Showing 126001 words to 129000 words out of 141223 words
Chapter 43 - RASHIN IYAYE Complete Document by Rabi'atu Muhammad Rabi'u Oum ARQAM.txt
haka ta daure taci abunda takeso tabar abunda bataso, har zuwa lokacin lunch shima Abinci wajen kala 10 akayi sai kace hauka,ita fa Sa'adatu tafara mamakin yawan ma'aikatan gidan aradu,Idan taga wannan bata kuma ganin Wata,sai da tafita wajen la'asar domin ta ɗan zazzaga gidan yaga ya yake,Anan mamaki ya kasheta gida iya gida,gajiya tayi da yawo ta dawo flour ta zauna tashiga tunnanin Rayuwa,wai ita Sa'adatu ce a Wannan aljannar duniya lalläi ne "Nikam naci sunana Sa'adatu sa'ar MATA domin nayi Sa'a ɗin,Haka ta ɓata lokaci har zuwa Sukayi dinner ƴaƴan suka tafi makwanci,itama kuma ta dangana ga aljannar duniyar Bedroom ɗin ta,tayi wanka zuciyarta Babu daɗin yau yini na biyu babu Ango,Lotion take shafawa taji An turo ƙofar ɗakin nata Babu excuse Tana ɗagowa kam Sukayi ido biyu da Alhajinta Hamza!
Cike da sassarfa ya ƙarasa gareta itama Tawowa tayi gareshi ku kwace irin sabbin Auren nanne Saurayi da budurwa da suka mallaki juna lokacin da suka yanke tsammani.
"Sai da Zuciyar Alhaji Hamza ta sosu tunowa da Yayi wannan zuƙeƙiyar Matar fa akwai wa'adi tsakaninsu,Amma da yayi tunanin irin ɗaukakar da zai samu da kuɗin da zai samu da ita sai ya basar!
"Haba Alhajina ina matsayin Amarya jiya fa rana tace Amma shine ka gujeni,nakira wayarka switch off meke faruwa? Cike da muryar kissa Sa'adatu ta faɗa!
"Aimun afwa Anam banji Daɗi bane jiyan, nikuma banson zuwarwa Amaryata Babu lafiya ne, yanzu bagashi nazo ba! Alhaji Hamza ya ƙarasa maganar haɗe da Tallafo fuskar Sa'adatu cike da ƙauna da so a zahiri a baɗini kuma tausayinta yakeji.
"Shine ya tayata ta kammala kimtsawa tai Shirin Barci,bayan shima yayi wanka haɗe shiryawar!
Sai kace wasu Ƙananan yara haka suka farantawa juna rai a Wannan daren.
"Amma me tun bayan da Alhaji Hamza ya samu nutsuwa da Sa'adatu ta Fara jin Wani mugun raɗaɗi a jikinta na Azaba kamar ana zuba MATA Ruwan zafi musamman daga ƙugunta zuwa tafin ƙafafuwanta,tun tana daurewa har tafara gazawa dan sai hawaye takeyi! Lokacin kuma Ita kaɗai ce ɗakin dan Suna kammalawa Alhaji Hamza ya shiga bayi ya kimtsa jikinsa ya fito ta shiga bayin, futowar da zatayi bata ganshi a cikin ɗakin ba.
Shi kam Alhaji Hamza ɗakin da Yake tsafinsa na cikin gidan yashiga,Bayan ya saka kayan tsafinsu,yai maganganun da zaiyi,sai ga wata mummunar Halitta ta bayyana,nan Alhaji Hamza ya zayyanewa wannan halittar cewa komai ya kammala Yanzu!
"Cikin wata murya akace "munji daɗi da wannan abu siiisooo Amma Wani Hanzari ba gudu ba Sai dai muyi amfani da jininta a koda Yaushe sadaukar da rayuwarta gaba ɗaya sai nan gaba,saboda yaranta Marayu Sannan akwai Wani sirri ajikinsu wanda mahaifinsu ya dafa su dashi,ga Abubuwan Alkhair daya aikata a rayuwarsa shine Yake bibiyar rayuwarsu, sannan kuma Irin Haihuwa ce dan haka Duk cikin data samu zamu ɗaukeshi kafin wa'adin da muka ɗibar MATA yacika,na ka sadaukar da jininta ga Alhaji gohliiiiiiiiiiii Yana zuwa Anan ya ɓace ɓat Mummunar Halittar shi kuma Alhaji Hamza ya Adana komai yacire kayansa ya mayar da wanda yashigo dasu ɗakin.
Haka Alhaji Hamza ya doso shashin Sa'adatu zuciyarsa da begen ƴaƴan da Aka Masa bushara dasu to amma Sadaukarwa ce ga aljani gohliiiiiiiiiiii,Shikam gohliiiiiiiiiiii Babu abunda nai Masa ba a duniya, ya iya bayar da Faɗima matarsa da Salim da salima ƴaƴansa uwa uba Inna da Baba ai kowa ƙarshene balle ɗan tayin da Yake Cikin mahaifa ( da Tuni Sa'adatu mushen gawarta xaije yagani,harda na yaranta to amma sanadin Hakan yasa abun yazo da ɗan sauƙi, Yanzu dai ga raɗaɗin da Sa'adatu takeji ajikinta kona menene oho?).
A Wannan Halin Alhaji Hamza ya tarar da Sa'adatu aciki sai kakkarwa takeyi,yana zuwa yace MATA lafiya? Nan tagaya Masa abunda takeji, shi kuma yace mata " ko dai dan an kwana biyu ba'a haɗu bane? Haka dai suka kwana tana tashan azaba acikin jikinta! Cikin ikon ALLAH Kafin safiya Babu raɗaɗin sai dai tanajin wajen kamar banata ba.
Komai na More rayuwa Sa'adatu tana samu gidan Alhaji Hamza yadda takeson rayuwarta. Haka take aiwatarwa,tuni su Hydar sun Fara zuwa school ko kunya aka musu transper daga wacce Abbu ya mayar Dasu.
Sa'adatu Kullum jinta take gatanan to kullum ana Shan jininka! Alhaji Hamza kuwa tuni ya ƙara kuɗi fiye dana da ya ƙara samun matsayi.
"Kulawar da Alhaji Hamza yake Bawa Sa'adatu ce ta damu mansurah bawai fa yadaina bin umarninta bane kawai dai tafiso taganta daga shi sai ita dan haka tai MATA mugun tsafi wanda dare ɗaya Sa'adatu ta Tashi bata motsi tana magana tana komai Amma ina Babu jikin motsawa!
Ga wata uwar Rama da tayi ta ban tsoro sai kace tsowuwa haka takoma,gwanin tausayi,Alhaji Hamza sai da yayi tsafin da ya shafe Zuciyar Duk Wani ɗan uwan Sa'adatu wanda zai tuna da ita balle har yazo gareta! A Wannan Halin Sa'adatu tayi ɓarin cikin na farko Ga wahala ga cuta, Ma'aikatan gidan ke MATA komai tana daga kwance, farouk da Haidar da Auta Hafsat kuwa Suna can sha'anin gabansu suje school suyi abunda sukeso a gidan Amma ko tuna uwarsu basayi(sharrin tsafi)......
_____HAJIYA BAABA A KANO____
"Tuni An kammala kammala gyaran gidan su Hadiyyah har Baaba tadawo Gidan,gidan Yayi kyau sosai gwanin burgewa,oga Hunaif da Zeenah sai murna sukeyi anzama kanawan dabo.
Zeenah kam ko sati batayiba ta gudu gidansu nada wato gidan Yaya Zakiyyah da Abbanta mukhtar tana ta Hidima da Twin's na'eem da na'eef har da Mammah ma, Yanzu anzama ƴan MATA ai ana secondary school ne js 2.
Shima Hunaif ɗan alƙawari gidan Aunty indo(Ƙanwar Ummu Rumana wacce ta shayarshi) Nan ya tafi wajen Abokin sha yarwarsa Abul khair,Aunty indo da mijinta sunyi murna hannu bibbiyu suka karɓeshi, sun tabbatar da ɗan halak suka riƙa ba shege ba dan kuwa gashi bai manta dasu ba,Duk da sunsha baƙin cikin kwaceshi da Hajiya sakinah tayi wancan karon, Yanzu sai labari.
"Anbar Baaba ita ɗaya a gida sai ƴar aikin da Abbu yakawota ta taya Baaba aiki,Aikuwa Khadija ta dawo gidan da Zama danta ɗebe MATA kewa meenal ƴar Kawu Isma'il biyo Khadija tayi Abinta,Ko kwana uku ba'ayi ba sai ga direban Alhaji Hamza dasu Hafsat da kayansu gaba ɗaya wai sun dawo gidan,idan akayi biki shikenan, Babu wanda yai Musu akace shikenan aikuwa sukaci gaba da Zama wajen Baaba sukabar Sa'adatu tana Shan azaba da gabza ita kaɗai Abinta..
_____MUTAN INDIA___
"Aradu bazaku shaida su AQEEL da AKEEL ba yadda suketa shining sunji gyaran angwanci na can ƙasar India,kyansu ya daɗa yawa ga gargasar nan ta jikinsu sai ƙalli takeyi,ni yasin ma sai naga kamar sun zama ƴan Indian ALLAH yasa su Hadiyyah su ganesu!
To maza ma sukayi kyau sosai Inaga mace Wato AKEELA ma sha ALLAH nace lokacin dana ganta,kamar ka sace ka gudu, An gyarata ciki da waje sai glowing takeyi,Ta doctor Najeeb kenan Sha Alwashi Likitan zuciyarta kamar yadda take kiransa.
Cike da kaya Niƙi niƙi suka antayo Nigeria kasarmu ta gado da shirin Bikin na kece raini, kowanne tsakanin AQEEL da AKEEL sai murna akeyi ana ta zumuɗin lokaci ya ƙarasa saura sati biyu kuma sati za'ayi anashan shagali.
Dan kuwa bikin ƴaƴan gata ne ƴaƴa ga Alhaji Ɗalhat Abdurrahman(Alhaji tallafy) ko ina sai zancen bikin akeyi tun daga kano har maƙoftan jahohin mu ke harda kashashen waje ma waɗanda Suke hurda da Abbu zasuzo gangamin wannan bikin dan ma An ɗaura Aure da daɗewa!Amma Abbu yace sai an kuma maimaita Wani saboda gata.
______AMARE____
"Tabarakallah ahsanul ƙaaliƙiin" haka nace lokacin danaje gidan Kawu Isma'il nai Arba da Hadiyyah da Hidayah tsabar kyaun da sukayi ga Wani arnen ƙamshin da sukeyi lalläi ne Wani gyara sai sudan, naga alama Zaton da su AQEEL sukayi ya Tabbatar na gyara me kyau dasuke Addu'ar za'a wa matan nasu Addu'ar ta karɓu,su kansu sunsan sun canza tun daga cikin su har waje,dan sun jima sa Fara Shan magungunan kara ni'ima wanda da jallar ƴaƴan itattuwa aka samar dasu irinsu rake,mazarƙwaila da kanunfari dasu kankana ne da sauransu bayan sun gama Shan maganin sanyi,sun haɗu fa komai yayi normal, yanzu Haka Shirin dawowa gida sukeyi dan Akan za'a yi shagalin bikin.
Ko da su AQEEL suka dawo sunso suzo gidan Kawu Isma'il wajensu Amma Aunty Hauwa fafur ta hanasu tace suyi haƙuri a kammala idan an kai musu su can su ƙarata,Dan gyaran da aka musu fatar jikinsu tayi santsi ga laushi kamar jikinsu kataɓa jini yayi tsartuwa! da ƙamshin da sukeyi komai ma iya faruwa idan suka keɓe dasu,shiyasa ta hana su zuwa,Duk da basuji daɗi ba haka suka haƙura da Umarnin Aunty Hauwa.
"Amma fa anashan waya Babu dare Babu rana,muyi vedio call inji AQEEL Inga me ake ɓoyemun da ba'aso nagani sai zuwa an kawomin ke gidana! Ita kuma Hadiyyah suyi vedio call ɗin haka zaita Santi da sururai da koɗa ta Akan kyan datayi,Yana inama Suna tare sai dai kawai tayi murmushi.
Shi ma AKEEL Hakan take gareshi anashan waya da vedio call ɗin, Hidayah tanashan Rashin kunya wajensa shi komai nasa Free yakeyinsa , ba kamar AQEEL da yake a baibai ba a wajen Hadiyyah take ganinsa kamar salihi nan kuwa yafi kowa Rashin kunya da komai ma...........
Muje next pages sun kusa ƙarewa in Sha ALLAH
✍️ALLAH
yakusa raba yari da ɓarawo RASHIN IYAYE yakusa gangarawa yaron da aka Haifa Fara typing ɗin Rashin iyaye ai Yanzu maybe ma ana aikensa😄😄 gashi har yanzu ban kammala littafin ba ALLAH yasa kafin na kammala kar yaron yafara Zuwa zance😅😅😅 Nikam oum ARQAM ALLAH yasa na kammala kwana kusa nahuta da fargabar typing kuma my Fans ku huta da zaman depon jiran update kuji shiru kunyi haƙuri dani fa sosai sai a slow fa🙏🙏
9/8/24, 8:08 AM - Rãbi'atou Aminou {Oum ARQAM}: *PAGE SIXTY SEVEN 67*
"Duk Abunda aka saka Masa lokaci zaizo ne sai dai ba'a saka ba,zara bata barin dami ni Rãbiat Wannan satin aka Fara bikin ƴaƴan gata AQEEL da AKEEL da AKEELA a gefe guda ma akwai ƴaƴan gata na Kawu Isma'il wato Hadiyyah da Hidayah dan gaskiya fa ya ƙuƙe sosai to bansaniba ko zaikai Alhaji Ammar musu wahala inda yana raye! Dan gaskia Kawu Isma'il fa Dukiya tayi kuka kawai wadaƙa yakeyi da ita kamar baijin fitar kuɗin!kamar a fanfo yake kunnawa suke zuwa.
Tuni Hadiyyah da Hidayah suka dawo gidansu na Ainahi suka zauna su da Hajiya Baaba,Babu laifi ƴan uwa sunyi kara Suna halartar bikin na kamar Lokacin bikin Zahra ba! Ko da Yake lokacin ai maraici yana kansu! Kuma dama ba'ayin abu dan ALLAH sai dai abun duniya ko ido(mahaifa guda Biyu ko Wani wanda ake girmamawa daya jibanceka) bansaniba ko dan ansan waɗanda su Hadiyyah suke Aurene? Ko kuwa dan idon Kawu Isma'il ne Yanzu?tunda wancan karon sheɗan yana kansa,yanzu kuwa ya sauka daga kansa.
Da kamun Amare aka Fara! Wanda Mommah ce ta haɗa Hadiyyah da Hidayah da Auta AKEELA aka kamasu a katafaren gidan Abbu wanda yasha kuɗi Babu wanda zaice ba sabon gida bane saboda tsa rashin da akayi an canza Abubuwa dayawa a gidan,sai ƙamshin sabon guri Yakeyi.
Wannan kamun Amare ya ƙayatar fiye da tunaninku Fans ku tambayi Rashin iyaye Fans group kusha labari irinsu Seerat da Haseena Aisha Sulaiman da MamaGee da mummy Waleed dan sune a gaba gaba harda Wani anko sukayi me kyau wai Duk saboda su kankaro ƙimarsu da mutuncinsu a wajen sai shiva da fita sukeyi anata hidima,wanda dama Yaya Zakiyyah ai Aminiyarsu ce dan bazance ƙawa ba,Duk Wani sha'anin bikin sa su akeyi aciki kai kace ƴan uwa ne😄 ni kam oum ARQAM ina gefe sai naga sun tafi nabisu a Baya,saboda ƙin Zakiyyah danayi abaya kar naje tana sane🏃♀️.
Ƴan uwa na nesa dana kusa Duk sunzo daga ɓangaren gidansu Abbu sai hada hada akeyi gwanin sha'awa,Jimmai da Shukhra Suna daga cikinsu ,kamar ba'a taɓa samun Wani saɓani ba tsakani kuma dama ALLAH haka yakeso idan ansamu saɓani a yafewa juna idan an nema kuma akoma mu'amala kamar yadda ake da ko fiye da haka ma Amma idan ba'a koma kamar daba ana gaisawa Hakan ma ba laifi bane.
Angwaye Ansha kyau sai wanda yagani a bikinnan dai AQEEL ya cire Glass ɗin sa dan haka babu wanda ya isa ya bayyana AQEEL ko AKEEL dan iri ɗaya sak suke komawa abunda Yake banbncesu ya ajiyeshi,sai Wani ƙalli suke gyaran Angwaye kam Yaji sai rawar ƙafa sukeyi Akan Haɗuwarsu da Matayen nasu a gidansu na Aure kowanne ƙiyasin da yakeyi kenan, musamman oga AQEEL dan sai a slow fa Ya kai geji shikam dama can haƙuri yakeyi Yanzu kuma yasan yanada dahir maganin matsalarsa, badon ma sharaɗin doctor ba ai da tuni yayi gaban kansa,to amma yanaso a kammala wannan biki yana cikin ƙoshin lafiya Abunsa,idan aka kawo Masa Hadiyyah in yaso acan komai sai ya faru yanzu kuma ai Babu batun Sharaɗin doctor da zaibi cin karensa Babu babbaka zaiyi.
Katafaren gidan Amare Ya ɗau harama komai yaji ma Sha ALLAH a gidan kai kace a India ne iri ɗaya sak yasin,sai dai idan ka kalli sauran gidajen wajen ba irinsu ba Suma fa amma sunyi Kyau Amma ginin namu irin na 9ja ne tsantsararre,yan unguwa sunsan waɗannan Amare da angwayen ƴaƴan gata ne ta yadda aka dinga shiga da kayan Abinci kamar ana zubawa a hamsha ƙin store wannan Duk aikin Kawu Isma'il ne yace su Hadiyyah bazasu shiga ba sai da gararsu.
Kayan lefen su Hadiyyah Nikam bazan iya magana akansu ba dan yasin sai nazata kasuwar kwari ta kano state ce yadda aka dinga shiga da akwatuna cikin gidan Baaba ba'a magana,Motocin da suka kawo kayan mallakin Amare ne inji Abbu,gwala gwalai acikin kayannan kamar Hajj Champ,iya su na hange saboda yadda suke ɗaukar idanuna sauran kayan kam tsoro sukaita bani,gashi su Seerat da Haseena Basu zo wajenba balle na raɓe ta jikinsu.
Haka aka cigaba da shagali da ƙasaitaccen wannan biki,Amare sun gaji da haɗuwa sai kace ba ƴan 9ja ba saboda tsabar kyau! dama can su masu kyau ne basuyi kwalliya ba balle yanzu kuma sunyi kwalliya,balle Amarya Duk muninta kyau takeyi balle kuma abu me kyau yashiga lalle,kai wannan Amare da angwaye kyau ne da kyau ya haɗu sun dace da juna fiye da tunanin me tunani, musamman Lallen da shukasha Ƙafa da hannun na asalin Sudan me haɗe da turaruka da wasu sirruka nasu na Sudan.
Ranar dinner wayyo ALLAH ni Oum ARQAM nera tayi Kuka na kaɗan ba abokan su AQEEL sun musu kara na gida 9ja dana India indai sukayi rayuwa,hakama su Hadiyyah ƙawayensu sun musu kara, Hajiya AKEELA ansha kyau sosai itada Angonta Doctor Najeeb,Suma iyaye da ƴan uwansa sunyi Masa kara,Ban gane ƴan Rashin iyaye Fans group ba gaba ɗaya saboda Suma sunyi ankon dinner ɗin,sai da na hangi seerat da ƴan kululluɓayan yara masu kama da juna guda Biyu tana tiri tiri dasu sannan na shaida ta Na'eem da na'eef ne sunyi masha ALLAH Amma Seerat sai yawo take dasu,ita Haseena Tana ta wajen Zakiyyah sai zuba abinci take tanaci ko koshi batayi MamaGee da mummy Waleed kuwa abun ba'a magana sai had hada sujeyi suyi nan suyi can da sunga Anbar juice ko ruwa zasu sakaye a jaka Aisha Sulaiman kuwa anacan ana tiƙa rawa kai taro yayi taro fa,Nima da bana rawa sai da Aisha Sulaiman ta rimbaceni bansan lokacin dana Fara takawa ba ina dansewa.
Hajiya Mommah ikon ALLAH Ansha kyau sosai,Ga Alhaji Abbu namu shima ba'a maganar kyau dama wajensa Su AQEEL suka ɗosano kyaun dana Ummul khair.
Har zuwa yau sati ana shagalin biki na kece raini Wanda yau ne biki ze kare,a yau ne Abbu yace za'a kuma ɗaurawa Ƴaƴansa Aure,aikuwa idan ka kalli ƙofar gidan Abbu da cikin gidan Duk girmansa da main faloun sa wanda yake yanawa da mutane a cike yake taf da mutane tun daga abokansa zuwa waɗanda ake zaman mutunci da al ummar gari waɗanda Abbu yakewa abun alkhair sun Nuna Masa zallar ƙauna da soyayyah,Duk wanda yaga waɗannan jama'ar tabbas yasan Abbu ɗan Arziƙi ne,Inaga komawa ga ALLAH yayi ai yadace dan Ma'aiki yace idan Mutane Arba'in suka sallaci gawar mamaci a kyautata Masa Zaton Rahmatullah.
Dubbai ko nace miliyoyin jama'a ne suka sake shaida Ɗaurin Auren Hassana(Hadiyyah) Ammar yaseer da Hassan(AQEEL) Ɗalhat Abdurrahman sai kuma Hussaina(Hidayah) Ammar yaseer da Hussain(AKEEL) Ɗalhat Abdurrahman Akan zunzurutan kuɗaɗe da Motoci har da gidaje ga kowannen su(karku manta Fans wannan ihsani ne kawai Abbu yabasu dan kuwa sadakinsu na farko da aka Ɗaura aure shine sadaki)
Wannan ɗaurin aure yayi Albarka sarakuna da gamnoni ga shugaban ƙasa da ministoci da kososhin gwamnati Duk sunzo bakajin komai sai tashin jiniya da algaita,Prime minister na kashashe daban daban sunzo kanon dabo saboda bikin ƴaƴan Alhaji tallafy.
Haka aka cigaba da shagalin biki bayan Angwaye sunje gidan Hajiya Baaba Ansha hotuna na kece raini abun sai wanda yagani su Seerat da Haseena sai shiga picture suke su a dole sai sunyi picture da double twins.
Har zuwa yamma lokacin da motocin Amare sukayiwa unguwar su Hadiyyah ƙawanya na jiran fito da Amare zuwa gidansu na neman tsira da taɓewa da neman neman aljannah da wuta(idan sunyi zaman ƙwarai su samu tsira da aljannah idan sunyi akasin haka su samu taɓewa da wuta ya ubangiji kabamu ikon yiwa mazajenmu biyayyah daidai gwargwado saboda mu samu tsira da aljannah ku barranta da taɓewa da shigar wuta🙏)
Sai sannan Twin's idanuwa suka raina fata sai Kuka sukeyi abun gwanin tausayi Amma ina a haka aka taitayosu aka fito dasu sai a waje sukejin cewa Kowacce motarta daban zata shiga kuma da Angonta a gefenta kawai! Sauran motocin zasu ɗauki Yan matan Amare da Danginsu Saboda suyi musu rakiya zuwa Gidajen Aurensu.
Jikin Kowacce Amarya ɓari yafara jin Wani sabon salon ɗaukar Amarya musamman Hidayah da tasan AKEEL ɗin ta baida kau da kai gareta indai sun haɗu saiya gwajilata,haka aka saka Kowacce a motarta bayan sunyi landing aciki divers suka ɗau hanya a nutse sauran motocin suka rufa musu Baya.
_____SA'ADATU____
"Tsafi gaskiyar me shi dan kuwa ko ƙadan Babu wanda ya tuna da ita daga ƴan uwanta har zuwa wannan shagalin biki da akasha na ƴaƴan mijinta ko nace ƴaƴanta ,ko ace ina Aunty su kansu su Hadiyyah sun manta da ita kwata kwata,koda yake tunda su Auta Hafsat dasu farouk suka mance da ita ai