Showing 15001 words to 18000 words out of 141223 words
Chapter 6 - RASHIN IYAYE Complete Document by Rabi'atu Muhammad Rabi'u Oum ARQAM.txt
in kunne yaji jiki ya tsira cewar baaba.....
Kwananau baaba biyu a Kano suka juya kaduna, saboda babu me jiyyar Inna acan, sai Ranar da zasu tafi Hunaif yadawo daga gidan Aisha ummansa, tun Ranar da sukazo baaba takaishi can, Kuma tana Gaya masa dama cewa Aisha itace ta raineka ta shayar dakai bayan rasuwar mamanka, sannan kadawo Nan wajena aikuwa Hunaif ya riqe wannan suna zuwa Kano yace "baaba kaini wajen ummana naganta(.. kujifa FANS yaro bai manta da alkhair ba..). Haka suka dinga Wasa da Abul_khair abokin shayarwarsa, Aisha da mijinta sunyi mamakin girman Hunaif yakusa yafi Abul tsayi ma, tunda dama shi dogone, Haka suka tarkata suka koma kaduna, kamar Aisha bazata bada Hunaif ba, kwanci tashi Babu wuya har Zakiyyah tayi Arba'in Hadiyyah ta koma gida.....
**************
Bari muleqa bangaren Hajiya sakinah man, ciwon qafa ne ya sakata a gaba, tun tana iya saukowa daga sama zuwa qasa harta daina duk abunda zatayi iya samane, idan qafarta ta tayar Mata da ciwo kamar bazata kwanaba, Kuma a wannan halin kawu isma'il sai yayi sati baizo ya duba data, sai Kuma taita kuka, tana tunanin Babansu Zakiyyah dashine da tuni hankalinsa ya tashi duk inda magani take zaije ya Nemo Mata, Amma isma'il ya zuba Mata ido, 'kafa ta fara kumbura ga qurji ne yafito a gwiwa ya zame Mata kamar wacce taqone gurin Babu kyan gani, anata jigilar asibiti, maganin hausa anayi Asiya da bilkisu da zainab y'ay'anta Mata sune suke wahala da ita sai Auta sulaiman,shikam isma'il Yana gefe abunsa sai yaga damar zuwa wajenta, Amma duk da Haka Bata gani tadinga masa addua kenan idan yazo sai kace shine yake mata komai,qafar Hajiya sakinah da tafara wari, abun Babu kyan gani, suna zuwa asibiti akace saidai a yanke, iya galabaita Hajiya ta galabaita Bata sanin abunda takeyi(... Lallai FANS duk abunda kakeyi dama ce kasamu yanzu ina iskancin Hajiya? Ina kud'in da take taqama dashi, Ina watsi da marayu da tayi yanzu keya amfana Mata?..) a halin haka aka yanke wa Hajiya sakinah qafarta ta dama, abun tausayi duk da farko banji tausayinta ba Amma rashin sassan jiki akwai tausayi......
Saida tayi wata d'aya a asibiti Ana Bata kulawa kafin a sallameta zuwa zuwa gida, liktoci sunce xa'a iya Mata qafar roba, kawu isma'il yace to zai duba yagani amma, kafin sannan kawai abata karfen da zata dinga dogarawa akansa,(... Hajiya tayi kuka da Ammar be da tun a Ranar zai bada kud'in ayi mata.. kad'an kika gani..)
Anata zuwa dubata a gida su Zahra Hadiyyah da Khadija da sauran yaran gidansu y'ay'an Kawu isma'il da y'ay'an Sa'adatu sunje dubata sunyi kuka ganin yadda Hajiya Takoma duk wannan fad'an Babu, jikinnan duk ta xazzage komai Yi mata akeyi, Babu qafa, rayuwa kenan Allah yakyauta........ Gadai Hajiya sakinah tafara girbar abunda ta shukawa d'an da da y'ay'ansa Dan taga qasa ta rufe masa ido............
**************
Babu abunda ya sauya dangane da Halin Alhaji na shaye_shaye, rashin mutunci kuwa Babu abunda ya fasa, shida kawu isma'il Babu jituwa yadinga zaginsa kenan, maci amana kacinye Mana kud'inmu gidan da muke ciki ma ka mallakeshi yakoma naka, mahaifiyarki ma ka aureta saboda cin amana Dan kaga Abbynmu ya rasu Allah xai saka Mana ne, abunda Alhaji kullum yake gaggayawa kawu isma'il keban, idan Sa'adatu tayi magana itama ya qare Mata " ai kema maci amana ce kika d'auki gidanmu da kud'in da mahaifinmu ya rasu yabar Mana kika mallakawa wannan banzan sai ya nuna kawu isma'il,bayan Haka saboda cin amana kika aureshi kikaci amanar Maman meenal(Hauwa yake nufi) wane irin Aminci be bakuyiba,Amma kika Mata hakan karki Kuma samun bakinki in Ina maganata da wannan maci amanar (kawu isma'il yake nufi) ire_iren kalaman da Alhaji yakeyi a duk Ranar datayi shaye_shayensa kenan, anan kawu isma'il zai masa duka, Shima Yana qoqarin ramawa, ita Hauwa kam Y'ar kallo ce, Sa'adatu Kuma saidai tashige d'aki abun tana damunta a zuciya, Zahra da Hadiyyah kuwa sai kuka suna tausayawa Alhaji irin wannan rayuwar daya tsinci kansa acikinta......
Yadda zaku fuskanta FANS baqin cikine da 'bacin Rai ya jefa Alhaji shaye_shaye, ta yadda Kawu isma'il ya kwace musu gida, dukiyars Kuma Wai Yana juya musu, da ribar ita ake musu wahala, ga auren da yayi na mahaifiyarsa itama Sa'adatu yanajin haushinta,tunda Abby yamutu Alhaji ya fara shiga damuwa, Allah sarki d'an marayan Allah wannan wane irin hakkine akan kawu isma'il da mahaifiyarsa Sa'adatu,fita wajen d'aya farane abokan banza suka ce masa indai damuwa ce Yana fara korawa zai barta, shi kuma dayake yarone Babu hankali Kuma maganin damuwar yake nema Babu tunani yafara kora maganin tari tun daga Nan Kuma Abu yayi gaba yanzu har wiwi Yana Sha, Kuma dai damuwar Bata barshiba Allah sarki rayuwa, kunji abunda Yasa Alhaji rayuwarsa ta lalace sanadin maraicin da Kuma halin mahaifiyarsa marar Imani Sa'adatu da kawunsa isma'il Maci amana,.......
Da Kawu isma'il yaga abun Alhaji Yana gaba shine fa ya jajirce akan cewa xai samo makarantar woro da tarbiyyah yakai Alhaji ya zauna acan, shikam abun nasa ya dameshi, kuji FANS kodai tonon sililin dayake masa ya dameshi nikam nasan badan ya samu tarbiyya bane......sai Dan ya bashi gurine..ya saka Ranar kaishi makarantar.
Itakam Hauwa tana gefe abunta tana cigaba da quntatawa Sa'adatu da habaice_habaice da makirce_makirce musamman idan Alhaji yagama tijararsa, to itama zata d'ora natane, tace" mutum yanzu yafara gani, tunda cin amana ne aikin mutum gashi a Halinki kin jefa d'anki a wani halin, ga y'ay'an abokiyar xamanki baki riqesu amanaba, kinci amana dayawa Sa'adatu bakiga komai ba, ire_iren maganganun da Hauwa take ya'bawa Sa'adatu kenan, dayake tasan batada gaskia ko tace ta tafasa balle sauke...
Keken d'inkin Zahra dama tun tuni ya lalace yanzu haka yaran Sa'adatu ne suke Wasa da qafar duk sun lallata sun karya, kafin ya lalace ma farouk da hydar ne suketa wanashi, Kuma Babu damar Zahra tayi magana, yanzu gashi ta iya d'inkin Amma Babu keken d'inki, ta tambayi kawu isma'il kud'in gyara zatakai keken yace Mata saiya samu, meyasa tabari Yara suka ka lallata Bata killaceshi ba, Shima sau nawa Yana gani anata wana keken batayi magana ba, sai yanzu to baxai bayarba, Haka Zahra ta haqura ta zubawa sarautar Allah ido,itadai bazatace ai Aunty tana kallo suke wasan dashiba bata hanaba, ko tace Ai Aunty zatai fad'a idan nai musu magana, ita Kuma Sa'adatu ko giyar wake Tasha bazata tambayeta kud'in gyaraba.....
A makotansu take zuwa tayi d'inkin, tafara kwarewa na Yara ake kawo Mata......
Da Hauwa ta fuskanci Keken d'inkin Zahra ya lalalcene, shiyasa take zuwa maqota ai kuwa kud'in gyara tabata aka kaishi aka gyara, sannan tasai Mata sabuwar qafar,domin wannan bazata gyaruba,kujifa FANS Hauwa tafi tausayawa su Zahra akan Kawu isma'il da Sa'adatu lallai rayuwa kenan, ai inda kayi alkhair a rayuwarka zaka samu Mai kula maka bayanka, koda wani bai kula suba,wani xai kula dasu, gashidai y'an uwan Alhaji Ammar hatta mahaifiyarsa da abokansa da Sa'adatu matarsa abokiyar xaman mahaifiyarsu Bata kula dasu yadda ya kamata sai Hauwa matar qaninsa Allah ka kula da bayanmu bayan qasa ta rufe Mana ido, Allah Yasa mu aikata alkhair a rayuwa kodan bayanmu a kula da ita tayi kyau
Muje zuwa next page FANS domin Miki mene xai faru Nan gaba wannan labarin akwai tausayi maraici cin amana da dai sauransu muje zuwa yanzu aka fara wasan............
*©️Rabiat Amin (oum Arqam ce)*
Domin shawara ko sharhi
*08128131163*
2/7/24, 4:28 PM - Rãbi'atou Aminou {Oum ARQAM}: *RASHIN IYAYE*
(Babbar musiba)
Daga *Al 'kalamin✍️ Rabiat Amin (oum Arqam)*
*08128131163*
✍️ Marubuciyar...
*Komai Nisan jifa* 📚
*Hakan ba kuskure bane*📚
*_____________*
MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION📚🖊️ *(M°W°A)*
'Kungiyar d'aya tamkar da dubu masu Nazari da Aiki da ilimi burin 'kungiyar a koda yaushe shine ta fad'akar ta Kuma wa'azantar ta Nishad'antar da masoyanta🤙
*____________*
*PAGE FIVETEEN 15*
Duk wani shirye_shirye kawu isma'il yayiwa Alhaji na kaishi makarantar horo da tarbiyyah ta matasa, Mai suna *TALLAFY CHARITY FOUNDATION(T°C°P)* Wanda dama an bud'e ta domin matasa irinsa masu shaye_shaye, acan Ana horar da matasa ilimi tun daga na addini Dana xamani aka koya musu sana'oi kala_kala Wanda idan angama Basu horo sun shiryu idan sun fito zasu dogara dakansu, lokaci kawai take jir karshen shekara yakusa, dayake haka tsarin makarantar yake duk shekara d'ai_ d'ai ake yaye matasa, Kuma cikin ikon Allah xakaga cajin wajen yaronka, duk abunda yake zai daina tun daga shaye_shaye, rashin kunya da sauransu Allah dai yataimaka Yasa akai Alhaji wannan makaranta a Sa'a Yasa shiryuwarsa ce zatazo...........
*TALLAFY CHARITY FOUNDATION{T°C°F}* wata Makaranta ce ta bada tarbiyya Wanda wani shahararren Mai kud'i ya tamfatsa ta, makaranta ce babba Wanda aciki Babu abunda Babu dakuna ne aka ginasu irin dai yadda tsarin Hostel na makarantun kwana take,Amma banbanci su shine ita kowanne gado guda d'ayane, akusa dashi akwai kwaba , sannan akwai taxara tsakaninsa da wannan gado sosai, haka tsarin d'akunan su suke, kowanne d'aki gadaje biyar_biyarne ne sannan akwai 'Bandaki acikinsa, akwai labulaye ajikin tagogi da bakin kofa gurin kwanansu kenan, wannan makaranta tana d'auke da dakunan kwana guda hamshin yakama Ana daukar mutane d'ari biyu da hamsin duk shekara....
Gurin d'aukar karatunsu na addini Dana boko, shima tsarin yadda ajujuwan makarantar boko yakene, akwai bencina, akwai allon rubutu da sauran abubuwan buqata.........
Sannan tsarin shiga makarantar kowanne yaro da iya karatunsa na addini Dana xamani inda ya tsaya xa'a had'ashi tare su d'auki karatu, kowanne ajin karatu mutum ashirin da biyar ne, makarantar tanada ajujuwa guda goma......
Farkon Kai yaronka wannan makaranta sai yayi tsawon sati hud'u shi kad'ai a d'aki d'aya saidai akawo masa abinci yayi wanka yayi sallah, kullum Kuma akwai Wanda zai shiga gurinsa Yana masa wa'azi da nuna Masa illar shaye_shaye da Kuma kwad'aita Masa zama yarona nagari iyayanka zasu saka maka albarka Kuma Allah zai maka albarkar, sai an tabbatar wannan nasiha yashiga jikinka, sannan xa'a fitar dakai daga wannan d'aki a kaika d'aki Wanda kuke ku biyar_ biyar Haka tsarin wannan makaranta take zakuji wasu abubuwan a gaba, duk wannan tsari na makarantar Babu ko sisi da iyayen Yara suke kashewa illah kawai xasu dinga kawowa yaransu kud'in abinci duk wata, da kud'in sabulun wanka Dana wanki sai Kuma matsalar rashin lafiya, Amma sauran duk Wanda ya assasa wannan makaranta ya d'auke nauyin akansa,sai kawowa d'an ziyara duk sati, saboda kwantar Masa da hankali ma hadda y'an uwansa ake zuwa suna jansa ajiki basa nuna Masa qyama kamar yadda suke suna Masa lokacin Yana kan shaye_shayensa a gida...............
Sa'adatu taji dad'in wannan makaranta da xa'a Kai Alhaji, suma su Zahra da sauran y'an uwa duk sunji dad'i d'an uwansu Mai hankali xai shiryu ya nutsu yakoma kamar yadda yake da, lokacin Abby Yana raye yaro Mai hankali da nutsuwa, Allah yabiye bakunansu marayun Allah..........
**************
Bari muleqa Wajen Zakiyyah muji wacce wainar take toyawa......
Tun bayan Arba'in da Haihuwarta Babu abunda ta rage na halinta da yawo da Tara maqota,yau tana can gobe tana can, Allah yabata yaro Mai haquri bashida rigima ko kad'an,wata Rana ma har kulleshi a gida takeyi idan Yana barci taje yawonta ta dawo, wataran ta sameshi ya farka Yana kuka ko Kuma Yana baccinsa, har gida Hajiya Jamila (mahmah) tazo taiwa Zakiyyah fad'a akan yanzu fa tayi hankali ta girma d'ane da ita yakamata tayi xamanta acikin gidanta, metake nema a wajen, ta rungumi Y'ar qanwarta ta zauna tare da ita tana koya Mata ayyukan gida tunda macece, kamar dai Zakiyyah taji, Haka mahmah ta fito ta koma gidanta.........
Zakiyyah tana da socket a kusa da jikin gadonta, saboda tsabar iskanci da rashin hankalin Zakiyyah saita dinga jona heater ajiki acikin karamin bukiti, ta d'ora akan gadon idan ruwan ya tafasa saita juye, tanada kettle a kitchen fa, Kuma tanada heater a bayi,
Tafison tayi amfani da wannan heater d'in, tun bayan haihuwar *ABIE* mukhtar yace Mata yanzu dai saiki daina kunna heater akan gado, Kinga akwai yaro Kuma shi yanada juye_juye kar watarana ki d'ora ruwa ki mance kin kwantar dashi.kinacan wani aikin yazo ya qone, Kuma Yana girma Yana wayo, shima ABIE yanada gadonsa, Amma Zakiyyah a kowanne kwantar dashi takeyi, indai ba da daddare bane Bata kwantar dashi akan nasa gadin, da Rana tafi kwantar dashi akan gadon nata, aikuwa dai Zakiyyah Bata jiba,Bata fasa d'ora ruwan akan gadonba,Kuma Bata fasa kwantar da ABIE akaiba,banda ma rashin hankali saiki daina kwantar dashi akan gadon,tunda bazakiji maganar daina d'ora ruwan zafi akaiba sai muce Allah ya tsare.........
Zeenah anata zuwa makaranta anqara girma yanzu zatakai 6years abunta gata itama akwai jikin girma, irin Mai riqonta , Allah dai ya rabata da halinta, tanason ABIE sosai taitai Masa Wasa Yana dariya, aikuwa Zakiyyah haka takeso idan ta Bata shi tai ficewarta Ranar da Babu nakaranta ta kullesu a gidan, Zeenah ansamu abunso aita Wasa dashi, ABIE yaro Mai haquri ya gado Mai sunansa........
Akwai makaranta yau Zeenah anacan, Zakiyyah bayan taiwa ABIE wanka, yakama barci,ta kwantarshi akan gadonta, itama saita jona ruwan wankanta a heater ta d'ora akan gado, tana Dora ruwan kuwa sai yawonta yaciyota, ta kulle gida tayi ficewarta FANS meke faruwa ........
************
Kawu isma'il fa Hulaqanci sosai yakewa Sa'adatu (Aunty) Haka kawai Babu gaira Babu dalili, Kuma tanata Dana sanin aurensa(... Wanda Ashe dama ta qarkashin qasa tabiyo kawu isma'il akan ya aureta,asiri tayi Masa,ta qulle bakin mutane yadda Babu Wanda zaice wannan Auren Bata kyauta ba saidai ace Allah ya Sanya alkhair..) yanzu kika fara Dana sani Sa'adatu,itakam Hauwa tana gefe abunda duk Hulaqancin da Kawu isma'il yakewa Sa'adatu itama Babu abunda ta fasa na habaici da hulakancin da takewa Sa'adatu,saima gaba , Kuma har sannan Hauwa tana bawa su Zahra Hadiyyah da Khadija kulawa sosai kamar y"ay"an cikinta, Zahra karatu yayi nisa, itama Hadiyyah suna shirin fara jarrabawar shiga aji shida na babbar secondary,Anzama y'an Mata sosai,kyau sai qaruwa yakeyi iyayi ya qaru da gwalli, saidai maganarta ta ragu yanzu maqerin budurci yafara qera Mana ita anfara hankali...........
Hajiya sakinah saidai muce alhmdllh tunda aka Mata Aiki aka yanke Mata qafa, shikenan lafiya tai Mata sauqi, yau da lafiya gobe Babu lafiya, gurin da aka yanke Mata wajen gwiwar ya kumbura suntum Yana zubar da ruwan mugunya, abun Babu kyan gani,kullum cikin kuka take duk Wanda yaje dubata saitayi kuka, duk ta sauke makaman yakinta, an tattaro Mata y'ay'an Alhaji Ammar Tai musu addua,ta nemi yafiyarsu akan,rashin kulasu datayi,sukam su Hadiyyah sunce Babu komai Babu abunda kikai Mana Kaaka Allah yabaki lafiya,cuta ba mutuwa bace,ita Kam Hidayah sai a waya sukayi da Hajiya sakinah Babu halin zuwa akwai makaranta, duk da hakan Hidayah tace idan akayi Hutu zatazo ta dubata, Hajiya sakinah dai sai shi musu albarka take,har Hunaif aka Bata suka gaisa, Hajiya sakinah taita kuka, data tuna abunda Tai Masa Yana hannun qanwar Mamansa ta daukeshi takaiwa su Zahra shi, ta tozartashi, Ashe dai yaro yanada sauran Rayuwa, Haka Hajiya sakinah take cikin ciwo, Kuma kawu isma'il yabada kud'in qafar roba xa'a Yi Mata,sai qafar tafara kumbura tana ruwa Babu damar ayi qafar,saidai jiran agani idan Allah Yasa ta warke, Ana kaita asibiti kullum a wanke qafar, asaka Mata magani, Kuma a gida anayin na hausa .. sai muce Allah yatakaitawa Hajiya sakinah wahala ya karbi tubanta ya yaye Mata.........
**************
Bangaren Hidayah mutanen kaduna itama abun Haka yake kamanninsu da Y'ar uwata yaqara fitowa sosai nidai bansan wacce tafi wata gwalli da iyayi ba,hakam bangaren tsarin jiki qirarsu d'aya da Yar uwarta tagwaitakarta Hadiyyah, dama itacan shiru shiru ce Hidayah sai abun ya qaru mutane da yawa suna cewa ita Y'ar hulakanci ce Bata kula mutane, jinta take kamar Y'ar wata da wani, Allah yaso munsan asalinta da bama anan garin takeba,Kuma Wai ance iyayenta sun rasu marainiya ce Kuma twin's be Wai, Haka y'an makarantar su Hidayah suke idan sun xauna sun dinga xancenta kenan, Allah yakyauta basusan cewa Haka halinta yakeba, Amma qawayenta sunsan halinta ba Haka bane saika zauna da ita zakasan cewa Haka Allah ya halicceta,shima Hunaif yanata girma Masha Allah an sashi a makaranta tun daga boko har islamiyyah akwai qoqari....
Babba tana zaune lafiya da jikokinta idan kawu isma'il ya Aiko musu da sabulu da kud'i ta kar'ba idan Bai turo ba Kuma ta haqura ta dogara da Allah, kud'in makaranta Amma wannan yasan Dole ya bayar duk lokacin da aka nema, shugaban makarantar dama yanada number d'in kawu isma'il d'in da lokaci yayi yake tura musu ta account..........
Muje zuwa FANS in Sha Allah next page zamu kammala tarihin wad'annan ahalai na Alhaji Ammar bn Yassir, Wanda yanzu labarin yafara bamuyi komai ba, Allah yabani ikon rubuta abunsa zai amfanar da Al uma Baki d'aya kuskure Kuma ubangiji ya yafemun azijancine na Dan Adam...
Nice dai taku Rabiat Amin (oum Arqam)
Domin shawara ko sharhi ku tuntubi wannan number *081281331163*
2/7/24, 4:28 PM - Rãbi'atou Aminou {Oum ARQAM}: RASHIN IYAYE*
(Babbar musiba)
Daga *Al 'kalamin✍️ Rabiat Amin (oum Arqam)*
*08128131163*
✍️ Marubuciyar...
*Komai Nisan jifa* 📚
*Hakan ba kuskure bane*📚
*_____________*
MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION📚🖊️ *(M°W°A)*
'Kungiyar d'aya tamkar da dubu masu Nazari da Aiki da ilimi burin 'kungiyar a koda yaushe shine ta fad'akar ta Kuma wa'azantar ta Nishad'antar da masoyanta🤙
*____________*
*PAGE SIXTEEN 16*
Duk wani cuku_cuku na tafiya TALLAFY CHARITY FOUNDATION kawu isma'il yagamawa Alhaji dakansa yakaishi makarantar tare da rakiyar Hauwa da sauran y'an uwansa, Babu Sa'adatu acikin Wannan tafiyar Dan lokacin kawu isma'il tsanar dayayi Mata abun yayi gaba, ko magana basayi Mata,Kuma abun Yana damunta sosai har kuka tana shiga d'akinta tayi, sauran Yara kuwa Babu abunda ya raga musu na hidimar da yake musu.......
Kamar yadda tsarin makarantar yake haka akayiwa Alhaji, Wanda kafin tafiyar Saida akasha fama dashi yanata zag_zage da rashin kunya ga kawu isma'il da Sa'adatu uwarsa......
Bayan tafiyar Alhaji TALLAFY CHARITY FOUNDATION ne Sa'adatu masifarta ta tashi ta inda take shiga batanan take fita ba, ta tasarwa kawu isma'il da tijara kala_kala take Masa akan ya dawo Mata da gidanta da sukayi musanye aidama ga gidansa Nan Daya Bata har yau Bai cika Mata kud'inta ba, to tafasa Haka kullum takewa kawu isma'il, to dama shi ya tsaneta bayason ganinta a tare dashi, zagi da cin mutuncin da take masa ya fara isarsa, maha'inci mayaudari Maci amana, ka kar'be min gadon y'ay'ana Kuma daga baya kazo kana hulakantani to Auren nagaji dashi ka sakeni Kuma kadawomin da gidana, ga gidanka can ,tun danaga take takenta dama hayar danasa acikin gidan daka bani