Showing 123001 words to 126000 words out of 141223 words

Chapter 42 - RASHIN IYAYE Complete Document by Rabi'atu Muhammad Rabi'u Oum ARQAM.txt

kusa dakai, tunda Basu da uwa Baaba ce matsayin uwarsu, dan kuwa yasan Halin Sa'adatu ya yunwar cikinsa, su Zeenah da Hunaif su taso a mahaifarsu,(dama kuma jinya ce ta tsayar da Baaba a Kaduna na mahaifiyarta kuma shekara Biyu da Rasuwar ta kenan,sai ƴaƴanta kannen Ummu Rumana kawai acan yanxu kowanne kuma yayi Aure da iyalinsa)
Ko da Abbu yaji wannan shawara ta Kawu Isma'il yayi murna,hakama su Hadiyyah ɗin,itama kanta Baaba batayi Musu ba,Amma sai biki yatawo zata dawo




_____SAADATU____


Alhaji Hamza ya dameta Akan shi fa so yakeyi ayi Aurensu da ita,ita kuma tace yabari Zatayi Auren ƴaƴa biyu ne(Su Hidayah) badon yaso ba ya Amince.
A daren Ranar kuma suna waya da yayarta zuwairah ta shaida MATA yadda sukayi da Alhaji Hamza ɗin,aikuwa nan zuwairah ta hau Sa'adatu Akan ina ruwanta da Wani Auren su Hadiyyah ƴaƴanta ne! Tayi Auren ta kawai,aikuwa Babu ɓata lokaci taiwa Alhaji Hamza maganar ta Amince Ayi Auren nasu kafin bikin ƴaƴanta ɗin.
Da Alhaji tallafy yaji zancen Auren Sa'adatu ALLAH yasanya alkhair yace(yana Mamakin halinta) Kawu Isma'il shima haka, Alhaji Gambo ma dayaji zancen auren da ALLAH yasanya alkhair yabita,Hajiya ikilima da Hajiya Sahura kam zaman lafiya mai dorewa tuni Asalamiyyah da Abbas(ɗan wajen Hajiya suwaiba) sun tasa sosai kamar Twin's abunsu,Har sannan Hajiya ikilima ALLAH bai bata Haihuwa ba.




Abbu ya karɓi gidan Sa'adatu za'ayi Masa gyara idan tayi Auren ta tare gidan Alhaji Hamza za'a zuba ƴan haya a dinga karɓarwa(farouk da Haidar da ALHAJI da kuma Auta Hafsat sai ita Sa'adatu ɗin) kuɗi a buɓe account ana tara kuɗin, Sa'adatu bata musa ba tasan kuɗin ta da gidanta Babu gyara Babu zago tunda Suna wajen Alhaji tallafy.


ALHAJI yana daga China jin mahaifiyarsa(Sa'adatu) Zatayi Wani Auren daban sai da yayi kukan baƙin ciki Amma ya ya iya, bayan mutuwar Abbiy aurenta uku kenan! kawu Isma'il,Alhaji Gambo Yanzu ga wannan ai shikenan, ALLAH sarki Ummu(mahaifiyarsu Hadiyyah) yasan da tana raye sa itace bazata iya Aure ba bayan mutuwar Abbiy Amma itakam Aunty (Sa'adatu) gashi tayi uku




Sa'adatu sai Wani rawar ƙafar Auren takeyi sai kace wata budurwa,har dasu magunguna takesha da gyaran jiki takeyi, wanda lokacin aurenta da kawu Isma'il da Alhaji Gambo Duk batayi ba, lalläi Alhaji Hamza na musamman ne kam (shu'uma Amma ga su Hadiyyah bata gyarasu ba),kuma sai walwali fa takeyi ko kunya,ha kuɗaɗen da Alhaji Hamza yake kashe MATA data ce kaza zai bata kuɗi ninkin abunda tace, sai murna takeyi,Alhaji Hamza ɗin shima sai murna yakeyi kamar bai taɓa aure ba ko kuma bai da mata har uku a gida, kamar yadda ya faɗa MATA,dan itafa Sa'adatu batayi bincike Akan sa ba batasan ɗan wane unguwa ko gari bane ta dai san shi kuma tanajin ana Zancen sa, saboda kuɗin sa.


An Ɗaura Auren Sa'adatu da Alhaji Hamza kuma cikin satin zata tare,wanda Khadija tace itakam bazata bita ba gidan Kawu Isma'il wajensu Hadiyyah takoma,dan haka da Sa'adatu ta tashi tarewa gidan Alhaji Hamza da Auta Hafsat sai farouk da Haidar kawai ta tafi dasu,gida ma Sha ALLAH aljannah duniya kenan Sa'adatu da ƴan uwanta sai murna sukeyi ganin Irin aljannar duniyar da Sa'adatu ta tako,sai shewa akeyi haka gidan ƴan uwa kowa ya watse ɗaki guda aka bawa su farouk da komai nasu aciki ga ƴan aiki a gidan kamar buɗar ido komai sai anya Sa'adatu Auta Hafsat ma akwai mai kula da ita,tun Sa'adatu na jiran Ango Alhaji Hamza Amma ina taji shiru Babu shi Babu labarinsa,gashi har gari ya waye an kwana an hantse Zuciyar Sa'adatu sai wasi wasi takeyi shin mai ya hana Alhaji Hamza zuwa gareta a yau din a daren Aurensu?
Nima dai oum ARQAM nayi mamakin Hakan!


My Fans kubawa Sa'adatu amsa?
Anya kuwa! Kodai Alhaji Hamza bashi da Lafiya ne? Amma mezai hanashi zuwa ga Sa'adatu


Muje next page Muje meke faruwa kuma!!!!!!






✍️oum ARQAM ce ontop 🥰
8/22/24, 9:16 AM - Rãbi'atou Aminou {Oum ARQAM}: RASHIN IYAYE
(babbar musiba)




*PAGE SIXTY FIVE 65*




____GIDAN MUKHTAR____


Komai normal fa Yake tafiya tsakanin Zakiyyah da Bilkisu bazaka banbance ABIE da Twin's cewa ƴaƴan Zakiyyah bane,saboda komai nasu yana wajen Bilkisu abun gwanin sha'awa na'eem da na'eef sunyi kuɓul kuɓul abunsu sun ƙara kyau kamannin su da juna Suna ƙara fitowa har kasa banbancewa akeyi,Amma saboda shaƙuwa Bilkisu tana ganewa.
Arziƙi mukhtar yaci uban nada bana zasuje su sauke farali Bilkisu Zakiyyah da shi kansa,ga ababan more rayuwa a gidan kamar me!Hajiya Jamila tafi kowa murna da wannan zaman lafiya na gidan mukhtar, yanzu haka Zakiyyah sai shirye shiryen bikin ƙannenta takeyi!magajiyar uwa kenan,su Hadiyyah sunajin daɗinta a Yanzu fiye da ƙima,a waya su Hadiyyah suke ce MATA Suna gidan Kawu Isma'il ai saboda ana gyaran jiki da magungunan Sanyi dana gyara Suna sha,tace ai shikenan dama itama zata musu ne Amma yanzu Abar Aunty Hauwa ɗin,idan yaso ta haɗa musu turaren jiki dana ɗaki dana kaya masu shegen kyau sai murna sukeyi inda dane ko kallo Basu isheta ba itama bata gyara kanta ba balle ta gyara wani.




Zahran Ibrahim ma ma Sha ALLAH tana cikin kwanciyar Hankali da nutsuwa tuni ta yaye twins ɗinta kullum ƙauna karuwa takeyi tsakaninta da mijinta da uwar mijinta Hajiya Maimuna tuni ta ɗauke twins,saboda tana sonsu, Zahra tuni an ɗora Karatu daga inda aka tsaya yanzu haka Suna shirin graduation ne na kammala phc ɗinta ALLAH ya taimaka






______ABBU____


"Subhanallah! idan kunga gidan da Abbu yasa ake tamfatsawa su AQEEL yasin sai kun razana saboda haduwarsa tun daga waje balle aje ga ciki kuma, oh no oum ARQAM! lokacin danake ƙofar gidan bansan lokacin da nayi tuntuɓe ba sai jina nayi a ƙasa na zube bakina harya fashe azaba tasa na dawo hayyacina ALLAH yaso ban zubar da haƙoran gaba ba.


Gaskiya Abbu ya kashewa ƴan lelensa maƙudan nerori,Asalin ginin acan new delhi suka ga irinsa yai Musu shine suka cewa Abbu sunaso,shi kuma takanas ya ɗauko magina daga can aka Fara aiki,dana shigo ciki yasin nazata a india nake,Amma seerat da Haseena da Aisha Sulaiman da MamaGee da mummy Waleed da sauran ƴan RASHIN IYAYE Fans idan BIKI yazo Kuka kai amarya Zaku kwashewa idanunku abunda nagani.
Ba gida ɗaya bane kowanne dana sa amma manne da juna suke,kuma kalarsu ɗaya Babu banbanci, wannan gida gari guda kenan,daga parking lot ma kafin kaje harabar gidan sai ƙafarka tayi raɗaɗi in a ƙafa ne sai dai mota dama, dama kar asa security yasin ƴan Maula nisan wajen bazaisa su shigo ba😄
Nima yasin banda mota iyaka ta wajen gidan nida ba mota ba,in ALLAH yasa Ranar kai amarya naga yadda tsarin cikin gidan yake.


Tuni Kawu Isma'il yayi oder kayan ɗaki dana kitchen daga germany ba ƙaramin kuɗi shima ya kashe ba, ankawo komai tuni an haɗa gida sai jiran lokaci.


Amare an kammala exam lafiya sai fatan sakamako mai kyau,dan haka babu wasa Aunty Hauwa da Zafi zafinta tasa aka Fara musu gyaran jiki mai inganci mairo ƴar sudan ta ɗauko cikin kwana biyu da Fara gyaran jiki su Hadiyyah suka Fara Wani shining fatarsu tayi fresh sai annurin haske take fitarwa,dama can su masu kyau ne balle an ƙara da gyara!ga kuma maganin gyara na musamman wanda ba illah acikinsa kayan fruit ne aka sarrafa su kala kala,ga maganin sanyi ma Duk haɗa musu akeyi su kansu sunsan jikinsu ya canza daga ciki har waje! Khadijatu ƴan mata sai shiga da fita akeyi ga meenal ƴar Kawu Isma'il itama an tasa ansamu ƴar uwa a kusa sai Sha'aninsu sukeyi Suna tsara yadda bikin zai kasance.






_____MOMMAH____




Za'a Aurar da ƴaƴa ai Babu Zama, Dubai tasa ƙawarta Hajiya indo tai MATA odar ta kayan lefe harda akwatuna abun sai wanda yagani akwatuna kamar buɗar idanuwa kayan ciki kuwa wai ku kiyasto su da kansu fans,dama Duk wasu Abu da Mommah takeso in batason zuwa ta siyo ita take sawa tai MATA tasan Babu gyara babu zago Hajiya indo ƴar Amana ce.
Inda Mommah take rawar jiki da bikin nan yasin ko ƴaƴan cikinta ne albarka,
AKEELA kam itama tuni anfara MATA gyaran jiki acan india da Mommah suka tafi idan suka tashi dawowa sai su dawo da angwaye gaba ɗaya,kunsan dai gyaran jikin indiyawa ko? To faɗar hadewar AKEELA ɓata lokaci da baki ne.






______AQEEL DA AKEEL_____




Anacan Karatun exam yayi nisa kai ya ɗau zafi final year ai dole a riƙe wuta,shiyasa ma suka saurara da yawan wayar da sukeyi dasu Hidayah sai sa'i da lokaci koda yake Suma lokacin Suna exam Suma.


AQEEL fa da Alama ɗan love ne koda yake mukam munsan da wannan ai tun yana ƙwailan sa😄 inda Yake shiga super market na Birnin new delhi irinsu 'mahathtra' da 'srini krishna' yana lodar kayan kayan sawa irin nasu can na fitsararrun indiyawa abun ba'a magana wasu kayan Nikam bansan ta Yaya Hadiyyah zata sasu ba wasu dasu gwamma Babu kunsan dai irinsu, dama irin kayan Suna tafiya da imaninsa a Lokacin da sukazo farkon Fara karatunsu badon yana situation ɗin abinda Jimmai da Usman suka Masa ba da baisan abunda zai faru dashi ba, da kuma Addu'ar Abbu garesu itace tai Musu kariya! Dan haka yanzo baje hajarsa yakeyi anan,yana ɗaukar kaya yana hasaso Hadiyyah acikinsu sai kaga yawani lumshe idanuwa kamar me jin barci.


AKEEL mutumin Hidayah ai dama shi kunsan halinsa babu ɓoye ɓoye a harkarsa,irin shigar sari dinsu da waɗannan ƴan kumnayen da awarwaro da sarkar kan goshi da wacce take haɗe da ta hanci shine hubby ɗinsa dan haka ya jidarwa hidayan sa wannan shigar yakeson tana Masa,Duk da shima ƙananun kayan ya ɗiba Amma ha kamar wannan ba.
Lallai waɗannan angwaye ƴan Ayi ne,
Suma fa za'a musu gyaran jikin da akewa angwaye na indiyawa haɗa baki sukayi gaba ɗayansu shiyasa ma bazasu tawo da wuri ba sai ankusa Fara shagali saboda kar gyaran yabi rariya cewar AKEEL.
Mommah AKEEL yacewa " meyasa ba'a tawo dasu Hidayah ba Suma amusu gyaran jikin tare da AKEELA ne mommata? Babu ɓoye ɓoye tsakanin Mommah da ɗan ta AKEEL dama shi ba kunya gareshi ba!
"Nayi tunanin haka AKEEL to amma da nayiwa Abbu magana cewa yayi Suna gidan kawunsu ana musu kuma ƴan sudan ne suke musu,Suma sudan badai gyaran jiki ba ga kamshi! AKEEL ya jinjina kai alamun ya gamsu da bayanin Mommah, ɗan gasken kuwa yana gefe baice komai ba Yasin, Alhalin shima yanason awa Hadiyyah Hakan.


Cikin dare AQEEL ya farka zai shiga bayi,to dama bai cire cire Glass ɗin sa sai zai kwanta,yana buɗe idanuwa yaganshi tarwai kamar yasaka glass ɗin aikuwa da mamaki ya mike Yaje bayi yadawo batare dayasa Glass ba,sai murna yakeyi koda Asba AKEEL yaga bro babu Glass yace 'bro kanason kayi amarci da cirarren haƙori ko lemon goshi ko? Dan Nikam bazan mulmula maka ba,kuma kasan idan ba'a mulmula ba Baya komawa! AKEEL yaƙarasa da dariyar shakiyanci haɗe da bugun kafaɗar ɗan uwansa!
"Bangaya maka ban...nan yakwashe yadda akayi jiya da daddare aikuwa AKEEL yayi murna jin AQEEL ganinsa yadawo normal sai ABunda ba'a rasa ba,aikuwa da suka Tashi sai da sukaje har sashen Mommah suka MATA albishir da Hakan kuma tayi murna(gida guda Abbu ya mallakawa su AQEEL a india suke ciki idan Suna da lecture suke school kawai,shima idan Yaje medical checkup anan gidan yake sauka, Yanzu ma Mommah da AKEELA a gidan suka sauka)


Ko da sukaje Hospital an duba idanun AQEEL doctor yace Masa ƙarfin ganinsa ya daɗu sosai fiye da da,dan Haka Glass ɗin da Yake Amfani dasu yanzu sun Masa ƙarfi,Amma bazai dinga Zama haka ba saboda kwayar idanun tayi rauni ga ƙura da rana za'a Masa wanda zai dinga bashi kariya daga hakan da kuma kara ƙarfin ganin, Aikuwa nan danan aka Masa wasu masu kyau, Doctor yace yanzu indai ba fita mai nisa zaiba saboda Iska ko ƙura dan cikin gida zai iya yawonsa ba Glass sai murna yakeyi,haka suka dawo gida, ABBU yana germany lokacin dan Haka da suka kirashi a waya suka faɗa masa yayi murna sosai.






______ALHAJI HAMZA____






"Na barka kayi Auren nan ne saboda naduba naga akwai samu Sosai a jinin matar da zaka aura,Amma idan ba Haka ba kai kasan ƙarya ne, MATA nawa ka nema da Aure na hanaka saboda Auren nasu Babu samuwa sai ma koma Baya ita kuwa wannan ai za'aje da ita!
Wata MATA nagani a zaune a Wani flour na Alfarma ta hakimce a kishingiɗe,Alhaji Hamza na Sa'adatu ya sunkuya a gabanta kamar mai neman gafarar ta! Cigaba da magana tayi "na Amince kaje gareta a yau na kammala Duk tsumakan da zanyi nayi,kana kusantarta Shikenan kakarmu ta yanke saka zamu samu ci gaba fiye da wannan muka samu nan gaba ta ƙarasa haɗe da nuna Masa Hanyar ƙofar fita,to "Shikenan ranki ya daɗe angama cewar Alhaji Hamza yana dosar ƙofar fita.


Hajiya mansurah kenan Matar Alhaji Hamza wacce matsafiya ce ta ƙarshe,sun haɗu ne a wajen wata ƴar tuwo tuwo bayerabiya ce talauci yai Musu yawa bata,shine Tasamu takewa ƴar tuwo tuwo wanke wanke shi kuma yana zuwa cin abinci wajen,anan mansurah taganshi kuma taji tana sonsa, akwai wata ƙawarta seraph (bayerabiya ce Amma arniya)mamansu tsafi takeyi taso Saka mansurah Amma taƙi,dan seraph Babu abunda ta rasa na more rayuwa tana Bawa mansurah Amma tace itakam bataso,kayan tsafin gwanda tayi wanke wanke a tasha, asalin su ƴan imo State ne,Alhaji Hamza shi kuma anan yake harkar gwangwan to a tashar yake Zuwa cin abinci dan kuwa Hajiya maira uwar ɗakin mansurah ta iya girki da Ma'aika tanta,tun da mansurah taga Alhaji Hamza ta ɗimauce akansa ta daina walwala shi kuma ko kallo bata isheshi ba,to anan ne fa seraph taga ƙawarta a halin da take Ciki,ta tambayeta anan ita kuma mansurah tagaya MATA son Wani takeyi,dayake son Alhaji Hamza yaiwa mansurah kamun kazar Kuka koda seraph tacewa mansurah zona kaiki wajen mamana zata samo miki hanyar da wannan mutumin zai so ki,Babu Musu kuwa ta Amince.


A Ranar maman seraph tasa mansurah a Hanyar tsafi,aka sata cikin ƙungiya mansurah Babu Wani ɗar ta Amince da Hakan,kuma acikin satin ta shawo kan Alhaji Hamza harya Fara kulata da magana.


A gida kano state kuwa Alhaji Hamza yana da MATA 1 Faɗima da ƴaƴa biyu Salim da salima ga iyaye da ƴan uwa,Amma ina tun Haɗuwar sa da mansurah tafara sauya Masa Hali sai ABunda tace Masa,yafarawa faɗima hulaƙanci da ƴaƴansa, sannan yace Aure zaiyi anan imo State yaga matar Auren bayerabiya ce kuma,aikuwa inna da Baba sukace Basu Amince ba, ko da Alhaji Hamza ya faɗawa mansurah Babu ɓata Lokaci ta bada jinin su ba'ayi sati ba sukace ga garin kunan tsiran Kwana Biyu batare da ciwon komai ba.


Kafin arba'in akayi Auren Hamza da mansurah Babu Wani bincike ko na komai,da zarar Wani ɗan uwansa yace Masa ya haka sai dai a wayi gari ya mutu.


Haka yatawo da mansurah kanon sabo gidansa ya haɗa su da faɗima waje ɗaya,Amma fa faɗima ta Zama hoto a gidan,saboda kowanne aiki itace meyinsa Duk wannan ƙauna da soyayya da Hamza yakewa faɗima mansurah ta kawar da ita,balle kuma su Salim da salima kamar almajirai suka koma,Hamza yazama ɗan mansurah.
Rana ɗaya mansurah tabada jinin Salim da salima aka wayi gari Babu su sun mutu,ko damuwa Hamza baiyi ba haka aka sittira su aka kaisu gidan gaskiya.


Faɗima kuma taci gaba da Shan wahala a gidan Alhaji Hamza ƴan uwanta da ƴan uwan Hamza Babu mai magana, tuni tsafin mansurah ya ƙulle musu baki.


Shi kuwa Alhaji Hamza tuni Mansurah yakoma a tafin hannunta sai ABunda tace Masa, kuɗaɗe kuwa ba'a magana Duk jinin da mansurah tabayar kuɗi ƙaruwa sukeyi a gareta,dan Haka Duk Wani abun more rayuwa dana ci ko Sha ko gidaje da kadadrori da Alhaji Hamza yake dasu a halin yanzu na tsafi ne wanda mansurah shima ta sashi aciki,bayan tai masa bayani, to dama sai ABunda tace Masa dan haka datai Masa tayi bai musu ba ya Amince,kuma har sannan sai abinda tace Masa.


Tun Wani ciki da faɗima Matar Hamza ta samu take Shan wahala har zuwa Haihuwa Babu wata_wata mansurah tabada jininta harna jaririn gaba ɗaya aka aika dasu,wanda wannan bada jinin shine ya zamo Duk wata ɗaukaka ta Alhaji Hamza da Yake kai a yanzu inda mutane suka sanshi ga kadarori Babu adadi,har sannan sai ABunda Mansurah tace dashi.


A Wannan lokacin ne kuma suka haɗu da Sa'adatu yana sonta har a ransa,Amma sai da Yaje yagayawa Mansurah data duba taga akwai samuwa da Auren nata jininta zai Amfani shine fa ta Amince Akan ya Aureta, kuma ya tawo da ƴaƴanta gaba ɗaya Gidan da zai ajiye ta.


Ruwan tsafi ne mansura take tsuma Alhaji Hamza dashi shiyasa ta hanashi zuwa a daren Aurensa da Sa'adatu,wanda Wani sirri ne nasu na matsafa wanda ALLAH ne yasan meta shirya da hakan, yau kuma gashi tace ya tsumu zai iya zuwa wajen Sa'adatun.


Sai rawar jiki Alhaji Hamza yakeyi acikinmota, direbansa yana tuka shi zuwa Gidan Sa'adatu sa'ar MATA ...


Next page Akwai buduri


Subhanallah meke faruwa ne?
Sa'adatu Kinga abunda son kuɗin ki ya jawo miki ko?
Wayyo ALLAH marayun ALLAH farouk da Haidar da Auta Hafsat


Mezai faru gaba shin Mansurah zataci galaba Akan Sa'adatu kamar yadda taci akan faɗima Matar Hamza ta farko da ƴaƴanta? Gadai Sa'adatu har gidan mijinta,itama kuma Mansurah ba'a shiga shirginta da mijinta............




✍️Oum ARQAM ce ontop 🥰
8/31/24, 12:42 AM - Rãbi'atou Aminou {Oum ARQAM}: *PAGE SIXTY SIX 66*


✍️oum ARQAM ce








"Lokacin da Alhaji Hamza ya ƙarasa gidansa wanda Sa'adatu take Ciki wajen maghriba ne,dan haka Kafin ya ƙarasa Anyi isha'i ma'aikatan gidan gaba ɗaya kowa ya kama wajen kwanansa,mai gadi ne kawai yake bakin aiki kamar Yasan yau mai gidan nasa zai Kwana a gida, dan haka driver yana horn aka buɗe gate ɗin ya cilla hancin motar cikin gidan,bayan driver Yayi parking Alhaji Hamza ya fito ya nufi Hanyar da zata sadashi da ainahin cikin gidan nasa,wajen Amarya tasha ƙamshi wato Sa'adatu sa'ar MATA.


Ɓangaren Sa'adatu kam ta tsinke da Al amarin Alhaji Hamza ganin takwana na hantse Babu ango Babu labarinsa,takirashi a waya switch off Duk mamaki ya kasheta!da kunya ta tambayi ma'aikatan gidan Alhaji kam,haka wajen breakfast Abubuwa kala kala akayi sai wanda taci,Hakanan su Hydar ma sai kulawa ta musamman ake Basu shida Hafsat saboda sune ƙanana, shi kam farouk ya ɗan tasa yaro ne nitsatste mai Hankali like su Hadiyyah.


Duk da Zuciyar Sa'adatu Babu daɗi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login