Showing 6001 words to 9000 words out of 141223 words
Chapter 3 - RASHIN IYAYE Complete Document by Rabi'atu Muhammad Rabi'u Oum ARQAM.txt
ta fita zuwa Kiran likita, Yan uwa da suke waje ganin ta fito a gigice rudewa sukayi,a rude suka biyo bayan likitan dayake qoqarin shiga wajen Alhaji Ammar d'in, Koda likita,yashigo Yana dubashi yace saidai haquri, Alhaji lokaci yayi ya amsa Kiran mahaliccinsa, innalillahi wa Inna ilaihi rajiun......
Ummu Ruman tanajin abunda likita yafada,ta yanke jiki ta fad'i Babu numfashi, sauran Yan uwa kuwa da Hajiya sakinah dayake tana gurin tazo, sai koke_koke sukeyi......
Taimakon gaggawa likitoci ska farawa ummu Ruman, bayan an lullube gawar Alhaji Ammar (...Allah yajikan mazan jiya,Allah yasa yadda yan uwanka da abokanka suke kulaka da y"ay"anka ya Dore har bayan ranka, ba ganin Ido za'a yiba..)
A motar asibiti aka saka gawar Alhaji Ammar zuwa gida Domin a kaishi makwancinsa, ita Kuma Ummu Ruman aka barta a asibitin Domin har sannan farfad'oba.....
********* ********
A can gida kuwa yau dama Sa'adatu batazo asibitin ba, saboda jiya tazo, ga ciki ya tsufa, daqar take Zama daqar take tashi,,,
Yara sundawo daga makaranta,kowanne jikinsa a sanyaye, musamman Hadiyyah, wacce take da surutu, Da neman fad'a wajen Yar uwata Hidayah, Amma ranar shiru,fad'an da suke da Hidayah na saka Kaya,inta dauka tace natane,duk da irin kayan daya, ba'a banbancewa, Amma saboda rigimarta,,,
Wayar Sa'adatu ce tayi qara, tana kusa da Alhaji, miqa Maya yayi, tana dubawa number ce Babu suna, Saida gabanta yafad'i, batasan kome yasaka hakan ba,tana d'agawa taji ance "Assalamu alaikum Sa'adatu, Isma'il ne(... 'Dan Autan su Alhaji Ammar ne,idan Baku manta ba...) Muryarsa Babu dad'i yake maganar, Sa'adatu tace Isma'il ya akayi? gabanta na fad'uwa tayi maganar, Isma'il yace Babu komai keda yara ku tawo gidan Hajiya, abunda yafada kenan ya kashe wayar....
Sa'adatu kallon wayar tayi gabanta Yana fad'uwa,jikinta yabata Babu lafiya, kodai wani abune ya samu Abby? (...Saikinje gidan kyagani Sa'adatu kyayi tambaya acan koba hakaba fans...)
Jikinta Yana rawa tacewa yara kuzo muje gidan Hajiya kawunku yakira waya Wai muje can, Allah sarki yaran sai suka Fara kuka kodai Abby rasuwa yayi?suka Fara tambayar kansu,sunsan dai haka kurin baza'ace suje gidan Kaaka su duka ba, Hakan suka fita, suna kuka,Adaidaita sahu, suka samu, wasu sukayi goyo wasu suka hau sama, Alhaji Kuma ya zauna a gefe, (.. mota ta alhaji ce, Kuma tana ajiye bashida lafiya an rufeta da tampol dama, Babu Mai hawanta...)
Kafin su qarasa har an d'auko gawar Alhaji Ammar, kofar gidan Hajiya sakinah cike take da mutane, suna qarasawa y"ay"an suka Fara kuka, Babu Wanda bai tausaya musu ba,maraici akwai ciwo..........
Ita kuwa Sa'adatu Allah ne yakaita cikin gidan lafiya Bata fad'i ba a qofar gidan, kuka take tayi kafin ta ta yanke jiki ta fad'i, Allah yakawo Wata makotansu Hajiya zasu shigo jana'iza, suka tallafeta,akayi d'aki da ita(... Inda ta fad'i akwai matsala fans faduwar Mai ciki, ga Kuma fargaba...)
Gidan haka ya gauraye da koke_koke saboda shigowar iyalan mamacin, da kukan da sukeyi, akwai tausayi,
********* ********
Acan kuwa Asibiti daqar ummu Ruman ta farfad'o, da kuka ta farka, yanata sambatu, da kukan Rashin mijinta uban y"ay"anta, Kuma jigon rayuwarta, kwanciya suka Bata, saboda tasamu wutu zuciyarta akwai fargaba a tare da ita,magiya ta dinga yimusu, su qaleta take wajen mijinta, suyi sallamat kafin akaishi kushewarsa,dayake Mahaifiyarta ce da kanwarta ,Wanda suke uba d'aya, dama sune tare da ita, ganin halin datake, ciki baza abarta ita d'aya aciki Asibiti ba,Babu musu suka yarda suka tafi, zuwa gida,(...kiyi haquri ummu Ruman sai haquri mutuwa akwaita da d'aci...)...........😭😭😭😭😭😭
Domin sharhi ko shawara sai a tuntubeni a wannan number *08128131163*
Saina jiku Yan amana
Muje next page fans
Abun akwai tausayi wlh , Kamar nayi kuka
✍️ Rabiat Aminu ( Oum Arqam 👩🍼)
2/7/24, 4:27 PM - Rãbi'atou Aminou {Oum ARQAM}: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/Cy82IooiC1LE5S0e2tkKcj
RASHIN IYAYE (babbar musiba)
*Labarine na tsantsar maraicin iyaye guda biyu akwai tausayi cin amana ha'inci dadai sauransu*
Na bude group dinnnan saboda comments ko sharhi na littafin RASHIN IYAYE (babbar musiba) please kubani hadin kai a kowanne lokacin danayi sabon post
*RASHIN IYAYE*
(Babbar musiba)
*✍️Daga Al'kalamin ©️Rabiat Amin*
(oum Arqam👩🍼)
*08128131163*
Marubiciyar
Komai nisan jifa📚
Hakan ba kuskure bane 📚
And now
RASHIN IYAYE (babbar musiba🙆♀️)
Labarine na tsantsar maraicin iyaye guda biyu akwai tausayi cin amana ha'inci dadai sauransu duk anan gaba zakuji.......
*__________________*
🌏 MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION📚🖊️(M°W°A)
*Kungiya d'aya tamkar da dubu masu Nazari da Aiki da ilimi Burin'kungiyar a ko da yaushe shine ta fada'akar da wa'azantar ta Kuma Nishad'antar da masoyanta.🤙*
*__________________*
*PAGE NINE 9*
"Lokacin da Ummu Ruman suka dawo gida, har an kammala had'a gawar Alhaji Ammar, Y'AY'ANSA da 'yan uwansa sai kuka suke abun tausayi, musamman da Ummu Ruman tashigo tana kuka, ga ranar datayi na lokaci d'aya.....
Itakam Sa'adatu da aka shigar da ita d'aki, suma tayi aka dinga Zuma Mata ruwa, daqar ta ta farfad'o, tana kuka maicin Rai, Matar kawu Isma'il Hauwa ce akanta take lallashinta(... Irin Facalar da ake qawance sosaine, sunsan sirrin juna, tare suke komai, itakam dama Ummu Ruman tana gefe Babu abunda ya dameta dasu...) Tana farfad'owa tafara kuka, sai haquri ake Bata, ana cewa tayi haquri saboda cikin dake jikinta sai haquri.......
Haka akakai Alhaji Ammar gidansa na gaskia, "Yan uwa da y'ay'a da Mata suka dinga kar'bar gaisuwa, abun tausayi, idan kaga Y'AY'AN kasan sunji mutuwar jajirtaccen uba a garesu, Wanda Basu rasa komai na rayuwa a wajensa ba.......
Zakiyyah ma kamar ta susuce saboda rashin mahaifi, kullum cikin kuka take(... Sai haquri kinji, Allah yasa mutuwar tasa ki nutsu kidaina ga'bunta,da rashin sanin ciwon Kai...)
Sai da Alhaji Ammar ya cika sati da rasuwa a gidan Hajiya sakinah duk akayi xaman ta'aziyyah, sannan iyalansa suka koma asalin gidansu......
Wanda komawar yaxamar musu wani tashin hankali, gashi suke kamar Abby zai dawo ne, Amma Ina yariga yatafi tafiyar da Babu dawowa,sai dai addua kawai zasu bishi da ita,daga iyayan har Y'AY'AN in suka zauna sai kuka sukeyi kawai, Babu Mai rarrashin wani, abokan Abby dasu kawu Isma'il sune suke ajiye musu kayan abinci, da kud'in cefane,Basu rasa komai ba, sai rashin mahaifi.......
Sun koma makaranta yara, duk jikinsu yayi Sanyi, maraichi ba Wasa ba, Allah sarki
Duk wannan neman fad'an da Hadiyyah takeyi a wajen Hidayah duk tadaina, ta Zama shiru_shiru, yanzu Babu surutu, Daman abunda ya banbantasu kenan, yanzu to sun xama iri daya, sai ankira sunansu wacce ta amsa sannan ake ganesu.....
Haka masu takaba suke takabarsu, tsakanin Sa'adatu da Ummu Ruman, duk sun rame sun fita kamanninsu, musamman Ummu Ruman tun bayan rasuwar Abby taketa Rama yau da lafiya gobe Babu lafiya, kullum cikin tunani, a hakan har hawan jini ya kamata Mai tsanani....
Ita Kuma Sa'adatu kwanan Alhaji Ammar talatin da rasuwa, Allah ya sauketa lafiya, ta haifi yarta mace taci suna *Hafsat*
Ranar da Sa'adatu ta haihu Rasuwar Abby ta zamo musu sabuwa, sunga daban da Abby yananan da tuni anfara dinke_dinke na suna, ga hidimar da zai Fara tun ranar Haihuwar har zuwa suna, hakan ma dai Babu laifi, (...Alhaji Ammar dama dayaga matansa cikinsu yakai wata bakwai,yake Ware kud'in da xai musu hidimar haihuwa dashi na kayan jarirai Dana Mai jego, yabawa Sa'adatu ta Fara siyayyah, kunsan dama itace Mai wannan hidimar daga nata har na Ummu Ruman itace Mai siyowa...) Ragon suna Kuma aka d'auka acikin kud'in Alhaji Ammar aka siya, hakan akayi wannan sunan, babu wani armashi.....
Zancen Rabon gado dama Bari akayi aga abunda abunda Sa'adatu zata Haifa, sannan ayi......
Alhaji Ammar yana Gina wani gida a gaba da gidansa kad'an irin ginin dayake ciki Amma be kammala ba, ga sauran kadarorinsa, da kudadensa, ga motarsa......
Ita dama Sa'adatu ta kammala takabarta, tunda ta haihu, saura Ummu Ruman kad'ai...
Haka sukaci gaba da zamansu, acikin gidansu, yau da dad'i gobe Babu dad'i, Ummu Ruman dai sai a hankali, ga Hunaif yaro Mai rigima yaita kuka kenan, baya yarda da kowa, bayan rasuwar Abby rigimar tasa ta qaru....
Zahra ta kammala secondary School d'inta, burin dama Alhaji Ammar Y'AY'ANSA suyi karatun boko, duk da Bai samu damar haka daga Zakiyyah ba akai Mata auren wuri. Anyi Mata registration na University,bayan tayi jamb dinta, ta samu gurbi a school of hygiene burinta kenan,tazama, jami'ar kiwon lafiya,gashi tasamu, duk da Tasha kuka, burin Abby kenan Allah yakaimu lokacin Inga zahrata ana zuwa jami'a , Ashe Allah bazaiyiba(.... Rayuwa kenan...)
Suma su Hadiyyah, Hidayah,Alhaji sun shiga babbar secondry, Farouk Khadija,sun shiga qaramar secondary, Haydar da zeenah Kuma suna primary, Allah sarki yara sun Fara sabawa da rashin Abby tare dasu, shine kullum take kaisu makaranta, Amma yanzu ina, saidai suje su hau Adaidaita sahu, Rayuwar kenan........
Hunaif da Hafsat haka suka bud'i Ido Babu kulawar Abby a garesu, sun cika marayu sosai, gwanda ma Hunaif Abby yasanshi, ita Hafsat ma da cikinta ya rasu fa, Allah sarki Rayuwa......
An kammala musu rabon gadu lafiya, Kowane ambashi Hakkinsa, na Sa'adatu tanada, Alhaji,Farouk Haydar da Kuma Hafsat, kaso uku da rabi kenan sai tumunin takabarta Kuma, ita Kuma Ummu Ruman tanada, Zakiyyah,Zahra, Hadiyyah, Hidayah, khadija,zeenah da Kuma Hunaif tanada Kaso hudu kenan sai Kuma tumunin takabarta...
Kungadai duk hassadar da Sa'adatu ta dinga yiwa Ummu Ruman lokacin batada d'a namiji, duk Dan gado ne tana ganin ai ita maxa ne da ita , ita Kuma Ummu Ruman Mata, Allah kenan gadai matan Nan da kuma Allah yakawomata Hunaif yasa tafi Sa'adatu d'in dai samun gadon, burin Sa'adatu kenan a kullum gado, ita kuwa Ummu Ruman baya gabanta, Allah sarki..........
Gidan da suke cikinsa a rabon Y'AY'AN Sa'adatu yazo, Shi Kuma Wanda Alhaji Ammar yafara ginawa yazo ana Ummu Ruman, Dan hakan an Ware kud'i za'a karasa gina mata, saita koma itada yaranta, ta barwa Sa'adatu nata....
Rayuwa kenan mutuwa Babu abunda Bata sawa,gashi yau Y'AY'AN Alhaji Ammar da matansa zasu rabu kowa yakoma gidansa.....
Tun bayan Rabon gadon da akayiwa iyalan Alhaji Ammar saine Kuma? Sai Kuma duk wad'anda suke taimakawa iyalan NASA suka jabaya da taimakon(... Lallai fans kujifa, da dukiyarsu kenan za'a dinga ciyar dasu,kud'in makaranta,suttura, rashin lafiya da sauran abubuwan buqata,lallai fans akwai matsala kenan, Allah sarki Alhaji...)
Kud'ad'en Alhaji Ammar Wanda take juyawa, su kawu Isma'il ya kar'ba, zaici gaba da juya musu, ribar ana musu amfani da ita, Shi Kuma har sannan dai Yana ajiye musu abinci, kud'in cefane Kuma cikin ribar kud'in dayake juya musu(... Lallai fans iyalan Alhaji Ammar suna cikin halin maraici fa, Babu idonsa komai yafara sauya musu...)
Rayuwa fa tafara sauyawa iyalan Alhaji Ammar, ba yadda suke rayuwarsu kamar da ba, akwai qalubale akansu sosai,.....
Kawu Isma'il shine yafanshi motar Alhaji Ammar yabada kud'in ta, dayake shima ba'a nesa yakeba, unguwar d'aya Amma da 'Dan tazara,duk kwana biyu Yana zuwa duba Y'AY'AN yayansa.......
tun bayan da Sa'adatu ta haifi Hafsat, sai kuma kullum Isma'il yake zuwa gidan, Wai Ashe son Sa'adatu yake Wai zai Aureta, (... Kujifa fans d'an Autan su mijinta, mijin nata yafishi komai...) Farko 'boye_boye Sa'adatu ta Fara batasan Ummu Ruman tasani, itada ba yarinya ai tasan komai, a hakan har magana ta fasu, cewa Isma'il zai auri , Matar Wansa........
Masifa da bala'i kenan, cin amana Sa'adatu tayiwa Hauwa matar Isma'il kenan, qawartace qus da qus, tasan sirrinta itama tasan nata, gashi Kuma zata Aure Mata miji,ansha ruwan masifa da Hauwa tazo har gida tayiwa Sa'adatu cin mutunci na qarshe, "azzaluma Maci amana,kamar ni Hauwa Sa'adatu Zaki auri mijina, bayan kinsan sirrina, mijin ma qanin mijinki, Allah ya Isa tsakanina dake, tana kumfar Baki da fita,daga gidan, sunyi baran_baran da facalarta Kuma aminiyarta,wacce sukasan sirrin juna wanda Sa'adatu ko gezau abunta, Aure dai Babu fashi, saita Auri Isma'il....
Shima Kuma Isma'il d'in, saiya fake da cewa ai don yakula da yara ne yasa zaiyi hakan, Kuma Hajiya sakinah ta goya Masa baya, akab ya auri Sa'adatu d'in, Hauwa har Yan uwa da Hajiya sakinah takejin haushi bayan Sa'adatu,Domin Saida yardarsu ai Isma'il zai Aureta d'in.......
Saura qiris a kammalawa Ummu Ruman gininta itada yaranta, Takoma gidanta, ta qale Sa'adatu a gidanta, kunga FANS sai tafi sakewa in tayi auren ma ko?
Ummu Ruman tana tunanin Lallai Sa'adatu, harta mance da Abby zatayi aure, aurenma kaninsa, itakam itada Aure har abada, wazata Aura? Har yaushe Abby ya rasu da zatai wani auren, duk da ba wucewa tayiba, inda ita Isma'il ya taya Aida bazata aureshi ba, to Ina Shi ina ita, ba sa'ar aurensa bace, ita ta girmi Sa'adatu, tsakaninta dashi akwai mutunci da girmamawa....
Wannan tunanin yasa Ummu Ruman kwanciya a asibiti, hawan jininta ya tashi,zuciyarta ma tanaso ta kamu da ciwo, dama Kuma ta rame tayi baqi ta fita daga hayyacinta, gaba d'aya tun bayan rasuwar Abby, ga rigimar Hunaif baya yarda da kowa...
Allah sarki Ummu Ruman kunji soyayyar gaskia, ita kuwa Sa'adatu aure ma zatayi ta shafe babun Abby, ta samu wani mijin mjinma qaninsa,tunda dai bayan rasuwar sa tad'an girgije alhinin rasuwar ya wuce ....
Wata sabuwa, sai Kuma Sa'adatu take yawo da Ummu Ruman cewa ai ba'kin cikin Isma'il zai Aureta ne yasa, zuciyarta take so takamu da ciwo, bakin cikin abun tasa a ranta(... Kuji FANS Lallai Sa'adatu bazata saduda ba ta koma ga Allah, nazata rasuwar Abby zatasa kiyayya da sharrin da takewa Ummu Ruman zata daina,tunda Wanda akeyi danshi baya Raye...)
Tunda akakai Ummu Ruman Asibiti batasan waye akanta ba, karkuso kuga y'ay'anta,wayyo Zakiyyah kullum tana zuwa asibitin, taita kuka, suma haka su Zahra, Hadiyyah, Hidayah, khadija, zeenah gani sukeyi itama Ummu rasata zasuyi kamar yadda suka rasa Abbynsu, kwanan Ummu Ruman biyar a asibitin, komai saidai ayi Mata Kashi da fitsari duk batasan tanayiba, duk Wanda yaganta sai ya tausaya Mata, ance ayi mata hoton 'kwa'kwalwa, Domin aga meyake damunta, 'yan wanta ne suka had'a kud'in, hoton, (... baza 'a dauka acikin duniyar da ake juya musu ba...) Anbiya kud'in hoton Ranar da za'ayi hoton Kuma Allah da ikonsa .................
Muje next page FANS, Wannan labari akwai tausayi bansan lokacin da nake share hawayeba,Ina tausayawa Ummu Ruman wlh da y'ay'anta da Kuma Y'AY'AN Sa'adatu d'in gaba d'aya Amma Banda ita Domin kuwa Bata tausayawa kanta ita d'in 😭😭😭😭😭😭
Karku manta dai har yanzu muna cikin tushen labarin wad'annan iyalan bamu dawo daga labarinba, tushen labarinne wannan .. karku manta kuci gaba da biyoni, har mukoma , cikin labarinmu da muka Fara daga farko Yan amana
Yanzu muka Fara akwai tausayi cin amana ha'inci maraicin iyaye guda biyu a tsakankanin watannin da Basu da yawa .......
✍️©️ Rabiat (Aminu Oum Arqam 👩🍼 ce)
2/7/24, 4:27 PM - Rãbi'atou Aminou {Oum ARQAM}: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/Cy82IooiC1LE5S0e2tkKcj
Na bude group dinnan saboda comments ko sharhi akan wannan littafi, please idan kinyi joining ki bani hadin Kai, duk lokacin danayi sabon Page's ki daure kibani lokacinku kiyimin comments, rashin hakan Yana sawa nayi removed d'in ki
✍️ *Daga Al 'kalamin ©️ Rabiat Amin (Oum Arqam) 👩🍼*
*08128131163*
Marubuciyar
KOMAI NISAN JIFA📚
HAKAN BA KUSKURE BANE📚
*RASHIN IYAYE* (babbar musiba)
Labarine na tsantsar maraicin iyaye guda biyu akwai tausayi cin amana ha'inci dadai sauransu
*__________________*
*MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION 📚🖊️(M°W°A)*
Kungiya d'aya tamkar da dubu masu Nazari da Aiki da ilimi Burin'kungiyar a ko da yaushe shine ta fada'akar ta Kuma Nishad'antar da masoyanta.🤙
*__________________*
*PAGE TEN 10*
"Allah da ikonsa ranar da za'a yiwa Ummu Ruman hoton 'kwa'kwalwar Kuma, Allah yai Mata Mata Rasuwa, tana jikin Mahaifiyarta kawai taga numfashi ta ya tsaya, dama tunda aka kaita asibitin ba motsi take ba, ta numfashi ake gane tana da Rai, idonta a rude yake dama, sai zubar hawaye dayakeyi, innalillahi wa Inna ilaihi rajiun! fad'ar tashin hankalin da Y'AY'AN Ummu Ruman suka shiga 'bata bakine! acikin wata shida ace ka rasa uwa da uba! wad'anda sune komai naka na rayuwa! mahaifi yafara rasuwa Wanda yakemusu komai! a haka suka haqura suka jure maraicin! saboda akwai uwa tare dasu, duk da dai Rayuwar tasu ba kamar da mahaifinsu ba, to yanzu gashi mahaifiyar ma, wacce take rage musu zafi, suke ganinta sukejin dad'i itama lokacin ta yayi, ta amsa Kiran ubangiji, Kar kuso kuga Zahra Hadiyyah da Hidayah, da Khadija, kamar zau haukace haka suka koma, itama zeenah duk da akwai kuruciya taji mutuwar "ummi" ga Kuma *Hunaif* d'an wata Goma a duniya, Allahu akbar , Rayuwa kenan sai haquri......
Zakiyyah tabada qaramin ciki lokacin, tana asibitin Ummyn tasu ta rasu, ai a take anan tayi 'bari saboda tashin hankali, sai kuka takeyi, to itama kenan FANS Wanda Basu shaku da Ummu Ruman ba, ba a hannunta ta tashiba, tana gidan kakarsu ta shiga wannan Hali inaga wad'anda suke tare....
Haka aka d'auko gawar Ummu Ruman zuwa gida, itama a gidansu akayi xaman makokin nata, Babu nisa da asibitin, kawai sai aka Kai gawar gidan anan aka dinga kar'bar ta'aziyyah, Allah yajiqan musulmi Baki d'aya....
Sa'adatu sai kukan munafurci akeyi, na mutuwar Ummu Ruman d'in, Sa'adatu kenan ga Ummu Ruman Nan tabar Miki duniyar, da kike cewa Wai bakin ciki take Miki Dan zakiyi Aure, Bata duniyar sai kiyi aurenki yanzu Babu Mai Miki ba'kin cikin, ita Tata ta qare ta tafi wajen masoyinta na gaskia mijinta Wanda soyayya tayi riba, zasu tashi ita dashi a lahira, kekam gakinan ga kawu Isma'il d'in nan.....
Kanwar Ummu Ruman Wanda suke uba d'aya, Aisha itace ta d'auki Hunaif, dama tun lokacin da aka kai Ummu Ruman d'in asibitin, tanada yaro namiji kusan tare suka haihu, gidanta take tafiya dashi, Yaita rigima acan, Amma kukan da yayi ranar da Ummu Ruman zata mutu yafi na kullum, tun dare yake kuka, yaqiyin shiru, Saida Ummu Ruman ta rasu Kuma yayi shiru, Aisha yace ka gano mutuwa kenan (... Allah sarki yaro ya hango rasuwar mahaifiyarsa, Wai dama ance yara suna ganinta...) Kafin rasuwar Ummu Ruman ana katashi ajikinta yasa nono, to bayan Rasuwar Tata Kawai Aisha saita Fara bashi nononta, ta hadashi da d'an ta tana shayarwa......
Bayan anyi sadakar bakwai Babu Wanda ya tambayi inda Hunaif yake, to yanzu dama Ina kud'i dadai Ummu Ruman d'ince ta rasu, Alhaji Ammar yananan da anyi rububin daukar sa Amma, dayake shima qasa ta rufe Masa Ido, Yan uwanwa Babu Wanda ya nemeshi, Allah ya kyauta...
Mahaifiyar Ummu Ruman Amina, shekara biyu da suka wuce ta koma Kaduna state da Zama, saboda jinyar Mahaifiyarta, ita kad'ai ta Haifa anan Kano, itama Yar Nan kanonce, mijinta ya rasu, shine tayi aure a kaduna state, to rashin lafiya takama ta, ita kuma lokacin mahaifinsu Ummu Ruman ya rasu, ita Kuma mahaifiyarta acan kaduna state duka maza ta Haifa, gashi tana fama da rashin lafiya 'barin jikinta