Showing 138001 words to 141000 words out of 141223 words
Chapter 47 - RASHIN IYAYE Complete Document by Rabi'atu Muhammad Rabi'u Oum ARQAM.txt
ba ni da Zaman jinya ƙiri_ƙiri tana kallon AQEEL zata faɗi haka Ko kunya!
Shi kuma AKEEL ɗin Zai ce "ba don hakinsu ba ai Nake barinki Albarkacin ɗan mu dake cikinta ne kawai!Amma da Sai wancan jarabatun ya kula da ita tana nuna AQEEL DA yatsa! Sai AQEEL ya yunƙuro Kamar Zai kawowa matar da mijinta Duka sannan sai su fice Suna dariya!!!!!!!!
Sa'adatu har gidan su Hadiyyah tazo cike da sanyin jikinta na ganin Irin Aljannar duniyar da twins suke cike nan Takuma tsoron ubangiji, lalläi Duk abunda ALLAH ya tsarawa Bawa kawai dole ne Amma idan ba haka ba ai.... Tana wannan tunanin ta ƙarasa ciki,dama tuni takira su Hidayah tafaɗa musu shiyasa security Basu hanasu ba sunsan da zuwansu AQEEL ya faɗa musu!
Ranar ba bu inda su AQEEL sukaje Suna gida suyi nan suyi nan saboda murnar zuwan Aunty, Aunty dai sai sussunne kai akeyi,alamun kunya,maybe tuna wulaƙanci data musu ne lokacin dazasu barkar Yaya Zakiyyah ne,batasan su sun Mance ba ma! Sun Mata jajen abunda yasameta da fatan ALLAH ya tsare gaba.
Sai da lokacin Sallah yayi su AQEEL sun fita masallaci(masallacin jikin gidan yake)
Sannan Sa'adatu tasa Kuka tana neman gafarar su Hadiyyah da Hidayah su Kam sukace tuni sun yafe Mata ALLAH ya karɓi tuba,tadinga warwarar cutar data musu tun fitar Ummu Rumana sukace ba komai,tace tagode cikin Kuka tace "ƴaƴan nan Ko haƙƙin Ummu Rumana Dana Ammar ya isheni a yanzu nakasa samun kwanciyar Hankali sai Kuka!gwanin tausayi!
Kiyi haƙuri Aunty tasu ta ƙare ai kici gaba da neman Rahmar ubangiji kina sadaka DA kyauta a zummar ALLAH yakai ladan garesu!
Daƙar ta lallasu kafin su AKEEL su dawo,
DA Sha Tara ta arziƙi suka aikata driver yamayar DA ita Har gida.
Sai da cikin Hadiyyah yakai wata huɗu sannan tayi lafiya abunta, sannan kuwa Duk wata hidima da za'a yi ta karatunsu a India dama Abbu yagama! Samun sauƙinta akeso kuma Alhamdullillahi.
Ranar tafiyar sunje sallama gidan Baaba kowa ma Sha ALLAH yake cewa Twins yadda suka murmure sun ƙara Haske sun huni a gidan,sun samu Baaba Dan ƴan ma tanta Khadijatu day meenal ƴar Kawu Isma'il sai ƴan matanci akeci ma Sha ALLAH anyi candy ana shirye shiryen Shiga University , Zeenah na wajen uwarta Zakiyyah Dama itama anzama ƴan MATA anshiga JS one!Hunaif dama yana wajen Aunty indo wajen Abul khair Dan uwansa shima ya Girma ana primary 4.
Har gidan Jimmai su AQEEL suka kai sallama,Taji daɗi da Hakan sosai,nan tamusu Addu'ar Alkhair.
Sanadin AKEELA suka San Shukhra Har gidanta sukaje,itama AKEELA ranar doctor Najeeb yakawo ta ranar ansha budiri an raƙashe Babu ƙarya a gidan Shukhra Kowacce da tsarabar cikinta Amma Banda matar AKEEL😄.Ita Hakan wai murna takeyi amarci sukesha Har sannan wai, sannan kuma su ba zulamammu bane irinsu day mazajensu.
Zaman AKEELA day Doctor Najeeb Sai ma Sha ALLAH zamane irin na so da ƙauna Kamar ɗaya ya haɗiye ɗaya,ba wani wulaƙanci na cewa ai ba shine ya sameta a budurwa ba no,zamane na Amana DA yardar juna,ai Doctor Najeeb yasan komai ƙaddara ce ta faɗa mata kuma shine na dakansa yamata aiki tana ƴar ƙaramarta.
Tuni ya Samar Mata admission a wata tsadaddiyar pravet school law takeson karanta Ko Dan saboda irinsu Usman, tana tausayawa yaran day akawa fyade,shiyasa da kudirce a ranta zata karanci Shari'a ta yadda zata zamewa irin waɗannan yaran da iyayen su Katanga Abar jingina,sudaina Jin tsoron kar ƙara ana tauye musu haƙƙi.
A ƙarshen ziyarar su Hidayah gidan Abbu sukaiwa tsinke karkuso Kuga murna wajen Mommah ta rasa ina zata saka su Ina zata ajiye! Ranar weakened ne Abbu yana gida nan yaita saka musu albarka! Yai musu nasiha Akan Zaman ƙasar da batasu ba musamman Matan Akan su riƙe mutuncinsu da darajar Aurensu Duk da yasan ba matsala Amma wannan yazama dole saboda halin Rayuwa,Anan yatuna DA Abokin sa kuma Amininsa Alhaji Ammar bn Yassir sai da Abbu ya share hawaye Suma su Hidayah haka AKEEL DA AQEEL ma sai da suka yi kukan,Bayan Tarin addu'oin nasara da fatan Fara karatu a Sa'a suka koma gidansu a washe gari suka ɗaga babban Birnin India wato New Delhi sai fatan nasara Rashin iyaye Fans kuzo kuje rakiya ƙasar India garinsu Shruti Haasan🥳.
Anan gida 9ja kam sai sam barka harkokin Abbu sai budewa sukeyi!!
Yanzu Tallafy foundation yakai inda bakuyi tunani ba sosai,miliyoyin yaran da silarsa suka shiryu ALLAH ne kaɗai yasansu,Da Yaro ya kammala Zai Dora karatun University anan gida 9ja Ko a abroad, idan kasuwanci yakeso Abbu Zai ɗauke Shi a company nasa,ga iyayen marayun da Yake ɗaukar nauyinsu wajen ci Da sha da suttura, Makarantu,Asibitoci,masallatai,rijiyoyin burtsatse da sauran abun buƙata Yanayi Bawa marasa ƙarfi jari,Aurar DA marayu Duk waɗannan Abubuwan Alkhair ɗin yanasa Hadiyyah ga iyayyensa DA Inno Alhaji Ammar bn Yassir da matarsa Ummul Khair, Addu'a ta alkhair shida zuri'arsa A kullim Alhaji Ɗalhat Abdurrahman A.k.a Alhaji tallafy A.k.a Abbu😇 yanasha
ALLAH kai mana arziƙin da zamu dinga amfanawa kanmu dashi (abunda kaiwa Wani ai shine kaiwa kanka saboda shine a lahira Zai amfaneka)
Anan 9ja yanzu ba Wani company sama da *TALLAFY GROUP OF COMPANY* wanda yake sarrafa kayan masarufi me kyau cikin sauƙi ƙananan companies ana sauke oder irinsu Usman,wanda yanzu anzama mutumin kirki sosai! harda ƴan tebura ma.
Ɓangaren *TALLAFY HOLDING* Hohoho Duk wata irin Mota Ko machine sabon yayi Ko tallan sa aka Fara in Sha ALLAH a anan Zaki Fara ganinsa cikin Rahusa,ga sauran kayan karafa rankacakaf Babu abunda Babu fa Kaya masu Aminci da sauƙi,andinga Oder Kenan!
Companies ɗin Abbu Suna da yawa my fans dayawa ya mallakawa su AQEEL su da jimawa,hardasu Hidayah acikin Rabo,kai ma Sha ALLAH ubangiji yaƙara arziƙi DA tsawon Rai Mai albarka.
Albishirin ku Abbu ya samu jirgin Sama nasa wato *TALLAFY AIRLINE* wanda za'a dinga jigilar mahajjata da sauran tafiyoyi a Farashi mai Rahusa!!!! Dan haka Rashin iyaye Fans ku tawo akaimu Makkah da Madinah Daga nan muzarce wajensu Hadiyyah a batiiiiiiiiiiiiiii
Tsakanin Abbu DA Kawu Isma'il zamansu sai Sam barka shima arziƙi ya faɗaɗa Amana kam yanzu Baya Cin ta kowa ma, Aunty Hauwa tana cikin kwanciyar Hankali da nutsuwa tare day mijinta, Yanzu haka ƴan uwansa Su Aunty Asiya Duk sun huta abunsu ALLAH ya ganar,balle ƴan gata su Zakiyyah, Zahra, Hadiyyah, Hidayah, khadijatu, Zeenah,Hunaif suda yasan Basu da uwa da uba,sai kaaka itama kanta tana wutawa dashi,gasu ALHAJI (wanda yazo wutun shekara gida kwanaki anzama aƙili ga addini,yaji abubuwan dasuka faru ga mahaifiyarsa yayi bakin ciki,Har Gidansu Hadiyyah Yaje lokacin sunanan,karatu ya miƙa ankusa Zama mechanical engineering) Farouk,Hydar da Auta Hafsat sunashan gata wajen kawunsu.
Komai ya wuce tuni Abbu yaiwa Kawu Isma'il magana Akan ya mayar day Sa'adatu gidansa Ko Dan Haɗuwar kan zuciyarsu baki ɗaya,ko musawa Kawu Isma'il bai ba sati bai zagayo ba aka Ɗaura aure tsakanin Kawu Isma'il da Sa'adatu!
Aunty Hauwa wannan karon bataji zafi Kamar wancan ba,Dan haka suka zauna Zaman Aminci itada da Sa'adatu Babu makirci Zaman Amana DA Aminci dama haka akeso ai, Yanzu kam Sa'adatu kuɗin Kawu Isma'il ma basa gabanta ita sai Sallah da istigfari take kullum carbi a hannu.
Gidan mukhtar da matansa Zakiyyah da Bilkisu sai Sam barka Suna zaman lafiya day Aminci ga Yar su Zeenah anzama ƴan MATA Duk da Suna da me musu aiki Amma Zakiyyah ta Hana Zeenah Zama dole tayi aiki,saboda bata manta Bakar wuyar da Rashin iya aikin gida da sangarta ya zamar Mata ba a gidan mijinta a farkon Aurenta ba Dan haka ta tsaya tsayin Daka ta jajarce Akan Zeenah kuma Alhamdullillahi da Alama kwalliya tabiya kuɗin sabulu,Dan Zeenah Babu abunda bata iyaba,ga nutsuwa fa hankali.
Su Bilkisu an kusa sauka ALLAH yarabata lfy.
Zahra ma sai son barka zamansu da Ibrahim ga ƴaƴanta gwanin burgewa Yanzu ma naga Wani cikin jikinta, dangi miji ma Alhamdullillahi.
______NEW DELHI_____
Sai da Suka wuta sannan aka Fara Shiga school ɗaukar lecture ALLAH yabada Sa'a!
Laulayi salamu alaikum Kenan ga Hidayah Suna zuwa India tafara Shi gwamma na Hadiyyah ma,Suma nan suka samu damar ramawa Iya yinsu,Suna kallo AQEEL da Hadiyyah in sunada lecture zasu fice Suna musu dariya Suma suji inda daɗi!
DA yake sunfisu baki ina sai sun rama,ai gwamma su sun Sha amarci dai.
A haka dai sai da suka daɗa wata Biyu Akan wutun dasukayi sannan suka Fara ɗaukar lecture cikin Aminci Kowacce Dama community health ta ɗauka sun Fara lecture tuni musamman Hadiyyah ma wajen wata Biyu!
Su Twin's brother dama kunsan medicine suke ɓida karatu harya Tura musu,Ga kasuwanci da sukeyi na company wanda Abbu ya mallaka musu Alhamdullillahi komai yana tafiya normal ana samun RIBA Mai albarka.
Duk Abubuwan dake faruwa a 9ja Suna Ji sunyi murna da mayar da Auren Kawu Isma'il da Sa'adatu.
Sun samu Hutu Dan haka masu Abu da abunsu tuni sukayo 9ja kuma daidai cikin Hadiyyah 9mnth, koda sukazo tuni Shukhra ta Haifi Yar ta mace an sha Sunan Maryam(sunan matar is'haq data rasu) Suna kiranta nasrim
Itama AKEELA an sauke namiji aka samu sunansa miƙdad ɗan ta tabarakallah ahsanul ƙaaliƙiin yanada kyau Sosai
Gidan Baaba Hadiyyah ta Sauka Duk da AQEEL bai so ba Amma ya ya iya sai haƙuri.
Ko sati ba'ayi ba ta Haifo Twins ɗin ta Duk Maza Bayan Tasha wuya, ƴaƴan ma Sha ALLAH Kamar ɗai ɗai,kai kace AQEEL DA AKEEL ne Suna jarirai!
Faɗar murna fa shagalin da za'ayi ɓata baki ne ƴan Rashin iyaye Fans nake hange wajen sunan Suna haskawa musamman su Haseena da seerat da Aisha Sulaiman da mummy Waleed da MamaGee Yara sunci sunan Ammar da Ɗalhat ana kiransu Aimaan da Amaaan ALLAH ya Raya.
An sha ALLAH shagali Hidayah da cikinta 5month itama
Kar muzo Kuga ɓarin kuɗin da akayi a shagalin hohoho.
Tsokanar da AKEEL yake Masa Har gidansa nacewa yazama gwauro yasa yakoma gidan Abbu DA Zama, haɗe da cewa Kaima akwai lokaci ai ɗan banza kawai!
AQEEL sai zarya gidan Hajiya Baaba yake Amma ina Hajiya Baaba ta rantse sai Hadiyyah ta Arba'ie kuma haka akayi,Tasha gyara na musamman ciki da waje dan haka Ranar kar kuso Kuga zumuɗi wajen AQEEL.
Aiman da Amaaan komai nasu na wajen Hidayah Dan ma cikin 7mnth na hanata Wani abu,hakama AKEEL komai ƴaƴana musamman dayaga Suna kama.
Mus'ab da Mahmoud ALLAH yayi mijin su Khadijatu da Meenal ne fa sukazo sunan 'Twins ɗin Hadiyyah aka Jone abunka da manya Babu ɓata Lokaci aka tsaida magana Khadijatu ta Mus'ab ce Meenal kuma ta Mahmoud ALLAH yakaimu lokacin lafiya.
An sha biki lafiya ankai Amare gidajensu,anashan ƙauna da soyayya abunka da ƴan Boko basu daɗe sosai ba suka Fara halartar University da suka nema kuma sun samu cikin ikon ALLAH.
Hidayah ta Haihu itama Twins again Amma Duk Mata ,ma Sha ALLAH Kamar su Hadiyyah na jarirai Suma ma Sha ALLAH an sha shagali,ankuma maimaita shagali Rashin iyaye Fans Masa gajiya da Hidima!
Yara sunci Suna Ummul Khair da Ummu Rumana ana kiransu Eaman da Amaanah
Tuni su Aiman da Amaan anfara Zama kamannin su da iyayensu Maza ƙara fitowa take,
Again sai da Hidayah ta Arba'ie a gidan Hajiya Baaba itama,sun rama tsiyar da AKEEL yadinga musu,sun dawo gida.
Rainon Eaman da Amaanah yana wajen Hadiyyah gwanin burgewa!
Haka Zaman waɗannan Twins yake day burgewa cikin Aminci da Yar dar juna,tuni Suna koma India Dan cigaban karatunsu....
A gida 9ja
Komai yana tafiya normal Hamshaƙin Asibiti Abbu yake tsamfatsawa ƴaƴansa da iyalansu wato *DOUBLE TWINS H&H CLINIC* an kammala komai jiran dawowarsu Ake a ƙaddamar DA buɗe Shi,su shekara Biyu da kammala karatunsu ma,sun jira matansu su ƙarasa su dawo gaba ɗaya ne.....
________
Yau Ranar farin ciki ne saboda dawowar su AKEEL DA murnar kammala karatun da su Hadiyyah suka yi,da kwali Mai daraja kowannen su!ga murnar buɗe Asibitinsu da za'ayi A washe garin ranar .
Faɗar shagali da bidirin DA akayi na yi murnar dawowarsu DA washe gari na buɗe Hospital ɗin su nayi pages 10 ban gama ba kuyi imagination ɗinsa.
An sha mamaki DA Al'ajabin su Aiman da Amaan wanda sunyi Girma sosai,Indianci sai kace ƴaƴan Salman Khan😄, Su Eaman da Amaanah ma Haka Yara ɓul ɓul Kamar ƴaƴan Indian koda yake ƴan India ne man,dama an sasu a school acan,kamarsu DA AQEEL DA AQEEL su Aiman ƙara fitowa take,Suma su Eaman kamarsu dasu Hadiyyah da Hidayah fitowa take abun gwanin mamaki DA burgewa kowa sai ɗauka yakeyi Yara Babu ƙiwa!
Anci an sha Anyi shagali kowa yayi murna A washe gari Hospital ɗin yafara aiki,Babu cutar da basa dubawa, Surgery, operation,Chemo ƙwararrun likitoci ga kayan aiki Daga Indian da Germany Abbu ya kawo Asibitin gasu AQEEL da AKEEL da Hadiyyah da Hidayah kuma Suma Suna Bada gudunmawa, Zahra ta Ibrahim ma tashigo tawagar, kai Wanga Asibiti ana yabawa da ƙoƙarinsa saboda Shi har masu kuɗi da masu Mulki rage fita waje sukayi neman lafiya Ko duba lafiya to me zasuje Suyi ga magani a gida 9ja, Abunda za'a musu acan Shi za'a musu anan fa asarar kuɗi(ALLAH yakawo mana wannan cigaban a zahiri a Nigeria alfarmar shugaba Saw🙏)
_____________
Ba'a Rufa shekara ba *DOUBLE TWINS H+H CLINIC* yadinga samun awards+2 Kala+2 na yabo da samun nasarori,saboda jajurtattun kuma ƙwararrun likitocin da suke kulawa da Al uma,gashi harda marashi Abbu yake turawa Asibitin a dubasu kyauta(karkuyi Zaton iya masu kuɗi ne no masu kuɗi su bayar aduba su marashi amusu saboda zatin ALLAH matuƙar Sum samu Katin DA Ake rabawa na ganin likita, weekend Aka ware musu. kai ma Sha ALLAH.
_____BAYAN WASU SHEKARU_______
Zama tsakanin AQEEL da Hadiyyah Alhamdullillahi komai normal akwai ƙauna da fahimtar juna ga ƴaƴansu twins Aimaan da Amaaan sai siddiƙa Mai sunan Mommah da akasa da kuma Rabiat (Adawiyyerh) karku manta marikiyar Abbu mana yan amana.
Ɓangaren AKEEL da Hidayah ma haka Zaman yake akwaiyarda da juna tausayawa juna Suma ƴaƴansu Bayan Eaman da Amaanah sun ƙara Ahmad da Mahmoud sai Ma sunan Mommah Suma Suna kiranta saadiƙa.
Rayuwar Ƴaƴan gwanin burgewa gwanin sha'awa ƙarya ne ka ware kace ga ƴaƴan Hadiyyah Ko Hidayah Ko ƴaƴan ma basa shaidawa in kuwa sun banbance to Yasin ba gaskia suka faɗi ba ƴaƴan Hadiyyah zasuce sune ƴaƴan Hidayah saboda yarda da Amana hakama wajen mazan tsakanin AQEEL da AKEEL banbanci a sunane kawai ɗaya Abiy Ɗaya Abbiy.
Zuri'ar Alhaji Ammar bn Yassir day Ummu Rumana tana cikin kwanciyar Hankali da nutsuwa cikin ikon ALLAH Bayan Duk waɗannan ƙalubalen da sukasha Yanzu yazamo tarihi dama haka Rayuwa take komai yawuce Kamar ba'ayi ba,shiyasa a koda Yaushe ka shuka alkhair Ko Dan saboda zuri'arka ALLAH ya dubesu.
ALHAJI an kammala karatu andawo 9ja fa nasara anzama samrayi Sosai ya Dage Aure zeyi Duk da su Hadiyyah Suna tsokanarsa bazasu Masa Aure yanzu ba yaro ne,aikuwa anashan danbarwa sai yace saboda bakida kunya ku Kalle ni da gemu na da hankali na sai ASA dariya gaba ɗaya! An sha bikin kece Raini shima yafara Tara kuɗaɗe.
Su Farouk Hydar anshiga University Suma anfara karatu.
Zeenah kam karatu ya nisa, Saura ƙiris Asha bikinta da Angonta Yusuf.
Auta Hafsat angirma itada Hunaif.
Su ABIE anzama samrayi fa su Haseena ku Nemo mata😄 ƙannen sa little Zakiyyah dasu Na'eem da na'eef Suma anfara tasawa ga iyayensu a gefe Zakiyyah da Bilkisu.
Zahra ma anzama manyan Mata fa ƴaƴanta Bayan Twins Tayi wasu ma,
Meenal da khadijatu ana Zaman lafiya a gidajen mazajensu Mahmoud da Mus'ab dama kunsan abokaine ƙud DA ƙud Dan haka ga gida ga gida,zumuncinsu ya ƙara ƙarfi! ga ƴa ƴa yansu bibbiyu Kowacce Maza
Sa'adatu zamansu da Aunty Hauwa da Kawu Isma'il Alhamdullillahi komai normal kuma ta Haifa Masa Yara biyu,
Ga iyalan Alhaji tallafy ma haka Abun yake Alkhair Baya faɗuwa kasa banza Duk abunda yakeyi shike bibiyarsu Duk wata nasara ALLAH yana Musu dashi kansa ma,Duk Wani ciwo na Zamani irinsu Suga,hawan jini, ALLAH ya tsallakar dashi kullum cikin ibada yake da godiya ga ubangiji,Duk Wani ƙablubale da suka fuskanta zamana tarihi Suma,kalli dai bala'in dasu AQEEL DA AKEELA da suka Shiga a hannun jimmai da Usman, Kamar bazai wuce ba sun Sha wahala da zalunci iri-iri.
Mahakurci mawadaci Mommah ma ALLAH yakawo mata rabonta itada Abbu Dan haka ta Haifa Masa Ummul Khair (Ammy su AKEELA suka Saka mata) Abdulrahman (Abul bait wai baban gida kakansu) da rabiah (Ummul bait uwar gida ) lallai Hajiya AKEELA an iya saka suna.
AKEELA itada doctor Najeeb Kullum ƙaunar junansu suke ga ƴaƴansu Bayan miƙdad akwai Ummul Khair (Nour) da Ɗalhat (Annour) da Safiyyah.
Saudi Da Madinah a Wannan family saidai basuyi niyyar zuwa ba Ko ALLAH Bai Amince ba saboda Tallafy airline nasu ne,fa sauran kasashen fa suke son zuwa.
Wannan family kullum Cikin Godiyar ALLAH day yawaita aikata Abubuwan Alkhair suke.
Itama Shukhra tana cikin Aminci da mijinta ta sake hayayyafa itama.
Daddy ɗan Shukra da Usman ya Girma Sosai ma Sha ALLAH,Amma Zancen duniya Baya ɓuya Saida yasan ta Yadda aka Sameshi yaci Kuka sosai,Har ya Haƙura saboda haka Usman ya Fitar dashi Daga ƙasar yayi Karatu acan Idan ya Girma sai ya dawo Lokacin Babu wanda ya isa ya nuna Masa yatsa.
Mama Jimmai Kullu nafsin zaa iƙatul maut,ankwanta DA ita ba'a Tashi da itaba,mutuwar farat ɗaya su Usman day Shukrah ansha Kuka Yanzu ba uwa ba uba sai haƙuri,an sha Zaman ta'aziyyah su ABBU Duk sun halarta.
______MURFI______
Ɓangaren waɗannan ma'aurata wato Hadiyyah da mijinta AQEEL DA Hidayah da mijinta AKEEL sai Sam barka da yarda da juna sun zame musu mijin Marayu kullum suna alfahari kasancewarsu a matsayin mazajensu Kamar yadda Matan Suma wato Hadiyyah da Hidayah suke Alfahari da zamowar AQEEL da AKEEL matsayin mazaje garesu da Alfahari samun siriki irin Alhaji Ɗalhat Abdurrahman wato A.k.a Alhaji tallafy A.k.a Abbu wanda suke Mantar dasu cewa RASHIN IYAYE...Babbar musibace wacce ada sun ɗanɗanata kwarai dagaske Amma saboda samun waɗannan jajurtattun kuma ababen Alfaharin a Yanzu sun warke wannan tabon,wacce irin rayuwace Basu Gani ba a duniya! wai don Sun rasa uwa da uba acikin shekara ɗaya DA Kaaka a cikin shekarar da batafi biyu ba shine aka mayar dasu ababen tausayi,ba don Basu da kuɗi Ko kadororin da za'a Kula su bane AA,tsabar zalunci da kuma da rasin idanuwa nan guda uku akansu wato uwa ,uba Kakar wajen uban! Lalläi kuwa RASHIN IYAYE (Babbar musiba)(ALLAH ya gafartawa iyayen waɗanda suka rasu acikinmu