Showing 60001 words to 63000 words out of 141223 words

Chapter 21 - RASHIN IYAYE Complete Document by Rabi'atu Muhammad Rabi'u Oum ARQAM.txt

Haka meenal ta fito taga lafiya meyasa yau umma bata tashesu ba, Saida kansu suka tashi!? Tunanin da takeyi kenan harta fito babban flourn gidan ai ganin umma da Babah tayi Duk a sheme Babu alamun numfashi!Babah kafafuwa a kumbure da hannu harda jini ma, itama umma hannun ya kumbura,uban Ihu Meenal ta saka! Wanda sauran kannen guda huɗu suka fito Suma suna ganin haka suka ka ma muka, suna ficewa waje. Dama maƙota tsammanin Hakan suke dan sunsan ƴan fashi kam sun jima a gidan bazasu ƙasa ɓarna ba, sai kuma ga ihun yara, Hakan yasa maƙota na kusa shiga gidan cikin tashin Hankali jin Meenal tana cewa wayyo umma da Babah sun mutu! Maƙota na sallallami suka antaya gidan zuciya da rai ba bugawa jin cewa Sun kashe Alhaji da Hajiya, saidai sukaje sukaga alamun suka sukasha a wajen ƴan fashin, dan haka suka tura komai baya na hulaƙancin Kawu isma'il suka sanyashi a mota shida Hauwa domin zuwa asibiti Hankali a tashe, aka bar su meenal a maƙota sunata Kuka abun tausayi.....








Muje next page Na tausayawa Hauwa da ƴaƴan fa🥲




Wayyo Kawu isma'il ɗinmu😢


Yanzu aka Fara wasan
Saura ƙiris mukawo tarihin Alhaji tallafy in Sha ALLAH nanne gaɓar daya dace kusan iyalan Alhaji tallafy ɗin dai sai kunfijin daɗi Akan tun baya, Zaku ruɗe wajen ganin bakin zaren yanzu kuwa kunsan wasu Abubuwan ai a Hakan, anyi sharar fage yanzu za'a kutsa cikin labarin kudai kubiyo
........


✍️OUM ARQAM ontop🥰
2/7/24, 4:28 PM - Rãbi'atou Aminou {Oum ARQAM}: *RASHIN IYAYE*
(Babbar musiba)




Daga *Al 'kalamin✍️ Rabiat Amin (oum Arqam)*


*08128131163*


✍️ Marubuciyar...
*Komai Nisan jifa* 📚
*Hakan ba kuskure bane*📚




*_____________*
MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION📚🖊️ *(M°W°A)*


'Kungiyar d'aya tamkar da dubu masu Nazari da Aiki da ilimi burin 'kungiyar a koda yaushe shine ta fad'akar ta Kuma wa'azantar ta Nishad'antar da masoyanta🤙
*_____________*


*PAGE THIRTY NINE 39*


"Ko da sukaje asibitin ba'a karɓe su kai tsaye ba sai da aka nemi ƴan sanda, saboda raunin da yake tare da Kawu isma'il sai jini yake Fitarwa,su kuma can maƙota ansamu wani munafikin ya kirawo ƴan jarida, Akan cewa ƴan fashi sun zo layinsu sun shiga gida ɗaya sunyi fashi har sun kai ga yiwa matar gidan da mai gidan dukan Kawo wuka,to kafin ƴan jarida harda na Gidan television ma duk suzo har anyi asibiti da Kawu isma'il,bayan sun gama jin ta bakin maƙota suka ɗunguma domin zuwa asibitin, lokacin ƴan sanda sun hallara dan haka suka ɗauki ɗan bayanan ƴan sanda kafin su ɗau hotunan su Kawu isma'il.
Duk wani taimakon gaggawa anbawa Hauwa da Kawu isma'il, inda aka samu tsagewar ƙashi a hannun Hauwa,abun yazo MATA da sauƙi, shikam Kawu isma'il karaya a hannunsa saboda lokacin da duwalle ya kawo mai duka da bindigar a kansu hannu ya saka ya kare, ƙafar sa kuwa akwai targaɗe a ɗayar, ɗayar kuma buguwa ce sosai dan haka gaba ɗaya ƙafafuhan a kumbure suke, ga raunuka abun ba bu kyan gani duk anmasa dressing ɗinsu, dai jiran farfaɗowar sa, dan Duk Abubuwan da Akayi Masa bai san anyi Masa ba, baya hayyacinsa saboda yakuma samun hutu yasa aka Masa allurar barci.


Ita kuwa Hauwa tun lokacin da aka Fara MATA gyaran hannunta ta farka,sai Kuka takeyi abun gwanin tausayi, dan haka likitocin suka MATA itama allaurar barcin dan ta samu nutsuwa, ba komai ne take sa Hauwa ku ka ba sai irin ha'incin da mijinta da muguntar da yayiwa marayun ALLAH ne, yanzu ya salwantar musu da kadarorin da Mahaifin su ya bar musu, Basu da tsuntsu Basu da tarko, lallai kaɗan ma yagani a rayuwarsa kam, kullum cikin nasiha da ban baki take Masa a kan sha'anin marayun ALLAH Amma bayaji har barazana yai MATA da duk sanda takuma saka Masa baki Akan harkarsa a bakin aurenta, shiyasa ta zuba Masa idanu, yanzu Baga shi ba kaɗan daga cikin Haƙƙin marayu ya fara bibiyarsa, kuɗin sa gaba ɗaya ya salwantar,ga bashin banki akansa, lallai kam Kawu isma'il kana ruwa fa waɗannan haƙƙoƙin ka kaisu ina ga na iyalinka.


______ zancen fashin da akayiwa Kawu isma'il yaje gidansu Hadiyyah,abunka da jini sun tausaya Masa sai Kuka suke da sukaji batun ance an Masa dukan Kawo wuka, yanzu haka ya na asibiti bai san a ina yakeba! Basu yi ƙasa a gwiwa ba wajen tafiya asibitin, jikinsu a sanyaye, ita kam Sa'adatu kadaran kadaham dan kuwa bata tausayawa Masa ko ƙadan ba,kunsan dai ABunda ke tsakanin sa da ita , ga kuma matarsa itama basa shiri ko ƙadan,ita haka tace ma ALLAH yasa sun kasheshi Daga shi har Hauwa ɗin, kuma anzo gaɓar da za'ayi fito na fito da ita dan kuwa ba bu ruwanta da wani fashi da aka Masa dole abiyata Haƙƙin ƴaƴanta da ke kansa a yanzu ba sai wani lokaci ba, dama tanada wannan a ranta sai ga shi kuma wannan ta ɓullo Muje Zuwa isma'il yanzu aka Fara wasan! Shure Shure baya hana mutuwa! Yanzu zan fito maka a kalata! Cewar Sa'adatu tana tafa hannayenta alamun ashirye ta ke.


_______ koda su Hadiyyah sukaje asibitin sannan Hauwa ta farka har Sannan sai aikin ku ka takeyi, tana ganin su Hadiyyah da Hidayah da kuma Khadija wani kukan ya ƙara kwace MATA, rayuwar waɗannan yaran itace abun tausayi ba bu uwa ba bu uba, gasu MATA sunason kulawa da ja ajiki, da tattali, Amma yanzu ƙanin mahaifinsu ya cucesu ya salwantar musu da dukiyar su,da ma yanzu komai dan kuɗi akeyi,koda ALLAH zaisa wani ya jiɓanci lamarunsu Amma ina sai addu'a kawai, sunga kukan da Hauwa take sai haƙuri suke bata "kiyi haƙuri maman meenal ƙaddara ce ta Riga fata,dukiya baƙuwa ce ALLAH zai sakawa kawunmu, kwana nawane zai mayar da dubunsu, ciwo kuma ALLAH zai yaye ma sa"cewar Hidayah ta na share ƙwallar idonta,
Jinjina kai kawai Hauwa ta keyi alamun taji, zuciyarta kuwa fal take da tausayin yaran, su yanzu haka tausayawa isma'il suke suna fatan samun sauƙin sa da dawowar kuɗin daya rasa, lalläi basusan me ya aikata musu bane, maybe suyi Masa tofin ALLAH tsine.


Daƙar Hauwa ta saurara da kukan da take hannu a kumbure, an gyara, ƴan jarida sun dawo sun ɗauki muryar Hauwa kuma ta Basu tabbacin abunda ya faru tun daga shigowar ƴan fashin.


Hauwa tacewa Hadiyyah da Hidayah suje gidanta su gyara MATA Abubuwan da ƴan fashi suka watsa, kuma akwai su meenal a maƙota suci abinci suyi wanka da Abubuwan da ba'a rasaba dan haka suka wuce Gidan Kawu isma'il. Sun tsorata da yadda suka ga ƴan fashin suka yi da gidan, sun barbaza kayan ɗakin Kawu isma'il komai filla filla, haka suka shiga gyara.


Lokacin asibitin ma Sha ALLAH su Bilkisu, Zainab da Asiya yayyan Kawu isma'il da kuma sulaiman ƙanin sa Duk suna asibitin abun tausayi sai tausaya ɗan uwan su sukeyi, Duk ƙannen Alhaji Ammar BN Yasir ne ai, Kowacce mace ta na Gidan mijinta da ƴaƴan su kuma, zumunci ne sai a Hankali tun bayan rasuwar Alhaji Ammar Kowacce ta janye jikinta sai a Hankali kawai, kafin ya rasu Amma kowa ƴaƴan Alhaji Ammar suje gidansa Amma yanzu shiru kakeji malam ya ci shirwa, shi kuma sulaiman shine Autan su Alhaji Ammar ne da ma yake Kula da sabgarsa tun bayan rasuwar sa kuma sai a Hankali Haka dai Hajiya Sakinah tadinga kula dashi,bayan rasuwarta kuma Babu mai kula shi ,kowa yaje gurinsa da buƙata sai yace halin rayuwa, haka dai Duk sukazo asibitin suna tausayawa ɗan uwan su isma'il wanda shi ba bu ruwansa dasu harkar gabansa yakeyi, dagashi sai ƴaƴansa,koda aka ba shi kuɗin marayun ALLAH sunsan za'a rina halinsa da kuɗi, to Amma mece ta su aciki? Ya kankane komai, kuma mutane suna tunanin zai Adana musu dukiyar su Amma ina!
Kawu isma'il ya farfaɗo ras Babu abunda zuciyarsa ko gangar jikinsa ya samu, sai dai cikin zuciyarsa sai ƙuna take Masa,sai hawaye yake yi na azaba da na baƙin cikin da yake ciki, yanzu ya zaiyi da rayuwarsa, dukiyarsa ya fece wai!? Lalläi akwai ƙura fa ba bu tsuntsu Basu tarko!? Lallai kam anzo gaɓar da zaice gaba ɗaya kuɗin marayun ALLAH harshi ƴan fashi suka kwamushe musu, in yaso za'a tausaya Masa ai, in yace ya ciyo bashin banki ne, mutane zasu taimaka ma sa ai, tanan kuɗin sa zai dawo, da ma batun kuɗin marayu kam yanzu basa gurinsa ƴan fashi su amshe,ire iren waɗannan zantukan Kawu isma'il yake saƙawa a ransa,duk da halin dayake ciki Amma mugun nufinsa bai barshi ba, dan haka da yayi shirun nan ƴan uwa sai Sannu suke Masa, abokan sa sunata zuwa dubiya da ALLAH ya sauwaƙa,su Hadiyyah sun komo asibitin Suma sunyi murna ganin Kawun su ya farfaɗo sai aikin Sannu suke Masa, haka ma ƴaƴansa su Meenal sunata aikin "Sannu Babah! Suna ta murna kuma ganin jinjina Babah da sauƙi.


Koda ƴan jarida suka dawo wajen Kawu isma'il, da jin ta bakinsa, ya Abubuwan suka wakana? Kuma wace irin ɓarna sukai Masa!? Ai Kawu isma'il saiya fashe da kukan makirci! Ya fayyace musu ƙaryarsa wacce da ma ya ƙware a cikinta, yanzu sun talauta ni sun cufeni, ba ma wannan ne abun ji ba, dukiyar marayun ALLAH da take wajensa, ya yi MATA ɓoye na ƙwarai har ita ƴan fashin suka sace shi kansa bai san adadinta ba, da a banki suke gaba ɗaya tsautsayi, ya sa ya karɓo ta ya Adana ta a gida, a she tsautsayi ne, yasa Hakan da fitar rabo, sai ya fashe da kuka!


Lallai kam kowa ya tausaya wa Kawu isma'il hatta ƴan jarida,da sauran jama'ar da suka saurari labaran a radio da kuma ma su kallo a tv, anata tsinewa ƴan fashi da tausayawa Kawu isma'il (lallai kam basusan ko wane shiba, bulus zaici kenan? Yaci dukiyar marayun ALLAH yaci bulus kenan?)


Su Hadiyyah da Hidayah ma sun tausayawa Kawunsu sunce ba bu komai dukiya ai baƙuwa ce ina Abby? Wanda ya bar musu dukiyar? To mema take amfana musu da dukiyar? Ya babbake ta ya cinye! Yanzu sai a wuta kuma, haka suka tattauna a tsakanin su da suka koma gida tsakanin Hadiyyah da Hidayah da Khadija, da kuma Farouk ɗan Sa'adatu.


Ko da Sa'adatu taji batun tsalle tayi ta dire Akan wallahi zai fito daga asibitin ne a kotu zasu rabu da isma'il,dole ya biyata Haƙƙin ƴaƴanta biyar bazata yafe ba, ƴaƴan na ai sun yafewa Kawu isma'il ɗin, nan kuwa gaba ɗaya ta ɗuɗdura musu Ashariya harsu Hidayah ɗin akan jin cewa sun yafewa Kawu isma'il, ɗin tace kuma dole ya fito da dukiyar marayun.


Hauwa Alhamdullillahi ta wartsake sai hannu dai, ambata sallama ita dan haka tai tafiyarta gida take jinya acan aka bar sulaiman yana jinyar Kawu isma'il, har Sannan Hauwa bata ce wa Kawu isma'il uffan ba! Haushin sa take ji ma, wannan ba bit ALLAH a ransa kwata kwata ji yadda ya sheƙawa ƴan jarida karyar cewa kuɗin marayu ƴan fashi ne suka ɗauke,a gabanta ya faɗi yadda yayi da kuɗin marayun ALLAH fa, Kuka kuɗin da ƴan fashi suka karɓa guda nawa suke!


Kawu isma'il yana lura da ita, sai sannan yatuna fa ya buɗe cikinsa a gabanta fa! Wajen ƴan fashi, subhanallah Amma yasan ai yadda zai ɓullowa al amarin, nata mai sauƙi ne.ita ɗin banza, shi yake aurenta ko itace take aurentasa.


Hakanma ƴan uwa su Goggo Aisya da Zainab sun saka ayar tambaya Akan abunda Kawu isma'il ya faɗawa ƴan jarida, Amma kuma ina ruwansa akwai ALLAH dai, ko gaskia ko akasinta isma'il ɗin ya faɗa.


Acikin wannan satin da abun ya faru ko wace kafar yaɗa labarai zancen fashin da akawa Kawu isma'il ake faɗa, anata tausaya Masa , ana ALLAH wadai da ƴan fashi, nan kuma ƴan siyasa da masu kuɗi suke ta kai harin tallafawa Kawu isma'il Akan abunda ya sameshi, daka me zai bashi jari zai biya Masa bashin da banki yake binsa kowa dai da inda zai tallafa Masa,kuma Duk ya na dawowa kunnan sa ran sa fes,jin cewa Abubuwan sunzo masa da sauƙi,asiri a rufe, shikenan an rabu(lalläi fans Kawu isma'il kwata kwata bashida imani da tausayi,gani yake yaci bulus Akan Abubuwan da ya aikata Hmm muje zuwa dai)




_______Ɓangaren su Zakiyyah kam Alhamdullillahi wajenta mukhtar ya kwana, shikam ABIE yana can wajen Bilkisu, tun daya gama murnar sa,Abban sa yace ma sa ai yanzu ya kwana a gidan ummansa ya kwana a wajen Ammin sa, ya ro kamar an gaya Masa, sai yace "Abbana jan dinga kwana da umma da Ammina ko ina! Ranar kuma da ya wuni wajen Zakiyyah da dare sai ya koma gidan Bilkisu, yabar Umman sa da Abban sa asa amarci kenan!🤣
Kwanan da sukayi Babu komai a cikinsa, sai Ban haƙuri da Zakiyyah ta dinga bawa mukhtar,Akan Abubuwan da suka faru, tana Kuka tana bashi haƙurin, kukan Zakiyyah da biyu na farin cikin dawuwar ta ga mukhtar da kuma yafe MATA da yayi,nan dai mukhtar ya dinga aikin lallashin Zakiyyah yana Kinga bakida lafiya.nace miki komai ya wuce fa! Idan ba haka ba kuma zan shiga fushi dake, so kike ciwon ki ya tashi, ne kinajin abunda likita ya faɗa Akan lalurar ki,
"kayi haƙuri Abban ABIE farin cikine ya sani Hakan ba komai ba,ai kaga dole naiwa ALLAH godiya, na nu na Masa cewa nayi taubatun nasuwa! Zakiyyah ta ƙarasa maganar da goge hawayen fuskarta, nan mukhtar ya matso gareta yana lallashi, lallai ALLAH sarki mukhtar yaiwa Zakiyyah halacci ta ko ina,Duk wani abu da tai Masa ya turashi baya, ya bata kulawa ya tausaya MATA halin da ta shiga, ita kam sai aikin godiya takewa mukhtar ɗin, a haka yayi kwana biyu a gidan nata, kuma jikinta alhamdullillahi za'ace, dama cutarta damuwar Rashin mukhtar, da kuma yunwa, da Rashin kulawa gareta, yanzu kuma Duk ta samu, Kunga sauƙi ya samu kenan, harta Fara Haske da murmurewa a kwana biyun da tayi da komawa gidan mukhtar ɗin, a ranar ne yayi nufin komawa gidan Bilkisu, ita kuma mar atussaliha tace Masa "Zaujin saleh maman ABIE tana buƙatar kulawa, kaga batada lafiya dan haka ka koma gidanta harta kuma samun sauƙi sosai, kaga yanayin ciwonta bayason kaɗaita, dan haka ma yafe mata kwana na harta kuma samun sauƙi, girki ma zan dingayi sai na aika MATA dashi, ta yi hutawarta yanzu ita abar a tausayawa ce! Shi dai mukhtar sai kallon Bilkisu yake jin maganar da takeyi, shin wannan wace irin mace ce? ALLAH yabashi ne, mai Hankali da tunani, a kullum burinta ta ɗorashi a kan hanyar dai dai, yanzu dai ga shi Duk Abubuwan da ya faru tsakanin sa da Zakiyyah, da Rashin mutuncin da tayi MATA farkon Auren su da Mukhtar ɗin, Duk ta tura baya ta rungumi Zakiyyah hannu bibiyu!
Matsawa yai kusa da ita da ma suna kan sofa ne! Rungume ta yayi tsam a kirjinsa Duk da haka da yayi da dabara ne, saboda halin da take ciki,hannun sa ya kai ya ɗago fuskar ta suna kallon juna!
"ALLAH yai miki albarka mar atussaliha, ya sauke min ke lafiya, ya haɗe mun kanku keda Maman ABIE, ALLAH ya Kaɗe fitina tsakanin ku, ya canzawa Zakiyyah halayenta, yadda Kika ɗauketa itama ta ɗauke ki ko sama da haka ma,tasan cewa yanzu ɗaya kuke, Hakan shine zai faranta min raina!"ALLAHUMMA AMEEN zaujin saleh in Sha ALLAH zaka samemu fiye da yadda kake tsammani ma, saboda yanzu maman ABIE ya haƙura da komai, ta yadda yanzu gaba ɗaya tayi Sanyi! Bilkisu ta faɗa tana dafa hannayen mukhtar da suke kan kumatun ta daya tallafe MATA su,
Hakane mar atussaliha ina fatan Hakan, Amma kuma zancen girki da kikace Zaki dinga yi, yanzu Kinga ke ma kina neman hutu fa!? Ki dai barta da dingayin nata kema kiyi naki ko!?
"Nidai ka barshi zan dingayi ka ji Zaujin saleh! Bilkisu ta ƙarasa maganar cikin shagwaɓa da nuna alamun rarrashi!
Mukhtar ya ce "shikenan Mar atussaliha ALLAH yai miki albarka, na yarda na Amince, dan innasan ban Amince ba zan sani ne, fushi ma ya isheni, ya faɗa yana lakace mata hanci da murmushi a kan fuskarsa! Yawwa nawan naji daɗi Bilkisu ta faɗa itama da murmushi a fuskar tata ta na kuma rungume mukhtar a Hankali.


Kamar yadda Bilkisu ta faɗa haka akayi mukhtar yana kwana gidan Zakiyyah yana ba ta duk wata kulawa,jiki Alhamdullillahi, da safe da rana da kuma daddare Bilkisu ta na girki itada Husna, har sannan ta na Gidan, saboda da ma ta zo ta taimakawa Bilkisu a aikin gidane,saboda yanayin jikinta, sai da taimako(bazan faɗi ko mene ba kwa gwani kawai, ƙawayen Zakiyyah balle kuyiwa ƙawata wani abu😊) wataran in sunyi girkin ta aika Husna ta kaiwa Zakiyyah wataran kuma suje tare, tun Zakiyyah na ɗarɗar da Bilkisu harta watstsake suna ɗan taɓa Hira abunsu, gwanin sha'awa, da ma ita Husna ai tasan Zakiyyah, tun kafin mukhtar ya auri Bilkisu ɗin,A haka Zakiyyah ta murmure sai da Mukhtar ya daɗawa Zakiyyah sati biyu sannan ya raba musu kwana, kuma Alhamdullillahi Kowacce tayi girki ta na aikawa da ɗaya itama, ga ABIE ɗinsu ko ina yananan sai murna da farin ciki yakeyi.


Ko da ƴan fashi suka shigarwa Kawu isma'il an hana a faɗawa Zakiyyah saboda halin ciwonta kar kuma wani abun ya kuma faruwa da ita, anfara samun kanta, shiyasa bata sani ba.sai da ga ƙarshe lokacin da Abubuwan sukayi tsamari zancen yayi yawane taji, koda taji bata wani tada Hankalin ta ba, ta kirasu Hadiyyah take musu zancen, sai sukace hakane saboda,katta ji wani fargaba yasa ba'a gaya mata ba, nan suka gaya nata abunda Aunty (Sa'adatu) tace zata kai Kawu isma'il ƙara, ALLAH ya sauwaƙa kawai tace, sannan tace ita fa da gaske ta yafe Masa, in ya cucesu kuma shida ALLAH, (fans da dane fa Zakiyyah zata ƙyale Kawu isma'il yanzu halin Zakiyyah na wani Rashin mutunci Duk babu tayi laushi, gaɓunta da Rashin mutunci da Rashin kunya Duk sun kwanta dama, lalläi Zakiyyah gidan Sa'adatu ya horaki🤣








**************






Alhaji tallafy ne yake zaune a ƙayataccen flourn gidan sa, yana kallon labarai a television, domin shi ma'abocin kallon labarai ne, anan yake cin karo da taimako ko wasu Abubuwan alkhair da zai tallafa da dukiyarsa ko jikinsa, dan haka baya rabo da Hakan, gefen sa Mommah ce, sai ɗaya sofa ɗin AKEEL da AQEEL suna

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login