Showing 90001 words to 93000 words out of 141223 words
Chapter 31 - RASHIN IYAYE Complete Document by Rabi'atu Muhammad Rabi'u Oum ARQAM.txt
hakan ma sun godewa ALLAH, Sai kuma data ji muryar maza ko ganin su zata shiga yanayi na tsoro da firgici wanda zaisa ta fice hayyacinsa, Doctor Maryam tacewa Abbu ya Kwantar da hankalinsa wannan ya ɗan wani lokaci ne a Hankali komai zai Fara sauƙi, dan haka ma doctor tace wa Abbu ɗin da su Aqeel su dakata zuwa wajenta, ganinsu yana furgitata, Abbu bai ji daɗin Hakan ba,Amma ya ya iya, kullum ana gasa MATA jikinta da Ruwan zafi, ga magungunan da ale MATA amfani da su take Sha kuma har da Jimmai a jinyar, ALLAH ya taimaketa bata haɗu da yoyon fitsari ba, san kuwa tashin Hankalin da doctor Maryam take gudu kenan ko rudewar ƙwaƙwalwa , to yanzu dai rudewar ƙwaƙwalwa aka samu,Duk wata kulawa tana samunta, Abbu kuma yana gaf da fasa ƙwai da tozarta Jimmai,dan kuwa yanzu Hankalinta ya kwanta,jin Akeela ta farfaɗo da rudewar ƙwaƙwalwa,haka ma Usman doctor Maryam ta faɗa Masa cewa ai tai MATA allurar,sai murna yakeyi dan kuwa ya zata allaurar tai MATA daya sata,nan kuwa bai san ALLAH ne ya sa Akeela ɗin ta farka a Hakan ba.ya daɗawa doctor Maryam kuɗin da yai MATA alƙawari, hakama Jimmai ya ƙara MATA, dan haka doctor Maryam ta killace su ta ajiye, wannan ma hujja ce.
Har anfara koyawa Akeela tafiya, dan kuwa sai da aka koya MATA, dan ta illatu fa da Kuka da karkarwar jiki ta Fara taka ƙafafuwanta taku ɗaya biyu sai a kyaleta.
_________Usman Duniya saboda jin ta Kowacce hanya dai asirinsa ya tonu, har sannan babansa yana asibiti, kuma yana gidansu yai kallonsa na banza ya hau network ya gama malelekuwa ya haƙura,A wannan yanayin yake kansance idan kuma abun yafi karfinsa, ya fita ya samu wata Mara kamun kan ya rage zafi,sai kuma kusancin da shida Shukra ƙanwarsa sai ya ke ɗarsa wani abu a Ransa game da ita..............
Muje next page....
Turkashi fans Usman me yake nufi ne?
Asirin jimmai kam yafara tonuwa konace ya tonu kawai fallasa ce Abbu bai MATA ba
ALLAH sarki Akeela ke kam kinji jiki
✍️oum ARQAM ce ontop 🥰
3/1/24, 5:39 PM - Rãbi'atou Aminou {Oum ARQAM}: *RASHIN IYAYE*
(Babbar musiba)
Daga *Al 'kalamin✍️ Rabiat Amin (oum Arqam)*
*08128131163*
✍️ Marubuciyar...
*Komai Nisan jifa* 📚
*Hakan ba kuskure bane*📚
*_____________*
MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION📚🖊️ *(M°W°A)*
'Kungiyar d'aya tamkar da dubu masu Nazari da Aiki da ilimi burin 'kungiyar a koda yaushe shine ta fad'akar ta Kuma wa'azantar ta Nishad'antar da masoyanta🤙
*_____________*
*PAGE FIVETY ONE 51*
Alhamdullillahi zamuce dan jikin AKEELA sai ABunda ba'a rasaba, tun ta na ruɗewa idan taji muryar maza ko ta ga maza har abun ya Fara sauƙi, dan kullum sai doctor Maryam tai MATA nasiha Akan nuna MATA waɗannan fa ƴan uwanta ne, Wannan kuma mahaifinta ne, bawai manta su tai ba fa, wai dai tagaya MATA cewa abunda wancan marar imanin yai MATA su har abada bazasuyi MATA ba, Duk da har sannan bata buɗe baki ta ambaci sunan wanda yai MATA ba, Alhamdullillahi ba'a buƙatar wannan da ma dan kuwa ansan wanda yayi, fatan SAMUN lafiya kawai ake MATA, kuma tana Shan maganin da zai taimaka MATA a ɓangaren ƙwaƙwalwar shima ana samun ci gaba sosai,yanzu tana Zama waje ɗaya dasu AQEEL da AKEEL da kuma ABBU har a ɗan taɓa Hira da ita ma, kowanne yana burin faranta MATA, da mantar da ita abunda ya sameta, Amma Duk da haka akwai damuwa a tare da ita,magana da walwala tai MATA ƙaranci.
Amma fa tun daga sannan AQEEL walwalar sa ta ragu gaba ɗaya,yanzu magana wahala take Masa, Hakama ba ta Amsa,kamar yadda doctor Najeeb ya faɗa zai sameshi ɗin,Amma kuma yace in Sha ALLAH komai zai wuce, wannan ba wata matsala bace,sai kuma abu na gaba a guji Ɓata Masa Rai, Saboda Duk sanda zai shiga ɓacin rai ko makamancin haka zai samu shaƙuwa da Ajiyar zuciya idanunsa zaiyi ja, da anbashi ruwa ya Sha, ya samu barci shikenan,zai farka normal, idan kuma aka ci gaba da tafiya a Hakan ana ɓata Masa Rai,ko ya shiga tashin hankali zuciyarsa zata samu matsala.
AKEEL ne dai normal tun suman da yayi,bashida wata damuwa,Amma kuma ganin ƴan uwansa Basu da walwala shima sai ya rage tasa.
ALLAH sarki ABBU shi kam ALLAH ya taimaka Masa,bayan hawan da jininsa yayi, tun lokacin da abun ya faru ABBU ya daina barci sai ɓarawo ya zauna yaita tunani kenan, Hakan ne yasa akai masa BP akaga jinin ya hau,aka bashi magunguna, doctors suna Bashi shawarwari to dan haka da sauƙi jikin, musamman yanzu da yaga jikin AKEELA yai sauƙi sosai,ta Fara mai da jikinta. Shi ma AQEEL Alhamdullillahi tun da ciwon ya sameshi har yanzu bai kuma ta shi ba.
Jimami dai anyi damfanfan ya mai naƙuda ta samu katifa, dai fantama warta takeyi a Asibitin ganin, asirinta ya rufu da ɗanta, har sannan ABBU bai fallasa cewa yasan Usman bane ya illata Masa Rayuwar ƴar sa guda daya tilo mace, Hakanan ya tsarwatsa farin cikin Ɗan sa namiji ya goga Masa baƙin fenti,ba don ALLAH ya taƙaita wahala ba ai da yanzu wane zancen ake? Tsaf zai iya tsine Masa ya fitar dashi da ga sahun ƴaƴansa, fyade ai ko ƴar wani yaiwa baze ƙyale shi ba balle kuma ƴar cikinsa shi ma ɗan cikinsa.
Ganin jikin AKEELA ya murmure ana Shirin Basu sallama, Hakama Jinin ABBU ya yi normal, tun da da ma shi mai miƙawa ALLAH zaɓi da addu'oi,hakane ya sa yasa bayan hawan Jinin bashi da komai, Amma in da wani ne ai maybe zuciyarsa ta buga, ko ya faɗi ɓarin jikinsa ya shanye, doctor Najeeb har office ya Kira ABBU shida doctor Maryam, suka nuna Masa kuɗin da Usman ya bada Akan a yiwa AKEELA allurar manta komai, da record ɗin tabbacin shine yaiwa AKEELA fyaɗe kuma da sanin mahaifiyarsa, itama Harda Bawa doctor Maryam kuɗi itama, har suka gama yiwa Abbu bayani bai ce komai ba, dan haka kawai ya miƙa wayarsa an tura Masa record ɗin komai, ya ƙarbi kuɗin, yaiwa Doctor Najeeb da doctor Maryam godiya Akan namijin ƙoƙarin da sukayi,yanzu badon akwai Amana ba Irin Wannan kuɗin da suka bayar, mai zai hana Doctor Maryam bataiwa Akeela Allurar ba,ku ma su rufe gaskiyar badon tun farko sun duba sun gani bashine ya aikata fyaden ba ma.
Zuciyar ABBU ta tunzura kamar zata Faso ƙirjinsa ta fito sai addu'a yakeyi shine kuma sai zuciyarsa tai Sanyi take ƙasa,a Hakan ya fito daga office zuwa ɗakin da suke zaman jinyar, ai kuwa Jimmai na zaune, kamar mutuniyar kirki, ABBU yana ganinta sai yaji kamar Yaje ya shaƙeta,tun tana shure_shure har tadaina, Amma ya mallaki kansa!
Abbun su Nikam ya maganar binciken wanda ya cuce mune? Jimmai har da sassauta murya wajen maganar!
Ai wanda ya aikata zaluncin nasanshi!nasan ko wanene!ba tun yau ba! Cikin Zafin zuciya ABBU ya idasa zancen!
"Alhamdullillahi naiwa ALLAH godiya Amma ta yaya? Cewar Jimmai har da ɗaga Hannu da safawa a fuska zuwa ƙurji, irin yiwa ALLAH godiya ɗin nan!
Kinga kuɗin da har ila yau, yazo Asibiti ya bawa Doctor Maryam mai kula da AKEELA akan tai MATA allurar da zata Mance komai,SABODA zalunci har da mahaifiyarsa a bada gudunmawa, da yake ita doctor ɗin tana da zuciyar imani zuciyar tausayi ta karɓi kuɗin, alamun zatayi aikin da suka sata, hakana ALLAH mai iko sai ya Tashi yarinyar a halin da suke fata,wanda sunyi tunanin yadda zuciyarsu Babu imani, da tausayi, sheɗan ya rinjayi zuciyarsu ita haka ta ta take, aikuwa ina tata tsarkakakkiyar zuciya ce! ABBU ya ƙarasa zancen da watsawa Jimmai kuɗin a fuskar ta,
Ita dai jimmai ba bu bakin magana! Tai suman wucin ga di!
ABBU ya ci gaba da magana " Wannan Ɗa da uwa sunyi asara, ALLAH zai nuna Musu zaluncin su! ABBU ya ƙarasa zancen da kallon fuskar jimmai wanda gumi ya jiƙeta, A aljihu ABBU yasa Hannu ya ɗauko wayarsa ya kunna Duk record ɗin daga na Usman har nata ita Jimmai ɗin, yadda sukayi da doctor Maryam, ai kafin Usman ya gama magana, na Jimmai ya shiga!
ABBU sai ihun Jimmai ya ji! Zata Fara Masa magiya!
Cikin tsawa ABBU ya ɗaga murya " Baki da bakin magana anan, Duk abunda Zaki faɗa bani da lokacin saurarar su!ki sani Duk wani zalunci da makirci da Kika ƙulla tsakani da ƴaƴana yanzu ALLAH yabani ikon sani kuma nabarki da ALLAH hakama Suma sun barki da ALLAH,Duk da ni ma inada laifi in sunzo sun gaya mun abunda kike musu nake kwaɓarsu na nuna Musu cewa, ai ke mahaifiyarsu, da kuma la'akari da yadda Inna Rabia tai dawainiya da ni ba bu cuta ba bu cutarwa, ko ƴaƴan data hai fa acikinta bazasu nunan ga ta ba, ashe abun ba haka yake ba, ita Inna Rabia samunta sai an tona, Duk abunda Kikai kanki kikayiwa ga amanar zumunci da Kika ci ita kaɗai masiface a gareki! Sai Yanzu ABBU yai Ajiyar zuciya! Wanda ɗakin yayi tsit kukan da Jimmai take ma ta daina ta yi shiru ta na saurarar maganganun da ABBU yakeyi!
Zuciyarta cike da mamaki da Al ajabi!
ABBU yaci gaba da magana "Malam Sallau da Yake shima zuciyar imani gareshi, da na je na tambayeshi bai ɓoyen komai ba ya feɗemin biri har wutsiya,nayiwa ALLAH godiya daya sa daga ke sai ɗanki ne masu zuciyar fir'auna, dan haka Yanzu ba bu abunda zan miki kije ke da ALLAH zakiga sakamako tun a duniya, kinci darajar Ummul khair dan kuwa munyi zaman amana da soyayya ni da ita, wanda ke Baki duba Hakan ba waɗannan ƴaƴan ko baki Aure ni ba ai ƴaƴanki ne Zaki iya kula dasu, Amma ina kamar ɗanki shi Zaki haɗa baki da shi ya cuci ƴar ƙanwarki wanda shima ƙanwar sa ce! Zakiga sakayyah in Sha ALLAH badai kin yarje masa yaci mutuncin zumunci ba,ya cuci marainiyar ALLAH ba, zakuga sakayyah, nayi alwashin Duk wanda na samu da aikatawa yarinyarta wannan mummunan aikin, da yiwa yarona mummunan sharrin nan sai munyi shari'ah dashi, to Amma ina ALLAH ya rufa Asiri, mutuncin ƴata wajen shari'ah bazai zube ba, bayan ke sai ni sai doctors ɗin da suka san meke faruwa, da Baba Sallau, bana fatan maganar zata futa, yanzu ma haka zan bunne ta sakayyah ce Zaki gani da Sannu! ABBU ya ƙarasa maganar da rawar murya da ajiyar zuciya alamu sun nu na zancen da yake faɗa yana taɓa Masa zuciya dauriya yakeyi kawai!
Jin ABBU yayi shiru sai yasa Jimmai cikin shashsheƙar kuka zata Fara magana "Dan ALLAH ka........... Ɗaga mata hannu ABBU yayi🖐️ wanda gama rubutunsa kenan, a wata farar ɗaukarda! Hullawa jimmai ya yi a fuska! Ga takarda nan hukuncin da zan iya yi miki kenan, dan haka banson ki ƙara ko minti 1a ɗakin nan,idan ba haka na komai na iya faruwa!
Jimmai tasan halin ABBU akwai zuciya!kamar yadda yace komai na iya faruwa hakanne, dan haka tana buɗe takardar daya bata tai tozalai da saki Biyu a jiki, da ɗan short rubutu.. kar ki barmun ko tsinke acikin gidana wanda kikasan mallakiinkine, azzalamu macuciya mai zuciyar fir'auna. Kuka jimmai ta fashe da shi ba bu tsammani ABBU yaga jimmai a gabansa ta dafa ƙafafunsa, tana Kuka "dan ALLAH ka yafemun Ɗalhat ni mai laifi ce a gare..... Wani kukan kura da ABBU yayi ya watsawa Jimmai Mari ai sai da jinta da ganinta na wucin ga di ya ɗauke, kafin ta dawo hayyacinta kuma sai ƙwallo da ita ya harba ta Jikin bangon ɗakin, Hakan ne ya dawo da Jimmai hayyacinta ba bu shiri ta buɗe ƙofar ta fice ta na mai Kuka..kona mene oho? Baki ya fashe hakana ta na ɗingisa ƙafa!
Sai sannan ABBU ya fashe da wani kuka abun gwanin tausayi, babban mutum kamar wannan, shigowar doctor Najeeb asibitin kenan, ya ga Jimmai ta fice ta na Kuka, ga fuska da jini ba ki ma haka, ko kallon ta bai ba yasan sauran may be Alhaji ne yai MATA Hakan,yasan jinin Alhaji ya hau kwanaki wannan ku ma abun zai iya sa jinin ya kuma Hawa, dan haka ɗakin da yasan Abbu yana ciki shi ya shiga,aikuwa ya sameshi ya na Kuka, dan haka yai tai Masa nasiha daga ƙarshe kuma tai MATA allurar barci dan ya samu relief.
AKEEL da AQEEL ku ma suna Gida lokacin da abun ya faru, dan haka Basu sani ba,suna Shirin fitowa daga gidan ne Jimmai ta shigo gidan, tana Kuka AQEEL da AKEEL ko kallonta basuyi ba, raɓeta sukayi zasu wuce dan haka, kawai sai ta zube gwiwa ta na Kuka " ƴaƴannan ku yafe mun dan ALLAH ko roƙar mun mahaifinku, nan kuma kamar zararriya ta Fara basu labarin yadda sukayi da Abbu harda buɗe takardar sakin da nuna musu,sai sannan AKEEL yayi magana "kamar yadda Abbun mu ya faɗa miki muma haka zamu ce miki, ALLAH ya saka Mana, in Sha ALLAH zai Kinga sakayyah ke da Usman kamar yadda Kuka tarwatsa Mana farinciki, ku ka cutar Mana AKEELA, ga ɗan uwana ma kin sashi a wani yanayi, sai sannan yakai duba ga AQEEL wanda yafara shaƙuwa da ƙafewar idanuwa, da sauri AKEEL ya ja hannunsa ya bar Jimmai a tsaye ta na kuka cikin ikon ALLAH yakaishi cikin mota, a machine sukazo o Yanzu kuma ai bazai yiwu su koma a machine ba, sa'i da lokaci malam sallau ya iya driving ABBU yana aikensa da ita ɗauko wani abu da makamancinsu.
Da Jimmai ta shigo sai da taiwa Baba Sallau magana wanda da batai Masa, shi kam ko kulata bai ba, dan kuwa da ma bata kulashi shima kam bai kulata ba, daga ƙarshe dai yace ALLAH ya shiryaki ya sakawa marayun ALLAH!
Ganin halin da AKEEL yasa AQEEL a mota ne yasashi dawowa wajen inda har AKEEL ya ɗauko trolley ɗin da sukazo ɗauka da kuma mukullin mota da yasa AQEEL ɗin aciki!
Itama jimmai ta ɗan kwaso kayan sawarta a trolly sannan ta wanke fuskarta ba bu jini, amma fuskar ta kumbura, hakama ƙafar ta kuma tsami daƙar take takawa, dan haka AKEEL da wata rana shi ma yanada zuciya, da sauri ya fusgo jimmai zuwa bakin gate ya wurgata, sannan ya miƙawa Baba Sallau mukullin mota alamu sun nuna ya jaso kenan, ABBU bai Basu damar driving ba a shekarunsu, shiyasa yasai musu machine, AKEEL ne ya buɗe gate baba Sallau kuma ya fitar da mota, sannan AKEEL yasa mukulli ya ƙulle gidan yazo ya shigo motar, Baba Sallau ya ja su zuwa asibitin, ko da suka fito har sannan Jimmai batayi nisa daga layin nasu ba dan kuwa akwai zurfi da ma sai mota ko mashine ne zai fitarka,abunka da unguwar masu Hannu da shuni.
Lalläi ne Jimmai ta girbi abunda ta shuka ko nace bata girba bama, dan kuwa waɗanda taiwa Abun sunce sun barta da ALLAH,kunsan kuwa shi ALLAH yana kishin byinsa, hakana yana gaggawar amsa adduar wanda aka zalunta kuma aka kawo Masa ƙara akan ya saka ko yayi hukunci akai, sai mu jira muga ikon ALLAH akan jimmai da Usman.
Yau dai Jimmai mai mulki mai izza mai zalunci yau itace ta fito a ƙafa ta na tafiya, hakana ABBU wanda da can baya taiwa asiri baya GANIN laifinta akan komai, yai shine yai MATA Hakan, Duk da ma dai yai MATA da sauƙi ko ba haka ba fans?
"Ƙwarai kuwa muguwa! azzaluma! baƙar ashana ƙona gari!
____________ daƙar daƙar jimmai takai ga bakin titi ta samu mota har unguwarsu, ko da tace Gida mahaifiyarta(mahaifinsu ya rasu shekarun baya) ta ga halin da take ciki ta tambayeta Amma ina ba bu amsa sai kuka, daga ƙarshe kuma ta gaya mata cewa wai Ɗalhat ya saketa saki Biyu! Uwar tace akan me Amma ina ba bu amsa, haka uwar ta rabu da ita, lokacin fuska ta haye sai sa tai MATA Ruwan zafi dan kuwa ta maru,marin da ABBU yai MATA, ƙafa kam ta kumbura itama,haka tai mata Ruwan Zafin itama, shu'uma sai ta ɓingire da barcin wahala na dukan da ABBU yai MATA da na tafiyar ƙasa kuma ba'a saba ba.........
______________ malam sallau yai parking acikin Asibitin,dan haka AQEEL bai farka da ga barcin da ya ɗauke shiba, ALLAH yaso acikin motar akwai ruwa dan haka AKEEL yana shiga ya ɓalle murfin ya bawa AQEEL bai yi gaddama ba kuma ya Sha, lokacin shaƙuwa tai yawa haɗe da Ajiyar zuciya hakana idanunsa sunyi jajir abun tausayi, dan haka yana Shan Ruwan barci ya kamashi, gashi har sun zo bai farka ba,dan haka Malam sallau ya fita hakama AKEEL,saidai Acn motar da aka kunna,aka barshi aciki yasamu relief.
"ABBU bashi da ƙarfin jini dan haka lokacin har ya farka,Ruwan da aka sakawa ABBU ya ƙare dan haka doctor Najeeb yazo cire Masa yagama zai fita suka haɗu da AKEEL mai shigowa, AKEEL da Baba Sallau suka shiga ɗakin,malam sallau yaiwa ABBU ya jiki da Addu'ar samun lafiya, hakana yai Masa nasiha a matsayin sa na Babba gareshi bawai wanda yake ƙasan sa ba, dan haka Abbu yaji nasiha yaiwa Baba Sallau godiya a haka Baba Sallau da ma mukullin gidan yana wajensa dan haka yakoma gida a napep.
Hakanan ABBU ya gayawa AKEEL yadda sukayi da Jimmai, AKEEL shima ya kwashe yadda sukayi da Jimmai a gida ya faɗa Masa.
Sa'i da lokaci AKEEL sai ya fita gano AQEEL ya farka,aikuwa komawarsa ta ƙarshe ya sameshi ya farka Amma bai tashiba, dan haka yana buɗe motar, ya gane idonsa biyu, sai da ya ɗau lokaci a Hakan kafin ya yunƙuro ya tashi daga kishingiɗen da yake, AKEEL ƙarasa bashi Ruwan dayasha yayi aikuwa bai musa ba ya karɓa, yai Ajiyar zuciya sannan ya riƙo hannunsa suka fito daga motar, zuwa wajen ABBU, nan dai ABBU yaiwa AQEEL nasiha Akan ya kwantar da hankalin sa yanzu kam ya rabu da Jimmai, Duk yadda sukayi ya kwashe ya faɗa Masa, shi dai AQEEL ba magana alamu sun nuna ya ji.
Ranar dai ABBU da AKEEL da AQEEL sukuku suka wuni suka wayi gari, sai a Hankali,Sai da sukaje ɗakin da AKEELA take, shi ABBU ya Mance ma AKEELA batasan komai ba! Dan haka ya shafa kanta yace. "Auta ta kiyi haƙuri komai yanzu ya wuce, jimmai da Usman ALLAH zai