hidayah, zahra da khadija, babu wacce ta tsana sama da Hadiyyah d'in, saqe_saqen datake a ranta kenan, Alhaji yace mata takoma gida, " to shikenan babu damuwa, amma kuma nabar hadiyyah kuma, ta fad'a cikin nuna tausayi, wanda shi kuma Ammaru hakan da sa'adatu takewa 'ya'yansa da nuna kulawa yakesa yake qara kaunarta a koda yaushe(... Lallai Ammar bakasan makircin sa'adatu bane...)........
A haka dai sa'adatu tadawo gida, cikin zuciyarta fal tsanar Hadiyyah, tana fatan ace ta rasu kowa yahuta.........
Kafin safiya kowa yasan da cutar hadiyyah, abunka da Ammaru yanada kud'i, haka 'yan uwa kowa yadinga zuwa da abun arqikinsa, ana fadanci, hakama hajiya Sakinah tazo itada Zakiyyah(... Yayarsu Hadiyyah...) Lokacin da Ummu Ruman takuma zuwa hankalinta a tashe jin cewa washe gari ciwon hadiyyah yakuma tashi, tana barci lokacin da tazo, babu yabo babu fallasa haka suka gaisa da sa'adatu da sauran 'yan uwa........
Hadiyyah tana farkawa taga ummunsu, aikuwa nan ma dai kukan tafara, ikon ALLAH kuma 'yan uwa duk ana tare, shima Alhaji Ammaru yananan......
Ummu kidaina barina kina tafiya kullum sai nayi kuka, nida Hidayah, kuma kin tafi da zeenah bama wasa da ita, indai kika kuma tafiya ummu zantayin kuka, kuma kaina ciwo yakeyi, ta qarasa tana kukan, tare da rungume ummu d'in kowa a gurin ya tausaya musu, itakam ummu Ruman babu bakin magana, tadai rungumeta, amma cikin zuciyarta babu dad'i.........
Nan dai Hajiya sakina tasan cewa cutar hadiyyah ya samo asali na rashin mahaifiyarsu a tare, anan kowa ya dinga tofa albarkacin bakinsa akan hakan, daga karshe dai Alhaji Ammaru yace zai mayar da Ummu Ruman d'akinta, Itakam ummu Ruman dama tana addua akan hakan kuma gashi ALLAH ya amsa mata rokonta, Ranar a asibitin ta kwana saboda jikin hadiyyah d'in, kuma ansamu cigaba sosai, kwanasu Uku aka basu sallama, kuma a washe gari aka mayar da AURENSU da Ummu Ruman, karkuso kuga murna wajen Hadiyyah........
Wata ba'ayi ba hadiyyah, takoma walwalarta ko yaushe tana maqale da Ummu, itakam hidayah dama gidan sauqi ce, su zahra da Khadija(... Ita datake kanwa ma bata kulafucin da Hadiyyah take...)
Sa'adatu fa tahi hausin wannan kome da akayi na Ummu Ruman, amma kuma saita nuna kamar babu komai, ita kuma ummu Ruman tacigaba da addua tare da kulaa da 'ya'yanta, kunsan addua bata fad'uwa kansa a banza, idan sa'adatu tayi makaircinta karshe ya koma kanta, ko kuma yaqi tasiri.........
Muje zuwa FAN'S yanzu wasan yafara wannan salon daban yake,
RASHIN IYAYE labari ne na tsantar maraicin iyaye guda 2
akwai tausayi da dai sauransu muje ziwa zakuji duk anan gaba
✍🏻Nice dai taku Rabiatu Aminu MUHAMMAD 'yar mutan kanawan dabo💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
2/7/24, 4:27 PM - Rãbi'atou Aminou {Oum ARQAM}: *RASHIN IYAYE*
(babbar musiba)
✍️Daga Al 'kalamin
*Rabiat Aminu Muhammad*
Marubuciyar
Komai nisan jifa📚
Hakan ba kuskure bane📚
And now
*RASHIN IYAYE (babbar musiba🙆♀️)*
Labarine na tsantsar maraicin iyaye guda biyu akwai tausayi cin amana ha'inci dadai sauransu duk anan gaba zakuji
🌏MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION📚🖊️
M.W.A
Kungiya d'aya tamkar da dubu, masu Nazari da Aiki da ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fada'akar ta Kuma Nishad'antar da masoyanta.🤙
*__________________*
*PAGE SIX 6*
"""Haka lokaci ya dinga tafiya,,,
Ummu Ruman taci gaba da xama agidan mijinta Alhaji Ammar ta rungume "ya"yanta, tana Basu kulawa....
Tun daga sannan Hadiyyah ta samu lafiya, Babu wata cuta Kuma,
Itama makira wato Sa'adatu tunda taga tadawo gidan Kuma, saita haqura da wannan makirce_makircen nata, suka zauna lafiya ta ciki na ciki ta baka na baka,kunsan dama xaman kishi.....................
Lokaci yanata tafiya duk 'yan matan Ummu Ruman Zahra, Hadiyyah da Hidayah, Khadija da Kuma zeenah duk sun tasa musamman Zahra Hadiyyah da Hidayah...
'ya'yansa mata Zakiyyah(ita dama tana gidan kakarsu) da Zahrah duk ya siya musu gold abunsu, sun tasa sannan Zakiyyah tana da shekara 15 ita Kuma Zahra tanada 13......
Suma yara maxan Alhaji, farouk da Haidar kowanne Yana Masa Hidima(...'ya'yan Sa'adatu...)
Zakiyyah 'yar gidan Kaka yarinyace,irin masu girman jikinnan baza kace 15years takeba, Amma duk Wanda yagani yasan akwai yarinta Kuma hutu ne yasa hakan,Domin kuwa Babu abunda takeyi gidan kaaka,daidai da girki,shara,wanke_wanke, duk bayi takeyi ba a gidan, gata yarinya mara wayo, ga'buwa, tana jss 3 ..............
Ana haka mukhtar yaganta, saurayine zaikai 30years yace Yana sonta, aikuwa Hajiya kaaka ta ara ta yafa, saita Aurar da Zakiyyah a wannan lokacin, shikam Alhaji Ammar Dan bayanda zaiyi be,akwaishi da biyayyah, Amma Zakiyyah guda nawa take? Meta iya da za'a mata Aure yanzu, Bata iya komai na mata ba, Kuma ko candy batayiba.....
ita dama Ummu Ruman Babu ruwanta da ita, tunda Hajiya kaaka ta dauketa, tabar mata ita, Amma Kuma rashin nutsuwar Zakiyyah Yana 'bata mata Rai, Kuma ko zuwa gidan batayi, balle ta dinga sat wasu aikace_aikace na gida, sannan ta dinga tsawatar mata, acikin tarbiyyarta to Amma Babu Hali......
Koda Alhaji Ammar yace mata wai Zakiyyah tanada masoyi itakam haka tace Allah ya kyauta, acikin zuciyarta cewa tayi Amma Zakiyyah tayi yarinta da aure,
Nufin Mukhtar dama asan dashi, idan yaso idan tayi candy anyi auren Amma Ina....tunda yazo Hajiya kaaka taketa azalzala akan ayi_ayi ai auren(...kujifa fans sai kace wacce ake neman Kai da ita Allah yakyauta halin Hajiya kaaka...)
Cikin qanqanin lokaci kuwa aka kawo kud'in Zakiyyah (yarinya sha_sha_sha) kowa yayi mamakin hakan, sai sannan Kuma Hajiya kaaka ta tasarwa Zakiyyah da koya mata abubuwa, Wanda batayi da to Allah yasadai Fan's ta koya d'in........
Anyi bikin Zakiyyah, Alhaji Ammar yayi mata Kaya nagani na fad'a, kowa yagani yasan 'yar gatace, saidai Allah yabada zaman lafiya.........
Su Ummu Ruman ana daga gefe abunta, Domin itama a 'yar gayya taje bikin gidan Hajiya kaaka........
Shekara d'aya da Auren Zakiyyah ta haihu, Amma Babu Rai 'Dan,dayake da akwai kud'i, wajen babanta Alhaji Ammar ranar suna bakuga mutanen da sukaje sunanba, bakwace Babu 'Da ba, har sannan Zakiyyah anashan ga'bunta haka dai Mukhtar yake haquri da ita, shima yasan yarinya dama ya aura sai haquri......
******** ********
Sai wannan Haihuwar Allah yabaiwa Ummu Ruman 'Da namiji, kar kuzo kuga shagalin da akayi, ranar sunan Hunaif, Anyi shagali da budiri, Alhaji Ammar yayi 'barin kud'i, ya wadata "ya"yansa maza da mata da suttura ta fitar suna, wannan Karan ma Sa'adatu Alhaji Ammar yabawa kud'i taje tasiyowa Ummu Ruman kayan Jaririn, itakam Bata damuba......
Alhaji Ammar kamar Bai ta'ba haifar namiji ba, Itama Hajiya sakinah tayi gayya sosai,(...ko kunya fans, ita datace Bata haifar namiji, sai mata...)
Itama lokacin Sa'adatu tanada karamin ciki ajikinta.....
Rayuwar gidan Alhaji Ammar Rayuwace ta Jin d'ad'i da walwala, Domin kuwa Babu abunda suka rasa na rayuwa, duk Wanda yagansu yasan suna cikin Gata.......basai sallah yakewa iyalansa d'inki ba, takalma da sauran abun amfani kuwa sai godiyar Allah komai a ajiye yake.......
Suma matan nasa duk haihuwa saiya canza musu kayan d'akinsu, Alhaji Ammar akwai hidima ga iyalai......
Hakama 'yan uwansa, mahaifiyarsa ma kullum cikin kula da ita yake, danginsa ana sonsa saboda kyautarsa, indai. Yana dashi to zai baka, mutane nawa yakai hajji da umara..........
Zahra, Hadiyyah da Hidayah Khadija da zeenah, da Kuma Alhaji da farouk da Haidar suna cikin Gata Babu abunda suka rasa.........
Allah yad'orqwa Alhaji Ammar son Zahra, komai tace tanaso xai Bata,hatta Keken d'inki yasai mata, lokacin ko iya Dunkin batayiba koyo takeyi, komai yace Zahra....
Twin's dinsa ma Yana nuna musu kuluwa Hadiyyah da Hidayah, yara masu kyau da shiga Rai komai nasu iri d'aya, saidai hali daya banbanta...
Hidayah akwai haquri, magana Bata dameta ba, itakam Hadiyyah akwai tsiwa da iyayi, Bata ragawa Kowa inya tsokaneta .......
Su Alhaji an Fara Zama saurayi shima komai Alhaji Ammar Yana Masa, tare da sauran 'kannansa Farouk da Haidar.........
A wannan lokacinne Alhaji Ammar yakamu da rashin lafiya, Hunaif Dan Ummu Ruman Yana da wata biyar a duniya, ita Kuma Sa'adatu tanada ciki wata takwas.............
Muje zuwa Fan's yanzu aka Fara labarin
RASHIN IYAYE babbar musiba labarine na tsantsar maraicin iyaye guda biyu, akwai tausayi, cin amana, ha'inci dadai sauransu duk anan gaba
Nice dai taku
Rabiatul adawiyyerh
2/7/24, 4:27 PM - Rãbi'atou Aminou {Oum ARQAM}: *RASHIN IYAYE*
(babbar musiba)
✍️Daga Al 'kalamin
*Rabiat Aminu Muhammad*
*08128131163*
Marubuciyar
Komai nisan jifa📚
Hakan ba kuskure bane📚
And
RASHIN IYAYE (babbar musiba🙆♀️)
Labarine na tsantsar maraicin iyaye guda biyu akwai tausayi cin amana ha'inci dadai sauransu duk anan gaba zakuji
*__________________*
🌏MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION📚🖊️
kungiya d'aya tamkar da dubu masu Nazari da Aiki da ilimi Burin'kungiyar a ko da yaushe shine fada'akar ta Kuma Nishad'antar da masoyanta.🤙
*__________________*
*PAGE SEVEN 7*
" "Yan biyu Hadiyyah da Hidayah suna junior secondary, komai nasu iri d'aya ne, ba'a gane kamarsu, sai a halinsu,sunashan Gata sosai, Shima Alhaji school dinsu d'aya, ita kuma Zahra tana senior school, duk a makaranta d'aya suke pravet ce Mai tsada, su Farouk da Haidar,zeenah da Khadija Suma duk suna zuwa, duk dai wani Gata 'ya'yan bin yassir suna dashi Babu abunda suka rasa, saidai kunsan Rayuwa ba komai kake samu 💯 ba....
in kukaga inda 'yan uwan Alhaji Ammar suke nunawa 'ya'yansa da matansa kauna abun ba'a magana, yanada kud'i, Amma Kuma Suma suna Yi musu bajinta.....
********* *******
Cutar data samu Alhaji Ammar itace ruwane yake tarar Masa aciki, in kuka kalleshi kwa zata haihuwa zaiyi wata Tara, tun a sanan yabiya kud'i Domin yaje saudia ya roki ubangiji akan allah ya saukaka masa ciwon, Amma fafur Hajiya sakinah tace itace zataje umarar badai shiba, shida bashida lafiya,bazai yiwu yaje wata qasa ba, yace mata zai tafi da Ummu Ruman, saboda ita Sa'adatu tanada tsohon ciki lokacin, fafur Hajiya kaaka tace, vata amince ba, ita zataje umarar tayi Masa adduoin, ai bakin mahaifiya kamar yankan wuqa haka take, saboda biyayyah ta Alhaji Ammar haka ya haqura ya qale kaaka ta tafi umarar, Shi Kim yazauna a gida saidai Yana zuwa hospital,kuma likitansa duk sati Yana zuwa ya duba Shi, Ana haka kuma sai Kuma ciwon ciki Mai tsananin gaske ya kamashi, Wanda tun Yana yiwa kansa komai Saida yadaina komai Yi Masa akeyi,ana hakan aka ce Dole aiki za'ai Masa,a zuqe ruwan cikin nasa, shine yake saka Masa ciwon cikin, Allahu Akbar Alhaji Ammar ko magana baya iyawa baya sanin Wanda yake kansa......
A AKTH aka bashi kwanciya, idan kukaga yadda 'yan uwa da abokan arqizi suke tururuwar zuwa dubiya, saikuyi zaton biki akeyi, flaks da cooler abinci kala_kala,(... Wanda akeyi danshi Bai San anayi bama, mutane basayin Abu Dan Allah, da ace bashida kud'i ko mutum biyar Allah yasa suje dubashi balle ma har Sukai Masa abinci, mugyara 'Yan uwa Riya batada dad'i...)
Allah sarki Ummu Ruman tunda Alhaji Ammar yafara rashin lafiya, itama tafara Rama, kana kallonta kasan Bata cikin kwanciyar hankali, sai kuka kawai aikinta, Yan uwanta suyita Bata haquri suna cewa cuta ba mutuwa bace, Amma itakam sai a hankali, ga Hunaif kunsan abunka da Bata ta'ba Haihuwar da namiji ba, yanada rigima sosai, yaita kuka baya yarda da kowa, kullum itace take zuwa asibitin, Sa'adatu ciki ya tsufa, ba kullum take zuwaba, lokacin itama jikinta yayi Sanyi duk wani iskanci ta ajiyeshi gefe,to Wanda ake danshi bashida lafiya,ga kuwa ciki haihuwa ko yau ko gobe.....
Hajiya sakinah tanacan saudia tana ibadarta ta umara, tanawa danta Kuma adduar samun sauqi, tunda kullum suna waya taji yane jiki, harta dawo gida, dataga halin da Alhaji Ammar yake ciki tayi kuka,tayi Dana sanin hanashi zuwa saudia d'in, yanason zuwa Amma ta hanashi,gashi yanzu baisan Wanda yake kansa ba......
Yara kuwa duk suna samun kulawa sosai, wajen 'yan uwan babansu da abokansa, komai ana ajiye musu da abinci da sauran abun amfani, suna zuwa duba Abby,Kuma kullum sai sunyi kuka musamman Zahra sun shaqu dashi, Shi yasa ma aka hanasu zuwa asibitin, Amma Hajiya sakinah tace a qale yara suzo duba mahaifinsu dame zasuji ne.....
Zakiyyah tana zuwa duba mahaifinta itama duk kwana d'aya,tana xaune da mijinta lafiya sai halinta na shashanci, Almubazzaranci,da Kuma ga'bunta da fita maqota,komai na gidanta maqota sune suke roqewa, gishiri Maggi, mai, tun abun baya damun Mukhtar har ya Fara damunsa, bacin ransa d'aya da ita shine rashin Zama a gida, ko ta tara Masa mata a gida, tun kafin Alhaji Ammar ya kwanta rashin lafiya aka Fara wannan sulhun tsakaninsu, Hajiya sakinah taje tai mata fad'a shima yaje, Amma da ankwana biyu zata Kuma komawa 'Yar gidan jiya,a haka yake haquri da ita darajar iyayanta(... Allah ya kyauta, musani cewa duk abubuwan da ake Mana kyautatawa yawansu darajar iyayanmu mukeci, da zarar qasa ta rufe musu Ido wlh Babu Mai kyautatawa garemu sai masu tsoron Allah kawai...) Matsalar Zakiyyah kenan........
Anyiwa Alhaji Ammar aiki lafiya, anata murna Domin ya samu sauqi, Yana iya gane mutane, Yana magana, ko sati ba'ayi da aikinba ruwan yadawo Wanda yafi nada, dama ta qirjinsa akayi aikin, aka saka roba ruwan yana biyowa, idan yaqarasa fita sai likitoshi su cire Masa, ruwan Yana qarasa fita aka cire Masa, ya samu lafiya, shine Kuma ba'ayi sati da aikin ba, wani ruwan take biyowa ta wajen da akayi aikin Yana fita da kansa, cuta tafi ta da Muni ya kunbura sosai, sai abunda Hali yayi dai Kam Alhaji Ammar.........
Za'a fitar dashi waje ai Masa aiki, an saka ranar aikin, ana gobe, tafiya, wajen la'sar ummu Ruman tana sallah kusa da gadon da take kwance, tayi ruku'u, kenan taji hannun Alhaji Sharaf a gadon bayanta, ya Fad'o ........... Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun Fan's meke faruwa da Alhaji Ammar ne?
Muje next page Domin muji meke faruwa.........
Akwai maraicin iyaye guda biyu a shekara d'aya,tausayi cin amana ha'inci dadai sauransu
✍️Rabiat Aminu ( Oum Arqam 👩🍼)
2/7/24, 4:27 PM - Rãbi'atou Aminou {Oum ARQAM}: *RASHIN IYAYE*
(babbar musiba)
✍️Daga Al 'kalamin
*Rabiat Aminu Muhammad*
*08128131163*
Marubuciyar
Komai nisan jifa📚
Hakan ba kuskure bane📚
And
RASHIN IYAYE (babbar musiba🙆♀️)
Labarine na tsantsar maraicin iyaye guda biyu akwai tausayi cin amana ha'inci dadai sauransu duk anan gaba zakuji
*__________________*
🌏MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION📚🖊️
kungiya d'aya tamkar da dubu masu Nazari da Aiki da ilimi Burin'kungiyar a ko da yaushe shine fada'akar ta Kuma Nishad'antar da masoyanta.🤙
*__________________*
*PAGE EIGHT 8*
" Ummu Ruman Bata kawo komai a ranta ba, da fadowar hannun Alhaji Ammar,tayi tunanin barci yayi hannunsa ya langa'bo.......
Bayan ta idar da sallah d'in, ta tashi Domin tagyara Masa hannun, Amma saime? Ganin idon Alhaji tayi abude Yana kallon sama, gigicewa tayi aguje