Showing 87001 words to 90000 words out of 141223 words

Chapter 30 - RASHIN IYAYE Complete Document by Rabi'atu Muhammad Rabi'u Oum ARQAM.txt

wajenta sukayi, Fuskarsu cike da tausayi ga ƙanwar ganin daga jiya zuwa yau yadda ta koma abun gwanin tausayi, fuska da idanu a kumbure, ga rama, shigowarsu batayi motsi ba ko ɗaya, dan Babu wanda yayi magana, AKEEL da AQEEL sai da suka matsa kusa da ita sannan suka haɗa baki wajen cewa " Auta ya jikin naki? Ai jin muryar da tayi ne AKEELA yasa ta ɗago da sauri ta ɗora idanuwa akansu da sukayi maganar! kafin kace kwabo kuma ta Fara zabure_zabure da fusge_fusge, sai hankalin AKEEL da AQEEL ya tashi, shi ma Abbu dake gefe Haka, cikin kwantar da Hankali doctor Maryam tace, ku kwantar da Hankalin ku, Yanzu kuje waje, ALLAH yasa ba abunda Muke tunaninsa bane zai faru da ita, dan gaskia a ƙananun shekarunta, yadda Wanda yai mata fyaɗen Yaje MATA Babu tausayi ba bu imani, shine yasa mata tsoro da firgici a zuciyarta, da ta ji muryar maza ko ganin maza zata iya shiga wannan yanayin data shiga yanzu ko fiye da haka ma Yanzu, fatan da zamuyi shine ALLAH yasa Hakan bai shafi ƙwakwalwarta ba,Amma yanzu kafin ta farfaɗo zasuyi MATA gwajin a ƙwakwalwarta su gani, zuciya da ruhin wannan Ahali ba saina faɗe ta ba, kuma kanku fans ya kike ji?


Duk wannan Tashin Hankalin da ake ciki Jimmai tana gurin tayi funfurus,har sannan ko ɗar Akan ƙudirinta na ɓoye wannan gaskia indai ba asirin bane ya tonu!


Daga AQEEL har AKEEL sai a Hankali yanayinsu,saboda zuciyar AQEEL ta samu wutu kawai allurar barci aka Masa, AKEEL da Abbu kuma sa a slow hakam Jimmai .


Abbu ya gargaɗi Jimmai karta baɗawa gidansu abunda ya faru, tabari Asiri ya tonu tukunnah,tayi niyyar faɗa Amma tunda taji likitoci sun ce ba AQEEL bane ya aikata wannan mummunan Aikin ba, da kuma cewa tabbas za'ayi bincike shikenan jikinta yayi Sanyi, dama ba'a gane cewa ba AQEEL bane ya aikata aida tuni tayi tonon silili kowa yaji, a tsinewa AQEEL ɗin, har kawayenta zata faɗawa cewa AQEEL yaiwa AKEELA fyaɗe, Amma yanzu kam itama a cikin Tashin Hankali take, sai kuma bayanin da doctor Maryam tayi, sai addu'a take Akan ALLAH yasa abun ya shafi ƙwakwalwar AKEELA ɗin, asirin ta dana Usman ya rufe, to sannan sai ta fallasa, yanzu haka harda riƙe carbi da addu'a, Akan ALLAH karya bawa AKEELA lafiyar da zatayi bayanin ga wanda yai MATA fyaɗe, dan kuwa bata tunanin wani yaga Usman, idan batayi bayani ba, za'ayi tunanin wani can da Ban ne yashigo gidan ya aikata wannan mummunan Aikin...............


Muje next page😭😭😭


ALLAH sarki AQEEL lalura ta sameka




AKEELA muna fatan abunda Jimmai take fata ALLAH yasa karya tabbata




Jimmai ko Hmmmmm








✍️ Oum ARQAM ce ontop 🥰
2/27/24, 1:30 PM - Rãbi'atou Aminou {Oum ARQAM}: *RASHIN IYAYE*
(Babbar musiba)




Daga *Al 'kalamin✍️ Rabiat Amin (oum Arqam)*


*08128131163*


✍️ Marubuciyar...
*Komai Nisan jifa* 📚
*Hakan ba kuskure bane*📚




*_____________*
MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION📚🖊️ *(M°W°A)*


'Kungiyar d'aya tamkar da dubu masu Nazari da Aiki da ilimi burin 'kungiyar a koda yaushe shine ta fad'akar ta Kuma wa'azantar ta Nishad'antar da masoyanta🤙
*_____________*








*PAGE FIVETY 50*




ina godiya ga masu sharhi musamman Seerat da Oum nawwar, Aishatu Sulaiman, MamaGee,mmn Aslam,Maman eyshat,mummy Waleed, bintufatima,,,,,,,,,, Marasa comment na ina godiya sosai Amma kuma zan dawo kanku irinsu kuna dayawa dai bazan iya jero sunanku gaba daya ba.......................








Tun da akawa Akeela da Aqeel allurar barci, lokacin dama gari ya waye Yanzu haka wajen 11 na safe, dan haka Abbu ya bar Jimmai a asibitin, yanason zuwa gida, zuciyarsa ba bu daɗi so yake yaje gidan ya Fara bincike Yanzu, ko da Akeela ta Tashin, ai shinenan dai, dan haka Akeel yace zaibi Abbu kuma bai Musa ba, Jimmai Zuciyarta kamar zatayi tsalle fa faso jin abunda Abbu yace "zanje wajen Malam sallau nai Masa tambayoyi shin wanene ya shigomin gida! Idan ba haka ba shi kansa sai na hukuntashi,dan kuwa shima yana cikin zargi, cikin in ina Jimmai tace "shikenan to Amma na tambayeshi wai ya zaga bayi! Ko saurarar me take cewa Abbu bai ba Akeel shi ma hakan, dan tashin hankalin ya daɗu,tasan muddin malam sallau yace Usman ya na Gidan shikenan shi za'a zarga ,Amma kuma Allah yasa malam sallau baya gurin shine kawai mafita.


Abun Hawa suka hau zuwa gida, malam sallau yana gurin da ya saba Zama,zuciyarsa sai wasi wasi take!ina masu gidanne yasan dai Alhaji baya gari,Amma yadda aka fita da yaran gidan ba bu lafiya har Yanzu kuma Babu wani mosti, ga Hajiya dai jiya ta dawo zuciya da jiki ba bu daɗi a yanda ya ganta,Duk da dai dama ba wata mu'amala mai kyau take Masa ba,ya haifeta Amma ta dinga daka Masa tsawa kenan, Abinci sai taga damar bashi, Su Akeel ne kawai yakejin daɗin su, ko Mutuniyarsa(Akeela) itace mai zuwa wajensa suna Hira,hakanan in tai girki (Babu abunda bata iya girkawa ba, Jimmai tai mata horon aiki) tana kawo Masa, saƙawa da kwancewar da yakeyi kenan, yaga Alhaji da Akeel sun buɗe gate sun shigo, dan haka da sauri ya ya ƙaraso wajen su "Alhaji andawo kenan? Saukar yaushe? Shi dai Abbu da zuciya ba bu daɗi kawai ɗaga wa Sallau hannu yayi ba bu magana,hakan ne yakuma sawa Sallau shiga cikin ruɗu, Aikuwa dai Babu lafiya kam Tunda ga Akeel da Abbu ai dai ba tare sukai tafiya ba,kuma ma shima ranga_ranga aka fitar dashi,ai kuwa g rama nan yayi,komawa kan Akeel ɗin yayi "ya jikin mutumin? Ina ɗaya Abokin nawa yaji sauƙi Amma shi ma? Ina itama mutuniyar tawa jikin da sauƙi Amma itama? Duk tambayoyin nan ya jerowa Akeel! Da sauƙi baba Amma sunacan Asibitin suna barci Nima farkawa nayi shine na rako Abbu Akeel ya ƙarasa bawa Malam sallau amsa yana gaba zuwa bin Abbu cikin gidan.


Ko da suka shiga gidan daƙar Abbu yai wanka ya canza wasu kayan, zuciya Babu daɗi, Hakama Akeel yayi wanka sannan ya ɗaukar wa Aqeel shima kayan da zai canza,da Duk abunda zasu buƙata, ya haɗasu a trolly guda, hakama Akeela Doctor Maryam ta Faɗi abunda zata buƙata a ɗauko mata, sai sannan Abbu ya zanyo trolly ɗin Akeel Babu ƙarfi,suna fitowa Harabar gidan Malam sallau yana hangowa da sauri yazo ya karɓa, Abbu ya bashi mukullin mota ya buɗe but ya saka ta, "Abbu yacewa Malam sallau Inason magana dakai yanzu! To Alhaji babu damuwa nan akwai rana, dan haka daga Akeel da Abbu da kuma malam sallau suka ƙarasa wajen da yake Zama Akan benci, wajen kuma inuwa ce,dan haka Malam sallau durƙusawa yayi a ƙasa bai hau bencin ba sai da Abbu yai Masa magana, kafin cikin girmamawa ya hau gefe ya fuskanci uban gidan nasa da ɗansa,dan yasan dai abun mai mahimmanci ne yasa hakan sannan kuma zuciyar ɗa da uban Babu daɗi daga ganin yanayinsu.


...Malam sallau nasan kasan abunda ke faruwa da yarana,da fitar dasu da akayi daga gidannan ba bu lafiya abunda yasa hakan shine.......turyan turyan Abbu ya zayyawana malam Sallau abunda ke faruwa bai ƁOYE Masa komai ba,tun kafin Abbu yagama bawa Malam sallau labari jikinsa yafara rawa, na tashin hankali jin abunda ya faru! Ka kwantar da hankalin ka malam ba bu wanda yasan wannan magana kaima abunda yasa nagaya maka saboda Inason ka gayan gaskiya Akan meka sani wanene yashigo mun gida?baka ga wata alama ba game da haka? Harda Kuka malam sallau yayi kafin ya ɗaga kansa domin tunani! Akeel dai yana gefe zuciya ba bu daɗi jin ankuma ɗago Masa da mikin dayake damunsa a zuciya da ganganr jiki!
Abbu ma saurarar malam Sallau wanda ya Fara magana...... Tiryan tiryan ya Fara bawa Abbu labarin Ranar da abun yafaru, yace shidai Babu inda yake zuwa, a gabansa Akeel da Aqeel suka tafi makaranta da safe hakama Akeela, itama Hajiya ta fita bayan fitar yaran, har dawowar Akeela sai da malam Sallau ya faɗa,Anan kuma yace sai kuma Usman daya fito shi ma bai jima ba ya dawo kuma bai kuma fita ba gaskia har Akeela ta dawo ya na Gidan,tabbas yajiyo wata ƙara kamar daga Gidan kuma muryar Akeela ce, dayake yasan akwai Akeela da wasa ita kaɗai sai bai kawo komai a raina ba, Amma bai kawo komai ba, lokacin su Akeel Basu dawo ba haka ma Hajiya, sai dawowar Aqeel cikin ciwo da ko maganar da ya saba yimin bai ba, ina ganin yanayinsa nasan Babu lafiya, Hakama sai dawowar jimmai, bata jima da dawowa ba sosai, sai ga Akeel yadawo har nake tambayar sa yau ɗan uwanka ya rigaka dawowa, shine ma yake cemin ai bashida lafiya ne,nace Masa ALLAH ya sauwaƙe naga alamar sa kuwa dan ko magana bai mun ba a gaggauce ya shige gidan, Akeel yana shiga bai jima da shigowa ba sai ga Usman a gaggauce yazo ya fice, alamu sun nuna kamar baya cikin Hankalinsa, a tsorace yake,ni kuma lokacin ina wajen flowers dan haka bai ganni,Amma nayi mamakin ganinsa a Wannan yanayi, sai kuma zuwan likita da fitowa da yaran a halin rai da rayuwa da akayi dasu.....anan malam Sallau ya sauke ajiyar zuciya!alamun yagama magana! Abbu da Akeel kam kamar zuciya zata faso ƙirji alamu sun nuna kenan Usman ne ya aikata wannan mummunan Aikin ga Akeela?
Tabbas Alhaji wannan yaron shine abun zargi yanzu,ganin a yadda ya futa a gidan, cewar malam sallau yana kallon fuskar Abbu!
Hakane malam shine abun zargi, Mahaifiyarsa tace mun ai tun ranar da na bar gidan nan shima ya tafi gidansu, kaga alamu sun nuna kenan tasan da komai Amma take ɓoyemun, Jimmai ta cuceni ta cuci ƴaƴan ƴar uwarta, kuma tacemun jiya ta tambayeka idan da wanda ya shigo gidannan kace Babu kowa? Lallai kam Hajiya ta iya ƙarya Alhaji ni ko saurarata ma batayi ba, balle taimun magana, aini bata kula ni ko ƙadan malam sallau ya faɗa yana riƙe baki jin sharrin da Jimmai tai Masa. Shi kam Abbu ya kasa magana lallai jimmai kenan da saninta Ɗan ta ya lalata Akeela, in bai mantaba da ma Akeela ta taɓa gaya Masa cewa Usman yana taɓa MATA jiki, Amma kuma sai Jimmai ta gwale ta, shi ma kuma lokacin baisan me ya sa yakasa ɗaukar mataki ba,dana sani Abbu ya shiga, na bawa jimmai yarda da amana ita kuma ta cinye ta, sai sannan kuma yake ganin baƙin Jimmai da tuna Duk wata badaƙala da zalunci da taiwa ƴaƴansa ya shiga dawo Masa a kwanya


Akeel yana zaune Duk tattaunawar da akeyi da Abbu bai magana ba, tsanar Usman ta shiga zuciyarsa yanzu da zai ganshi sai ya kasheshi kuwa, hakama maama Jimmai, dama su sun jima da tsanarta yadda take gana musu azaba! Kawai dai dan Abbu baya ganin laifinta ne, kuma agabansa ma tanai musu,Amma baya magana, in sun gaya Masa yace ai uwarsu ce bayason irin wannan halin! Shiyasa komai ya damalmale ai,yanzu Abbu ba ga shi ya gane gaskia ba.




Nan dai Malam sallau ya kwantar wa Abbu hankali Akan kar ya nuna yasan Usman ne ya aikata wannan mummunan Aikin, yabari Akeela ta farka, aji ta bakinta kuma a gaban jimmai za'ayi komai ai taji,fallsara,in yaso anan Duk wani hukunci da Abbu zai MATA sai yai MATA, kuma Duk motsin jimmai ɗin yasa shi a idonsa, Abbu ya amince yaiwa Malam Sallau godiya sosai kafin jiki Babu ƙwari su shiga mota zasu koma Asibitin'kowanne zuciya Babu daɗi, Akeel ne ma yake dan faɗawa Abbu irin cin kashin da Jimmai tai musu, Abbu dai jinjina kai kawai yakeyi, Amma yakasa magana.






********************


Jimmai tana ganin Abbu ya fice daga asibitin ta kasa zaune ta kasa tsaye, yanzu idan Abbu yagano gaskia wajen Malam Sallau fa? Amma kuma ai Usman yace daya fita malam Sallau baya gurin,yanzu dai matsalar farkawar Akeela ce cikin Hankalinta tashin hankalin ta, dan haka takira Usman ta faɗa Masa, shi kuma yace gashinan zuwa zai san abunda zaiyi da Akeela ɗin,aikuwa cikin muntuna sai gashi yazo asibitin, uwar taje ta tawo dashi, bai tambayi jikin Aqeel ba balle Akeela wanda shine silar komai, doctor da take dubata yace yanason gani, nan kuwa aka nuna Masa office ɗin Doctor Maryam,yana zuwa kuɗaɗe masu maiƙo ya ajiye a gabanta, yace nine naiwa yarinyar nan fyaɗe, inason ki MATA allurar da zata manta komai, koda ta farka Shikenan bazata ce nine ba, wannan kuɗin Kafin al ƙalamine, indai ta farka a Hakan to madallah zan ƙara miki wasu kuɗin,Duk bayanin da Usman yakeyi doctor Maryam tana kinsa, kuma dama a kawai waya a hannunta yana Fara bayani ta shoga record, sai ta badar ta ajiye wayar, a zummar fuskantarsa takeyi,sai da yagama bayani sannan doctor Maryam tace bakada matsala indai akwai kuɗi a hannunka, Amma kai kam meyasa ka aikata wannan ga ƙaramar yarinya? Baka tsoron mahaifiyarka tai fushi dakai in taji Kaine ka aikata, baiwar ALLAH tananan cikin jimami, nan Usman ya kwashe da dariya kafin yace "Doctor ai plan ne tasan komai yanzu haka ma ita ta Kirani, sai da zuciyar Doctor Maryam tai motsi jin abunda ya faɗa, daga ƙarshe dai ya fice daga office, ɗin ran sa fesfes jin Doctor zatai Masa aikin daya sata shikenan komai yazo da sauƙi.ita kuma doctor Maryam ta Adana record ɗin ta,ta dannawa doctor Najeeb Kira kafin kace kwabo yazo office ɗin anan ta gaya Masa Duk ydda sukayi xa Usman, harda share hawaye tayi, shima Doctor ya girgiza jin ashe Duk abunda Jimmai takeyi pretending ne, to Amma waɗannan ƴaƴan me sukai MATA haka, har ɗan ki yayi wannan mummunan Aikin ki rufa Masa Asiri, haka ƴaƴan ƴar uwarki, kuma ƴaƴan mijinki, nan dai suka haka plan Akan kar a nunawa, Abbu yanzu sai ya gama bincikar gidan tukun, kuma ko Akeela ta farka a Hankalinta ta zauna tai mata bayanin komai, ta Zama kamar bata Hankalin na ta, ta yadda za'a kama Usman da Jimmai cikin ruwan Sanyi,daga ƙarshe suka rabu,kowanne jiki Babu ƙwari.


Yaje gurin Jimmai ya faɗa mata yadda sukayi da doctor har dasu murmushi jimmai tayi makira!...... Kiyi komai kifi na ganinka mai jar koma asirinki dana ɗanki ya tonu, Abbu kar yake kallonki


Kafin kice me ya fice da ga Asibitin domin zuwa gida a Fara sana'ar da aka Saba, babansa ba bu lafiya yana asibiti, acan aka kwantar sa, dan haka gidan kullum shine a ciki in dai bai je asibitin ba,sai ƙanwar sa Shukhra in tadawo daga school tazo ta shirya tai asibitin itama.da sauran ƴan aikin gidan.




_____________ jimmai tana ganin Usman ya bar asibitin sai ta shige office ɗin doctor Maryam wai har Yanzu Akeela bata farka bane doctor, An cutarmun ƴa ALLAH ya saka MATA, sai sharar ƙwalla take, Doctor Maryam kam kallon ta kawai takeyi, lallai wannan Babu imani, kalli kamar gaske,nan tai MATA bayanin cewa" ai ki kwantar da Hankalin ki Maama pretending ya ƙare, yanzu Usman ya bar office ɗin nan, zan muku aiki Akeela kam ai ba ita ba farkowa a Hankalinta,sai ga Jimmai da murmushi, ai ban san yaga miki ni na sani bane shiyasa, Amma yanzu kam ai normal ne doctor, komai yazo cikin sauƙi, Nima zan ƙara miki wasu kuɗin,tun shigowar ta itama doctor Maryam ta danna record, tana gama zancen tayi save nasa, ita kuma jimmai ta fice daga office ɗin, ta koma ɗakin da suke zaman jinyar.


Dan haka batasan dawowar su Abbu ba, anan doctor Najeeb yake cewa Abbu Aqeel ya farka kuma Alhamdullillahi yayi wanka ma,yanzu akai masa kayan sawa ya canza, tare suka shoga ɗakin da Akeel, Akeel ɗin ne ya taimakawa Aqeel yasa kaya, nan Akeel ya kwashe Duk yadda sukayi da Baba Sallau ya faɗawa Aqeel ɗin, nan idanun Aqeel sukayi ja ƙarshe yace tabbas Usman zai aikata fiye da Haka Abbu, ya faɗa yana kallon mahaifin nasa da yake zaune a gefensu yana tausaya musu,
Shi ma Aqeel haka yagayawa Abbu cewa ko lokacin da lalurar sa ta tashi Usman yace Masa akwai hanyar warkar da matsalarta shine, ya dinga kallon finafinan batsa, zai samu nustuwa, kuma Abbu Babu kunya ko tsoro a gaban mu yake kunnawa yana kalla, sai dai mubar wajen musamman ni sai yaga ina zaune zai zo ya kunna, saboda yasan matsala ta, Nikam bana Zama, haka ma Akeela sai nawa tana cemin Usman yana kai hannu jikinta, ta mareshi Amma maama Jimmai ta zage ta tace zataiwa ɗan ta Sharri, kaima Abbu haka kace Akeela ɗin ƙarya take,sai Kuka ga Aqeel!


Nan dai Abbu ya lallashin ƴaƴan nasa, da nuna musu kuekurensa,Akan cewa shi zuciya ɗaya ɗaya yake zaune da Jimmai, kuma ma yadda Inna Rabia ta riƙeshi ya zata itama jimmai haka take riƙonsu, shiyasa ma baya yarda da abunda zasu zo Masa da shi, kuma wani abun ma ƙasa magana yake suyi haƙuri, nan dai ya lallashe su Akan komai ai yazo ƙarshe,zuciyar Aqeel kamar zatayi tsalle ta faso ƙirjinsa, idonsa idon Usman sai ya hallakashi hakama, maama Jimmai itama saiya shata MATA layi, Abbu ya ce karsu nuna wata alama agaban Jimmai yadda zatasha jinin jikinta, dan haka sai suka ɗunguma ɗakin da take zaune har Abbu.


Makira harda murna da cewa "ƴaƴana naji daɗin ganinku a haka, ta faɗa da ƙarasawa wajensu da tafa kafaɗar kowanne su, AQEEL kamar zai bankadeta haka yaji Amma kuma ya fuske,hakama Akeel , shikam Abbu zuciya ta yunƙuro Masa ganin jimmai Amma shima sai ya mallaki zuciyar,
Ya kuwa Malam sallau yaga wanda ya shigo gidan? Inji jimmai tana kallon Abbu wanda ya zauna a ɗaya daga cikin kujerun ɗakin, "Abbu yace MATA yace Babu kowa, kamar dai yadda Kika faɗa min, yace ma ai kin tambayeshi! sai ga Jimmai da Ajiyar zuciya a bayyane wanda Akeel da Aqeel da kuma Abbu sai da suka kalleta, lalläi jimmai abun naki yakai limit..


A haka suka zauna a Asibitin, zuciya babu daɗi, Akeela ta farka sai dai ABunda aka guda shine ya faru, dan ƙwaƙwalwar ta kam ta shiga wani yanayin da su doctor Maryam Basu so ba, Babu damar tambayarta abunda ya faru da ita, Amma kuma in ita ALLAH yabata ikon faɗa zata faɗa Amma Hakan ma abune mai wuya, dan ƙwaƙwalwar tayi raunin tuna Abunda ya faru da ita, saboda birgicin da ta shiga cikin lokacin faruwar Abun,Amma ya zasuyi da ikon ALLAH,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login