Showing 69001 words to 72000 words out of 141223 words
Chapter 24 - RASHIN IYAYE Complete Document by Rabi'atu Muhammad Rabi'u Oum ARQAM.txt
cinye dukiyar marayun ALLAH dakayi bansan meyasa ba? Ko da yake zalunci ne ai yasa! Alhaji tallafy ya faɗa ya kallon Kawu isma'il ɗin a karo na barkatai!
Su kam ƴan ɗakin har sannan Basu dawo daga suman wucin gadi da sukayi ba najin cewa Ƴan biyu suna da Aure! Balle kuma masu gayya masu aiki Hadiyyah da Hidayah ɗin, Kowacce idonta a zare yake gwajin tausayi!
Balle ku ma su AKEEL da AQEEL su ma sock ɗin ne tare da su,to yaushe akayi Hakan amma ba su sani ba!
Sai Alhaji tallafy yai wa Kawu isma'il ɗin ya fayyace musu wannan sirrin na Auren ne ya sa suka dawo hayyacin su domin suji yadda Abun ya faru...
Cikin murya na rawa da alamun kunya Kawu isma'il yace "tabbas hakane kamar yadda Alhaji ya faɗa sirrin da ke tsakani Alhaji tallafy da yayana Ammar shine... isma'il tsakanina da Ɗalhat munyi alƙawari cewa zamu haɗa su Hassana da Hussaina ta da Hassan da Hussain na sa Aure, saboda mu ƙara danƙon zumunci da ke tsakaninmu, kuma kasan ina son twin's tun bayan da aka haifawa Ɗalhat ɗin, to ni ka ashe ALLAH yasa Nima zan samu nawa, kaga cikin ikon ALLAH sai gashi yabani ya bashi kuma kowane iri ɗaya, ka ga idan muka haɗasu Aure abu zanyi armashi zai to albarka in Sha ALLAH,Duk da dai yaran na mu ba wani girma sukayi ba, dududu Shekarar su Hassan din tara ne, sukuma su Hassana huɗu,haka yaya ya sameni yake gayan bayan sun gama magana dakai, Kawu isma'il ya faɗa yana kallon fuskar Alhaji tallafy ɗin kafin yaci gaba!
Ni kuma nace "tabbas hakane yaya wannan abun ai ba wani abu bane, aure baya ƙanƙanta, musamman ma kune iyayansu su kune maɗaura aurensu, in yaso idan suka girma sai a faɗa musu, kawaii, Yaya yacemun" yawwa isma'il ka fuskanceni kenan inaso ka Zama shaida ne, saboda halin rayuwa,yau gareka gobe ga ɗan uwanka, in Sha ALLAH gobe zamu haɗu da kai da Ɗalhat ɗin sai mu ƙarasa maganar ka ji ɗan uwana,Haka muka ga ma wannan maganar dashi, ni nayi gidana shi ma ya tafi gida.
Kamar yadda ya faɗa a washe gari muka haɗu dakai, a masallacin da kuke Sallah bayan an idar da Sallah, kuka yiwa Malam liman magana Akan kuna so a daura Aure da yaranku, Amma yarane sosai, shi kuma malam liman ya tambayeku Hakan bazai Zama an tauye Haƙƙin yaran ba, kar su girma kuma basason junansu, sai Kuka ce in Sha ALLAH Hakan bazai faruba, dan kuwa zakubi Duk hanyar da Zaku saka shaƙuwa tsakanin yaran na ku,har su Fara son junansu in yaso idan lokacin faɗar yayi cewa an Ɗaura musu aure baza'a samu matsala ba,malam liman yai adduar alkhair, dan haka Kuka ce ba sai mutane sun san da ɗaurin Auren ba, in ya so ALLAH yakaimu suka ƙara girma mutane sa sani,in aka tashi shagalin biki.
kai da ɗan uwanka khalil, nikuma nida yaya aka Ɗaura Auren a wannan lokacin,kamar yadda addinin musulunci ya koyar, na dubi fuskar ka data Yaya ba bu abunda yake fita sai murmushi, kai kace Auren da aka Ɗaura na manya ne...Kawu isma'il ya ƙarasa fallasa sirrin muryar sa ta na rawa( bansan meyasa Hakan ba tunawa yayi da ɗan uwansa? Ko kuma nadama ce ALLAH masani)
ALLAHU AKBAR! ALLAH yajiƙan Yaya Ammar Yasa aljannah makomarsa Cewar Zainab da Asiya yayyan Kawu isma'il ɗin, Amma ko meyasa bai faɗa Mana ba ar Hajiya oho! Sai ya faɗawa azzalumi irinka, kai ka baka faɗaba, ALLAH wadaranka isma'il, cewar Zainab ta na share hawaye, da ka bari kenan yaran nan su dinga kula Samari kasan da aurensu, sannan inta ka ma kuma a Ɗaura musu aure, kai wane irin azzalumi ne Wai isma'il, ai dai kasan Aure kan Aure haramun ne, sannan mace da Aurenta ta kula wani namijin, ai shima Haram ne ko? Asiya ta kuma faɗar Hakan Duk suna kallon Kawu isma'il wanda yayi abun tausayi kamar ruwa ya cinye shi, to rai wajen Ashirin kowa kallon sa yakeyi, ga uban abun kunya ace asirinsa yanzu ya tono, ai da kunya kuma a gadon asibiti, shi da take tunanin arziƙin sa ya zo,sai tonon silili ku ma ya sameshi, da jin kuna kaicona! Ni isma'il ya haka kuma!
Sai ƙwalla nagani a idon su Hadiyyah da Hidayah bansan ko na menene ba! Na tuna Abbi ne ko kuma kukan Auren sa ke kan su ne oho!
AKEEL da AQEEL ma fuskarsu ba bu ya bo ba bu fallasa, dan ko shi AKEEL ɗin mai sakin fuska gani nayi fuskar ta Zama iri ɗaya data AQEEL, shi ta AQEEL ku ma sai tafi da can kafin yafara sakewar nan ko mai Yasa Hakan oho? Kubiyo oum ARQAM a Sannu.
ALLAH sarki Hauwa idanuwa sunyi ja jur alamun anata Shan Kuka, da kuma tunanin wane irin miji ALLAH ya haɗa ta dashi ne?
Alhaji tallafy dai ya na zaune har sannan a kan kujera ko da Kawu isma'il yazo ƙarshe a zancen sa Banga canzawar da yayi ba, to mene bai sani ba fans?
Amma meyasa to isma'il kasan da Duk wannan Amma baka faɗawa kowa wannan sirrin ba? Bayan mutuwar Alhaji Ammar BN Yasir ɗin? Tun da baka ga alamun ya faɗa wa Hajiya ba ma? Dan inda sun sani tun a zaman taaziyyar sa zakaji ana zancen, Hajiya ma Zaku iya zancen da ita Da sauran ƴan uwa?
"Ka gafarceni Alhaji tun bayan ɗaurin Auren da akayi ba'a ɗau wani lokaci ba gaskia,yaya bai kuma mun zancen kaba, kuma ban kuma kin ɗuriyarka ba kaima, da naga haka Yaya yaci gaba da harkar sa, Nima kam mene nawa aciki? Yaka aka ɗauki shekaru har ALLAH yaiwa Yaya rasuwa, banji anyi zancen AUREN ba, ni ma Kuma ban yiba,har ALLAH yaiwa Hajiya itama rasuwa,Lokacin ma ai ƴan biyu sun Zama ƴan MATA,har sannan dai kuma Banga alamun ma suna kula wasu samari ba, harna auri Sa'adatu nai zaman gidan na su Banga alamun suka kula Samari ba,sai a ƴan kwanakin nan kuma, cikin bikin ƴar uwarsu, suka samu ƴaƴan manya, Anan tunanina Ya sauya tun da kai dai ba'a gan ka ba, kuma ba bu wanda yasan da wannan auren sai malam liman, kuma ALLAH yai Masa rasuwa tuni, kuma yaran ƴaƴan manya ne, tun haduwarsu da su Hidayah su ka faramun alkhair na kuɗi, shiyasa kawai nayi watsi da wannan auren nasa wannan agabana, saboda nasan na warke yaran marayu ne ba bu uwa ba bu uba, nine dai wanda za'ai wa alkhair sanadin su...
Kawu isma'il ya ƙarasa maganar yana sunkuyar da kai alamun Rashin kyautatawa ga furucinsa!
"ALLAH kuwa ya kyauta maka isma'il, kaikam bansan kuɗi wane irin so kake musu ba, Akan kuɗi kaketa saɓawa mahaliccinka zaka Ɗaura Auren kan Aure, ga cin amana dakayi nacin dukiyar marayu, da Haƙƙin zumunci, Duk dai Akan kuɗi ALLAH yasa dai wannan tonon sililin yazama izina gareka, ya sauya ma ka halaye, Amma ASARA kayita isma'il ta Rai bata kuɗi ba!
Alhaji tallafy ya faɗa yana duban fuskar Kawu isma'il ɗin
Sai sallallami ke tashi daga bakunan ƴan uwansa, Kuka gasu Hidayah da Hadiyyah, su ma ku ma su Zakiyyah da Khadija ba'a barsu a baya ba, hakama sauran abokan arziƙin da suke wajen..
"Haƙon ka bai cimma ruwa ba kam, dan Mus'ab zubair Ƙaraye da Mahmud kabir Duk ƴaƴan abokaina ne, kuma abokan su AKEEL ne shima kansa mijin Zahra Abokin su ne, Duk shirina ne, saboda ya ran ja fuskanta basa kula wasu samarin, shiyasa nasamu Mus'ab da Mahmud Akan su dinga kular mun da su, azummar su na sonsu, su sa musu sharaɗai,banda kula maza su nuna musu sunada kishi, da sauran su,nace musu ƴaƴan abokina ne, shine nakeson suyi muni wannan aiki, nan danan suka amince kuwa, dan yara ne masu nutsuwa da tarbiyyah,sai da suka Fara zuwa wajenka neman izinin zuwa zance, na zata sasuzo suce ka ce Musu ai yaran matan Aure ne Amma ina, sai kace gasunan ALLAH ya Tabbatar da alkhair, kuje wajensu nabaku izini, Hakan kuwa yai mun ciwo, jin ka wulaƙanta Auren yaran, saboda kuɗin da yaran sukazo maka dasu ko money mangal? Alhaji tallafy ya ƙarasa maganar da tambaya ga Kawu isma'il ɗin!
Shi kam Kawu isma'il bai magana ba dan yasan cikin maganar Alhaji tallafy ba bu ƙarya!
Anan dai Alhaji tallafy yaiwa kawu isma'il fallasa irin wanda bai taɓa tunanin za'a yi Masa a Duk irin abunda ya shuka da zalunci a tsawon rayuwar sa ba! Kar ya ta ƙare kenan bori ya Kar boka!
Da zancen makarantar su Hadiyyah da Hidayah da kai Alhaji tallafy foundation da akayi Duk Alhaji tallafy yace Duk acikin Shirin sane, na kyautatawa iyalan Alhaji Ammar BN Yasir ne da kuma, tsare Auren yaransa dake kansu ne! A farkon haɗuwar su da irin gararin rayuwar da suka tsintsi kansu sanadin zaluncin isma'il da kuma na Sa'adatu ga su Hadiyyah da rabuwarsu da juna na tsawon shekara,Duk ya tausaya musu kuma yayi baƙin ciki da Hakan.
Ƴan uwa suna ta godiya ga Alhaji tallafy ga irin jajircewa da yayi Akan iyalan abokinsa.
Shi kam Alhaji tallafy sai murmushin ƙarfin Hali yakeyi, da nu na Babu komai ai shida marigayi akwai Amana ai.
Kawu isma'il dai ba bu bakin magana idon sa ya yi jajur, abun gwanin tausayi,
Hauwa kam ba bu musu race " a yau ba sai gobe ba dole ka sakeni bazan zauna dakai ba azzalumi, ba bu wanda yayi magana jin furucin Hauwa, ganin ta na tujara ne Kawu isma'il yace na sake ki Hauwa fa kikace?! bazaki tausaya min ba!? A halin danake ciki ba? Wallahi na yi nadama!? Kawu isma'il ya faɗa idonsa yana taruwa da ƙwalla!
Kai kasan wannan nadamar ba ni ba komawa cikin gidanka,har abada! Ka ƙaraci tsiyarka! tun da kai azzalumi ne, zaluncinka ya yi yawa! Hauwa ta faɗa gwanin tausayi tana share hawaye, Meenal ce kawai a Asibitin dan haka ta riƙe hannunta ta fice daga ɗakin tana sharar hawaye!
Suma su Hadiyyah da Hidayah kukan suke hakan Mommah, wanda tun da sukazo batayi magana ba kuma batayi motsi ba, jin irin waɗannan ƙulle ƙullen da Kawu isma'il ya aikata da zalunci, gurin su ta je ta na mai rarrashin su Akan su daina kukan, sai Shafa kansu takeyi, kamar ruwa ya cinye su shirun sukayi, tunda Mommah tai musu magana!
AKEEL da AQEEL da suka Zama mutum mutumi basusan meke faruwa ba, saboda hankalin su sun tafi hutu, har sannan kuma na su dawo ba, Alhaji tallafy ya Miƙe alamun sai fice Hakan yasa guard ɗinsa su ma miƙewar haɗe daiwa su AKEEL magana cewa zasu wuce,har sannan ba bu nutsuwa tare da su haka suka fice daga ɗakin su ma,zuwa mota.
Kafin shigar Alhaji tallafy mota sai da yasamu ƴan jaridar nan ya fayyace musu komai, na cewa Kawu isma'il ƙarya yake Duk abunda ya faɗa musu a baya, dukiya ba ƴan fashi bane suka sake ba, hannun jari yasaka ALLAH yaso shine, da tuni yai cuci marayu, kuma yaiwa ƴan fashi Sharri!, ƴan jarida an samu abun da akeso dan haka suka, suka naɗi muryar Alhaji tallafy, sannan suka ɗunguma ɗakin da Kawu isma'il yake dan su kuma samun tahoto,bayan sun yi sallama da Alhaji tallafy ya shige motarsa zuwa gida.
Da ma kuma fitar Hauwa Saida ta samesu da ma tai magana dasu Akan ƙarya mijinta yake nacewa ƴan fashi sun sace dukiyar marayun ALLAH, da Duk wani tuggun da ya ƙulla,aikuwa suka naɗi muryar ta, ga kuma Alhaji tallafy shi ma ya kuma.
Aikuwa ƴan jarida sun samu abunda sukeso, dan Aunty Zainab da Asiya sun bayyana musu komai su ma,su dai su Hadiyyah basuyi magana ba da sauran ƴan uwanus, dan kuwa koma dai menene ai Kawu isma'il ɗin Kawunsu ne dan uwan mahaifinsu baza sosu abunda zai tozarta ba Duk da shine ya janyowa kansa ɗin,Amma su kam ba bu bakin magana
Zakiyyah ma batayi magana ba,
Daga ƙarshe Kawu isma'il suka dangana gareshi, waƙa abakin me ita kenan, nan cikin Kuka kuwa da nadama tare da shi, ya warware gaskiyar zancen cewa ea hakanne Sharri yaiwa ƴan fashi, Amma yayi nadamar Duk abunda ya aikata.
ƴan jarida na fita daga ɗakin kuwa kowa ya watse a ɗakin su Hadiyyah su aunty Zainab kowa ya kama gabansa, zuciyarsu ba bu daɗi kowa ya ci Kuka.
An bar Kawu isma'il shi kaɗai a Asibitin, wanda sai ku ka yakeyi gwanin tausayi!
Ai kafin kace mene yan jarida sun yaɗa zancen ko ina ya ɗauka cewa wannan wanda akaiwa fashin da yace sun sace dukiyar marayun ALLAH ƙarya yakeyi, sai tsinewa Kawu isma'il jama'a sukeyi, kafin dare ai sai zuwa ganinsa akeyi Ido da Ido ana ALLAH wadai gareshi, sai da likitoci duka ga abun zai wuce ƙima ne suka hana kowa zuwa wajensa.
Wannan kukan da Tashin Da Kawu isma'il yake ciki ne ya sa jininsa Hawa, kafin kice me zazzaɓi ya kamashi, ba bu Shri likitoci suka ma sa allurar barci ko ALLAH yasa ya samu sauƙi.....
ALLAH sarki Kawu isma'il yaban tausayi sosai yasin🤧
Meke faruwa ne AKEEL da AQEEL🥲
Kuma su Hadiyyah da Hidayah hakan🤔
ALLAH sarki Hauwa🤧
Muje zuwa ƴan Amana akwai sauran tafiya fa
✍️OUM ARQAM ce ontop 🥰
2/7/24, 4:30 PM - Rãbi'atou Aminou {Oum ARQAM}: *RASHIN IYAYE*
(Babbar musiba)
Daga *Al 'kalamin✍️ Rabiat Amin (oum Arqam)*
*08128131163*
✍️ Marubuciyar...
*Komai Nisan jifa* 📚
*Hakan ba kuskure bane*📚
*_____________*
MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION📚🖊️ *(M°W°A)*
'Kungiyar d'aya tamkar da dubu masu Nazari da Aiki da ilimi burin 'kungiyar a koda yaushe shine ta fad'akar ta Kuma wa'azantar ta Nishad'antar da masoyanta🤙
*_____________*
*PAGE FOURTY THREE 43*
"Mukhtar ne ya zo ɗaukar Zakiyyah da Husna, daga asibitin, saboda da ma haka suka shirya, shine zaizo ɗaukar su,dan ita Bilkisu batazo ba, anyi nauyi sosai Zama daƙar tashi daƙar sai fatan sauka lafiya.
Ya na ganin halin da su Hadiyyah suke ciki,kawai sai yace bari ya sauke su gida,in ya so sai Suma su tafi gida, ba bu wanda baya ku ka acikinsu har Husna ma,wanda ita tausayin rayuwarsu ne yasa ta ku kan,suna ta fe a mota sai ku ka kawai suke, Musamman Zakiyyah itama fa ta iya ku ka,abu kaɗan ke sata kukan, shi dai mukhtar sai suyi haƙuri yake ce musu Amma ina! Kamar tunzura su yakeyi,ku ma ya tambayi ba'a si ba bu shi,dan haka yasa a ransa ko mene dai ya faru wannan abun yanada zafi gaskiya,in Yaje gida Zakiyyah ta wuce ya tambayeta yaji.
Har suka je gidan su Hadiyyah har sannan suna kukan, dan haka kawai mukhtar bai bar Zakiyyah ta shiga gidan ba,yana parking suka buɗe murfin motar sukai cikin gida,shi ma yaja motarsa sai gidansa.
Sannan ku ma har Alhaji gambo ya fita,dan haka Sa'adatu suka iske ita ɗaya a gidan,ana Hakimce a kan sofa, bayan angama ƙullawa su Hajiya ikilima makirci, shi dai Alhaji gambo hankalinsa ya gushe kwatakwata,kuma fans kunsan dai mutumin da bai samu Haihuwa da wuri ba,koma mene zai iya aikatawa ace matan da suke tare ba sune suka samu cikin ba Auren daya ƙara ne,ai Kunga sai anyi uziri, musamman ma ace irin Sa'adatu mai kissa da kisisina ce ALLAH ya haɗa shi da ita, ai fanfo zata kuma Masa, ta dulmiyar dashi,Akan zautuwar da yayi, to Sa'adatu ma tayi kissa haka kurum balle kuma ta samu abun kissar,yanzu ma tunanin da take kenan,wane makircin zata ƙulla ne da zaisa Alhaji gambo,ya sallami su Hajiya ikilima ne? Ta Zama ita kaɗai, musamman cikin nan dake jikinta,in ta Haifi namiji ai shikenan,kaakarta ta yanke saƙa, komai na dukiyar Alhaji ya zama nata, sai yadda ta ga da ma,in ya mutu kuma shikenan da ma ba bu mai sisin kwabo aciki,lallai wani hanin ga ALLAH BAIWA ne,in isma'il ya cinye mun gadon su Alhaji, wannan fa, shi ma dan ba yadda zanyi ne, Amma koya ne zan maganin sa!
Zancen zucin da Sa'adatu takeyi kenan ta na daga zaune! Shi yasa batasan su Hadiyyah sun shigo ba,
Da su Hadiyyah su ka shigo gidan ai sai suka ƙara ƙarfin kukan su,su na shigewa ƙuryar ɗaki gaba ɗayansu!
Sai sannan Sa'adatu ta dawo hayyacinta, da ga zuzzurfan tunanin da takeyi,wanda likita ya hanata yi,saboda ya na shafar lafiyar cikin dake jikinta da ku ma damuwar da tasawa kanta a ƴan kwanakin nan wanda bamusan mene yake damunta ba?
"Zuciyarta ce ta wani irin bugawa jin su Hadiyyah sun shigo su na Kuka,dan haka harda tuntuɓe da bakin ƙofa wajen shida ɗakin na su, dan ta ji meke faruwa?ko dai wani abunne ya faru?to ai ko da ta tawo lafiya ƙalau ta barosu,su na wasa suna dariya, tana wannan zancen zucin ya ƙarasa ɗakin!
"Ku kuma lafiya kuke?Zaku shigowa mutane gida ku na Kuka? Sa'adatu ta faɗa zuciyarta cike da tararrabin abunda zasu faɗa MATA!
Hadiyyah cikin ku ka tace" wai Aunty ashe wannan Alhaji tallafy ɗin, Abbi ya sanshi,Wai kuma ƴaƴansa tuntuni aka haɗamu Aure dasu tun kafin mu girma" Hadiyyah ta ƙarasa cikin Kuka!
Ai Sa'adatu batasan lokacin da ta zauna ba bu shirba, dan cikinta yai wani irin juyawa wacce ta fice ƙima!
Da rawar baki Sa'adatu tace"ban.ban..ban...gane me kike faɗa ba Hadiyyah? Abokin Abbi kuma?An Ɗaura muku Aure da ƴaƴansa? Lallai kam Ɗalhat ne ai!
Sai sannan Hidayah tai magana "Aunty kinsan da ma komai Amma ki ka ƙi faɗawa kowa?!
Ita dai Sa'adatu batasan me Hadiyyah tace ba, saboda su man wucin gadi ta tafi! da azabar da mamarta take MATA! Dan kuwa wannan ta shin Hankali ne wanda ba'a saka Masa rana ba!da tunanin ya Hakan ta faru kuma!
Tunani ta lula na yadda abun ya faru..... Abbi ya shigo gida ranar Sa'adatu ce da girki ba yan ya kammala Abubuwan da ya sabayi, ya Kira Ummu Ruman da Sa'adatu ya haɗa su waje ɗaya a falourn sa, Anan yake faɗa musu cewa shi da Ɗalhat sun haɗa aurensu Hadiyyah fa yau ɗinnan, kuma da isma'il akayi komai, yana son a dinga kai su Hadiyyah gidan Suma su AKEEL adinga kawo su nan,tanan za'a samu shaƙuwa tsakaninsu wanda ko da sun girma za'a iya samun daidaito tsakanin su kawai sai a bayyana, to tun daga sannan kuma ba'a jima sosai ba, alaƙar dake tsakanin Abbi da Ɗalhat tai Sanyi, suka daina alaƙa, tun daga sannan kuma komai ya tsaya, bayan rasuwar Abby kuma ita bata faɗa