Showing 114001 words to 117000 words out of 141223 words

Chapter 39 - RASHIN IYAYE Complete Document by Rabi'atu Muhammad Rabi'u Oum ARQAM.txt

madaidaiciya!
Gyaran murya Abbu yayi sannan yace " ya isa Hakan Isma'il kukan na menene kuma? Kasan halina da kake ciki ko? Baka da LAFIYA,dan haka ka saurara kanka,komai ai ya wuce ko? To ALLAH ya kiyaye gaba,ya karɓi tubanka!
Cikin shashsheƙa kawu Isma'il yace "To shikenan Alhaji adaina Amma abunne yazo mun a bazata,dole Nayi kukan murna,kullum cikin tsammani da tashin Hankali nake,na jiran sammaci daga kotu ƙarshe kuma a miƙani GIDAN gyaran Hali! Kawu Isma'il ya ƙarasa da share hawayen nadama!
" Komai ya wuce ai shiyasa ma nazo wajenka na gaya mata na biya maka,SABODA nasan hakan zai zame maka barazana ga lafiyarka!
Duk irin tattaunawar da su kawu Isma'il da Abbu sukeyi a kunnen Hauwa wanda tabasu guri dan kuwa bai kamata ta zauna Suna magana ba,jin Abunda suka tattauna cikin murna take gayawa innarta jin Abunda Alhaji tallafy yai Musu, wannan ai ba baƙon abu bane,a garesu sunyi murna Suma da fatan gamawa LAFIYA! Yanzu haka tun zuwansa Unguwar Duk da basaja yayi bai ɗauko bodyguard ɗin sa ba ,hakana ba motarsa me number ya ɗauko ba,da Yake akwai mutane a ƙofar gidansu Hauwa ɗin sai da WANI Mutum yaganshi Aikuwa " sai gashi la Alhaji tallafy ne ai ALLAH yaƙara lafiya da nisan kwana mai albarka, shine da ƙofar gidansu Hauwa yanzu haka ya cika da hayaniya da jiran fitowar ABBU, yanzu haka hayaniyar Har cikin gidan.


Again Abbu Yaiwa kawu Isma'il Albishir da mallaka Masa ɗaya daga cikin gidajen da ya mallaka da suke Na'ibawa, kai ma Sha ALLAH gidan yayi kyau sosai Babu Abunda kawu Isma'il ko Hauwa zasu je dashi na Amfani in ba kayan sawa ba,ya kuma Bashi jarin da zai cigaba da kasuwancin da yafi wayo Akai wato shaida Dabbobi yana rabawa mahauta Suna yankawa su Bashi kuɗinsa! Waɗannan Abubuwan Alkhair da Abbu Yaiwa kawu Isma'il Albishir dasu faɗar farin ciki ko godiyar da kawu Isma'il Yaiwa Abbu Alƙalamina ni Oum ARQAM yasin bazai iya rubutawa ba domin sai ya karye,ku kimanta my Fans.
Ganin irin ruɗewar da kawu Isma'il yayi tasa ABBU baiwa kawu Isma'il zancen Shirin Bikin Kece raini na su Hadiyyah ba yabari zuwa Monday ɗin Lokacin kawu Isma'il ya shiga nustsuwar sa,dan Abbu yanzu Yaga kawu Isma'il ya shigo shock da murna na kuɓutarsa daga tsaka mai wuya,Haka Abbu yabar gidan yanashan addu'a wajen iyayen Hauwa da Hauwa balle kawu Isma'il kuma, haka ya fita ƙofar gida daƙar yasamu ya bar unguwar SABODA cikowar mutane,kuma Saida yayiwa kowanne Alkhair, Alhaji tallafy kenan irin murnar da jama'a suke in sun ganshi abun ba'a magana ko sarki sai haka,bakomai yasa Masa Hakan b sai Alkhair da yakeyi, (ALLAH kabamu ikon aikata Alkhair a koda Yaushe kodan Ranar mutuwarmu ma samu shaidar Alkhair,yanzu kam nasan Abbu ko mutuwa yayi ai shaidar Alkhair ce zata isheshi kuma dama haka akeso🙏.......oum ARQAM✍️)








______Gidan Alhaji Gambo_____




"Cikin ikon ALLAH cikin Hajiya suwaiba yakai wata tara harda kwanaki ma,Abun gwanin tausayi Duk ta canza ta kukkumbura to ya ilayi Haihuwa ga wanda ya taɓa ma ya yacika balle baka taɓa ba ga jiki anfara ɗan Jan shekaru ALLAH yakawo dole aji jiki, Duk da abun ba'a nan yake ba.


Cikin ikon ALLAH yau ta Tashi da naƙuda Amma Abun yaci tura,sai Suma take tana neman gafarar abokan zamanta,itama Hajiya Sahura ciki fa ya girma wata bakwai fa! Amma da sauƙi ita SABODA itace ƙarama acikinsu dama Hajiya ikilima ce uwar Gida.


Alhaji Gambo dakansa ya ɗauki suwaiba zuwa asibiti tare da ikilima Anbar Sahura a gida.
Tunda sukaje Asibitin ake Abu ɗaya Haihuwa shiru, likitoci suka ce saidai ai mata C's karfinta ya ƙare ɗan cikinta ma ya galabaita, an shiryata zasu shiga ɗakin tiyata ta farfaɗo!
Alhaji Gambo sai Kuka yakeyi ya ƙara imani da tausayawa MATA, riƙe Hannun ikilima tayi cikin Kuka "ki riƙe Duk ABunda na Haifa ikilima na bar miki shi duniya da lahira,Nasan bazan Tashi ba,Alhaji ka yafemun ina neman alfarmar ku nemar mun gafara a wajen Sahura,hakanan Sa'adatu itama..... A haka dai aka gurgura gadon suwaiba zuwa ɗakin tiyata.
Cikin nasara Anyi sa'ar ciro Ɗa namiji ma Sha ALLAH!
An fito da Suwaiba daga ɗakin tiyata zuwa ɗakin wutu,
Ƴan uwnta sai rige rigen karɓar jariri suke,anata cewa ashe da rabo Suwaiba zata Haihu, hakama Alhaji Gambo sai barka ake Masa!
Amma ikilima da Alhaji Gambo jikinsu a sanyaye suke tun daga wasiyyar da Suwaiba take bayarwa, to amma ance tana lafiya,barci ta samu ne' shine ɗan hankinsu ya Kwanta, ba sosai ba Alhaji ya ɗauki ɗa yai Masa addu'a itama ikilima ta ɗauka sai da hawaye ya zubo MATA,tana tunani a Ranta ko itama tana da rabo?
Alhaji Gambo Gidan Sa'adatu Yaiwa tsinke nan ya gaya MATA cewa suwaiba ta sauka an samu ɗa Namiji, Yanzu haka Abincin yakeso ta girka zaikai Asibiti, saboda ikilima ce a wajenta,ita ma Sahura batajin daɗi ne itama saura ƙiris,Karku manta Fans Sa'adatu batasan da samuwar waɗannan cikin na suwaiba da Sahura ba,lokacin tana kan bala'in ta bata Kula Alhaji Gambo suyi maganar arziƙi balle ya sanar da ita"


Jin abunda Alhaji Gambo ya faɗa ai sai ga Sa'adatu ta miƙe tsaye da a Zaune take ko nuna da mutum a kusa da ita da maganar da Yake bata saurara ba da!
"To maci Amana wanda bai san mutunci ba ba ɗan halak ba kaikam uwarka da ubanka sunyi asarar Haihuwa! Har kana da bakin da zakamun maganar cewa suwaiba ta Haihu,Gani mayyah zan cinye ta ita da ɗanko? baka gayan ba sai naji Haihuwa ko? To baza Ayi girkin ba butulu watsatstse kawai"
Zuciyar Alhaji Gambo tayi baƙi jin munanan kalaman da Sa'adatu take jifan shi dasu,bakinsa a buɗe! Kafin yafara magana! Duk da yana cikin damuwa da firgicin farfaɗo war Suwaiba,saboda wasiyyar da ta dinga bayarwa,Amma Duk da haka sai da ya Kula ta
"Ke Yanzu Duk maganganun da Kika jefeni dasu ai kece Kika dace da Hakan,karki manta fa Ikilima Ƙawar kice Kika Aure ni,hakanan yadda akayi akai Aurenki da Alhaji Ammar ai na Sani,ga kuma Wani abun kunyar Auren Isma'il da kikayi Hauwa fa babu wanda yake tsakaninku sai ALLAH amma kikaci Amanarta Kika Aure MATA miji, da Yake yin bana ALLAH bane ba'a je ko inaba gayyar ta watse! Nima cika yaudareni na ɗauko wa kaina kara da kiyashi, Ko Alhakin Ikilima bazai barni ba dole akwai SAKAYYAH,tunda na aureki ban huta ba,Babu kwanciyar Hankali tare dani, Ballagaza kawaii!
Alhaji Gambo ya ƙarasa zancen da sauke ɓoyayyiyar ajiyar zuciya wanda ko Babu komai yau dai ya nunawa Sa'adatu bafa tsoronta yakeji ba,yana ƙarasa maganar ya ɗau hanyar barin gidan!
Aikuwa Sa'adatu jin kalaman da Alhaji Gambo ya yaɓa MATA! Tai kukan kura ta shaƙi wuyan rigarsa tamau ta murɗe kamar zata kaishi lahira!
"Ai komai zaka faɗa min butulu kufan wuta!matsiyaci sake ni Yanzu dan kuwa Zama Tsakanin ni dai ayau ya ƙare!
Idon Alhaji Gambo fa yayi jajur! Ina bakin magana ma se gumi Yakeyi? Daga can yai kukan kura ya warɓar da Sa'adatu gefe! Ya riƙe wuyansa ya kama tarin wuya!sai da yadawo Ɗan hayyacinsa tukunnah yace " ai basai kinmun haka da nasan cewa ke ƴar Akuya bace, kije na sakeki....na sakeki...na sakeki saki uku kenan! Banza ƴar wahala in Sha ALLAH sai Kinga SAKAYYAH Duk wanda Kika cuta sai ALLAH ya saka Mas......
Tun warɓar da Sa'adatu da Alhaji Gambo yayi taji zafi! Dan haka yana tarin dawowa hayyaci ta miƙe da ƙar da nufi kitchen ta ɗauko wuka taiyo kansa gadan gadan da ita! Bai ƙarasa maganar da zaiba ganin Sa'adatu da wuƙa a miliyan yabar gidan,Acan yabar motarsa.....
Sa'adatu hawayen baƙin ciki take! Lalläi ma ita Gambo zai wa haka! Ashe suwaiba da Sahura ciki ne dasu,in Sha ALLAH sai ɗan suwaiba ya mutu,ita kuma Sahura idan tazo Haihuwa ta rasu! Addu'ar da Sa'adatu takeyi kenan!


Alhaji Gambo Gidansa na Asali yakoma wajen Hajiya Sahura,koda Yaje ya sameta cikin zulumi da tunanin ko ya suwaiba an haihu? Dan Duk a kiɗime suka fice shi Alhaji da ikilima anan gida suka bar wayar su,
'Ya dai Alhaji fatan Suwaiba ta sauka?


"Ƙwarai dagaske an samu ɗa Namiji,an MATA C's, Yanzu ma naga bakijin daɗi Abinci za'a musu akai can Asibitin, sai kuyi keda su dela da mero(ƴan aikin gidanne)ya ƙarasa zancen zuciyarsa a cunkushe da baƙin cikin da Sa'adatu ta yarfa masa,
Alhaji fatan dai tana lafiya? Idan an kammala Abincin sai mu tafi baki ɗaya,naga idanunka yayi ja ne! Sahura ta ƙarashe maganar da duban fuskar Alhaji Gambo! Babu komai Sahura kawai dai Farko da tayi jinkirin Naƙuda ne nashiga damuwa Amma yanzu Alhamdulillahi ya ƙarasa zancen da kawar da damuwar da Sa'adatu ta jefa shi. Cikin ƙanƙanin lokaci aka kammala Abincin,Alhaji Gambo ya aika direbansa gidan Sa'adatu ya ɗauko motar da ya bari acan.


Acan Asibiti kuwa Suwaiba ta farfaɗo cikin ikon ALLAH aka nuna MATA ɗanta tai Masa Addu'a, sai kuma wasiyyakafin daga bisani Numfashinta ya ɗauke gaba ɗaya,Rai yayi Halinsa innalillahi wa Inna ilaihi rajiuuun ALLAH ya karɓi shahadar ki, A daidai lokacin da ƴan uwanta da Hajiya ikilima Suke kukan rabuwa da Suwaiba sannan su motar Alhaji Gambo ta danno cikin Asibitin,ai ganin Suna Kuka ba sai angayawa Alhaji Gambo abunda ya faru ba, Tashin Hankali da ba'a saka Masa Rana.


Faɗar Halin da Alhaji Gambo ya shiga da rasuwar Hajiya suwaiba ɓata baki ne,hakama Sahura ga ciki ajikinta ga Tashin Hankalin abunda yai ajalin suwaiba itama shine ajikinta,Ko itama Hakan ce zata faru da ita? Jininta yai mummunan Hawa, ga kumburi.
A haka aka ɗau Hajiya suwaiba zuwa gida aka sallaceta aka miƙa ta zuwa gidanta na gaskiya (ubangiji ya kyauta ƙarshen mu....✍️oum ARQAM)
Haka aka cigaba da karbar gaisuwar Hajiya suwaiba (haka dama rayuwa take ALLAH yayi suwaiba zata Haihu wanda take damuwa da Rashin haihuwarta to amma kuma gashi ALLAH yabata Haihuwar ashe ba itace zata raine shiba,saidai wata,Amma ai da Daɗi tunda za'a dinga tunawa da ita kuma tabar mai MATA addu'a)
Haka gidan yazamo shiru yaro yaci sunan Abbas kuma yana wajen Hajiya ikilima kamar yadda uwarsa tabata shi, sai fatan ALLAH yatayata riƙo,aikuwa ta riƙeshi Hannu biyu kamar ita ta haifeshi, Farko madara aka Fara Bashi daga ƙarshe Hajiya ikilima ta nemo magani tayi wanka Ruwan nono yakawo aikuwa tafara shayar da Abbas cikin Aminci(ALLAH sarki Rayuwa ikilima bada Haihuwa ba Tasamu Yaro daga sama,dama abun haka Yake ALLAH yasa idan da rabo kema ki samu naki)


Sa'adatu fa taji Haushi sosai ko gaisuwar Hajiya suwaiba batazo ba, kuma bataiwa Alhaji Gambo gaisuwa ba.


Su Hadiyyah sunyi baƙin cikin Rabuwar Sa'adatu da Alhaji Gambo,Duk da bata faɗa Musu asalin mene ya haɗa ba, Ranar da akayi gurmi basa Gidan gaba ɗaya,sun kaiwa Zakiyyah ziyara ne, sai da suka faɗawa mazajensu kafin su fita,dan kuwa lokacin shaƙuwa da soyayya a waya ta ƙaru tsakaninsu Duk da har yanzu Basu zo garesu ba,Suna shirin kawo musu ziyara ne, Haka gidan yakoma yanzu Babu Namiji.


Hajiya Baabah takoma Kaduna ita dasu Hunaif da Zeenah saboda school,ita data dawo sai ALLAH yakaimu bikin su Hadiyyah.






_____GIDAN MUKHTAR_____






Gidan zaman lafiya kenan! Tunda cikin Zakiyyah ya isa Haihuwa Bilkisu ta ɗauke MATA komai na Aikin da takeyi, wanda ita Zakiyyah ɗin ba haka taso ba,to amma ya ta iya Dole ta haƙura,saboda wahalar da takesha da Cikin tunda yai wata bakwai, yai Wani Irin girma ga nauyi, gashi mukhtar yace baison scanning ALLAH yakaimu Haihuwa anga ko menene ma! Idan Zakiyyah ta zauna daƙar take Tashi ga wata ƙiba data ƙara ta mamaki!
Yau Zakiyyah ta Tashi da naƙuda,karku manta dai Su Haseena da seerat da Aisha Sulaiman Bilkisu nurse ce ko? To dan Haka cikin nasara Ta taimawakawa Zakiyyah da taimakon ALLAH ya Haihu lafiya ta sulluɓo tagwayenta maza masu tsananin kama da juna kamar su ɗaya da mukhtar, faɗar murnar da wannan Ahali sukayi ɓata baki ne! Haka Zakiyyah da taimakon Bilkisu ta gyara jikinta! Haihuwar tazo MATA da sauƙi , hakama babies! bakin ABIE da yaƙi rufuwa Ganin an samo musu sabbin babies har guda Biyu,itama little sai murnar ganin yara takeyi dan kuwa akwaita da son Yara!
Kafin Rana tayi sai zuwan barka akeyi,hakana Hajiya Jamila(maman mukhtar) sai murna takeyi da godiya ga ALLAH ta dauwamar farin cikin mukhtar da daidaituwar zaman lafiya na matansa,itama tazo wajen ganin jikokinta biyu kyautar ALLAH............




Kawarku dai seerat da Aisha Sulaiman da Haseena an sauka saiku shirya zuwa barka




Wayyo Hannuna yasin nagaji hakanan Muje next page




✍️Oum ARQAM ce ontop 🥰
6/30/24, 8:56 PM - Rãbi'atou Aminou {Oum ARQAM}: *RASHIN IYAYE*
(babbar musiba)



Mallakar Rãbiat Ãmin {oum ARQAM}
08128131163


Marubuciyar
Komai nisan jifa
Hakan ba kuskure bane


____________________
*MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION M.W.A*
____________________


*PAGE SIXTY TWO 61*




Lalai ne su seerat da Haseena d Aisha Sulaiman an tafi kwari market da wambai market dake kano siyayyar kayan da zasu saka na sunan ƙawarsu Zakiyyah da gudunmawar da zasu baiwa ƙawarsu😊


______USMAN______


"Addu'a bata faɗuwa ƙasa a banza,Yau da gobe tafi ƙarfin wasa neman gafarar da yaje wajen Jimmai da Shukrah yana Kuka! Tasa har suka daina ƙin kulashi idan yana kukan Jimmai tana cemai "hakan ya isa ka tashi kai tafiyar ka, ALLAH ya yafe maka ya shirya ka! Sai shi kuma Usman ɗin yace "Ameen Maama" zuciyarsa tana Masa Daɗi da Hakan da da bata kulashi kuma fa!
Itama Shukrah idan yana MATA magana da neman yafiya sai tace Masa "Kadaina Kuka Yaya komai ya wuce ALLAH ya yafe maka"
Nan ma sai yace "Ameen little sis" sunan da Yake kiranta dashi tun a da.
Tun daga sannan kuma sai ya samu salama a zuciyarsa yakan shiga ɗakin Jimmai ya zauna duk da dai ba Wani Hira suke ba, Amma da da zaman gidan Yake Masa Zafi fa.


Tuni Shukrah sun kammala exam sai shirin fitowar sakamako me kyau, Shi kuma daddy yana zuwa school Abunsa,sai murna yakeyi Abbansa ya dawo(Ai haka Daddy yake cewa, dama yana damuwa da Rashin Abba a gidansu,kowa Abokansa yana cewa Abbansa yai mai kaza yai mai kaza Amma shi Babu, Yanzu kuwa yasamu Daddy shi yasa yake ta murna...Nikam oum ARQAM nace Daddy aikuwa Abbanka na gaskiya ne Wannan ko ba haka ba Fans)


Tunda Shukrah take zaman gida ba school sai Hakan yafara Bawa Jimmai tsoro,wai kar Usman yakuma aikatawa Shukhra abunda yai MATA baya(tsiyar aikata Zina kenan haka take ko mutum ya shiryu da zarar an ganshi da MATA ko ya keɓe dasu sai Ayi tunanin aikatawa yakeyi, ALLAH yarabamu da Aikata Zina) dan haka yau da ya shiga su Gaisa Jimmai take cemai "Nifa zaman gidannan dakai tsoro yake bani, dan haka ka samu wajen komawa,bazan iya zama dakai da acikin gidannan da Shukhra ba, tunda kai baka sa tausayi da Imani!
Jin furucin da Jimmai tayi sai da Usman yasa Kuka " illar zinah kenan maamah, Amma ni yanzu ko wata mace aka bani me zan MATA Maama,Ai sai mace halal ɗina, wanda nake tsoron me Aure na a Yanzu dan babu macen da zata zauna dani tasan bana Haihuwa,sai ya ƙara ƙarfin Kukan nasa!
Ɗa da mahaifi sai ALLAH sai da Jimmai taji Wani abu a Ranta da kukan Usman!
Ko me yafaru kaine kajawowa kanka ai!DUK wanda yabi son zuciyarsa ƙarshen sa Nadama ai, ALLAH ya yafe maka dai,zancen matar Aure kuma tunda da kuɗin ka bazaka rasa ba,ai za'a samu wacce tai auren Farko bata Haihuwa saika aureta ku rufawa kanku asiri(lallai ne ALLAH yasa asamu Nikam, Usman fa yana da matsala ta wannan fannin,kyanta yasamu mai Rauni itama).
Hakan ne Yasa Usman tun daga Ranar ya ƙauracewa zaman Gidan, sai Dare yake komawa gida,saboda Hankalin Jimmai ya kwanta!


Jikin Jimmai Alhamdullillahi Yanzu tana miƙewa ta ɗan ɗingisa,tana tafiya ba sosai ba,kuma tana kula Usman duk da ba kamar da ba!


Hakanan Shukhra itama tana kulashi sosai,bazadai su koma kamar da ba ai abun da kamar wuya!


Yo to dama Dukiyar da Mahaifin Su Usman ya bar Musu tun bayan rasuwar Baba mariƙinsu, da ɓacewar Usman yasa Umma ta Bawa Junaid!ɗan yayarta da take wajensa yanzu,Yake juya musu dukiyar, tasu,Amma Yanzu tunda Usman ya dawo kuma ya nutsu,umma take shirye shiryen dawo wa da Usman dukiyarsa Hannunsa,ta Shukhra kuma aci gaba da juya MATA ana samun riba.


Cikin Aminci Usman ya karɓi dukiyarsa, ya sai gida mai kyau yana laluban Matar Aure, Ya sai mota mai kyau ma.


Ya Gina ƙatuwar plaza yasa haya, hakanan ya buɗe manyan shaguna ya zuba kaya yana siyar da wayoyi,caza,power bank, earpiece, da dai sauran abunda yashafi waya, ma Sha ALLAH Anata samun costumer, ya buɗe Branch Biyu yanzu haka.


Takanas ya ɗauki Jimmai har Gidan Abbu neman yafiya!


Fa fur aka hanasu shiga gidan, Saboda tuni Malam sallau Abbu yai Masa alkhair da yawa ya bashi jari ya yalwata Masa,inda shine ai zai san Su Jimmai ɗin.


Securities ɗin bakin gate ɗin Gidan Abbu ,sun hanasu shiga,Saida Usman ya fito daga mota,A bakin gate ɗin Gidan, saboda horn daya damesu dashi ne yasa,suka leƙo daga cikin gidan, ko Alfarmar matsawa jikin gate ɗin ba'a bashi dama ba, yadingi musu magiya ko kallonsa basuyi ba daga ƙarshe ma suka koma cikin gidan.


Zuciyar Jimmai fal nadama ganin Abbu ya kuma tsantsara gidansa ya ƙara girmansa da gidajen maƙotansa ya Basu wasu gidajen, duk matakin NASARA da Abbu da dukiyarsa Jimmai ta sani, nadama takeyi ,ita burinta ma Abbu ya yafe MATA, saboda tayi nadama Yanzu.


Usman ni ba number Ɗalhat ba kaima Hakan,balle mu kirashi da Sauran ƴaƴansa ma,kawai mu juya gida,kaje can Foundation Ka samo Mana number ɗin sa in yaso muyi magana dashi,daga baya idan yasanar da securities ɗin bakin gate sai mu shiga!
"A'a Maama mu jira ko ALLAH zaisa Wani yafito a gidan sai mu samu mafaka.


Abbu yau Monday yana gida, fitowa yayi domin tafiya wajen Kawu Isma'il suje banki,kamar yadda suka tsara.


Yana fitowa sai ya tarar securities ɗinsa a bakin gate kamar Wani abu na faruwa!
Bodyguard ɗinsa suka taso zasu buɗe Masa mota, ya ɗaga musu hannu bada wanda zanje tafiyar sirri ce!


Securities Suna ƙarasowa cikin gidan Yake tambayarsu meke faruwa a wajen da suka fita?


Nan john ya zayyanewa Abbu yadda sukayi dasu Usman, ABBU sai ya shiga tunanin ko si wanene? Kawai ya yanke shawarar cewa a buɗe Musu su shigo? Sai ABBU yakoma cikin gidan ya fasa fitar! Sai ya gana da baƙin( Abbu yanada haka Baya hulaƙanta Duk wanda yazo nemansa)


Security ɗaya Yaje yabawa Usman damar shigowa da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login