Showing 111001 words to 114000 words out of 141223 words
Chapter 38 - RASHIN IYAYE Complete Document by Rabi'atu Muhammad Rabi'u Oum ARQAM.txt
isha'i ɗin bai ga bro ba,may be yana ɗaya ɗakin nasu dake wancan part ɗin ko yana ƙasa shi hakan ma yai Masa daɗi!
"Ƙara shingiɗa yayi lokacin da yaji wayar tayi ringing!
"Assalamu Alaikum wa rahmatullah"
!Yaji muryarta cikin nutsuwa da Sanyi! Wanda sai da ya ƙara gyara kwanciyarsa haɗi da sauke ɓoyayyiyar ajiyar zuciya! Kafin ya Amsa sallamar
" Wa'alaiki salam wa rahmatullah"ya mayar mata kamar yadda tai Masa!
Sai kuma yayi shiru,itama shirun tayi,sai da taga shirun yayi yawa! Sannan Hadiyyah (lallai ne ALLAH ya taimaki AQEEL wacce yai zata itace tasa,kutayashi murna) tace " bangane me magana ba!
"Kina magana Da Hassan Ɗalhat ne" tunani Hadiyyah ta tafi wanene Kuma Hassan Ɗalhat? Ita dai a school ɗin su ba wanda take kulawa,hakanan bata Bawa wani mai wannan sunan number ɗin ta ba,ita da Babu inda take fita ma sai school,tunda maganar Aurensu ta ɓullo wai sai sun tambayi mazajensu!ta ina zasu tambayesu Alhalin Basu da number ɗin su kuma su bazuwa wajensu suke ba!
"Ya dai naji kinyi shiru ko baki gane me magana ba har yanzu,tunaninki bai katse na! (Lalläi wai dama Fans AQEEL yana magana da yawa irin Haka,Amma in da bro ne yace ya dameshi)
Bari nai miki gwari gwari "AQEEL ne!
Ai Hadiyyah zare idanuwa tayi kafin ƙwarewar Babu gaira Babu Dalili ta biyo baya"
Jin ta ƙware sai AQEEL yaji Babu daɗi,sai naji muryar sa yana "Sannu me kike ci ne?jin abunda yace sai tarin ya lafa ta Fara kame_kame kafin tace
"Babu komai kawai ji Nayi tarin yazo ne"
Gyara kwanciya ya ƙara a karo Babu adadi,dan muryarta tana Masa daɗi ne,fiye da tunanin mai tunani,har da ajiyar zuciya kuma🤔
Ita dai Hadiyyah zuciyarta fal da tsoro da tunanin yadda ALLAH yayi da ita ne, tasan halin AQEEL tasan sunansa, shine wannan mai tsare girar,kamar Baya magana, yai ta Wani yatsine yatsine ga Glass a idanunsa wanda yaƙara Masa kwarjini da kyau, ALLAH ga marainiyar ALLAH ka daidaita mata wannan Bawa da ka haɗasu inuwa ɗaya tun basusan kansu ba, ni ƴar nan wannan ne mijina na Babu! Tunanin da ya addabi zuciyar Hadiyyah kenan tun lokacin da tasan AQEEL shine mijinta.
Tunanin ta ya Katse lokacin da AQEEL yace MATA " Inason nasan da wacce ALLAH ya zaɓa mun matsayin MATA ne, shin me shuru shurun ciki kamar kurma ce? Ko kuwa me surutun ciki kamar aku ce?
Sai da dariya ta kwacewa Hadiyyah bata shirya ba! Jin abunda Yake faɗa gwanda in yace me surutu kamar aku,Amma idan yace me shuru shurun ciki kamar kurma ai shima Duk ɗaya ne,dan kuwa gwanda Hidayah dashi,dan ganinsu da tayi sau Biyu taga shi ko hirar da suke da Hidayah taga kam shi da ɗan uwansa shi kaɗai yake murmushin sa Amma shi baisan anayi ba!
Ya naji kinyi dariya ne ko me shuru shurun ALLAH ya haɗa ni da ita ne? Aikuwa da sake dan sai kin koyo surutu a wajen sis ɗin ki kafin akawo min ke cikin gidana,bazan ɗauka ba ayi shuru kamar kurame labarai zanzo a dinga bani da Hira cikin walwala(lallai Haseena kinji wai AQEEL ne yace zantuka hakan)
"Lalläi ma aikuwa nice Yanzu ya za'ayi kenan,banson hayaniya, surutu yana damuwana,sai dai kayi Haƙuri dani a Hakan!
Hadiyyah da tsinci kanta da faɗawa AQEEL Hakan(kunsan dama ai ita aku ce baki abun magana kamar yadda AQEEL ya kirata dashi)
"Hmmm Zaki zo mun cikin gida a Hakan zakiga yadda zanyi dake ne, wannan bakin saina gyara Shi ko ta tsiya da Arziƙi! Shima AQEEL ya tsinci kansa da faɗar Hakan
ALLAH ya taimakeni ni Hadiyyah! da Hidayah ALLAH ya haɗa da wannan data bani Alhamdulillahi! To Amma kuma ya Hadiyyah zata ƙare da wannan mai surutun tsiyar!
" Dan ALLAH kayi haƙuri karka tursasani saina iya surutu da magana,kawai kayi haƙuri dani kaji!
"Za kigani kizomun gidana a Hakan" inason Inji sunan ki ne,Nasan dai Hadiyyah da Hidayah ne to wacce aciki?
"HADIYYAH ce"
Lalläi sunan ku akwai daɗi sosai,Amma nafijin daɗin Hadiyyah Duk ma'ana daya ne Amma wajen Furtawa akwai banbanci HADIYYATULLAH Da HIDAYATULLAH Duk ma'anar su guda ce wato KYAUTAR ALLAH kunci sunanku kam ƴan biyu KYAUTAR ALLAH! Ya ƙarasa zancen da murmushi wanda har kunnen Hadiyyah!
Wanda itama murmushin tayi,
Sannan itama tace Nima sunanku yanamun daɗi musamman naka AQEEL!
Lalläi ne to kinsan ma'anar sunan ne? Ya jefa MATA tambayar nan! Yana lumshe idanu,alamun yau fa anjima ana magana,Babu sabo dole ya gaji, dan ma yanajin daɗin Hirar da Abar ƙaunarsa,gajiyar Duk ta kau
"Ea Nasan ma'anar Sunan AQEEL (wanda hausawa Suke ɓatawa suce Haƙilu,fatan fans kungane) Sayyadina AQEEL BN Abiy ɗalib yayan Sayyadina Aliyu ƙanin Sayyadina Ja'afar bn Abiy ɗalib
"Ma Sha ALLAH lallai ne kinsan ma'anar sunana, ƴar albarka!
Saura Sunan bro ɗina!nidai bansan ma'anar sunan sa ba,ban ma taɓa ji ba sai a wajensa!
Aikuwa sunansa yana da ma'ana mai kyau shima,zan gaya miki ne!
Kinsan wane ya zaɓa Mana sunan?
"A'a saika faɗa!
Ummuh ce tasa Mana shi da Hassan da Hussain kawai ake Kiranmu!
Kingane wacce ummuh ko?
"A'a gaskiya to ummuh ku Mana ai Abbu yabani labarin Hakan!
"ALLAH sarki Rayuwa kamar ba'a zauna ba, ALLAH yai Musu Rahma gaba ɗaya dai cewar Hadiyyah!
Shi kuma AQEEL ya Amsa da Ameen ƴar albarka!
_Abun mamaki sun shafe fin awa uku Suna waya! Sai kace sun jima tare Babu wanda zaice a Ranar suka Fara waya, mamaki na yafi ga AQEEL ma shida baison surutu ko ƙadan,gwanda ma Hadiyyah Baki Abun magana ce dama! Sun Sha hira sosai, To dama dai Hadiyyah tunanin AQEEL yai MATA yawa,shi kuma AQEEL ɗin shima wannan vedios ɗin yasa yafara jin Wani abu game da yaran tun sannan,sun rabo kowanne zuciyarsa ciki da nishaɗi da Annushuwa zuciyar AQEEL fal mamakin surutun Hadiyyah Mutuniyar da Bata magana a zahiri ,amma kuma sai mamakin yakau a Ransa shima ai baida magana Amma yanzu yayi maganar sosai ma! Yayi barci cikin nishaɗi da tunanin Hirar da suka yi shida matarsa! Har sannan bro bai shigo ba ko ina Yaje?
AKEEL
_Shi ma fita can yayi ɗaya dakinsu,dan yasan bro bazai barshi yayi wayar sa cikin kwanciyar Hankali ba,haka zaice ya dameshi da surutu,maganin kar ayi kar a Fara(lalläi AKEEL to shima yanacan yana soyewa daga tsaya,bazai ce ka dameshi na)
Dan haka sai da shima ya kammala komai nasa sannan ya kishingiɗe a sofa! Ya rangaɗa Kiran wayar!
Gidansu Hidayah yau Baabah itada da su Hunaif da Zeenah harda farouk da Haidar ma da Hafsat sunwa gidan Zahra tsinke can Zasu wuni,shiyasa Gidan yayi shiru, sai Hadiyyah da Hidayah kawaii sai kuma Sa'adatu a ɗakin ta tanacan abun duniya ya dameta, ta saƙa wancan ta kwance wancan,akan Alhaji Gambo dan har Yanzu bata kulashi ko yazo gidan ta ringa Masa hulaƙanci kenan,Amma Baya fasa zuwa Gidan a Ranar kwananta dan ya Bawa Kowacce haƙƙinta,Amma idan yazo Babu kwanciyar Hankali gareshi a wajen Sa'adatu!
Ita Hadiyyah tana falourn su tana kallo abunta,lokacin da AQEEL ya kirata, shi yasa tasha wayarta itada mijinta Babu takura.
Ita kuma Hidayah tana cikin ɗakin su a kwance Akan gadonsu,lokacin da AKEEL itama ya kirata tana ɗakin!
Da AKEEL yaga wayar tana ringing ba'a ɗauka ba har ya fitar da rai za'a ɗauka,zuciyarsa tana bugawa Akan shin wacece daga ciki matarsa irinsa aku! ko kuwa irin bro kurma! Shi kam a zuciyarsa yana Addu'ar ALLAH ya saɓa halaye a waɗannan matan nasu, shi yasamu mai shurun kamar kurma, yakoya mata surutun, shi kuma bro ya samu mai surutun Kamar aku ta koya Masa surutun! ya Zama mutum kamar kowa ba Kullum baki a rufe ba kamar kurma..tunanin sa ya Katse lokacin da yaji an ɗaga wayar!
Acan ɓangaren Hidayah kam tana kallon wayar tana ringing Amma miskilanci ya hana ta ɗauka,sai da taji ƙarar wayar ya dameta tana shirin kashe MATA dodon kunne(a cewar ta fa) sai ta ɗaga ba tare da tayi magana ba!
Ganin an ɗaga Babu magana ne yasa AKEEL yace " "Assalamu Alaikum fatan ina magana da matana ce?
AKEEL ya faɗa yana murmushin sa mai burgewa!
Mutuniyar ku taji sarai abunda yace Amma tai burus! Ya dai ko baki ji nane matar! AKEEL ya kuma faɗa,zuciyarsa tana Addu'ar ALLAH yasa mai shuru shurun ce tasa,kuma kamar yaji alamun Hakan indai ba network bane yasa yaji Hakan ba!
"Yadai matar ko abun ya tashi ne,ai na ganeki ni a Hakan ma ina maraba da wannan Rashin surutun indai surutu ne idan kinzo gidana na koya miki kinji!
Sai a sannan Hidayah tai magana
" To baki abun magana Hakan da kayi tabbas ya nunan cewa kaine AKEEL daga kirana a waya har kafara damuna da zancen ka, wanda Babu comma, balle full stop.
Lalläi ne ni kike gayawa Hakan, AKEEL ya faɗa haɗe da sakin Ajiyar zuciya jin muryar ta mai Sanyi,
"Ko ma dai menene yanzu nidai mijin kine,dole abini yadda nake,kuma surutun nan dai dole kema ki koya ki dinga yinsa,Zama tare dani ai zai sa ki koya,yanzu ma wazaice kece kin buɗa baki kinata surutu!
"Kai haka ma zakace mun ina surutu to ai saina kashe wayar kawai! Cikin shagwaɓa Hidayah ta ƙarashe Zancen!
"Aimun afwa ranki ya daɗe! Bazan kuma faɗar haka ba!
Yanzu dai kinsan sunana ma kin faɗa, nasan sunanku Hadiyyah da Hidayah to waccece aciki Dan ALLAH?
"To wannan HIDAYAH ce, ba aku mai bakin surutu bace Hadiyyah irinka ba, ni kam dama ita kasamu. Dana huta da surutun ka!ta ƙarasa maganar cikin ƙosawa
"Nikam nayi murna da Hakan ai,dana sameki matsayin MATA ta! Indai surutu na ne karki damu bazai dameki ba,tunda zan mayar dake kalata bada jimawa ba!
"Zamu gani kuwa bazaka koyamun surutun ka ba,saidai na koya maka Rashin magana ta Hidayah ta faɗa cikin murmushi jin wannan surutunsa yafi na wancan Ranar!
To mu ƙulla alƙawarin Hakan Duk wanda ya rinjayi ɗaya daga cikinmu, idan Kika koma surutu na na ciki wasa,idan nakoma kurma kamar ke ko kincini wasa! Ya ƙarasa maganar sa dariya!
"Shikenan na yarda da wannan Zancen, Amma shine kake cemin kurma ko? Cike da shagwaɓa (Lallai Hidayah masu shuru shurun nan sai a barsu sun iya soyayya kalli dai yadda AQEEL shima yayiwa Hadiyyah)
Shikam AKEEL jin shagwaɓar da ake Masa ne,yasa wata ƙauna da soyayya tana shigarsa ta wannan tahalika, lallai AKEEL ma da bai damu da wannan ba barshi da surutunsa, soyayya Ruwan zuma.
Sun jima Suna hirar su cike da soyayya,wanda rabin hirar Duk AKEEL ne Yake jan maganar ita kuma Hadiyyah sai ta mayar Masa da Amsa! Sun yi Hira mai tarin yawa, AKEEL sai bata labarin vedios ɗin daya Gani yakeyi yana kwasar dariya,itama tagaya Masa cewa ai sunga wannan Vedios ɗin itada Hadiyyah Amma fa sha'anin AQEEL da HADIYYAH yafi kowanne dariyar,sai kuma nasu ta yadda ita ɗin take bawa AKEEL ɗin Haushi na Rashin dariya in anmata wasa,Hakan shi kuma yanasa AQEEL nishaɗi,Duk da a farko shima AKEEL ɗin yaci dariyar shakiyanci a Lokacin da Hadiyyah ɗin take koke_koke bata yarda da AQEEL,shi kuma Hidayah tana yarda dashi!
Ansha nishaɗi a ɓangaren wannan masoya Suma kamar sun jima tare, Nikam oum ARQAM sai na nemi shuru shurun Hidayah na rasa,Kodai abunda AKEEL yace na zai mayar da ita mai surutu idan sun zauna waje ɗaya zai tabbata? Tun da dai yanzu gashi a waya ma yafara canza ta!
"AKEEL yace wai ke taka mai mai ma ya sunan ki ne na tagwaitaka?
Cike da nishaɗi Hidayah tace "Hussaina Mana!Kaifa?
AKEEL yace
Hussain na Hussaina man,ai sunan mu ɗaya kai wannan abu yamun daɗi sosai matana!
Kinga bro shima Hassan na Hassana kenan komai namu iri ɗaya,an Haifemu mu bibbiyu sannan mun Auri mata Suma su bibbiyu ga sunan mu iri ɗaya ma, dama muna da wannan burin nida bro ashe ma ALLAH ya tsara Mana Hakan! Ya ƙarasa Zancen Cikin Nishaɗi! Suma sun jima Suna Hirar har wajen 11:00 na dare, dan Basu Fara wayar ba sai wajen 9:00 sunyi Sallama cikin ƙaunar juna kamar bazasu rabu ba.
Tana kammala wayar ta kashe kayan kallon tayi ɗaki Abinta zata kwanta, dan su Baabah Basu dawo ba ba har sannan maybe sai nan gaba Ibrahim mijin Zahra ya kawosu har gida.
Ta tarar da Hadiyyah a kwance tayi barci,Dan ita wajen 8:00 suka Fara wayarsu wajen 10:00 suka kammala,itama Azkar tayi ta kwanta abunta.
Bata jima da kwanciya ba mota tai horn alamun su Baabah sun dawo, Mai gadi ya buɗe musu gate(Alhaji Gambo ne yakawoshi saboda idan yana gidan inzai shigi Babu mai buɗe Masa) kowanne yana shigowa makwanci ya nema an raba dare a Hanya.
AKEEL yana kammalawa waya da Abar ƙaunarsa kawai sai ya tashi daga sofa,ya shige cikin ɗakinsu na barci domin ya kwanta anan kawai.
Lallai ne yau soyayya tayi daɗi abunda Basu taɓayi ba shida bro raba makwanci yau sunyi sanadin ƙauna.
A Masallaci suka haɗe da bro sai hararar sa yakeyi,Akan shine yau ya Kwana a ɗaya part ɗin alhalin yasan basa Hakan,abunka da mai surutu nan ya gaya Masa cewa Hira da matarsa ce tasa shi Hakan ko kunya bai jiba! Ko da Yake basa ɓoye wa juna komai!
Shima AQEEL ɗin ya gaya Masa yadda sukayi da tasa matar Amma baice sun jima Suna waya ba,kawaii dai yace sun gaisa,ko da Yake bro ai dai zai Gani tunda ɗaki ɗaya suke kwana.
"A wajen breakfast Abbu yake tambayar AKEEL ya sun Kira yaran kuwa?
Baki Abun magana wato AKEEL nan ya Bawa Abbu labarin yadda sukayi cikin nishaɗi,harda AQEELshima yadda sukayi.
Abbu yana ganin yadda ɗan sa yadda Yake fara'a yasan tabbas yanason Yarinyar!
Idon Abbu yanakan AQEEL yaga yadda shima fuskar sa sake take ,aikuwa yaga yana Wani makirin murmushi wanda bana komai bane illah na shima yanason Yarinyar ne,Amma kuma miskilanci da zurfin ciki ya hana ya nuna kamar yadda ɗan uwansa yake nunawa,cikin zuciyar ABBU murna da godiya ga ALLAH ne da ALLAH ya haɗa ƴaƴansa da abunda sakeso,da kuma cikar burin marigayi Amininsa Ammar ALLAH Kenan mai yadda yaso.
Abbu ya nunawa Mommah AQEEL na murmushin da yakeyi, Mommah da Abbu suka haɗa ido Suna murmushi na jin daɗi, Mommah take "my son meke faruwa kake murmushi kai kaɗai ne tun ɗazu? AQEEL baisan ma tana magana na zuciyarsa tana can tunanin masoyoyar sa Hadiyyah ne, Abbu yace Mommah ta ina AQEEL zai jiki yanacan ya faɗa shauƙin soyayya!
AKEEL ya taɓo AQEEL tun farkon maganar Mommah!
maganar da Abbu yayi kuma a kunnen AQEEL dan haka yanajin Abunda Abbu yace sai ya Mike yana murmushi alamun kunya yabar dining ɗin,sai gaba ɗaya akasa dariya!
cikin nishaɗi suka kammala breakfast ɗin kowa yakama gabansa.
ABBU ya yanke shawarar zuwa wajen Kawu Isma'il Akan Zancen.
____GIDAN JIMMAI__
Usman kam zaman gidan baya masa daɗi kwata kwata, jimmai bata kulashi balle Shukhra,da Daddy kawaii yake Zama yai taiwa yaron wasa ko yai Masa home work, sai ya fita yake samun sukuni, abokansa kam sunga canji ga Usy yanzu bai kula MATA ko wucewa ƴan MATA sukazo yi sai ya kau da kai, ga ramar da yayi sunyi tunanin cutar da yayi ce tasa shi yana warwarewa zai koma ruwa(ALLAH sarki bakusan Usman yanzu ya shiryu na duniya ta bi dashi)
Yana zuwa can gidan Umma itama Duk da na wai Wani kulashi takeyi ba, insun zauna ta dinga Masa nasiha ne Akan ya kiyayi duniya ga dai yadda tai Masa,yaci gaba da istigfari da neman gafarar jimmai da Shukhra ɗin, Usman cikin damuwa yace "umma kullum saina Basu haƙuri na nemi gafara Amma basa kulani,kaci gaba da Basu haƙurin kasan abunda Kayi Hukuncin da yafi hakama an maka, Amma kaci gaba da neman gafarar yau da gobe sai ALLAH,kuma akwai ƙaunar ɗa da mahaifi tsakaninku da Jimmai haka na itama Shukrah akwai ƙaunar ƴan uwantaka da shaƙuwa mai Zafi,sa Sannu komai zai wuce ne.
Waɗannan zantukan da suka tattauna da Umma sai yaji zuciyar tayi Sanyi, ya ɗauri ɗamarar cigaba da neman gafafar su, ya ƙudircewa Ransa zaije har gidansu AKEELA da AKEEL da kuma AQEEL ya nemi gafararsu dan yasan Abubuwan bazai tafi daidai ba in bai nemi gafararsu ba.
Tun daga Ranar Usman ya dage da istigfari da Hailala da salatin Manzon ALLAH, da tsaiwar dare da neman gafarar ALLAH Akan zunuban da ya aikata a Baya, kusan dama shi ALLAH gafurur raheem ne yana amsa Addu'ar bayinsa ne masu neman gafarar dan haka........
Yasin nagaji wai wannan typing me tsayi haka ku tara next page gaskia dan kuji ko mene zai far......
Yawan Comments ne next page kuma🥱
✍️Oum ARQAM ce ontop 🥰
6/30/24, 10:47 AM - Rãbi'atou Aminou {Oum ARQAM}: *RASHIN IYAYE*
(babbar musiba)
Mallakar Rãbiat Ãmin {oum ARQAM}
08128131163
Marubuciyar
Komai nisan jifa
Hakan ba kuskure bane
____________________
*MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION M.W.A*
____________________
*PAGE SIXTY ONE 61*
Kwana biyu kunjini kurum🌝 yasin ina busy ne🥱baku ba Nima na ƙagu🥹 na kammala Cikin ikon ALLAH🙏, ai wannan Littafin yasha jinkiri ALLAH yasa ma Alkhair ne😩 tun 1/1/2023 fa na Fara shi😳 bansan Ranar gama shi ba kuma amma dai saura ƙiris👌
_______ABBU_______
" Kamar yadda ABBU ya ayyana a Ransa Hakan yayi,kwana biyu tsakani ya dangana ga gidansu Hauwa wato wajen kawu Isma'il.
Sun tattauna zantuka da yawa,ciki harda yiwa kawu Isma'il Albishir da cewar ya biya Masa ragowar bashin da banki Suke binsa, shiyasa ma tun sallamarsa Daga Asibiti Basu kawo masa ziyara, Abbu yace Masa "saura kwana biyu a sallameka naje bankin nasa Hannun Akan zan biya maka cikon bashin,yanzu in ALLAH yakaimu Monday tunda yau Saturday zamuje banki na Basu ragowar kuɗinsu in yaso sai ayi rubutu,kasa hannu nasa" ALLAH ya kiyaye gaba"
Sai ga kawu Isma'il yana Kuka wiwi! Gwanin tausayi yana tawa Abbu Addu'a ta Alkhair da Fatan ALLAH yayiwa zuri'a albarka!cikin kukan yake cewa " ALLAH kenan me yadda yaso da bayinsa ALLAH na tuba yaran dana dinga cuta na daƙilewa Rayuwa SABODA son zuciyata sune yanzu sanadinsu ALLAH yakawo mun Ɗauki, Nikam Isma'il naga rayuwa tabbas nasan cewa Ɗa na kowa ne,bakasan wanda zaka mora ba,wanda ka kyautatawa sai ALLAH yaso ya kyautata maka, ALLAH ya gafartawa Yah Ammar! Ka yafemun cin Amanar dana maka, ta tozarta ƴaƴanka, yanzu gashi ALLAH ya nunan iyakata tun ba'aje ko inaba, su ɗin ta sanadinsu da arzikinsu rayuwata zata ƙarasa na tuba"
Ganin Irin kukan da kawu Isma'il yakeyi sai da Abbu ya tausaya Masa yasan cewa tabbas Isma'il ya dawo Hanya