Showing 96001 words to 99000 words out of 141223 words

Chapter 33 - RASHIN IYAYE Complete Document by Rabi'atu Muhammad Rabi'u Oum ARQAM.txt

Usman ya lallashi Shukhra ya fito daga ɗakin dan kuwa zamar Masa da tayi ajiki ya jefa shi cikin Wani yanayi!saboda kar asamu akasi yasa ya fice.


Ɗakin Umma Yaje wacce taci Kuka, cikin alamun damuwa ya dinga kwantar MATA da Hankali,kafin yafice, ɗakin ABBA wanda yake barcin wahala da aka haɗa Masa da allura!


Haka wannan Ahali suka kasance cikin baƙin ciki Abba da Umma da uwar gayya Shukrah Duk ta rame, har Asibiti ta kwanta likita yai MATA gargaɗi Akan ta kula da damuwa kar yashafi ɗan cikinta, kuma daga Umma da Abba Babu wanda yayi yunƙurin zubar da cikin sun zubawa sarautar ALLAH idanu.


shi kuwa Usman tunda yaji cewa Shukrah tanada ciki yasan cewa tabbas nasane, ko wata fargaba baiji ba, cewa Shukrah ƙanwarsace uwa ɗaya uba ɗaya,ita yaiwa ciki kuma ba'asan ko wane ba! Yabar mutane cikin damuwa da azaba, musamman ita Shukra ɗin datake tunanin samuwar cikinta, kamar dai yadda yaiwa AKEELA fyaɗe haka ya sha shantar da zancen, shirin barin garin yake ma, da kudirce a Ransa Shukra nazata haihu yananan ba, ɗa ko ƴa kuma zai Bashi kulawa tunda dama ɗan ƙanwar sane ba wanda zai zargi Wani abu.


Kwanciyar Shukra a asibiti sai sannan Umma take gayawa Jimmai meke faruwa! Sai ga Jimmai tana Kuka wiwi da tsinewa wanda yaiwa ƴarta haka,sai Ku ka take, tana lallaɓa Shukra Akan tagaya MATA wane Amma amsar daya ce! "Maama bansan wanda yaimun cikin nan ba" tun daga sannan Jimmai ta ƙasa lafiya, hawan jini ya kamata ga targaden da Abbu yaji MATA har sannan tanajin zafinsa sa'i da lokaci.
Tuni Usman yabar gari a zummar Wata seminar ya samu, yana waya dasu Umma da Abba yana Kwantar musu da Hankali, haka ma Shukra, jimmai kuwa ko nemanta baiyi ba, sai itace ta nemeshi take Masa zancen cikin Shukhra! Babu kunya Babu komai yace ciki nawane, Duk yadda yayi da bawa Shukra maganin da yayi Saida yagayawa Jimmai wanda kafin tagama ji dama a tsaye take, sai uwarta ji tayi ta faɗi tiiiim! Cikin sauri tazo ta gareta Amma ina Babu numfashi, kururuwa inna tasa a waje da gaggawa maƙota suka cika gidan, kafin mene an taimaka ansa Jimmai a mota sai Asibiti,aka bata taimakon gaggawa,jininta yayi sama sosai hakan yasa paralyse ( cutar ɓarin jiki) ya sameta ga bakinta ya karkace Babu ikon magana sai yawu ne yake zuba Duk mai imani idan yaga halin da Jimmai take xai tausaya MATA! A haka har aka sallamota aka dawo Gida, Babu Wani cigaba, saidai a Kwantar a tayar tanason magana Amma Babu hali, sai kuma yawu na zuba, weekend yazo AKEELA tazo gaisar da kaakar ta anan taga halin da Jimmai take ciki, Duk da Hakan ta tausaya MATA, Amma ina Jimmai na tozali da AKEELA jiki ya Fara kakkarwa alamun tanason magana amma ba bu halin yi, AKEELA ganin halin da Jimmai take ciki sai da tayi Kuka.
Inna ce ke kula da Jimmai dan haka sai a Hankali har tayi kashi da fitsari bata gyara ta ba,Duk jikinta ya ɗauke alamun kwanciya ga najasa kullum acikinta take.


ALLAH kenan Jimmai tasan kowane yaiwa ƴarta ciki ba kowa bane illa ɗan ta na cikinta ,Amma Babu bakin magana, sai dai kukan kawai


Watanni haka suka shuɗe cikin Shukhra ya isa Haihuwa, ta lalace ta jeme, shima Abba jikin sai a Hankali, gwanda Umma, bata da jini ko ƙadan ga kumburi gwanin tausayi, dan Haka aka ce C's za'a mata, anshiga da ita ɗakin kafin ayi ALLAH ya saiketa lafiya ta samu ɗan ta Namiji,mai kama da Usman sak! Babu wanda yakawo komai tunda dai ɗa kama da yayanta yakeyi kuma itama Suna kama, haka aka MATA kowanne irin taimako da kulawa suka dawo gida zuciyoyinsu babu daɗi,sai Da aka sallamo Shukra sannan aka gayawa waya a waya, ta mance da wata jimmai a gurin tana sallallamin ta " Shukra ta haihu, ALLAH gamu gareka ALLAH ya tonawa maci amana asiri,Amma kuma ta yaya ma wai Wani ɗan Iska yashigo gidannan yaiwa yarinyar nan ciki!ita kuma ba ko ina take Zuwa ba,ko a makaranta tana Zuwa Wani gurin ne,karfa yarinyarnan ta raina Mana Hankali fa ciki da ba'asha a ruwa dole akwai wanda yai mata,kuma ma ai amfani dakai bakaji alama ba kana budurwa, zanzo gidan ne dole yarinyar nan ta faɗa Mana gaskiya,nan dai suka tattauna da inna da Umman Shukrah.
Jimmai Duk hirar da suke tanaji zuciyarta sai ƙuna take ba bu bakin magana,sai Kuka take haka inna ta lallasheta Amma taƙi shiru,nan danan zazzabi ya rufeta.


Shukra Babu Aiki sai Kuka ko kula ɗan batayi, cikin ku ka take gayawa my bro aikuwa ya dinga kwantar mata da Hankali,Amma taƙi, picture ɗin yaron yace ta tura Masa, aikuwa cikin Kuka tace! "ni yaya Babu ruwana dashi! Naji dai ance yana kama dakai, komai da komai, ɗaukar min picture naga my son, sis kiyi haƙuri ki Kula da yaronnan kinji! Babu ruwansa! Nan dai Usman ya dinga lallashin Shukra Akan kula da babyn,Amma Babu Wani cigaba, dan bata shayar dashi sai madara kuma Babu wanda ya takurata,inna har gidan tazo ta inda tashiga batanan take fitana Akan Shukra ta gaya mata gaskia Akan wayai mata ciki Amma magana ɗaya ce batasan wanene ba!
ALLAH sarki Abba haka ya dangana ya barwa ALLAH hakama Umma sai Jan Shukhra ajiki suke Amma ina!
Baby yaci sunan Kabir sunan Babansu Shukra An Kiransa Daddy,yaro sak Usman kamar an tsaga kara,wane Zai kawo wani abu Akan hakan?
Usman yadawo gidan daga tafiya haka yake kula da Daddy kullum yana wajensa, ALLAH yasanya Masa ƙaunarsa a zuciyarsa,yana kula da ɗansa yana fakewa da ɗan ƙanwarsa ne.
Haka yaro yai ɓulɓul dashi, Shukra takoma school abunta,an faɗa batada LAFIYA ne abunka da makarantar kuɗi, AKEELA tai jimamin abunda ya faru da Shukra ta tausaya mata,Amma kuma tasan cewa Alhakin fyaden da Usman yai matane ya faɗawa Shukra ƙanwar sa, ABBU yasan da zancen abunda ya faru da Jimmai da ƴar ta Shukra ko ya nuna yaji yasan cewa kaɗan ya Fara gani,saura Usman shi ma zaiga sakayyah ne.








********************




*NEW DELHI*






Farkon zuwansu AKEEL India Babu Wani karatu da AQEEL yakeyi sai damuwa da take Ransa,Hakan yana damun ɗan uwansa inya cika matsa Masa Akan karatu kuma cutarsa ta Tashi,dan haka yake tsoron Masa magana,yana kiran Abbu ya gaya Masa, halin da ake ciki Abbu inya kirashi sai dai yayi shiru in yana Masa faɗa, Ɓangaren lalurar sa ta desire (sha'awa) kuma dama ita sai da kwanciyar Hankali take samun mutum, dan haka kwata kwata yadaina ciwon cikin nan,balle ya fita hayyacinsa, sai ABunda ba'a rasaba tunda kuwa Namiji ne shi kuma me lafiya.
Sai da suka ɗau watanni acan kafin ALLAH ya taimaka AQEEL yafara karatu,dayake akwaisu da ƙokari kuma Duk course ɗaya suke wato community health,har sannan Saida Glass AQEEL yake Amfani,shine kawai banbancinsa da ɗan uwansa,suna waya da AKEELA akai akai nan take gaya wa AKEEL abunda yafaru da Jimmai da Shukra, ALLAH ya sauwaƙe kawai yace, shi AQEEL dama ba Wani magana da sakewa yakeyi ba sai a slow ita kanta AKEELA ɗin ba Wani kulata kamar da yake ba,mutumin da da komai Auta AKEELA Amma yanzu sai a Hankali,to itama ma ai sai a slow ɗin dan Duk cikin damuwa suke, AKEEL ne me dama_dama.






Ɓangaren su AKEELA
________Tun bayan barin AKEELA asibiti ALLAH ya ɗorawa doctor Najeeb ƙaunar AKEELA dan farko ma yazata tausayin ta dayake ji ne,Amma ina ƙauna ce Ashe, Babu Wani ɓata lokaci ya gayawa Abbu, shi kuma Abbu yace "Babu matsala Najeeb kaga dai ABunda ya faru da ita ko,banson asamu matsala daga Baya ne! Cikin karaya Abbu yaƙara sa xancen, kuma ka ga dududu yarinyar nan banda ƙaddara guda nawa take ko 14years batayi ba, "ea yallaɓai Babu matsala kuma zan jira ta ƙara girma ,magana dai nayi saboda kasan da maganar! Doctor Najeeb yaƙara magana cikin girmamawa.
Aikuwa Abbu yayi murna da Hakan yagawa AKEELA yadda sukayi da doctor Najeeb ita kunya ma taji, kamarta ace anaso,su AKEEL sunyi murna da haka ALLAH ya rufawa ƙanwarsu asiri suna murna ALLAH ya sakawa doctor Najeeb da alkhair.


Doctor Najeeb Baifi 25years ba ɗan masu kuɗi ne sosai, kunsan sha'anin kuɗi nan danan yana kammala karatu yasamu aiki,kuma yanada ƙokari sosai, dan Kano ne shine na uku a gidansu,akwaishi da Hankali da nutsuwa Bashi da wata matsala,koda yaiwa Mahaifin sa zancen AKEELA, Bappan sa yasan Alhaji Ɗalhat ma ai Babu damuwa ya amince,ya kirashi a waya sukayi magana Akan sai yarinya ta ƙarasa secondary school sannan,in yaso ta ci gaba a ɗakin mijinta da karatun.


Mommah ta Zamarwa AKEELA kamar mamanta, komai yi MATA takeyi, hakana kullum cikin kiran su AKEEL take da kwantar musu fa Hankali Akan komai ya wuce tana Basu kulawa sosai.


Dawowar su AKEEL wutun farko Abbu yabiya musu suka je gaba ɗaya suka sauke falali harsu inna Rabia da Baba Sallau, komai yana tafiya daidai, foundation kuwa yafi da haɓɓaka, daga garuruwa ake kawo Yara.




Hakana Daddy tuni yayi wayo abunsa har sannan anrasa ubansa,ya saba da Usman sosai, har sannan Babu nafamar da Usman yayi sai ɓare barikinsa dayayi,gida guda ya ware inda yake kai MATA kala_kala yana watsewarsa dasu, ko kunya ko tsoron ALLAH to mutumin ma da yayiwa ƙanwarsa wazai ji kunya a duniyar nan,sai ɓarin naira yake musu.
Jimmai dai har gida Umma tazo da daddy taganshi, sai da ta razana ganin kamminsu da Usman kamar lokacin tana goyonsa sai Kuka kawai takeyi, ana share MATA hawaye Babu halin magana,su dai Basu kawo komai a ransu ba,indai Usman yazo haka Take kukan nan hakana AKEELA, ko kuma haka kawai ma, Usman shi kuwa ko ajikinsa in yazo tana Kuka kallonta yakeyi Babu kunya ma a tare dashi, da tafiya ta miƙa ma daina zuwa gurinta yayi dan kuwa duniya ce shi yanzu a gabansa, Jimmai kam har sannan Babu Wani cigaba game da jikinta.
Shukra kam magana Bata ɓuya sai gashi ana zunɗenta ai tayi cikin shege Babu damar taje makaranta ana matsawa daga jikinta, ashe ashe lokacin data haihu akwai wata ƙawarta itama ankawota zata haihu anan taga Shukrah da ciki, nan kuma anzo makaranta ance batada LAFIYA,sunzo dubata kuma anhanasu ganinta ance bata gida, aikuwa makaranta ta gagari Shukra Babu damar shigowa gidan tunda akwai masu gadi, Suna da groups na makaranta ga numbers ɗin ƙawayenta har anan habaici ake MATA Akan tayi cikin shege,Babu wanda bai san abunda ya samu Shukra ba yanzu Duk layinsu....






Lalläi ne Jimmai abunda ka shuka.....




Su AKEEL dai ABunda tai niyya garesu gashi bai faruba....


AKEELA ta samu mijin Aure Babu wanda yasan meya sameta...


Su AKEEL suna karatu....


Usman shikam sai duniya ta horarsa Inaga xaiyi nadama




ALLAH sarki Shukra laifin uwarki da yayanki ya shafeki




Wannan wace irin masiface ka Haifi ɗan shege kuma ace yayanta yai maka cikin kai jimmai kin cuci kanki, Alhakin marayun ALLAH ne




Muje zuwa dai




✍️Oum ARQAM ce ontop 🥰
4/18/24, 9:37 PM - Rãbi'atou Aminou {Oum ARQAM}: *RASHIN IYAYE*
(Babbar musiba)




Daga *Al 'kalamin✍️ Rabiat Amin (oum Arqam)*


*08128131163*


✍️ Marubuciyar...
*Komai Nisan jifa* 📚
*Hakan ba kuskure bane*📚




*_____________*
MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION📚🖊️ *(M°W°A)*


'Kungiyar d'aya tamkar da dubu masu Nazari da Aiki da ilimi burin 'kungiyar a koda yaushe shine ta fad'akar ta Kuma wa'azantar ta Nishad'antar da masoyanta🤙
*_____________*








*PAGE FIVETY FOUR 54*








Ko ina ka ji ana zancen Tallafy foundation saboda irin taimakon al Uma da cibiyar takeyi a koda Yaushe,tsakanin Abbu da al uma sai addua hakan ne yasa a koda Yaushe dukiyarsa take gaba,gashi yana ganin alkhair ta ko ina Babu indai a baɗin Nigeria zakace tallafy foundation a rasa wanda zaice bai sanshi ba, ga kuma Tallafy group of company, Babu abunda baya oda na kayan abinci da sauran kayan provision, da kuma Tallafy Holding company Duk wasu kayan karafuna da kayan wuta fanka generators,ion, fridge, da dauransu ga kuma injinan mota, har mota yake daga kashashen waje Kowacce irin mota akwai.
Tun farkon Fara tasowar Abbu Alhaji Ammar BN Yasir yasan shi sosai Saidai kuma ina bai sanshi da Wani Tallafy ba, ai da yasani da tuni ya lalaubo Abokin amana,har Abubuwan da yake Amfani dasu yana siya a company ɗin, Rashin sani yafi dare duhu gashi kuma har ALLAH ya ɗau ran Alhaji Ammar Babu rabon ganawarsa da Aboki ko nace ɗan uwa nagari.






______AQEEL DA AKEEL______ yadda a koda Yaushe Addu'ar da akewa Abbu shi da zuri'ar sa itace take tasiri akansu dan kuwa ALLAH yana Basu Sa'a Akan sha'anin karatunsu sosai, Duk Wani shashanci da majority wanda suka tafi karatu ƙetare sukeyi irinsu shaye_shaye,neman MATA ALLAH ya tare su dashi, musamm AQEEL shi da dama baya shiga harkar kowa inba ɗan uwansa ba,balle kuma wata mace, miskilanci fa sai ABunda yayi gaba yana girma shima yana ƙara girma miskilancin, ɓangaren Cutarsa kuwa Duk yadda zata kaya ɗan uwansa baya sakashi a damuwa balle cutarsa ta Tashi, Amma kuma idan wataran yatuna irin wahalar da sukasha a Hannun jimmai sai dai ɗan uwan yaga idonsa yayi ja yana shaƙuwa, sai barci shikenan kuma, zamansu a New Delhi kam sai san barka, ABBU da Mommah da kuma AKEELA Suna zuwa dubasu idan Akeela anyi hutun school, Anan ma ABBU yake zuwa a duba lafiyarsa shida iyalansa shiyasa ma kamar su AKEEL suna kusa da iyayensune.
AKEEL da AQEEL akwai kyau da tsafta sosai ba'a banbacesu saita halayya da kuma Glass a fuska.








*****************






Usman fa duniya da tsinke akeci Lallai barikince a gaban sa, din da Hakan bappa da Umma basusan halin dayake ciki ba,daga gida kuma yaga gidan yai Masa kaɗan Rana Tsaka aka nemeshi aka rasa ya shiga duniya, Duk hankalin bappa da Umma ya tashi kwana biyu Basu ganshi ba idan ankira wayarsa ba'a samun sa,sai adduoi ake da nema Amma shiru, sai da aka ɗauki wajen wata guda sannan yakira su yake cewa shi fa ya koma kudu da Zama su tayashi da addu'a,kawai Amma gidan su abokinsa yakoma kuma zai samu adimission anan yaci gaba da karatun sa,saboda yatawo da takardunsa nan, Ko jiran maganar da bappa yake Masa baiyiba ya kashe wayar gaba ɗaya,wa afka masha'arsa shida sabuwar budurwarsa me suna Alxendara, ƴar Wani mai kuɗi ce yanzu haka shi da ita shirin barin ƙasar suke yi.
Tun daga sannan kuma ina ba'a sake jin ko motsin Usman a waya ba iyayen sunyi Kuka Amma ina sai Haƙuri.


Shukhra dai makaranta ta gagareta saboda tsamgwamar da ake MATA,Babu dama ta fito a unguwar,shikam Daddy yai wayo abunsa Babu abunda ya dameshi, ganin gidan Babu kowa daga ita sai shi ahaka shaƙuwa ta shiga tsakanin Daddy da Shukrah, tafara jansa a jiki,tun yana tsoronta harya daina, komai ita take Masa shaɓanin da Umma ko ƴan aiki, sanadin tafiyar Usman tasa Bappa yakamata cuta sosai jininsa yai sama sosai kwana biyu tsakani yace ga garinkunan, bappa yanason Usman sosai, darajar ɗan uwansa, umma tasha Kuka haka ta haƙura tafara takaba harta kammala Babu ɗa Babu jika. Su Shukra ansha kuka da daddy, wanda ya zata bappa ne mahaifinsa, har bappa ya cika yana ALLAH ya saka miki Shukra wanda yai miki wannan zaluncin Duk inda yake kar ALLAH yarufa Masa Asiri, ALLAH ya bayyana shi.




_____JIMMAI____
Jimmai kam jiyya tayi jiyya yanzu tana Zama da kanta, bakinta ya daina zubar da yawu Amma fa babu magana,hakana tana ɗan motsa hannunta guda ɗaya,hakanan Babu tafiya sai Kuka, rana tsaka inna ta kwanta barci aka Tashi rai yayi halinsa, mai jiyyar Jimmai an mutu haka jimmai akasha Kuka, sai Shukra ce tadawo gidan take jiyyar Jimmai ita da Daddy suka dawo,indai jimmai yaga Daddy sai tayi Kuka, shi kuma kamar son kukan yake haka zaizo gefenta ya zauna ga ɗan banzan surutu,sak dai Usman lokacin yana yaro idan jimmai ta kalleshi, sha'anin jiyya sai Haƙuri musamman yarinya kamar Shukra dan haka sha'anin kula da Jimmai sai a Hankali,Babu wata cikakkiyar tsafta da dinga wari da zarni kenan, Duk abun bukata umma ke aiko musu dashi


Umma kuma ƴaƴan ƙanwarta ta ɗauko suke tayata Zama, itakam batada matsala tunda ta shuka alkhair...




______AKEELA_____
Tana cigaba da karatunta yanzu haka ta shiga babbar secondary tana Aji biyu, ta xama cikakkiyar budurwa ma Sha ALLAH ga kyau da nutsuwa, Amma indai ta tuna Abunda yafaru da ita saita kasance cikin damuwa, kullum Mommah cikin Kwantar mata da hankali take, tsananin ta da doctor Najeeb kam soyayya suke mai tsafta,yace MATA ai munkusa zama abu ɗaya, burina akoda Yaushe in ganki a gidana,sai ta karaya tace wane abu ɗaya kuma Wane zumuɗi zakayi alhalin ni da ba cikakkiyar budurwa ba da ta faɗi haka Doctor Najeeb zaita gaya mata kalamai masu sanyaya zuciya Akan shi ma ruwansa da wannan burinsa a koda Yaushe ita wannan kuma ai ƙaddara ce to shiyasa wataran take samun salama a zuciyarta.


Koma Alhamdullillahi yana tafiya daidai a Wannan ahali dai ABunda ba'a rasa ba, har zuwa lokacin dawowar Hankalin Abbu ya nemi Abokinsa, Ammar BN Yasir da baƙin cikin Samun rasuwarsa da yayi, da halin da ya fuskanci ƴaƴansa Suke ciki, na maraici da takura a wajen Sa'adatu, shine fa ya bibiyi ahalinsa ya taimaka musu sosai, yaiwa Kawu Isma'il talala, da fayyacewa su AKEEL cewa ai suna da Aure dasu Hadiyyah da Hidayah. Da kuma dawowar su AKEEL gida Nigeria wanda shine ma farkon Fara labarin Alhaji tallafy da iyalansa ɗin, fa sauran Abubuwan dasuka gabata garesu.


Hakana har sannan Jimmai tana cikin jiyya, kuma ko da wasa AKEEL da AQEEL ko AKEELA basa zuwa dubata, balle kuma ABBU sun ɗau zafi da ita sosai, Hakan yana sata tayi Kuka sosai,Babu bakin magana, kuma har sannan Babu duriyar Usman, yanacan yanacin duniyarsa da tsinke, ya cilla london Ƴan matan turawa kala kala yake mu'amala dasu, ga shaye_shaye da yakeyi na garari.


Shukrah kam dai a unguwarsu jimmai ta samu salama ba'a tsangwamarta dan har ta koma school, kuma tayi ƙawaye da yawa, su sun zata Daddy ƙaninta ne,ganin Suna kama, shi ma Daddy an sashi school ɗin yazama ɗan Saurayi kamanninsa da Usman ƙara fitowa sukeyi,yaro dai kam har sannan an rasa ubansa abu kamar al mara🤔


To ƴan amana anan na kammala tarihin iyalan Alhaji tallafy kuma in Sha ALLAHU page nagaba zamu ɗora daga indai muka tsaya.....






Shin AKEEL DA AQEEL zasu karɓi su

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login