Showing 18001 words to 21000 words out of 141223 words
Chapter 7 - RASHIN IYAYE Complete Document by Rabi'atu Muhammad Rabi'u Oum ARQAM.txt
shekara tayi da suka bani kud'in hayar na sallamesu Kuma bansa wani ba, maganar Sa'adatu kullum kenan ga kawu isma'il,,,,,,
Wannan rigimar har Saida taje kunnen Hajiya sakinah, aikuwa tayiwa kawu isma'il tatas, acikin fad'an datayi Masa tace" isma'il da bakinka kacemun gidan y'ay'an Sa'adatu daka kar'ba kabata nata kayi Mata ciko, sana'a takeyi dasu Ashe duk qarya kakeyi,Dan haka ka mayar Mata da gidanta in kanason zaman lafiya da kwanciyar hankali, haka Hajiya sakinah taiwa kawu isma'il tatas ya dawo gida ransa a matuqar 'bace, Bai jima da dawowa ba Sa'adatu ta d'ora nata tijarar to dama zuciyarsa a kusa take, a take anan yaiwa Sa'adatu saki d'aya bayan ya gaggaya Mata maganganu, ko ajikin Sa'adatu dam burunta kenan ta gaji da xama da Kawu isma'il ga Hauwa ma ta dameta.......
A gurin Hauwa kamar sallah Wannan rabuwa da akayi tsakanin Sa'adatu da Kawu isma'il, kawu isma'il Kam haka yace a gobe ba jibi ba xai tattara yanasa_yanasa yabarwa Sa'adatu gidanta yakoma nasa,
Allah sarki su Zahra Hadiyyah da Khadija marayun Allah sun girgixa da wannan lamari daya faru, yanzu shikenan gatan da Hauwa ta Samar musu acikin gidanga ya qare wahalarsu xata dawo sabuwa, gashi yanzu Babu namiji kenan acikin gidan, kawu isma'il suke gani suji dad'i shi ya zamar musu kamar Abby, kukan da suke tayi kenan tun Daren da wannan husumar ta faru...
Da safe y'ay'an Hauwa da y'an uwanta sukaje gidan kawu isma'il suka sameshi Babu wani datti sosai sai abunda baza'a rasaba suka gyara gidan, kafin azahar kawu isma'il ya kashe kayansu dake gidan Sa'adatu ko tsinke Bai bari ba,ko sallama Hauwa Bata yiwa Sa'adatu ba balle kawu isma'il su Zahra dai ansha kukn rabuwa, haka kawu isma'il da Hauwa suka har gidan Sa'adatu suka qaleta ita kad'ai sai Zahra Hadiyyah da Khadija da y'ay'anta farouk da hydar da kuma Hafsa wacce lokacin tuni ta yayeta ko nace ma ta zama budurwa,surutu salo_salo har aikenta akeyi maqota....
Tun daga Ranar rayuwar wad'annan marayun ta sauya kawu isma'il akan abunda Sa'adatu tayi Masa kwata_kwata yadaina kulasu sai yaga dama yake zuwa dubasu, abincin da yake ajiye musu sai ya qare Bai kawo wani ba Wai saboda bakin cikin Sa'adatu zataji.............
**************
Bari mu dawo wajen Zakiyyah....daga zuwa maqota ta samu Hira saita mance da cewa ta d'ora ruwan zafi Kuma tabar ABIE akan gadon,, acan gida kuwa ABIE ya farka daga barci yanata wasansa, to saiya fara shure_shure har yazo wajen botikin ruwan zafin ai Yana shurar bokitin aikuwa ya tintsire akan gadon, ita Kuma heater tana jikin socket saita maqale ajikin gadon taci gaba daci abunda ruwan Daya zubo saiya wankewa ABIE qafafuwansa, a take dayaji ruwan zafi ya suma,saboda azaba, ita Kuma katifa ta dinga naso har Saida taso wajen cinyoyin ABIE har gurin gadon bayansa wayyo ABIE ya qone, Saida Zakiyyah tagama iskancin surutunta sannan ta dawo gida, lokacin heater Kuma takama fuskar kadon gurin yayi ba'kikkirin sauwa kad'an wuta takama a gadon gaba d'aya sai hayaqi gashi ita heater d'in tayi jajir abunta, salati ta fara sannan taje ta d'auko wani katako ta bige heater wacce saura kad'an tayi bindiga, sai sannan takai duba ga ABIE har sannan barci yake, a tunanin Zakiyyah fa, ai tanakai hannu kansa taga idonsa a bud'e ya qaqqafe a gigice tasa hannu xata d'aukeshi,Wanda garin hakan ta kwashe Masa qunar gadon bayansa sai ganin fad'owar fata tayi iwu iya karfinta tasa tana na shiga uku na lalace jama'a ku kawomin d'auki, kafin me maqociyarta Maman Waleed itace kawai taji aguje ta shigo gidan, domin taga me yake faruwa, Zakiyyah miqa Mata ABIE tayi tana cewa" duban ABIE Maman Waleed ya qone dayawa wayyo nashiga uku,yanzu mezan cewa mukhtar ya hanani jina heater akan gado Amma banji ba,gashi yanzu yaronsa ya qone,Kuma ya rasu, tunda baya motsi zancen da Zakiyyah takeyi kenan tana kuka, haquri dai Maman Waleed take bawa Zakiyyah sannan tace kawoshi mugani, ki d'auko hijab d'inki, muje mukaishi asibiti, Amma Bari a zuba Masa ruwa Naga suma yayi ai ba mutuwa ba, aikuwa Ana zubawa ABIE ruwan sanyi ya farfad'o Yana sheqa uban ihu, Wanda Bai samu damar yinsa ba sai yanzu, abun tausayi wlh,da sauri Zakiyyah suka tafi asibiti da ABIE Yana tsala iwu, da sukaje asibiti gaba d'aya kafafun ABIE sun sa'bule da bayansa haka likitoci suka sa'bule Kunar aka wanketa da hydrogen, Babu kyan gani, zasu dawo gida likitoci sukace kwanciya xa'a Basu sai ya warke tukunna, Maman Waleed ta Bari a wajen ABIE domin ta Bari wayarta a gida Kuma Bata gayawa Mukhtar halin da ABIE take ciki ba, tana zuwa gida ta tarar gadonta yakama da wuta sosai har zuwa saman d'akin duk Fentin ya qone, aguje ta fito tana neman taimako mutan unguwa aka had'u aka kashe Wannan wuta Allah yaso ita gadon sai bangon d'akinta Daya kone, sai kuka take tana danasanin barinta gidan Bata yarda da maganar mijinta ba gashi tafara gani, takira mukhtar tagaya Masa duk abunda ke faruwa, hankalin mukhtar yayi mugun tashi baro kasuwa yayi sai gida lokacin Zakiyyah tananan Bata koma asibiti ba, dayazo ya sameta yai Mata dukan tsiya ga gaggaya Mata magana Mai ciwo, karshe yace wlh indai wani Abu ya samu yarona ya rasu wlh saikinyi Dana sani a rayuwarki, kalli yadda saboda Baki da hankali da tunani hi yadda kika mayar da gidan, na hanaki jona heater kinqiji gashi sanadin hakan kin qona mun yarona da gidana, na hanaki fita maqota kinqiji,yau dai Zakiyyah Babu rashin kunya sai kuka daban haquri takewa isma'il, a Haka suka koma asibiti mukhtar Saida yayiwa ABIE kuka ganin yadda ya qone sosai, ya Kira Hajiya Jamila ya fad'a Mata abunda yake faruwa, Koda tazo taga abunda ya samu ABIE duk qaunar da takewa Zakiyyah yau Kam ta sire Mata tatas tayi Mata, ta inda take shiga batanan take fita ba,duk Wanda yazo yaga halin da ABIE yake ciki a y'an uwanta Dana mukhtar kowa sai yayi Mata fad'a, itadai Babu bakin magana sai kuka, Anan suke kwana a asibiti domin jinyar ABIE, Zeenah kuwa da akazo da ita daga halin da ABIE yake ciki taita kuka abun tausayi, a wajen Maman Waleed aka barta saboda makarantar ta, kawu isma'il dayaso yaga yadda ABIE yaqone Saida yayiwa Zakiyyah mugun duka a asibitin sannan yaita bawa mukhtar haquri, itama Hajiya sakinah Babu halin zuwa dubiya saboda kafarta Bata fita,ta kirata a waya tayi mata tatas, fad'an tsakanin da Allah a wannan karon tayi Mata,itadai Zakiyyah Babu bakin magana, baaba mutan kaduna itama dai takira Zakiyyah tayi Mata fad'a "wato duk abunda nake Gaya Miki Zakiyyah bakiji ba ko ai shikenan Allah ya kyauta inkin kashe aurenki Babu ruwana nikam, Hidayah da Hunaif suma sun Mata yamai jiki, sunce xasuzo Kano idan anyi wutu,,,,, dayake Allah ya taimaki ABIE Kuma yanashan nono baiyi wata d'aya a asibiti ba ya samu sauqi qunar ta warke sai dai abunda baza'a rasaba,suka dawo gida, Zakiyyah kamar tayi nadama nake gani FANS fa .....
*************
Ba'ayi wata d'aya da yiwa hajiya sakinah 'kafar roba ba itama d'aya kafar ta kamu da ciwo, ciwo kuwa sosai har wari takeyi, ana shirin yankewa Allah yayi ikonsa akan Hajiya sakinah ta amsa Kiran mahaliccinta, Allah sarki rayuwa gashidai itama ta Hajiya sakinah taqare duk wani qale_qalen duniya tabarshi inda Alhaji Ammar ya tafi gashi itama taje, Allah ya yafe was Hajiya sakinah kura_kuranta, Haka aka akayi zaman ta'aziyya aka kammala, shikenan su Hadiyyah Babu uwa da uba yanzu Kuma Babu kaka, wacce duk da hakan Ana raga musu wani Abu saboda idonta, shi kansa kawu isma'il saboda Hajiya sakinah yake musu wani abun badon Allah ba.....
Mutan kaduna Hajiya baaba da Hidayah da Hunaif sunzo gaisuwa Amma kwana d'aya sukayi saboda school suka juya gida, y'ay'a da jikokin Hajiya sakinah da y'an uwa da abokan arqizi sunji mutuwarta to dama Haka rayuwa take kowa na hakane saidai fatan cikawa da Imani............
Muje zuwa FANS a next page zamu dawo dafa labarinmi in Sha Allah, Kuma yanzu wannan labari yafara, na wannan ahali ....
✍️oum Arqam ce
2/7/24, 4:28 PM - Rãbi'atou Aminou {Oum ARQAM}: *RASHIN IYAYE*
(Babbar musiba)
Daga *Al 'kalamin✍️ Rabiat Amin (oum Arqam)*
*08128131163*
✍️ Marubuciyar...
*Komai Nisan jifa* 📚
*Hakan ba kuskure bane*📚
*_____________*
MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION📚🖊️ *(M°W°A)*
'Kungiyar d'aya tamkar da dubu masu Nazari da Aiki da ilimi burin 'kungiyar a koda yaushe shine ta fad'akar ta Kuma wa'azantar ta Nishad'antar da masoyanta🤙
*____________*
*PAGE SEVENTEEN 17*
"Rayuwa fa ta sauyawa marayun Allah fiye da yadda zakuyi tunani, tun barin kawu isma'il cikin gidansu ya banzatar da rayuwarsu ko waiwayarsu bayayi, Dama abincin dayake kawowa Auren Sa'adatu ne sukaci darajarsa tun da Auren ya rasu shikenan kuma, tun bayan ficewar kawu isma'il daga gidan Sa'adatu tasanya cigiyar y'an haya wad'anda zata saka acikin gidanta, saboda ta ragewa kanta wasu abubuwan na rayuwa, Dan kuwa itadai da bakinta bazata wani tambayi isma'il kud'i ba, taqaleshi da haqqinsu akansa, kunji FANS Saida yazo kanta sannan tasan cin hakkin marayu.......
Abubuwa sai gaba sukeyi a Wannan halin Hadiyyah da Hidayah suka kammala secondry school d'insu, yau da dad'i gobe Babu dad'i, tun bayan kammala makarantar su Kawu isma'il Bai leqo gidanba, itakam Hadiyyah tanada burin cigaba da karatunta kamar yadda Zahra taci gaba, yanzu gashinan karatun ta yayi nisa gwanin sha'awa, kud'in mota ta samu har gidan kawu isma'il, Ranar da tasan xata sameshi ta Gaya masa cewar Hadiyyah "munyi candy nida Hidayah kawu, Kuma munason ci gaba kamar yadda Abby yakeson muyi karatu Allah Bai kaishi lokacin ba,kawu isma'il yace naji abunda kika fad'a Ina sane daku ai, Kinga yanzu kasuwancin sai a hankali Kuma karshen shekara yazo duk ban kar'bi bashiba Ina kar'ba zanmuku registration keda Y'ar uwarki, Kinga banjima da yiwa Alhaji hidimar makaranta ba,ga 'batamun Rai da Auntynku tayi(Sa'adatu) shiyasa nafita daga harkarku,Inna Baku Abu kamar har ita nabawa, Hadiyyah kiyi haquri da daina saurarar ku danayi, Sa'adatu ce ta janyo muku Hadiyyah tayi murna sosa da wannan magana ta Kawu isma'il na cigaban karatunsu, Kuma tayi baqin cikin Jin cewa abunda Aunty tayi masa me Yas yadaina kulasu, Banda abun Kawu isma'il su Ina ruwansu,hakadai tayini a gidan Hauwa tana Bata haquri akan kawun nasu dacewa tana masa itama nasiha akan daina kulasu datayi yamance abunda Sa'adatu tayi Masa, Koda yake ai laifinsane, Banda hakan wannan Abu da sukayi tun daga aurenta har musanyan gida ai Bai kamata ba,,, sai yamma tadawo gida abunta, Bata jima da Candy ba kuma tayi saukar Al qur Ani Mai girma, Masha Allah Hadiyyah akwai qoqari sosai ba iya qur Ani Mai girma ta sauke ba hadda wasu littattafan addini d'in ahlari,ishmawi,iziyyah, risala bangaren fiqhu kenan, bangaren hadisai kuwa irinsu bughyatul Muslim,umdatul ahkam, Bukughul maram, riyadus salihin, bangaren sirah ma ba'a bar Hadiyyah a baya ba ta kware a Wannan fannin, indai taji tarihin maaiki ko sahabbansa in Sha Allah ta haddace kenan, Dan d'aya daga cikin baiwar da Allah yaiwa y'an biyu Hadiyyah da Hidayah kenan riqe Abu ba kasafai suke mantuwa ba, tauhid ma ta karanta littattafai da dama, Masha Allah xamuce domin kwakwalwar Hadiyyah da babu Wasa tun daga na addini har na Boko, nasan xasuyi mamakin a Ina kamar Hadiyyah Mai qananun shekaru kamar hakan ta iya wad'annan littattafai saina ce muku, tsarin islamiyyah tasu akwai malami Wanda idan kana da sha'awar ka iya wani littafi Babu takura bayan Wanda ake muku acikin ajinku, xaka iya zuwa da Wanda kakeso malamin yadinga biya maka to anan Hadiyyah tayi wayo data kammala wannan littafi zata saka wani,anan tasan wad'annan littattafai d'in da wasuma wad'anda ban ambataba, sunyi karamar Al qur Ani Mai girma Babu wani shagali Dan ko walima batayi ba irin yadda sauran y'an qjinsu sukayi,lokacin kawu isma'il yayi fushi dasu, kannen ummy d'in su Wanda suke uba d'aya da namiji guda d'aya Wanda suke uwa d'aya uba d'ayan sai Kuma y'an uwa na dangi sune suka had'a Mata daga Mai kawo flour, take away, Leda da sauransu a Haka tayi Y'ar walima Tata Babu yabo Babu fallasa, Ranar sunyi kuka daga Hadiyyah d'in har Zahra yadda suka tuno da ace Abby Yana raye Wannan Rana tazo da anga yadda ake karyar kashe kud'i, akan su, da qaryar y'an uwa sai a d'auka Biki akeyi a gidan nasu ko suna, Amma yanzu Kam mafi yawa dangin ummy ne sukazo sai Zakiyyah mutuniyarku itama tayi hidima ga qanwarta, aidai Kunga anan tayi hankali ko?😅dangin Abby kalilan saboda yanxu qasa ta rufewa Hajiya sakinah ido ragowar kulawar da ake Basu bayan nutsuwar Abby ta qare itama,sun tuna lokacin da Zahra tayi sauka Abby Yana raye sunsha kuka irin hidimar da akayi,gidansu kamar ana Biki ko suna, qaton rago Abby ya yanka a saukar Zahra Amma wannan karon Kam ko kaza ba'a yankawa Hadiyyah ba Yarinya Mai kokari hakan ga littattafan data sauke bayan Al qur Ani Mai girma sukam sunga rayuwa, makarantar bokonsu tare take da islamiyyah a hade Kuma dama kana Candy kake saukar Al qur Ani Mai girma, ka kammala makarantar gaba d'aya kenan, yanzu saidai asanar Mata wata islamiyyah ta unguwa kenan,to Allah Yasa kawu isma'il yayi hakan kar yace bashida kud'i yanzu karshen shekara yazo .....
**************
Hidayah sai godiya Babu abunda xatace da Baaba domin kuwa kulawa daidai gwargwado tana Bata itada Hunaif, tunda sukayi candy bayan Hadiyyah taje gidan kawu isma'il tagaya Mata cewa ai kawu yace Yana sane dasu xai musu registration naciga da karatunsu bada jimawa ba, yanzu kam bashida kud'i, tun daga sannan taci gaba da zuwa ismaliyyah abunta, ba tsarin makarantar su d'aya ba Kano da Kaduna kowanne da irin tsarin pravet school dinsu, tasu Hidayah iya Boko ce, islamiyyah kuma saidai a saka wata daban, itama Kam badai kwakwalwar ba bansan Wanda yafi wani ba,sun rabu da Y'ar uwarta ne bawai rabuwa ta karatu ba duk abunda Hadiyyah take koya shi Hidayah take koya, da d'aya ta saka littafi xata gayawa d'aya itama Kam zata saka sai ayita rige_rigen gamawa, lokacin dama suna tare da juna tare ake musu qarin, bayan komawar Hidayah kaduna anan ma Bata fasa hakan ba, wani malami Mai qoqari ya sauke littafi da dama na addini shi Hidayah ta samu yake mata qari Masha Allah tana iyawa, Koda itama tayi saukar Kare daga dangin Abby Babu Wanda yaje Mata, iy_iyasu dangin ummy na kaduna da qawayenta nacan sune suka tayata murna, Hadiyyah Zahra Khadeeja hydar farouk kawu isma'il ne yakaisu a motarsa,ta Abbynsu Hidayah d'in Bata jima a hannunsa ba yasai wata jibgigeyi wacce tafi Wannan tsada da girma, ko kallon Sa'adatu baiyi ba, itama Hauwa da y'ay'anta biyar sunje Taya Hidayah saukar Al qur Ani Mai girma, Hajiya Zakiyyah a mukhtar yakaita itada Zeenah tsakanin saukar Hadiyyah data Hidayah watanni ne, dai_dai gwargwado itama Hidayah baaba da sauran y'an uwansu sun Mata wahalar saukar saidai ba kamar ace Abby Yana rayeba, maraici Kam y'ay'annan kun ganshi a duniya lallai wad'annan y'an biyu Abin asone, Haka akasha hidima kafin sudawo gida..............
**************
Tun bayan qonewar da ABIE yayi mukhtar ya canzawa Zakiyyah duk Wannan kulawar da uwa uba haqurinsa ya qare,duk Sandra zata Yi wani kuskure zai rufe idonsa yaci Mata mutunci, yace" tunda Kinga Ana rabuwa dake shine iskancinki da hulakancin ki yake yawa ko to kin kaini bango, kinata cin darajar ummy da Abby har suka rasu Baki daina halinki ba, Hajiya Kaaka ma(sakinah) kikecin darajarta itama ta rasu Baki daina halinki ba , to wallahi yanzu Babu darajar Wanda zakici idan kikayimin Yi miki zanyi, tunda Baki da mutunci,tun bayar warkewar ABIE Zakiyyah halinta ya dawo na fita maqota,Amma dai tadaina jona heater akan gadon, Zeenah anata zuwa makaranta abunta, gata itama da wayo da qoqari, Hajiya Jamila tacewa mukhtar gaskia Zakiyyah batada Hankali sosai hakan, sai a qunar ABIE nagani,nikam ko xaka qqra aure ne hakan nake ganin kamar zaisa tayi Hankali, kaga Naga Y'ar wajen kawunka bilkisu ta kammala karatunta na nursing, yarinyace Mai hankali baxaka samu sa'bani da itaba, inaga idan Zakiyyah taga ka Aurota zata dinga koyi da ita Kuma xata rage fita yawo maqota, saidai ta zauna a gida sudinga koqarin faranta maka Dan kowacce mace bataso taga kishiyarta tafi kulawa da mijinta,a zahirin gaskia bilkisu yarinyace Mai hankali da nutsuwa Y'ar wajen qanin Maman mukhtar ce, dama Kuma sun saba dashi akwai mutunci tsakani, tajima tana sonsa, mukhtar baiyi gaddama ba yacewa Hajiya Jamila Mamansa Allah Yasa sanadin Auren Yasa Zakiyyah ta gyara halayenta, Amma shikam halinta ya isheshi, bayan Gama Wannan tattaunawa mukhtar Yana dawowa gida yacewa Zakiyyah xan qara aure, Wanda Zan aura kinma Santa bilkisu ce, banson fitina tsakaninku da ita, Kinga ma ba xaman gidannan Koda yaushe zata dinga yiba tana zuwa hospital ,kiyi haquri Zakiyyah Wannan Auren bayana nuna cewa nadaina sonki bane, Haka mukhtar yadinga gayawa Zakiyyah kalamai na kwantar da hankali Amma bayan Gama maganar da bud'ar bakin Zakiyyah haka tace "Ina ruwana da qara aurenka inma guda uku xaka auro akaina zasu zauna, matsalar kace kaida wata bilkisu bansan taba, qarin aurenka ko d'aya bazai dameniba ka qara aurenka Mana(... Anya kuwa FANS Zakiyyah tanada Hankali, Amma mijinka abin sonka yace zai qara aure ka fad'i Wannan magana,Wai Ina ruwana ka qara aurenka, kodai sai munkai ta asibitin mahaukata?) Lallai Wannan magana da Zakiyyah tayi ta girgixa mukhtar ba kad'an ba, Rashin hankalinta da shasancinta uwa uba ga'buntar maganarta sun bashi haushi duk da bayau ya Saba Jin su ba , Amma nayau daban suke, Zakiyyah Bata sonsa ko kuwa shiyasa Bata nuna kishi akansa ba dayake xai qara aure?.... Mukhtar Yana tambayarku FANS kubashi amsa..............
Koda aka gayawa bilkisu cewa, mukhtar zata aura Babu wani damuwa ta amince, abunka da dangi d'aya Nan danan aka Kai kud'in aure harda saka Rana ma,sai zuwan Biki kawai,,,,, y'an uwan Zakiyyah duk Wanda yaji mukhtar xai qara aure tausaya Mata ake Amma itakam ko ajikinta sai tace Ina ruwana akaina zata zauna tazo ga gidannan ...............
Muje next page In Sha Allah daga shi page din zamu dawo daga ainahin labarinmu, acikinsa zamuji yadda rayuwar Alhaji ta kasance a makaranta,shin yafara karatun ko kuwa? da sauran labarin da bamu kawo ka'barsa ba , kamar yadda yake a page one na farkon labarinmu,idan Baku