Showing 117001 words to 120000 words out of 141223 words

Chapter 40 - RASHIN IYAYE Complete Document by Rabi'atu Muhammad Rabi'u Oum ARQAM.txt

motar sa,lokacin har Usman ya yanke tsammanin shawarar maama a barin wajen,dan haka cikin. Rawar jiki ya tashi motar ya cilla hancinta cikin gidan bayan security ya zuge musu gate?


Sai da Usman yai parking inda ya kamata, sannan ya riƙo Jimmai ya taimaka MATA ta fito, ya riƙeta a hankali! Da taimakon ma'aikatan gidan suka shigar dasu falourn baƙi na Gidan,Mai aikin Mommah ta sanar da ita akwai baƙi, Babu Wani ɓata lokaci irin na wanda suka ci suka tada kai, Mommah ta fito, zuwa taga baƙin ta, cikin fuskar alamar bata gane ko su Wanene ba suka Gaisa, Jimmai ta yaba da Matar da Ɗalhat ya Aura! Dan haka Jimmai tace "Jimmai ce ƙanwar Mahaifiyar su AQEEL (kuji fa Haseena da seerat da Aisha Sulaiman,dama tasan da Hakan)
" ALLAH sarki Sannu ya jikin kuma naga bakya jin daɗi ma,Cike da jin nauyi Jimmai ta amsa da yawwa!
Usman ya gaisa da Mommah cikin girmamawa,itama ta Amsa (Mommah ta gane Usman tunda Jimmai tai bayanin wacece ita)


Mommah waya ta Kira Abbu ta shaida Masa ko su Wanene suka zo, zuciyar Abbu kamar zata fashe tunu Abubuwan da Jimmai tai Masa Amma daya dingi addu'a sai yaji abun yafara sauka,


Dan Haka yaƙaraso falourn cikin zati,ya samu kusa da Mommah ya zauna fuska Babu yabo Babu fallasa, Jimmai ta gaisa da Abbu kafin tafara Kuka tana neman gafararsa "ka yafemun Ɗalhat naga ishara a duniya Duk sanadin Alhakin ka dana ƴaƴanka.......nan ta kwashe komai daya sameta bayan barin gidansa da abunda yasamu Usman ɗin shima ta zayyanawa Abbu,mene baƙon Abbu abinda ya sameta da Usman ne kawai bai saniba dan haka Abbu yace "ALLAH ya yafe Mana gaba ɗaya, kinga illar cin amanar zumunci ai, ƙarshe Halin da kikaso jefa ni kinga ni akanki, Yanzu me gari yawaya ace ɗan ki yaiwa ƴar ki ciki ta haihu ai abun da kamar wuya! ALLAH dai ya kiyaye gaba kawai,"Kinga dai Yanzu Duk ƙula ƙullar da kikayi na rabani nida Amininsa Ammar komai ya warware, yanzu haka ƴan biyunsa ne ke Auren su AQEEL wanda tun a wancan lokacin aka Ɗaura, Yanzu shirin tarewa Akeyi, Da Duk wata nasarori daya samu saida ya zayyanawa Jimmai,itama AKEELA ALLAH yakawo mata mijin Aure, Doctor Najeeb dai ta sanshi ai, da tare za'a haɗa Auren danasu badon shi AQEEL ɗin da Yake da matsala ba!
"ALLAH sarki ƴaƴana Suna Inane in nemi yafiyarsu, musamman AKEELA da AQEEL jimmai ta faɗi cikin kuka da nadama haɗe da face Majina!
Shima Usman cikin kukan nadama ya zuba gwiwa a ƙasa yafara neman yafiyar Abbu! ABBU ya dafa kansa yace " ALLAH ya yafe Mana gaba ɗaya, Halin mahaifiyarsa nason zuciya yajefa ka a Wannan Halin tashi ka koma ka zauna a kujera!


Mommah again kiran AKEELA tayi a waya tace tazo babban falour, minti Biyu AKEELA bata ƙaraba sai gata,
Kusa da mommah ta zauna! Cikinta a sanyaye dan kuwa tagane Usman da maama Jimmai!
Tana ƙarasa Zama Jimmai ta Fara Kuka da neman gafarar ta,shi ma Usman haka!


Sai da AKEELA tai Kukan tuna irin uƙuba da azabar da Usman ya gana mata,Amma sai tayi tunanin ai komai ya wuce Yanzu,yada tada Usman da Jimmai tabbas sunyi nadama, ta tuna gudun tozarcin miji idan ya sameta ba a budurwa ba to ALLAH yai MATA liɗifi likitan da ya MATA aiki yasan komai, yasan iftila'in daya sameta Hakan data tuna ne yasa zuciyarta ta ɗan yi Sanyi! Tace " ALLAH ya yafe Mana gaba ɗaya AKEELA ta faɗa muryarta da alamun kuka tana ficewa daga faloun.


Zuciyar Jimmai da Usman tayi Sanyi jin cewa AKEELA ya yafe Musu duk da bata kallesu da idan kulawa ba!


AQEEL da AKEEL sun fita basa Gida Sannan,cikin ikon ALLAH Kafin tafiyar su Usman sun dawo, mommah ta kirasu a waya sukazo falour Suma nan dai Usman da Jimmai suka nemi gafarar AQEEL cikin kukan, domin kuwa shine babban wanda aka cuta, a maka ƙazafin zinah da ƴar uwarka uwa ɗaya uba ɗaya! Ai da ciwo!
AQEEL yana gama jin abunda su Usman suka zo dashi bai ja Wani lokaci ba yace " AlLLAH ya yafe Mana gaba ɗaya idanunsa sunyi jajawur!Alamun ran ƴan maza ya ɓaci(Nikam Oum ARQAM nace ALLAH Yasa kar ciwonshi ya dashi) yana faɗa ya fice daga falourn,shima AKEEL Ganin Halin da ɗan uwansa yake ciki bin bayansa yayi yana tausayawa Jimmai da Usman ganin Halin da suka koma,dan ma baisan abunda Yake damun Usman bane shiyasa,da lalatar da yayiwa Shukhra.


ALLAH Sarki Mommah Saida tasa akawa Jimmai da Usman girki duk da bakinsu Babu Daɗi an ɗago da ɓacin rai ,haka suka baro gidan! zuciyar su fal farin cikin yafiyar IYALAN ALHAJI TALLAFY..






______KAWU ISMA'IL___




Tun bayan da Jimmai da Usman suka nemi yafiyarsa shikam yabaro gidan, saboda zuwansu banki shida Kawu Isma'il ɗin.




Kawu Isma'il kam yana shirye Abbu yana aka gaggaisa, Sannan Abbu yasako zancen Bikinsu AQEEL!
Kawu Isma'il kam cike da ƙasƙantar da kai yace ' aini Alhaji bani da tacewa Duk sanda aka tsayar da maganar Bikin ina maraba da Hakan!
"Ai ba haka bane Isma'il haƙƙinka ALLAH ne baka, dole mubaka Haƙƙin" Abbu ya faɗa haɗe da murmushi yana duban Kawu Isma'il ɗin!
To Shikenan nikuma na wakiltaka Akan ƴaƴan nan Duk abunda Kayi daidai ne, to Shikenan in Sha ALLAH nan da wata huɗu masu Zuwa za'a Sha BIKI,abunda Yasa ma nakai wannan lokacin su AQEEL zasu koma makaranta su ƙarasa exam ɗinsu banso su tafi tare ne,gwanda idan Anyi exam ɗin idan zasu koma nan gaba sai su koma gaba ɗaya ,akuma cigaba da Karatu,Suma su Hadiyyah da Hidayah ɗin sai a nema musu admission acan!
"Ma Sha ALLAH Alhaji ubangiji yasaka da alkhair yasa afi haka ALLAH yiwa yaran albarka!
"Ameen Ameen Abbu ya faɗi.


Sannan ABBU yasako zancen dukiyar su Hidayah!sun tattauna akan Dukiyar su Hadiyyah dake Hannun Alhaji tallafy ɗin, da tsawon lokacin da tayi a wajensa juya musu akeyi, Yanzu haka ma ansamu riba mai tarin yawa, an buɗe musu Account ana zubawa.


Daga ƙarshe Abbu yace shi fa zai dawowa da Kawu Isma'il ɗin Dukiyar dan shine a haƙƙu daya riƙe musu,tunda su mata ne yawanci, ALHAJI kuma bai mallaki hankalin kansa na,hakana sauran ƙannensa,aikuwa Kawu Isma'il harda rantsuwar sa Akan shi ya wakilta Alhaji tallafy Akan dukiyar !
Ba yadda Abbu ya iya haka ya karɓa, ya Kira direbansa dake waje a waya,ya shigo da fayal da rubutun komai na dukiyar, dan haka Abbu yasa Hannu shima Kawu isma'il yasa hannu ( Aikuwa Dukiyar su Hadiyyah Babu gyara Babu zago ALLAH yatayaka riƙo Abbu)


Sai da aka kammala komai tukunnah suka ɗunguma zuwa banki,Nan ma Duk abunda za'ayi akayi Abbu Duk yabiya kuɗaɗen da ake bin Kawu Isma'il haɗe da saka Hannu, anan ma Saida Kawu Isma'il yakuma Kuka,wanda bana komai illah na farin ciki,Da Abbu yakuma cewa "in Sha ALLAH nan da kwana uku wadnesday zaka koma sabon gidanka! Sai farin ciki haka Abbu da kawu Isma'il suka rabu cike da farin ciki.


Kwana uku tsakani kuwa kawu Isma'il shida ƴaƴansa da Hauwa da rakiyar ƴan uwanta suka koma gidan da Abbu ya mallakawa Kawu Isma'il ɗin, Wani ƙarin Armashin har dasu mota a gidan! Gida gari guda KOWA sai Santin gidan Yake, yafi wancan gidan nasa nada nesa ba kusa ba!
Hadiyyah da Hidayah sun ƙara ƙaunar Mazajensu jin irin tagomashin da Abbu yaiwa kawunsu!wanda yazama abun tausayi a yanzu, Hakanan su Zahra,da Zakiyyah mai jego sun Kira Abbu sun Masa godiya,kai Alhamdulillahi Kawu Isma'il fa anfaso gari,acikin satin yakoma harkar sa ta cinikin Dabbobinsa, mutane sai mamakin Hakan suke, Abokan kasuwancinsa nada sun dawo Harda sabbi ma, dayawan jama'a Suna tunainin ta Ya ya Isma'il komai nasa yadawo,sai kuma su tuna da sirikin Alhaji tallafy ne fa,yaiwa Wasu ma balle sirikinsa.




_____H+H= HASSAN(AQEEL) & HASSANA (HADIYYAH)______




Sun wata irin shaƙuwa da juna a waya,in aka ce muku AQEEL ne Yake zuba zance da surutu a waya saika ƙaryata,to amma ga zahiri ni Oum ARQAM ina gani,to dama ita Hadiyyah gwanace a fannin surutu dan haka ko ajikinta buɗe Baki take sunashan Hira,Anan kuwa AQEEL ya Tabbatar cewa Mrs parrot ɗin da yaso itace matarsa,ai sai murna a zuciyarsa,
"Halawatiy"(Lallai Larabci ) nayi murna fa, Kinga abunda na zata shine! amma da yasin wannan bakin sai yasha Hukunci a wajena! Dole ya horu ya koyi surutu! Amma Yanzu tunda baki abun magana ne ai Shikenan ni Haka nakeso!idan kina mun magana ji nake kamar na janyo lokacin da ya rage Mana akawomin ke gidana,Gani gaki saboda murna nayi alƙawari Ranar bazan iya Barci ba saboda murna! Wannan uban zureren zancen AQEEL yake fitowa dashi daga bakinsa kamar ba Shiba!
Murmushi me sauti Hadiyyah tayi wanda tasa AQEEL yajishi har cikin ɓargo da jijiyarsa sai da ya lumshe idanu, haɗe da cije leɓan kasa, shi kaɗai yasan Abunda yajeji a Wannan lokacin(kunsan dai AQEEL basaina faɗi muku ba)
"Ajnabiy" kana bani mamaki fa idan kace inda bana magana sai kaiwa bakina hukunci to ta yaya? Hadiyyah ta ƙarasa zancen da sugar shagwaɓa!
'Hmm ALLAH ya taimakeki bake bace da Kinga yadda zan ladabtar dashi ɗin! Yanzu ma idan surutun ki yamun yawa nasan ta yadda zan ladabtar dashi! Ya ƙarasa zancen da magana ƙasa ƙasa yana makirin murmushi!


Hakanan a Kullum suke ɓata lokaci a waya suna Shan soyayyar su,Wataran idan Abun yai yasa sai AQEEL yacewa Hadiyyah "Halawatiy kunna data muyi vedio call Please inason ganinki, ai kuwa Hakan zata kasance online ɗin Suna kallon juna Cike da so da ƙauna Suna hirarsu,idan yaga AQEEL ɗin yafara sauka daga layi ta kashe Data ɗin ta,tana mamakinsa, lallai ita Hadiyyah ALLAH ya haɗa ta da gamon ta da Ganin AQEEL Babu sauƙi fa, daga Ganin fuskar ta Alhalin jikinta Akwai kaya hakana kanta da kallabi saiya Fara, sakin layi!
Haka sukeshan soyayyar su idan AQEEL yace zaizo,sai tace ita dai a'a tana tsoronsa ne ma,idan yazo daga ita sai shi sai ALLAH kuma yasan matarsa ce ai akwai matsala cewar Hadiyyah,to amma yace mata Dole zaizo ne, shi da AKEEL su rakasu ayiwa Yaya Zakiyyah barka,su gano takwarorinsu, "nima ALLAH yabamu twin's ɗin nan da shekara me zuwa ko wata tar... Tanajin abunda AQEEL yace Hadiyyah tai saurin kashe wayar cike d Alkunya tana mamakin Ajnabiy ɗin ta.






_______H+H=HUSSAIN(AKEEL)& HUSSAINA(HIDAYAH)______




Suma ɓangaren su tun kan aje ga tarewa a gidansu da ƙudurin AKEEL na koyawa Hidayah surutu har tafara Koya ma a waya,idan Hidayah tana waya Abun zai baka mamaki, Duk da babu abunda zaka zaka tsinta a Hirar ta ta Amma tabbas zakasan waya takeyi, kuma surutu take zubawa Babu ƙarya!
AKEEL fa ansamu aiki,shi surutu ba wahala yake Masa ba! dan Haka kullum cikin waya yake da Hidayah,yana kasheta da kalaman ƙauna, kunsan dai irinsu Hadiyyah masu shiru shirun nan idan suka samu soyayya sunfi uwar kowa baje kolinsu (gadai AQEEL)
AKEEL yana kasheta da kalamai tana Masa shagwaɓar data saba!
"Kinsan ALLAH "My Final choice" (Nan kuma turawane) inason Rashin maganar nan taki, hakanan nakeso ni nakoya miki surutun, Amma ace mace taita zance ai banso nidai! AKEEL ya faɗi haɗe da Dariya a ƙarshen zancen!
"My only one Kenan"kai kuma da kake zancen kamar lalataccen fanfo kuma fa,ni nace me da kake damuna da surutun? Da shagwaɓa Hidayah ta faɗa
"Ai so nake ki koyi surutun tun kafin akawoki gidana, idan yaso dakinzo cigaba zanyi wajen koya mikin!


"Ai shikenan nidai nace bazan koya ba!


"Lalläi ma yarinya yanzu me kike idan ba surutun ba?
"Amsa dai nabaka Akan maganar da kamun,haka fa aketa dambarwa Tsakanin Hidayah da AKEEL Akan ita bazata koyi surutunsa ba, shi kuma yana Dole saiya koya mata.


Sunata Hirar ta soyayya, Yake ce MATA za suzo shida AQEEL su rakasu ayiwa Yaya Zakiyyah barka kafin Suna, dan haka ma ta tanadar masa Abun daɗi, dan yanason yaci girkinta tun Yanzu yaji ya yake!


Indai girkine "my only one" baka da matsala dashi har abunsha ma zan tanadar maka!
Sai dai fatan kara cikani da surutun ka a Zahiri!


"Karmu cika juna da surutu dai ai kema me surutun ce yanzu cewar AKEEL,cike da Farin ciki da Annushuwa suka rabu a wayar.




Hadiyyah tacewa Hidayah "sis kinji wai zasuzo mu rakasu ayiwa Yaya Zakiyyah barka" Ea Nima haka Yake gayan Yanzu cewar Hidayah!
Nikam ina tsoron zuwan AQEEL wajena fa sis! Hadiyyah ta ƙarasa zancen da zaro idanuwa tana kallon ƴar uwarta!
"Wane irin tsoro kuma sis keda zakiyi murna?
Baza ki gane abunda nake nufi bane sis,ni nasan ko wanene AQEEL sai a slow fa daga Gani baida Haƙuri cike da karaya ta ƙarasa zancen!
"Lallai kin haɗu da gamonki Nika Babu ruwansa zancen girki yaimun ma, kuma bai taɓa nunan Hakan ba"cike da murna Hidayah ta ƙarasa zancen
"Lalläi ma sis kinmanta wai da AQEEL da AKEEL Duk ɗaya ne, kowanne da Halin sa dai Shi AKEEL baida tone tone ne,shi kuma AQEEL Baya barin magana acikinsa,koma dai me Zaki ce Yasin AKEEL ba Ruwan sa!
Ai shikenan sis zamu gani ALLAH yakaimu lokacin cewar Hadiyyah tana tagumin neman mafita tsakaninta da mijinta AQEEL,ita kuma Hidayah tai shigewarta ɗaki.........




Wash Hannuna..............yasin nagaji hakanan Muje next page




✍️oum ARQAM ce ontop 🥰
8/10/24, 12:06 AM - Rãbi'atou Aminou {Oum ARQAM}: *RASHIN IYAYE*
(Babbar musiba)






Mallakar Rãbiat Ãmin {oum ARQAM}
*08128231163*


Marubuciyar
Komai nisan jifa
Hakan ba kuskure bane
*___________________* *MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION (M.W.A)*
*__________________*


*PAGE SIXTY THREE 63*




Alhamdulillah my fans I'm back again🙋‍♀️,Ina godiya sosai da addu'oin ku gareni naji sauƙi sosai, ALLAH yabar zumunci🤝 muci gaba da gashi❤‍🔥






"Kamar yadda su AQEEL suka faɗi hakan ta faru,kafin Suna da kwana Biyu sukazo wajensu Hadiyyah dan zuwa yiwa Yaya Zakiyyah barka!
Bayan su tawo da kayan jarirai da sauransu niki-niki kamar za'a buɗe kanti harda tagomashin gudunmawar Abbu.
"Karkuso kuga rawar ƙafa wajen Twin's su AQEEL yau za'a gana da Ababan ƙaunarsu! Ɓangaren su Hadiyyah ma abun haka Yake kowa sai murna yakeyi,to dole ai wannan shine farkon Haɗuwar fuskokinsu a matsayin ma'aurata kuma masu son junansu!
Ko da su Hadiyyah suka gayawa Auntynsu(Sa'adatu) zancen zuwan mazajen nasu cewa tayi "mecece tawa aciki? Matsalarku ce! Ni dama na matsu kuyi kuyi ku tafi can ku ƙari tsiyarku,nagaji da wannan iskancin na waya cikin dare Duk abunda kukeyi ina sane daku!(Fans ko Sa'adatu tamance Suna da Aure ne?) Kaji dashi kiji da abunda Yake damun ki ƴar wahala.


"Kwalliya sosai su Hadiyyah suka Sha, kamar ka sace su ka gudu, Yasin babu ta yadda zaka ganesu abun gwanin burgewa! Sai kamshi sukeyi,Kowacce zuciyarta cike da tarrabanin wace tarba zata samu wajen angon nata, musamman Hadiyyah datasan halin nata mijin.




AKEEL da AQEEL Suma An Sha gayu Suma kamar ka sace ka gudu, yau kwalliyar ta musamman ce garesu naga alama! Ga shinnan yasha gyara ga saje da gemu sai ƙyalli yakeyi gwanin burgewa,gargasar nan ta Hannu ta kwanta luf-luf sai ƙyalli, musamman AQEEL da wannan glass na fuskarsa ya ƙara Masa kyau shine banbancin dake tsakaninsa da ɗan uwansa Kenan!
Mommah tace"ma Sha ALLAH Twin's ɗina kunyi kyau Sosai, ALLAH ya haɗa fuskokinku da alkhair!
Shikam Abbu sai tsokanar AQEEL Yakeyi ganin sai wata firirita Yakeyi Akan wannan futar wai shi me MATA! mutumin da yake Wani shan kamshi Kwanakin baya! "Ikon ALLAH Mommahn AQEEL Kinga Ɗanki sai rawar ƙafa yakeyi zuwa wajen ƴata ko kunya ni Ɗalhatu! lalläi ɗan ki Bashi da kunya! Aikuwa an kunne AQEEL sai ya noƙe alamun yaji kunya ya kuma ɗaure fuska! Abbu da AKEEL dake gefe suka sa dariya! Mommah tace "haba Abbun AKEEL ai wannan maganar ta wuce da jimawa, please abarmun ɗana ya wataya!itama cike da dariyar ta ida maganar, cike da nishaɗi dai su AKEEL suka baro gidansu kowanne zuciyarsa kamar Auduga tsabar fari!
Bayan Abbu ya yankawa AQEEL warning Akan Hadiyyah tunda yasan halinsa,kuma ya tunasar dashi batun likitansa! Sai naga jikin AQEEL ɗin yayi Sanyi da tunin da Abbu yamasa!
Ƴan nema kowanne mota ya ɗauka guda,Abbu yace su hau ɗaya Ilu driver y kaisu Amma ina sukace dakansu zasuje Babu matsala,Sai da Abbu yai Musu Addu'ar Alkhair sannan kuma a irin motocin da Abbu yake fitar sirri a irinta suka ɗauka,idan ba haka ba daƙar su AQEEL zasusha da mutane dan kuwa Tallafy dai ba ɓoyayye bane balle number ta motarsa.
Suna zuwa unguwarsu Hadiyyah sukayi parking a Layin, kafin AKEEL ya Kira Hidayah a waya cewar sun iso,sai da Hidayah ta leƙa ɗakin Sa'adatu Again ta sanar MATA sun iso bata daddara ba,aikuwa cikin tsawa tace "naji sai akayi Yaya kuma! Taja tsaki
Hydar suka aika domin yai Musu iso cikin gidan,
Ɗakin Sa'adatu sukaiwa tsinke kamar wata ɗan daren goma Sha ɗaya haka Suke gwanin burgewa, sai da taji Wani dum tsabar ganin kyaun Twin's Duk da tasansu lokacin ƙuruciya Amma yanzu ai ba wasa ba,tana Wani shan kamshi ta amsa musu, sannan suka ajiye mata salala, suka baro ɗakin zuwa hanyar waje,yar banza da Yake taga kuɗi sai tace "ya haka kuma AKEEL ku shiga Suna ciki ko gaisa Mana, sannan In yaso sai ku tafi gidan Zakiyyah ɗin ko ruwa ai kwa Sha!
Cikin sinne kai suka amsa da to 'kafin suyiwa falourn su Hadiyyah tsinke.
Duk maganganun da sukayi su Hadiyyah naji, jin cewar su shigo falourn Kowacce sai jikinta ya Fara karkarwa, Hadiyyah ɗaki ta gudu ita kuma Hidayah ta maƙure a faloun cike da kunya.
AKEEL yana shigowa faloun ya wurga idanuwa yaga mutum ɗaya kunsan shi dai sai cewa yayi "ina ɗayar kuma? Mu da zamu ganku tare kamar mu haka gwanin burgewa! Shi kam AQEEL yana tsaye bai magana ba!
Ni dai wannan bansan Kowacce ba,da nasan wannan Hadiyyah ce Babu shakka cikin ɗakin nan zanwa tsinke dan kuwa nasan Hidayata tana ciki! Cike da dariya da tsokana yayi maganar haɗe da nuna Hidayah dake gefe, wanda tunda taji yayi magana tagane kowanene Aku bakin magana ne wato AKEEL mijinta!
Yanayin yadda Hidayah ta share su kanta a ƙasa ne tabbas yasa AQEEL ganeta dan indai Hadiyyansa ce dole ya shaida,bai ce komai ba ya dumfari cikin ɗakin dake gefen sa wanda yake da yaƙinin Hadiyyah tana ciki,ganin ɗayan kofarsa na kulle ga key nan ajiki.
Hakan da AQEEL yayi ya tabbatarwa da AKEEL cewa yatafi wajen Matarsa ne Wannan itace tasa,ai Babu wata wata AKEEL cikin sassarfa ya tafi wajen Hidayah! Gaba ɗayanta ya ɗago ta daga zaunen da take Cikin muryar raɗa yace "wato ko aina

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login