Showing 99001 words to 102000 words out of 141223 words

Chapter 34 - RASHIN IYAYE Complete Document by Rabi'atu Muhammad Rabi'u Oum ARQAM.txt

HADIYYAH DA HIDAYAH ko ya abun yake?


Ya Rayuwar Usman zata kasance?




Jimmai mece makomarta Duk Suna sauran pages na gaba




OUM ARQAM ce ontop 🥰


Aci gaba da gashi ƴan amana
4/23/24, 11:44 AM - Rãbi'atou Aminou {Oum ARQAM}: *RASHIN IYAYE*
(Babbar musiba)


Mallakar Rabiat Amin {oum ARQAM}
08128131163


Marubuciyar.....
Komai nisan jifa
Hakan ba kuskure bane


____________________
*MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION (M.W.A)*
Kungiya ɗaya tamkar da dubu masu nazari da aiki da ilimi burin kungiyar a koda Yaushe shine ta faɗakar ta kuma wa'azantar ta nishaɗantar da masoyanta 🤙
____________________


*PAGE FIFTY FIVE 55*




Up
Up
Up
Up


Burin seerat da Aisha Sulaiman da MamaGee mmn Aslam Maman eyshat mummy Waleed yacika mundawo daga tafiyar dogon zangon da mukayi na saurarar Rayuwar iyalan Alhaji tallafy da gwagwarmayar da sukasha Yanzu kuma mun dawo inda Muke a labarinmu ALLAH yabani ikon kammala wannan labari lafiya Yasa ya Amfani al uma, kuskuren dake ciki ina roƙon ALLAH ya yafe mun🙏




_____BANGAREN SU ZAKIYYAH_______




Zama tsakanin Zakiyyah da Bilkisu sai sam barka,Duk tunanin da mukhtar yake na ganin bazasu zauna LAFIYA ba, Amma ina ita dama Bilkisu baya tunanin za'a samu matsala da ita, Zakiyyah yake tunanin kuma gashi CIKIN ikon ALLAH Tunda ta dawo Babu wata matsala da ta taɓa faruwa tsakanin su kamar da can Baya,yanzu Zakiyyah tayi Hankali da tunani burinta kullum ta kyautatawa mijinta mukhtar bataso taga tafi ABunda Ransa zai sosu ko ƙadan,shi kuma Hakan da takeyi shine yake ƙara ƙaunar ta a Ransa, Duk wannan tsanar da yai MATA ta Baya yanzu a Hankali Take gogewa, ko da Yake dama Halin Zakiyyah mukhtar yake ƙi ba wai ita kanta ba yanzu kuma Alhamdullillahi komai ya gyaru sai dai zaman tare wata rana dole a ɓatawa juna idan kuma aka nemi ya fiya da gafafar juna shikenan.


ABIE ɗan gatan mamman(Zakiyyah) sa da Amminsa(Bilkisu) Kowacce yana son zama da ita, ita Zakiyyah bata ɗaukar sangartar da Bilkisu takewa ABIE shiyasa ma yafi Zama a can gidanta ,nan Babu faɗa balle hantara Duk abunda zaiyi bata mai magana, bawai abu marar kyau ba, ya rone mai kazar_kazar yadinga wasa kenan Yaje nan da gudu yafito nan ga haɗa kaya to ita Zakiyyah bata ɗaukar haka, Bilkisu me ɗauka haka take cewa lafiya ce da ƙuruciya idan ya daɗa wayo bazaiyi ba to barin da Bilkisu takewa ABIE yayi Hakan shine fa yake Masa daɗi yake zaman gidanta can.


Tun bayan daidaituwar komaj tsakaninsu mukhtar dama tuni ALLAH ya buɗa Masa ƙofofin samunsa ga kuma kwanciyar Hankali da Yake samu wajen iyalansa, Suma su Zakiyyah ɗin Suna roƙarsa Akan ya haɗe su guri guda sukam zasufi jin daɗi shima kuma hankalinsa zai,kwanta idan yana zaune waje ɗaya, Duk da dai unguwa ɗaya suke sai tazara wacce batada yawa sosai, tun daga sannan shima dama yana burin Hakan, gidan kusa da Bilkisu ya siya ya shigar dashi gidan abunka da kuɗi cikin ikon ALLAH aka Fara ginawa, Bilkisu takoma gidan Zakiyyah dama shima gidan Babu laifi yanada girmansa, gini yayi nisa jiran haihuwar Bilkisu sukeyi kawai da zarar ta haihu zasu tare a sabon gidansu wanda aka kawatashi yayi kyau sosai,part ukune sama da ƙasa Kowacce nata daban sai turakar mai Gida da ɗakin ABIE shida ƙannensa masu zuwa haka ma an tanadi na mata tun da yanzu ALLAH yafara ba su haihuwar, Bilkisu kam ana jiran tsammani ciki ya shiga wata na goma ma Amma har yanzu sai fatan sauka lafiya, Zakiyyah ce takeyin komai a gidan Duk da Bilkisu tana cewa ta barta tayi itama.




______BANGAREN ALHAJI GAMBO____




Tun da aka Masa Allurar barci bayan zubewar cikin Sa'adatu sai da ya ɗau lokaci kafin ya farfaɗo, jininsa ya hau sosai, ALLAH ne ya taimaka paralyse bai kamashi ba,sai da aka bashi gado saboda ya ƙwallafa rai Akan wannan ciki gashi kuma ya zube, kamar ƙaramin yaro Alhaji Gambo da ya tuna sai Kuka,abun gwanin haushi gwanin tausayi,sai kiran Hajiya ikilima, da Hajiya suwaiba da kuma Hajiya sahura a waya ake gaya musu cewa Alhaji fa ba bu lafiya yana asibiti Duk fushin da suke da Alhaji Akan wulaƙancin da yadinga musu Akan cikin Sa'adatu da sukaji Babu lafiya sai da hankinsu ya tashi Babu shiri sukayo asibitin gaba ɗayansu, Halin da suka samu Alhaji Gambo aciki sai da Kowacce ta tausaya Masa ganin yadda a lokacin kaɗan ya zabge yanata uban Kuka, sai Kowacce tsoron ALLAH ya shigeta da tausaya Masa, saboda Kowacce tasan Zafin Rashin Haihuwa dashi suke fama har yanzu Suma, Alhaji yanzu ALLAH yabashi kuma ya karɓa, ALLAH buwayi gagara misali kenan yabada lokacin da bakayi tsammani ba hakana lokacin da zai karɓa ma haka,
Sai Sannu suke wa Alhaji Suna bashi haƙuri Akan yadaina Kuka ALLAH zai kawo Wani ne da yardar sa.
Alhaji shima kanshi nadama yake da kunyar matansa ta yadda lokacin cikin ya juya musu Baya yake musu hulaƙanci, Amma gashi shi yanzu bashida lafiya Duk sun damu, ALLAH kenan shiyasa a koda Yaushe idan zakayi abu ka dinga tunani da hankalin gaba.


Sa'adatu tun bayan ɓarin da tayi mugun ciwon ciki ya sata a gaba sai da aka MATA wankin ciki, ko lokacin da su Hajiya ikilima sukazo wajen Alhaji tana can ɗakin da take jiyya,bayan sun gama da Alhaji da lallashi ya samu barshi, suka rarrafa zuwa ɗakin da aka kwantar da Sa'adatu domin su dubada,dan kam ganin abunda ya faru da Alhaji Da ita kanta Sa'adatu ɗin sai imani ya shigesu suka sauke Duk makaman yakinsu Akan Sa'adatu yanzu shukam sunga ikon ALLAH, Duk abunka da isarka da tinƙa wonka akwai lokacin yi daga Alhaji har Sa'adatu ɗin su kam su Hajiya ikilima tausayinsu sukeji ma, idon Sa'adatu biyu da suka shiga ɗakin sai Khadija a Zaune ta gaisar dasu, Sa'adatu dai baƙin ciki goma da Ashirin ga na ɓarewar cikinta ga na zuwan su Hajiya ikilima asibitin uwa uba ga na su Hadiyyah na samun mazajen nunawa Sa'a uwa uba ga siriki kamar Alhaji tallafy, Suna MATA ya jiki Amma ko kulasu batayi ba idanunta ta rufe ma, su sunyi Zaton barci ma takeyi dan haka suka fice zuwa wajen mijinsu.


Da suka koma Alhaji Gambo ya tashi daga barcin dama barcin Rabi da Rabi ne,Suna ta Masa Sannu da nasihohi anan yake kenan gafararsu, Hajiya ikilima tace "ai Babu komai Alhaji, yanzu ta lafiyarka mukeyi kuma ƴaƴane muna roƙon ALLAH yabaka ma ba ɗa guda ɗaya ba! Cikin muryar ciwo Alhaji Gambo yace " ALLAH yabiye bakinki suwaiba yabamu masu albarka Kowacce acikin ku ban fiddau tsammanin samun rabo daga gareta ba. Duk murmushi sukayi sukace ALLAH ya tabbatar da Hakan Alhaji.
Cikin ikon ALLAH a Ranar aka sallamo Alhaji daga Asibiti sai gida ranar girkin Hajiya ikilima ne dan Haka daga Asibiti gidansu sukayi dashi.


Itama Sa'adatu an sallameta tayo gidanta,zuciyarta ba bu daɗi, wato Alhaji ita zai juyawa Baya ganin cikin jikinta Babu da ita yake zance,su zuba dagashi har matan nasa shege ka fasa.


Tun bayan Hakan data faru Alhaji Gambo ya Zama mutumin kirki tsakanin matansa Kowacce yana mutinta ta, Suma kuma Suna faranta Masa shaɓanin Sa'adatu yanzu sai Wani Shan ƙanshi da wulaƙanci take Masa! Amma shikam yana kau da kai ya na rabuwa da itane.




______ HADIYYAH DA HIDAYAH_____


Sukam gaba ɗaya Hankalunsu ya ƙi kwanciya Kowacce bata son Abokin Rayuwar da aka haɗata dashi, saboda sukam akwai waɗanda sukeso Mus'ab da Mahmoud ,Amma za'a musu haka, a yadda suke ganin waɗannan ƴaƴan na Alhaji tallafy basu da mutunci musamman ɗayan ma,wanda har sannan Kowacce batasan wanenen nata ba,tunda kuwa sun san dai ƴaƴan biyu ne kuma ba'a ce ke ga naki ba kema ga naki su dai sun san sunan ƴaƴan AKEEL da AQEEL kuma AQEEL ne na HADIYYAH, shi kuma AKEEL na HIDAYAH amma kuma basusan su a zahiri ba ne hulaƙancin ne na wacce oho, Hakan ne Yake sasu cikin tashin hankali, ga kuma mutuncin Alhaji tallafy a idanunsu ta yadda yadinga kulawa dasu da sauran ƴan uwansu, shi dai bashi da damuwa ƴaƴan nasane sai a Hankali Amma ya suka iya haka zasu haƙura su bawa zuciyarsu haƙurin Hakan, Amma a fuskar ƴaƴan tun a Asibiti Suna ganin tsantsar Rashin yarda a idanun ƴaƴan, Amma sukam zasuyi biyayyah ga Mahaifinsu na Auren da yayi musu tun suna ƙanana kuma yana yare yanzu da Babu Ransa bazasu iya bujirewa umarnin mahaifin nasu ba, ALLAH sarki Zakiyyah tun Bayan da abun yafaru kullum sai ta Kira ƴan uwanta a waya tana Kwantar musu da Hankali Akan su Kwantar da hankinsu in sha ALLAH su AQEEL zasu so su, kar su farawa Alhaji tallafy butulci na ƙin ƴaƴansa,zuciyar su Hadiyyah tana Sanyi ganin ƴar uwarsu yanzu tayi Hankali ta zame musu kamar uwa, itama Zahra Hakan takan kirasu tai musu NASIHA, tanacan tana zamanta da IBRAHIM ɗin ta cikin kwanciyar Hankali harda rabo ma tuni ansamu,g Khadija a gefen su itama Yarinya ce me Hankali da tunanin kullum tana nusar dasu itana Amfanin da Abbiy yagani ya haɗa wannan Auren suyi masa biyayyah zasu gani a gaba da kuma alkhair ɗin Alhaji tallafy garesu,Hakan shine sanyaya zuciyar ƴan biyu, sai dai idan sun tuno ogannin nasu AKEEL da AQEEL sai zuciyar kowanne ya tsinke, Sa'adatu kuwa bata daɓa ce musu komai Akan Auren ba, ta fake da batada LAFIYA ne.


Daga Hadiyyah har Hidayah Basu da aiki sai tunani, Hajiya Baabah mutan kaduna itama ya Kira tai musu murna da suka kasance ƴaƴan Alhaji tallafy ne abokan rayuwarsu a matsayinya na kakarsu itama tai musu faɗa Akan su Kwantar da Hankalunsu komai me shigewa ne ALLAH ne yasan meya ɓoye Akan wannan abu.




____GIDAN ABBU___




Harkokinsu sukeyi kamar yadda suka saba, Babu wata matsala, saɓanin twin's Amma su Abbu Suna sane Suna kula da yanayinsu suka yi burus dasu, musamman uban gayya uban ƴan miskilanci, ita kuwa AKEELA tana gidan kuma sai murna takeyi da batum da taji na waɗannan tsala_tsalan twin's ɗin sune matan yayyenta,da ma tun farko taji sun kwanta a Ranta ashe_ashe sai murna da farin ciki takeyi. Hakana itama Mommah, Abbu shima murnar yakeyi ganin su Hadiyyah Basu watsa Masa ƙasa a idanunsa ba na bujirewa abunda suka ƙulla shekarun baya,sune da ma abinji Amma su AKEEL da AQEEL nasu mai sauƙi ne Duk abunsu basa tsallake umarninsa sai agama ƙuncin zasu saukone musamman AKEEL uban ƴan barkwanci,ya kudircewa Ransa muddin su Hadiyyah sukace basaso za'a fasane, Duk da dai wannan abu bamai sauƙi bane dan kuwa yana son cikawa abokinsa amininsa kuma ɗan uwansa Ammar BN Yasir burinsa,to abun yazo da sauƙi alamu sun nuna sun Amince Kenan kukan ne kawai akayi shi.


Yaune bayan sun kammala cin Abinci gaba ɗayansu Abbu, Mommah, AQEEL, AQEEL da AKEELA Suna zaune a falourn ƙasa Abbu ya ɗauko waɗannan vedios ɗin nasu AQEEL dasu HIDAYAH Duk Suna ƙananun Yara zai kunna musu su gani,bai gaya musu ba kawai dai yace zai musu suprise na wani abune,dan haka fuskar AQEEL da AKEEL, gatanan dai ne sauran kuwa fuskarsu wasai a sannan ABBU ya kunna vedio na farko............




Muje next page ƴan amana domin muji yadda zata kasance




Gadaisu AQEEL anzauna za'a kalli vedios na ƙuruciya da soyayya da suka nunawa su Hadiyyah ko Hakan zai sauko da zuciyar su?


Su kuma su HADIYYAH ko ta Yaya zasu ga masu vedios ɗin?


Ya Kawu Isma'il ne wai?


Ku Muje zuwa in Sha ALLAH komai zai warware




Nice dai tamu oum ARQAM
4/25/24, 2:54 PM - Rãbi'atou Aminou {Oum ARQAM}: *RASHIN IYAYE*
(Babbar musiba)


Mallakar Rabiat Ãmin {oum ARQAM}
08128131163


Marubuciyar....
Komai nisan jifa
Hakan ba kuskure bane


____________________
*MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION M.W.A*
____________________




_______WAI INA HAUWA DA KAWU ISMA'IL NE?_______


"Hauwa tana riƙe hannun meenal,idonta yayi ja jur itama ƴar ku ka takeyi, "mama kiyi haƙuri Kinga Abbanmu bashi da lafiya ki kemo ki kula dashi, yanzu Abba abun a Kula ne, saboda halin da yake ci....dan ubanki rufemun baki, ke in kinada Hankali kyaso na zauna da mahaifin naku,Zama dashi ai ƙaddara ce! Hauwa ta tari numfashin meenal haɗe da fincikar hannunta suna ficewa daga asibitin suna tsaida abun Hawa,ita dai meenal bata kuma magana ba,ganin maman tasu ta ɗau zafi dayawa, kuma da ma maman tana da haƙuri Abba bango ya kaita ne.
Mota bata sau ke su a ko ina ba sai a ƙofar gidan Kawu Isma'il sauran yaran ta kwasa da ɗibi kayan sawar su suka ɗunguma Zuwa gidansu Hauwa ɗin.
Basu dau Wani lokaci ba suka je gidan, malam mahaifinta ya na ƙofar gidan nasu,ganin halin da ƴar tasa take ga ƴaƴa ga kawa,kuma ko kulashi batayiba yadda ta saba idan tazo Hakan yasa yabi bayanta zuwa Cikin gidan.
Goggo mahaifiyarta ta samu a Zaune Akan tabarma ta na lazimi da casbaha, ganin irin shigowar da hauwa tayi ya sa goggo katse lazimin ta fuskanci Hauwa wacce ta saki Kukan baƙin ciki,
A sannan malam ya ƙarasa shigowa cikin gidan,
"Ke kuma meke faruwa Zaki kamawa mutane ku ka kamar wata ƙaramar yarinya? Furucin malam Kenan
Goggo tace" Babu Sallama fa kawai sai Kuka naji a kaina, badai Isma'il ɗin bane wani abu ya sa meshi ba? Inji goggo
Antaɓawa inda Hauwa yake MATA ƙaiƙayi cikin ku kan ta zayyanewa iyayen nata abunda ke faruwa!
Tana kaiwa ƙarshe kuwa Malam yace" a kan wannan abun Zaki baro gidanki kun Riga kun tara yara, ai saidai kiyi haƙuri, tun da ALLAH ya kawo ƙarshen lamarin Isma'il ɗin ai yanxu kuma shiryuwa yayi ta,sai dai akiyayi gaba,yanzu Isma'il ai abun a tausayawa ne a jiɓanci lamarinsa a Wannan Halin, haba Hauwa sai kace ba ke ba ke fa me tausayi ce, yanzu inkin rabu dashi a I dai uban ƴaƴanki ne ina kikeson ya jefa rayuwarsa,ko kun rabu baku rabu bane,dan haka ki share hawayenki haƙurin da nasanki dashi kije kici gaba in Sha ALLAH zakiga amfaninsa, nan itama goggo ta sa baki " ki koma Gidan mijinki yanzu ba sai anjima ba, kuma abunda nakeso dake banson ki hulaƙanta Isma'il,muddin kikayi Hakan baza kiga daidai na,yanxu in kinada Hankali sai ki tantsi ƴaƴa ki tawo Mana dasu nan, mahaifin nasu kuma fa?kinsan tsarin malam gidansa ba'a yaji,nan dai Malam da goggo suka yiwa Hauwa NASIHA Akan zaman ta da kawu Isma'il shiyafi alkhair gareta Akan zaman gidan, da kuma yanzu ai shi abun tausayi ne, ba don son ran Hauwa na ta juya ta koma inda ta fito, zuciyar Hauwa Babu daɗi, Amma ina tanada haƙuri ga kuma biyayyar iyaye.


Gidan Kawu Isma'il ta koma, bata koma a Asibitin a Ranar ba sai su Meenal ne Suma koma, zuciyarsu shar Mama ta dawo gidansu.


______Tun bayan watsewar kowa daga asibitin, da tafiyar Hauwa,bayan likitoci sun kori ƴan jarida da sauran jama'ar gari ƴan kallo, kawu Isma'il abun duniya ya isheshi zuciyarsa kamar zata fito waje,ga tozarci gashi Hauwa ta gujeshi, shikam ina zai saka Ransa, "Wannan wacce Irin Rayuwa ce ni Isma'il ta sameni? Na rasa Abubuwa da yawa kuɗin da nakewa yanzu Babu, kuma Babu mai tausaya mun tunda jama'ar gari sunsan ABunda na aikata! Allahu ka yafemun kasanya tausayina a zuƙatan al uma!
Banking da Kawu Isma'il ya ciyu Bashi Lokacin da ya ɗiba zai biyasu kuɗin su yayi Harda kwanaki ma, ga jaridar da aka fitar ta Wannan satin maudu'inta akan kawu isma'il ne da duk abubuwan da ya aikata na zamba da munanan ɗabi'unsa duk an zayyana su ajiki, Aikuwa kunsan dai banking basa ASARA, takanas har gida suka kawo Masa sammaci Akan Suna buƙatar maƙudan kuɗinsu a yanzu ba sai gobe ba,sai suka tarar da Gidan nasa a kulle,suka tambaya kam akace musu ai mai gidan bashi da lafiya yana asibiti suka tambayi asibitin Babu ko tausayi ko imani, ko da Yake ina banking yaga imani shida ko mutum yana kwance an Masa suttura kafin akaishi makwanci sai an biyasu bashinsu kafin a binne mutum.
Hannunka Baya ruɓewa ka yanke ka yar Zakiyyah da Zahra dasu Khadija duk suna zuwa wajen Kawu Isma'il su zauna dashi a Asibitin ko zaiji daɗi,Duk da karayar da yayi ta Fara warkewa Amma ba'a Fara koya Masa tafiya ba, muddin yaran zasu zo Kawu Isma'il ya dinga sunkuyar da kai Kenan alamun kunya.suna kula da halin da yake shiga a Duk lokacin da sukazo Duk da ko daɗewa ba'ayi da faruwar al amarin ba.
Yau Babu wanda yazo daga su meenal sai Hauwa wacce bata shiga harkarsa biyayyar iyaye ce ta dawo da ita gidan Kawu Isma'il ɗin, shi hakan ma yayiwa Kawu Isma'il daɗi tun daa dai ta dawo ai shikenan, yau da gobe ai tafi karfin wasa zata sauko ne.


Kawu Isma'il yayi shiru abun duniya ya isheshi,kawai yaji sallama ba sai an faɗa ba yasan Ma'aikatan banking ne, jikinsa ne ya Fara! rawa sai yanzu ya tuna da bashin baking dayaci, Basu kula da halin da yake ciki ba, suka miƙa Masa takarda ta neman kuɗin su nan da kwana uku idan ba hakaba za'ayi gwanjen gidan da Yake ciki, dan kuwa shi kadaine yanzu kadarar sa, kadarorin ya zuba oda ga yadda ta ka ma, sauran kuɗin kuma nasu Hadiyyah ne Kawu Isma'il ya karɓe dukiyar marayun ALLAH zai kula musu da ita ba bu gara ba bu zago.


Wayyo Kawu Isma'il yabani tausayi matuƙa, ƴaƴansa sai Kuka suke, Hauwa kuwa ba'a san a wane halin take ba dan fuskarta Babu yabo Babu fallasa, numfashin Kawu Isma'il ɗaukewa yayi dan bala'in da bakin cikin da ya shiga, Babu shiri aka Masa taimakon gaggawa,har da su oxygen, sai da ƙar ya farfaɗo, ALLAH sarki Hauwa MATA da miji sai ALLAH, Hakan ce ta kasance da ita, kalamai masu sanyaya zuciya da kwantar da hankali ta dingawa Kawu Isma'il Akan yayi haƙuri, ALLAH ya soshi da rahma da yayi Masa haka tun a duniya, dan kuwa da anje lahira abun bazai kyan gani ba,dukiya da Haƙƙin maraya bala'ine babba, wannan yana sanyaya zuciyar Kawu Isma'il duk da dai Babu daɗi ace masifa kala kala daga Wannan sai wannan!


Kwana uku tsakani kuwa banking yayi gwanjon gidan Kawu Isma'il, Amma ina kuɗin da Suke binsa yanzu, gidan bai biya ba, duk da haka jira Suke ya samu sauƙi ya Basu ragowar kuɗinsu ko kuma su kaishi prison, duk wanda yake jin haushin Kawu Isma'il Akan abunda yayi sai da ya tausaya Masa balle me ƙaunar sa, yanzu dai ina dukiyar dayake taƙama da ita?

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login