Showing 102001 words to 105000 words out of 141223 words

Chapter 35 - RASHIN IYAYE Complete Document by Rabi'atu Muhammad Rabi'u Oum ARQAM.txt

Ƙadan daga cikin masifar da take samun mai cin dukiyar maraya kenan, matuƙar bai nemi gafararsu ba, kuma ya dawo musu da dukiyarsu wacca yaci ba, abu goma da Ashirin f
Ga kuma cin amanar zumunci da yayi. ALLAH ya tsare mu cin dukiyar maraya da cin amanar zumunci.








_________ AKEEL DA AQEEL_________


"Tun da Abbu ya kunna Vedios ɗin Babu wanda yai motsi cikinsu kowanne da abunda Yake saƙawa a zuciyarsa, Amma idan sukace Vedios ɗin Baya burgesu ko kuma bai ba su nishadi ba ƙarya ne, su Abbu da AKEELA da Mommah Babu abunda suke kwasa sai dariya, ganin yadda su AKEEL da AQEEL lokacin Suna yara yadda kowanne Yake burin ace ƙanwarsa tafi ta kowa,da Duk Wani shirme da suka dinga yi akansu Hidayah ɗin,ga ƙaunar da aka zuba musu tun da ƙuruciya sai kace wasu manya,har lokacin da suka ɗan tasa Kowacce burinta ta Bawa yayanta abunda ta sai kace wasu manya abun gwanin dariya!
Jin dariyar su ABBU taƙi karewane Yasa Babu shiri mai gayya mai aiki wato oga AQEEL ya tashi cikin sauri yabar falourn jin dauriyarsa ta ƙare,shima AKEEL kamar jira yake yabi bayansa suka bar su Abbu a flourn to dama Vedios ɗin ya ƙare,suka bar su Mommah baki a sake haɗe da kunshe dariyar da sukeyi.
ABBU yace ƙyale ƴan wofi mu mukayi farin ciki da ganin wannan vedios ɗin balle su ma,zasu gama abunsu ne, haka Abbu ya haɗa kashe kayansa kowanne yashige wajensa suna kwasar dariya.




AQEEL da AKEEL kuwa Basu tsaya a ko inaba sai daƙinsu AKEEL ne yafara dariya da kuma cewa " bro kalli wani abu sai kace a shirin film ko a Novel wai ni dakai ne Muke wannan show ɗin,lallai ne dole su Abbu suyi Vedios ɗin nan, yana dafa kafaɗar AQEEL yana ƙarashe maganar!
Shi dai AQEEL bai magana ba sai dai murmushin da yakeyi a daidai lokacin, yana Zama a kujerar da ɗan uwansa ya zauna, "abun nan bro Nima yabani mamaki sosai,wai mune Muke Wannan abu KAMAR wasu manyan Samari kai ALLAH ya shiryamu fa, ai dole su ABBU su yanke Mana hukuncin Aure ya ƙarasa maganar ya na murmushin gefen baki, jin ABunda AQEEL yace ya daɗa sa AKEEL dariya, haɗe da cewa "musamm kai sai kace irin wannan ƙaton saurayin nan,kanayin abu Cikin gadara da taƙama kai dama,bro haka kake tun asalinka, Ashe abun naka gaba yayi ba bayaba! ALLAH ya shirya ka kai dama tun Asalinka kai mai izza ne da gadara, ga maganinka nan Abbu yayi Nima ka zanyo min Aure tun bansan mene shi ba, gwanda ma kai ai dama da sonsa ka ta......Duka AQEEL ya kaiwa AKEEL a Baki yana shigewa toilet yabar AKEEL yana kwasar dariya abunshi.


Tun da yashiga toilet vedios ɗin nan yake dawo Masa na rayuwar ƙuruciyarsu suda waɗannan yaran,wani abune yaji yana shigarsa game da hakan a haka ya kammala abunda zaiyi ya fito daga toilet ɗin.


Inda ya bar AKEEL anan ya sameshi a Zaune shima ya faɗa duniyar tunani "lallai wannan abu da mamaki yake ni dama yaran nan suna burgeni ashe dama da alaƙa TSAKANIN mu! Ikon ALLAH!
Zama kusa dashi da AQEEL yayi shine ya dawo dashi daga tunanin daya lula"
"Bro ganin vedios ɗin nan danayi ya Sanya nafara jin Wani abu game da yaran nan,Amma kuma bansan wacce daga ciki tawa ba? In dai wannan me surutun ce ai kuwa Kullum wannan bakin saina Masa hukunci kasan abunda banso kenan! AQEEL ya faɗa yana ɓata fuska!
"Kayi ta tawa Kenan bro Nima dama suna burgeni kasancewar su twin's kamar mu,ga kuma halin da suka tsinci kansu, Amma Nima idan wannan me shiru shirun ce Nima ALLAH bazan ɗauka ba dole ta koma kamar ni,banson mutum ya zauna kamar dutse,nan dai sukai ta tattaunawa tsakaninsu abun gwanin sha'awa kowa yana faɗar albarkacin bakinsa.


Tun daga sannan kuma sukeson ƙara ganin wannan vedios Amma ina! Ai da kunya su tunkari Abbu, mutanen da suka nuna basason Hakan, Kowacce hanya sunbi ko ALLAH zaisa su ga flash ɗin a inda Abbu ya ajiye Amma ina!








_______GIDANSU HADIYYAH______

Ko ƙadan Basuji daɗin abinda ya faru da kawu Isma'il ba,kuma har jaje sukaje suka Masa,hakama su Zahra kai abun yaiwa Kawu Isma'il Zafi fa, yaran da yaso ya wulaƙanta su sune suke kulashi,har ita Zahra tagayawa Ibrahim hakana itama Zakiyyah ta faɗi ma mukhtar ALLAH ne yasan me zasu Masa.


Alhaji fa andawo daga tallafy foundation anzama Saurayi sosai ga Hankali kai bakace shine ba a shekarun Baya ba, yadda rayuwarsa taso gurɓacewa,ya sauke al Ƙur'ani mai girma ga sauran littattafai abun gwanin sha'awa,ha Sana'a daya koya ta gyran kayan wuta,waya, computer,fanka,tv kai cikin ikon Duk Wani abu wanda yake amfani da wuta zai iya gyarashi, kuma Duk a tallafy foundation ya koya, kowacce Sana'a ana koyawa sai wacce kaga damar koya,saboda haka ma Alhaji tallafy ya ɗau nauyin karatun Alhaji wanda zai karanci electrical engineering a China in sha ALLAH.


Gida ya kacame da murna da dawowar Yaya Alhaji, barinma abokan wasa Hadiyyah da Hidayah Duk da dai har sannan walwalar su sai a Hankali.


Tun bayan tafiyar Alhaji foundation da Abubuwan da ya faru dabayanan sai da Alhaji yaji labarin, yayi murna da mutuwar Auren Aunty (Sa'adatu) da kawu) sannan kuma yayi murna da yaji labarin ai ƴaƴan Alhaji tallafy sune mazajen su Hadiyyah sai tsokanarsu yakeyi, dayaga basa so kuma sai ya koma nasiha,da nuna musu cewa fa ƴaƴan Alhaji tallafy Basu da matsala sun gaji halin Mahaifinsu bazasu wulaƙantasu ba in Sha ALLAH,saboda suna Zuwa foundation lokaci Zuwa lokaci kuma basa wulaƙanta mutane,har sannan dai Hankalin su Hadiyyah bawai ya kwanta da su AKEEL bane kamar yadda kowa Yake karfafa musu gwiwa,ganin Alhaji bazaiji daɗi ba idan Basu sake ba yasa suka sake kamar sunji nasihar ta sa,Hakana yaji Auren Aunty (Sa'adatu) da Alhaji Gambo, wannan kam sai da ya canza fuska, Amma bai magana ba ,haka yasa Hira kafin Yaje ya wuta.


Sai da suka keɓe da Auntyn tasa sannan yai magana "haba Aunty har yanzu bazaki daina haka ba mijin Hajiya ikilima fa Kika aura alhalin ƙawarki ce,baki ga Auren ki fa Kawu yadda ya zame miki a ha...... Ya isheka ai ka dawo banson jin Kowacce magana daga bakinka idan ba hakaba zan saɓa maka wlh, cikin fushi Sa'adatu tai maganar" wanda dama cikin baƙin cikin Alhaji Gambo take tun bayan sallamarsa daga Asibiti, ga na su Hadiyyah kuma shine shi kuma yanzu zai zo ya ƙara MATA wani"
"ALLAH ya wuci zuciyar ki Aunty cewar Alhaji yana barin ɗakin haɗe da yiwa mahaifiyarsa Addu'ar shiriya dan kuwa har yanzu da sauran ta , lallai Alhaji yayi Hankali da tunani in da da ne ai da tuni ya mayar MATA da magana, Tallafy foundation kenan ALLAH yasakawa Abbu da alkhair akan Samar da wannan cibiya, mai ba da tarbiyyah da taimakon al Umar musulmi musamman marayu.


Yaushe Sa'adatu zatayi Hankaline da tunani, ai ko ganin ɗan ka ya Zama nutsatstsen yaro ga sana'ar sa a hannu ai ya isa kayi Hankali ka sauke kome ke kanka,dan kuwa ai da tuni ya zama ɗan daba.


Alhaji bai zarce ko ina ba sai ɗakin su Hidayah,domin acigaba da hirar yaushe gamo, Duk da Ransa Babu daɗi Akan abunda Aunty tai masa,ganin ƴan uwansa yasa ya Mance Duk wata damuwa tasa, ACIKIN hirar sune ma ALHAJI yake cewa "sisters zan shigo ɗakin Abbiy, naji yana faɗawa Kawu, Duk da akwai ƙuruciya sosai gareni lokacin,sai na fasa shigowa na tsaya naji "Akwai wata jaka Isma'il acikin ɗakin nan waje kaza, lokacin yana Rashin lafiya,kafin akaishi asibiti yacewa Kawu dan ALLAH ya Adana Masa ita, yasan wannan cutar ba ta tashi bace, idan yaransa sun girma yanaso ya Basu ita, to tun daga sannan zancen jakarnan yake raina,har ALLAH yaiwa Abbiy Rasuwa, Ganin Aunty da kawu sun jone wai shine zai aureta, da irin zaman da suka Fara tsakaninsu Babu tausayawa gareku, Aikuwa naji Kawu Isma'il yana gayawa Aunty wai Abbiy yabashi wata jaka shi har yau bai duba ba Amma may be takardun wasu kadarorin ne aciki, ai kuwa sai Aunty tace yakamata kawai ka duba kagani idan yaso sai muyi kashi mu Raba ni dakai tun da Babu wanda yasani,sai da ƙirjina ya buga Lokacin! ALHAJI ya faɗa,banyi wasa ba,dama ɗakin Abbiy Kawu Isma'il yake ciki bai kulle ba yafito ɗakin Aunty cikin ikon ALLAH kuwa na haura sama inda Abbiy yagawa Kawu Isma'il nan kuwa nake ma duba sai ga jaka,na mayar da komai Yadda yake na fito, sai daƙina da ita,anan nai MATA kyakykyawan ɓoyewa yanzu haka inason muga ko mene aciki! ALHAJI yanakai nan a zancen ya ya saki murmushi,su dai su Hadiyyah jikinsu Duk yayi Sanyi jin wasu kuma Abubuwan da kawu ya shirya wanda asirin bai tonu ba sai da Alhaji ya dawo, Hadiyyah take "shikenan bro Amma ba yanzu ba sai ka kuma wutawa! Yadda kikace haka za'ayi ƴar kanwata,yasin ƙarya kakeyi na girmeka! Cewar Hadiyyah cikin tsiwarta dama ALHAJI tsokana tashi faɗar Hakan.


ALHAJI yace tun lokacin dana fuskanci Kawu Isma'il baiga wannan jaka ba, matsala ta Fara faruwa tsakanin Aunty dashi,ita tana tunanin ya salwantar da dukiyarne, shikuma yace MATA ai bai ban gantaba,ni kuma dama ga baƙin cikin danake ciki ga wannan yasa ni a halin dana tsinci kaina Amma Yanzu kam ai sai labari in Sha ALLAH Bayan wuya sai daɗi sister's ɗina.....




Tofa ƴan amana!!!!
Muje dai zuwa next page dan muji yadda zata kasance, Amma fa nasha typing yau wayyo🤧


✍️oum ARQAM ce ontop 🥰
5/7/24, 3:00 PM - Rãbi'atou Aminou {Oum ARQAM}: *RASHIN IYAYE*
(babbar musiba)



Mallakar Rãbiat Ãmin {oum ARQAM}
08128131163


Marubuciyar
Komai nisan jifa
Hakan ba kuskure bane


____________________
*MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION M.W.A*
____________________


*PAGE FIFTY SEVEN 57*




_______WAI INA USMAN NE?_______




___Usman Kowacce mace mu'amula yake da ita, Babu ruwansa da yarinya ko babba,indai ya taya aka siyar Shikenan,Ance zara bata barin dami kuɗin da yakewa MATA bushasha dasu sun tasamma ƙarewa, harka kenan zata dakata, farkon zuwansa UK da ma barikince ta kaishi ba Wani abu ba dan Hakan ƴan Homosexual (ƴan neman maza) suka kawo Masa tayi Amma farko yaƙi amincewa, kuma ba ƙaramar dukiya zai samu dasu ba,


Yanzu ganin Babu kuɗi saboda shi harkar MATA yakeyi, Hakan kuwa akayi sai ga Usman tsundum a harkar neman maza, idan yasamu kuɗin kuma sai ya nemi MATA dasu, innalillahi wa Inna ilaihi rajiuun Abun Usman gaskia yayi yawa, bayan bin maza da MATA harda Shan giya,
Haka Yake fantamawar shi, kwata kwata ya manta da rayuwar mahaifiyarsa da ƴar ƙanwarsa wacce ya cuta ya barta da miki acikin zuciya, balle wata Akeela kuma.
Yajima da wannan harkar, matsalar da ya Fara fuskanta itace ta ciwon ciki mai tsanani kamar ze mutu daya ziyarci asibiti akace hantar sace ta Fara kamuwa da ciwo, hankalin Usman ya Tashi sosai, Amma doctor ɗin ya Kwantar Masa da Hankali akan in yanashan magani kuma yana kiyaye dokokin da aka gaya masa zai warke ragal,to amma Usman ya Riga yai mugun sabo da Shan giya ya kasa daina Sha,a haka fa yake rayuwarsa, sai abu na biyu riƙewar Baya da ciwon kai mai tsanini ma bari ɗaya, inda nan ma doctor yace Masa Homosexual da Yake ne yasa Masa Hakan,idan bai dai na ba nan gaba tashi ma zai daina,kuma sexual infection zai kama Shi,wanda al aurarsa zata samu rauni da matsalolin da zai fuskanta a ɓangaren mu'amular sa da MATA, bincike ya nuna yana yawan mu'amula da mata kuma mabanbanta ,kuma Baya kare kanka daga haka! Duk bayanin da doctor yakewa Usman yanaji hankalinsa ya tashi sosai,to amma kuma gaskia bazai iya rayuwa Babu mace ba,nan Doctor yabashi SHAWARA Akan kawai yayi Aure ya zauna da iya matarsa, ko kuma ya zaɓi mace ɗaya ya dinga mu'amula da ita,sannan homosexual yadaina yi saboda jijiyoyin al aurarsa sun Fara sanyi nan gaba akwai matsala .


Usman Ya bi maganar doctor ta xama da mace ɗaya ,wata baturiya mai suna clara, ta maƙalewa Usman dan kuwa Usman irinta ne yana MATA abunda yakeso, takeso,kuna jarumine kamar yadda clara take faɗawa Usman, dama hakane yasa ta amince da Zama dashi, dan kuwa da kuɗi a hannunsa, ya mallaki Abubuwa da yawa ga dukiya, nan Usman yaci gaba da Zama da clara ita kaɗai, Shan giya ma da ya ga ciwon ciki yana so ya kashe shi sai ya daina sha yafara jin sauƙi, Homosexual ne dai bai fasa ba saboda anan yake samun kuɗi idan suka ƙare fa. Matsalar da Usman ya Fara fuskanta da clara itace ƙorafin ita gaskia bashi da lafiya Baya gamsar da ita, shi kansa Abun yafara damunsa Akan Rashin jimawa,ga Wani ciwo da Yake damunsa mai tsanani a gabansa, yai tunanin hakan ne yasa Baya jimawa, Yaje wajen doctor yai Masa Bayani, inda yace Masa Homosexual ɗin da yakeyi ne yasa Masa, hakan kuma idan bai Dena ba nan kaɗan wajen zai samu raunin da yafi na da ma, hankalin Usman ya Tashi haka yadawo gida da tulin magunguna.








_____SU HADIYYAH DA HIDAYAH FA?___


Haka ALHAJI sai da yayi wajen sati biyu, sannan ya ɗauko wannan jakar, Sa'adatu batasan wainar da ake toyawa ba, dan yanzu ko kula yaran bayi takeyi ba har ALHAJI shima haushin sa takeji, dan Haka ma Duk budurin da akeyi bata sani ba.
A ɗakin su Hadiyyah aka buɗe jaka, kunsan mene aciki🤔 ba komai bane illa wasu flash sai kuma wasu takardu wanda su Hadiyyah basusan ko ma mene ne ba!
Dan haka takan takardun suka bi in da ALHAJI yace zai karanta a fili kowa yaji kamar haka zuwa ga Ƴaƴana ƴan biyu Hadiyyah da Hidayah...... Nan dai ALHAJI ya karanta musu Duk abunda takardar ta ƙunsa, ba komai bane illa yadda aka Ɗaura musu Aure dasu Akeel kamar yadda Alhaji tallafy ya faɗa musu, sai nasihar da yai musu, na Masa biyayyah Akan Auren, domin kuwa nasan wannan ciwon bazai barni ba nakai har lokacin da zan gaya muku komai ba basuyi mamakin Hakan ba,da ma ai sun yarda da abunda yafaɗa da kuma Kawu Isma'il shima, sai kukan kewar Abbiy da sukayi sai suka ga kamar a gabansu, Wannan flash ɗin ba kowa bane illah ku dasu Akeel da irin soyayyar da suka nuna muku tun ƙuruciya, nasan in Sha ALLAH zai faranta ranku, kusan cewa ba mu haɗa ku Aure ba sai dan mu karfafa Amincin da ke tsakanin,kuma kuma in sha ALLAH zakuyi alfahari da Hakan, ALLAH sarki su Hadiyyah sai suka ga kamar yanzu Abbiy yake maganar, kawai flash sukeson gani,gashi yanzu Basu da TV, nan ALHAJI yace bari ya fita wajen abokinsa Imran ya karɓo laptop ɗinsa,aikuwa yai Sa'a yananan dan haka Babu wata damuwa ya ara Masa dai gashi yadawo!
"Vedio na farko da su Hadiyyah suka Fara kalla na dambarwar da akasha tsakanin Akeel da Aqeel ne na yadda kowanne Yake Bawa ƙanwarsa kulawa,sai ga su Hadiyyah suna dariya da shewa wacce sun manta rabon da suyi irinta,Hakan har ya damu Sa'adatu wacce take can ɗakin ta, ci gaba sukayi da kallon vedio bayan vedio, sun samu nishaɗi sosai Amma kuma Kowaccen su zuciyarta tana waswasi Akan abokin rayuwarta dan kuwa, sunga yadda su AQEEL suka canza da da da Yanzu ba ɗaya ba Amma sun barwa ALLAH komai shine Zai shiga lamarinsu akai!
"Lallai su Hidayah Irin Wannan nuna soyayya haka nasan Yanzu soyayyar da Za'a Sha sai tafi ta da dan Yanzu anyi hankali!cikin tsokana ALHAJI yayi furucin yana kallon ƴan biyu, aikuwa ko wacce ta russunar da kai suna dariya ƙasa ƙasa, Hadiyyah ce tace" kai wai me yasa baka da kunya ne ALHAJI mu fa yayyenka ne kake faɗa Mana Hakan" cikin tsare gira Hadiyyah ke zancen! Nan ba dambarwa ta kaure tsakaninsu ALHAJI yana shine babba dan kuwa akwai shi da son girma, Alhalin yasan sun bashi watanni ƴan biyun! Ƙara hayamiyar ne yasa Sa'adatu fitowa daga ɗakinta zuwa wajensu rai a ɓace!
"Wannan wane Irin iskanci da hulaƙancine Zaku mayarwa mutane gida kamar na mararsa Hankali! Duk sai suka shiga taitayinsu kuma, shi ALHAJI ya fice zuwa mayarwa da Imran laptop ɗin sa jikinsa a sanyaye,dan kuwa bayajin daɗin Hakan tun da yadawo yaga Aunty kamar batason dawowarsa ne ko me?
Ta juya tanawa su Hadiyyah kallon banza! Tana kallon jakar dake gefensu, dan kuwa ta tunata, wacce take tunanin Kawu isma'il ya salwantar da ita, "wannan jakar fa nan sukayi mata bayan abunda jakar ta ƙunsa jikinsu a sanyaye, sai taji zuciyarta tayi Sanyi jin ashe isma'il dagaske Yake ɓata tayi, tayi alwashin cin uban ALHAJI idan ya dawo,wato ita zai wulaƙanta Akan jaka ya ɗauke ya ɓoye, to abunda Yake tunani ba shi bane ai ɗan banza marar mutunci, cewar Sa'adatu acikin zuciyarta,kafin ta fice abunta,ko ta tambayi ina takardun ta karanta,ko itama abata flash ɗin tagani.


Hakan yabawa su Hadiyyah mamaki matuƙa! Akan wannan Hali na hulaƙanci da Shan ƙamshi da Aunty take musu, tunda tasan wannan zancen, fans Nikam nace musu hassada ce ai tasa ta Hakan🌝 ,abun suka yakice.


Wani nishadi su Hadiyyah suke Ganin wannan vedios ɗin, da kuma mantar dasu baƙin cikin da su Mus'ab da Mahmoud suka sanya su,Duk da ɓangare guda akwai tausayawa kansu da sukeyi in suka tuna dasu Akeel da yanayin da suka shiga tun jin su matansu ne tun da jimawa.




_______GIDAN MUKHTAR_____




cikin ikon ALLAH! ALLAH ya sauki Bilkisu lafiya inda ta Haifo baby gil, me kama da ABIE sak, wanda dama mukhtar suke kama dashi Kenan,daidai lokacin da an kammala ginin gidan da zasu koma ansaka komai na more rayuwa aciki, dan haka suka koma gidansu da sabuwar baby kamar yadda ABIE yake kiran babyn dashi.


Babu wanda yakai Zakiyyah murna, tunda akayi haihuwar bata zauna ba tayi wannan tayi wancan, kai bakace Zakiyyah bace 🤔 Husna ƙanwar Bilkisu ita ce zatazo ta zaunawa Bilkisu saboda aiki Amma fa fur Zakiyyah taƙi tace Husna tayi zamanta ita me takeyi, Amma Duk da haka sai da baba kulu kakarsu mukhtar tazo ta zauna a wajen Bilkisu saboda wankanta da na Baby, kunsan dai Halin Zakiyyah bata iya wankan babyn ba ita ma 😅, wannan abu da Zakiyyah tayi ya ƙara MATA ƙima a idon mukhtar wanda dama tuni ƙimarta ta dawo, haka ma wajen maama(Hajiya jameela maman mukhtar) wacce

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login