Showing 39001 words to 42000 words out of 141223 words
Chapter 14 - RASHIN IYAYE Complete Document by Rabi'atu Muhammad Rabi'u Oum ARQAM.txt
anata yi maka asiri kala_kala ha dole ka Zama haka ba.
"Bayan Sa'adatu ta gama hirarta ta 'kawarta Hajiya ikilima, sai da yamma tayi sannan tai mata sallama, tai tafiyarta gida, lokacin su Hadiyyah har sun manta da komawa gida suma,nan dai sukai mata yamai jiki tace da sauqi, kuji 'karya
"Tun bayan zuwan Sa'adatu gidan abokin Alhaji Ammar bn Yassir Alhaji gambo fa da labarin da ta bashi nacewa ai isma'il ya saketa, sai kuma yafara tunanin ta da 'kwadayin aurenta, Saida yasan yadda yayi ya saci number d'in Sa'adatu a wayar matarsa Hajiya ikilima kuma aminiyar Sa'adatun a zummar zai kirata su kulla ala'ka, ta Aure
ita ma Hauwa matar kawu Isma'il ta koma gida lafiya, kuma taiwa mijinta albishir d'in cewa aikuwa Alhaji tallafy d'in yace zai d'auki nauyin karatun su Hadiyyah zuwa university zai musu komai,da to take amsa mata kawai, dan hankalin sa yana kan system d'insa yana WANI Aiki Akan hannun jarinsa da ya zuba, kuma riba ma sha ALLAH an Fara samu fa, yafara jin alert ta account,
Mai gida bakayi murna ba, cewar Hauwa
To tashi zanyi ina rawa da wa'ka sannan zakiji cewa ina murna, please ki 'kyaleni Aiki nakeyi fa,
Shikenan ai ALLAH ya kyauta maka,
Nan kuma ta gaya Masa cewa Alhaji yayi 'kalau abun sa Duk WANI rashin Kunya da shaye_shaye ya daina, yazama yaron kirki,
"Ai dama nasan za'ayi hakan tallafy foundation in dai yaro ya shige ta cikin ikon ALLAH yana shiryuwa ALLAH yasaka Masa da alkhair dai
Allahumma Ameen cewar Hauwa tana barin gurin
ganin hankalin mijinta yana kan system d'in sa alamu sun nuna WANI Abu mai muhimmanci yakeyi
A dai dai lokacin kuma ya kammala aikin da yake a system d'in sa , yace Hauwa kulu ina Zaki kuma Mai naji kina cewa Akan su Hadiyyah ne? Banji sosai ba ,naji dai kince zancen karatunsu ko? Alhaji tallafy zai d'au nayi to shi kuma me ya..........
Muje zuwa next page muji abunda zai faru
Me kawu isma'il zai fad'a Akan cigaban karatunsu Hadiyyah?
Ya batun Sa'adatu da Alhaji gambo shin zata amince Masa idan ya miqa buqatarsa gareta????
Da sauran su
Lallai Sa'adatu kin xama maci amana kenan mazajen aminanki ne ke Kuma suke son ki lallai, ALLAH yasa dai karta amince......
😭😭😭😭😭😭ALLAH ya gafartawa Zainab da y'ay'anta Baki d'aya ya haskaka kabarinsu ya kar'bi shahadarsu Yasa aljannah makomarsu baki d'aya yabawa y'an uwa da mijinta Haqurin Wannan jarrabawa🙏🙏🙏
✍️Oum ARQAM ce ontop
2/7/24, 4:28 PM - Rãbi'atou Aminou {Oum ARQAM}: *RASHIN IYAYE*
(Babbar musiba)
Daga *Al 'kalamin✍️ Rabiat Amin (oum Arqam)*
*08128131163*
✍️ Marubuciyar...
*Komai Nisan jifa* 📚
*Hakan ba kuskure bane*📚
*_____________*
MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION📚🖊️ *(M°W°A)*
'Kungiyar d'aya tamkar da dubu masu Nazari da Aiki da ilimi burin 'kungiyar a koda yaushe shine ta fad'akar ta Kuma wa'azantar ta Nishad'antar da masoyanta🤙
*____________*
*PAGE TWENTY NINE 29*
An saka Ranar Auren Zahra da saurayinta Ibrahim bala wata biyu,Wanda da ma an jima da yin zancen Auren exam ta tsayar,lallai ne lokaci yazo zamuga kawu isma'il Wanda aka bashi gidan su na ga do aka saka y'an haya yace idan ALLAH yakaimu Auren su sai Ayi musu wahala da kud'in hayar.
"Kamar yadda Alhaji tallafy yai al 'kawarin Zuwa wajen su Hidayah HAKAN akayi, kowa yasan Alhaji sananne ne a garin, dan haka bai d'au body guard ko d'aya ba, sannan motar d'aya daga cikin ma'aikatan foundation d'insa ya aya Mai sau'kin kud'i,bai samu wata matsala ba ta ganeshi har layin su Hadiyyah yaje yayi parking d'in motar dakansa, a bakin gate d'in gidan, wani yaro ya gani shi d'aya yace shiga kace Alhaji 'Dalhat ya na magan, ai Baaba naji tasan Alhaji tallafy ne, Ranar kuma Duk yaran gidan sunanan babu school ismaliyyah kuma sai azahar, shi kuma shigar wuri yai musu, wannan karon ma an samu sa'bani da sa'adatu batan, taje wajen saukar Y'ar 'kanwarta.
"Haydar Baaba ta aika tace "kace ya shigo Alhajin, nan danan Kuwa Alhaji ya shigo a Flourn su Hadiyyah Baaba tai Masa iso,
"Shikam Alhaji tallafy tun daga gate d'in gidan da tsarin ginin yasan tabbas Marigayiya Alhaji Ammar bn Yassir shima kam ya dama lokacin Yana raye, Amma ga yadda halin rayuwa ya Sanya iyalansa, d'aya d'an sa ma ya fad'a shaye_shaye, kuma yaga tsa rin gidan Duk ya lalace fentin gidan Duk yayi ba'ki da tiles din jikin bango Duk ya ciccire, 'kofofi Duk sun lalace, tarazo ne a tsakar gidan Duk ya faffashe,alamu ya nu na da ice suke amfani ga haya'ki nan Duk yayi shaida, fanfon dake wajen wanke_wanke shima kansa ya cire,Baya tunanin da ruwa ma a gidan yanzu, kai abubuwa da Yawa Duk sun lalace a cikin Wannan gida, Duk a lokaci guda Alhaji tallafy yayi nazarin wad'annan abubuwan,
'farko so yayi ya Aiko bodyguard D'IN sa yai Duk WANI Abu game da zancen school D'IN su Hadiyyah din, Amma Kuma sai yayi tunanin yazo da kansa kawai, Ashe ALLAH ne yaso yazo Dan yaga abubuwa da Yawa da suke bu'kata, Alkhair baya fad'uwa kasa a banza.
Lokacin da Alhaji tallafy ya shiga flourn sun gaisa da baaba cikin mutunta juna tana bashi girma yana Bata,haka ma yaran gaba d'aya sun gaisar dashi ciki da tarbiyyah, shikam ya yaba yarannan, musamman twin's.
Sun tattauna da Baaba Akan zancen school D'IN su Hadiyyah, sannan Baaba ta 'kwad'a musu Kira, dan bayan gaisar da shi da sukayi falon Sa'adatu suka koma su Basu guri su xanta, bakin Hadiyyah da Hidayah ya'ki rufuwa tun zuwan Alhaji tallafy domibln sun san zancen school ne. Murna ta 'karu lokacin da Baaba ta kirasu,sun tawo a tare cikin nutsuwa,shikam wad'annan Yara ALLAH ya Sanya Masa 'kaunar sa a cikin zuciyarsa tun lokacin da d'an uwansu Alhaji ya Basu labarin sa,
Sun yi magana dashi Inda ya tambayesu wane course suke buqata a university d'in to ra'ayin su yazo d'aya Duk community health suke so, ya jinjina musu kuma ya Basu kwarin gwiwa, sannan yace anku sa Jamb da UTM in Sha ALLAH zai sai musu form, zai Aiko bodyguard D'IN sa sai su cike sunyi Murna sai Godiya suke Masa, yace babu Komai kamar y'ay'ana twin's nake kallon ku, su ma haka suke ra'ayin su d'aya su ma,
"Sun yi magana da Baaba Akan zaman Hidayah a Kaduna state,sai dai ta dawo kano d'in su xauna ita da Y'ar uwarta suyi karatun tare,dan dama dole ce ta rabasu,yanzu Kuma sun dawo, Baaba tace ba bu Komai sai ta koma da Hunaif da Zeenah d'in, ta d'ebe mata kewar Hidayah d'in,kuma shi ma zai sa su a makaranta Mai kyau kuma zai dinga musu aike , Ita kam Baaba ba bu bakin magana sai Godiya take Masa yana ba bu Komai, Baaba kam tasan alkhair Alhaji Ammar bn Yassir ne yake bibiyar ahalin sa, Amma irin wannan tago mashin alkhair haka,kai ma sha ALLAH.
A haka Alhaji tallafy ya gama Duk tataunawar da zaiyi da Baaba ya kammala, CIKIN salama sannan yai musu sallama.
Alhaji tallafy yaga Zakiyyah yayi tunanin Zuwa ziyara gida tayi.
'Bayan tafiyar Alhaji tallafy daga gidan sai murna ta kacame tsakanin su, twin's kam baki yaqi rufuwa,yanzu sun dawo guri d'aya ga karatunsu ya kusa d'orawa burinsu kenan kuma burin mahaifinsu Akan su Ashe zai cika ALLAH yasakawa Alhaji tallafy da alkhair dai.
'ko da sa'adatu ta dawo Duk yadda sukayi da Alhaji tallafy Baaba ta gaya mata, Amma ko ta nuna wata murna sosai, zuciyarta, sai quna take mata, Akan me Alhaji tallafy zai d'auki nauyin karatunsu kuma, da ta sani bata ce aje wa Alhaji Visiting ba, ai da be gan su ba, lallaai Sa'adatu baki sani ba ai ko da basuje ba shi kam Alhaji tallafy yayi niyyar tallafawa marayun ALLAH kuma ta Allah bataki ba shi Mai haquri yana tare da ALLAH.........
'kwana biyu tsakani Baaba tai haramar tafiya gida Kaduna state ita da Hunaif da Kuma Zeenah, domin batayi gaddamar tafiya ba, saboda Hunaif itakam tana son sa, ALLAH yakaiku Lafiya, Alkhairin ALLAH ya kai miki Baaba, Baaba tace wa Hidayah in ALLAH yakaimu lokacin bikin Zahra sai na tawo miki da kayan ki da sauran abubuwan Amfaninki, sai da Baaba tayi kukan rabuwa da Hidayah itama tayi kukan, sabo kenan.
Haka Hadiyyyah da Hidayah suka ci ga ba zama tare da juna, a gefe guda Suna ta shirye shiryen bikin Zahra.
Zakiyyah Kam kud'in ta sun 'kare Wanda take ci, Wanda take Samu a gidan darajar idona Baaba ne, da kuma Zeenah, idan an bata nata taka wo mata taci.
Rayuwa fa taiwa Zakiyyah zafi sai ta wuni ta yini bata ci ba, su zahra da Hadiyyah da Hidayah kam har kar gabansu sukeyi basa shiga wurimin ta shi yasa zaman gidan yai mata za fi, babu Mai kulata kuma Wannan hud'ubar Baaba ce, Khadija ce Mai kulata kawai ita ma idan ta na makaranta shikenan.
Itama Hidayah ta samu koyarwar a islamiyyah d'in su Hadiyyah,su kam Yara sai mamaki suke su biyu irinsu d'aya haka, dan ma basa saka kaya iri d'aya nata Suna Kaduna state ai da abun sai yafi mamaki,sun fad'awa Mai makarantar cewa Amma fa sun kusa Fara zuwa school bai jii dad'i ba.
**************
Tun bayan da wowar su AKEEL daga tallafy foundation, abubuwa da Yawa suka sauya na damuwar AKEELA da d'an sau'ki kam, tun ta ta ga abun da ta gani kuma ta ji abunda ta ji,sai tausayawa ma'abota foundation D'IN takeyi musamman su twin's d'innan.
Shikam AKEEL dama damuwar ta sa da sau'ki Amma yana tausaya twin's din nan shima Kuma sun burgeshi, matuqa, shi kuma AQEEL dama bai gan su ba, yadai ji labarin su a Wajen AKEEL dan da sun zau na zai Fara ba shi labarin su, "bro ka ga wad'annan twins d'in y'an uwan wannan yaron na foundation d'in Abbu, ai suma kamar mu suke, kamar su d'aya, na so ka gansu, yadda Muke dakai d'aya Mai surutun tsiya, d'aya kuma bata da magana sosai, Amma dai ta fika magana dan ina kula dasu tana wa sister d'in ta magana in tai Mata Amma ba sosai ba, please bro kai ma kazama kamar ta, idan nai maka magana ka din ga mayar min, kadaina mun shiru ko ka dinga d'aga min kai kaji, rayuwar twins d'innan abun sha'awa, ina so mu zama irin su, kullum hirar da AKEEL yake wa AQEEL Kenan, tun Ba ya magana in Yana bashi labarin har yake magana,sannan Kuma yana son shi kam yaga wad'annan twin's din da brother d'in sa yake basa labarin su.
'ko da Abbu yaje gidansu Hadiyyah, sai da yadawo yake Gaya wa Ummuh Anan suke jin yaje,sai AQEEL yake tunanin ina ma Abbu yaje dasu gidan sun gan su d'in, ko dan ya huta da labarin da AKEEL yake ba shi na su,
'Da haka kuwa AQEEL ya d'an saki ransa KA'DAN, dan ana d'an Hira da shi yace "i ko a'a" Wanda da Ba'a samun haka sai dai d'aga kai ko kuma ya saka idon sa ana mutum alamun yana ji kenan,
wannan canza war da AQEEL yayi tafi yiwa AKEEL sama da kowa a gidan dad'i, Amma da kuwa kamar ba shi da d'an uwa abo kin yin Hira,yanxu kam ma sha ALLAH
Tun da dai asalin su da ma shi AQEEL ba Mai magana bane sosai, Amma sauyawar sa ta samo a sali ne tun daga lokacin da wannan mummunar 'kaddarar ta samesu musamman shi da AKEELA, HAKAN yafaru Duk sana din Rashin mahaifiya gare su, da cin amanar da Ammar su ta yi a garesu shine sanadin komai da ya sauwa rayuwar AQEEL da AKEELA, Duk da YANZU ka so 50% CIKIN100% ya ragu sai abun da Ba'a ra sa ba,
Amma abubuwan sun yi yawa fa, a hakan ma an sha fa ma da AQEEL da AKEELA d'in kafin samun sau'kin rashin lafiyar da kowannen su ya had'u da ita, Duk da kowanne da kalar ta sa cutar Amma sanadin ta guda d'aya ne
Yan amana Muje page 30 domin muji yadda zata kaya
Amma YANZU aka Fara wasan.....
Rashin IYAYE Akwai maraici, tausayi,cin amana da kuma xazzafar soyayyah Mai tsayawa a rai
😭😭😭😭😭ALLAH ya gafartamawa zainab da iyalanta gaba d'aya ALLAH ya haskaka kabarinsu ya kar'bi shahadarsu baki d'aya ya bawa mijinta da y'an uwanta ha'kurin jure rashin su 🙏🙏🙏🙏
✍️Oum Arqam ce
2/7/24, 4:28 PM - Rãbi'atou Aminou {Oum ARQAM}: *RASHIN IYAYE*
(Babbar musiba)
Daga *Al 'kalamin✍️ Rabiat Amin (oum Arqam)*
*08128131163*
✍️ Marubuciyar...
*Komai Nisan jifa* 📚
*Hakan ba kuskure bane*📚
*_____________*
MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION📚🖊️ *(M°W°A)*
'Kungiyar d'aya tamkar da dubu masu Nazari da Aiki da ilimi burin 'kungiyar a koda yaushe shine ta fad'akar ta Kuma wa'azantar ta Nishad'antar da masoyanta🤙
*____________*
*PAGE THIRTY 30*
"Alhaji Gambo ya Kira Sa'adatu a waya kamar yadda ya d'au al wa shin Kiranta,
Sa'adatu tana zaune a Flourn ta, tana tufka da warwara Akan sha'anin Rayuwa yau da dad'i go be ba bu, wai sune suke cikin wannan Hali na Rayuwa, Anya Kuwa zata jure!
Dama Sa'adatu ita da y'an uwanta basa Auren wan da ba shi da kud'i,in kuwa suka ga Mai kud'i ko a malamai sai sunyi asirin da zai so su, to hakane ma yafaru da Alhaji Ammar bn Yasir d'in shima ai ba son ALLAH bane, ta malamai ta bishi har ya Aureta, san nan Kuma tazo ta 'kalla bawa Ummu Ruman a CIKIN gidan ta, Wanda kuma tun kafin Alhaji Ammar bn Yasir yazama WANI suke tare, tun daga gidan haya Duk wahala Ummu Ruman ta sha a CIKIN gidan ta, Saida dad'i yazo sun Fara Tara Yara ALLAH ya had'a shi da Sa'adatu tazo CIKIN gidan ta dinga takura mata,makirci kala_kala ta shiga ta fita ta raba ta da mijin sai da ALLAH yakawo karshen abin sannan har saki biyu Sa'adatu ta sa Alhaji Ammar bn Yasir yaiwa Ummu Ruman ALLAH ne yayi zatayi Masa takaba ma, ai nasan baku manta da halin Sa'adatu ba.duk y'an uwanta babu wanda yake Auren talaka sai Mai kud'i, kuma ya na autar su idan yana da mata to matar zata koma bora in Basu koreta daga gidan ba ma gaba d'aya,kuma y'ay'an mijin su dinga gallaza musu, akwai ya yar Sa'adatu Wanda take zawarci akwai kanwarsu Mai kud'i take aure tazo haihuwa ta rasu,saboda abun kunya sai Wannan ya yar tasu babba ce fa ya yar Sa'adatu ce, ita Kuma 'kanwar tasu Sa'adatu ma ta girmr ta, Amma tana mutuwa suka din ga shiga su na fita har Saida mijin 'kanwar ya Auri babbar yayar ta su, saboda abun kunya ALLAH ya kyauta, suma su Sa'adatu Akan kud'i ba bu abun da baza su yi ba.
"Ringing d'in wayarta ne ya dawo da ita daga tunanin da takeyi,
ba 'kuwar number ta gani, da kamar baza ta d'au ka ba sai kuma ta d'auka
"Assalamualaikum wake magana?
" Fatan da Hajiya Sa'adatu nake magana? Cewar Alhajin gambo
" Ea nice! Wake magana?
"Ma sha ALLAH Alhajin gambo ne, fatan kinje gida Lafiya? Tun ranar da Kika zo nake son kiranki,Amma Kuma bani da number d'in ki,sai a wayar Hajiya na Samu!
Sa'adatu kam mamaki ta shi ga, meya sa Alhajin gambo ya kirata?
"Sa'adatu na ji kinyi shiru? Ko da WANI abun ne?
" A'a Babu komai mamaki dai nake na Kiran da kai min, ai ba yau na Fara zuwa gidan ka ba, baka ta'ba Kira na kayimin ban gajiya ba!
"Lallai Sa'adatu ban da abin ki lo kacin da kike zuwa gi da na, ai da aurenki kike zuwa, mezai sa na Kira ki a waya ki na Matar aboki na? Yanxu kuwa babu igiyar ko wa a kanki, kin san dai manufar da ta sa na kiraki ko' sabo da ke ba Yarinya bace
Duk su ba dad'in da Alhaji gambo yake yi Sa'adatu tana saurarar sa
"Auren ki zanyi Sa'adatu kuma nan ba da jima wa ba, ko dan na karewa Abokina iya linsa, tun da shi Isma'il bazai iya ba ni ALLAH ya kawo ni!
"Alhaji Wannan zancen da kakeyi Duk na ji, WANI han zari ba gudu ba kar ka manta Alhaji Ikilima 'kawa ta ce fa 'kud da 'kud, bana son halin da mu ka shiga tsakanina da Hauwa Matar Isma'il yakuma faruwa da mu,Amincin mu ya ta'bar'bare fa Alhaji!
Duk Wannan ba damuwa bace Sa'adatu, yanzu da Kuka rabo da Hauwa mene ya same ki? Kuma na ga Aure sunnar ma'aikin ALLAH ne, ba zaman da duro muka 'kulla ba, ba kuma mummunar Ala'ka ba, share komai zanzo gidan ma!
Nan dai suka d'an ta'ba Hira tsakanin su, ba suyi sallama ba sai da suka tabbatar da tsayayyiyar magana, kuma Sa'adatu ta Amince da Alhaji Gambo.
Dama zuciyar Sa'adatu ba 'kin Auren Alhaji gambo zatayi ba, ta yi hakan ne sabo da bariki, kar Alhaji gambo ya ce ta amince nan da nan.
Sa'adatu ta yi murna sosai fa da Alhaji gambo yai mata zancen Aure, ita da ma burinta a koda yaushe Hakane, tun AUREN ta da Isma'il ta ke murna, sai da Isma'il d'in yq zamar mata mugu ne ta yi dana sanin Auren sa, Amma da kam murna takeyi ta haye ta bad Ummu Ruman a ta sha sai kuma ga shi Ummu Ruman d'in ta bar mata duniyar ga ba d'aya, shi kawu Isma'il d'in da take murna a kanshi ya so ya cu ceta ya 'kwa ce mata gidan y'ay'anta,ku ma dukiyar y'ay'anta yanzu ta na hannun sa yana so ya cinye.
Su na gama wayar ta Kira Fa'izah yayarta ta gaya mata cewa ta yi kamun Alhaji gambo abokin Alhaji Ammar bn Yasir d'in, kuma mijin Hajiya ikilima aminiyarta !
Yaya fa'izah ta ce babu komai ki aureshi ina ruwan mu da wata hajiya ikilima Auren ta ya ke ke ma auren ki zaiyi,to shinenan Yaya cewar sa'adatu tana ka she waya.
Tun DAGA sannan Alhaji Gambo suka jo ne da sa'adatu, kuma har gi dan yazo, ko kun ya tun da Alhaji Ammar bn Yasir ya ra su bayan gaisuwa bai Kuma zuwa gidan ba,dai sana din Sa'adatu, su yaran ba su ka wo komai ba, tun da sun san shi farin sani abokin Abby ne,sun