Showing 48001 words to 51000 words out of 141223 words

Chapter 17 - RASHIN IYAYE Complete Document by Rabi'atu Muhammad Rabi'u Oum ARQAM.txt

Ribar da ya samu, ya kuma narkawa ya tura musu, wannan karon babbar harka, ce ga Kawu isma'il har ya Fara lissafin filaye da gidajen da zai saya idan odar ta sauka, da irin motar da zai siya har yayi oder jiran riba kawai yake ya tura kuɗin ya karɓo motar, ƴaƴan sa ma tuni ya janza musu makaranta fiye da wacce suke zuwa a da, tun Hauwa ta na Masa nasiha yana ma ta faɗa har ta zuba ma sa Ido, akan wannan wadaƙa da ƙudin, kuɗin su wanene? Ko dai dukiyar marayuce? Ranar da tayi Masa wannan tambayar ne yace in dai takuma saka ma sa baki da magana akan abunda yakeyi a bakin aurenta, idan zakuma ta yi bismillah, ai kuwa tun daga sannan Hauwa sai Ido duk abunda mijinta zaiyi, Amma kuma tana Masa Addu'ar ɓacin ra na.


Tun daga sannan cima da gayu da zauna a gidan Kawu isma'il ƴaƴansa dashi kansa sai wadaƙa suke su tsoma biyar su wanke goma, ya manta da ƴaƴan ɗan uwan sa marayun Allah, bikin Zahra kuna ga Fan's haka yace ha shi da kuɗi Amma yanzu ku diva?


ya na saune zaman jiran oda, yana Hangoshi ya xama one in town, wannan motar da yayi oda ta na ran sa dan haka ma, ya je banki ya ciwo ba shin 30milions dan ya sayi motar da kuma ɗin ka sababbun suttura da sauran gyaran da zaiwa gidansa, da ma tuni ya siye gidan ku sa da shi da yake kango ne, zai faɗada gida na sa, duk maƙota su na kallonsa ga shi irin mutanen nan da Babu kyauta ko sadaƙa ne Kawu isma'il, maƙotan sa ba sa zaman arziƙi.




15milions yaje banki ya ciro ya ta wo da su gida, da ita sai cimma ginin gidan da sauya Masa fasali, ɗaya kuma 15milions ɗin ya turawa wanda yayi oder ta mota a gurinsa, a cikin babbar jaka, sai wani tunƙawo ya ke wai shi Jan wuya an zama Alhaji, ma'aikatan banki kuwa su ka loda ma sa kuɗi a butt sai gida.


Duk wannan kuɗin da aka loda Masa a kan idon wani ɗan daba mai suna ROCI wanda da ma shi abunda yake ka wo shi banki kenan, ya saka Ido, akan masu haɗ_hada da shige da fice da kuɗaɗe ya na da uban gida SNAKE wato 🐍 hamshaƙin ɗan fa shi ne, duk abunda yake faruwa shi ROCI shine yake sanar wa da snake ɗin in dai akayi ca mama ana fitar ma sa da na sa kason,yau ya zo sai Allah ya ƙadddara Kawu isma'il yazo banking fitar da kuɗi, kuma yaga zunzurutun kuɗin daya fitar da su zuwa gidansa, dan haka ya hau machine ɗin sa shi ROCI ya biyo ba yan motar ka wu isma'il domin ya ga no gidansa, kuma ya sanarwa sa Snake uban gidansa..........






**************




Mu leƙa gidan Mukhtar fans, tun ba yan dawowar sa da ga ɗaurin Auren Zahra Bilkisu ta fahimci akwai abun da yake damunsa, kun san ita ku ma Bilkisu abun da ta tsana kenan,ganin mai gidanta a ha lin damuwa, ba ta tambayi me yake damun sa ba, ba wuriminta bane, huriminta shine ya fitar da shi da ga damuwar da ya kasance a ciki shine abu mafi mahimmanci a rayuwarta,sai kuma da ga baya idan ya gaya ma ta damuwar ta sa idan ta na da shawara ta bashi ko mafita ta gaya ma sa ta yadda zai fita da ga halin damuwar da yake ciki, wannan shine siffar Mace ta gari ƴan uwa a kullum muzamo masu kula da damuwar mazajenmu kamar Bilkisu, ya dai seeerat da Haseena Kunga dai Mace ta da ƙawar kuce me zatayi? Sai dai ta kuma ɓata ma sa rai,


Da wannan da mar Bilkisu ta fitar da Mukhtar da ga damuwar da yake ciki, wanda mudai bamusan mene damuwar ba, Amma zamuso muji in zai gayawa mar atussaliha(sunan da Mukhtar yake kiran Bilkisu da shi kenan🤣aikuwa dai ta ci sunanta)




Tun daga sannan ya Mance da wa ta Zakiyyah kamar da daya Mance da ita a ba bin rayuwarsa, sai silar zuwansa Auren Zahra yanzu kam yakuma mancewa🤣


ABIE dai ya na damun Mukhtar da Ummunah jani Abbana(Ummunah zani Abbana) sai kawai ya shareshi ya rabu da shi har ku ka yake akan hakan Amma mukhtar sai yace Masa Ea zan dawo maka da ita, to sai yayi shiru a haka yake rarrashinsa, bai taɓa ma sa zancen a gaban Bilkisu ba, ko da yake dai Matar so ce sai abunda tace ko da a gabanta ya faɗa,


Yau ma dai mukhtar ya na dawowa daga Bilkisu har ABIE su ka tawo yi Masa Sannu da zuwa tun da ga bakin gate,ya fito da ga motarsa ABIE sai murna Abban sa ya dawo,kafin Husna, ƙanwar Bilkisu ce ta zo gidan Hajiya jamila shine fa ta biyo mukhtar ɗin da yaje su gaisa da Hajiya ɗin, budurwace ma Sha Allah tana da ɗan jiki dai dai misali, ta fito da ga motar ta juya baya zata rufe ƙofar motar, ABIE ya hangota, da sauri ya buɗe baki ya ce " Abbana Ummunah ce ta dawo ko? Ranar nan ai munje mun ganta,ku ma kace jaka dawo min da ita, yanzu cine ka aukota Abbana? Yana nuna bayan Husna mai rufe mota, a kunnen Bilkisu ABIE yai wannan maganar,


Kafin Mukhtar yabawa ABIE amsa har Husan ta ƙaraso wajen, kuma ABIE sai ya kama ku ka ganin ba Ummunsa bace,Yaya Husna ya santa farin sani sosai ABIE dan tana zuwa gidan ku ma idan yaje gidan Hajiya jamila ya na ganinta, kuma itama Bilkisu tana zuwa da shi gidansu.




Ba sai ABIE yakama burgima da kukan ba Ummunsa aka da wo ka sa da itaba,


Mukhtar ya na aikin lallashin ABIE wanda yake aikin ku ka, da burgima a ƙasa.




Bilkisu ta ja hannun Husna ƙanwarta suka shige cikin gida fuskarta Babu ya bo ba bu fallasa, jikinta a sanyaye, Inaga Bilkisu ta zata mukhtar ɗaukar ABIE ya ke suke zuwa bikon Zakiyyah,idan zasu makaranta ko zai ɗaukoshi, ko kuma in suka fita da yake ya na ƴar fita da ABIE ya sanyashi a gaban mota.....






Lallai kam ya zata ƙarke da Kawu isma'il ga shi dai Rico ya bishi, ku sanya shi a Addu'a Allah ya tsare Masa dukiyarsa 🤣


Ga Bilkisu kuma ta ji abunda ABIE yake faɗa har ta yi fushi, ga ta kuma ƴar gaban goshi, ya kuke tunanin zata kasance, kunsan dai mar'atussaliha ce ga mukhtar bay son ɓata mata rai😇


Su Hadiyyah da Hidayah kuma buri ya cika ga shi kuma an tsunduma a kogin lobayya 🥰


Lallai akwai cakwakiya nan gaba,🤣😇


Labarine mai tausayi cin amana da tsantsar maraicida sauransu akwai..........


Kubiyo
✍️ Oum ARQAM a Hankali domin warware muku cwakwakiyar da komai ma.........
2/7/24, 4:28 PM - Rãbi'atou Aminou {Oum ARQAM}: *RASHIN IYAYE*
(Babbar musiba)




Daga *Al 'kalamin✍️ Rabiat Amin (oum Arqam)*


*08128131163*


✍️ Marubuciyar...
*Komai Nisan jifa* 📚
*Hakan ba kuskure bane*📚




*_____________*
MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION📚🖊️ *(M°W°A)*


'Kungiyar d'aya tamkar da dubu masu Nazari da Aiki da ilimi burin 'kungiyar a koda yaushe shine ta fad'akar ta Kuma wa'azantar ta Nishad'antar da masoyanta🤙
*____________*




*PAGE THIRTY FOUR 34*


Tun bayan kammala bikin Zahra da akayi, Zakiyyah kam takama wani tari mai wuya, wanda idan ta Fara kamar numfashinta zai bar gangar jikinta,irin dai masu asma sauƙin tarin shine tayi amai, anan zata samu sala ma farkon tarin kenan, lokacin kuma ba bu mai bi takanta, su Hadiyyah da Hidayah suna school, sauran yaran ma hakan,dai Sa'adatu ita kuma da ma na harkar juna suke shiga ba,Shiyasa ƴan uwan Basu san halin da take ciki ba ko ƙadan.


A haka a haka fa tari ya Fara ga ba wa Zakiyyah, idan ta Fara ta rin kuma sai ta ga ɗan tsallin jini a inda tai tarin bakinta yana gurin,Duk wannan yabiyo bayan damuwar da ta sawa kanta ne,akan mukhtar tun da yazo bikin Zahra, ta ga a fuskarsa baima gane ta ba, kuma kamar bazai yafe mata kuskuren ta a gareshi ba, sai kuma uwa uba yunwa da take damunta , ga baƙin cikin Ƴan uwanta gaba ɗaya sun daina kulata, hatta Baaba ko da tazo bikinnan iskar da ta ɗaukota bata kallaba kamar ita ƴar ga ta ai abunnan sun mata yawa sosai, yarinya kamar Zakiyyah ƴar gatan uwa da uba, ga kaakarta Hajiya Sakinah datake a wajenta ƴar lele, ai Abubuwan nan sun mata yawa zuciyar ta bazata iya ɗauka ba,ire_iren tunanin datake a koda yaushe kenan,shine yake ta azzara ma ta komai.


Yau ma ire_iren tunanin da ta durfa fa kenan, Duk da ta na yakicewa saboda azabar da take Sha idan tayi, Amma abun ya gagara gareta.


Ƴan biyu Hadiyyah da Hidayah shigowarsu kenan da ga school sun ga ji tun safe, ɗakin nasu suka shigo Kowacce ta cire uniform ɗin, maghrib ta gabato ɗauro Alwala Kowaccen su ta yi domin gabatar da sallah, Hadiyyah ta Riga idar da Sallah, dan haka ta ƙarasa cikin ɗakin na su, a dai_dai lokacin da Tarin da Zakiyyah takeyi ya Fara nisa sosai, sai yi take ba bu ƙaƙƙautawa ga idonta ya ƙafe numfashinta kam ya jima da sassarƙewa like asma, Ihu Hadiyyah ta kurma ta na zuwa kan Zakiyyah ɗin ta na jijjigata! jinin da take Fitarwa ya fi na kullum, dan yau gashinan a bakinta sosai kamar ta kwurɓu kunu, Hakan ne ya ƙara tunzura ihun Hadiyyah! Ba Hidayah da ta sallame Sallah da ga falour ba hatta Sa'adatu, wacce ta ke shirya girki dan yau I tace da miji, sai da ihun ya girgizata batasan lokacin da ta fito da ga kitchen a kuje ba ta na nufar ɗakin su Hadiyyah ɗin,ko da ta shi ga ɗakin Hidayah har ita ta ƙarasa wajen ƴar uwarta ita ma kuma ta aza na ta ihun! Halin da Sa'adatu ta ga Zakiyyah aciki ita kan ta Duk ra shin imanin ta saida ta razana,sauran yaran ma su Khadija da Haydar da Farouk da kuma Auta Hafsa Suma ihun ya sa sun shigo ɗakin ga ba ɗaya Suma sai ihun yaka gidan ya zama kamar gidan makoki!


Daga uwar har ƴaƴan ba bu wanda ya kawo tafiya asibiti, sai aukin kukan da jijjiga Zakiyyah da Hadiyyah da Hidayah da suke, wanda lokacin ita ma ta dakata da Tarin numfashinta ya tsaya tsak! Alamun ba bu Rai ta re da ita,Ihu ya ci uwar na da,kenan Hadiyyah da Hidayah kam sannan da suka ga ba bu numfashi a jikinta sai suka ajiye ta suka kuma da sa Ihu, itama Sa'adatu da ta taɓa Zakiyyah ta ga komai na ta ya saki kukan ta Fara Amma ba kamar na sauran yaran!


Duk da Yanayin unguwace wacce ba lallai ajiyo abunda ke faruwa a maƙota ba, to ihun ya yi yawa sai da maƙotan suka jiyo, aikuwa suka Fara shigowa ana Zakiyyah ce ta rasu sai sallallami akeyi.


A wannan halin ne mai gida Alhaji gambo ya danni hancin motarsa layin,tun da ga nan yafara cin karo da ƴan tsirarun motane har ya ƙaraso ƙofar gidan anan yaji cewa wai Zakiyyah ce ta rasu, ai ko ciki bai kai motar ba ya ƙarasa da ƙafar sa cikin gidan, har ɗakin da su Hadiyyah suke ɗin, yasamu sai ku ka suke Babu wanda ya rufe Zakiyyah da ake ikirarin ta rasu ɗin, aikuwa nan yafara baɗa dayaga bakinta akwai jini, nan aka ɗaukota aka Sanya a motar Alhaji gambo ɗin jikinta gaba ɗaya ya sake, da Hadiyyah da Hidayah aka ta fi waɗanda suke ku ka kamar ba bu gobe, ɗan uwa kenan, wanda komai yafaru tsakaninku idan wani abu ya sameka saiya ji Babu daɗi, Allah yaqara Mana zumunci a tsakaninmu da ƴan uwan mu🙏
Anbar Sa'adatu a gidan Akan idan suka je asibiti komai yake faruwa sai akira a sanar da ita, a haka mutanen da suka taro a gidan suka warwatse suka adduar samun sauƙi ko Allah ya jikan rai idan sa'i yazo, sauran yaran Sa'adatu ta Fara rarrasa Haydar da Hafsa dan sune yara Amma Khadija da Farouk ai Babu wannan sunsan komai, Amma har sannan hankalinsu a tashe ya ke.


Ko da motar Alhaji gambo ta ƙarasa asibitin da sauri likitoci suka karɓeta aka Fara bata taimakon gaggawa, tabbas da ranta,Amma fa ta Sha wuya sai sannan hankalin su ya ɗan kwanta domin kuwa robar ƙarin numfashi aka saka mata sannan numfashinta ya daidaita, abun gwanin tausayi kamar ba Zakiyyah ƙawar seeerat da Haseena ba😢.
Sai sannan Alhaji gambo ya Kira Sa'adatu yake gaya MATA, cewar ta tawo da Abubuwan buƙata ya gaya MATA sannan ya kashe wayar.


Likita ne ya Kira Alhaji gambo office ɗin sa, anan yake Masa bayani kamar haka, me ya faru da wannan yarinyar a ƙarancin shekarunta da ba su gaza Ashirin da biyu zuwa da biyar da zuciyarta ta Fara kamuwa da ciwo haka Alhaji? Cewar doctor yana kallon Alhaji gambo!


Sai da ƙirjin Alhaji gambo ya bada sauti daram! Jin tambayar da likita yai Masa,
Alhaji gambo ba shi da masaniyar komai kunsani Fan's, dan haka ya ɗan nawa likita labari a taƙaice na Zakiyyah wanda ya sani,har fitowar ta da ga gidan miji, abunka ga likita nan yasan cewa tabbas ta Sanya damuwar rabuwarta da mijinta ne ko kuma ɗan ta da aka rabata da shi, nan dai likita ya gargaɗi Alhaji gambo Akan ai wa Zakiyyah abunda takesu idan ta biɗa bayar farfaɗowarta kodan zuciyar ta ta ƙarasa kamuwa da ciwon, sai kuma yunwa nan ma da likita ya faɗawa Alhaji gambo ta na damun Zakiyyah ɗin wanda itace ta sa mata tarin, da amai a farko,kafin zuciyar itama ta kawo na ta gudunmawar, nan dai likita ya nawa Alhaji gambo shawarwari Akan Zakiyyah ɗin, shi Alhaji gambo yayi zaton damuwar da Zakiyyah ta ke cikine yasanya ta kasa cin abinci, nan kuwa bai san sharrin Sa'adatu bane da Kuma ita Zakiyyah ɗin Rashin kunyarta ta janyo mata Hakan,da kuma Rashin jin magana.


An bata gado a nan, su ƴan biyu da Alhaji gambo yai musu bayanin abunda likita ya ce sun yi kuka, na yunwar da take damunta sunsan wannan su ma da kamshonsu a ciki, Amma matsalar damuwa da zuciya kuma wannan basusan ko mene sila ba, dan kuwa sunsan dai su Zakiyyah bata damu da Mukhtar ba balle ABIE harkar gabanta takeyi har bayan dawowarta gidan na su, kodai daina kulatan da sukayi ne sila? Wayasani ƴan biyu ku bari ta tashi saiku tambayeta😄 komai da Zakiyyah take buƙata na taimakon gaggawa an mata kuma ma sha Allah dan kuwa ancire Robar ƙara numfashi Amma ba ta farkaba, numfashinta ya daidaita , har Sa'adatu ma tazo, ta tausaya wa Zakiyyah ɗin sosai, suna zaman jungum_jungum Zakiyyah ta Fara motsawa, rige_rigen zuwa wajenta sukayi, Sa'adatu ce ta Fara zuwa gaban gadon wanda Zakiyyah taketa juye_juye kamar bata hayyacinta ta na ƙokarin cire ƙarin Ruwan da yake hannunta, Hadiyyah da ma tuni ta Garzaya kiran likita, ai kuwa tare suka shigo dashi, ya zo dan ya ƙarawa Zakiyyah allurar barci ko Allah zai sa ta samu nutsuwa ta farka daidai, anmata allurar, wanda kafin tafara aiki je ne bakin Zakiyyah ya ke furta "Ka yafemun mukhtar Duk abunda nai maka! ka yafemun mukhtar! Ire_iren zancen da Zakiyyah ta ke furta wa kenan har allura ta yi aikinta.


Daga Sa'adatu har Hadiyyah da Hidayah Duk mamaki ne a fuskarsu mene haɗin Zakiyyah da Mukhtar kuma?ita da takewa Rashin mutunci, bata damu da shi ba kuma, tabar su kam cikin duhu, sun bar haka a Zafin ciwo kawai ne, Shi da ma tuni Alhaji gambo ya bar asibitin.


Bayan Zakiyyah tayi barci, litika yace Duk yadda ake ciki wannan mukhtar ɗin da take akbata, cutar ta ta na alaƙa da Shi, dan haka a nemo shi ko ta halin ƙa_ƙane a nemoshi kafin farkawarta ta biyo, inji likita ya na ficewa da ga ɗakin, yabar su baki sake, yanzu ta yaya za su nemo mukhtar? Suce Masa mene? Shawarar da sukeyi kenan a yanzu....




**************






Ko da Mukhtar ya ƙarasa cikin gidan da ABIE a hannunsa, lokacin har Bilkisu ta kai Husna ɗakin da zata zauna kafin ta tafi gida,ita kuma ta dawo falour ta na zaune abunta, ku sa da ita ya zauna da ABIE a hannunsa wanda har sannan yake ku ka, miƙa hannu ta yi ta ƙarbeshi, ta na lallashinsa,Akan yayi shiru, "Ammienah Ummunah Abbana yace je damomin da ica gaci hal yanju bata dawo ba" cikin kukan ABIE yake faɗawa Bilkisu ɗin,ita dai batayi magana ba Akan wata ummansa,aikin lallashi takeyi na ya yi shiru Amma ina yaƙi shiru, kishin ƴan matan ya ta shi kenan, ko da yake Bilkisu ba ta shiga abunda bai shafeta ba,yanzu kuma abunda ya shafi uba da ɗansa da uwar ɗansa shiyasa maybe ba ta shiga ba,tun ya na bore ABIE Akan Ummunsa har barci ya kashe shi ya na ajiyar zuciya,bayan ta kwantar shi a ɗakinsa tai ma sa shirin barci tai Masa addua ta fito da ga ɗakin domin zuwa na ta ɗakin.


Ta samu mukhtar ya na lissafin kuɗi dan haka ita ma ta yi shirin barcin Duk da lokacin bai wuce tara na dare ba, yau da wuri yadawo ne.


Bayan ya kammala lissafin kuɗin da yakeyi,ne ya fuskanci mar atussaliha ya ji me yake damunta tun da ya dawo ya ga kamar ta na da damuwa!


Mar atussaliha me yake damun ki? tun da na shigo farko naga ba haka na shigo na ganki ba! Da walwala na sameki Amma tun Daga lokacin da ABIE yai zancen mahaifiyarsa na ga kin canza mun!? mukhtar ya ƙarasa maganar ya na tallafo ta zuwa jikinsa, alamun rarrashi!
"Zaujin saleh abar maganar nan kawai, abunda ya shafi Maman ABIE ba bu ruwana aciki,kadaina sakani ciki, wannan tsakanin kune , Babu Ruwan Bilkisu a ciki! Ta ƙarasa maganar ta na janye jikinta da ga na sa,
Ƙara riƙeta yayi a jikinsa sannan yai magana
"Ki kwantar da hankalin ki mar atussaliha, ba bu abunda ya ke tsakani na da ita ni a yanzu, Rabuwarsu ta gabato ma, zancen ABIE kikaishi gefe kawai ki ajiye, Zancen ɗaurin Auren

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login