Showing 84001 words to 87000 words out of 141223 words

Chapter 29 - RASHIN IYAYE Complete Document by Rabi'atu Muhammad Rabi'u Oum ARQAM.txt

ma wai sunan ƴar ƴar uwarki haba ai zaluncin yai yawa!


A haka AQEEL ya farfaɗo,kamar yadda ya saba farfaɗo wa, dan haka nurse tazo tai kiran Ɗalhat Akan yazo AQEEL ya farfaɗo, Lokacin jimmai tace wa Ɗalhat bari taje gida ta tawo da abincin dare,bai hanata ba kuma bai bata amsa ba a haka ta fice da ga Asibitin, Ɗalhat ne ya nufi ɗakin da AQEEL yake, Alhamdullillahi kamar yadda yasaba tashi haka ya tashi, Babu wani razani ko jin kunya, na cewa tabbas shine ya aikata wannan mummunan Aikin! Dan haka Doctor Najeeb ya kuma Tabbatar wa ƙazafi ne aka ƙullawa AQEEL ɗin da cutarsa, da sassarfa Ɗalhat ya ƙarasa, ga AQEEL ɗin yana Masa Sannu, yana amsawa shi kuma daƙar saboda har sannan mararsa tana Masa ciwo kaɗan, kafin AQEEL ɗin yace "Abbu Yaushe kadawo? Nazata sai jibi zaka dawo?doctor Najeeb waje ya Basu, aikuwa Hakan yaiwa Ɗalhat daɗi, dan Haka yabawa AQEEL amsa da " eamn dawowa nayi kawai sai na sameka a halin da kake ciki! Meyasa bakyasha maganin ka ba? Kasan doctor yace kadaina sakaci da Shan magani!
Cikin dauriya AQEEL ya kwashe Duk yadda ya kasance dashi tun da ya tashi da safe har sukaje school da zuwansu masallaci da tawowar sa gida Shan magani, inda yace Abbu nidai nasan na shiga cikin ɗakin mu daga nan sai Yanzu dana farka! AQEEL ya ƙarasa gayawa Abbu haɗe da cije bakinsa!
Tunda AQEEL ya Fara yiwa Ɗalhat bayani zuciyarsa ta Fara cinkewa lallai akwai lauje cikin naɗi, Amma Babu komai yanzu saura AKEEL farfaɗowar sa da kuma me gayya me Aiki AKEELA! Ɗalhat ya ayyana a zuciyarsa
Jinjina kai Ɗalhat kawai yayi yana shafa kan ɗan nasa,cike da tausayi yanzu da tuni shikenan ya tsine Masa, ko kuma ana kallonsa da aikata babban zunubi irin Hakan, shi AQEEL da baisan me yake damun mahaifin ba ma! sai ya tambaye shi ina AKEEL domin kuwa ya saba yana farkawa yake ganin sa tare dashi, Ɗalhat yace ai halin da AKEEL yaganka a cikine ya sashi shima sai da aka kawo shi asibitin ya Suma! Zuciyar AQEEL sai ta shiga wasi wasi ai ba yau yafara Suma ba Akan lalurar sa ba, kuma AKEEL bai taɓa Suma ba shi sai yau? Me Hakan yake nufi? Kuma ya ga alamun kamar Abbu yanada damuwa a Ransa, zantukan da yake mamaitawa a zuciyarsa kenan, suna wannan halin Nurse ta shigo tace shima AKEEL ya farfaɗo Amma sai Kuka yakeyi, doctor zai Masa allurar barci ya hana, daga Ɗalhat har AQEEL wanda komai ƙarfin Hali yake tare suka Mike tsaye jin abunda nurse ta faɗa, dan haka tare suka bi bayanta zuwa wajen AKEEL, AQEEL yana mamakin kukan da akace AKEEL yanayi, shikam Abbu bai mamakin Hakan ba, ALLAH yasa wani abu AKEEL ɗin ya gani zai warware musu komai inji Abbu a Ransa.




Haka suka ƙarasa cikin ɗakin da AKEEL yake gurshe ƙen Kuka, baisan da AQEEL aka tawo ba ya zata Abbu ne kaɗai dan haka tun daga baƙin ƙofar da AKEEL ya hango Abbun ya Fara magana har sannan yana Kuka


"Abbu ɗan uwana bazai aikata abunda naganshi a ciki ba, AKEELA nagansu tare alamun yai MATA fyaɗe kace Abbu mafarki nake ba gaskia bane, ɗan uwana ba yau yake cikin wannan halin ba,wanine yakeson cutar damu,shiyasa yai Masa Hakan,sai yau za'ace yayi Zina,zinar ma da ƙanwar mu wayyo ALLAH na Abbu cikin kukan yake zancen!
Dayake cikin ƙaraji yake zancen, AQEEL da yake bayan Abbu saboda marar sa a Hankali yake tafiya,shi kuma Abbu yana zumuɗin ganin AKEEL da abinda zai faɗa,shiyasa bai wani kula da yadda AQEEL yake tafiya ba,balle ya riƙo shi,! Duk maganganun da AKEEL yake a kunnen AQEEL,zuciyarsa bugawa ta fara da sauri da sauri,jiri ne ya ɗebe shi, sai da ya dafe bango da ma ga jiki ba bu daɗi, ALLAH ne yabashi ikon ƙarasawa ciki,shi dai Abbu kallon AKEEL yake cikin tausayi,sai kuma AKEEL ɗin yaci gaba da magana ganin shigowar AQEEL ɗin " bro bakai ka aikatawa AKEELA wannan Aikin ba ko?kace sharri akai maka? Kan AQEEL ya kuma kullewa da wanga al amari! jijiyoyin jikinsa sun kuma tsinƙewa! jin abunda AKEEL yake faɗa
Shi dai AKEEL cikin futar hayyaci yake magana, saboda ya tsorata da ganin halin da AKEELA tace ciki, jini kamar an yanka ƙaramar dabba, ga kuma ɗan uwansa kusa da ita,abun ba bu kyan gani! Abbu Yaje kusa dashi yana lallashin sa Akan "ba ɗan uwanka bane ya aikata MATA kaji AKEEL ɗina ka Kwantar da hankalinka ganin kamar baya hayyacinsa ne yasa Abbu yaiwa Doctor alamar yai Masa allurar barcin aikuwa yana Masa kafin kace me barci ya ɗauke shi,
Doctor yacewa Abbu in Sha ALLAH zai farfaɗo cikin Hayyaci in Sha ALLAH.


AQEEL kamar mutum_mutumi jin waɗannan kalamai da Ɗan uwansa yake faɗa, cikin tsinkewar zuciya ya Fara magana "Abbu ku futar da ni daga wannan duhun,wanene yaiwa AKEELA fyaɗe? Ni ne kuma? Ganin ya fita hayyacinsa ne Abbu yajo wajensa, yana Babu komai AQEEL da komai Abbu gashi AKEEL yana gayamun,wasu maganganu anya AKEELA fyaɗe sannan kuma ance nine innalillahi wa Inna ilaihi rajiuuun! Wayyo Abbu bani bane,shiyasa AKEEL yashiga wannan Hali, kaima shiyasa naga ka dawo alhalin tafiya kayi, wallahi Sharri akamun cikin ku ka gwanin tausayi AQEEL yake zancen!kafin daga bisani ya sulale ya faɗi ƙasa a sume...................




Muje next page😭😭😭😭 hawaye ya cikan idanu ya hanayi ganin screen ɗin wayar balle naci gaba da typing




✍️oum ARQAM ce ontop 🥰
2/26/24, 10:16 PM - Rãbi'atou Aminou {Oum ARQAM}: *RASHIN IYAYE*
(Babbar musiba)




Daga *Al 'kalamin✍️ Rabiat Amin (oum Arqam)*


*08128131163*


✍️ Marubuciyar...
*Komai Nisan jifa* 📚
*Hakan ba kuskure bane*📚




*_____________*
MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION📚🖊️ *(M°W°A)*


'Kungiyar d'aya tamkar da dubu masu Nazari da Aiki da ilimi burin 'kungiyar a koda yaushe shine ta fad'akar ta Kuma wa'azantar ta Nishad'antar da masoyanta🤙
*_____________*






*PAGE FOURTY NINE 49*






Tun barin jimmai daga Asibitin dataje gida kasa Samar da abincin da tacewa Abbu zata ɗauko tayi! Sai saƙawa da kwancewa takeyi, da yadda zata ɓullowa wannan al amari da yake tunkaro ta itada Usman, dan indai asirin Usman ya tonu shine yaiwa Akeela fyaɗe itama ta shiga ciki.


Sai kaiwa da kawowa takeyi a flourn ta, daga ƙarshe ta Kira number Usman dan tagaya Masa abunda ke faruwa, idan da wani shiri da zasuyi to!


Lokacin Usman yana gidansu a kwance a ɗakin da ya kasance nasa tun kafin barinsa gidan,dan wan Babansu mai kuɗine sosai, Sana'ar daya saba yakeyi yanzu haka wato kallonsa na Vedios fin batsa, dan ya manta wata Akeela yanzu,ko tausayin halin daya barta Bai tuna ba, tsabar Rashin imani! Jimmai tana Kiransa sai sannan yadawo hayyacinsa saboda yatafi wata duniyar,kiran ne ya ɗan dawo dashi hankalinsa! Yana ɗagawa yaji muryar uwar tasa da alamun damuwa da Tashin Hankali! CIKIN muryar da ta daɗe ta tsumu a iskanci, dan kuwa Duk wanda yaji muryar yasan Babu nutsuwa sai wani shaƙewa take yana ajiyar zuciyar! Maama meke faruwa ne! Jimmai tanajin muryar sa tasan da abunda yake shukawa,Amma ko ta kula! Babu lafiya Asirinka yana daf da tonuwa!saboda Abbunsu yace zaiyi bincike Akan Hakan, wai kula likitoci sunce bashi bane yayi fyaɗen! Ko shine ma a matsayin sa na ƙaramin yaro Bazai iya fatattaka mace ba irin haka, dan kuwa akwai tausayi a Ransa da kuma Rashin sabo, ga wacce yaiwa yarinya ce ko kukan da takeyi kafin aikata fyaɗen zai sa yaji tsauyinta ya fasa aikata, Duk bayanin da Jimmai take wa Usman yanaji kuma sai Duk wannan yanayin daya shiga jin abunda uwarsa ta faɗa sai ya watstsake yaji tashin Hankali!
Nashiga uku maama yanzu mene mafita? Kar asirina ta tonu!Nima shine Tashin hankalina Usman, meyasa ka aikata wannan Aikin ma wai? Yanzu gashinan kadani a fargaba kaima kasa kanka! Nan dai suka dinga tattauna ta yanda zasu ɓullo wa lamarin Duk ta yadda zasu ɓullo sai suga ba mafita,a haka dai ta kashe wayar jiki ba bu ƙwari ta waɗa kitchen domin Samar da abunda zata koma Asibitin da shi, Zuciyarta sai tsalle take kamar zata fita daga ƙirjinta,kar ma Ɗalhat yai tunanin wani abu da Rashin dawowar tata, dan haka abu mai sauƙi ta dafa,ta kama hanya ta koma Asibitin.


_________ Ɓangaren Usman ɗin ma Hakane, dan kuwa kallon dayakeyi kashe shi yayi, komai na duniya tsaya Masa yayi,yanxu idan asirinsa ya tonu ina zaisa kansa? Dawane idanu zai ga Abbu? Abbu Babu abinda baya yi Masa tun daya dawo gidan kamar mahafinsa haka yake,Duk abunda yaiwa su AKEEL da AQEEL haka yake Masa, baya banbantawa,! Tunanin da yakeyi kenan, har Yanzu, daga ƙarshe yace koma dai menene ya kashe ishirwata ai, kuma ba kasheni za'ayi ba, ƙarƙari ya saki Maama,sai me matsalarta ce, a haka ya kau da Duk wani tashin hankali daga Ransa.




*******************




Can Asibiti kuwa ALLAH yaso AQEEL bai kai ƙasa ba Abbu ya taro shi, dan haka sai da aka saka Masa Robar ƙara numfashi kafin numfashin ya daidaita, aka haɗa Masa da allurar barci.


Idan Kuka dubi Ɗalhat saikun tausaya gareshi, ƴaƴa uku rigis Duk ba bu lafiya, ƙarshe ma aka ƙwallafa yaron sa cewa shine yaiwa ƙanwarsa fyaɗe,ai ba kowacce zuciya bace zata ɗauki wannan Abubuwan,shima adduar da yakeyi ne ta tausasa masa zuciyarsa,ai da shima halin da zai shiga sai ALLAH.


Jimmai ta ɗauke hankalin sa daga kan ƴan uwansa, ba sosai yake kula suba, macewa yakeyi da su ma, haka na Suma ta juyar musu da hankalin basa nemansa, shiyasa bai Kira kowa ba yagaya Masa wannan tashin hankalin ba, gwanda ma haka dan kuwa wannan ai tonon asirine, gwanda ma idan gaskiya ta bayyana sa sani koya Kuka ce fans?


Doctor Maryam yace a ƙyale Akeela ita kaɗai batason, hayaniya, saboda zuciya da ƙwaƙwalwar ta sun shiga wani yanayi, yanzu ma fatan farfaɗowar ta lafiya CIKIN Hankalinta shine fatan kowa, Amma Duk da haka Abbu yace yanason ganin Autarsa yaga halin da take ciki! Doctor Maryam batayi Musu ba tai Masa jagora har zuwa ɗakin da Akeela take!
Tana kwance Akan gadon kamar gawa, ga Robar ƙara numfashi, ga ƙarin Jini, anai MATA ta zubar da jini fa, abun gwanin tsautsayi kamar me Haihuwa ko ɓari!


A Wannan yanayin Abbu ya shigo ɗakin, ya tarar da ƴarsa kamar Gawa, Abbu baisan lokacin da Hawaye suka shiga zubo Masa a fuskar saba, doctor Maryam ,sai nuni take masa yayi haƙuri, saboda ba bu halin magana, shikam Abbu sai kallon Akeela yake kamar ba itaba, wannan itace AKEELA cikin lokacin ƙanƙani tai wani mugun rama, ga idanuwanta sun kumbura, abunka da Fara fuskarta tayi jajur hakama leben bakinta, kamar jini ya kwanta, dan ɗan iskan rufe MATA baki yayi da nasa, ganin taƙi daina Masa ihun neman taimako! Haka dai Abbu jiki Babu ƙwari ya fito daga ɗakin, zuciyar ciki da baƙin cikin halin da aka saka Masa ƴa,da Ɗaura ɗamarar fito na fito da Duk wanda yaiwa ahalinsa wannan mummunan Aikin,Babu tausayi Babu imani, yadda ya shayar dashi shida ƴaƴansa Ruwan guba, da azaba shima haka zai shayar dashi Ruman azaba na ɗaukar fansa, kowanene kuwa, yadda bai ji tausayin yarinya ƙarama ba ya keta MATA alfarma ba, sannan yaiwa ɗansa Sharri Akan shine ya aikata,shima bazai saurara Masa ba, shi ma AKEEL gashi yana cikin wani Hali daban, tsakaninsa da wannan mutumin shine ALLAH ya saka Masa yai gaggawar tona Masa Asiri, yana waɗannan tunanin yadawo ɗakin da aka tanadar Masa dan Zama, wani tunanin ya shiga, a haka Jimmai taxo ta sameshi,jikinta a sanyaye ko kulata bai ba,ko kula abincin bai ba ai cin Abinci na lafiya ne, cikin jimami kamar gaske Jimmai, ta tambayi Abbu shin wani ya farka a tsakaninsu? Anan yake ce Mara ea AKEEL da AQEEL sun farka, Amma AKEEL sai Kuka yakeyi,shi kuma AQEEL lafiya qlau ya farka,Amma kuma da akace AKEEL yana Kuka shine AQEEL ya biyoshi anan yaji zancen da AKEEL yake yanzu haka shima ya faɗi cikin wani yanayi sai da aka saka Masa Robar ƙara numfashi ma! Ƴar banza harda su nuna alamun tausayi, da Addu'ar ALLAH ya sauwaƙe, da cewa ALLAH ya tona asirin wanda ya aikata wannan aikin, Allahumma Ameen ko fans? zakuce nasan


Kada na jima ko? Me gadi na tambaya waya shigo da bananan shine yace bai sani ba wai, ya zaga bandaki lokacin gaskiya, shi dai Abbu bai magana ba.




Cikin ikon ALLAH AKEEL ya farka kuma cikin aminci Babu kukan ko ɗaya dan haka Abbu , Abbu cikin tausasawa ya Fara tambayar sa cikin lallashi, ya hakan ta faru meya gani da ya Suma, da kamar bazaiyi magana ba daga ƙarshe kuma ya warwarewa Abbu komai tun daga barowar da AQEEL yayi wajensa daga masallaci, har zuwa gida da yayi yana shiga ɗakinsu, yaga AKEELA da AQEEL a halin da ya gansu, sai a sannan kukan da take rikewa ya kufce Masa, Abbu ne ya Fara warwarewa AKEEL cewa ai ba AQEEL bane ya aikata wannan aikin, kamar yadda Doctor Najeeb yaiwa Abbu bayani haka taiwa AKEEL, kuma cikin ikon ALLAH ya fahimtu sosai,Duk da har sannan zuciyarsa Babu daɗi " Nima Abbu aban yabani mamaki sosai, brother bazai aikata wannan aiki ba,kuma AKEELA ma haba, to Abbu wane zai shigo gidanmu ya aikata wannan aikin ga AKEELA? Shin ina Maama? Abun yafaru Abbu? Dole ayi bincike sosai, cikin ƙaraji AKEEL ya ƙarasa zancen dan kuwa zuciyarsa tana ƙuna da halin da aka jefe ɗan uwansa da ƴar uwarsa? In sha ALLAH AKEEL zan yi wannan binciken!kaji ka Kwantar da hankalinka.


Yanzu ina shi brother ɗin? Nan Abbu ya faɗawa AKEEL yadda ya faru da AQEEL ɗin, dan haka AKEEL yakuma Kuka, "yace ALLAH ya saka Mana kowanene yai Mana wannan mummunan Aikin cikin Kuka ya ƙarasa maganar, ka Kwantar da hankalinka kaji yaron kirki, yanzu Abbu inason ganin halin da Brother yake da kula sister? Ka kwanta ka huta kaji yarona barci sukeyi kamar yadda ka farka cikin aminci in Sha ALLAH su ma haka zasu farka kaji da lallashi dai aka samu AKEEL ya haƙura da zuwa wajen ƴan uwan nasa.




A cikin Daren dai shima AQEEL ya farfaɗo sai dai jikin sai a Hankali, kuma da AKEEL da Abbu sukazo wajensa,sai aikin Kuka AQEEL yakeyi "Abbu saboda ALLAH ya jarrabeni da Yanayin halitta ta shine aka yimin Sharri, Akan nine naiwa ƙanwarsa fyaɗe!?shi wanene ma? Ya aikata wannan ga Auta(AKEELA) sai Kuka dai yakeyi daga baya ya Fara shaƙuwa sai Kuka idonsa ya Fara ƙaƙƙafewa! AKEEL da ke kusa dashi shima kukan yafara! doctor Najeeb yana gurin dan haka yai maza yai Masa allurar barci,da kuɗi da komai, anan Akayiwa AQEEL Duk wasu gwaje_gwaje anan kuma aka tabbatar da cewa zuciyarsa ta shiga firgici, lokaci Zuwa lokaci zai dinga shiga Irin wannan yanayi, na shaƙuwa da ƙafewar idanuwa,Amma da yayi barci ya farka shikenan, daga haka kuma zuciyarsa zata iya kamuwa da ciwo dan kuwa taji tashin hankalin da bata taɓa ɗauka ka, za'a samu sauye sauye daga gareshi, walwalar sa zata ragu sosai, da magana ma saboda zuciyarsa da ƙwaƙwalwar sa ta shiga ruɗani, ALLAH ne ya kiyaye bata bugaba tashi ɗaya,dan haka Yanzu sai a san abunyi,a kuji Ɓata Masa Rai.


ALLAH sarki Abbu tashin hankali wanda ba'a saka Masa Rana, kunji bala in da ya samu Abbu kuma, ga AKEELA bata farka ba, Jimmai wannan haƙƙi ki kaishi ina? Duk fa wannan budurin da AQEEL yayi bayan farkowarsa da farkowar AKEEL Duk tana wajen sai aikin Kuka take kamar gaskiya, Alamun tausayi.




Haka wannan Ahali dai suka kasance cikin tashin hankali, tsakanin Abbu da AKEEL wanda shi jikin Alhamdullillahi, yanzu AQEEL da AKEELA ne kawai saura, sai Jimmai mai tararrabin tonuwar asirinta dana ɗanta, shine kawai tashin hankalin ta.


Kafin safiya CIKIN ikon ALLAH shima AQEEL ya farka, wanda doctor Najeeb yacewa Abbu CIKIN lallashi zai Masa bayanin ai ba shine akace ya aikata ba,shi AKEEL kawai dai yayi tunanin hakan ne dan kuwa shi da ita ya samu a gidan daya dawo daga masallaci ɗaukar karatu, shiyasa Amma bashi suke nufi yayi fyaɗen ba, doctor Najeeb shi ma sai da yaiwa AQEEL bayani dallah dallah Babu ƁOYE ƁOYE, Duk wannan CIKIN salon kwarewar aikine dan AQEEL ɗin ya kwantar da Hankalin sa,Amma yanayin daya samesu a ciki Duk sai da ya gayawa AQEEL ɗin, da gwajin da akai masa Akan ba shine ya aikata ba, Yanzu kawai bincike zasu Fara Akan wanene ya aikata wannan aikin shine yanzu burin mahaifinsa, dan haka AQEEL an ɗan samu salama a yanayinsa, dan tunda akai masa bayanin komai, ya ɗan ji sanyi, ba sosai ba yanzu wane mara imanine ya aikatawa ƙanwarsa wannan mummunan Aikin,har CIKIN gidansu, wannan ne yake cin zuciyarsa,Amma ya na daurewa ko dan ɗan uwansa daya damu da damuwarsa da kuma mahaifinsu wanda a tsaye dare ɗaya ya rame.


Sai washe gari wajen asba ALLAH yabawa AKEELA ikon farkawa, Babu iface ifacen da takeyi,da fisge_fisge,kawai sai hawayen da takeyi ga idonta yana motsawa,tana buɗeshi kuma, dan Haka doctor Maryam ta na wajenta,tai ta mata magana Amma ina taƙi amsawa,Babu Alamun tana jinta ma, Nurse Biyu ta Kira suka taimaka mata aka ɗauki AKEELA aka kaita bayi, kafin sannan da ma an haɗa ruwa mai zafi da magunguna a ciki, wanda zai taimaka mata ɗin ƙin yai saurin warkewa,sai da tayi ƙara da aka motsata wajen ɗaukar ta, Zuwa bayi, abun tausayi wajen gashin da za'ai mata, sai Ihu takeyi, kuma har sannan da ɗan jini,dan Ruwan da aka saka ta ya ɗan canja, wajen ruwa huɗu Nurse ɗin sukai mata, sannan suka mata wanka,aka fito da ita, sun shiryata cikin uniform ɗin asibitin aka zaunar ta, Amma ina ta kasa sai jinginar da ita akayi a jikin fillo,sai sannan Doctor Maryam tacewa Nurse su faɗawa Doctor Najeeb cewa yarinyar ta farka,Amma yanzu ma sun gyara ta saboda hankalin iyayenta da ƴan uwanta ya kwanta.


Doctor Najeeb kam ya faɗawa Abbu cewa AKEELA ta farka, kuma Alhamdullillahi, to da ma ba barci sukayi ba, tun jiyan zuciyoyi ba bu daɗi, Aikuwa kafin kice me sun ɗunguma Zuwa ɗakin da AKEELA take ciki, harda AQEEL wanda Alhamdullillahi shima Amma shi yasan meyake ji,


Sun sameta yadda doctor Maryam ta gyara ta, Abun tausayi daga AQEEL har AKEEL rige rigen Zuwa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login